TOP HAUSA NOVELS atOptions = { 'key' : '20e08520dad54dbf6d9e963271

MIN QALB 🥰 PAGE 46/47

 Mamuh#*_MQ 46/47_*



_INA MASU SHA'AWA DA QAUNAR KARANTA LITTAFIN DAZAI SANYASU CIKIN NISHADI DA DAWWAMÀMMIYAR NISHADI TO GA DAMA TA SAMU KU NEMI LITTAFIN_ _*WASA DA ZUCIYA*_  _NA ZINNEE SMART  WANDA TSARUWAR RUBUTUNSA DA TSAFTARSA TAREDA DADINSA SAIZA KU KAMU DA QAUNAR RUBUTUNTA A KARATUN LAYIN FARKO DAN SAMUN WANNAN QAYATACCEN LABARIN NATA ME SANYAYA ZUCIYAR ME KARATU

TA WANNAN NUMBERN_

👇👇👇

08080840567





*******

Yau kwananta uku da dawowa batareda ta sanarda kowa dalilin dawowarta ba tadai ce musu hutu tasamu me Dan tsayi shiyasa tazo Dan haka Babu Wanda yasa ko kawo tunanin komai cikin ransa gameda zuwan ko tsakaninta da mijinta sai suka hau shaanin gabansu aka bude majalisar me zaman kanta gidan kawu tasu maman junior Dan har wasu abubuwan gyare gyare suka Fara Shirin Fara harhadawa Amatun na gyaran jiki Dana cikin jiki musamman ma iyami da dama batai gyaran yarta ba lokacin da akai auren Dan haka yanzu zata gyara abarta.


MAHMOUD ZABEERA kuwa tunda yaji daga bakin kawu tana gida taredasu sai hankalinsa yadan kwanta  Amma duk da hakan a matse yake daya dawo Nigeria din tun kafin kowa yasan halinda suke ciki Dan shi kunyama zaiji ace matarsa ta tafiyarta  Yana yawon neman komawarta ko Modibbo saiyace ba MAHMOUD ZABEERA din dasuka sani bane gashi kamar zuwan nasa Kai tsaye bazai samu ba sbd wani urgent work Kuma daya taso Masa Wanda dole saiyaje Dan haka zarah kawai zata taho Nigeria shi zai wuce inda zaije daga Nan daga can zai wuto Nigeria din.


Yau kwananta bakwai da zuwa zaune suke suna fira itada anty salamatu da iyami Dan yau Yan firar tasu duk basanan sunfita anguwa Dan haka yau gidan tsit ba hayaniya sai su kadai USI ma yadawo asibiti da wuri yau Yana dakinsa baccin gajiya yakeyi sbd a asibitin ya kwana yau.


Sallamar umme sukaji Muhammad na bayanta tafe cikin gudu hannunsa riqeda Ben10 soldier dinsa dayafi so cikin kayan wasansa Yana Kiran sunan anty salamatu yana shigowa yaga mummynsa a zaune da gudu yayi kanta Yana cewa''


Mumma mumma.


Rungumesa tayi tana cewa''


My Muhammad has become a superman ji wannan gudu fuiiiiii.


Dariya yayi Yana Jin dadin Superman data kirasa Yana sake hayewa jikinta yace"


Mumma where is my Daddy?

Inason ganinsa i miss him""yafada Yana leqa bayanta da kallon koina Yana son ganin baban nasa.


Murmushi tayi tana zaunar dashi gefenta tace"


Muhammad look"tafada tana nuna Masa su iyami tace"


Baka gaida grandma ba da antyty dinka"cewar anty salamatu.


Gurin iyami ya nufa Yana miqa Mata biscuits din daya Ciro aljihunsa wanda yakawo Mata yace"


Kaka iyami ga biscuits da umme ta siyomin ki ajewa kawu.


Dariya dmtayi tana jawosa jikinta suna sake gaisawa da umme data zauna tana amsa gaisuwar Amatu data salamatu tana cewa''


Amatu wato muda muka matsu dason ganinki gamu munzo Muhammad ya isheni Wai babansa yakeson akaisa gurinsa shine nace Bari muzo dai idan yaganki qila ya rage fitinar neman uban.

Murmushi kawai tayi batareda tace komaiba saita kamo wani zancen suka fada wani zancen Bayan anty salamatu takawowa ummen ruwa da brabiskon dasukai Wanda ummen na sonsa sosai musamman yanda iyami keyinsa yayi wani irin laushi.


Sai dare umme ta tafi tabar Muhammad dayace gurin mamansa zai zauna.

Washe gari kwananta Tara kenan da zuwa suka shirya itada anty salamatu suka fita da motar USI daya bar musu Wanda duk yanda taso taja motar kasawa tayi sbd yanda ta koya tuqi a Greece daban da tuqin nan din Dan haka Dole tabar anty salamatu da USI ya koyawa tuqi sbd fita da iyami ko lalurar gida idan antashi Dan yakan bar musu mota ya tafi asibiti musamman idan acan zai kwana.


Family house dinsu maman basiru sukaje barkar haihuwar da qanwar maman basirun tayi shiyasama kwana biyu basa zaman fira sun Dan jima acan kafin suka baro suka nufi kasuwa siyayyar takalman iyami data Basu saqon anaso sun qare daga Nan gurin bada dinki suka Amatu tabada dinkuna sai yamma sosai suka dawo gida Dan haka suna komawa sallah kawai sukai sukaci abinci Amatu ta kwanta Dan matuqar gajiye take.


Washe gari tana buqatan gyara kanta daya Fara damunta suka shirya zuwa blue fox itada anty salamatu Dan haka guraren 12 suke fice bayan sunfara biyawa sun ajiye Muhammad a zabeera taje ta gaidasu Andi dasukai mamakin Jin zato hutu Ashe Amma sanin ba ayi maganar tarewarta ba yasa suka barta takomawarta gidansu inda ta sauka saidai Kam tunda har tazo Dole ayi maganar tarewarta ta tare sbd daga yanzu idan tazo ta sauka a gidan mijinta dama tuntuni anyi gyaran sashen marigayi Dr khalil  an rushe komai ansauya tsarin gurin gababaki daya Kuma sai akai qatuwar katanga aka zagayayesu cikin qaramin gate me kyau tareda sashen zarah sai harabarsu ta zama daya me girman sosai.


Daga zabeera blue fox din suka wuce suna Isa Allah ya hadata da manager kuwa ai Nan ya tsaya kallonta cikin girmamawa da sauri ya qaraso Yana cewa''


Ran Amaryar zabeera ya dade yau an tuna baya kenan.


Dariya taso Yi ta gimtse tana kallon gurin da aka sauyawa tsari me kyau fiyeda da ga girma da fadada gurin da akayi ya sauya matuqar Dan yanzu ma tun a gate Saida tickets ake shigowa ga uban securities tana jinjina kai tace"


Manager komai na blue Fox yasamu sauyi Banda Kai kana Nan yanda kake  har halayen.


Dariya yayi Yana cewa''


Allah ya taimaki Amatun zabeera ai mu Babu wani sauyi daya fiyemin blue fox musamman yanzu datake zaman mijinki Dan kuwa ya jima ya siyeta gabaki dayanta Kuma nasan idan Allah ya yadda sbd ke ne tunda kowa yasan har yanzu kina qaunar blue fox dinnan shine yayi Mana dukkanin wannan gyare gyaren Takoma kamar turai yanzu hadda sashen geaming da sports munada aciki haka Kuma komai namu anqara fadadashi daga restaurant din har spa din dasauransu.


Girgiza Kai tayi tana kallonsa tace"


Ga antyna dai ku gaisa sbd Naga ko ganinta bakayiba sbd dadin labari.

Da sauri ya kalli anty salamatu dake sanye cikin riga da skirt na red embellished atampa da gyalenta red shima sai tsawonta me tsari ya fito cikin dinkin riga da skirt din ya washe dukkanin haqoransa da fara'a yace"


Sannu da zuwa blue fox Ina Miki barka da zuwa sirikar me gidanmu.


You'll never change manager" Amatu tafada tana yin gaba Yana biye dasu Yana musu bayanin yanda tsare tsaren gurin yake ayanzu da kansa yaje jiki na mazari ya karbo musu tickets na komai da zasuyi yakawo musu a kebantaccen gurin da sai oga zabeera din yazo da kansa shikadai ke zama acan suka Fara cin snacks kafin suka nufi spa Dan komaima yimata zaayi.

Da gyaran Kai aka Fara musu kafin da aka gama aka koma gyaran qafafuwa daganan aka koma gyaran jiki.


Basu baro blue fox ba sai magrib suna isowa gida itace tafara fitowa tana juyowa sai Jin Muhammad tayi a jikinta ya Fado Yana mata "oyoyo mummah"


Da mamaki take kallonsa suka nufo cikin gida tana cewa''


Waye ya dawo da Kai?bakace Kuma gurin umme kakeso ba sbd ka ringa wahalarda mutane zaka ringa saka masu kaika da dawo dakai yawo.


Daddy yazo Dani...


Kallonsa tayi da sauri tana kallon bakinsa daya furta dadyn tace"


Dadynka Kuma?


Eh dady ne yadawo yau yazo Dani yace muzo mutafi da mummah.


Kallon inda yake kalla tayi numfashinta nason sauya fita ta hanyar qara sauri tana dannewa ta kalli gurin tagansa zaune Kan kujerun harabar gidan tareda kawu 

Kawu sai zuba yake Masa Amma shi idanuwansa na kanta ya zuba Mata su cikin yanayi da kasalar da ganinta ya sakar Masa idanuwansa na bayyanarwa sbd wani lumshewa dasukeson Yi Amma Basu lumshe din ba.


Bugawa ZUCIYARTA ke Naman Yi sbd wani irin kyau da sheqi tareda qwarjinin da Allah ya horewa wannan bawa nasa MAHMOUD DAHEER ZABEERA ta dauke idonta ahankali tareda juyawa ta shige ciki batareda tabari kawu ya gansu ba Dan yanzu zai Fara kawo Mata zantukan tazo ga mijinta.


Suna shiga daki tashige ta tube saidatai wanka kafin tayi sallar magrib da yanzu aka gama ta sanya doguwar riga mara nauyi me kamar boubou ta fito tana tambayar abinci ta nufi kicin ta dauko zobon da iyami keyi tana sawa a fridge sbd baqi dakuma kawu dakeson ruwa me kala ta fito tana Shan zobon saiga USI yashigo yace taje palon kawu yana namanta.


Can ya wuce Kai tsaye sbd ta daina Jin hayaniyar Muhammad tasan sun tafi ne tunda dare yafara Yi takumasan babansa bai Bari ana fitar dare dashi.

Tana shiga da Muhammad din tafara cin karo kwance yayi bacci jikin kawu  tana ganin hakan saita daure fuskarta taqi kallon dayan gefen Dan taji ajikinta MD ne agurin.


Kallon kawu tayi muryarta na daidaituwa cikin nutsuwa tace"


Kawu likita yace kana kirana.


Eh mijinki ne gashinan zaune yazo tun dazu bakwanan yanata zaman jira.

Miqewa kawun yayi daukeda Muhammad ya fice yakaiwa iyami dakinta ya fita zuwa gurin abokanan hirarsu ta dare a qofar masallaci.


Kawun na fita ta nufi qofar fita itama batareda ta kalli inda yake ba ko qofar Bata qarasa isaba taji yariqo hannunta tareda dawo da ita baya har bayanta na gugar qirjinsa ya bude baki da muryarsa me taushi yace"


Why?

Meyasa Zaki taho a irin yanayin da kike ciki Kuma ki dauki fushi Bayan nine yakamata na dauki fushin tunda kin baro batareda sanina ba.


Juyowa tayi ta kallesa ahankali kafin ta zame hannuwansa cikin nata daya riqe ta wuce tabarshi tsaye Yana kallonta.


Qofar data fice yabi da kallo Yana Dan rintse idonsa ya sauke numfashi Yana komawa zaune dama yasan Amatu bazata sauko acikin sauqi ba.

Hakanan ya fito ya wuce batareda kowama yasaniba Yana Isa gida ko abincin dare daqyar yaci sbd kada Zarah daya lura kamar itama tafara iya Magana akan Abu tayi Magana bazai iya daukar wani stress Bayan Wanda yake daukaba yanzu aikin dayayi a Sudan duk tsawon kwanakin baiwani bada hankali yayi Abinda yakaisa ba sbd har lokacin komai Kiran dazaiyiwa Amatu baya samunta,

Wanka yayi ya kwanta kawai dama akwai gajiya a taredashi sbd yau din ya dawo.


Washe gari ma taso fita Amma iyami ta hanata sbd cewar mijinta na gari ba Maganar yawo yanzu Dan haka Dole ta zauna gida tana kallo su Anty salamatu hadda iyamin suka tafi gurin sunan qanwar maman basiru suka barta.


Tana zaune Palo tana kallo sama sama bayan la'asar har bacci ya Dan Fara daukarta taji qamshin imperial majesty na shiga hancinta kobata juyoba tasan shine zai shigo palon ta tashi zata shige daki tun bai qarasa shigowaba tana kaiwa tsakiyar palon Yana shigowa da sallamar cikin sauti me taushi ya tsaya gabanta Yana kallon fuskarta dake daure tam sai yaji jikinsa yayi sanyi ya rasa kalmar furtawa ya riqo hannunta cikin nasa idanuwansa na kanta a gajiye da wannan fitinar yace"


Wannan shirun naki is killing me 

Kiyi mgn Koda zakiyi fada ne I'm ready Zan dauka infact I won't say a word indai har Zaki sauko.


Bata kallesaba ta kwace hannunta a hankali kafin tace"


Zan kwanta Kuma bakowa a gidan nikadai ce.


Tunda yadawo gida zarah ta rasa gane kansa abun duniya ya isheta ga cikinta nada damuwa an hanata sakawa Rai damuwa Amma wlh bazata iya rashin damuwarba sbd Abinda take gani shi ake Kira da asalin damuwar,

Yau satinsa guda cif da dawowa Amma yarasa gane Kan Amatun tun abin na iya tsakaninsu har gidansu Amatun dai kowa yasan Abinda yake faruwa kawu dayaji hadda 6arin ciki tayi sai baiji dadin yanda MAHMOUD din yabari tadawo ba ita kadai cikin yanayi irin wannan Amma zamansa uba saiya ringa bin Amatun da rarrashi har gwara iyami na Dan Mata zafi wani lokacin Amma duk da hakan shidai MAHMOUD baiga sauqi ba saima yakoma ya hurawa su Andi wutar batun tarewar Amatun Wanda yabar Andi cikin mamakinsa dakuma tunanin shima wato lokacin gyaransa yayi a hannun Amatu sai suka aikawa kawu yace zai Basu ranar tarewa idan yayi mgn da Amatu.

Jin hakan sai tension dinsa yafara bayyana ga aikinsa Dan duk wasu ayyukansa da meetings dinsa na watan kusan duka yayi postponing dinsu sbd kwanakin Yana samun matasalar saurare a bangaren aikin shiyasa ya tsayar.


Batareda tsayawa neman bayanin kowaba yasa aka Zo aka zubawa sashen sabbin royal furnitures masu kyau da tsari saidai har lokacin Amatu takasa tsayawa dashi ko Magana suyi tun Yana daukar Muhammad Yana zuwa dashi harya Bari kada ya kwashi sanyi da yawa 


Zaune yake Yana duba wayarsa hankalinsa gabaki daya baya Kan wayar Yana wani gurin..

Fitowa tayi daga dakinta cikin Dan adonta na riga da skirt na atampar data Dan fitar da qaramin cikinta daya Fara Dan turowa ta kallesa tana nazarinsa tsawon lokaci kafin ta sauke numfashi ta nufi kicin ta bude fridge ta dauko Masa lemondrink da cup ta Dora Kan tray ta dawo takawo gabansa ta ajiye tareda zama gefensa ahankali tana budewa ta zuba Masa ta miqa Masa ahankali tareda Kiran sunansa cikin sanyin murya.


Waiwayo yayi ya kalleta tareda kallon kwalliyar jikinta datai Masa ya karbi drink din Yana qaqalo sahirtaccen murmushi ahankali yace"


Thank you and you look great.


Kurbawa yayi ya ajiye Yana kashe wayarsa gabaki daya ya ajiye ya qara daukar drink din yanasha harya shanye ya ajiye cup din yasake Dan juyowa ya kalleta Yakuma cewa''


Thank you"Yana maida kallonsa kan TV Yana kallon news.


Jinjina Masa Kai tayi tareda fuskantarsa gabaki tana jinjina qarfin Rai irin na MAHMOUD din dayake dannewa da boyewar abindake ransa kamar yanda ya Saba boye al'amura saidai yanxu wannan damuwar ta dabance Dan itadake taredashi tana iya hango damuwa ataredashi.


Numfashi takuma saukewa akaro na biyu kafin ta Kai hannunta ta Dora Kan nasa ya juyo ya kalleta da idanuwansa dasukai laushi sbd rashin isashen bacci ta bude baki ahankali tace"


I'm really sorry MD sbd tun farko daban Bari ta tahoba da duk haka bai faruba,

Laifina ne na yarda Kuma Inshallah idan munhadu Zan fahimtar da ita hakan but for now idan akwai ta inda Zan taimakawa alamarin let me know please..


Shiru yayi idanuwansa a rufe na mintuna kafin ya budesu ahankali ya juyo ya kalleta na mintuna Yana NAZARIN yanayinta ya bude baki yace"


She respects you fiyeda komai sbd tanajin nauyinki fiyeda komai because of the old relationship that you two shared Wanda deep down haryanxu tana Miki kallon yayarta.


Kallonsa take da dukkanin girman idanuwanta bugun zuciyarta na sauyawa sbd Fara tammahar inda zancensa keson dosa muryarta na rawa tace"


To ta Yaya hakan zai.....


Ki tayani fahimtar da ita Abinda nakeson tagane please.


Saura qiris zuciyarta ta buga daga cikin qirjinta ta da Abinda ya fada din,

Wani dishi dishi take neman Fara gani sbd bugawar da zuciyarta keyi da sauri,

Wani irin zafi yafara taso Mata tun daga cikin qasan zuciyarta Yana mamaye zuciyar Tata take taji tsanarsa nason darsuwa a zuciyarta akaro na farko a rayuwarta Amma ta yakice hakan tareda kallonsa cikin Ido ta bude baki Kai tsaye tace"


For the first time yau MAHMOUD ZABEERA ka farkar Dani daga wani babban kuskuren danake ciki,

Miqewa tsaye tayi ta kallesa cikin muryar dake bayyanarda jarumtarta tace"


Zuciya ce a kirqina ba dutse ba dan haka inaga ko dan Abinda yake cikina na cancanci wata karramawar Amma duk da hakan tunda ka buqata Zanyi mgn da ita Amma bisaga sharadin idan Bata dawoba Nima nagama zaman gadin gangar jikinka sbd inason ayau kasan sonka zuciyata ya Kama bawai zuciyar ya cinye ba.


Zaiyi mgn tabar gurin batareda ta tsaya sauraronsa ba ta nufi dakinta ta shige tareda rufowa ta Isa bakin gado ta zauna tana son fashewa da kuka Amma Abinda takeji yafi qarfin kukan  sai kawai ta miqe ta zari doguwar hijab da keys din motarta ta fice tanajin idan Bata bar gidanba komai zai iya faruwa.


Tana Isa gidansu Kai tsaye dakin ummanta ta wuce ta zube Kan gado sai alokacin wani gigitaccen kuka ya 6arke Mata me ciwo.


Umman data fito toilet taganta tana kukan sai kawai ta barta tayi me isarta kafin tabar gefenta Takoma Kan kujerar dakin ta zauna tana kallonta tace"


Wannan kukan dakikeyi ki Dena zarah sbd Abinda yake taredake Wanda baya buqatan irin wannan tashin hankalin tunda kinfi kowa sanin yanda cikin baida qwari.


Tashi zaune tayi tana share hawayenta ta zare hijabin jikinta ta dago ta kalli umman dake Mata kallon jiran jin dalilin wannan kukan.


Bude baki tayi ta korowa umman bayanin komai zata Dora da wata maganar umman ta daga Mata hannu cikin takaicin ZARAn da cewa''


Zarah kinada matsala babba idan har Baki dawo hayyacinki ba,

Shi so da zaman aure duk ba hauka bane,

Ta Yaya Zaki maida kanki doluwar qarshe akan gudun zuciyar namiji,

Shin meye amfanin rayuwar aurenda babu fahimtar tunani ko Babu so ana zaman aure me Dadi idan kowa yasan mutunci da darajar kansa data abokin zamansa,

Matsalarki zarah itace kin kasa bawa kanki darajarda shima abokin zaman naki zai baki,

MAHMOUD ya zaune dake cikin girmamawa da mutuntawa tsawon shekaru masu tsayi batareda ya taba complain ko nuna muzantawa garekiba duk da kece Kika kasa kawo sauyi da shaquwa acikin auren naku sbd kece mace kinada hanyoyi da damarmaki da Zaki sauya MAHMOUD tun  kafin wata tashigo rayuwarku Amma Kika kasa yanzu abin yazo a biyu na farko koki yarda ko karki yarda MAHMOUD son mararsa AMATULLAH yake so me tsanani musamman tunda yanzu gatanan tana bude Masa hanyoyin sanin zamantakewar aure sannan akwai fadanda ko sunyi abunsu na tsakanin ma'aurata ba huruminkineba Shiga gashinan yanzu kin qare zuwa bikon kishiya Wanda idan dai baki koyi sanin darajar kankiba data Kama kanki akan Abinda Babu ruwanki har ruwan wanka kina Kan hanyar daukarwa kishiya Dan haka kada kiga laifin mijinki laifinkine

Da Zaki farka ki nuna Masa kinsan darajar kanki data aurenki da zamanki matarsa tsaf zakiga yazo yazauna daku anbawa kowacce haqqinta anzauna lafiya.

Bance kinyi baya ba sbd wannan halindakike ciki Allah na gani Kuma Yana sane wlh zakiga irin tanadin sakamon da Kika samu agaba Amma gskia zarah ki farka Babu Wanda zai qwaceki a cikin wannan yanayin sai kanki da kanki Zaki qwaci kanki ki tashi kije bikon naki dakika daure kanki da zakiyi Danni bana cikin wannan mutuwar zuciyar.


Mutuwa jikinta yayi ta miqe ta wanko fuskarta tadawo ta dauki keys ta fice batace qala ba ta shiga mota ta nufi gidansu Amatu.

Tana Isa tayi parking ta fito tana daidaita kanta da nutsuwarta ta nufi ciki ta Isa qofar Palo tashiga da sallama 

Su iyami dake zaune palon duk suka juyo suna kallonta

Saiga Amatu ta fito daga kicin daukeda indomie data dafo tana ganinta itama ta tsaya cak tana kallonta.


Anty salamatu ce tayi saurin miqewa tana cewa''


Zarah kece da yamman Nan sannu da zuwa.

Iyami ma cewa take"

Qaraso ki zauna zarah kinji sannu da zuwa fitar yamma.


Murmushin qarfin hali tasaki tana qarasowa ta zauna tana kallon Amatu dake kallonta tana Mata sannu da zuwa itama.


Murmushi tasaki tana cewa''


Amatu idonki kenan.


Indomin ta ajiye tana murmushi tace"


Anty zarah kedai karkice komai nakira wayarki Allah harso biyu bana samu.


Zobo anty salamatu takawo Mata suna qara gaisawa zarah tace"


Iyami wannan 'yar Taki zaneta zamu farayi sbd tashin jinta yanzu kiduba kiga yanda takasa aje fushin datakeyi damu shiyasa nazo da kaina nabata hkr tunda taqi sauraron mijinta to gani nazo Dan yau bazan fita gidan nanba saida ita.


Kallonta Amatu tayi cikeda mamaki tace"


Anty zarah.


Tsit antyn tayi sbd tsawon lokaci sai yau takirata anty zarah complete.


Juyowa tayi ta kalleta zuciyarta na rauni da damuwar datake ciki Amma tana daurewa kada ta gasa ta bude baki zatayi mgn sukaji sallamarsa dukkaninsu suka juya.


Iyami na ganinsa gaisawa kawai sukayi ta miqe ta bar gurin hakama anty salamatu.

Kallonsa zarah tayi harya qaraso gabanta baice komaiba ya kamata hannunta ya miqar da ita yace"


Let's go.


Kallonsa tayi da idanuwanta dake son cikowa ya sakar Mata murmushin dake nuna banhaqurinsa Yana girgiza Mata Kai yace"


Ita tariga ta taho gidansu ke dakike taredani bazan Bari ki barni ba,

Bazaki bawa kowa hkr ba sbd selfishness ba.


Wani irin sanyin Dadine yake kwaranya cikin zuciyarta haryana bayyanuwa Kan fuskarta tasaki wani yalwataccen murmushi tana girgiza Kai tace tunda nazo zankoma da ita idan har da akwai mutunci da ganin girma a tsakaninmu.


Gyaran muryar kawu sukaji daga bayansu suka juya Banda Amatu da abun duniya ke neman shawa Kai.

Palonsa suka nufa aka zazzauna Nan ya rufe Ido duk su dukan yayi musu fada tareda sanarwa da kowa laifinsa Kuma ya buga rantsuwar yau Amatun a gidanta zata kwana da daddare iyami da salamatu zasu kawota.


Godiyar da MAHMOUD din yaringa yiwa kawun yasa su iyami Jin wani iri sbd zarah din.

Bayan tafiyarsu Amatu Tasha kuka harta gaji iyami ta kalleta tana cewa''


Amatu kiji tsoron Allah kobaki zauna da mijinki lfy Dan Allah ba Kya zauna dashi lafiya kodan baiwar Allan Nan tasamu nutsuwa gidan aurenta,

Karki manta shifa aure hkr ne cikinsa kusan gabaki daya,

Bakiyi rayuwar zaman aureba da Khalil ya rasu sai yanxune zakiyi rayuwa Kuma wlh duk Kika dagawa MAHMOUD hankali har hakan yasa aka Shiga haqqin zarah Allah bazai barki ba,

Matar Nan koba komai wlh duk Wanda yasameta abokiyar zama ya huta a rayuwa sbd matardake danne kishin Mijinta Dan kawai a zauna lfy ai itace abarso da tattali Banda shi so yake wani dabam,

Dan haka Amatu Dan Allah ki dauke Ido ki koyi hakuri Kuma ki zauna da Matarnan tsakani da Allah kamar yanda kuke ada ni wlh tausayi take bani Kuma Ina tsananin ganin girmanta.

Itadai Amatun Banda hawaye Babu Abinda takeyi sbd hukuncin da kawu ya yanke akanta ta wani bangaren Kuma yanzunema zasu Fara tsara zaman auren dakuma kishin tunda yanxune za'a hadesu araba musu kwanan aure da komaima.


Daki Takoma anty salamatu na hada Mata sauran kayan Sha da iyamin ke hada Mata kullum tun ranarda aka Fara maganar tarewarta.


Har dare Basu Gama Shiri ba sai Bayan ishai tayi wanka ta shirya cikin wata farar lafaya da wani lace me taushi aka bita da turaruka masu sanyin qamshi suka fito bayan kawu yaqara tashi nasihar.

Andi ne dakansa ya aiko drivern dayazo daukarsu suka nufo zabeera inda ake jiran isowarsu.

##Mamuh#*_MQ 48_*

Post a Comment

0 Comments