TOP HAUSA NOVELS atOptions = { 'key' : '20e08520dad54dbf6d9e963271

'Yar Tsakar Gida 3 page 26-27

 Amrah kece haka.? Zaid yayi maganan yana kallon yanda ta haye sosai . Murmushi Amrah tayi Yayin da Nurayn ya furta “ Amrah na fama da Nauyin jiki amma an kusa ai ko ? Ya kare maganan yana kallon Amrah.  Murmushi ita dai Amrah tayi bata ce komai ba . Yayin Nusaiba ta katse tana cewa " Nifa nazo ne nagani don ina zaune nace Momy Bara na leka Amrah kila fa ta haihu . Dariya suka saka duka harda Amrah . Zaid ne ya katse su da cewa “ Lallai har yanzu Nusaiba da yarinya ce ke , Amrah ba'a faɗa maku ba . Humm Ya Zaid kenan baka san Waye ya Nurayn ba , zai fa iya ta haihu yaki faɗa na kwana biyu yace bai so a dame ta . Dariya Nurayn yayi yana cewa " Kaman kin san abin da nake tunani kenan , saboda hayaniyar nan da baby zata ji ko da jikin ta . Humm masu mata wannan kulawa haka .? Cewan zai yana masa dariyar shakiyanci . Muma dai Bara muzo muyi auren nan don nurayn kwanan zaka zama Daddy . A'a ka zauna dai . Nurayn yayi maganan yana murmushi . Muryar Amrah ne ya katse tana cewa " A'a Ya Zaid waxa ka Aura.? . Kallon Nurayn Zaid yayi yana masa Alama da ido . Kawai sai nurayn ya fara dariya yana cewa " Wannan to gashi nan dai ƴammata n nasa Ni dai Baga daya da yace zai aura ba ,amma ban san Ni ba yanzu ...wacece ciki Meema ko Nafee ko ....A'a Noory ba wanda zai Aura a cikin su , Ni da fa Nusaiba nake so ya Aura hakan zaifi kaji ya Zaid. 


Ɗauke wuta duka sukayi har da nusaiba . Wanda ganin haka da sanin waye yayyun nata yasa ta cewa " Kai Amrah zaki ja mun cin mutumci ina zaune lau , Nima ina da Wanda nake so . Wani irin dariya Zaid da nurayn suka kwashe dashi , don Dai Nusaiba tasan Zaid ba tsaran ta bane ko ƴammatan shi b Ajin ta bane sun ɗaran mata . Kici² tayi da fuska ...wannan yarinyar zan Aura Amrah , a hannuna aka haife ta , wai ma ta isa Aure ne .? 


Idon Nusaiba ne ya kawo ruwa , miƙewa tayi kunsan ta da fushi tana ɗaukar jakan ta . Dama na faɗa Miki cin mutunci zasu yi mun . Sai Anjima dadin Abin Nima baka mun ba . Ƙarya kike yi Nussy romantic guy kama na Kice ban Miki duk samarin ki babu kamana kin san dai nasan su ko.? Kallon su ba tayi ba , Amrah ne take fadin Nusaiba don Allah ki dawo ki rabu dasu....Amma ina Nusaiba fa  tayi gaba . Miƙewa Zaid yayi cikin sauri yana ɗaukar Keys ɗin sa . Bara na maida ta gida,amma Amrah kin kawo shawara matsalar haukar Autanci ke dawainiya da ita . Murmushi Amrah tayi tana faɗin yauwa Ya Zaid ka rarrashe ta ,don Allah kar ka tsokane ta irin yanda ka mata yanzu. An gama Matar Boss . Yayi maganan yana kallon nurayn. Murmushi Nurayn yayi yana faɗin " Wai tafiya zaka yi ?. Aaa dole na naje na Rarrashi Babyn Momy kar ina zaune yanzu naga kiran Mommy . Dariya suka sakawa yana ficewa daga Falourn cikin sauri kar nusaiba ta bar gidan . 

A farfajiyar gidan ya tadda ita drivern ta na kokarin buɗe mata moto . Ammm kana ji dakata . Cewan Zaid yana takowa zuwa inda suke . Kallon nusaiba yayi wanda Fuskar ya duk ya kacame da hawaye idanun ta sunyi luhu² . Ka bari Ni zan kawo ta kai ta fi . wane babu inda zai tafi wato na koma ku cigaba da faɗa mun magana kuna mun dariya kawai sai ta cigaba da kuka har da shashaƙa . Ohhhh I'm sorry Nussy wasa fa nake yi shima nurayn wasa yake Miki , Ni na isa nace bana son ki ? . Waye kake son ? Don Allah Ni dai ka rabu Dani Ya Zaid ai nasan ƴammatan naka sun fini to dama Ni wai ma meyasa Amrah tayi hakan . Abun dake zuciya ta ne ta gani wanda Ni kasa fadi sai kuma ita ta faɗa.  Kallon sa Nusaiba tayi cike da mamaki kana yace " Eh Nusaiba ina son ki ba wasa ba. Su kuma girlfriends dina wannan soyayya kawai na shan minti yanda kika sani bana aure ba . Kece zan Aura don haka ki aje tunanin bana son ki ,ina son ki , kuma nasan kema kina Sona ,idan bakya Sona a hankali zan saka ki soni zuciyar ki ta amince da hakan . 


Kana so na fa kace ? Wannan ba gaskiya bane ya Zaid kullum tsoka na ta kuke yi kaida Ya nurayn sai yanzu kace kana so na ..? Tsiwan ki nake so da duka komai naki ma . Yayi maganan yana Tsokanan nata . Shiru tayi tana kallon sa , kana yace " Nusaiba Munyi rayuwa nasan fiye da yanda nurayn ya sanki ya kuma san halinki saboda Nine kike kawo ma ƙaran duk wani da yayi Miki ko mukayi miki kaman haka dai , kin san me yasa nake jin son ki , saboda tare muka yi rayuwar America kina rawar kai amma baki taɓa lalata da kowa ba . Rayuwar ki ya burgeni, Muje moto muyi magana ". Kallon drivan tayi a Tsiwa ce tace " to sai ka tafi tun da duk ka gama jin abin da zaka ji😹 . Dariya Zaid yayi yana kai hannun sa tare da Amsan jakar Hannun ta , Murfin motonn ya bude mata tana shiga ya rufe yana komawa mazaunin nasa tare da yin horn yana barin cikin gidan . 


Haɗa Ido Nurayn da Amrah suka yi yayin da Amrah tace " Noory kaga Abin da na gani kuwa .? Dariya ta bashi hakan yasa shi murmushi yana cewa ' Ni ban ga komai ba . A'a noory ka gani mana jaka fa ya riƙe mata hummmm Su Ya Zaid manya . Amma noory gaskiya ya kamata ko Idan Nusaiba ta yarda ayi Auren nan kamin na haihu . Kafe ta yayi da ido kana mata alamun kiss 😘 da labɓan sa , itama yi masa tayi tana ɗariya ne taji Muryar sa yana cewa “ Dadi na dake Hauta I like you . Hummmm ta gimtse Fuska tana juyawa ciciɓi² irin tafiyar masu juna biyu . Amrahn Noory baki ce komai ba .  Like You too ..... I love you ....! Share sa tayi don ta san idan tabi tana sa to sai su ɓata lokaci a haka yana aikin tsokanan ta ya kuma nace mata . Ko tayi fushi sai yasa ta sauka . Rayuwar su abun burgewa. Hohoho ALLAH sarki rayuwa wai kun tuna Amrah kuwa ?? Kun tuna da rayuwar su na ya makaranta? Yau gasu a lemar aure matsayin mata da miji masu ƙaunar junan su da Bama junan su kulawa. Ni kaina burgeni suke🤪 .


Tun daga wannan rana soyayya fa tayi karfi tsakanin Nusaiba da Zaid don ba'ayi sati biyu ba Iyayen Zaid suka zo neman Auren Nusaiba inda aka basu tare da tsaida lokaci ba mai tsawo ba . 

Ana haka ne Amrah ta haife yaran ta yan biyu masu matuƙar ƙyau kaman su kaman mahaifin su nurayn mace dana miji . Namijin sunan sa Rohaan ita kuma macen aka sanya mata Daneen . Mashaallh abu sai hamdala yara sun ga gata mai jego taga Gata ta bangarori daban daban . Mom Sa'adah kuwa kaman zata zuba ruwa ƙasa tasha don farin ciki . Ƙyautar ta ga mai jego har da mukullin moto kayan jirarai kuwa motonn su guda shima anan aka bar motonn na mejego ne . Fadin farin cikin da Nurayn yake a wannan lokaci ba'a magana . Su baba kanol wuuuuuu hummmm mun ga arziki an kuma barin sa . Ammie Hafsat Allahu Akbar har da kukan farin ciki haka ta Rungume yaran nan duka ajikin ta . Anan Amrah kuka ita kuka ,abun nasu duka abun tausayi ne da kuma muce Alhamdulillah . 


Bata yi wata biyu da Haihuwa ba cikakke Nurayn da Amrah suka ɗaga zuwa ƙasar Switzerland don Hutawa na musamman da yawon bude ido wanda basuyi ba lokacin Amarcin su . Kwana ki talatin suka yi suka dawo don Auren Zaid da Nusaiba wanda Alhmdlh aure ya dauro amarya ta tare gidan mijin ta kula da soyayya ba'a magana . Komai kam sai dai muce Mashaallh . 


Fitowa Mom Aslaaamm tayi tana zama gyefen sa tare da kai idanun ta tana leƙa wayar hannun sa inda yake chart da ƴammatan sa . Humm da dai Auren kayi ka huta da ɓata lokaci . Ga ƙanwar ka nan da yara har biyu . Kallon Momyn sa yayi yana cewa " Kin manta ga Zulai nan da su Hajara har yanzu basu yi Aure ba ,kamata baba ya auran dasu sadaka . Na shiga uku .! Cewan Momy aslaam tana kai masa duka . Laifi na dana tsaya magana da kai . Takare maganan tana mikewa tare da nufar falon tsakiya . Dariya Aaslaam yayi yana cewa" Ba gashi yanzu kin bani Wuri ba Momy . Muna nan inshallah zamuyi auren nan ba da jimawa ba . Suma ALLAH Ubangiji ya basu Mazaje na gari .  Ita kuwa dai baba Zuwai a yanzu an koma sayar da kunu da La'asar rayuwa kenan dama duk abin da mutum ya shuka wallahi sai ya girba ko yaki ko yaso. Allah ka Bamu ikon aikata alheri Amin.


Bayan wasu shekaru . 

Ina wasa dake ne Daneen...? Ba zaki bani ba ...? Naji Muryar Amrah ya katse Ni da nake kutsa kaina ixuwa falourn . Da gudu naga Daneen ta sauko hannun ta dauke da Wayar Amrah wacce take saukowa daga stairs din tana biyo bayan Daneen . Rohaan ne yayi karaf yana riƙe Daneen tare da cewa “ Mommy na kama Miki ita bata da kunya yarinyar nan ,kuma Daddy ne ke goye mata baya , ita wai ga Daddy girl . I'm not a girl Rohaan stop it . Baka ji me Daddy yake ce kun Young lady . Sakin baki nayi ina ƙare ma Daneen kallo yarinya wacce bata fi shekaru Bakwai ba take da wannan iyayen , hummmm ko da yake su nusaiba ne iyayen ai😹 barewa batayi gudu dan ta ya rarrafa ba . Takowa Amrah tayi tana faɗin kama mun ita ai yana can Resting room da  Azmi a hannun sa sai na yi maganin rashin kunyar nan naki yau...kin san Meye lady ma kuwa ƙwailan ki dake . Kuka Daneen ta fashe dashi tana sakin wayan a ƙasa da gudu tana nufar Resting room tare da nufar inda Nurayn yake , yana nan Tsayayyen namiji Arrogant ya tara ƙasumba dai dai yayi dan ƙiba ga wani yar tumbi da ya saki . Har a lokacin bai kai 40 ba . Ihun ta yasa shi saurin kallon Hanyar shigowa cike da rashin ƙwaɓo don ya sargantata sosai yar gatan sa ce ko a school sunan Daneen Daddy's Girl. Faɗawa jikin sa tayi tana fashewa da kuka tare da cewa " Daddy Mommy ne . Mommy ...! Ya furta yana kai hannun sa cikin sauri tare da Rungume ta a jikin sa . Rarrashin ta yake yi tare da cewa " Laifi kika yi ka momy ko.? Gyada masa kai tayi alamun eh kana cikin shashsheƙar kuka irin na yara tace " Game nake son yi a phone Din ta Daddy kuma ta hanani wai Rohaan zata ba saboda ɗazu ya taya ta aiki Ni kuma bana son aiki Daddy ciwo nake yi. Murmushi yayi don yasan ƙiwuya ne da ita ,halin Daneen sosai yake dauke masa kewar nusaiba tana yarinya shi kam Rohaan Haka yake da Mom Sa'adah a lokacin yarintan sa . To yi shiru kiyi barcin ki zan samu Mommy Anjima zata bata ki wayan . Wani wayan ai ta kashe mun yanzu . Yau kuma sai na zane yarinyar nan . Muryar Amrah ya katse sa wanda ta dauko Bulalan chaji wai zata bugi Daneena . 


Tsayawa nurain yayi yana kallon ta kana Daneen ta ƙara shigewa jikin sa a tsorace . Hade giran sama yayi dana ƙasa yana cewa " Na faɗa Miki Daneen Bata isa duka ba ,kar ki Kuskura koda wasa ki buge mun Daneen . Jin haka yasa Daneen mikewa da gudu tana barin Resting room ɗin . Kallon sa Amrah tayi tana daure fuska tare da yarda bulalan ƙasa . Murmushi yayi yana aje  Azzmi a kujerun sa tare da miƙewa yana takowa zuwa inda take . Kauda kan ta tayi gyefe yana tsayawa Amrah na Fushi kike yi ? . Wani kallo tayi masa tana cewa " Dama kullum sai mun yi faɗa da kai har yanzu . Dariya yasa yana kai hannun sa tare da sakawa a tsakiyar Nonuwan ta yana karkaɗa mata Amrah Amrah Amrahn Noory....yayi maganan yana jan ta Tsokana . Don dole ta sakin masa dariya tana faɗin " Meye haka Noory ka bari yanzu fa mun fara girma . Waye fara girman ? Shekaran ki nawa suke yar Yarinyr ki dake ALLAH ya baki yaya a sama har uku . Kallon sa tayi zata yi masa magana taji ya rungume ta yana haɗa bakin shi da nata yana Tsotsan laɓɓan ta hannayen sa yana zura su cikin ƙirjin ta yana wasa da nonon ta . 


Ke Daneen baki sa hankali ko ? Mommy fa tayi fushi dake yau kin lalata mata waya. Gashi ke bakiyi game din ba nima ban yi ba. Mommy tayi fushi sosai ne .? Daneen ta katse Rohaan . Of course yes . Kije ki bata haƙuri . Kice momy sorry ba zan ƙara ba . to muje tare sai ka tayani bata Haƙuri. Riƙe mata hannu Rohaan yayi yana cewa muje to . 


A hankali suke raba bakin su kana ta juyo saurin kallon Su Rohaan tayi wanda suke tsaye suna kallon su . Kai me kuke yi anan .? Mommy sorry..... Sorry Kuma.? Ta maimaita tana kallon Nurayn Wanda yake bin bi da murmushi, wai noory me suke nufi yaran nan. Haƙurin mene kuke bani , bana ce idan zaku shigo wuri kuna taking escuse  ba babu  sallama kun faɗo kuma kun tsaya kuna kallon mutane . Momm sorry laifin Rohaan ne . Cewan Daneen kamin tace " Hakuri yazo tayani na baki . Amma kika ce kuma laifin sa ne Amrah ta katse ta . Jin Hannun Nurayn tayi yana rike nata tare da matsa mata dan yatsan ta a hankali . Yana kai Fuskar sa tare da shaƙar ƙamshin ta yana kai hancin sa zuwa saman wuyan ta a hankali yake kissing ɗin ta . Woww 😍 Cewan Daneen Tana ware ido tare da hade hannayen ta irin na yaran nan masu Azaban wayo . Rohaan Daddy love mommy so much . Janye jikin ta Amrah tayi tana masa Wani irin kallo kamin tace " Halin ka halin wannan Yarinyar dukan su basu da kunya . Dariya Nurayn ya hau yana furta haƙuri fa suka zo su baki . Yayi maganan yana riƙe hannun ta juyowa tayi tana kallon sa kana taga ya daga mata Gira yana furta " I love You forever . We love you Mommy forever Muryar yan biyun nata ya katse su Rohaan da Daneen . Murmushi Amrah tayi tana ware Hannun ta tare da rage tsawon ta da gudu duka suka faɗa jikin ta tana Rungume su . Kusan mintuna biyu kana ta ɗago tana kallon Nurayn a hankali idanun ta suka fara zubo da hawaye na farin ciki da ganin abun Allahnta . Nurayn ta kira sunan sa Wanda a yau shine rana na farko a rayuwar sa wanda ta taɓa kiran sunan sa dai dai yanda yake . My lab . Ya furta yana kallon fuskar ta tare da kai taffan hannun sa duka biyun yana shafa Kuncin ta da hawayen dake bin Kuncin nata. A hankali ta motsa laɓɓan ta tare da cewa “Na gode.....! 



Tammat bi hamdulillah.

Alhamdulillah

Alhamdulillah 🙏🏻💃🏼 done and dusted.


A yau na kammala maku wannan littafi nawa na yar tsakar gida na gode na gode sosai da Soyayyar da kuka nuna mun a wannan littafi ALLAH Ubangiji ya bar zumunci ya ƙauna. Taku har kullum mai maku fatan Alheri har abada Aysha Mamanteddy. Sai kuma mun haɗu a sabon littafi na gaba wanda zai zo maku very very soon.....💃🏼 . 


To masoya na mabiya wannan littafin kaɗai nake so suyi mun comment base on this novel Yar tsakar gida . 


Na daya ☝🏻

Mene ne abun da ya ƙayatar dake a cikin wannan littafi na YAR TSAKAR GIDAA.? 


na biyu ✌🏻

Wani faɗakarwa kika ɗauka a cikin wannan labarin nawa na ƳAR TSAAKAR GIDAA.?


Na uku 🤟🏻

Wani abu ne ya ɓata Miki rai game da labarin ? Manufa na wani wuri ne kika so ace ya kasance yanda kika so amma kuma sai ban yi hakan ba . 


Na hudu 👌🏻

Ina so ko wannen ku ya faɗa mun kallon salon labarin da kuke na gaba . Kaman Irin ace Sympathetic Story ko sexy story ko Romantic story  . Sannan ina so muyi labarin na gaba ne base on how Nigeria is now......👺komai a faiyace so i need your loving and support , zan yi hakan ne a yanayin yanda kuka yi sharhin ku . Don haka koya kika ga labari na if You're interested just read it , don komai ina yin shine with my experience ba labarin Gizo da ƙoƙi nake yi ba , faɗakarwace da kuma halin da muke ciki nake haskawa na nuna don haka Ni baƙuwar sanyi ce a wani lokaci amma idan kika yi la'akari da sunana Aisha kar kiyi tsammanin zaki faɗa mun na kasa mai da Miki , social media nake kika kun zanci uban ki .....Wallahi wallahi wallahi rantsuwa uku nayi inada fara'a da haba haba da jama'a amma bani da kirki ga wanda bai san kirki ba . Don haka kowa yayi zagi a kasuwa yasan da  wanda yake yi , riƙe alƙalamin ki in riƙe nawa that's is best solution idan kunni yaji gangar jikin ya tsira ko nace kin tsira daga tijara na 😏☹️ . Bari mu dawo kan hanya  ya labarin yar tsakar gida ya ƙayatar dake ko kuwa akwai inda bai Miki ba just feel free and told me, I don't have any with you my people maman teddy taku ce 💯 .


Na ƙarshe kuma wani irin fatan alheri zaki mun addu'a kawai nake so daga gare ku idan ba damuwa . Sannan wannan maganan da nayi zaku iya yin sa ta comment GRP wanda basa GRP kuma na Comment zasu iya mun magana private ,haka akwai wanda basa da ra'ayin magana a comment section Suma zasu iya mun magana private a kowa Ni lokaci , Before I start my new novel .  Lab You all🥰.


    *Anty Aysha Mamanteddy*

Post a Comment

0 Comments