TOP HAUSA NOVELS atOptions = { 'key' : '20e08520dad54dbf6d9e963271

SAKAYYAH page 65

 Ajere-Ajere motocinsu suka fara shiga harabar gidan Innayi. Moddibo kuwa sassayan numfashi ya fesar a hankali ransa cike da mamakin, shin meyesa Abban Jameel yace su sauƙa anan duk da yasan cewa ba wasu wadatattun ɗakuna bane a gidan, kasancewar daga ɗakin Innayi sai Side ɗin sa dake da 2 bedroom sai single room a bakin ƙofar falon, yace wa Abba su sauƙa a hotel daya musu booking Amma yace a'a yaƙi masa musu ne, saboda bai san mai ya shirya ba duk da yafi tunanin Abba yace hakane ko sai sunci abinci kafin su tafi Masauƙinsu.


Akuma dai-dai lokacin motocinsu sukayi Parking a farfajiyar gidan.

Daga can waje kuma cikin sassarfa Haiydar da Bashir suka nufo gidan wanda har sun dauki hanyar komawa gida kasancewar sun jira su basu zoba sai kuma suka hango motocin su.


Acan harabar cikin gida kuwa cike da matsanancin mamaki da al'ajabi Moddibo ke bin baki ɗaya ilahirin gidan da kallo wanda aka tsara shi yayi masifar kyau wasu dan ƙara dan ƙaran Side ne akayi su guda biyu wa ɗan da kusan komai nasu irin nasa ne sai dai basu da wadatan flowers kamar nashi cikin fesar da numfashi da mamakin dake kwance saman fuskarsa ya ziro ƙafarsa na dama kafin ahankali ya gama fito da gangar jikinsa daga motar, hannunsa na riƙe cikin na Khausar still Idanunsa na bin harabar gidan da kallo.

Akuma dai-dai lokacin Idanunsa suka sauƙa kan Abban Jameel, Lamiɗo da Malam Ahmad suna sauƙa daga kan barandar ɗaya daga cikin Sabon Side biyu da aka gina still da mamaki ya maida kallonsa kan Innayi data fito daga Motar da suke.

Murmushi Innayi tayi ganin kallon mamakin da yake bin gidan dashi kana tace.

“Bismillah ku shiga side ɗinka”.

Kallon yaushe akayi wannan ginin yayi mata, fahimtar kallon da yake mata yasa ta jinjina masa kai tare da cewa.

“Tun kwanaki ai aka fara ginin saboda sanin cewa zamu zo Auren su Jameel, kana lokaci zuwa lokaci zamu buƙaci zuwa nan tunda ni da kai dai ba zamu manta garin Membila ba”.

Sanyayyar ajiyar zuciya ya sauƙe kana yayi murmushin gefen baki sosai yaji daɗin hakan saboda bawai ya tsani garin Membila bane saboda ya samu nasa garin, kawai dai Membila ta fita a ransa ne saboda rasa amininsa, Amman duk da haka yasan gari Membila garine wanda yake da tarihi arayuwarsa yana jin Membila na cikin garin da yake tamkar tsagin jikinsa, ya sani bazai manta garin arayuwarsa ba, ko ina yaje a duniya watara zata faɗo masa arai kuma dole zai buƙaci jin yana son zuwa cikin garin.


Anutse Didi ta fito kana Lalla Khadijah, Lalla Hafsat, Sai Rahama tana fita ta nufi gefen Khausar fuskarta ɗauke da murmushi tace.

“Woww Lalla Khausar haka garinku yake daɗi?,Masha Allah kina jin weather Mai daɗi haka Masha Allah i like it”.

Murmushi Khausar tayi kana ta gyaɗa mata kai da faɗin.

“Aikuwa zaki sha sanyi”.

Idanu Rahama ta lumshe sai kuma ta buɗe tace.

“Aikam akwai sanyi kam, duk da muma A Morocco ana mana sanyi but time to time ne amma bai kai wannan ba sanyin nan daban ne”.

Ta ƙarashe maganar tana ƙanƙame jikinta waje ɗaya jin yanda sanyi ke ratsata.


Kallon Khausar dake ɗan lumshe idanu Didi tayi kana ta maida kallonta kan Moddibo cike da kulawa tace.

“Aleeyu ku shiga ciki yarinyar ta gaji da zaman motar nan ”.

Kai ta gyaɗa Tare da cewa.

“Toh”.

Sai kuma ya damƙe hannun Khausar cikin nasa tare da ɗan janyota jikinsa suka nufi Side ɗin sa.


Gaba Innayi tayi tana mai cewa.

“Didi, Lalla Khadijah Lalla Hafsat Bismillah”.

Kai suka gyaɗa tare da bin bayanta suka nufi ɗaya daga cikin Side ɗin.

Akuma dai-dai lokacin Ummi ta fito daga Side ɗin fuskarta ɗauke da farin ciki da mamakin ganinsu tace.

“Masha Allah sannunku da zuwa, sai yanzu kuka iso, da naji ku shiru-shiru har nake cewa barin tafi wata ƙil zaku kai dare”.

Ta ida maganar tare da rungumar Didi itama Didi rungumeta tayi tana cewa.

“Masha Allah fatan mun sameku lafiya”.

Kai Ummi ta gyaɗa tare da riƙo hannun Lalla Hafsat tace.

“Alhamdullah.  Bismillah mu shiga daga ciki”.

Cike da farin ciki suka bi bayanta...


Abban Jameel kuwa shi yayi wa Abualeey, Waziri, Galadima, Baffan Zakariyya, Dr Jameel Zakariyya jagora zuwa Side ɗin da suka fito ko wanne yana ɗauke da 3bedroom manya,-manya wanda aka shirya su da kaya na alfarma da kawa ɗaya daga cikin ɗakunan Dr Jameel, Zakariyya da Ibraahim ne aciki.

Sai kuma na biyun Abualeey ne da Waziri, Sai kuma Baffan Zakariyya, Galadima.

Acan Side ɗin su Ummi kuwa Didi da Rahama ta nunawa ɗakin farko inda zasu zauna kana bedroom ɗin gaba ta kai Lalla Khadijah, Lalla Hafsat,da Niyna.

Sai da ko wannensu yayi wanka kana suka canza kaya zuwa mai ɗan nauyi amma ba can ba saboda yanayin sanyin garin kafin suka gabatar da sallolin suka ɗan huta tare da taɓa hira sai kuma suka fito Falo Ummi da kanta tayi musu iso zuwa dining.

 Didi na murmushi ta shaƙi sanyayyar Iskar garin da kuma wanda bishiyoyi da flowers ɗin gidan ke kaɗawa tace.

“Kai Alhamdulillah Masha Allah weather garin nan akwai daɗi ”.

Murmushi Ummi tayi tare da cewa.

“Aikam sai dai akwai sanyi”.

Sai kuma tayi serving ɗin su da lifiyayyan abinci iri iri na alfarma da suka musu.

Akuma dai-dai lokacin Haiydar da Bashir suka shigo bayan sun fito daga ɓangaren su Abualeey Haiydar na bin Falon da kallo yace.

“Ummi ina Addah Khausy?”.

Ɗan Murmushi Ummi tayi tare da faɗin.

“Tana side ɗin Moddibo”.

Cikin sassarfa ya juya da niyyar fita sai kuma yayi saurin juyawa ya kalli Didi cikin girmama ya ɗan rusunar da kanshi yace.

“Ayyah Didi kuyi haƙuri na manta bamu gaisa ba ina yininku fatan kunzo lafiya?”.

Dariya tayi tare da faɗin.

“A' lafiya lau anyi kewar ƴar uwa ko?”.

Dariya yayi tare da kama hannun Bashir da yake gaida su daga nan suka ficewa kai tsaye Side ɗin Moddibo suka nufa.


Acan Side ɗin Mazan ma haka ya kasance Abban Jameel da kansa yagabatar musu da abinci na alfarma da girmamawa sosai Abualeey suka jinjina mutunci da karramawarsu...


Haiydar da Bashir kuwa tun daga kan step ɗin Side ɗin Moddibo suke ƙwalawa Khausar kira suna cewa.

“Addah Khausy! Addah Khausy!!, Addah, Khausy!!!”.

A kuma dai-dai lokacin Khausar da Moddibo ne tsaye Dining hannunsa na cikin nata cikin taushi ya ranƙofa kanta tare da sassauta murya yace.

“Me zaki ci?”.

Kanta ta langwaɓar tare da tsirawa jerin abincin dake dining ɗin ido lumshe idanunta tayi tare da fara buɗe womers ɗin cikin yanayin jin sanyi ta motsa laɓɓanta tare da cewa.

“Ga nan tuwo miyan kuka kasa min kaɗan zanci ”.

Ajiyar zuciya ya sauƙe tare da faɗin.

“Masha Allah zauna toh bari na zuba miki”.

Da dan sauri ta juya jin Bashir da Haiydar na cewa Addah Khausy Addah Khausy hannunta dake cikin nasa ta janye ta juya cikin sassarfa ta nufi ƙofan anufinta tayi  gudu.

Da wani irin sauri Moddibo ya riƙo tsintsiyar hannunta yace.

“Kiyi haƙuri Minha na tuba dan Allah kada kiyi gudu”.

Ɗan ware idanunta tayi tare da faɗin.

“Su Bashir da Haiydar ne fa”.

Kafin ta ƙarasa suka ƙara so cikin falon tare da rungumeta shima Bashir cikin sauri ya rungumeta ta gefen Haiydar.

Murmushi Moddibo yayi tare da harɗe hannunsa aƙirji yana kallonsu da tattausan murmushi bisa kekkyawar fuskarsa.

  

Khausar kuwa kallon Bashir tayi tare da cewa.

„Bashir ina Asma'u?”.

Murmushi yayi kana yace.

“Ba tazo ba wai ita kunya Amarya baza ta zo ba”.

Dariya mai tauri ta sanya tare da faɗin.

“Don Allah yanzu baza tazo ba haka zata min kenan?”.

Kai ya gyaɗa tare da cewa.

“Wallahi fa taƙi zuwa tun safe taƙi zuwa ayi shara da ita wai Ummi tayi haƙuri”.

Dariya Khausar ta sanya tace.

“Lallai dai kam”.

Haiydar kuma hannunshi yasa cikin nata.

Cikin mamaki ta kamo hannun tare da kallon faratunsa hararansa tayi tare da cewa.

“Me haka zaka wani tare farce kamar mace?”.

Cikin lingwaɓar da kai yace.

“Na gaza koyan yanke wa nefa, Mommy kuma tace in dai bazan koyaba bazata yanke minba”.

Murmushi tayi tare dasa hannunta ɗaya ta dungure ƙeyarsa tare da cewa.

“Shine daga isowata zaka haɗani da aikin yankewa”

Ta ƙareshe mgnar tana jawosu suka zauna bisa kujerun Dinnin table ɗin.

Moddibo kuwa a kujerar dake fuskantar Khausar ɗin ya zauna, yana maiyi mata wani arin amintaccen kallo ya fahimci akwai tsananin shaƙuwa da so tsakaninta da Haiydar duk da yawan faɗan da suke a da. 

Anan sukaci abinci tare.

Kana sukayi ta hira kiran sallan Magrib ne yasa duk mazan sunka tafi masallaci.

Kana basu dawoba saida sukayi sallan Isha sannan suka dawo nan kuma suka sake dasa sabon hira.

Hakama Abban Jameel dasu Abualeey.

Suma su Didi da Ummi haka ta kasance a wurinsu.


Misalin sha ɗaya su Lamiɗo suka yiwa su Abualeey saida safe kana suka tafi.

Su kuma duk sukayi shirin bacci suka kwanta.


Ummi dake tare da Malam Ahmad ta nufi sashen Khausar tana faɗin.

“Bari in je in jawo su Haiydar dan na lura su yau in zasu samu a nan zasu kwana”.

Kai ya jinjina mata tare da jingina jikin motarsu ya tsaya jiran fitowarta.


Ummi na shiga ta kalli Haiydar dake zaune gefen Khausar tace.

“Ku tasa mu tafi”.

Da sauri Khausar ta miƙe tare da cewa.

“Toh Ummi bari in ɗauko mayafina mu tafi”.

Juyawa Ummi tayi jin Moddibo na cewa.

“Ina zaki je?".

Idanunta ta narkar kana tace.

“Zanje gida mana”.

Yana tsuke fuska yace.

“Da Izinin wa?".

Murmushi Ummi tayi tare da kallon Haiydar da Bashir tace.

“Haiydar kuzo mu tafi dare yayi mu barsu su huta”.

Saurin kallon Ummi Khausar tayi tace.

“Ayyah Ummi dan Allah ku jirani ya za'a kuma ace bazan jeba don Allah kayi haƙuri”.

“Da Izinin wa?”.

Ya maimaita tambayar yana mai tsuke fuska.

Kamar za tayi kuka tace.

“Da Izinin ka mana”.

Kai tsaye yace.

“Toh ban bada Izini ba”.

Ummi kam hannun Haiydar da Bashir taja suka fice.


Sai da suka sauƙe Haiydar agida kafin suka wuce.


Haiydar na shiga Falon Momy ya shiga da sauri ya zauna gabanta kan lallausan Darduma da take bisa alamu shafi da witri tayi.

yayin da ta jingina kanta jikin kushin cike da matsanancin farin ciki yace.

“Momy".

Cikin tsira nasa ido ta gyara zamanta tare da cewa.

“Na'am”.

Murmushin fuskarsa ya faɗaɗa tare da faɗin.

“Kin ga yanda Addah Khausy ta dawo kuwa Momy?”.

Kai Momy ta girgiza kana tace.

“A'a ya ta dawo?”.

Zama ya gyara yace.

“Wallahi idan kika ganta zakice Balarabiya ce Masha Allah Subhanallah, tayi wani irin fari mai masifar kyau farinta har wani ƙelli takeyi”.

Ɗan ware idanu Momy tayi tare da faɗin.

“Allah ko?”.

Kai ya gyaɗa yace.

“Wallahi fa”.

Daga nan suka cigaba da hira.


Acan ɓangaren su Moddibo kuwa cikin tura baki Khausar tace.

“Haka kawai ahanani zuwa gidan mu yanzu Fisabilillahi muna ƙasa ɗaya gari ɗaya ace bazan ga Momyna ba?”.

Kansa ya ɗaura bisa kafaɗarsa yace.

“Na isa? Ai ban isa in hana ki ganin Momyn kiba? waya isa ya raba uwa da ɗa?  ban isa in ra Baki da Momy ba.

Kawai dai nima bana so ara bani da ɗana akusa dani ne shiyasa”.

 Cunno baki tayi tana kallonsa cike da shagwaɓa hanci ya lakace mata kana ya cigaba da cewa.

 “Kuma ina so ki huta nasan in kunje hira zaku tayi baza ki huta ba kiyi haƙuri ki kwanta kiyi bacci ki huta gobe da kaina zan kai ki muje mu gaida Momy”.

Ajiyar zuciya ta sauƙe tare da cewa.

“Da sassafe”.

Kai ya gyaɗa cikin tabbatar wa yace.

“In sha Allah in dai mun karya”.

Lallausan murmushi ta sakar mishi tare da riƙe tafin hannunsa tace.

“Toh shikenan”.

Bedroom suka wuce sosai tsarin ɗakin yayi kyau komai yayi yanda ake buƙata kana agyare tsaf-tsaf sai tashin ƙamshin roomfteshner yake, zama tayi kan gadon tare da jingina kanta da jikin gadon.

Moddibo kuwa gefenta ya zauna yana ɗan matsa mata ƙafafun yace.

“Kinga tafiyar nan da akayi mai ɗan tsawo sai nake ga kamar ƙafarki ta kumbura”.

Idanunta dake lumshe ta ɗan buɗe ta kalli ƙafan sai kuma ta gyaɗa masa kai tace.

“Eh dama Ni haka nake in dai na ɗanyi tafiya mai tsawo amota Normal haka yake min,  zuwa safiya zaka ga ya watse”.

Ajiyar zuciya ya sauƙe tare da faɗin.

“Kuma ahaka kike so ki tafi kije ki zauna ba kiyi bacci ba”.

Ya ƙare maganar yana jan yatsun ƙafar tata tare da ɗan mammatsa mata su, sassayan numfashi ta fesar tare da muskutawa, da sauri ya ɗan tallabota tare da gyara mata kwanciyar saboda ganin duk ta sake alamun bacci mai nauyi takeji.

Ahaka ya cigaba dayi mata massage suna hira jefi-jefi har bacci ya ɗauketa.

 janyota jikinsa yayi ya haɗa hannunsa waje ɗaya ya tofa musu addu'a ajikinsa ya fara shafawa kana ya shafa mata.


Washe gari bayan sun kammala breakfast da duk wani abu da za suyi Kai tsaye sashen su Didi suka shiga bakinsu ɗauke da sallama suka shiga bayan sun gaigaisa Moddibo ya kalli Didi tare da cewa.

“Didi zamu je wurin Momy”.

Kai Didi ta gyaɗa kana tace 

“Ok sai munzo muma yanzu Ummin Jameel zata zo mu taho tare”.

Kai ya gyaɗa yana ɗan matsa hannun Khausar yace.

“Toh shikenan sai kun zo”.

Daga nan suka miƙe suka fito da kansa ya shiga mazaunin driver, kana ta shiga gefen mai zaman banza, cikin nitsuwa yaja suka tafi anutse yake driving yana Jin wani yanayi na daban.


 Titinan garin ya zubawa ido lokaci ɗaya kuma tunanin J ɗinsa ya faɗo masa sai kuma yake tuna Lokuta da dama Idan yana tuƙi J na gefensa ko kuma J na tuƙi shi yana gefensa jikinsa ne yayi sanyi, tafin hannunta ya riƙo tare da mannawa kan cikinta yayi shiru kwayar idanunsa na tsats-tsafo da ruwan hawaye.

Tuni ta fahimci yanayin da yake ciki cikin sanyi da rauni tace.

“Allah ya jiƙan Yah Jameel Allah ya mishi Rahma Allah ya gafarta masa” 

Araunane yace.

“Ameen Ya Allah Minha”.

Tana matsa hannunsa dake cikin nata tace.

“Yah Jameel yanzu baya buƙatar kukan nu addu'ar mu yake buƙata”.

Cikin ƙoƙarin hana hawayen sa zuba yace.

“Nima haka nakeso ina ta ƙoƙarin hana zuciyata da Idanuna kuka akan J sai dai muyi ta mishi addu'a Amman wasu lokutan ina gaza hana kaina hawaye a kanshi saboda nayi rashine da har yau ban samu madadinsa ba”.

Cikin tausasawa tace.

“Na sani Yah Mu'allim to Amman Allah ya fimu sonshi, kuma dama shi ya bamu shi dan haka addu'a kawai zamuyi ya mishi”.

Cikin sanyi yace.

“In sha Allah za muyi masa”.


A kuma Dai-dai lokacin mai gadi ya buɗe musu gate ɗin gidan Lamiɗo Parking yayi kana suka fita da sauri ta nufi harabar gidan da nufin gudu,

saurin riƙo hannunta yayi cikin tsira mata idanu ya langwaɓar da kai yace.

“Kar kiyi gudu mana wai ke bakya jin tsoron ki faɗine”.

Kai ta ta gyaɗa tace.

“Toh ai sauri nake inje inga Momy".

Sake langwaɓar da kai yayi yace.

“Ai zaki ganta Minha ba sai kinyi gudu ba tun da gaki cikin gidan”.

Ko gama rufe baki baiyi ba ta hango Raudat riƙe da Comb da kifiya bisa alamu kitso zata tafi. 

Da sassarfa ta nufeta tana kiranta,

Ita kuwa Raudat jin muryar Adda Khausy tane yasa ta ɗago kanta aiko ganinta ne yasa ta buga tsalle cike da matsanancin farin ciki tace.

“Addah Khausy”.

Da wani irin sauri Khausar ta janye hannunta dake cikin nasa ta ruga da gudu.

Atsorace ya sanya tafin hannunsa biyu ya dafe kansa kana ya motsa laɓɓansa tare da faɗin.

“Ya Salam ki daina gudun nan”.

Ina bata saurareshi ba da gudu ta rungume Raudat Raudat kuwa tsalle ta riƙa yi ajikinta tana cewa.

“Oyoyo! Oyoyo Addah Khausy!, Mommy Addah Khausy!! Tazo Addah Khausy!!!,Oyoyo”.

Cike da matsanancin farin ciki Khausar ta ɗaga ta sama ta riƙa juyawa da ita a tsakiyar gida wanda hakan ne yasa baki ɗaya mutanen gida suka san cewa Khausar tazo.


Dai-dai lokacin kuma Haiydar ya fito daga ɗakinsa.

 Da gudu Sulaiman ma ya fito daga sashen Hajiya Bunayya atare suka rungumeta suna faɗin.

“Oyoyo Addah Khausy ”.

Khausar kuwa cike da matsanancin farin ciki take jujjuyawa atsakiyarsu ruggume da Raudat tsam a jikinta.


Jin sowarsunw yasa Momy dake zaune falonta ta miƙe da sauri ta fito jin sautin muryansu na tashi cak ta tsaya ta riƙe ƙafan Falon tare da tsirawa Khausar idanu tana kallonta cike da so, ƙauna, bege, kewa irin na uwa da yarta.


Khausar kuwa sai juyawa take dasu tana ƙyalƙyala dariya sai kuma tayi saurin sake su ta nufi Momy tana gudu tare da faɗin.

“Oyoyo Momyna”.

Runtse idanunsa yayi sai kuma ya ɗan ɗaga saitin muryansa yace.

“Dan Allah Momy kice mata ta daina gudun nan zata yiwa kanta Illah fa”.

Murmushi Momy tayi tare da kallon Khausar kallo ɗaya ta mata ta fahimci tana da ciki wanda har ya ɗan tasa ga wani irin kyau da tayi sai ƙelli take zubawa ga ɗan cikinta daya turo gwanin kyau ya zauna a jikinta cib da cib sai ƙugunta da ya ƙara faɗi.

Cikin sauri da bege Minti ta rungumeta asanda ta isa gareta sau kuna tace.

“Ke meyesa bakya girmane. Khausar wannan guje-guje har yanzu baki barshi ba”.

Murmushi tayi tare da sake Momy sai kuma ta sake rungumeta kana ta sake ta ta kuma sake rungumeta ɗan turata Momy tayi tare da faɗin.

“Ni matsa ahanya Bismillah Moddibo shigo".

Sai alokacin Haiydar ya miƙawa Moddibo hannu kana yace.

“Yah Moddibo Bismillah mu shiga”.

Kai Moddibo ya gyaɗa suka shiga bayan sun zauna a falo Momy da kanta ta kawo musu Drinks da Snacks da ruwa ta ajiye musu agabansu.


Raudat kam cike da farin ciki ta kwanta kan Khausar tana ta nuƙurƙusata,

ahankali Moddibo ya riƙo tafin hannunta yace.

“Kiyi haƙuri Aunty Raudiy adaina danne Adda Khausy kar aji mata ciwo”.

Cikin jin daɗi Momy ta kawar da kanta jin yanda yake mata magana cike da kulawa sai kuma ta miƙe tace.

“Bismillah kusha ruwa bari nazo ”.

Ta ƙarashe maganar tana fita kai tsaye bedroom ɗin ta ta wuce.


Acan ɓangaren Hajiya Bunayya kuwa a dai-dai lokacin zaune take aruwan zafi idanu ta tsirawa ruwan tana kallon ƙananun tsutsotsin farare masu jajayen kai wanda ga duk kan alamu sune suke addabar ta da jarabar ƙaiƙayi wanda zuwa yanzu tsakaninta dubaranta da gabanta ya wawake tuni sun fafeta ta kashin ta da gabanta ya haɗe saboda masifar ƙaiƙayi da yanda suke cinta taje asibiti har ta gode Allah abanza kana ta kira matar data haɗa su da Boka Gillaw.

Taje ta faɗawa Boka Gillaw ga abinda yake faruwa yace wannan sakamakon aikin su suke girba babu abinda zai iya kada su sake kiransa,  dama shi ya gaya musu idan buƙata ta biya su biya kuɗi idan kuma bai biya ba shikenan suji da kansu.

Matar ta tambaye shi mai zai basu amma yace babu abinda zai basu wannan Sakayyar sune babu wanda ya isa ya kawar da Sakayyar zunubansu ne ya sauka akan su Babu ruwansa suji da kansu shima yaji da kansa.


Tuno waɗanan maganganun ne yasa ta fashe da marayan kuka mai cike da nadama mara amfani, tana cikin kukan ta jiyo sautin muryoyi ana cewa Oyoyo Addah Khausy ahankali ta juye ruwan  tana kallon tsutsotsin masu masifar gudu da ƙaiƙayi dole sai ta shiga ruwan ɗumin ne take ɗan jin sauƙi.


Tana fitowa daga Bathroom ɗin ta zaune gefen Amina dake kwance kan gadon wacce ta rame ta zama wata halitta daban kamar ƙwarangwal tana nan tamkar wacce babu numfashi ajikinta kuka ta fashe dashi tare da cewa.

“Amina kinga Sakayyar abinda mukayi ko. Ubangiji ya kama mu tun a duniya Allah ya kamu da Sakayyar tarin zunubanmu Amina ya zamuyi?”.

Araunane Amina ta ɗago kanta cikin muryanta da baki ɗaya ya koma na wata halitta ta kalleta duk ta disashe baki ɗaya kamanninta da siffofinta ya fara zama na maciji ne ko menene dai ho da kyar ta buɗe bakinta tace.

“Umma munemi gafarar wa'anda muka cutar tun kafin dare ya mana ”.

Cikin rauni da zubda hawaye Hajiya Bunayya tace.

“Dole ma mune mi gafarsu su yafe mana nasani wannan Sakayyar abinda nata yiwa wannan baiwar Allah ne, da abinda nayi wa ƴarta da kuma yanda nayi ta zubar mata da ciki sannan nasa aka kashe Ramadan yanzu shine Allah ya jarabceni da wannan abin”.

Kuka sosai Amina ta fashe dashi tana ji kamar adawo mata da lokacin baya ta gyara kuskurenta.

Ita ma Hajiya Bunayya kuka ta fashe dashi Asiya ce ta shigo ta zauna gefen su ta shiga rera kuka cikin rauni da tausayinsu tace.

“Umma ku nemi gafarar Momyn Khausar da Khausar duk wanda ku kasan kun cutar kunemi gafarar su Allah gafururrur rahim ne shima zai yafe muku sai kuma ku nemi gafarar Allah akan shirka da kuka yi Allah ya yafe muku ”.

Cikin raunin Murya da shesh-sheƙa Amina ta gyaɗa mata kai tare da faɗin.

“In sha Allah zamu nema amma Addah Asiya ki taya mu basu haƙuri ”.

Kai Asiya ta gyaɗa tare da cewa.

„In sha Allah yanzu ma mukayi waya da Samira Sani take cemin itama jiya baki ɗaya Momyn ta kwana tayi tana ta ihu acikin gida gaba ɗaya tazama kamar mahaukaciya, ita tana jin tsoro yanzu zata dawo nan ma”.

Atsorace Hajiya Bunayya ta dafe kuncinta tace.

“Yau sun shiga ukunsy Hajiya Lami fa ta haukacene”.

Cikin sanyi da zubda hawaye Asiya tace.

“Haka dai alamu suka nuna Umma Allah ya yaye muku ya dubeku da idon Rahama”.

Cikin rauni da tarin tsoro Hajiya Bunayya tace.

“Ameen”.

Amina kam sai hawaye take tana nadama da danasanin abinda ta aikata.


Acan Falon Momyn kuwa bayan Moddibo yasha ruwa kana yaci Snacks da Drinks Momy ta fito suka gaisa bayan sun gaisa ta kallesa da kulawa tace.

“Ina su Didi kuma?”.

Sake sunkuyar da kansa yayi tare da cewa.

“Momy su Didi suna gida amma sunce zasu ɗan fito zuwa azahar, sannan zasu fara ta gidan su Ummu kafin suzo”.

Dai-dai lokacin kuma Asma'u ta shigo Falon bakinta ɗauke da sallama kasancewar Haiydar ya kirata ya sanar mata Khausar tazo gida.

Khausar na ganinta ta miƙe da tsalle kana ta haɗa da gudu suka rungume juna da Asma'u suka fara juyawa atsakiyaar Falon.

Cikin tsuke fuska Moddibo ya kalli Asma'u tare da faɗin.

“Asmau me haka ki sake ta?”.

Ahankali Asma'u ta sunkuyar da kanta ƙasa sai kuma ta saki Khausar ta tsugunna gefen Moddibo cike da ladabi tace.

“Yah Moddibo sannu da zuwa Ina yini”.

“Lafiya”.

Ya faɗa yana ɗan sake Fuskara sai kuma yace.

“Ke baki ga yanayin yanda ƙawar taki take bane kike mata irin wannan rungumar?”.

Dariyar dake cinta ta danne ganin yanda Khausar ta Cunno baki kana tace.

“Yah Moddibo ayi haƙuri”.

Yana murmushi yace.

“In sha Allah yanzu dai akiyaye”.

Kai ta gyaɗa tare da miƙewa ta riƙe hannun Khausar suka nufi bedroom ɗin ta.

Ganin haka yasa ya miƙe tare da cewa.

“Momy bari in fita dan su Dr Jameel na jirana zamuje gida Abban Jameel ”.

Mommy na gyara mayafinta tace.

“Ayyah ai nima Jameel ɗin nan ina so akawo minshi in ganshi Haiydar yata bani labarinsa”.

Cike da girmamawa yace.

“In sha Allahu Momy za'a kawo miki shi”.

Murmushi tayi tare da faɗin.

“Toh ka gaishe su”.

Amsawa yayi kana ya fita.


A dai-dai lokacin kuma Didi, Lalla Khadijah, Lalla Hafsat, Suna gidan Ummin Jameel duk sun gaisa da ƴan Uwanta wanda suka fara taruwa saboda bikin bayan sun gama suka fito zuwa gidansu Momyn Khausar.


Suna shiga Falon dai-dai lokacin Asma'u da Khausar na kitchen Khausar har mamakin kanta take saboda ƙosai da kunun gyaɗan da taci da safe, kana yanzu kuma Asma'u da kanta ta tuƙa mata tuwan Semovita da miyar ɗanyen kuɓewa aƙaramin dining Dake kitchen ɗin suke zaune.

Khausar kam ta kasa daina mamakin kanta yanda take cin tuwon sosai kallon Asma'u da itama tayi wani irin kyau na ban mamaki tayi ta fito a asalin amarya tace.

“Wallahi Asma'u har mamakin kaina na keyi rabona da abinci hakafa nafi wata huɗu”.

Murmushi Asma'u tayi tare da cewa.

“Ikon Allah baby ɗan albarka yasan yazo garinsu kenan”.

Murmushi Khausar tayi tare da sunkuyar da kanta ta ɗan kalli cikin,

dai-dai lokacin kuma suka jiyo sallamarsu Didi sun shigo gidan cikin wani irin...

Post a Comment

0 Comments