TOP HAUSA NOVELS atOptions = { 'key' : '20e08520dad54dbf6d9e963271

MIN QALB 🥰 PAGE 32-33

 _NAGODE_*_MQ 32_*


Gyara zama anty zarah tayi tana sake qurawa fuskar Amatun datayi haske sosai Ido tana maida kallonta zuwa hannuwanta dasukai haske sosai har wani yellow yellow sukayi taji hankalinta nason tashi gabanta na faduwa ta maida kallonta Kan fuskarta tanabinta da kallo ko Ina har zuwa qasanta ta ajiye cup din furar da Amatun tasa aka kawo Mata tana cewa''


Amatu yanayinki na bani tsoro da rashin nutsuwa sbd yanayinki na nuna kamar bakida jini,


Ruwa idanuwanta ke qoqarin kawowa tana kallon fuskarta Amatun dake zaune ka kwantarda kanta jikin sofa idanuwanta a lumshe Wanda yanzu hakan yazama tamkar dabia gareta sbd aduk lokacinda ta zauna tayi shiru idanuwanta take lumshewa sbd tunanin rayuwarta data juya Mata kamar upside down Dan kuwa sai yanzu take sake tabbatarda rashin Dr khalil zabeera arayuwarta babbar gibi ce ga rayuwarta sbd shine farin cikinta, walwalarta,gatanta,burinta,alfaharinta, nutsuwarta gatanta dama asalinta gaba daya...


Hawayen datake riqewane suka gangaro daga cikin rufaffun idanuwanta Wanda yasa hankalin Anty zarah sake tashi tunanin qilan eh da gasken Amatun batada jinin tunaninta ya zama gaskia ta dafe goshi tana rintse ido cikin tsananin damuwa da firgici tace"


Amatu Dan Allah ki bude Ido kiyi magana wannan kukan naki na zuci Yana wahalardamu masu qaunarki,

A zabeera kaf gaba daya yanzu Babu Wanda akeji dashi ake tsananin qaunarsa fiyeda kowa kamarki sbd kece Abinda duniya gaba daya ta shaida Dr khalil zabeera naso fiyeda komai har rayuwarsa,

Damuwarki damuwar kowa ce,

Kukanki baqin cikin mune,

Amatu Dan Allah kiyi hkr ki dauki dangana tareda daukar qaddarar rashin Dr Khalil sbd ganinki ahaka na karya dukkanin qwarin gwiwar ummen khalil,

Yanzu Amatu bansan yazanyiba gaki da rashin lafiya ajikinki ta zazzabin dare kullum Amma kinki ko karban magani gashi yanzu Ina sakaran ko jini na neman gagararki Amatu meyasa,meyasa......hawaye ne suka katse Mata takasa qarasa maganar ta miqe da sauri zata bar gurin Amatu ta riqo hannunta ahankali tana bude idanuwanta dasukai jajir ta zubawa fuskar anty zarah din dake hawaye tanajin qaunarta tako Ina tana shigarta tareda tausayinsu su duka.


Jawota tayi ta maidata zaune tana kallon fuskarta ta tashi zaune ahankali tareda sake hannun anty zarah din tana dauke idanuwanta daga kallonta ahankali ta bude baki cikin yanayi na karyewar zuciya tace"


Anty zarah meyasa kike qaunata har haka?

Meyasa keda Dr kuke min irin wannan son haka?

Anty zarah kinsan arayuwata bantaba samun soyayya irinta Dr khalil zabeera ba,

Shine ya koyamin sonsa alokacinda zuciyata batasan wata soyayya ba saita kudi,

Shine yabani sunan mutunci da martabar mace,

Dr khalil zabeera yazabi soyayyata fiyeda komai da kowa,

Yasa zuciyata takamu da zazzafar soyayyarsa me wuyar Bari bare mantawa Amma yatafi ya barni a daidai lokacin da zuciyata batasan komai da kowaba bayanshi,

Meyasa yatafi yabarni anty zarah Ina tsananin buqatarsa.......


Rufe Mata baki anty zarah tayi tana girgiza Mata Kai hawayenta itama suna gudu tace"


Amatu kada kiyi sa6o ki dauki dangana shima da ana bada zabin mutuwa da bazai taba zabin barinki ba sbd bazaiso ganinki cikin irin wannan halin dakike cikiba yanzu..

Kiyi hkr ki rungumi hukuncin ubangiji akanku hakan da yayi shine daidai kizama me godewa ubangiji aduk halinda Kika tsintsi kanki.


Sauke Kai Amatun tayi hawayenta suka Gama gangarowa ta dago tana sharewa ta kalli anty zarah datake kallonta cikin tsananin damuwa ta sauke ajiyar zuciya ahankali tareda lumshe ido ta bude ta miqawa anty zarah din hannu tana kallon cup din furar data kawo Mata.


Da sauri anty zarah din ta dauki cup din ta Bata tana bayyanarda Jin Dadinta na sassautowa da Amatun tayi cikin guntun zumudi tace"


Thank you AMATULLAH.


Da sauri Amatun ta kalleta tana fasa Kai cup din bakinta sbd duk duniya Dr khalil dinta ne kawai ke Kiranta da cikakken sunanta AMATULLAH.


Fuskewa anty zarah tayi tana qaqalo murmushi ganin tana neman dawo da gaba baya tace"


Banma iya fadar sunan yayi Dadi ba kaman yanda ake fada.


Ganin tashiga kame kamen fadar sunan datayi yasa Amatu sake sauke ajiyar zuciya tana Kai cup din bakinta  tana kurba ahankali ta lumshe ido tana gyara jinginawarta  sbd dadi dakuma karbuwa dataji bakinta da cikinta sunayi da furar saita saki jiki tanasha ahankali furan na sake sanyata lumshe ido.


Anty zarah ganin yanda furan tasamu karbuwa sosai agun Amatun yasata miqewa da sauri ta nufi fridge ta dauko gaba daya jug din furan ta dawo dashi ta ajiye gaban Amatun tana cewa'' 


Kawo cup din aqara zubawa Kisha 

Dama nasan zakiji Dadinta sbd har sabuwar Madara na zuba Miki aciki.


Qara Mata tayi takuma shanyewa Saida ta shanye kusan cup uku kafin tace ta Isa abarta haka.


Cikin Jin Dadi anty zarah tagyara zama tana Mata fira ahankali tana matsa Mata qafafunta dasuka Dan kumbura sbd zama guri daya 

Ahaka har bacci ya dauketa cikin nutsuwa Wanda rabonta da irinsa tun kafin rasuwar mijinta sai yau.


Gyara Mata kwanciya zarah tayi kafin ta zame ta fice daga part din gaba daya takoma nasu Nan ma wani aikin tahau sbd MAHMOUD datake saka ran  dawowarsa ayau din duk da gaba daya yinin ranar basuyi wayaba dama itace tafi Kira to itakuma yau ganin yanayin sauyin jikin Amatu yasa hankalinta yadan dauku ko yanzu tana ganin kamar hasashenta gaskia ne Amatu na buqatar ganin likita jikinta bai nuna tana lafiyaba 

Dole zata fadawa umme kokuma MD idan yadawo yau asan nayi kada wani ciwo ya kamata basuda masaniya.


Aikin gyare gyare da girki suka hau Yi itada hafsatu sbd tuntuni ta zauna tayi nazari zata dauki shawarar Amatu ta kawo gyara arayuwar aurenta da tsakaninta da mijinta,

Zata cire shakku da tsoron mijinta ta fuskanci reality rayuwar aure sukeyi ba zaman darasiba Dan haka zata sauya kanta ta sauya zamantakewarta da MAHMOUD ZABEERA kada tayi sake lokaci ya qure Mata.


Sai yamma suka Gama komai tayi wanka ta sanya doguwar riga ta atampa tareda yafa qaramin qyale akanta ta hada abincin data dibarwa amatu ta jera a tray hafsatu ta dauka suka nufi can.


Koda suka shiga futowarta wanka kenan itama ta sanyo riga da skirt na atampa ta sanya.,

Abin mamaki maimakon taji kayan sun Mata yawa sbd Rama saitaji kamar skirt din ya kamata hakama rigar.


Kallon anty zarah dake kallonta cikin yanayi na tunanin dabasanma na menene ba haka kawai idan tana kallon Amatu wani lokacin saita Shiga tunanin yanzu saime Kuma zaizo gaba a rayuwar Amatun.


Anty zarah kina ganin na qara jiki ne kokuwa nece naji hakan?


Numfashi anty zarah din ta sauke tana matsowa gaban Amatun ta Dan ja rigarta daga gefe gefe taji ba wani space tasaki murmushi tana cewa'' 


Gskia baki wani qara ba inaga sbd dai kin Dade baki sakasu bane shiyasa gashi bakida wasu tsofin kayan bare kisaka Amma kiyi hkr kiyi manage tunda ba abin ado bane Kuma ba fita zakiyi ba bare kice Zaki takura.


Gyada kanta tayi tana sanyawa kanta hula Mara nauyi ta Dan saki fuska ta qaqalo murmushin yaqe sbd faranta ran Anty ZARAn tace"


Anty zarah wannan qamshin na Rabin ranki ne?

Sbd nasan shi kadaine akewa wannan Shirin na musamman.


Kasa boyuwa farin cikin anty zarah yayi ta saki annushuwa sosai tana cewa''


Amatun kin bawa MAHMOUD sunan Dole Wanda harya zauna cikin kaina Nima RABIN RAN ANTY ZARAH.


Falo suka fito suna cigaba da Dan fira sama sama sbd karta zaqe da yawa ganin Amatun tafara sakewa.


Suna zama tace"


Anty zarah kokinsan meyasa idon mutum ke nauyi wani lokacin kamar zasu juye ga ciwon Kai me tsanani???


Kallonta da kyau zarah tayi kafin tace"


Kinajin hakan ne?


Gyada Kai tayi ahankali tana cewa"


Qila sbd kukan danakeyi ne koyaushe.


Aa Amatu ba lallai hakan bane ni nafi zargin rashin ishashen jini atare dake kibari Akira likiti ya dubaki.


Ba buqatan hakan anty kawai daima yanzu Kwan biyun Nan nadainajin nauyin idon ciwon Kai me tsanani yafi damuna idan akwai maganin ciwon Kai kawai kiban danasha shikenan zanji sauqinsa Inshallah.


Akwai ibuprofen agurina Yana maganin ciwon Kai sosai yanxu idan na koma xan aiko hafsatu takawo Miki kisha kafin ki kwant kafin safe zakiji wasai.


Nagode anty zarah Allah yabarki da Rabin ranki yabaki zuciyarsa.


Wata Yar dariyar farin ciki tasaki tana qoqarin dasawa zuciyarta zancen ta hanyar cewa amin saidai Kuma wani sashen na zuciyar na ganin kamar da wuya samun zuciyar MD ZABEERA koba agurinta ba ko agurin kowama.



Salman ne yashigo palon daukeda babbar ledar fresh fruits da ledar gasassun kifin dasuka gasu cikin source din veg chips sai qamshi sukeyi.

Da kallo dukkaninsu suke binsa har su hafsatu suka karbi kayan hannunsa sukai kicin dasu Dan zubowa a tray ya qaraso ya zauna gefen anty zarah Yana kujerar dake kallon ta Amatu Yana kallonta cikin yanayi na tsananin kulawa Yana tambayarta Yaya take

Ta amsa Masa cikin yanayin sake bawa kanta qwarin gwiwa sbd su masoyanta dasuka damu kansu akan damuwarta.


Maida kallonsa yayi Kan anty zarah dake yankawa Amatu kankana cikin fruits dinda su hafsatu suka kawo bayam sun sake wankowa yasaki murmushi Yana cewa''


ZARAH Ashe MD yadawo yau.


Dagowa tayi tana Masa kallon mamaki da tambaya tana miqawa Amatu kankana a qaramin plate da fork.


Ganin alamar batasaniba akan fuskarta yasashi karban plate din dashima take miqo Masa ya gyara zama yafara Sha kafin yace"


Kafin nafita da yamman Nan Naga shigowar motarsa an daukosa daga airport Amma sashen Modibbo Naga motar ta nufa Kuma acan mukayi sallar magrib tare agun Modibbon Amma dai by now inaga yabar sashen Modibbo.


Kallonta Amatu tayi tana sake murmushi ahankali cikin nutsuwa tace"


Barka anty zarah.


Itama murmushi ta mayar musu tana gatsa apple ahankali zuciyarta na shiga yanayi na 'yar damuwa tana basarwa sbd qilan yakirata bayan dawowarsa din Dan tabar wayar acan sashensu tana charging.


Ganin hankalinta bai Kan Yar qaramar firar dasukeyi yasata miqewa tareda Yi musu Saida safe daidai fitowar anty salamatu daga dakin dayake zaman nata a zaman dazatai agidan kafin sukoma inda suka fito.


Qarosowa tayi suka gaisa da zarah dazata fice kafin ya qaraso ta zauna gefen Dr salman suna gaisawa Yana janta da Yar firar dasuka Saba tun amatu nasaka musu baki hartayi shiru ta lumshe ido tana saurarensu sbd kanta dake sarawa.


Shigowar hafsatu ce data dawo tasata bude idanuwanta ahankali ta saukesu akan hafsatun tareda karban maganinda anty zarah din ta aikota takawo Mata ta juya ta fice.


Miqewa tayi da kanta ta nufi kicin ta bude fridge ta dauko ruwa ta bude tareda ballo maganin Tasha ta maida sauran ruwan tareda fitowa tayiwa salman Saida safe ta wuce daki direct tayi sallar ishai ta kwanta sbd tsanani dataji kamar Kan nata nayi Dan har jiri jiri take gani.




Zarah kuwa bayan tabawa hafsatu maganin takaiwa Amatu direct sama ta nufa dakin MD bayan tasake fesa turare ta daura dankwalin kayan jikinta tana sake gyara zaman curves din rigar taje ta hado Masa abincin sukai Masa marasa nauyi a tray ta Isa qofarsa tayi knocking so daya kafin ta tura qofar tashiga bakinta daukeda sallama cikin yanayi na nutsuwa.


Fitowarsa wanka kenan Yana tsaye gaban mirror Yana goge ruwan jikinsa ahankali ya dago ya kallota ta jikin madubi da fararen idanuwansa ya amsa sallamar ahankali cikin muryarsa data kashe jikinta Nan take.


Kallonsa takeyi da dukkanin idanuwanta da bakinta da hancinta da nutsuwarta da komaima nata sbd wani sheqi da jikinsa yakeyi na hutu dayake samu.


Jin shiru yasashi juyowa ahankali ya kalleta yaga yanda duk ta sake gurin kallonsa ya dauke Kai ahankali tareda bude wardrobe ya janyo jallabiya Mai tsantsi da taushi brown ya saka tareda fesa spray dinsa na imperial majesty ya nufa kujera ya zauna Yana daukar wayarsa dake kashe ya kunna tareda dagowa ya zuba Mata manyan idanuwansa ya bude baki ahankali yace"


Nasameku lafiya?


Dan firgita tayi da tareda dauke idonta akansa cikin tsananin Jin nauyin mayen kallon datazo ta tsaresa dashi batareda yimasa ko sannu da zuwaba bare gaidashi.


Cikin Dan Jin kunya ta qaraso gefensa ta zauna ahankali ta ajiye tray din akan table tana saita kanta cikin Jan mutuncinta a natse tace"


Barka da dawowa,ya hanya?



Ajiye wayarsa yafarayi bayan ya saka silent ya Dan juyo ya kalleta cikin nutsuwa har zuwa adon datayi dominsa ya sauke ajiyar zuciya ahankali kafin ya dauke Kai Yana Dan sakin fuska yace" 


Alhamdulillah,

Ya kuke?


Sake kallonsa tayi sbd yanda gabaki daya ko awaya yawanci tambayoyinsa suka koma Mata kalmar KU.


Jin shiru yasashi dagowa ya kalleta ya sake maimaita tambayarsa da cewa''


Kuna lafiya???


Zuba Mata Ido yayi sbd amsa yakeson ji.


Akwai matsalane acan gefen??


Sai alokacin ta kallesa cikin Ido sbd sai alokacin ta fahimci Amatu yake nufi ta saki ajiyar zuciya tareda sake murmushi tana gyada Kai tace"


lafiya kalau Nake su Amatu ma lafiya kalau suke saidai duk da Bata fadaminba inaga kamar batada lafiya sbd sauyawar datayi ga ciwon Kai me tsanani datace tana........


Tari me qarfi ya sarqesa na abincin dake bakinsa,

Spoon din faten dankalin daya maida cikin plate batareda yakai bakinsaba kamar yanda yayi Niya yasata kasa qarasa fadar Abinda take fada tana kallonsa ta kalli abincin cikin mamaki da fargaba tace"


Ya salam,

Sorry,

Lafiya?

Akwai wani Abu ne tareda abincin?



Dan lumshe ido yayi tareda budewa batareda ya kalletaba yace"


I lost my appetite.


Cikin damuwa ta matsosa da sauri Yana dafasa cikin kulawa tace"


Bakada lafiya ne?

Ko akawo wani abincin?


Numfashi ya sauke Yana sake kallonta yace"


No I just lost the need to eat karki damu.


Kasa hakura tayi ta zubo Masa coconut drink dinda tafi awa biyu tana hada Masa sbd sanin Yana qaunarsa ta zubo a cup ta miqa Masa cikin sauri da kulawa daidai kiran Salman zabeera nashigowa hannun dayayi niyyar karban drink din datake basa shi ya wuce dashi ya dauki wayar Kai tsaye Abinda bayayi Kiran farko ya daga waya,

Yanaji a rayuwarsa daga Modibbo sai Khalil ne kawai ke Masa Kira daya ya dauka.


MD Amatu ce ba lafiya sosai she's ko numfashi batayi and she is bleeding ba kakkautawa am taking her to hospital...


Aje wayar yayi Yana qoqarin saita nutsuwarsa 

Saikuma kawai ya miqe tareda daukar wayarsa da key din mota yafice.


Bayansa zarah tabi da kallo kafin tabi hannunta dake sangale da cup din data miqa Masa bai karba ba tanaji wani nauyi na danne zuciyarta Wanda yasa idanuwanta cikowa da hawayen dabatasan Kona menene ba.

#Mamuh#*_MQ 33_*




Ahankali ta sulale zaune hawayen datake qoqarin maidawa suka gangaro,haka kawai zuciyarta kejin zafin Abinda yayi Mata din a yanxu

Aqalla koma menene tunda ba mutuwa akace Amatun tayi ba ya kamata yayi Mata mgn kokuma ya karba Abinda take miqa Masa din,


Share hawayen tayi tareda ajiye cup ahankali ta miqe ta fice tana qoqarin cire damuwar abin kwata kwata cikin ranta sbd idanma ta barshi cikin ranta itace zata fi kowa wahala.


Bedroom dinta ta nufa tareda sanyo gyale ta dauko wayarta ta fito tana latsa Kiran anty salamatu.


Cikin sanyin jiki da kulawa tace"


Anty salamatu menene yasamu Amatun?

Kuna Nan kokuwa anwuce asibitin?


Numfashin damuwa anty salamatu ta sauke cikin tsananin damuwa tace"


Wlh haka kawai muka dinga Jin nishinta da salati Koda mukazo harta some ga jini ba qaqqautawa sai zuba yakeyi gamu dai muna isowa asibiti yanzu tareda MD da Dr salman.


Katse wayar tayi ahankali tareda sauke numfashi tana sake bawa kanta qwarin gwiwa da hkr ta nufi sashen umme tana amsa Kiran mominta data Kira tana Mata barkar dawowar mijinta lfy.


Tana shiga umme na fitowa da jaka a hannunta Nuratu na biye da ita hankalinsu a matuqar tashe musamman umme dako lulluba gyalenta daidai takasa tadai ratayosa a wuya ta gyara cikin mota idan tashiga.


Fadawa motar tayi itama tace zata bisu zuwa asibitin suka wuce sbd zumudi ma Nuratu ce ta tuqa motar sbd bazasu jira shigowar driver ba daga main gate tunda akwai tafiya daga gate din farkon zuwa ciki.


A mota umme ta kalli zarah datai sanyi tana cewa''


Zarah menene yafaru ne? ko bayan magriba dinnan nayi waya da ita najita lafiya kalau har Ina godewa Allah danaji muryarta tafara sakewa da walwala,

Shin da akwai matsala ne tuntuni daban saniba kokuwa yanxune kawai abin yasameta?


Numfashin damuwa anty zarah ta sauke ta kalli ummen cikin sanyi tace"


Lafiya kalau nabarta bayan magriba dinnan tadaice tanata fama da ciwon Kai me tsanani sai jiri hakama gskia ta sauya sosai Dan saima ni nakega kaman batada jini sbd yanda tayi fayau fayau,


Kallonta umme tajuyo tayi gaba daya zuciyarta na bugawa daidai isowarsu asibitin suka fito suka nufi hanyar dakin dasukasan Dole tanacan sbd asibitin mijintane aka kawota,

Cikin tsananin damuwa da firgici umme ta kalli anty zarah bayan sun iso qofar dakin sun tarardasu salman a tsaye suna jira cikin rashin sukuni

Tace"


Zarah meyasa baki fadamin dukka wannan ba sai yanxu?

Shin Bayan jiri da ciwon Kan metace Miki tanaji?


Dan jujjuyawa tayi ta kallesu ganin kowa ya juyo ya zuba Mata ido Yana jiran amsarta Jin tamvayar da ummen tayi Mata MD ma dawowarsa kenan daga amsa wayar Modibbo ya qaraso Yana kallon yanda sukai cirko cirko.


Cikin kulawa tace"


No Kan ne kawai da jiri take min complain to saina Bata Ibuprofen maganin ciwon Kai........


What??????


Dr Fatima data fito dakin tafada cikin tsananin firgici tana qarasowa tace"


Ibuprofen?

Wayace kibata Magana batareda taga likitaba ya rubuta Mata?

Shin kinsan maganin dakika batane yasata cikin wannan hadarin gashi tana qoqarin rasa cikin dake jikinta......


Mene????umme tafada da tsananin qarfi tana zaro idanuwanta 

Ta juyo gun zarah cikin kidima tace"


Meyesa Zaki Bata magani bakisan aikinsa ba?

Meyasama baki fadawa kowaba zaki dauki magani kawai kibata zarah?

Innalillahi Dr Fatima meza'ayi yanzu Dan Allah kada kubari cikin Nan ya zube Dan girman Allah ku taimakamin ku tsaida cikin Nan.


Nuratu da anty salamatu ma kusan duk acikin shock sukace Dr Fatima Dan Allah ataimaka.


Salman ma cikin tsananin damuwar yace"


Maganin da hafsatu takawo Mata dazun shine Kika aiko Mata?


Dafe goshi yayi cikin damuwa yace"


Dakin Fara tambayana na duba kafin kibata tunda Ina Nan I cud have checked.


Mutuwar tsaye zarah tayi tana rarraba idanuwanta a tsakaninsu cikin tsananin firgici da tashin hankali kowa na jeho Mata tambayar meyasa meyasa.,

Shin suna tunanin kaman da gangan tabata maganin ne? kokuwa suna tunanin zata iya cutatar da Amatun be?


Cikin muryarsa data sanyata juyowa ahankali ta kallesa taji ya fuskanci Dr Fatima cikin murya me nutsuwa yace"


Na menene ibuprofen din?


Na ciwon Kaine Amma irin strong din Nan kwata kwata masu ciki basa shansa infact kamar abortion pills ne ga masu ciki marasa qarfin jini ko kadan,

Gskia this is serious sbd gashi ta zubarda jini sosai har jini ma Muna buqata gskia but yanxu dai we are trying our best mugan mun tsaida jinin.


Kai tsaye yace"


Wat are the chances na cikin?


I can't say sir but just pray and have faith we will try all the best we can Dan muma Muna son cikin

Sai Maganar jinin daza'a saka zamu Kira blood bank dinmu mu....


No bana buqatan na blood bank din afara Shirin diban ledan jinin kawai.


Kallon cikin idanuwansa zarah keyi tanason ya kalleta ta karanci yanayinsa da yanda ya karbi zancen itace tabawa Amatun maganin Amma yaqi kallontan saima qoqarin juyawa dayakeyi yaga Andi da kansa tareda Modibbo a bayansu suna kallonsa cikin nustuwa,


Cikin alfahari dashi Modibbo ya jinjina Masa Kai yace"


Abinda kace shine daidai bama buqatan jinin wani gurin dabam munada wainda zasu bada jini da dama...


Andi na kallon fuskarsa dake sunkuye Yana karantar yanayinsa na kulawa da damuwa da yayi akan iyalin Dan uwansa Khalil alokacinda baya rayen ya jinjinawa qoqarinsa cikin yabawa yace"


Bama buqatan jinin kowa acikin dangi ma tunda uban Dan gashinan a tsaye bazai rasa jinin bayarwaba.



Office din Dr ashir suka nufa acan yasake musu bayani tareda Basu tabbacin Inshallah komai zai daidaita kafin suka tafi.


Iyami da kawu ma tuni suka iso asibitin

Hankalin kowa nasake hargitsa musamman yanxu da kowa yaji zancen da akwai ciki kowa yaji batareda dogon nazari ba saiyace meyasa zaa Bata magani ba tambaya 

Hakan yasa anty zarah komawa gefe ta zauna cikin yanayi na tsananin damuwa da danasanin Bata maganin duk tasan cikin rashin sani tayi Amma yanda firgici kesa kowa tambayar Yana sata muzantuwa duk da Suma ta musu uxuri sbd tasan firgici ne da tsoron Abinda zai biyo baya.


Iyami ce tadawo gefenta ta zauna tana qoqarin danne damuwarta ta kalleta tace"


Karki damu zarah ko zubewa cikin yayi qaddararsa ce,

Koni da agabana take kowane irin magani Zan iya Bata na ciwon Kai tunda bamu sani ba.


Daga Mata Kai kawai zarah din tayi batareda ta iya ko magana ba 

Duk Wanda zaiga gangancin Abinda tayi bazata damuba mutum biyu kawai takeson su fahimci niyyarta da rashin saninta,

Daga MAHMOUD sai Amatun

Amma sai zuciyarta na ganar mata zaiyi wuya MAHMOUD yayi Mata kuskuren fahimta sbd yafi kowa sanin Abinda zata iya aikatawa musamman akan Amatu da kowa ya shaida da zuciya daya take qaunarta.


Cikin ikon Allah ansamu anshawo Kan matsalar jinin ya tsayu cikinma ya tsayu saidai Kam Babu dogon aiki ko motsin dazai iya taba lafiyar cikin Dan haka hutu ne kawai akeso tayita yi jinin ma ansaka Mata roba daya Kuma alhmdlh jikin bai wani Yi baiyiba tafarko har so biyu anty salamatu da iyami na Bata tea sbd sune suka kwana anan.


Hankalin kowa ya kwanta musamman umme da tunda safe Takoma asibitin kusan tareda zarah suka iso Dan motarsu atare tashigo harabar asibitin Kuma kowanne da kayan breakfast ya iso.


Gaisawa sukayi suka Isa dakin tare alokacin anfito da ita wanka kenan iyami nasaka Mata doguwar riga mara nauyi.


Gaisawa sukayi umme na zama kusada Amatun tana qarasa gyara Mata Sanya rigar sai kaffa kaffa takeyi Wanda yasa Amatun kallonta tasaki guntun murmushi tareda riqe hannunta tace"


Umme bafa fashewa zanyiba kiketa Yi kaman kwai.


Babu Wanda be bayyanarda murnarsaba a fili da Abinda tafada sbd tun bayan rasuwar Khalil yau ne farko datai Abinda yake asalin dabiarta wato yanko Magana ba taunawa.


Dariyar farin ciki umme tayi bayan tagama gyara Mata zaman rigar ta zaunar da ita an jingina Mata pillow tace"


Ni ummen Kuma ake fadawa haka Amatu.


Murmushi tayi tace"


Umme ji nayi kamar kina min susa ne Yana sani waiwayi.


Kallon anty zarah tayi zatayi Magana saiga MD ZABEERA yashigo atake imperial majesty yacika gurin da sanyin qamshi Wanda yasakata lumshe ido sbd qamshin daya samu karbuwa daga yanayinta na ciki 

Anty zarah ma lumshe ido tayi cikin yanayi na damuwa sbd jiya baikoma gidan ba sai dare sosai yanzu da safe Kuma tana tashi tahowarta asibiti tayi kawai sbd tayi tunanin Yana Nan din Ashe sai yanzu yake isowa gashi haryanxu basuyi Magana ba tana buqatan Magana dashi taji nasa tunanin akanta.


Ahankali ya qaraso ciki Yana gaidasu umme da iyami kafin ya maida kallonsa kadan akan gadon Amatun wadda ta bude idanuwanta adaidai lokacin sukai Ido cikin Ido

Da sauri kowannensu ya dauke idanuwansa shi Yana basarwa itakuma tana Dan tsuke fuska.


Kasa hkr zarah tayi sbd tanason Jin bakinsu su biyun akan alamarin ta juyo ta fuskancesa cikin tausasa harshe tace"


Ina kwana?


Kallonta yayi a natse ya amsa Yana qoqarin juyawa ya fice tace"


Ba laifina bane Abinda yafaru jiyan inatason inyi bayani Amma kamar kowa yakasa fahimtata.


Tsit dakin sukayi sbd Jin zancen nata musamman Amatu datakejin zancen yanzu.


Umme ce tayi saurin kallon Amatu kafin ta maida kallonta Kan zarah din tace"


Ba kasa fahimtarki akaiba zarah Amma ta Yaya Zaki yanke bata Magani without any consulting?

Da idonki Kinga Abinda yafaru da ita akan hakan,

Bai kamata ki kasa fadawa kowa Abinda yake damuntaba tun farko you should have told me ko Kuma MAHMOUD.


Cikowa idanuwanta sukai da hawaye bayan sunyi jajir ta dago ta kalli MAHMOUD din daya juya baya din bai fita ba yanajin saukar maganganun ummen har cikin ransa sbd idan har zarah tayi Dan kulawa ga Amatun bai kamata suga laifinta ba saidai ba halinsa bane tsayawa hayaniya.


Kallonsa zarah tayi ahankali tace"


Kana tunanin hakan kaima?


Rintse idanuwansa yayi tareda juyowa ahankali ya kalli Amatun da itama idanuwanta sukai jajir kafin ya kalli zarah din cikin radadin Abinda zai fada yace"


U could have asked kafin kibata maganin tunda Salman na Nan kokuma kifadawa ummen tun farko

This is irresponsible of you zarah...


Cikin bayyanarda tsananin damuwarta Amatu tace"


Me kukeyi wa anty zarah haka?

Kallonsa tayi Ido cikin Ido tace"


Kuna tunanin anty zarah zata iya cutatar Dani ne ko me? Ni banganeba,

Nice nace anty zarah tabani magani idan tanada bayan haka idan anty zarah tasan Ina tareda wani Abu atare Dani wlh bazata taba bani Abinda zai cutatar daniba bama haka wlh na tabbata a duniya idan akwai meson Abinda yake taredani bayan ni da mahaifinsa da Yana Raye to anty zarah ce idan da ace tasani,

Meyasa zaku dasa ayar tambaya akanta Bayan dukkanin shedarta yakamata ku bayar,

Umme kadaki zargi anty zarah akaina ko Abinda yake taredani Dan Allah ko anan gabane hakan Yana karya zuciyar me hakuri wlh,

Zaku iya dasa Mata wani tunani na dabam Bayan ba haka takeba kunfi kowa sani musamman Kai zatafi Jin zafi idan kayi Mata wannan tunani""taqarasa fada tana dauke idanuwanta daga cikin nasa daya zuba mata Yana kallonta da idanuwa a bude sbd akaro na farko ta tayasa fadar Abinda yake cikin zuciyarsa sbd shine yafi kowa sanin zarah bazatayi ko kusan hakanba Akan wani bare akan wannan silly yarinyar.


Numfashi ya sauke ahankali tareda kallon cikin idanuwan Amatun kafin ya juyo ya kalli zarah da idanuwanta sukai jajir cikin kulawa da taushin harshe yace"


Lets go.


Kallonsa tayi zuciyarta na narkewa,fushinta na wankewa sbd yanda yayi ya nuna kulawarsa gareta tareda nuna damuwarsa akanta

Cikin sanyi tace meyasa nakesonka sosai hakane MAHMOUD DAHEER ZABEERA?


Ahankali ta sauke idanuwanta daga kansa tana cewa''


Nakawo Mata breakfast inason zanbata da kaina.


Wani irin kallon are you kidding me?yayi Mata Yana mamakin halinta na rashin Jin zafi.


Murmushi tasake cikin sanyi tareda daga Masa Kai

Ahankali yace ok tareda juyowa ya fice zuwa office din Dr Fatima.


Qoqarin zuba Mata abinci umme tayi Amatun tayi saurin hanawa tana kallon anty zarah cikin murmushi tace"


Umme antyna ce zata bani abinci da kanta Dan Allah.


Kallon zarah din umme tayi cikin Jin nauyi kadan duk da ita Bata dauki maganarsu cin fuska ga zarah din ba sbd tun farko yakama kafin kabawa wani magani kabari likita ya rubuta Masa Mana.


Iyami ce taqara dorawa da bawa zarah haquri tareda matsa Mata ta matso Dan bawa Amatun Abinda takawo Mata.


Cikin farin ciki da cire damuwar Abinda ya wuce din ta zubawa Amatun kunun gyada da plantain ta miqa Mata tana cewa''


Kici sosai sbd kisamu qarfin haihuwa idan lokaci yayi Dan karki manta da alqawarin da kukaimin keda Dr khalil na cewa zaku bani Abinda zaku Haifa tun a wancan cikin na iska.


Dariya kowa yayi a dakin Banda Amatu da kewar Dr da tunaninsa ya dawo mata.


Yamma sosai aka sallameta Salman ya kalli su kawu da iyami Bayan dukkaninsu sun fito harabar asibitin za'a tafi gida yace"


Kawu muje saina saukeku a gida su Kuma su tafi a motar umme ga Kuma motar zarah MD ma Yana cikin asibitin Naga shigowarsa kafin ayi sallamar inaga Yana tareda likitocin.


Kallon salman din kawu yayi kafin ya maida kallon gun umme da Amatu yace"


Ai Amatu tafiya zanyi da ita tayi takabarta tareda renon cikinta a gida sbd hankalin iyami rabuwa zaiyi da ni kaina....


Zaro idanuwa waje umme tayi hakama zarah dashi kansa Salman din.


Cikin rawar murya umme tace"


Kawu kayi hakuri Amma bangane ainihin Abinda kake nufi ba.


Ina nufin tunda dai dama gida zata dawo ko Bayan takaba gwara Takoma can din tayi zaman idan yaso bayan haihuwar sai asan nayi......


Bayansa dukkaninsu sukabi da kallo Babu me iya Magana sbd girgizar zancensa 

Ganin suna kallon bayansa yasashi juyawa sai sukai Ido biyu da MAHMOUD dake tunkarosu cikin tafiyarsa me nutsuwa.

##Mamuh#

Post a Comment

0 Comments