TOP HAUSA NOVELS atOptions = { 'key' : '20e08520dad54dbf6d9e963271

SAKAYYAH page 70

 Haka dai yinin ranan Didi suka yini da ita kana suka kwana Asma'u kuwa sai da Dr Jameel ya gama duty inda suka tafi tare da barin Dr Esha.


Washe gari da sassafe Asma'u ta zo hannunta riƙe da wani madaidaicin Basket Dake ɗauke da Warmer masu kyau bisa ga duk kan alama abinci ne tayi kana kafadarta maƙake da waya ta ƙara sa shiga ɗakin alamar waya take yi sai kuma tace.

“Eh Ummi gata nan ma yanzu na shigo”.

Ta ƙare maganar tare da miƙa wa Khausar wayar kana ta ajiye Basket ɗin hannunta tana mai gaida Moddibo dake magana da Dr Jameel.

Khausar kuwa cikin sanyi tace.

“Ummi” 

Cike da kulawa Ummi tace.

“Khausar lafiya dai kike jin jikin ki ba abinda yake Miki ciwo?”.

Kai ta gyaɗa kamar tana gabanta tare da cewa.

“Ummi ba abinda. Yake min ciwo fa”.

Cikin jin sanyi da tausayinta Ummi tace.

“Toh Allah ya rabaku lafiya ”.

Tana ɗan lumshe Idanunta ta gyara zamanta tare da cewa.

“Ameen ya Allah Ummu kuyi min addu'a”.

“In sha Allahu muna miki kuma zamu ci gaba daya miki yanzu ma mukayi waya da Momynki tace min yanzun jirginsu zai tashi”.

Juyawa Khausar tayi ta kalli agogon wayanta tare da cewa.

“Yanzu ma ai sun tashi tun da gashi har tara da rabi kuma tara dai-dai ma jirginsu ya tashi”.

Cikin sauƙe numfashi Ummi tace.

“Toh Allah ya kawo su lafiya”.

Ameen ta amsa suna cikin waya da Ummi taga kiran Hajja Nana ya shigo ta wayarta cikin sauri ta miƙa wa Asma'u wayarta kana tayi picking nata takai kunnenta atake muryan Hajja Nana ya ratsa kunnenta tana cewa.

“Khausar”.

Ahankali Khausar tace.

“Na'am”.

Cike da so irin na Kaka da Jika Hajja Nana tace.

“Ya jikin naki?”.

Tana ɗan lumshe Idanunta ta gyara zamanta tare da cewa.

“Da sauƙi”.

Cikin sauke ajiyar zuciya Hajja Nana tace.

“Jiya mukayi waya da Momy take cewa baki jin daɗiba ma tana kan hanya zata zo”.

Kai ta gyaɗa tana kallon Asma'u dake cire warmers cikin Basket tace.

“Eh lafiya lau ba abinda ke damuna Hajja Nana amma wai ance Theater za'a min”.

Cikin son kwantar mata da hankali kana da son sama mata nutsuwa tace.

“A'a kada ki damu ki kwantar da hankalinki ai Theater ba abinda yake yi nima in Sha Allahu da izinin Ubangiji zanyi ƙoƙari in zo”.

Murmushin tayi cikin jin daɗi ta gyara zamanta tare da cewa.

“Allah ya kawo min ke lafiya Allah yasa ki same ni araye”.

Cikin rashin walwala Hajja Nana tace.

“Wani irin magana ne wannan in Sha Allahu ma araye zan sameki kar ki karya min zuciya”.

Murmushi tayi tare da faɗin.

“Toh Allah ya kawo ki lafiya”.

Ameen ya Allah ta amsa kana sukayi sallama.

Kallonta ta mayar kan Moddibo dake riƙe da hannunta cikin rauni yace.

“Kina so ki karya min zuciya ko Minha? wani irin kalma ne kike faɗa haka”.

Ɗaya hannunta ta ɗaura akan nasa tare da cewa.

“Bakomai Yah Mu'allim”.

Dr Jameel kuwa kallon Asma'u dake tsaye gefensa yayi wacce tunda ta cire Warmers cikin Basket bata zauna ba yace.

“Toh ki zauna mana”.

Ahankali tace .

“Toh bari in sa mata abinci”.

Idanunsa ya zare tare da cewa.

“Dear wa yace Miki idan za'a yiwa mutum Theater yana cin abinci ai baza taci abinci ba sai bayan an fito da ita”.

Kallonsa Khausar yau cikin langwaɓar da kai tace.

“Kuma wallahi yunwa nake ji Dr”.

Idanunsa akan Asma'u yace.

“Ki ƙara haƙuri in Sha Allahu ana fito dake ba daɗewa zaki samu ki ɗanci wani abu”.

Rau-rau tayi da Idanunta tare da faɗin.

“Toh shikenan”.

Bayan zuwan Asma'u ba daɗewa Niyna da Innayi suka iso wanda hakan yasa Didi ta samu ta koma gida tayi wanka ta sake shiryawa.


 12:30pm dai-dai suka fito da niyyar komawa Asibitin wanda kuma yayi dai-dai da Jirginsu Ummu ya kusa sauƙa hakan yasa tace da Ibraahim dake driving ya wuce da ita Airport kana sai motar Hadimai dake biye dasu wanda sun kai huɗu motar Ajere-Ajere suke tafiya motar Hadimai ɗaya agaba saina su Didi sai kuma sauran ukun abaya ƙarfe 1:05pm dai-dai suka shiga cikin airport Akuma dai-dai lokacin jirginsu Momy yayi Landing.


Bayan Fasinjoji sun fiffito Momy ta fito hannunta riƙe da Raudhat yayinda wani yaro daga cikin ma'aikatan wurin ke gabanta da troling su.

A hankali take tafiya tana  ɗan jujjuya ido alamar tana neman ta inda zataga fuskantar da ta sani, sai kuma tayi saurin juyawa jin Raudhat na cewa.

“Oyoyo Didi Yah Ibraahim Oyoyo”.

Murmushi Momy tayi kana tace.

“A'a gasu can ma”.

Ibraahim kuwa sunkuyawa yayi tare da buɗewa Raudhat hannu da gudu tajeta ta rungumesa tare da cewa.

“Ina Addah Khausy?”.

Yana ɗan Sharking ɗin hannunsa acikin nata yace.

“Addah Khausy na asibiti”.

Cike da zumuɗin son ganinta tace.

“Toh mu tafi inganta ina son ganinta ”.

Miƙewa yayi tana riƙe hannunta yace.

“Toh shikenan ”.

Cikin sassarfa Didi ta rungume Momy tare da cewa.

“Momyn Khausar Barka da zuwa”.

Fuska ɗauke da Murmushi Momy tace.

“Barka dai ya mai jikin?”.

Suna tafiya Didi tace.

“A'a Alhamdulillah mai jiki tana can anata hira da ita amma yanzu nan da minti arba'in za'a shiga da ita sai muyi ƙoƙari mu tafi asibiti kafin a shiga da ita”.

Momy ta gyaɗa kai tare da cewa.

“Toh shikenan”.

Daga nan suka shiga motoci Madadin su wuce gida kai tsaye asibiti aka wuce dasu.


Dai-dai lokacin kuma Lalla Khadijah da Rahma ne da Asma'u ke tare da Khausar, cikin kulawa Lalla Khadijah ke kallon Khausar ɗin jin yadda tayi mgnar a yunwace.

“Ayyah Rahma kije ki tambayi Dr Jameel, zan iya shan tea ne”.

Cikin kula Rahama tace.

“Ai ɗazuma naje Lalla Khausar cewa yayi ki ɗan ƙara haƙuri”.

Gyara zama Lalla Khadijah tayi tare da cewa.

“Kiyi haƙuri ko Khausar ba komai zuwa yamma dai zaki samu kici wani abu”.

Ɗan kwaɓe fuska tayi tare da kallon Asma'u dake cewa.

“Toh ni bari inje in kira Dr suzo su shiga suyi mata mana ta samu taci abinci”.

Ta ƙare maganar tana fita.


Su Momy kuwa da Didi tafe suke suna hirarsu, duk da dai duk karfin hali suke.

Raudat kuwa sai surutu take zubawa Ibraahim.


Acan asibitin kuwa lokacin da Asma'u take ta kira Dr zuwa lokacin 1:30pm yayi, haka yasa suka fara shirya komai, nan da nan suka gama shirya komai da komai na asibiti kasancewar ƙarfe 2:00 dai-dai za'a shiga da ita ahankali Dr Eshaa ta shiga ɗakin hannunta riƙe da wani riga da hula irin wanda ake sawa idan za'a shiga da mutum ɗakin C's miƙa mata rigar tayi tare da cewa.

“Gashi zakisa wannan ɗin”.

Kai Khausar ta gyaɗa tare da karɓa kana ta juya ta kalli Moddibo cike da tarin ƙaunarta da kuma tausayinta Moddibo yace.

“Insa Miki ne?”.

Langwaɓar da kanta tayi tana rau-rau da Idanunta tace.

“Nikam tsoro nake ji zuciyata bugawa take Yah Mu'allim”.

Kamota yayi kana ya ruggumota jikinsa cikin wata amintacciyar murya mai cike da jin ƙai da tausayi yace.

“Bakomai Minha, ba abinda zai sameki sai alkhairi kinji ko Minha”.

Ya ƙarashe Maganar cikin sanyi haka nan yake jin jikinsa ya mutu kana zuciyarsa na tsinkewa ya rasa mai yake masa daɗi a duniya.

Ganin haka yasa Dr Jameel da Dr Eshaa juyawa suka fita Ahankali Asma'u ta yunƙura da niyyar fita da sauri Khausar ta riƙo tsintsiyar hannunta tare da cewa.

“Asmeey ina zaki je?,Ki tsaya mana”.

Cikin rauni da karyewar zuciya Asma'u ta kalleta kana tace.

“Khausar abinda kike faɗa yana tayar min da hankali ance Miki bakomai a Theater Nan Amma sai wasu maganganu kike masu tarwatsa lissafi da hargitsa mana nitsuwa”.

Araunane ta sunkuyar da kanta tare da cewa.

“Toh ya za muyi da abinda Ubangiji ya tsara mana Asma'u”.

Cikin ƙarfafa mata gwiwa tace.

“In sha Allahu Alkhairi Ubangiji ya rubuta mana”.

Kallonsu tayi sai kuma tace.

“Hmmm Allah yasa”.

Asanyaye Asma'u tace.

“Ameen”.

Shiru ɗakin yayi na wasu mintuna katse shirun Khausar tayi ta hanyar cewa.

“Gashi kuma har yanzu Momyna bata zoba”.

Kallon time Asma'u tayi tare da faɗin.

“Ai zata zo kafin a shiga dake in Sha Allahu yanzu naji Didi na waya da Innayi tana cewa sun taho asibiti”.

Sake jingina bayanta da jikin Moddibo tayi kana tace.

“Allah ya kawo su lafiya ta ganni inganta koda ma na karshene waya sani!?”.

Cikin sauri Moddibo ya sake janyota jikinsa ya rungumeta haka nan yaji wani irin rauni tausayi jin ƙai baisan lokacin da shesh-sheƙan kuka ke taso masa daga ƙasa ba yace.

“Minha meyesa?”.

Kai ta girgiza tare da cewa.

“Bakomai fa Yah Mu'allim”.

Haka yaita rarrashinta tare da kwantar mata da hankali yace.

“Bakomai Minha babu abinda zai sameki sai alkhairi lafiya za'a shiga dake afito dake lafiya”.

Ɗan Murmushi tayi tare da cewa.

“Ameen Yah Mu'allim in Sha Allahu ya Mu'allim na daina damuwa amma ina neman yafiyarka iya tsawon rayuwar da mukayi tare tun daga makaranta har zuwa dana kasance ƙarƙashin Inuwar Aurenka idan akwai abinda nayi maka ka yafe min kayi min aikin gafara”.

Cikin sauri ya sake ƙanƙameta ajikinsa kana yace.

“Babu abinda kika yimin Minha.

Ni kuma me zakiyi kin aduniya Ni babu abinda kika yimin kuma koma akwai na yafe miki duniya da kiyama”.

Kanta ta sake mannawa da ƙirjinsa tare da cewa.

“Nagode Yah Mu'allim”.

Ahankali Dr Eshaa ta sake turo ƙofar ta shigo tare da kallon Moddibo tace.

“Asa mata rigar yanzu fa sauran minti goma a shiga da ita kunga har 1:50 yayi”.

Kai ya gyaɗa kana ya cire mata rigar jikinta ya zira mata na asibitin sai kuma ya tsugunna ya zare mata skintied dake jikinta ya cire ya ɗaura akan gadon da take kwance ya riƙo hannunta yayin da ƙafanta ke sanye cikin wani takalmin roba  mai taushi Ahankali ya kama gashin kanta ya nannaɗe kana ya tura acikin hular rigar sai kuma ya sakar mata da lallausan murmushi yace.

“Kin kuwa ga yanda kika yi kyau cikin kayan nan kuwa?”.

Murmushi tayi tare da cewa.

“Hmmm”.

Matsowa jikinta yayi tare da tallafo kanta ya manna da ƙirjinsa kana ya mata kiss agoshi yace.

“Kinyi kyau sosai tare dani za'a shiga ayi Theater dake kinji Minha”.

Kai ta gyaɗa tare da faɗin.

“Toh Yah Mu'allim”.

Yana ɗan janta jiki yace.

“Ana Miki Theater za'a cire mana ɗan mu kina gani muna hira”.

Saurin kallonsa tayi sai kuma ta zaro idanunta tace.

“Yah Mu'allim wani irin Theater ne ina kallo”.

Yana matsa hannunta acikin nasa yace.

“Kawai za'a Miki alluran kashe zafi ne sai ayi Theater kina ji kina gani muna kuma hirarmu Yah Mu'allim ɗinki a kusa dake”.

Cikin sauri ta girgiza masa kai idanunta na tara hawaye tace.

“Um-um nikam bana son wannan Yah Mu'allim a cire min hankalina kawai ayi min Theater”.

Ganin alamar hankalinta ya fara tashi ya sassauta murya tare da cewa.

“Haka kike so?”.

Kai ta gyaɗa dai-dai lokacin Dr Jameel ya karaso yace.

“Bakyaso amiki kina kallo?Idan kina so na sai a jawo Mirror a sama Anuna Miki kina kallo”.

Da sauri ta runtse idanunta tare da manna kanta a dantsen hannun Moddibo tace.

“Nikam ina tsoro nice zan tsaya har acire ɗa ajikina?,Nikam bana so wallahi Dr Jameel kawai dai ayi min alluran da zai cire min hankalina gwara ayi min shi ina bacci in na farfaɗo in ganni da yaro na”.

Moddibo na shafa bayanta ya kalli Dr Jameel tare da cewa.

“Ayi mata yanda take so”

Kai Dr Jameel ya Jinjina kana yace.

“Toh shikenan ba matsala haka za'a yi mata”

Fita sukayi dai-dai lokacin kuma su Momy suka shigo cikin sassarfa taje ta rungume Momy.

Momy kuwa cikin sauri ta lumshe Idanunta jin hawaye na tsats-tsafowa cikin sanyi da rauni tace.

“Ubangiji Allah ya rabaku lafiya Khausar Allah yasa ayi aikin nan cikin lafiya akan alkhairi Allah ya fitar dake lafiya ".

Araunane ta kalli Momy tare da faɗin.

“Ameen ya Allah Momy Allah ya amsa kiyita min Addu'a Momyna kiya femin idan akwai abinda na taɓa yi Miki na cutar wa ko ɓacin rai”.

Da ɗan sauri Momy ta mari kumatunta kadan kana tace.

“Me kikayi min?,Ni babu abinda kika yimin Mamana Ubangiji Allah ya fito miki dashi da sauƙi”.

“Ameen ya Allah” ta faɗa tare da sakin Momy jin muryan Raudhat wacce suka shigo da Ibraahim da sauri ta risina ta rungumo Raudat cike da farin cikin ganinta Raudat tace.

“Oyoyo Addah Khausy ”.

Rungumeta Khausar tayi tana Murmushi cike da farin ciki Raudat ta cigaba da cewa.

“Addah Khausy wannan kayan fa”.

Kallon jinkinta tayi sai kuma tace.

“Raudat Theater za'a yimin”.

Cikin rashin fahimta Raudat tace.

“Addah Khausy menene kuma Thearter?”

Ɗan murmushi tayi tare da cewa.

“Abinda aka yiwa Momy lokacin haihuwar ku keda Ramadan”.

Jim tayi sai kuma tace.

“Toh Addah Khausy Allah ya kawo miki sauƙi da lafiya”

Cikin sanyi da rauni tace.

“Ameen ya hayyu ya ƙayyum”.

Moddibo kuwa Ahankali ya kamo hannunta ya tsayar da ita sai kuma ya juyo da ita gaban Momy yace.

“Momy ayi mana addu'a Allah ya fito damu lafiya ”.

Ahankali Momy tace.

“Ameen ya Allah Moddibo”.

Ahankali Khausar ta sake janye hannunta ta rungume Momy sai kuma ta rungume Didi Dr Eshaa ce ta ƙaraso tare da cewa.

“Lokaci yayi fa kizo mu tafi Khausar”.

Cikin sanyi ta kamo hannun Asma'u.

Ita kuwa Asma'u tuni take zubda hawaye hakanne yasa ta kauda kanta gefe tare da ruggumeta.

Ganin hakane yasa Modibbo ya kamo hannun Khausar ɗin suka juya suka nufi cikin ɗakin.


Anutse Khausar ta juya ta fara tafiya Ahankali tana waiwayen su cikin ƙarfin hali Momy tace.

“Mene kike tafiya haka kamar Kazar da ƙwai ya fashewa aciki, kiyi maza kishiga ayi Miki minti nawa kin fito hankalin ki kwance Mamana kike tafiya kina sanɗa”.

Juyawa tayi ta kalli Momy cikin sanyi da langwaɓar da kai tace.

“Momy ba sanɗa nake bafa yunwa nake ji shiyasa bani da ƙarfi”.

Jin haka yasa Moddibo ya sauƙe ajiyar zuciya tare da cewa.

“Shikenan toh tunda yunwa kike ji”.

Ya ida maganar tare da tsugunnawa ya ɗauke ta cak kamar Baby ya rungumeta.


   Raudat dake kallonsu ne ta sanya dariya kana ta buga tsalle tare da faɗin.

”Iyeeee Addah Khausy kin lale kinji daɗin ki Yah Moddibo ya ɗaga ki”.

Ibraahim dake bayanta ya matsa kusa da ita tare da ɗagata sama kana yace.

“Toh kema kiji daɗi an ɗaga ki”.

Cike da farin ciki ta riƙa ƙyalƙyala dariya tana cewa.

“Addah khausy Bye bye sai kin fito”.

Juyawa Khausar tayi ta kalleta kana tace.

“Toh Raudy na”.

Su Momy kuwa shiru kawai sukayi tare da rakasu da ido.


Suna shiga ɗakin direct kan gado Moddibo ya kwantar da ita Dr Jameel kuwa gefen kanta ya tsaya yana Murmushi yace.

“Mrs Mouley Ya kike?”.

Idanunta akan Moddibo tace.

“Lafiya”.

Yana kallon Norse biyu dake tsaye gefe hannunsa riƙe da wani ɗan tiren silver yace.

“Ina yake Miki ciwo?”.

Baki ta Cunno gaba still idanunta na kan Moddibo tace.

“Nifa babu inda yake min ciwo”.

Murmushi yayi tare da faɗin.

”Masha Allah”.

Sai kuma ya matsa kusa da Dr Eshaa ya miƙa mata alluran yace.

“Gashi kiyi mata”.

Karɓa Dr Eshaa tayi kana tayi mata.

Dr Jameel kam sake matsawa kusa da ita yayi tare da cewa.

“Mrs Mouley me kike ji yanzu?”.

Cikin wani irin yanayi data fara tsintar kanta ta lumshe Idanunta tare da cewa.

“Wani irin bacci mai daɗi nake ji Yah Mu'allim ”.

Ta ƙare maganar tana sauƙe sassayan numfashi.

“Masha Allah”.

Cewar Moddibo yana matsa hannunta cikin nasa.

 Dr Jameel kam Murmushi yayi kana yace.

“Asha bacci lafiya”.

Ahankali tace.

“Toh”.

Sai kuma ta sake lumshe Idanunta tare da buɗe su ta kalli Moddibo sai kuma ta juya ta kalli Dr Jameel Ahankali ta sake kallon Dr Eshaa.

Cikin wani irin murya na magagin bacci tace.

“Dr Eshaa”.

Cike da kulawa tace.

“Na'am Mrs Mouley”.

Cikin yanayin baccin dake fusgar idanunta tace.

“Bacci nake ji”.

Murmushi tayi tare da cewa.

“Toh gaki ga Mijinki akusa dake kiyi bacci”.

Ɗan jujjuya idanunta tayi tare da faɗin.

“Ta ina yake?”.

Da hannu ta nuna mata gefenta kana tace.

“Ba gashinan kusa dake ba”.

Ƙyafƙyafta idanunta dake cike da bacci tayi tace.

“Ina yake ban ganshi ba bacci nake ji”.

Dai-dai lokacin kuma alluran ya gama fara aiki ajikinta ta narke idanunta suka tafi luuuuu.

Moddibo kuwa Ahankali ya ɗan sun kuyo kanta tare da faɗin.

“Minha! Minha!! Minha!!!”.

Yi tayi kamar zata buɗe idanunta kuma ta kasa kasancewar alluran ya gama game jikinta ya saki sai kuma ta buɗe idanunta cikin magagin bacci tace.

“Yah Mu'allimmmmm”.

Shikenan kuma sai bacci.

Sake sunkuya kanta yayi tare da cewa.

“Minha”.

Dr Jameel dake kallonsa yace.

“Kai ka daina ma kiranta allura ya fara aiki ajikinta bari muzo mu fara aikin mu”.


Momy kuwa toilet dake cikin ɗakin da aka kwantar da Khausar ta shiga tayi alwala kana tayi sallar Azahar kasancewar su Didi already sun idar.

Momy kuwa koda ta idar addu'a ta shiga yiwa Khausar kan Allah ya fito da ita lafiya haka ma su Didi, Innayi, Niyna ke tayi.


Ahankali Moddibo ya juya ya kalli Dr Jameel tare da cewa.

“Wai da kai za'a yi Theater ne?Dr Eshaa baza ta iya bane?”.

Kai Dr Jameel ya jinjina kana yace.

“Zata iya amma dole sai da taimakona”.

Ya ƙare maganar yana kallon Norse biyu dake tsaye.

Cikin sanyi Moddibo yace.

“Toh shikenan”.

Ahankali Dr Eshaa ta zuge zip Dake gaban rigar yanda baza aga al'amuran ta ba sai cikinta daya bayyana a fili,

cike da kwarewa suka fara Thearter cikin abinda bazai gaxa minti goma sha biyar zuwa ashirin ba suka cire yaro fari ƙall kyakkyawan jariri gwanin ban sha'awa.

 Dr Jameel na ɗago shi ya cilla ihu Yararai-yararain alamar lafiyayyan yaro cikin sauri Dr Eshaa ta miƙa hannu zata karɓe shi sai kuma tayi saurin ja baya tana Murmushi ganin yanda Moddibo ya buɗe rigarsa ya tallafi yaron ya manna shi da jikinsa.

Murmushi Dr Jameel yayi tare da yin ƙasa da murya a hankali yace

“Wai kai ma ka zama Likita ne?”.

Cikin matsanancin farin ciki da wani irin azabebben ƙaunar yaron daya mamaye ilahirin jikinsa yace.

“Ba dole ba”.

Dariya Dr Jameel yayi tare da faɗin.

“Aikam toh yanzu dai a bawa Likitarmu ta gyarashi tukunna”.

Moddibo na sake ƙanƙame shi jikinsa yace.

“Wani gyarawa sai na kaiwa Didi ta ganshi”.

Dr Jameel na saka hanglove acikin wani ɗan silver dake riƙe hannun Norse's dake tsaye yace.

“Zaka kaisa amma ka bari agyara shi tukunna”.

Kai Moddibo ya gyada tare da miƙawa Dr Eshaa jaririn ta amsa tare da miƙawa Norse's ɗin karɓa sukayi kana suka je suka fara gyara jaririn.

Su kuwa Dr da Dr Eshaa nan take suka cigaba da aiki bayan sun gyara sun gama komai suka sa mata plaster kasancewar ba ɗinki bane atake suka ƙarasa mata komai kana suka balle wani abu daga jikin gadon ya zama dai-dai yanda suke buƙata,

 kana Norse's ɗinsu suka fara tura gadon yayinda ƙarin ruwan ke maƙe a hannunta.


Cikin sauri Moddibo ya matso ta gefenta ganin kamar ta buɗe Idanunta sai kuma tayi saurin rufe su Ahankali yabi bayan gadon.

Dr Eshaa kuwa juyawa tayi ta koma bayan Norse's ɗin dake gyara jaririn karbansa tayi ta cigaba da gyara shi da kanta...


 Su kuma suna fita kai tsaye wajen Didi da Momy suka  nufa.

Momy, Didi, Innayi, Niyna kuwa cikin sauri suka mike hangosu ta window da sukayi Norse's kuwa dakin hutu suka nufa kafin su shiga ma sun buɗe musu ƙofa kawai shiga sukayi.


Akuma dai-dai lokacin Lalla Khadijah da Rahama suka shigo harabar Asibitin wanda dama sunje sun saukowa Khausar da Baby abin buƙatarsu ne.


Khausar kuwa Ahankali ta sake buɗe idanunta sai kuma tayi sauri ta rufe ganin kamar Mutanen da Kai suke tsaye bada ƙafafunsu ba kasancewar har zuwa lokacin alluran bai gama sake taba Ahankali ta sake buɗe idanun tana ɗan jujjuya kanta Ahankali.

Cikin wani irin matsanancin ƙaunarta da matsayin mai girma da take dashi a zuciyarsa ya matsa daf da ita ya riƙe hannunta cikin wata sanyayyar murya mai cike da aminci da sadaukarwa yace.

“Minha”.

Idanunta ta sake buɗe wa sai kuma ta sake rufe wa.

Norse's ɗin kuwa zaman gadon suka gyara kana suka gyara mata ɗaurin ruwan dake jikinta kana suka juya suka fita.

Kujeran dake gefenta ta wajen kafafunta Momy ta zauna.

Moddibo kuwa kujeran dake gabanta daf da kanta ya zauna yayin da Asma'u Rahama, Lalla Khadijah suka ɗaya gefenta.


Ibraahim kuwa bayan Moddibo yake tsaye 


Niynah da Innayi kuwa zaune suke bisa carpet dake shinfiɗe.


Fuskarsu ko wannensu ɗauke da matsanancin farin ciki.


Anutse Moddibo ya ɗaura hannunsa na hagu akan gashin girarta yana ɗan kwantarwa yayin da yake motsa laɓɓansa yana mata addu'a.

Didi kuwa cikin sauri ta nufi waje jin Dr Eshaa na cewa.

“Didi ga mai gida ya ƙara so”.

Cikin sauri da matsanancin farin ciki Didi ta karɓesa kana tace.

“Masha Allah Fatabarakallahu Fi Ahsanil Khaliƙin Masha Allah”.

Sai kuma ta rungumesa Momy kam baki ɗaya hankalinta na kan ƴar ta.


Da sauri Rahama taje ta karɓi Yaron ta zuba masa idanu tana kallon baiwar kyau da Allah ya zuba masa yaro ɓulɓul dashi fari ƙal.

Rungumesa tayi tana cewa.

“Alhamdulilah Alhamdulillah nayi yaro Ni zan riƙa masa wanka ina rainonsa”.

Murmushi duk sukayi kana Innayi ta karɓesa ta kalla tare da miƙawa Lalle Khadijah cikin matsanancin farin ciki take masa addu'oi.

Cikin matsanancin farin ciki Asma'u ta leka fuskar yaron tare da shafa kansa tace.

“Baby ka wahalar mana da Maminka bazan ɗauke kaba har sai taci abinci tukunna”.

Dariya suka sanya Kana Niyna ta karbi yaron sai kuma duk suka koma suka zauna akan Lallausan Darduma Asma'u kam gefenta ta koma ta zauna.

Ibraahim ne ya amshi yaron tare da rugumeshi tsam a jiki yace.

“Welcome to the world *Keyan*. “.

Ma'ana King kenan.


Murmushi Didi tayi tare da cewa.

“In sha Allah kuwa”.


Khausar kuwa Ahankali ta motsa laɓɓanta a hankali murya can ƙasa tace.

“Yah Salam, Yah Mu'allim”.

Kasancewar da sunansa ta tafi kana kuma bayan sunan Allah data kira  da sunansa ta fara farfaɗo wa.

Da sauri ya sunkuya kanta yace.

“Na'am Minha”

Still idanunta na lumshe tace.

“Yah Mu'allim”.

Ahankali ya sake sunkuyar da kansa daf nata har suna shaƙan numfashin juna yace.

“Na'am Minha”.

Hannunta ta yunƙura kamar zata ɗaga sai kuma taji ta kasa fuska ta narke tare da cewa.

“Yah Mu'allim ka ɗaga min hannuna”.

Dai-dai lokacin Dr Jameel ya shigo cikin sauri yace.

“Kada ka ɗaga mata hannunta ka bari sai ta ɗaga da kanta”

Kallonta Moddibo yayi cike da tausayi sai kuma ya gyaɗa masa kai yace.

“Ki ɗaga hannunki mana Minha ai zaki iya”.

Idanunta ta rufe kana ta sake buɗe su cikin narkewan murya da sanyi tace.

“Yah Mu'allim ta ina kake?”.

Cikin tsira mata idanu yace.

“Gani nan Minha gani kusa dake”.

Rufe idanunta tayi ta buɗe tare da cewa.

“Ina Momy”.

Cikin sauri Momy tace.

“Gani nan Mamana gani nan kusa dake ki kwantar da hankalinki”.

Ƙyafƙyafta idanunta tayi tare da cewa.

“Yah Mu'allim ka zauna daidai mana meyesa kake zaune da kan ka?”.

Da mamaki yace.

“Zaune da kai kuma?”.

Murmushi Dr Jameel ya masa kana ya masa alamar alluran ne bai sake taba har yanzu.

Muskutawa yayi tare da faɗin.

“Toh Minha na gyara”.

Motsa idanunta tayi tare da cewa.

“Toh”.

Sai kuma ta buɗe idanunta ji tayi kamar alluran ya fara saketa ahankali ta ɗago hannunta sai kuma tayi saurin sakewa tace.

“Yah Mu'allim ka tayani in ɗaga hannu na mana”.

Kai ya girgiza tare da cewa.

“Ki ɗaga da kanki mana”.

Momy kam na zaune gefenta ta tsira mata Idanu.


Didi kuwa wayane maƙale kunnenta cikin jin daɗi da girmamawa tace.

“Alhamdullilah Abokinka, Amininka, Jikanka Kuma Sarki mai Jiran gado ya fito duniya”.

Abualeey dake zaune cikin Fada ya gyara zamansa cike da matsanancin farin ciki yace.

”Masha Allah Alhamdulillah Allah ya raya mana shi bisa Imani”.

Cike da jin daɗi tace.

“Ameen”.

Kana ya katse kiran.

Abualeey kuwa cikin jin daɗi ya juya ya kalli Waziri, Galadima da sauran fadawa yace.

“Alhamdulillah an cirewa Matar Aleeyu ɗa namiji lafiya lau ”.

Cikin sauri da jin daɗi Galadima yace.

“Alhamdulillah”.

Waziri kuwa juyawa yayi kana yayi Sujudur Shukur tare da cewa.

“Alhamdulillah abu duk yanda ake fata haka ya tabbata magauta basu sami yanda suke soba”.

Kai Abualeey ya jinjina kana yace.

“Idan munyi sallar la'asar sai muje asibiti Mu duba ta”.

Amsawa sukayi daga nan suka ci-gaba da zaman fada.


Agefen Khausar kuwa zuwa yanzu ƙarfin jikinta ya fara dawowa Sai dai har yanzu alluran bai gama saketa ba bisa duk alamu maganar da take Sambatune.

Ahankali ta ɗago hannunta kana ta ɗaura kan cikinta ta shafa ɗagowa tayi ta kalli Moddibo tare da cewa.

“Yah Mu'allim”.

Kallon hannunta yayi tare da faɗin.

“Na'am Minha”.

Idanunta alumshe tace.

“Ina cikina”.

Juyawa yayi ya kalli Kyakkyawan Jaririn dake hannun Ibraahim yace.

“An cire mana Baby”.

Idanunta ta rufe kana tayi Murmushi tare da cewa.

“Yah Mu'allim”.

Hannunsa ya ɗaura kanta tare da faɗin.

“Na'am”

Tana shafa cikin tace.

“Ka ganshi?”.

Kai ya gyaɗa tare da cewa.

“Eh na ganshi?”

Murmushi tayi kana tace.

“Momy na ta ganshi?”

Kai ta gyaɗa tare da faɗin.

“Eh”.

Murmushi ta sake yi still tana shafa cikin tace.

“Didi da Asma'u fa su ganshi?”

Kai ya sake gyaɗa wa tare da cewa.

“Kowa ya ganshi”.

Baki ta tura gaba cike da shagwaɓa kamar za tayi kuka fuskanta ta shafa kana yace.

“Minha ya akayi”.

Fuska ta sake narkarwa cikin mayen allurar tace.

“Yanzu shikenan kowa ya rigani ganin ɗana”.

Murmushi yayi kana Didi ma tayi Murmushi Asma'u kam dariya tayi tare da cewa.

“Aikam dai kece karshen kallo duk mun riga ki”.

Baki ta Cunno gaba.

Didi kuwa sake matsawa kusa da ita tayi kana tace.

“Kiyi haƙuri Ɗiyata In sha Allahu zakiga ɗan ki”.

Sake narke fuskarta tayi tare da cewa.

“Hmmmm”.

Sai kuma ta jinjina kanta tare da juya kanta gefe tace.

“Yah Mu'allim”.

Ahankali yace.

“Na'am”.

Lallausan Murmushi ta saki tare da cewa.

“Yah Mu'allim ina sonka”.

Kansa ya sunkuyar ƙasa tare da sakin Murmushi kana ya ɗago ya manna mata kiss agoshi.


Ahankali ta cigaba da kiransa.

“Yah Mu'allim! Yah Mu'allim!! Yah Mu'allim!!!”.

Duk kiransa da take yi yana amsawa.

Cikin sanyin murya da shagwaɓa ta cigaba da cewa.

“Ina sonka! Ina sonka!!,Ina sonka!!!Yah Mu'allim Kasan ina sonka ko?”.

Dariya Asma'u ta sanya tare da cewa.

“Dan Allah kar ki dame mu ai mun san kina sonshi”.

Ta ƙare maganar tare da ciro wayarta tana mata video Khausar kuwa jin abinda Asma'u ta faɗa yasa ta Cunno baki gaba har lau kuma cikin mayen take.


     Moddibo kuwa wani Amintaccen Murmushi mai cike da jin daɗi gami da shauƙi ya saki Sambatu take yi amma yana masifar jin daɗin su.

Aƙage da kuma shauƙi yace.

“Na sani Minha?”.

Sake Cunno baki tayi tace.

“Yah Mu'allim kaima  kana sona?”.

Tafin hannunta ya matsa tare da cewa.

“Ina sonki Minha Ina sonki ina sonki Minha”.

Cike da kunya Didi ta koma kan Darduman ta zauna.

Momy dake zaune gefensu kuwa sunkuyar da kanta ƙasa tayi.

Lalla Khadijah Rahama Asma'u Dr Jameel kam Murmushi kawai suke suna sake jaddada ƙauna da shaƙuwar dake tsakanin su sun lura Moddibo yama mance da suna wajen.

Khausar kuwa cikin Sambatu da azabebben ƙaunarsa tace.

“Ina matuƙar Ƙaunarka Yah Mu'allim tun ina JSS one fa nake sonka kasan kafi duk malaman makarantar mu kyau ko ina ka sani ko?”.

Cikin jin daɗin gami da farin ciki yace.

“Uhmmm”.

Cikin narkekkiyar murya tace.

“Da gaske fa kafi duk mazan duniya kyau, sajenka mai kyau, ai kasan ina son sajenka ko Habibeeey”.

Lallausan Murmushin mai cike da farin ciki yayi tare da cewa.

“Yesss na sani”.

Cikin tsokana Ibraahim yace.

“Toh ashe fa tsohuwar soyayyace, ashe nima sai in fara aje saje”.

Murmushi sukayi baki ɗaya, Asma'u kuwa gefen Dr Jameel daya riƙo hannunta yaja ta ɗan matso still tanayiwa Khausar video.

 

Ita kuwa Khausar Jujjuya kai tayi tare da tura baki sai kuma tace.

“Ina sonka har rainafa, kuma ina tsoron kayi min kishiya bana son rayuwa da kai da kishiya Yah Mu'allim kayi min alƙwarin baza kayi min kishiya ba, kuma ka ƙi kayi min alƙwari Yah Mu'allim”.

Gashin girarta ya shafa kana ya kwantar kanta ya sunkuya ya kai bakinsa saitin kunnenta ya raɗa mata.

“Minha aike ta musamman ce arayuwata koda wata mace takasance kusa dani Babu wata mace da zata kai ki matsayi da daraja akusa dani”.

Idanunta ta buɗe ta kallesa kana cikin wata sanyayyar murya mai cike da shauƙi da bege ta ƙyafƙyafta idanunta tare da cewa.

“Yah Mu'allim ina son ka”.

Murmushi yayi kana yace.

“Naji”.

Kanta ta juya ɗaya gefen tare da cewa.

“Didi?,Didi!!”.

Didi dake gefe  tace.

“Na'am Khausar ”

Baki ta tura kana ta marairaice fuska tare da cewa.

“Didi ki faɗa masa ina son shi Dan Allah kar ya yimin Kishiya”.

Murmushi Didi tayi kana tace.

“Shikenan ɗiyata kwantar da hankalinki kin ji”.

Sake tura bakinta tayi tace.

“Ina Momyna?,”.

Kallon Momy Didi tayi tare da cewa.

“Gata nan”.

Ɗan buɗe idanunta tayi tace.

“Momy ki matso ta nan mana”.

Miƙewa Momy tayi kana ta matsa kusa da kanta ta tsaya jin alamun ta kusa da ita tace.

“Momy”.

Anutse Momy tace.

“Na'am”.

Tana ɗan Murmushi tace.

“Momy kinga Babyna?”.

Kai Momy ta gyaɗa tace.

“Eh”.

Kwanciyanta ta gyara tare da cewa.

“Momy kinga yaro na ko?,Didi tace namiji ne?”.

Kai Momy ta gyada kana tace.

“Eh”.

Murmushi ta saki tare da faɗin.

“Momy dawa yake kama?”.

Murmushi Momy tayi tare da juyawa ta kalli Jaririn dake hannun Niyna kana ta juya ta kalleta tare da cewa.

“Da Ramadan yake kama Khausar”.

Wani Amintaccen Murmushi ta saki mai cike da jin daɗi kana tace.

“Alhamdulillah Momy na samu mai kama da Ramadan".

Kai Momy ta jinjina tace.

“Sosai ma”.

Fuskarta ta shafa tare da faɗin.

“Momy Kyakkyawa ne kenan?”.

Ta ƙarashe Maganar da alamar tambaya kana da Murmushi afuskarta.

Kai Momy ta gyada tare da cewa.

“Kyakykyawane Mamana ɗan ki kamar Balarabe”.

Tana Murmushi tace.

“Ai tunda aka ce da Ramadan yake kama nasan kyakkyawane Momy”.

Sai kuma ta Maida idanunta kan Moddibo tace.

“Yah Mu'allim kaji wai ɗan mu da Ramadan yake kama, kyakkyawane ko?”.

Kai ya jinjina kana yace.

“Kyakykyawa ne yama fiki kyau ai?”.

Baki ta tura gaba tace.

“Ni dai bai fini kyauba”.

Murmushi yayi yace.

“Toh naji bai fiki kyau ba Rigimatu, ki Kwantar da hankalinki”.

Asma'u kam sai dariya suke mata.

Haka ta cigaba da surutu da Sambatu har kusan karfe huɗu zuwa lokacin already alluran ya gama saketa ta dawo hayyacinta.


Kallon Moddibo tayi tare da cewa.

“Yah Mu'allim zan tashi zaune”.

Sumar kansa ya shafa tare da cewa.

“Toh ki taushi ki zauna mana”.

Fuska ta narke tare da cewa.

“Ka tayani”.

Cikin yi mata kallo mai haɗe da zazzafan yanayi yace.

“Toh ki tashi ki zauna mana ai likitoci sun hana in tayaki, ki tashi da kan ki mana”.

Baki ta tura  tayi ta ƙorafi misalin 4:15 ta mike ta zauna da kanta kasancewar ta tashi ta zauna da kanta yasa Dr cewa Moddibo ya tallafa mata amaida ta ɗaki ta taka da ƙafanta.

Da ƙafanta ta taka aka canza mata ɗaki wanda akwai step agabansu suna komawa ɗaki Asma'u ta zauna ta gabanta Moddibo kuma nata bayanta.


Kallon Dr Jameel Asma'u tayi tare da cewa.

“Dr”.

Yana gyara abin karfen gadon yace.

“Na'am my Dear”.

Kai ta langwaɓar tare da faɗin.

“In bata abinci?”

Kai ya dafe kana yayi Murmushi tare da cewa.

“Kai ke dai baki ɗaya na lura bama ta ɗan mu kike ba ta Ƙawarki kikeyi”.

Dariya Momy tayi kana tace.

“Da gaskiyar ta wa yake ta ɗan ku”.

Murmushi Moddibo yayi tare da faɗin.

“Momy harda kema bata ɗan mu kike ba wato ta ita kike ”

Cikin sauri Dr Eshaa tace.

“To ai har kaima bata ɗan ka kake ba ta ita kake tunda ka ɗauke sa aɗaki baka sake ɗaukar saba kana riƙe da hannunta yanzu dai lokacin sallar la'asar yayi atafi ayi Sallah.

Zuwa biyar a ɗan asa mata abinci.

Cheaps kaɗan da tea rabin cup”.


To sukace kana su tafi masallaci, su kuwa matan sukayi salla a nan.


Sai ƙarfe biyar dai-dai 

 Asma'u ta ɗan sa mata cheabis ɗan kaɗan sai tea rabin cup, kamar dai yadda sukace mata.


 Bisa jagoranci likitoci ta matsa ta riƙa bata taɓa ci.

Moddibo kuwa kanta ya riƙa shafawa tare da cewa.

“Minha kinga muje muyi alwala muyi sallah na roki Allah ya baki lafiya ya raya mana ɗanmu”.

Lallausan murmushi ta sakar masa kana ta gyaɗa kai shi kuma ya zauna gefe, nan dai ta gama ci, kana ta ɗan gyara manta.


Dai-dai lokacin kuma Abualeey suka iso, bisa jagorancin Ibraahim m suka nufi dakinta dai-dai lokacin da suka shiga a kuma dai-dai lokacin Khausar ta fara wani irin....

Post a Comment

0 Comments