TOP HAUSA NOVELS atOptions = { 'key' : '20e08520dad54dbf6d9e963271

'Yar Tsakar Gida 3 page 7-10

 Cikin Sauri Amrah ta fara ƙoƙarin ƙwace Jikin daga na Nurayn wanda sai a sannan ya janye bakin sa daga nata , har kuma a lokacin bai Juyo ya kalli inda Aslaam yake sirfa masifar shi ba , wani Hausan nasa ma abun dariya ce don ba fitar da ita yanda ya dace yake yi ba . Still hannun sa yasa yana shafa Gyefen Kuncin ta cike da Wani irin soyayya mai kidimantar da bawa da kuma Bama zuciya tausayin sa ƙwarai,don shi sam idanun sa a rufe suke . Ba tare da Su Mommy Aslaaamm sunji mai yace mata ba sai dai bakin sa da suka ga ya motsa a Miskilance kamun ya juyo yana kallon Aslaaamm wanda ya gama fusata da Al'amarin Nurayn a cewan sa “ Wannan shine rainin hankali da tacewa....Ɗan jan iska Nurayn yayi yana furzar da Huci kana ya kalli Amrah wacce har a lokacin idanun ta Basu tsaya sa zubda Ƙwallah ba , haka kuma bata daina ƙoƙarin son zame hannun ta daga riƙon da yayi mata ba.  Idanun sa ya kafe ta dasu wanda Ganin hakan yasa Amrah dakatawa da kiciniyar ƙwatan kan ta . A Miskilance yana ɗan kuna haɗe giran sa wanda ya saba sakata ladab idan yayi mata hakan nan take natsuwar ta ke dawo mata , da hakan ya saba yi mata koda kuwa yana buƙatar ta ne , don dole zata amince masa sai daga baya ya dawo kaman haka ya dinga kwantar mata da kai . Yace next time ba zai ƙara ba 🤔kuma bashi zai hana shi idan ya ɗebo jarabar nasa ya😜kun dai gane . Cike da miskilalliyar Muryar sa ya furta " menene...? 


Ba Amrah bace ta saki Baki na Mamaki Mommy Aslaaamm ma Juyawa tayi suna haɗa ido da Aslaaamm , wanda Ganin hakan yasa Aslaaamm nufar sa yana kai hannun sa tare da ƙoƙarin ɓanɓare Amrah daga riƙon da Nurayn yayi mata . Wai ka san me sunan abun da ka Shigo kana mana kuwa ? . Kallon Aslaaamm Nurayn yayi kana ya sauke hannun sa daga na Amrah yana ja baya kaɗan. Sai kuma ya ɗan saki Murmushin nan nasa da zan rasa na Meye ma , Ɗan motsa laɓɓan sa yayi yana Lumshe Sexy eyes ɗin sa tare da Girgiza kan sa yana furta " Aa Aslaam sai ka faɗa . A ƙufule Aslaaamm ya furta " wannan shi ake kira da brain washing. Ka iso mana gida ka kama riƙe mana Yarinya kana aikata haramun ko ka manta ba matar ka......kaiiiiiii.....!! Nurayn ya wani daka ma Aslaam gigitaccen Tsawa wanda sai da kaf ilahirin Falourn ya amsa . Nan kuma take idanun sa suka fara sauya kala tamkar damusa . Da gudu Amrah ta yi bayan Aslaaamm tana kokarin shigewa jikin sa ne , Nurayn ya furta " Na rantse da Allah yau sai kun bani matata...! Babu inda zan tafi sai da Amrah , matata ta ce . Ni mijin ta ne kuma na Sunnah kai ne zan tuhume ka akan riƙe mun hannun ta da kayi matar kace kana da iko da yin haka n ne. ? 


Amrah shiga ki dauko Mayafi mu huce .


Da Sauri Mom Aslaaamm ta nufo inda Nurayn yake don ta tsorata da al'amarin sa , Nurayn please ka saurara, ka Natsu kaji . Ƙwantar da hankalin ka . Mommy me yasa zaki basa Haƙuri ? Kalli fa yanda ya faɗo mana gida, sannan wai magana yake na taɓa masa jikin matar sa .? Aslaaamm enough...! Ya isa . Ai gaskiya ya faɗa matar sa ce . Bana son ƙara jin bakin ka , wuce ciki .  Wani irin kallo Aslaaamm yayi ma Mom yana ƙoƙarin bude baki yayi magana ta kuma daure fuska tana masa Umarnin ya basu wuri ,don ta fahimta idan ta zuba ido to za'a yi abun da ba'a so...! Cike da jin zafin Nurayn Aslaaamm ya wuce yana ƙoƙarin barin cikin gidan baki daya ba tare da yama san inda zai nufa ba . Ran sa a ɓace yake babu abin da yake gani na Nurayn baƙi Fache sharara fuskar Amrah da yayi da Mari . 


Nufa motonn sa ya yi yana mata key tare da danna horn yana ficewa daga Gidan baki daya . 


Kallon Nurayn Mom Aslaaamm tayi kana tace " Zauna ka huta sai ka ....No need Mom , ya katse ta yana sauke mata idanun sa kamin ya cigaba da cewa " Amrah zaki bani yanzu mu tafi . Ni na sake ta , kuma na maida matata . Haahhwww 😨 Mom Aslaaamm ta bude baki na Mamaki kana ta ga ya juya yana kallon inda Amrah ke tsaye dauko Mayafin ki mu wuce . Wani irin kallo Amrah ke bin sa dashi nan take Zuciyar ta ya fara ƙiyasta mata anya Ƙwaƙwalwar Noory ba fara samun matsala ba . Abubuwan nasa sun fara wuce gona da iri . A'a ba zata bi ka Nurayn. Muryar Mom Aslaaamm ya katse shi wacce tayi Maganan cike da sanyi. Ohk ya furta yana juyawa tare da maida hannayen sa cikin Aljihu . Mommy Amma Ni mijin ta ne ?  . Yayi Maganan yana kafe Mom d idanun sa wanda cike da rashin Fahimtar me zai yi Mom Aslaaamm tace " Eh kwarai haka yake . Gani tayi ya juya yana kama hannun Amrah tare da kokarin jan ye ta daga Falourn yana nufar Hanyar fita.  Innalillahi wa'inna ilaihir raji'un Nurayn wai kana lapiyar kuwa .? I'm not ....!! Ya furta cike da ƙaraji wanda yasa Amrah fasa ihu tana kiran sunan Mommy tare da kai hannun ta tana kokarin kamo Mommy wacce tayo kan Nurayn tana faɗin " Nurayn wannan fa ba abu mai kyau bane . Nurayn.....! Kallon Mom Aslaam bai yi ba ya nufi da Amrah Farfajiyar gidan , Mommy na binsa wanda nan take securities suka taso masa suna attacking din sa da bindigogi . 


Wani irin kallo Nurayn yayi masu kana ya saki yar dariya wanda sai da Amrah ta kara tsorata . A da baya yanda taga sunyi attacking din sa tayi tunanin ta tsira ne Dole zai barta anan , amma ganin irin murmushin da nurayn yayi yasa ta ƙara fashewa da kuka don sarai babu halin sa daya da bata sani ba . Noory na tambaye ka So na kake yi yanzu ko kuwa ƙina kake yi.? Hannun sa yasa yana Fiddo da wani abu mai kama da card yana daga masu wanda Ganin hakan yasa Securities din saurin ƙasa da bindigogin nasu sun san mallakin sunan nasa tun ba a Nigeria ba , sun kuma san wani shahararren ne da America ma jin shi sunan shi take bare kuma nan gida Nigeria 🥵 . Tsoro ne ya kama Mommy cikin sauri ta dubi securities din tana Cewa " au barin sa zaku yi ya tafi mun da Ƴa ta .? . 


Juyawa Nurayn yayi yana sakin ma Mom murmushi kana yace " Mom na gode sai mun sake haɗuwa . Noory me kake yi haka .? Wannan ba so bane hauka ne .! Amrah ta furta tana mai daga Muryar ta da ƙarfi wanda Ganin haka yasa Nurayn bude motonn yana tura ta tare da rufewa cikin wani irin mahaukacin gudu ya bar compound din tare da ficewa yana ɗaukar hanya.....ihu Amrah keyi haka Mom Aslaaamm wacce take ta kwaɗa kiran sunan Nurayn Amrah .....A moton Amrah kuka take tana furta " Wannan sam ba so bane noory ka daina so na wannan ƙiyayya ce....! “ Da wuri haka ? , Humm ,Zaki maimata wannan Maganan taki Amrah ,Duk da kinyi shi a lokacin da bai dace ba ”. Muryar Nurain ya katse ta wanda jin haka yasa Amrah Fiddo da idanun ta tana masa Wani irin kallo na rashin Fahimta . Gani tayi ya sakin mata Murmushi yana maida Kallon sa Driving ɗin da yake yi . Noory me zaka mun ? Ka maida Ni wurin Mommy kar .....Yi mun shiru Amrah.! Ya katse ta ba tare da juyo ya kalli inda take ba . 


Itace ta haife ki Mommy Aslaam din .? Me yasa zaki ce Kada Dad ya maida Auren Ammmie Hafsat? . Wani irin kallo Amrah tayi masa Fuskarta na narkewa, hannun tasa tana share hawayen da ke Zubo mata kamin kai tsaye ta furta " Saboda na tsane ta .! Ohhhh da kyau.”. Ya furta yana yi mata wani kallo mai kama dana Rainin hankali dama ya iyasa. Lumshe idanun sa yayi yana ƙara ware su a bisa Kyaƙyƙyawar fuskar ta kana yace " Wannan ma zaki maimaita shi kuma sai kinyi kuka da idanun ki Amrah, babu duka babu faɗa rayuwar mu ce zamu sauya ma salo😎❤‍🔥.  Muryar Amrah ne ya hau Rawa na kuka mai cira , Noory ka chanja me nayi maka Ni to...? Ammie na kika tsana...! Dole ki so ta , Dole ki ƙaunace ta dole sai kinyi hakan Amra.  Dama baka da tausayi na .? Ta yi maganan tana kwantar da Muryar ta na sarewa wasu irin Zafafan ƙwallah na cigaba da Zubo mata , Shikenan ta saka Noory ya tsane Ni ...ta Furta Maganan a zuciyar ta a zahiri kuma tana mai fashe masa da Wani irin kuka na ta shiga uku....!


Kallon ta baiyi ba ya don tafiya ce ya dauka miƙaƙƙiya wanda bata san ina zai kaita ba . Bata kare mamaki da al'amarin nasa ba sai da taga ya kara daga sautin waƙar Alaan yana cigaba da Driving hankalin sa ƙwance . 

**

A wani irin gudu Na tashin hankali Aslaam ke yi da moton tuƙin ganganci a haka ya nufo layin Kanol Auwalu Ɓaidu. Ba tare da ya tsaya kallon kowa ba ya wuce kan sa tsaye cike da sassarfa da zafin jini irin nasa yana kutsa kan sa izuwa cikin gidan . Tsaitsaye ya gansu kowa cirko² ciki har da Mom Aslaam su baba Adamu da Shi kan shi Alh Tama . Mommy ina Amrah....? Ina take ...? Tana ina ..??? Ya jero mata tambayoyin a lokaci guda.  Wani irin gumi Mom ke ratso ta , sam ta kasa magana , sai Muryar baba Yusufa ne ya katse su yana cewa " Aslaaamm Amrah a ko ina take zata kasance ne cikin aminci inshallah, tana tare da mijinta Nurayn ya tafi da ita ,ba kuma musan inda ya kai ta ba . Who's that nonsense..? Waye Nurayn mijin ta ...? Ya maimaita maganan yana kallon baba Yusufu kana yace " Ba mijinta ba ne . Saurin dafa shi Daddy Tama yayi kana yace " Calm down My Son . Ka natsu kaji Zamu bincika mu gano inda ..... Dad a haka ne kuna tsaye kuke tunanin ganin sa . Ina da masters akan ilimin psychology na karance shi in and out a Maganan na yan Daƙiƙu . Wannan ya wuce inda kuke tunani , akwai abun dake Zuciyar sa , kuma it's hardly ku gan sa a sauƙaƙe . Ni ba zan jira wani ya nemo sa ba ,Ni da kaina zan nemo sa . Sannan Amrah ta gama zaman Nigeria, ana SO dole ne....? . Maganan Aslaaamm yake yi a zafafe cike da ƙunar rai wanda kamin yaji na bakin su Ya juya yana barin cikin gidan . 


Kallon su Baba Yusufu Mom Aslaaamm tayi idanun ta na kawo ruwa cike da nuna tsoro tace " Shikenn na shiga uku , Aslaaamm kar ya dawo mun da halayyar sa ta da ,wanda naga sauyi tun dawowar mu . Ki kwantar da hankalin ki Inshallah babu abun da zai faru . Cewan Daddy Tama yana kallon Fuskar Mom wanda suka fara fidda hawayen masu ɗumi . Sauke Numfashi yayi cike da hikimar sa duk da Furucin Aslaaamm ya ɗaga masa hankali yasan kafiya da naci irin nasa ,amma a haka ya danne Zuciyar sa don kar su fahimta wani Abu ya cigaba da cewa " kowa yayi karin kumallon sa kuwa ? Dan kallon kallo aka hauyi , kana su tsinkayi Muryar sa yana Cewa" Ina Larai da Baba Zuwai sune manya su fito ina son Magana dasu , yanzu kowa Na cikin gidan nan bana buƙatar ganin ya ƙara ɗaura sanwa da kuɗin jikin sa . A kira mun Zuwai da Larai . Yana Gama fadin haka ya juya yana barin tsakar gidan yayin da Mommy Aslaaamm tabi bayan sa da kallo , a Zuciyar ta tana cewa " To wai Meke shirin Faruwa ne? Nurayn ya gudu da Amrah bai damu ba . Dama fa.....Kasa kare Maganan zucin nata tayi kamin ta yi saurin juyawa tana kallon matan gidan da suke ta farin ciki da kwarara ma Daddy tama godiya . 

Ficewa tayi daga gidan tana shiga moton ta inda ta Kalli driver tana faɗa masa ya kaita gidan Daddyn Nurayn nan take .

**

Tun da suka shiga gidan Amrah ke kuka haka ta zauna a tsakiyar Falourn tana miƙe ƙafafunta tare da cigaba da rera masa kuka , amma sai gani tayi  ya juya yana nufar Wani hanya mai kaman Corridor duka wurin wani transparent Glass ne , zuuuuuuuuuuu taji ya bude tsoro ne ya kamata ganin da kati yake amfani wurin Sarrafa komai na cikin wannan gidan , a maimakon key . Yana shiga wurin ya mai da ya rufe tana zaune, fiye da Mintuna Hamsin ta kuma jin motsin fitowan sa . Kallo Ɗaya yayi mata yana kauda kan sa cikin nuna mata baƙuwar Sabuwar halayya ya furta " Zan dawo nan ba da jimawa ba . Bin bayan sa tayi da kallo sam ta kasa masa Magana tana gani ya tafi ya barta da shaƙar ƙamshin sa kawai sai Amrah tasa hannu tana fashewa da kuka tare da furta " Wayyo Ni Amrah.!

**

A hankali take saka ƙafafun ta cikin tafiyar ta irin na masu ƙiba da jikin mata Mommy Aslaaamm ta kutsa kan ta Izuwa cikin Falourn Mom Sa'adah . A tsaitsaye ta gan su wanda ko ba'a faɗa maka ba kasan Babu lapiya .  Assalamu alaikum. Ta furta tana kallon su Daddy Mommy da nusaiba wacce idanun ta sunyi lugu² Saboda Tsaban kuka . Ihu take yi tana faɗin " Mommy ki ba Ya Nurayn haƙuri Wallahi Ni kashe Ni zai yi da duka Mommy... Mommy Daddy na tuba Wallahi ina son Amrah, kar ku bari nima yayi mun irin na Naana . Jan numfashi Mommy tayi tana maida idanun ta ga Inda Mommy Aslaaamm ke tsaye . 


Kune Warhaka sannu da zuwa . Mommy ta Furta Maganan tana kaƙalo murmushin Dole . Girgiza Kai Mommy Aslaaamm tayi a sanyaye ta Furta " Ba lapiya ba zan iya ganin Nurayn?. Kallon Daddy Mommy tayi kana ta cija laɓɓan ta da yar karfi idanun ta sun yi ja , a hankali ta fara labarta masa aika ² n da Nurayn yayi ma Naana wacce ake tunanin hada auren su , yanxu haka tana gadon asibiti,bayan yayi mata dukan Tsiya ya kuma dauke ta ya kaita har Farfajiyar gidan su ya wurgar . Yanzu Familyn Naana da Iyayen ta sun ce basu yarda ba ,rikicin da ake ciki kenan . Sannan mun kan mu neman Nurayn muke yi Bamu san ina yake ba . A Halin yanzu zuciya ta ta karaya na fara yanke wa da dukan wannan al'amarin . Kawai sai Mom ta fashe da kuka tana jan numfashi da kyar zuciyar ta na mata ba daɗi . 


Innalillahi wa'inna ilaihir raji'un . Mom Aslaam ta furta tana sakin hangbag din ta tare da dafa Royal cushine din falon tana zama jaɓar akan daya daga ciki tana mai kai hannun ta tare da dafe Saman Goshin ta .

**

11:05am.

Tun da ya fita bai dawo ba har zuwa wannan lokacin , don sai da ya gama ƙaddamar da aikin sa kana ya nufo gidan inda babu kowa daga shi sai Amrah ko ma'aikata securities Duka basu fi shida ba suma iyakar su gadin wajen Gidan , don gida ne wanda aka narka arziƙi amma baiyi shi cikin mutane ba . Shigowan Nurayn yasa Amrah saurin Ɗagowa tana kallon sa . Miƙewa tayi tana bin sa da kallo cikin kuka ta furta " Noory don Allah...... Fadi maganan ki kai Tsaye. Yayi mata Maganan yana kafe ta da Sexy eyes din shi na rashin mutunci . Cikin kuka ta furta " Ka mai Dani Gida na hakura da kai Wallahi tsoro kake Bani yanxu . Takowa yayi yana isowa inda take kana yakai hannun sa yana jagowa tare da kwantar da Taffan sa bisa ƙugun ta . Kiss me😘 .....” . Ya furta Maganan yana kafe ta da idanunsa babu alamun wasa , sakin baki da idanu tayi tana kallon sa . Zaki yi ko kuwa nayi Miki? Still kina so na Amrah,ba zaki taɓa daina so na ba . Oya matso nan kusa yayi maganan yana kai laɓɓan sa tare da kama Lips din ta yana fara tsotsan mata cikin wani irin salo , Tabbas a yanxu tana jin banbanci ba ya mata komai cikin tarairaya kaman da , ya koma mata Arrogant man , wanda idan yana bukatar abu yin sa yake yi ko kina so ko Bakya SO. Hannu sa taji yana motsa ta tare da shafa gadon bayan ta zuwa Manyan Mazaunan ta Still yana wani irin mata kiss na Ƙwartanci wanda bata san shi da irin wannan halayyar ba . Jan jikin ta tayi da ƙarfi tana yin baya tare da sakin masa Sabon kuka tana cewa " Noory ka rabu Dani . Tayi Maganan tana cigaba da saka masa kuka .  


Wani irin kallo Yayi mata kana ya tako yana zuwa inda take , cikin Muryar sa na babu Wasa ya furta " kece zaki yi mun ma , bani zan Miki ba . Hummmm Dan huci ya furzar kana ya cigaba da cewa " Ina tunanin mun baby a tare dake , so idan nace zanyi zan iya takura ma bbyn mu but idan kene i will manage.  Wani irin kallo Amrah tayi masa sam ta rasa Fahimtar inda zancen nasa ya nufa . Ni zan maka mene.? Ta Furta tana ƙara narke fuska , shiiittt sex 🍌 ya furta yana kafe ta da idanun sa ,kana yace Ni zan iya taimakawa da yin romance  . Wayyo na shiga uku Wayyo........!

Yanda take masa Ihun ya kusa saka sa Dariya ta koma tamkar ba ita ba , wannan dan fuffuzgar duka ta watsar tana masa ihu iya ƙarfin ta , tamkar wanda taga Abin tsoro . Danne Dariyar sa yayi kamin yace " Ihun me kike yi haka Amrah? Kukan ki banza a wurin nan , saboda babu mai ceton ki a nan , gwara ma kiyi shiru kar kiyi ta wasting energy din ki a banza.  Kallon sa Amrah tayi kana tace " Noory me nayi maka don Allah? . Babu abun da kika mun , kawai dai ina buƙatar matata kusa dani ai ba laifi bane don na buƙaci yin hakan dake . Noory nifa ba matar ka bace a yanzu .! Haka ake auren ? A gaban kowa ka sake Ni , ta yaya zaka dauko Ni daga.....Keee Ya isa da ALLAH. Ya katse ta cikin ɗaga murya , lokaci daya fuskar sa ta Sauya .  Ke me kike taƙama dashi Amrah? Saboda ina son ki ne zaki ja mun rai ? Ko kuwa Saboda Ammie tayi Miki laifi ba zaki yafe mata ba har kike faɗin kar Daddy ya dawo da ita Rayuwar ku ? Ko kuwa don kin fahimci ina Miki makantacciyar soyayya .? Maganann yake a zafafe tare da nuna mata wani irin fushin sa wanda bata taɓa ganin yayi mata irin shi ba . Hasali ma ita gaba ɗaya ganin sa take tamkar fa bashi ba bane Nurayn ɗin nan nata . 


Jikin ta ne ya hau kyarma na tsoro don ita har ga ALLAH bata son tashin hankali . Muryar sa ta ji yana katse ta da cewa " Ba zan ƙara Neman ki ba ko wani Abu naki ba , tun daga kan ki har jikin ki , ki tsuma kayan ki kisha . Juyawa yayi fuuuuu yana ƙoƙarin barin Falourn,sai kuma taga ya ja ya tsaya yana juyowa tare da mata wani irin duba, yana mai sauke wani wahaliyyar Numfashi da ya jawo ta da kyar . Kiyi farin ciki. Ya furta Maganan ya saka kan sa tare da barin Falourn yana barin Amrah nan tsaye baki bude . A hankali Amrah ta sulale anan ƙasa kukan ma ta gagara yin ta , Motsa laɓɓan ta tayi a hankali tana furta " Wannan wacce irin rayuwa ce nake ciki Ni Amrah? . Yau NOORY ne ya da kan sa yace.....kasa ƙarika Maganan tayi Sakamakon zuwan wasu irin hawayen da bata shirya zubowa su ba . A hankali ta ja jikin ta cike da sanyi irin nata don jikin ta yayi sanyi Qlau nadama take yi akan kalamanta bisa gare sa . Ya zanyi babu yanda Zanyi da kai Noory tun da ina Son ka ..! Ta furta zancen tana saka hannun ta tare da goge Hawayen fuskar ta . Idan ka Dawo zan baka Haƙuri Ni taka ce har Abada . Tayi maganan tana mai watsa idanun ta zuwa hanyar da taga ya fice , a tunanin ta Nurayn zai dawo , sai dai kuma tasha mamakin ganin tun wannan lokacin har rana tayi sanyi Babu nurayn sai daga karshe ma Wani ne ya kawo mata abun da zata ci da hantsi. A haka har yammaci shiru babu Nurayn . Tsoron gidan ne ya kamata gani tayi komai yayi mata faɗi Still wannan Mutumin ne daya daga cikin masu tsaron gidan ya kawo mata dinner. Duk da taso tayi masa tambaya ina Nurayn amma kuma sai ba tayi hakan ba , don yanzu ta fara Fahimtar waye Nurayn da kuma zafin kishin sa ga zuciya , wannan yasa ko Magana bata yi ma secutin ba .  


Bedroom ta nufa tana Shiga ta kai tsaye ta wuce Privacy Tare da watsa Ruwa tana dauro Alwala . Bayan ta ida sallah ne ta zauna kan sallaya tana kai kukan ta gurin mahalicci na tsawon lokaci kana Daga bisani ta nufi inda ta aje Dinner din nata tana fara cin abincin don kuwa kwana biyu bata iya zama bata ci Abinci ba sam . Duk da tsoro a zuciyar ta amma a haka ta kammala koman ta tana saka Sleeping drees tare da nufar Ƙayataccen Bedroom din ta tana kwantawa .  


A hankali Ta Lumshe idanun ta wasu irin hawaye na bin Kuncin ta , To Noory zai dawo ? Ko kuwa fushi dani yayi ..? A'a dole ba zai barni ba , kila yana cikin gidan nan , kuma nasan ko mun dare zai zo inda nake don baya iya barci ba tare da Ni ba . Haka tayi ta saƙa zancen zuci a haka har barci ɓarawo yayi Awon Gaba da ita . 


Sapiyar Laraba

8:05am...

A hankali take Ware idanun ta wanda suka tasa tare da dan kumbura na Tsaban kukan da tasha daren jiya . Sauke ƙafafun ta tayi a hankali zuwa Carpet din dake gaban gadon ta . Kan ta na mata Wani irin nauyi da ciwo . Ganin Al'amarin take tamkar a mafarki yau fa tsawon kwana ki Takwas bata saka nurayn a idanun ta ba , tun wannan Maganan da yayi mata , har yau bai kara zuwa inda take ba . Ba kuma Tasan halin da Yan uwa da shi kan sa yake ciki ba . Tunanika iri iri sun adabi Ƙwaƙwalwar ta.  Tayi kukan har ta gaji, sannan ko tayi mawa securities din magana Amsan daya ne " Oga bai zo ba . Kuma Maganan haka take don baya zuwan , yana can gidan Hajiya Kaka ya tare suma sun rasa ya zasu yi da kafiyar Nurayn. 


Anyi anyi ya faɗa inda Amrah take yaƙi sai dai kullum yace " Matar shi tana cikin koshin lafiya.......! Abun da Amrah ba ta sani ba , sunan Nurayn baya cikin gidan ba kuma ya zuwa inda take ,amma duk wani motsin ta babu abun da baya gani don gaba ɗaya inda take wuri ne da ya zuba basira ta hanyar na'uran ɗaukar duk wani abu dake Faruwa yana daga inda yake yana connecting da system din sa zai ga komai . Wannan yasa zuciyar sa jin sassauci bisa ga Kewar ta da yake yi . Ya kuma saka mawa ran sa dangana, duk da yana azabtuwa da hakan , amma so yake sai Amrah ta gane kuren ta , tasan Matsayin sa da kuma Matsayin Ammie , so yake duk wani tsana ya kau na Ammie a zuciyar ta .

[9/3, 5:55 PM] Anty Aisha Mmn Teddy Marubuciya: *🛖ƳAR TSAAKAR GIDAA🛖*

Romance love and Sympathetic Story.

Post a Comment

0 Comments