TOP HAUSA NOVELS atOptions = { 'key' : '20e08520dad54dbf6d9e963271

'Yar Tsakar Gida 1-2 page 27-34

 Zama suka yi tsumi ko wacce tamkar Ruwa yaci ya cinye ta . Cike da Takon nan nasa ya ƙariko inda suke  yana zama a daya daga cikin Royal cushine din falon bai ce dasu komai ba tsawon mintuna kusan biyu . Ta Gyefen ido Nana ke masa wani kallo kamin Nussy ta miƙe sum sum tana barin falon tare da shigewa Bedroom din su . Hakan ne yaba Nana itama tashi daga inda take tana bin bayan Nusaiba . 


Takaici sosai ya turniƙe sa Amma kuma ya rasa ya zaiyi dasu , don Aikin gama ya riga ya gama . Wani irin murmushi yayi wanda Naana ta tsani taga yayi mata irin sa , don idan yayi wannan murmushin tasan tabbas sai tayi kuka sau babu iyaka . Hajiya Sa'adah ce ta shigo Falon tana ganin sa Zaune ƙafan sa a harɗe , haka Giran sa yake a hade . Ɗan sai tayi don jikin ta bai bata ba . Tafi kowa sanin Waye Nurain, sannan a wannan halin da ta ganshi tasan da Abin da yake kisimawa a zuciyar sa ,wanda idan yayi shi ba zai ma kowa Dadi ba . 


Juyawa tayi tana kallon Labaran gida Nigeria da ake Haskowa a tashar BBC kana cike da kokarin ganin ta kawar masa da tunanin nasa tace " A'a Yau Nurain ne da sauraren labarai haka ?. 


Idanun sa a Lumshe suke , ba tare da ya buɗe su ba ,amma komai ganin sa yake tarrr. 


Jikin Mommy Sa'adah ce yayi Sanyi Tabbas tana jin tsoron ganin sa a irin wannan halin . Lokaci Ɗaya ta fara tuno  da shekaru goma da suka wuce  Rayuwar su a America  . Tun da suka dawo dashi can suka raba shi da Amrah har yau Nurain bai dawo masu yanda yake ba . Wannan Fara'ar nasa duka sun nema sun rasa , miskilanci ya zama jinin jikin sa .


A hankali Mom Sa'adah ta juya tana kallon Jidder mai Aikin ta Wacce take daga Bayan ta . Am..Amm Jidderh maza kawo ma Nurain Cofee yanzu .  

 


Ɗan risinawa Jidder tayi tana furta " Tom Hajiya . 

Hummmm Matsawa Kusa Dashi Mommy Sa'adah tayi tana zama gyefen sa tare da kai hannun ta tana kama hannun sa . Shiru tayi na kusan mintuna uku har Jidderh ta dawo tana aje masa coffee mug din tana juyawa . Nurain ...! Ta kira sunan sa a sanyaye tana mai motsa bakin ta da zummar cigaba da masa magana ne taga Ya Janye Hannun sa daga nata yana miƙewa tare da Nufar Upstairs. Idanun Mom Sa'adah ne ya kawo Ruwa , Tabbas nasan mene ke damunka , Sannan nasan me zai sanya ka farin ciki amma babu yanda zanyi Matsalar ba daga Ni bane , Daddy ba zai Amince ba saboda Dalilin sa guda Daya tak.....!


**

Kallon Nana Nusaiba tayi wacce take hada kayan ta a trolly tana faɗin Yau zan bar gidan nan , Ban san wani mataki Nurain zai dauka akai na ba . Gwara na tafi a yau tun kamin ya yanke hukuncin da ba zai mun dadi ba...[8/14, 10:50 PM] Anty Aisha Mmn Teddy Marubuciya: *🛖

Ban gane ba , me kike nufi Naana? Wai tafiya zaki yi takan Wannan dan Abun? , Nifa ina tunanin da Wuya yaji maganan da muke yi . Don Allah ki aje kayan ki ,ki bari sai ana jibi daurin Auren sai ki koma . Nusaiba ta ƙare maganan tare da takowa zuwa inda Naana take . Hannun ta tasa tana Amsan trolly bag din nata tana kokarin Matsar da shi gyefe ne Nana tayi caraf tana riƙe Trolly ɗin nata . A'a Nana wallahi ba zan Zauna ba , Har yanzu baki san soyayyar dake  tsakanin Nurain da Wancen tsinanniyar yarinyar ba , sannan ma wai kin san me naji akan ta kuwa ?. 


Mtswww gaskiya kin fiye tsoro da yawa Nana saboda mun sa an mata hakan to Meye ne.?  Kin san da Soyayya tsakanin su kuma kike yunƙurin yin nesa da shi? , Ai a ganina wani faraga  kika bari wanda zai yi sauƙin haduwar Soyayyar tasu , kin manta Nana a gaban Mu a gaban ki a gaban Mom da Dad fa yace " Yana Son Ta kuma zai Aure ta . Matsala ne kwance a ƙasa . Gaskiya bana jin ki tafi a halin yanzu.  Shiga jikinsa zaki yi sosai daga nan zaki kawar da duk wani soyayyar Amrah a zuciyar Ya Nurain . Hummmm Numfasawa Nana tayi tana gyada kai tare da sakin wani irin shu'umin murmushi kana tace ' har abada Nurain ba zai taba Auren Amrah ba . Ki ma kwantar da hankalin ki .


But why do you said that.? A ƙwayar idon ya Nurain kike ganin tsananin son Wancen Yarinyar , amma fa ki kwantar da hankalin ki Cox nafi tunanin Tausayi ne ba so ba .  Humm koma dai Meye Nussy ki kwantar da hankalin Daddy ne ba zai taba amincewa da Auren ba . A yau naji labarin da tuni nake son sanin gaskiyar zancen . Amrah bata da cikakken Uba . Ina nufin Yar zina ce .! A kwararo akayi cikin ta yanda naji and Bata da Uba uwar ta ma ta gudu ta barta a wulaƙance a kaskance . Shiyasa bata jin dadin gidan Kanal Ɓaidu suke azabtar da ita . Na kuma san Nurain yasan Wannan labarin . 


Wani irin Fiddo da Idanu Nusaiba tayi tana Furta " Are You serious? . Da gaske Bata da iyaye ba yar sunna bace yar zina ce.? Of course yes." 

Nana ta katse ta tana wani irin murmushi . Dariya Nusaiba ta fashe dashi tana faɗin " Alhamdulillah , Dama bana Son haɗa Jiɓi da Talaka. Kin ga kuwa dole Ya Nurain ya haƙura da ita , Cox Dad ba zai Amince ya Auri Yar da bata da Asali ba . Ai ke ko yanzu kika koma gida ,kiyi barcin ki har da mashuri Nan da Sati biyu Amarya kike a wurin Ya Nurain . Dariya Nana tasa tana jan Trolly ɗin ta tare da gyara Mayafin fuskar ta wanda tayi Rolling fuskar zuwa kan ta dashi . Transparent  Glass ta saka a fuskar ta Wanda ya kusa mamaye Rabin fuskar nata . Kallon Nusaiba tayi tana ɗaga mata Hannu tare da cewa " Ohk Bye Baby . Bye bye ...” 

**

Ƙwance yake a ƙwarmin wanka ruwa na sauka masa a hankali ta Shower🚿. A hankali ya ware tsayayyun idanun nan nasa daga Ni kasan fir fir fir suke  na sanin Duniya . Motsa bakin sa yayi yana furta " Amrah ....” Miƙa hannun sa yayi yana Yamutsa Sumar kan sa da ruwa ya shiga ta ko ina . Really love you my Barbie. Ƙara Lumshe idanun sa yayi yana tuno da Murmushin nan nata Tare da Hasko Fuskar ta Wanda a duk sa'ilin da tayi shi Sai gyefe da gyefe na Kuncin ta ya loɓa ( Dimple).  Ƙaran Kiran Wayar sa ne ya katse masa tunanin kyaƙyƙyawar Babyn tasa ,  yana ɗan Ware Idanun sa tare da Kallon wani cube da aka tana je shi na musamman don aje phone's . Sunan Bathroom ne amma tsaruwan sa da kyaun sa ya zarce na falon komai na wurin White and cyan colour ne . Kasantuwar baya da nisa daga inda yake zuwa inda Wayoyin nasa suke yasa shi kai hannun sa yana Kallon Screen ɗin Wayar . Fuskar sa nan take ta sauya , Idanun sa na sauya kala daga fari zuwa ja na tsananin ɓacin rai , kun san zuciya irin nasa don shi mutum ne mai Zuciya Ga Tijara . Sam baya jin haufin marin mace don Zaid bai san darajan mata ba . Yasha marin ƴammatan nasa babu iyaka , akan Amrah ne yasan what's the true love? He really failed in Love.  Sunan Pheenerh ya gani yana Ji tamkar ya cilla Wayar cikin Baf din.  Takaici ne ya ciyosa ji yake tamkar yaje ya shaƙe ta ya huta . Mtswwwww tsaki Zaid yajah yana aje Wayan inda yake .  


Ina so na ganta .! Ina so naga Amrah yanzu . Miƙewa yayi yana fitowa daga cikin shower din tare da Kai hannun sa yana Ɗaukar Towel yana zagaye iya Kugun sa dashi . Madubin Dake gaban sa ya kalla yana Bin fuskar da kallo zuwa Faffaɗan ƙirjin sa inda Suma ya rufe luff. Toilet silipers ya saka yana nufo hanyar Bedroom din shi tuno da Amrah kuwa zuciyar shi wani sanyi yake ji yana Ratsa shi ta ko ina . Fuskar sa har fidda Annuri yake yi na tsananin So . Kamin wannan lokaci kuwa Pheenerh ta kira sa sau babu iyaka amma bai tsaya bi ta kai ba .

**

Zama tayi a tsakiyar ɗakin Lanti wacce ta kama Hannun ta tana gasa mata da Ruwan ɗumi , shafa Hannun nata take yi da wani Small Rag tana danna inda yayi kumburin dukan da Baba Zuwai tayi mata . Amrah kiyi hakuri ki ƙara riƙe maraicin ki . Duk Abin da zaki ji ance kar ki ɗauka , Baki da Wani Uban da ya wuce kanal ɓaidu , Kuma tabbas da yana raye shi da kansa zai faɗi Gaskiyar Al'amarin.   Girgiza Kai Amrah tayi tana gyaɗa ma Lanti idanun ta na tsiyayar da Hawaye na azaba .  Fuskar ta Lanti ta kalla inda Gyefen Kuncin ta yayi jajir na shatin Mari . Jikin ta kuma tasha dukan da itace.  Humm ALLAH kenan .! Abun da Lanti ta furta kenan tana cigaba da matsa Kuncin ta inda yayi jajir . Mama Lanti nasan baba na ya mutu , Amma ita Umma ta fa .? Tana raye ? . 


Humm Amrah maganar Gaskiya mahaifiyar ki Hafsa bata kyauta ba . Duk da Anyi mata Tijara iya Tijara kawo ki gidan nan da tayi , amma ita macace ,mace kuma da Taushi zuciya aka santa ba da zafi irin haka ba . Meye ribar ta na yin hakan .? Kasa magana Amrah tayi tana kallon yanda Lanti ta zage tana masifa tare da faɗa akan Abun da Umman nata tayi . Mama Lanti kiyi Haƙuri , Komai Umma ta tayi tana da dalilin ta , kuma ko bayan Rai na taxo kice mata na yafe mata .” 


Ɗago ido Lanti tayi cike da karyewar zuciya take kallon Amrah wanda kamin tayi mata magana Sallamar wani yaro ya katse su . Wai ana sallama da Amrah a ƙofar Gida . Saurin kallon yaron Amrah tayi jikin ta na daukar Rawa kar kar kar . Juyowa tayi tana kallon Mama Lanti kamin ta cikin zubda Zafafan Ƙwallah ta furta " Wallahi Mama ban san Waye ba. Kayya .! To Meye na kukan ? Ai kin isa a fara sallama dake yanzu , maza tashi ki sa hijabi Kiga Wake sallaman dake . Idan kin dawo sai ki faɗa mun yanda kuka yi . Nidai abun da nake so dake shine ki cigaba da tsare mutuncin kan ki Amrah ,baki da Gata sai na ALLAH . Juyawa Lanti tayi tana cewa " Maza kace gata nan zuwa .” 


Da gudu yaron ya juya yayin da Baba Zuwai ta banko labulen dakin Lanti tana faɗin " Ta je ina .? Ga yayyun ta nan Zaga² basuyi Auren ba sai ita ƙaramar su ce zata fara fita zance ?. Ba tare da Lanti ta kalli Zuwai ba tace " Ke tashi saka hijabi ki fita ki bani Wuri ,naga Wanda zai hanaki zance a cikin gidan nan. Jiki babu kwari Amrah ta miƙe tana ɗaukar Hijabin ta tare da saka silipers,raba Baba Zuwai tayi da ta kasa magana don tijaran Lanti ya fi nata . Yammmmm sauran matan gidan da ƴammatan suka bita da ido har ta fice . Zulai ne ta kalli su Hajara tana cewa " Muje muga Wani mahaukacin ne yazo Wurin yar zina.? Kila bai sani bane . Dariya Hajara ta fashe dashi tana faɗin muje sai mu sanar masa da Asalin ta ,idan yaji gobe tabbas ba zai dawo ba .  


Ɗingishi take yi tana jan ƙafan nata da ƙyar tare da fitowa zauren gidan nasu na biyo . Dam³ Ƙirjin ta ya buga da ƙarfin Gaske Lulun idanun ta na ƙara firfitowa . Kallon kallo taga suna yi tsakanin su su biyun Zaid da Nurain .  Noory .....! Ta furta a sanyaye , Maida kallon su suka yi zuwa inda take , don tana fitowa Nurain na zuwa anan ne ya ga Zaid , wanda nan take ya faɗa tambayar Zuciyar sa mene ya kawo Aminin sa gidan Wacce yake SO .? Katse sun da tayi ne ta hanyar kiran sunan Nurain yasa su duka kallon inda take . 


Cikin Sauri Zaid ya ƙariko inda take cike da sassarfa da zafin jini irin nasa ya kai hannun sa tare da tallabo Kuncin ta inda yaga shatin Mari ta ko ina kumatun ta sunyi girma sunyi jajir . 


Barbie mene ya same ki ? What's wrong with you ?, are...... Maganan sace ta Datse sakamakon Jiyo salatin su Zulai da suka fito suna tafe hannayen su duka biyun . Saurin janyewa tayi daga Riƙon da Zaid yayi mata yayin da Nurain ya kai Hannun sa yana riƙe Hannun Amrah ram . Au Dama ya tabbata , Ashe karuwa ce ke Amrah ? Yanzu abun naki har a zauren gidan Ubanki.? Hajara tayi maganan tana kama bakin ta irin na makirci da nuna mamaki . 


Aaaa Ahir dakata ...Zulai ta katse ta tana daga mata hannu tare da cigaba da cewa " nan ba gidan Uban ta bane , ita fa ba kowa Bace Fache Yar zina . Mara Asali da tushe . Waye ya maran mun fuskar mata.? Waye ya duki Amrah ...? Cike da Arrogant Voice din shi ya katse su Giran sa na tattarewa . Wani irin kallo Zulai tayi ma Zaid tana kama Ƙwankwaso tare da cewa " To me zaka iya idan nace Nine.? . Kamin Zaid yayi wani yunƙuri Nurain ya afka mata wani irin lafiyayyun Mari yake shimfida ma fuskar Zulai wanda a sakanni yayi mata Mari sun fi goma . Gaba ɗaya ta dauke wuta sai wani kukan zuma da take ji ko Muryar su bata iya ji bare ta gani sai duhu kawai da take gani.  Zabura Hajara tayi tana yin baya tare da cewa " Wallahi Su Baba Zuwai ne ba Zulai bace ku bar dukan ta don ALLAH . Gaba ɗaya Hajara ta diririce ta tsorata a ganin ta Nurain Soja ne . Dan duka yake ma Zulai har da yin ball da ita . 


Saurin Nufar Nurain Amrah tayi tana kuka iya ƙarfin ta Muryar ta har ya disashe riƙe sa take yi tana faɗin " Noory ka bari , Noory ka daina dukan ta .

To uban Waye ya duke ta .? Zaid ya katse Hajara don baya takan dukan da Nurain ke yi ma Zulai tamkar zai kaita lahira . Cikin gidan Hajara ta nuna masa da hannu wanda bai tsaya tunanin komai ba ya afka kan tsaye yana kiran Sunan Zuwai.....Zuwai .." wacece Zuwai a cikin gidan nan .? 

Da hakan ya sanya kansa zuwa cikin tsakar gidan yana huci . 


Gaba ɗaya Amrah ta gama tsorata da gudu ta juya tana ficewa daga Zauren tare da barin layin ba tare da Tasan inda zata nufa . Hasali gaban ta ma bata gani haka ta faɗa ma ƙaramar titin layin su ....Wani irin ƙuuuiiiiiiiii kaji ƙwaltan ya ɗauka , ALLAH ne ya kiyaye don saura kadan Moton ta kwashe ta . Cak..... Ta tsaya tana dafe kanta tare da kiran sunan ALLAH . Buɗo Murfin Moton yayi cikin sauri yana ƙoƙarin yin mata Tsiya kawai sai ya tsaya cak yana kallon ta . My wife ....! Ya kira sunan ta yana cire baƙar gilashin idanun sa . A hankali Amrah ta ware idanun ta tana ganin Kyaƙyƙyawar Baturen da bata san daga inda yake ba , kuma batasan me ya kawo sa Nigeria ba , don dai bai kamata mata da Wanda yayi haihuwar Africa ba ma baki daya . Waye kai ...? Nice matar naka .? Ɗan shiru yayi yana kallon ta tare da sakin mata Murmushi don baiji mai tace ba kwata² tun da ba iya Hausan yayi ba . Motsa Laɓɓansa yayi yana furta Wow . Juyawa tayi tana kokarin wuce shi don idanun tsirarun mutanen Hanyar akan su yake . Heeee....Hello ..I'm Aslaam........! Hello baby girl 🥰.

Sam Amrah ta gagara tsayawa haka kunnuwan ta sun kurumce daga jin komai har da daga Muryar da Aslaam ke yi mata yana kiran sunan sa iya ƙarfin sa . Ganin ta fara yi masa nesa yasa shi Saurin shigewa moton nasa yana bin bayan ta , ɓangaren Amrah kuwa Haushin Wannan saurayin ne taji ya kamata , wanda a lokaci guda yake kokarin ɓata mata lokaci da wani banzan turancin sa . Shan gaban ta taga yayi da Moton sa ji kake ƙuuuuuuuiiii yana haɗa tayar da da Ƙwalta . Wani irin zabura Amrah tayi tana Jah baya tare da bin moton Aslaam da kallo tana lulu da idanun ta , buɗe Moton yayi yana fitowa fuskar sa cikin fara'a , You Are beautiful, I love you Amrah .” 

Wani dam dam ƙirjin Amrah ya buga mata da ƙarfi wanda tsoron ta ya gaza ɓoyuwa har a ƙwayar idanun ta sun bayyana . Cikin harshen Nasara ya kuma furta mata " Did you hearing English very well . Wani kallon ƙasa da sama Amrah tayi masa tana ganin Al'amarin nasa tamkar rainin hankali. Kauda kan ta tayi daga gyefe jikin ta na tsuma na Tijara don ganin Aslam take dan rainin hankali .  

Ohk Sorry kiyi Haƙuri. Ya furta yana takowa zuwa inda take tsaye . Kallon sa Amrah tayi cike da tsiwan da bata san tana da shi ba tace“ Ok now you can speak Hausa instead of English . Ashe abun duk ƙarya ne . Don Allah malam ka bani hanya , i have a lot to do now. , I don't have any time to waste it here . Humm Numfasawa yayi kana ya shafa Sajen Fuskar sa daya tara na rashin kunya kai da gani kasan akwai rashin ji . I'm sorry my beauty . Ban iya Hausa ba , but i can try my best now . Sunana Aslaam , nazo daga Ƙasar Spain acan aka haife Ni acan na taso ,duk da kasancewar Iyaye na cikakkun yan Nigeria ne .but my Dad and mom  suna aikin su acan . Dad dina business Man ne yana Kasuwancin Sa tsakanin Nigeria To Spain zuwa Germany . 

Ohhhh....! 
Bawan Allah Na gaji da Wannan maganan taka, it is my business to know who are you ? Or About your family that's not my  business. It yours . 

Tun da ta fara maganan yake kallo dan mitsulun ta . Wani irin murmushi ya saki yana Faɗin " You Are my Wife . Just  you have to start preparation of our Wedding . Amma baka da Hankali . Ina da Hankali Amrah .  Innalillahi wa'inna ilaihir raji'un . Wai waye kai ne ? Ya akayi kasan sunana ? Me yasa kake kirana matar ka . WHO are yhu please .? Na gaji da Wannan zancen naka . 

That's is what you suppose to say ...Wannan ya kamata kiyi magana tuntuni ba ki tsaya kina ihu a titi ba. Amma fa kyau ma kika kara yi , I really love yhu Amrah . Bawan Allah kuka kake so nayi maka ne ? Meye haka , don Allah waye kai .? Amrah tayi maganan tana narke masa fuska lokaci daya idanun ta na kawo ruwan Ƙwallah....” 

Zaki iya shiga moto na muyi maganan anan .? Saurin Girgiza masa kai tayi tana cewa " A'a wallahi baxan shiga ba . Ban san ka ba . Ni kuma nasan , the first Dana fara Ganin ki a Twitter ne aka yi posting Hoton ki , tun daga Spain na taho just because of you My lab💓 . Yanzu zaki iya shiga muyi magana a natse . Ki natsu Ni baxan cutar dake ba .Sunana Aslaam Ahmad . Iyaye na haifaffun Nigeria ne . Nine dai ba Haihuwar nan ba ,ba kuma rainon nan ba .  Hawaye ne suka fara zubo ma Kuncin ta . Ya ALLAH..., Ta furta tana kallon sararin samaniya . Aslaam ta kira sunan sa cikin sanyin Muryar ta , kamin ta cigaba da cewa " Bana Twitter i think I'm not that person who you are looking for . Sunana Amrah kaga can layin nan ne gidan mu . Wallahi ko nokia bana da ita bare babban Wayar yin Twitter . Tayi maganan don sam ta manta da Wayar ma da Doctor Zaid ya bata . Bazan cutar dake ba Amrah , please trust me . Ya furta yana yi mata ƙasa da murya kaman wanda zai mata sujada.......!

Post a Comment

0 Comments