TOP HAUSA NOVELS atOptions = { 'key' : '20e08520dad54dbf6d9e963271

MIN QALB 🥰 PAGE 7-8

 11, 6:12 PM] Zafafa: *_MIN QALB 7_*

_mamuhgee_



Kai tsaye change room dinsu ta nufa ta sauya kayanta zuwa na aiki ta fito tana gyara zaman qaramin Rolling dinta a wuya tana Dan yamutsa fuska tace,


Ni wannan aikinma harya Fara isata sbd wannan kayan aikin kullum mutum atakure bazan iyaba aje aikin zanyi na huta kafin daga baya zanda usi yasamomin wani yanzu dai kafin na ajiye zansamu kudinda zasu riqemu kafin asamo wani.


Tana isa reception dinsu manager  dinsu na isowa 

Shigowarsa kenan Yana waya yayi Mata hannu cewar ta tsaya yagama wayar

Wani harara tabisa dashi tana dauke Kai sbd manager dinnan nasu tafara gano take takensa akanta bazai shiga hankalinsaba sai ranar data sanfe duk wani arzikin dake aljihonsa,

'daga Masa qafa takeyi sbd kudaden datake sanfewa na restaurant Dan kullum saita diba son ranta take tafiya gida Bari tayi yaringa ji da 'daya Amma yakasa Kama kansa,


Kullum sai ayi rikici gun lissafin yanda kudi ke ba'ta Amma ankasa ganewa har so biyu ana sauya cashiers din aje kudin Amma 'yanda kasan 6era ne me satar ko clue bata bari bare amayi zargin mutum ne me satar.


Kallon qeyar kansa tayi tana sakin murmushin qeta tace"


Manager tashi aiki zakayi kwanan Nan...

Maganarsa ta kwasheta ta 'dago tana kallonsa tana 6oye murmushin gayyar datakeyi tace"


Barka da zuwa manager,

Kazo lafiya?


Washe haqora yayi Yana gyara zaman medical glass dinsa cikin son nuna shi wani ne yace"


Yawwa lfy klau amah 

Dama sbd matsalolin damuke fuskanta na 6acewar kudi a bangaren restaurant namu yasa na yanke shawarar maidaki gefen saloon sbd zamu dauki mummanan mataki akan maakatan restaurant din banason asaki acikin Abinda baima shafekiba,

Dukkaninsu maganinsu zamuyi saisun fitar Mana da 6arawon cikinsu.


Kallon Wawa taqare Masa kafin tayi fuskar marayu taredayin qasa da Kai cikin nuna maraicinta tace"


Nagode da hakan Dan ni ko yanda alamarin kudi dake gudana agurin banma saniba,

Banmasan meke faruwa a gunba da azo adauki alhakina abatamin suna kawuna ransa ya baci ciwonsama na hawan jini zai iya tashi idan yaji hadda ni acikin wainda zaa tuhuma da sata Kai Allah dai ya tsareni ya rabamu kalmar sunan satama batada Dadi.


Sake washe baki yayi ganin kamar yayi Abinda ya burgeta taji Dadi ya sake gyara tsayuwa Yana katse Kiran dake shigowa wayarsa yace"


Ai dama shiyasa naga yakamata a sauyaki saga gun sbd kada sunanki ya baci gashima Kinga Ashe kawunmu zai iya samun damuwa.


Tana qaqalo murmushi tace'


Eh dama gashi Muna fama dashi yau ciwo gobe lafiya ko tashi zaune baya iyayi" yaqarasa fada tana soke kanta kasa.


Subhanallah Ashe dai alamarin sosai ne to Allah ya sawwaqa inshallah yau ko gobe idan nabar office zanje nadubasa.


Zakasan me ake nufi da asalin sunan sata idan kaje duba kawo ka laluba kaji usi ya sanfeka tass""tafada qasa qasa tana Masa kallon sakarai....


Me kikace????


Eh cewa nayi akaini inda aka sauyamin din manager.


Yawwa muje'' yafada yanayin gaba tana binsa abaya tana sake 6ata fuska sbd Sam ita Bata wani son wani canje canje ita dake Shirin barin aikin ake Mata wani yaje Jaye Amma dai bangaren saloon din idan taga yamata zata zata Dan jima Amma yanzu babbar damuwar shine kafin ta 'dan gama gane Nan bangaren harta Fara samun damar sanfesu za'a dauki lokaci qila gashi komai nasu yayi qasa na abinci iyami kasuwancinta na Saida garin 'dan wake baya tafiya da albashinta suka dogara yanzu sai Abinda tasamo ko usi yasamo.....


Katsewa tunaninta yayi daidai lokacinda suka iso bakin qofar saloon din dake cikin blue fox din sbd wasu manyan hamshaqan Mata data hango ta cikin glass,

Sake 'daga wuyanta tayi tana 'dan leqawa tasake hango wasu 'yan Mata daga dayan gefen take tasaki ranta tana cewa"


Yauma ranar sa'atace kenan

Nakusa zamowa shiyasa Allah yasa aka daukeni daga Inda mutane basa ajiye jakarsu Amma anan dole mutum ya ajiye jakarsa tunda aiki zaa Masa,

Numfashi ta aje tana cewa"


Inshallah usi nakusa samun kudin karatunka Dan Banda buri yanzu dayafi kayi karatu sbd Kaine namiji qarfinmu zaifi qarewa akan naka kawuma ga manyanci na rufarmasa.


Tana cikin tunanin taji muryar manager na cewa"


Shikenan amah kuje ga shugabarku Nan zata baki Abinda zaki ringa yi

Sai akula please amah.


Gyada Masa Kai kawai tayi sbd tuni hankalinta yayi ciki a matse takeda tashiga ai madam bell na cewa tazo sushiga tayi gaba

Tana tura qofar glass din wani sanyin qamsh ya dameta ta lumshe ido tana qurewa gurin kallo daga sama taji madam bell na cewa"


Oya amah kije gurin anny gatacan tana sawa wata Rolex ki riqe Mata tana sawa idan kungama saikizo kiyi kallon yanda zan gyarawa waincan baqin namu qafafu.


To tace tana ajiye Jakarta a inda aka nuna Mata cikin haushi ta nufi anny din ta karbi robar Rolex din a karkace ta riqe tareda dauke Kai sbd yanda daga zuwanta ko Dan mutuntawar Nan Babu adai nuna maka Kai ba kowa bane face 'dan aiki.


Yini tayi aiki ranar sbd kowane aiki madam bell sata takeyi ayi da ita sbd ta iya gabaki daya Bata zaunaba tundatashiga gashi aranar taga asalin  ire iren Mata masu kudi wainda suke cikin kudi,

Matane sai masu arziki da wainda suka fito gidan arzikin sune kawai ke shige da fice agurin wasu na fita wasu na shiga shiyasa gabaki daya taji yanxu zatayi kudi wato ma a restaurant bataga komaiba sbd can iyajacinsu Kai abinci su dawo.

Sai yamma sosai Takoma gida a matuqar gajiye dan haka tana dawowa ta tarar ana fada hadda dambe da anty salamatu da maman basiru gasu maman junior a gefe anata qara zugawa kawu dai na zaune a shimfidarsa yaqi ko kallonsu bare ya matsa jira yake wani shegen ya fado Masa ya dauko musu motar yansanda ayi me kankat.


Kota kansu batabi ba ta wucewarta daki tana cewa'"


Allah yasa ayiwa maman basiru dukan sakwara muga qarshen qaryarta.


Washe gari ma da wuri sukaje aikin bayan ta biya cafe din kusada layinsu tabada cikon kudin scratch card din usi dazai zana waec Wanda shi baima sani ba.


Koda ta Isa gun aikin yauma Babu sauqi aiki tayi sosai ha lokacin tashi,

Kwanaki kadan tayi a saloon din ta iya aikinsu ba laifi Dan dama daurewa takeyi tana aiki sbd samun sanin Yaya kan gurin yake kafin tafaracin ubansu da halinta musamman madam bell databi ta addebeta da aiki sai janta ajiki takeyi tana yabonta ita kuwa sai sake musu kwantan 6auna takeyi Amma dai abokan aikinta sunfara sanin halinta sbd ba sauqi a tsakaninsu qaniyarsu takeci har mamakinta sukeyi yanda madam ke yabonta sbd batasan waye amah din ba.


Yau hakanan ta tashi da annashuwarta shiyasa batayi lattiba kamar yanda tasaba ta Isa blue fox din tana zuwa ta sauya cikin kayan aikinta suka hau aiki,

Customers biyu yau ta tsamewa kudi a jaka Kuma dukkansu Babu Wanda ya lura bare yagane harsuka tafi ta qirge kudinta tsaf kusan dubu goma sha biyu ta maida jaka tana cewa'


Saura dubu talatin da daya su cika kudin jarabawar usi ya Allah kabani ikon hadasu kan lokac......


Bata qarasaba wasu manyan hamshaqan Mata guda biyu suka shigo gurin tareda wata kyakkyawar budurwa tana biye dasu,


Kallo 'daya tayi musu tasaki baki tana cewa' Masha Allah da ganin wainnan hajiyoyin da hutu ya bayyana ataredasu.


Cikin gaggawa madam bell ta rude jiki na rawa take musu sannu da zuwa kamar zata kwanta su zauna akanta tsabar rawar jikin tarbonsu.


Cikin girmamawa aka wuce can qurya dasu spa room dinsu madam bell nacewa"


Welcome ma,

Welcome ma I've arranged komai da Kika bugo zakuzo kuyi in no time za'a kammala.


Suna shiga suka zauna tareda ajiye manyan jakunkunansu 

Haj Maryam dake waya har lokacin ta ajiye Tata akan kujerar bakin qofar shigowa tareda tsayawa jikin window tana sake bude muryarta gurin yiwa 'danta Salman fadan karya dawo yanxu sbd wani banzan nadin sarautar MAHMOUD dinda basuma wani San juna ba sbd ita din qanwace ga Modibbo ta Dade a gida sakamakon mijinta daya rasu shekaru goma kenan yabarta da manyan 'yaya biyu rak da nuratu da Salman din.


Umme kawai aka farayiwa gyaran sbd sanin idan haj Maryam tafara waya saita share awanni tanayi itakuma nuratu dama gyaran Kai ne zaayi Mata so tanacan guri daban.


Cikin nutsuwa anny keyiwa umme gyaran itakuma tana dudduba wayarta ahaka harsuka gama qafa daya 

Amah dake tsaye tana jiran haj Maryam tagama ita zatayiwa taja boyayyan tsoki yafi so ashirin harta gaji da tsayuwar ta Dan zauna gefe kan kujerar aikinsu kamar ance ta kalla saikuwa idanuwanta suka sauka kan jakar dake Kai wasu sabbin bunch na dubu dubu na leqota batasan sanda ta saki siriyar dariyar farin cikiba a boye tana sauke numfashin farin ciki tace"


Sa'a sa'a wlh saina fanshe zaman jirana danayi akan jakarki.


Fakaitan haj Maryam din tayi taga har lokacin waya takeyi tabada baya ta dawo da kallonta kan umme datayi nisa a taba wayarta ta 'dan matsa tana  zirara hannunta ahankali sai akan kudin ta janyosu batareda tsoroba ta cusa cikin robar hannunta ta kayan aiki saita miqe tareda ficewa.


Wani tsalle ta daka tareda kallon kudin tana washe baki tace' 


Hummm.


Cikin Jakarta tasaka kudin tareda kaiwa ta boye cikin kayanta kafin tadawo sparoom din tana wani basarwa annashuwa na fita a fuskarta Takoma tana zaman jiranta tana cewa'"


Ko darema kikai kina waya zanjiraki Dan nagama cire kudin zaman jirana.


Anny nagama yiwa umme ta miqe ta ficewarta.


Sai bayan fitar anny tagama wayar tazo ta zauna amah din tafara yimata har aka gama tas ta ficewarta.


Tsabar zumudin kudin kasa Bari tayi atashi taje gurin madam nema alfarmar tafiya gida da wuri sbd uxuri ana Bata dama ko kayanta Bata sauyaba ta tattaro su ta fito zuwa gida tana tafe tana lissafi cikin ranta fal farin ciki.


Wayarta ta fiddo tareda lalubo numbern usi taji switch off taja tsaki tana cewa'"


Dama nasani tun ahekaranjiya na lura ka Saida wayarka sbd kudin daka bawa iyatu na garinta da jarin ya karye

Karka damu kaida kawu duk saimun siya waya yau yaqarasa fada tana sakin murmushi itakadai a hanya.


Ganin napep yaqi samuwa yasa tadan Fara takawa tana tafiya a gefen hanya

Tayi nisa sosai wata qatuwar baqar mota Tasha gabanta tayi saurin matsawa tana qoqarin zubawa ko waye zagi.


Parking motar tayi aikuwa itama cikin tsananin masifa ta matso taga uban waye yake neman kassarata adaidai gabar datake ganin tayi kudi.


Cak ta tsaya lokacinda Glass din motar ya zuge tayi Ido hudu da matarda tabaro blue fox dinsu.


'dan hadiye fushinta tayi tareda 'dauke Kai zata tafiyarta tana damqe jakar kudinta.


Kudin dakika dauka nabiyoki karba ko"""""kamar daga sama taji saikar zancen ta tsaya cak tareda rintse ido tana damqe Jakarta tace'"aiko wlh banyarda Naga samu Naga Rashi bazan bayarda kudin nanba kome zaayi.


'dan qaqalo sakin fuska tayi tareda juyowa tace'"


Hajiya Dani kike???


Murmushin takaici umme tayi tareda cewa shigo muyi mgn idan bakyason Tarawa kanki abin kunya anan gurin.


Murmushi tayi tareda Dan matsowa jikin motar tayi qasa da murya tace"


Haj aini bana gudun abin kunya sbd acikinsa nake

Banda kowa Dan haka Babu Wanda zanjawa abin kunyar yi mganarki hajiya.


Kallonta umme tayi cikin tsananin qyama da mamakinta amatsayin mace ta yamutsa fuska tace"


Kudin dakika dauka nakeson kidawo dasu kokuma na miqaki hannun Yan sanda su rufeki har sai anmanta da sunanki.


Dariya amatu tasaki tareda dafe bakinta tace'


Haj canza dai Amma amatu Bata tsoron 'yansanda ataqaice Babu station dinda basusan niba.


Qarara mamakin umme ya fito tana sake kallon amatu din qyamarta na sake shigarta Dan tuni taji yarinyar ta sake fita ranta Sam Bata ko qaunar magana da ita Amma tun yanda ta lura tana kallon jakar  haj Maryam cikin kwadaituwa da yanda ta dauki kudin cikin tsananin kwadaituwa dasu da yanda take kallon kudin ta fahimci soyayyarta da kudi ba 'yar kadan bace shiyasa taqi tonata Kuma ta mayarwa da haj Maryam kudin ta biyota sbd ganin qila itadin zata iya aikinsu.

#mamuh#


_____________________

KUNA BUƘATAR A TALLATA MUKU KAYAN SANA'ARKU A PAGES ƊIN BOOKS ƊIN ZAFAFA BIYAR 2021?.


To kuzo ga dama ta samu💃🏻💃🏻.


        Ina ma'abota son a tallata musu hajojinsu a kafafen yanar gizo suke?.


Tofa kuzo dama ta samu, dan jerin gwanon haziƙan marubanku ƴan biyar sun fiddo muku da hanyar da kuma kasuwancinku zai zagaya lungu da saƙo ta dalilin shafukan littatafai.


Ga duk mai buƙatar a saka masa tallan kayan sana'arsa a shafin littatafan mu na zafafa biyar zai iya tuntuɓar waɗan nan Numbers 0903 234 5899 or 09033181070 ta vWhatsApp, idan har agama buks ɗin kana buƙata a sakamaka talla zamu saka maka akan farashi mai sauqi. Idan kuma wasu adadin pages kake buƙata koda ɗaya ne duk zamu saka maka akan farashi mai sauƙin gaske🤓.


Kuyi maza ku kawo, mai haja shike talla, mai saya kuwa shike neman sauƙi😻😻😄🤗.


______________________


#MIN QALB❤️

Mamuhgee


ZAFAFA BIAYAR


SIRADIN RAYUWA

safiyya huguma


MIN QALB

mamuhgee


YANKAN BAYA

billyn Abdul


KIBIYAR AJALI

Miss xoxo 


ABINDAKE CIKIN ZUCIYATA

hafsat rano


Pay @09033181070

Or 09032345899

[3/13, 5:49 PM] Zafafa: *_MIN QALB 8_*

_mamuhgee_


Kallon tsantsan mamaki da firgici yanzu takewa amatu din tana kallon qafafunta zuwa hannunwanta dasuka Saba dauka da zuwa stations takeyi mamakinta na qara girmama musamman shekarun amatun datake ganin bazasu haura ashirin da uku ba,


Gyara zamanta tayi cikin motar tana 6oye mamakinta tareda 'dan kallon amatun datake qara damqe jakarta sbd kudin dake ciki alamar bakin Rai take da kudin ta saki wani guntun murmushi tana nazari wani abu kafin ta kalli fuskar amatun tana cewa'"


Ta yaro Mai takeyi Bata qarko

Idan har kinawa kudi wannan son ta tabbas zan baki kudinda kaf zuriarku bazaku iya qirgasuba,

Sake kallon amtun tayi tareda sakar Mata murmushi kafin yace"


Amatu idan da zaki bude idonki ki kalli Abinda nake qoqarin yi zaki fahimci Abinda nafada bashi nake nufiba sbd danaso kamaki da yanzu kin jima da sauya kammani a cell and banyi Miki Kama da wadda kike tunanin zaki fadawa bakya tsoron yansanda,

Amatu akwai rayuwa me kyau danake Miki fatan samu Wanda zaki manta da yanda ake sata,

Zaki samu rayuwarda ko a mafarki bakiyaba tunaninta,

Zaki samu duk wani Jin Dadi da kudinda saikin rabawa 6arayi 'yan uwanki ta yanda Suma bazasu qara tuna sunan sataba.


Wata siririyar dariya amatu tayi tareda sakin jakarta datayiwa riqon Gam Gam tana gyarawa jakar zama a kafadarta tareda gyara tsayuwarta tace"


Hajiya mama Allah ne kawai zai iya cike gurbin kwadayin samu kudi danake dashi Dan gurbin me mugun zurfi ne cikesa ba qaramin aiki bane

Kiyi hkr da wannan kudin Dana dauka tunda dai kinsan ba komai bane acikin arzikin da kike dashi to Allah ki barmin kawai sbd Nima dai bazan iya bayarwar ba.


Bude jaka umme tayi tareda ciro wasu bunches din guda biyu ta miqa Mata tana cewa'"


Ungo ki hada Dana hannunki ki hau abin hawa gobe zandawo spa dinku muyi mgn.


Tana gama fadar haka tace'"


Hafiz muje.


Jan motar yayi suka bar gurin da speed me qarfi suka barta da baki a bude tana kallon kudin hannuwanta da qafafunta na rawa sbd wannan ne karo na farko data taba ganin kudi a fili haka irin Wainnan Kuma ma a hannunta da sauri ta turasu jaka tareda fadawa ckin napep dinda ya tsaya gabanta Yana tambayar Ina zuwa malama?¿


Tunda tashiga napep din take share zufan dayaqi tsaya Mata gaba 'daya kanta ya shiga lissafi Bata taba tunanin kudi irin wannan zasu rudataba duk tsananin samu kudinta dubu talatin ne zuwa qasa albashinta ma duka duka dubu goma sha uku be duk wata saina mutane idan ta sanfo Amma yau itace keda kudi dubu 'dari uku a hannunta amatsayin nata bama na sata ba""wayyo Allah" tafada tana dafe gashi.


Kasa wucewa gida tayi direct ta kalla me a daidaita din tace yabiya da ita ta bakin Luna inda tasan usi na can.


A daidaita din na tsayawa bakin Luna ko fitowa batayiba ta hango bakin gurin cike an taru Kuma daga gani rigima akeyi babba sbd har mitar 'yan sanda ta iso gurin.


Da sauri ta fito tana cewa me napep din" Ina zuwa

Ta qarasa gurin da sauri sbd hango usi da ake kokuwar sakawa cikin motar Yan sanda Yana cijewa su Kuma sai dukanda sukeyi.


Tana isa ta qwacesa da qarfi tareda shiga gabansa tana karesa tace'"


Lafiya meyake faruwa??


Cikin sa'a Allah yasa insfector falalu ne a shugaban tafiyar Wanda tunda dadewa yayi sonta Amma ganin batamasan meye rayuwa ba batada mahimmanci agareta yasa ya qayaleta Dan dole Amma Allah yagani yaso aurenta.


Kallonta yayi Yana cewa'"


Amatu kibari idan munje can office zamuyi magana saiki San Abinda yayi.


Juyowa tayi ta kalla fuskar usi da harsun fasa gefen bakinsa taji wani mugun 'daci ya sauka zuciyarta ta juyo tana cewa'"


Idan zaa kamasa meyasa sai andakesa?

Laifin meyene da bazaku Bari sai anje can dinba kafin kufara hukuntasa?


Kallonta yayi tareda matsowa yayi qasa da murya yace"


Amatu karki Bata Mana aiki Kinga mutane na kallonmu kiduba can kiga kudin me gurin Luna din aka dauke daga tuhumarsa saiya Kama fada da yaran gurin gashinan yanzu an fasa kan 'daya acikin gurin Dole zamu tafi da usi.


Akaro na farko dataji ta tsani falalun cikin fidda 6acin ranta tace"


Duk cikin wainda akayi fada dasu usi ne kawai Wanda zaa Kama kokuwa Dan shi bashida kowane?


Kinga ba anan zamuyi wannan zancen ba sbd wannan laifin babban laifine yanzu haka yaron Yana asibi antafi dashi Babu me tabbacin kozai tashi Dan haka matsa muyi aikinmu 

Ku kamasa mine.


Kallonsa tayi da sauri zata tareda yayi saurin fitowa bayanta tareda miqa kansa sbd ganin idan bai miqa kansaba zasu iya ture amatun.


Yana kallonta yashiga motarsu Yana cewa' amah kije gida ba Abinda zai faru.


Tana kallo suka tafi dashi ta dafe Kai tana rintse ido cikin takaicinl ta juya takalla gurinda akayi fadan duk jini da kwalabai an faffasa ga kujerun gurin duk ayi jefa dasu.


Adaidaita ta nufa ta fada da sauri tana cewa yabi bayan motar yansandan.


Koda ta isa station din harsun cike Masa casefile da cewa yayi attemptin kisa take a qarfafa alamarin tini sukai masa mugun duka,


Duk yanda taso ganinsa ba dama abin wannan karon yayi qamari gashi ankira asibiti yaron har lokacin bai farfadoba gashi ya rasa jini sosai haka tayita yawo tsakanin asibiti da station a yinin ranar har kusan qarfe goma Bata koma gidaba qarshe ma dai kawu yazo sukaita yawon fafutukar case din Amma 'yan sandan sun shafawa idonsu toka sunqi sauraronsu.


Sai dare sosai suka dawo gida itada kawu ko abinci bataciba ta shige daki saidai iyami tabita daki da abincin ta takurata taci kadan.


Washe gari tunda safe suka koma station din gaba dayansu harda iyami amma ko abincin dasuka kawo Masa anqi karba itada iyami suka kwasa sukaje asibiti gurin yaron sbd falalu ya tabbatar Mata da ko yaron yatashi sai iyayensa dashi sun janye qara zaa saki usi.


Kwana uku suna Abu 'daya duk wani cin hanci tabawa shegun sunkasa sakin usi ga asibiti andaura musu nauyin lalurar qaton saurayin Wanda taci alwashin cin ubansa idan ya warke.


Kwanansu biyar suna wahala kafin aka sallami kabiru din tun a asibiti taja ta tsaya ta kalli yayan kabirun da innarsu tace su janye qara tunda dai yasamu lafiya.


Qiri qiri suka qi janye karar Dan wata sabuwar rigima ta qullu tsakaninsu dasu kabirun kawu tas Saida ya 'debe musu albarka Amma sukaqi.


Station suka dawo tasamu falalu tayi Masa bayani ya kalleta bayan sun kebe kebe"


Amatu ki dage su janye qarar Nan sbd kowane lokaci yanzu kotu zaa iya tura case din Kuma wlh ana zuwa kotu gidan yari usi zaije hakan qara tabarbarewar kawai zaiyi gwara ya tsaya a iya sata kar abin yamasa yawa.


Oga falalu yanda kasan kafiran farko haka mutan Nan suke tsabar taurin Rai,

Munyi munyi sunqi janyewa ni wlh banmasan ya zanyi musu ba Dan dai tabbas bazan bari akai usi gidan yari ba akan wannan Dan laifin da Babu tabbas din shine yayi.


Amatu duniyarce ahaka 

Yanzu wainnan dakuke fama dasu Dan sunga duk kune marasa qarfi da ace case din da manya akeyinsa da yanzu case din ya mutu

Kusamu wani abu kubawasu yaron Inshallah zasu janye.


Numfashi ta sauke ahankali tace''


A rayuwa meyasa kudi sune masu mahimmanci,

Meyasa kudi zaifi rayuwar 'dan Adam mahimmanci,

Shin Dole masu kudi sune suke rayuwa yanda sukeso su huce takaicin komai a duk lokacinda sukeso.


Kiyi hakuri amatu Babu yanda zanyi be Dana taimaki Miki akan case din Nan.


Karka damu oga falalu Inshallah zasu janye badai kudine matsalar ba??daga yanzu kudi bazasu Kara zama matsalarmu ba arayuwa,

Munga mummanan banbancin da akoyaushe ake nuna Mata fificin me kudi shine mutum mukuma muda dabba duk daya,

Ako yaushe muna qoqarin taka matsayin mutane kamar kowa Amma koyaushe ana sake durqushemu Alan hakan,

To idan hakane kudi sundaina zama matsalarmu zamu nemesu ta duka hanyar data dace matuqar hakan zaisa musamu daraja kamar kowa,


Ada mun dauka maraici rashin kowa shine matsalarmu data saka bamada daraja agun mutane sai yanzu nake gano kudin dai sune komai,

Idan bakada kowa matuqar kanada kudi ko bolace ta haifeka mutane zasu bika.



Akaro na farko a rayuwarta tundata girma hawaye suka ciko idonta ta maidasu tana girgiza Kai tace"


Karka tashi aiki oga falalu zanje nazo dasu ayau zasu janye qararsu a shirya takardun.


Tana fitowa tace kawu ya jira zataje tazo da masu qarar.


Gida tafara biyawa ta dauko kudin daya rage cikin kudaden ta qirga dubu dari da talatin da shida ta zuba jaka ta fito ta fice iyami ba batasan tashigoba.


Gidansu kabirun ta nufa cikin sa'a har yayansa da innar duk sunanan suna ganinta kowanne ya tsuke fuska alamar bazasuyi Mata alfarmar datakesoba murmushin takaici tasaki tana qarasowa tsakar qaramin gidan ta zauna gaban innar tana cewa"


Inna barka da yamma,

Kabiru ya jikin?


Ciki ciki innar ta amsa saidaima kabirun ne ya amsa da sakin fuska.


Bata tsaya batawa kanta lokaciba ta ciro dubun dari ta ajiye gaban kabiri tana murmushi tace"


Kabiru maganar janye qararku haryanxu bazaku janyeba kodan ana tare...


'dan washe baki kabirun yayi Yana kallon kudin kafin ya kalli innarsu da yayansa yaga yanda Suma suke yiwa kudin kallon qurulla suna zazzare idanuwa ya kalli amatun Yana qaqalo murmushin Shima yace"


Nifa dama usi abokina ne su innane suka dage da qarfafa qarar ni dama ban riqesa ba na yafe Masa tun ranardana samu kaina.


Cikeda mamaki innar tace"


Au kabiru hakama zaka fada?

Duk Abinda mukayi badan Kai mukayisaba shine yanzu tsabar rashin godiya zakace haka

Shikenan tinda haka kace ai saimu cire kanmu muma a janye qarar tunda kaida mukeayi danka baka ganiba.


Yayansa ma matsowa yayi Yana cewa'"


Inna qyalesa yayi maganin gobe Babu shegen dazai qara shige Masa gaba idan haka takuma samunsa Nima nacire kaina zuwa zanyi yanzu na janye qarar tunda abin nasa yazama raini.


Numfashi amatu ta sauke tareda rintse idanuwanta ta bude tana qara jinjina alamarin mutane.


Miqewa tayi tana cewa to tunda dai can kayi gurin janye qarar Bari nabika muje tare Amma Bari na tafi da kudin idan ya janye saina basa yadawo muku dasu ko?? Tafada tana dauke kudin tana sakawa jaka ta zura takalmanta tana cewa''


Acikin minti biyar kudi yayi aikin dana fi sati inayi Amma sun kasa fahimtata.


Adaidaita 'daya suka shiga suna Isa station din atake ya janye qarar tabiya kudin beli da tarar me shago dubu talatin kafin aka Basu usi din sukayo gida.


Tun a hanya tafe suke cikin adaidaita Amma batace qalaba tayi nisa sosai cikin tunani,


Ta gaji da wannan masifar ta kullum suna police ko gidan yari,

Duk yanda taso Hana USI rigima takasa sbd da rigimar sukeci suke Sha suke rayuwa,

Baya tunanin kansa sai nata danasu kawu,

Dukkanin aikin datakeyi tana ajewa shine yake samo matasu shi ya gammaci rigimar Amma dai ita yafison tayi aiki,

A iya saninta usi ya fison shi yayi satar a rufesa akan tayi shiyasa yaketa shiga rigingimu Yana kawowa gidan kafin lokacin albashinta

Ga kawu maganarma ace yayi sanaa Bata tasoba sbd tsufa daya taso Masa bama zai iyaba musamman tun zamansa gidan yari wahala ta cinye Rabin qarfin qafafunsa shiyasa yanzu yake Dan fama dasu,


Babban mafitar datake gano musu ayanzu itace usi dayake namiji yasamu yayi karatu yasamu damar daukar dawainiyarsu Nan gaba itadai karatu baya gabanta shiyasa duk burinsu itada kawu ya qare akan Usin yayi karatu Amma Abu ya gagara komai sai qara lalace musu yakeyi.


Koda suka Isa gida jiki a sanyaye kowannensu yashigo ita dakinta ma ta wuce Kai tsaye 

Kawu ma haka

Usin ne dai iyami ta zaunar tareda dauko ruwan zafin data Dora na jiran tsammanin Abinda zaa dafa suci ta gaggasa Masa fuskarsa da wuyansa da bayansa dasuka kukkunbura sbd duka da tsamin dasukayi.


Haka suka kwana dukkaninsu Babu Wanda yaci abinci bayan usi da maman junior takawowa taiba yaci sbd lurada basuda abincin ci

Dama Kuma dabi'ar jama'ar gidance taimakon juna duk da irin zaman fitinar dasuke yi idan sunga juna a matsi suna taimakawa junansu sai dai idan masifar ta tashi akwana a yini anayi.


Washe gari sauran canjin hannunta dasuka rage dubu biyar da dari uku su ta bawa iyami dubu biyo aka siyo musu waina sukaci sauran Kuma ayi dubarar abinyi tayi Shirin fita aiki tasa Usin ya shirya tafadawa iyami idan kawu ya tashi asibiti zata Kai usi sbd dukkanin raunikansa sun kumbura sosai ga yankan kwalba a gefen cikinsa gwara suje asibiti tun wuri.


Ganin kudin hannunta nada dama Dama yasa suka nufi wani babban private asibiti dake hanyar gurin aikinta ta baya cikin sa'a kuwa suna zuwa ba layi aka Basu izinin shiga.


Usin ne a gaba tana bayansa fuskarta fayau ba wata walwala ayau sbd tunanin raunikan na Usin kada wata matsala ta biyo baya.


Doguwar rigace a jikinta irin ta gwanjon indiyawa din Nan sbd tana doguwa sai sukai Mata kyau gashi Dan hijabinta na iya wuya ne na uniform din aikinta.


Sanyin AC da qamshin office din yasa ta lumshe ido tareda sakin murmushi tana kallon Usi dashima dadin sanyin AC din yasashi sakin murmushi Yana kallonta qasa qasa tace"


Usi karkayi saurin bashi amsa idan ya tambayeka Dan mu samu mu more sanyin AC dinnan na kwana biyu bansamesa ba sbd banje aikiba

Kodan AC bazanyi saurin aje aikin blue fox ba.


Gyaran murya doctor din yayi sukai saurin kallon inda yake zaune cikin fararen kaftans dasukayiwa kyakkyawar fatarsa kyau fuskarsa daukeda wani sahirtaccen murmushin dayasa amatu bude baki akaro na biyu dataga kyakkyawan namiji Mai wata irin Kamala da kwarjini saidai wancan din nasu insfector Garba ba murmushi a fuskarsa saima wani irin izza Mai bada tsoro sabanin wannan da kyakkyawan murmushinsa yaqara kyakkyawar fuskarsa kyau,

Tasaba da ganin irinsu insfector Garba dasu Sargent salisu da manager dinsu dasukeda fuskoki kamar tuwon daya tashi shiyasa yanzu take ganin wannan amatsayin kyakkyawan dayafi kowa.


Fadada murmushinsa yayi har haqoransa suka bayyana Yana kallon fuskarta sbd yaji Abinda suke fada yace"


Bismillah to Nima bazan tambayeka da wuri dinba.


Sosa Kai usi gayi Yana cewa''


Kyaleta Wasa takeyi likita.


Kallonta yasakeyi akaro na hudu yana qara fadada murmushinsa yace"


To kema Bismillah zoki zauna.


Qarasowa tayi ta zauna tana kallon sunansa da aka maqala a table dinsa DR KHALIL ZABEERA.


murmushi tasaki tana fadan sunan a hankali sbd hada kalmomin Dan karatun nata sai ahankali.

#mamuh#


_________________

KUNA BUƘATAR A TALLATA MUKU KAYAN SANA'ARKU A PAGES ƊIN BOOKS ƊIN ZAFAFA BIYAR 2021?.


To kuzo ga dama ta samu💃🏻💃🏻.


        Ina ma'abota son a tallata musu hajojinsu a kafafen yanar gizo suke?.


Tofa kuzo dama ta samu, dan jerin gwanon haziƙan marubanku ƴan biyar sun fiddo muku da hanyar da kuma kasuwancinku zai zagaya lungu da saƙo ta dalilin shafukan littatafai.


Ga duk mai buƙatar a saka masa tallan kayan sana'arsa a shafin littatafan mu na zafafa biyar zai iya tuntuɓar waɗan nan Numbers 0903 234 5899 or 09033181070 ta vWhatsApp, idan har agama buks ɗin kana buƙata a sakamaka talla zamu saka maka akan farashi mai sauqi. Idan kuma wasu adadin pages kake buƙata koda ɗaya ne duk zamu saka maka akan farashi mai sauƙin gaske🤓.


Kuyi maza ku kawo, mai haja shike talla, mai saya kuwa shike neman sauƙi😻😻😄🤗.


______________________


#MIN QALB❤️

Mamuhgee


ZAFAFA BIAYAR


SIRADIN RAYUWA

safiyya huguma


MIN QALB

mamuhgee


YANKAN BAYA

billyn Abdul


KIBIYAR AJALI

Miss xoxo 


ABINDAKE CIKIN ZUCIYATA

hafsat rano


Post a Comment

0 Comments