TOP HAUSA NOVELS atOptions = { 'key' : '20e08520dad54dbf6d9e963271

'Yar Tsakar Gida 1-2 page 5-8

 


Kallon Manyan idanun ta yayi yana ɗan yin ƙasa da kansa tare da kallon Ƙwayar idanun Amrah yana cewa " Mene kika ce.? . Cike da Sanyi don jikin ta ya ida mutuwa Ganin yanda tayi sharkaf a ruwan nan yau tasan Da tsumammun kaya zata Wuni har ta kwana ,hakan yasa ta yin laƙwaam takaicin Nurain ne yanzu take ji ,don idan da bata biyo sa ba Da hakan bai faru da ita ba a ganin ta . Cikin Nuna ka dameni tace " Nurry .! Dariya yayi mai fidda Sauti fararen hakoran sa na bayyana tare da Siririn Hushiryar sa . A dakyau. Suna mai daɗi . Ya ƙare maganan yana kallon ta tare da mata Murmushi . Cike da Rashin Sanin makaman zancen nasa ta juyar da kan ta gyefe tana kallon Ababan Hawan dake Wucewa gefi² ,don bata ƙara bi ta kansa ba bare tasan Mene yake yi .  Ruwan ne ya ɗan fara Ɗaukewa wannan yasa Amrah murmushi tana leko da kanta ta Wajen Lange ² Rufin mai tsiren . A hankali ta ɗago da idanun ta sama tana kallon yanda ruwan ke saukowa ta saman Fale-falen Shagon ,wannan yasa ta cike da murmushi takai Hannun ta tana tarawa ruwan na zuba a tsakiyar taffan hannun ta . Tsayawa yayi yana kallon ta tare da murmushi kamin Nurain shima yakai hannun sa yana Daura Hannun ta a saman taffan hannun shi yana tarawa a tare da nashi . Waigowa tayi tana kallon sa a wannan karon dariya tayi masa tana cewa " Nurry Ruwan ya kusa ƙarewa muyi sauri muyi sauri fa kar ruwan ya dawo . Amrah ce tayi maganan cikin Sauri tana janye Hannun ta daga nashi tare da Fitowa daga Rumfar tana nufar inda keken Nurain yake . Bayan ta ya biyo yana Tahowa tare da Hawa yana dorata bisa cike da nishaɗi suke tafiyar don a yanzu ruwan ya dauke sai dai Ɗan yayyafi . Fuskokin su kawai zaka kallah ka tabbatar da suna jin daɗin kasancewar su a hakan . 


Tafiya ce ta mintuna Goma sha biyar ya kasu zuwa ga layin su . Lokaci daya Fara'ar nata ya Ɗauke , Kirjin ta taji yana buga mata da ƙarfi tuno da Baba Zuwai da tayi . Nurry Sauke ki anan. Bakin sa yakai zuwa Saitin kunnen ta yana cewa " Ina ne Gidan ku anan da zan sauke ki .?  . Nidai A'a ka sauke Ni idan ba Haka ba Zulai ta ganni a keken ka zata faɗa ma Baba Zuwai ne . Kallon Gyefen sa yayi yana kallon Gidan Mahaifin sa kamin yace " Ni kin ga gidan mu Amrah, Kema muje ki nuna mun gidan ku .A'a Nidai Ka sauke Ni anan zan maka kwatance daga nan . Tsayawa da keken nasa yayi yana kai bakin sa dai dai Kunnen ta sauka to . Cikin Sauri Amrah ta dure tana kallon sa tare da kama Ƙugun ta tana cewa " Naƙi na kwatanta maka Nurry . Tana faɗin haka ta Zura da gudu tana barin sa anan tsaye . Keee Kee Amrah..! Ina ma ta sauke shi lungun da zai kaita Gidan su tayi Saurin bi tana Dariya a ganin ta Wayo tayi masa. Murmushi Nurain yayi yana faɗin " Zan kama ki ai .


Komawa yayi yana nufa Gidan su tare da tsallaka karamar Titin . Gate Man ne ya kalli Nurain yana cewa " Nurain ka dawo ruwa ya duke ka. Wani irin kallo Nurain yayi masa yana kauda kai tare da kokarin shiga cikin gidan da keken sa . Bude baki Mai Gadin yayi zai kara masa magana cike da jaraba Nurain yace " Da ruwan ya buge Ni Magani zaka mun ne kome ne . Ibeg just open the door . Jikin Mai Gadin a sanyaye ya bude masa ƙofan gate din Nurain na shigewa daga ciki . Mama Nanny ce take tsaye a baranda tun saukar Ruwan take jirar tahowar Nurain don yau tasan babu lafiya . Ganin sa da tayi yasa ta Saurin tahowa a wannan yayyafin tana nufosa tare da kama shi tana Rungume shi jikin ta , Wani iliya mai Bama ma flowers ruwa yana amsan keken nasa . Ayya Sorry My Nurain ... gaskiya Ruwa n nan bai ƙyauta mana ba . Taho muje a sauya  uniform din. Ba tare da ya tanka mata ba yabi bayan ta suna shigewa daga ciki . 


**

Ɓangaren Amrah kuwa a zaure ta laɓe tana tsoron shiga cikin gidan , tun daga Zauren take jin Hayagagan Baba Zuwai tana cewa " To gidan Uban ta ta tsaya ko Uwan ta har karfe Uku Da kusan Rabi yau zanci Uban yarinyar nan Wallahi zata dawo ta same Ni . Jikin Amrah ne ya hau Rawa daga tsayen da take , idanun ta na fara Ambaliyar Ruwan Hawaye mai tattare da maraici da tsoro ga tashin hankali . Kaman daga sama ne ta jiyo Muryar Zulai wacce bata san ta fito ba tana cewa " Laa Baba Zuwai ga Shegiyar nan ta maƙale a zaure , bata son ta shigo ne don kar ta kai Miki Tallahn yayi kwantai . Laha'ila kunji baƙin hali irin na yarinyar nan aiko yau sai naci Uban ki . Baba Zuwai tayi maganan tana leko Zauren tare da kamo Amrah tana jawo ta zuwa cikin Tsakar gidan . Kuka Amrah ta fara tana faɗin " Don Allah Baba Zuwai kiyi Haƙuri wallahi Zani Tallahn Ruwan sama ne ya sa na fake a hanya . Wani irin kallo Baba Zuwai ta watsa mata tana daga hannun ta tare da fara Wanke Fuskar Amrah da Mari jikake tasss⁴ har sau hudu .  Jummai ne ta miƙo mata Bulalan Inji tare da Cewa" A'a kar ki Wahalar da hannun ki ga Bulalan da zai shiga jikin ta ?. Amsan Bulalan Baba Zuwai tayi tana Wani irin dukan Amrah tamkar wacce take bugun baligar mace nan ko yarinya ce yar shekaru 7 . Tun Amrah na kuka har sai da bakin ta ya mutu . Sannan Baba Zuwai ta rabu da ita ,don tafi mintuna talatin tana dukan ta kaf cikin Gidan nan babu wanda ya fito Kwatar ta . Numfasawa Baba Zuwai tayi tana cewa " Dan uban ki kuma ki Ɗauki Tallahn Gyaɗan  gashi can ,na ɗari Biyar da hamsin ne ,Naira daya ya ɓata sai naci Uban ki Wallahi . A hankali Amrah ke jan jikin ta , fuskar ta duk ya kumbura na tsaban Mari hannayen Ta duk sunyi shatin bulala suna zubda jini . Jan jikin ta tayi tana Ɗaukar Farantin gyaɗan tare da Ɗaurawa a saman kan ta . Idanun ta na ganin duhuwa Ga yunwa ga duka da tasha na mutuwa . Nufar Hanyar kofar gidan tayi tana tangaɗi kaman zata kife . 


**

Zaune yake a saman Ƙayataccen Bed ɗin shi ,ƙafafun shi na akan jikin Mama Nanny wacce take ta matsa masa ƙafan a hankali tana basa labarai masu daɗi ,tamkar yanda mahaifiyar sa ke masa . Kallon Nurain nayi Da yake sanye cikin Kananun kaya Rigar jikin sa T.shirt Blue sai Wandon jikin sa Farin jeans mai ɗan yalwa bai takura shi ba .  Sunan Labari Mama Nanny ke basa Amma sam baya ta kan ta idanun sa na akan laptop ɗin sa dayake playing Game . Saurin Kallon Nanny yayi yana kiran sunan ta da "Halima Ƙarfe nawa yanzu.? . Ɗaga idanun ta tayi tana kallon Agogon dake maƙale a bangon Bedroom din nasa kana tace "ƙarfe Huɗu da rabi . Ohhhh God . Saurin Miƙewa yayi yana Zura Room silipers din sa tare da cewa " Ina zuwa .? Ficewa yayi daga Dakin yana nufar Wajen Farfajiyar gidan,inda ya hango mai Gadi can zaune a Kujeran sa . Nufar inda yake yayi ,yayin da mai gadin yayi Saurin muskutawa yana Miƙewa tsaye tare da cewa " Barka da fitowa Nurain . Bude mun kofa ,ina kujeran nan naka ? , Kasa mun a waje zan zauna yau .! Cike da dan gajeren mamakin yau Shine zai zauna a waje.  Yaron rainon turawa sam baya son hayaniya kullum yana daki yau shine zai zauna a waje . Murmushi yayi yana cewa " Ohk sir . Yanda suke basa Girma ka rantse babba ne nan kuwa yaro ne wanda a wannan lokacin baifi Shekaru 16 ba. Jiki na Rawa Gate man ya aje masa Robber chair tare da ja gyefe Nurain na zama . Mintinan sa baifi Uku da zama ba ya hango Ta dauke da farantin gyaɗa a bisa tsakiyar kan ta . Idanun ta na kallon Ƙasa . Jan jikin ta kawai take yi dagani kasan da Akwai Abin dake damunta . Idanun sa ya kafe a kanta na yan Daƙiƙu har ta zo ta gaban sa zata Wuce bata Gan shi ba don gaban ta kawai take kallo . Motsa Laɓɓansa yayi yana kiran Sunan ta yanda zata ji shi " Amrah....! 

A hankali ta ɗago da idanun ta tana sauke su bisa Fuskar sa ,wani irin sanyi taji ya ziyarci zuciyar ta , nan take ta Wangale masa baki tana dariya tare da Cewa" Kaine ....?


**

```LONDON```

*JENNYLYN_MARCADO INTERNATIONAL SCHOOL*

SS 2 class . Hayaniyar Ɗaliban gaba Ɗaya kake ji tun daga Upstairs din har ƙasan ajijuwan . Gaba daya yaran Class din basu wuce 12 ba mata da mazan su . Malaman nasu da yawa sun shigo akan suyi shiru Amma kuma sam hakan ya gagara don su a ganin yanzu seniors ne daga Wannan Term Din zasu shiga SS3 . tsiiitt naji Ajin yayi kaman ruwa ya cinye su ,Wannan yasa  Ni saurin juyawa ina maida idanuna kan kofar shigowa ajin . Wani cute Handsome boy na gani Sanye cikin kayan Sport wear na Makarantar . Fari ne Tassss dogo ,suman kanshi yayi Askin su ta zamani gaba an tara gashi baya an kankara , Gyefen Kunnen sa Dan kunni manne na gani Yayin da Fuskar sa ke cikin tabarau irin manyan nan amma fari ne . Ko ba'a Faɗa maka ba Ɗan Wani Attajirin ne sannan kuma ɗan gayu mara ji na ƙarshe . Mamaki ne ya kamani ganin Yanda Kaf student din suka tashi daga Seat din su suna furta "Good morning Zaid. Takowa yayi yana shigowa kaman wani malamin su yana faɗin " Morning Friends ...mu zauna ko.? Yayi maganan Fuskar sa dauke da Fara'a wanda da gani kasan ba ma'abocin yin Fara'ar bane , a yau yana cikin Wani farin cikin ne da dole sai ya bayyana . Zama yayi a cikin Gang din Abokan nan sa su biyar yayin da daya daga cikin su ke tambayar sa " Zaid Wannan Fara'ar fa meke faruwa ne.? Kallon Abokin nasa Zaid yayi yana cewa " Abokina Nurain zai Dawo America da zama , a bakin Momyn sa naji nan da 2 mount zai taho America . 


To Kai ai anan London kake shi kuma America zaije Meye Amfanin Farin cikin.? Murmushi Zaid yayi yana cewa " Transferring komai nawa zan yi na koma America, dama Daddy na acan yake ,Mom ne ke nan . Yana dawowa zan koma can muyi SS3 a can the same school zamuyi dama primary tare muka yi , Secondary ne yace shifa Nigeria yake so kaga yanzu haka the next 2 mount yana America................

Nigeria
Zuba mata lumsassun idanun sa yayi na yan mintuna kaman mai observing wani abu daga gare ta ,kana ya ɗan kauda idanun sa daga gareta yana mai cewa " Taho mu shiga ciki . Ƙara Ware Lulun idanun ta tayi akan sa kamin cike da tsoro tace " A'a Ba zan shiga ba , tallan Gyaɗa zan tafi sai zuwa Gobe Zamu hadu a makaranta ai ko.? Ta ƙare maganan tana masa tambaya. Humm ɗan sauke Numfashi yayi tare da Ɗaga mata Gira yana cewa " Eh gobe zamu haɗu bama iyaka gobe kaɗai ba ,kullum zamu Haɗu dake. Ki shigo Muje cikin Gida Duka gyaɗan Zan siye . Hahhhh Ta buɗe baki cikin sauri tana Wangale sa tare da Faɗaɗa Fara'ar ta tana faɗin " Noory da Gaske duka zaka saye .? Murmushi yayi yana Kuma cewa " Eh mana Amrah taho muje.  Cike da mamakin to ina zai kai Wannan gyaɗan tuli haka tabi bayan sa suna isa bakin Gate ɗin ya matsa gyefe yana cewa ita ta fara yin gaba ,yana tasa ta a gaban sa . Sam idanun ta baya kan Gidan da suke shiga don mamaki ya hanata kallon harabar Gidan . Noory Amma Gyaɗan nan ai tayi maka yawa . Kallon ta Nurain yayi yana ja cak tare da tsayawa , Hannun sa ya miƙa mata yana karɓan tray din gyaɗan ba tare da yace mata komai ba ya juya yana kallon Baba mai Gadi . Amsa kuci duka , ka aje Tray din idan mun fito zan Amsa . Ganin tulin Gyaɗan yasa Baba mai Gadi Sakin Murmushi yana ware dafaffun Haƙoran sa tare da sambaɗa ma Nurain Godiya . Ƙafadan ta ya dafa yana ruƙota tare da cewa " Ko zaki ci ne kema.? . Duk da tana Son cin Gyaɗan don kuwa rabon ta da Abinci tun daren jiya amma tafi bukatar kudin Baba Zuwai ta gansu ciff ta kai mata su ko tayi kwanan sukuni ,wannan yasa ta cewa " A'a Ba zan ci ba . Ina kudin yake to.? 

Kallon ta yayi saurin yi cike da Tsokana yake cewa " Au kudi zan biya ki ,gashi bana da kudi yanzu ya kenan Amrah.? Innalillahi wa'inna ilaihir raji'un ta furta tana fashe masa da kuka tare da Ɗaura Hannun ta Bisa saman Kan ta . Wasu irin shatin duka ya gani a hannayen ta wanda cikin sauri yakai hannun sa yana riƙo duka hannayen nata biyu . Bakin Nurain ne ya hau Rawa cike da daga murya yake fadin " Amrah Wannan dukan Meye ? , Waya buge ki haka .? . Kallon sa tayi idanun ta na cigaba da tsiyayar da Ƙwallah , cikin karfi ta fizge Hannun ta daga gare shi tana cewa " Ai kaine ka ja mun aka duke Ni ,sai da na faɗa maka duka zan sha idan na tsume a ruwa ,sannan kuma da kayan zan yi bacci . Kuma ai kai ne ka jani da surutu .....ke tambayar ki nake Waya bugeki haka .!! Yayi maganan cike da Tsawa a kuma zuciye...Bakin ta na Rawa don ta tsorata tace " Ba..b..baba Zuwai ne . Don Allah Ka bani gyaɗan na tafi ko kudin gyaɗan idan baka bani ba ina komawa Gida Sai na kusa mutuwa ,tana maganan tare da kama hannayen ta tana Wasa da yan yatsun ta haka idanun ta na a kasa sam bata son kallon ƙwayar idon sa don wani irin Juye mata taga yayi ya koma tamkar Zaki . Hannun ta ya kama yana cewa " Muje Gidan naga Ita Baban taki . 

Saurin kallon sa tayi tana cewa " Noory me ne zaka yi to idan kaga Baba Zuwai.? . Kashedi zan mata ta daina dukan ki , Saboda bana son ganin hakan , sannan ai laifi na ne , Ni na tsayar dake ,me yasa bata zo Ni .... Cike da Yarinta Amrah tayi Saurin riƙe masa hannu tana Girgiza masa kai tare da cewa " A'a Noory kar kaje Mamana ne fa . Kaji Noory? , Tayi maganan cike da rarrashin sa don tasan idan yaje to ita zai ja mawa . Yatsan hannun shi ta kama tana riƙewa tare da cewa " Kaga Ni ma ciwon fa baya mun zafi . Hummmm Sauke Ajiyar zuciya yayi yana kallon Inda Amrah ke nuna masa shatin dukan da yayi jajir wai amma tana faɗa masa ba zafi . Tausayin ta ne yaji ya ninku a zuciyar sa . A hankali ya kewaya da Hannun sa yana Rungumo ta tare da nufar Falon cikin Gidan. 

Mama Halima ne ta taso tana saurin ƙarisowa inda Nurain yake ,cike da mamaki take furta " Nurain Wannan Wacce yarinya ce ..? Tsayawa yayi yana kallon Nanny kamin ya kalli Amrah itama wacce take kallon sa . Kaman zai mata magana sai kuma ya kama Hannun Amrah yana ƙoƙarin Wayewa benen dake tsakiyar falon inda Bedroom din sa yake . Ganin haka yasa Amrah saurin riƙo hannun sa tana tsayawa ,wannan yasa Nurain juyowa yana kallon ta . Bari na faɗa mata ba mama ce ba .? . Hannun sa yakai yana shafa Gyefen kwantacen Girar sa kamin ya Girgiza mata kai yana cewa " Wannan mai AIKI ce tana kula dani sosai ,amma biyan ta ake yi ,sai dai tana kokari Nanny tace sunan ta Halima . Noory ....! Amrah Ta kira sunan sa tana kallon sa kamin tace " Babu kyau kiran sunan manya ,kace mata Mama idan ba haka ba ,Bazan biyo ka ciki ba , komawa zanyi . Murmushi Mama Halima tayi tana faɗin " A'a yarinya Bakomai ku shiga .  Maƙale Kafaɗa Amrah tayi tana cuno dan ƙaramin bakin ta tare da cewa " A'a Ni komawa zanyi na fasa shiga . Sorry I'm Amrah , Mama kiyi Haƙuri ...Nurain yayi maganan yana kallon Fuskar Amrah tare da murmushi yana cewa " Shikenan Amrah.? . Gyada masa kai tayi tana murmushi tare da cewa " To muje . Hannun ta ya kama suna shigewa daga ciki .Bin bayan su Mama Nanny tayi tana tsintar kan ta cikin jin dadin haɗuwar Nurain da Amrah haka kawai . 

Tun da ta shiga Bedroom din take bin ko ina da kallo ,ganin Wurin take tamkar a mafarki ba a zahiri ba ,don bata taɓa riya ma zuciyar ta akwai Wuri mai ƙyaun wannan Wurin a duniya ba. Amrah Taho ki zauna anan . Yayi maganan yana nuna mata Gyefen Gadon sa inda ta tsaya tana kallon sa kana tace " Idan na zauna jiki na zai tsuma maka Katifa . Dan Rintse idanun sa yayi don bai san me zai mata ba . Wannan yasa shi kare mata kallo yana cewa " Zaki iya zama da Towel.? Meye Towel kuma.? . Ohk ina zuwa , yayi maganan yana nufan inda Waldrop din sa yake . Gani tayi ya dauko farin Towel yana cewa " Gashi ki daura Wannan sai ki bani kayan ki ,Mama Nanny ta Wanke Miki su kamin ki tafi zasu bushe . Kai Noory na gode sosai.... Tana maganan cike da jin dadi sam bata tsaya bi takan sa ba ,don ita bata san darajar jikin ta ba ta fara kwabe Skirt ɗin jikin ta kasa . Kee Keee....yayi saurin dakatar da ita yana faɗin " Ba'a cire kaya a gaban mutane .  Amsa Towel ɗin Bara in juya baya idan kin saka sai ki mun magana . Kallon shi tayi tana murmushi kamin tace " Kalli Noory ina da Pant a jiki na . Kauda kan sa gyefe yayi ba tare da ya kalleta ba ya mika mata Towel ɗin yana faɗin " Ɗaura sai kizo muyi Karatu ...! Yeeee Noory karatu zamu yi ? Amma fa ban iya ko ABCD ba . Murmushi yayi yana Fiddo da Wasu English taxt book na primary 1 . Tare da Exercise book da pencil . Amrah da pencil kuke Amfani ko .? Watsar da kayan uniform din tayi a Gyefe tana saurin zuwa inda yake tana zama gyefen shi . Eh Noory koya mun yanzu . Murmushi yayi yana buɗe Littafin Straight for English inda Tsakiyar littafin Aka yi zanen likita . Laa Noory Wannan ai malamar Asibiti ne . Cike da rashin Fahimtar Hausan nata yace " Likita ko , Doctor . Nan gaba Nima likita nake na zama , Mom Dina Nurse ce ,Amma Ni nafi son na zama medical Doctor . Kefa me kike so zama for your future life . Shiru tayi tana tunanin Abun da zata ce . Dai dai Mama Nanny na shigowa . Nurain Akwai Abin da kuke bukata.? Eh Mama ga kayan Amrah nan a wanke mata a goge mata kamin ta tafi ,sannan a fara kawo Abinci muke buƙata . Ohk Mama Nanny tace tana kwasar kayan tare da ficewa dasu a hannu . Noory ina so na zama kaman mama Nanny ce . 

Cikin Kullewar kai yace " Nanny ..? But Why? , Me yasa Amrah kike so ki zama irin ta.? . Cike da Yarinta take kallon sa kana tace " Saboda tana kulawa da kai sosai , Ni kuma Baba Zuwai bata kulawa dani, ina so na kula da yara iri na nan gaba .  No ba zaki nanny ba , ki ƙara tunanin wani abun dai da kike so ki zama think very well Okay.? . Uhmmm ta ɗan jan tunanin ta kamin tayi saurin cewa " Yauwa ina So na zama Babban mutum kaman kai din nan." Kechewa da dariyar da bai shirya ba yayi kamin yace " That's Very Good Amrah . Kina son haka , Yanzu sai kinyi karatu kin mun Alƙawari zaki yi karatu ko ina tare dake ko bana tare da ke.? Ki mun Alƙawarin Hakan .? . Ɗaga masa kai tayi da hannu tana cewa " Eh mana Noory nayi maka Alƙawari zanyi Karatu don na zama kaman kai . Murmushi Nurain yayi yana cewa " to mu fara mu gani . Bude littafin yayi inda farkon page din ya fara da ALPHABET.nan take ya fara karanta mata A_Z . Wanda sosai yayi mamakin fahimtar Yarinyar. Kamin Mama Nanny ta kawo masu Abinci ta kusa iyawa ,wannan yasa koda Ta hada masu abincin tana gama ci ta Cigaba da karatu don ita so take ta zama kaman Nooryn ta. 

Wuraren Karfe 6:30pm . Ta kammala karatun ta tasss ta iya kuma tasan Alphabet a ido da kuma kawo shi a haddace . Kallon ta yayi yana miƙa mata uniform din da Aka wanke aka goge ga sabon jaka da Farin safa.  Noory Wannan ai ba kayan makaranta na bane ko?. Murmushi yayi yana kallon Mama Nanny itama dake Murmushin kamin Tace " Amrah sune , kullum idan kin dawo ki rinƙa kawo mun ina wanke Miki kinji . Na gode mama . Amrah tayi maganan tana kallon Nurain dake ta kallon ta . Gobe idan kika kawo mun Karatun duka akan ki to bayan sayen gyada da sanyi har kyauta zan baki . Dariya tasa sosai tana cewa " Da gaske Noory ? , Gobe zan kawo maka duka..........
**
To yau dai da Alama  Wannan Yarinyar ta shirya miki Asara Zuwai . Har yanzu ana kiran Sallah amma shiru kake ji . Jummai ce mai maganan tana yi tare da surfe Wake . Kai Wannan yarinya anyi tsinanniya . Tirr duk inda aka ce maka shege yake to sai ya nuna halin sa, Bara ta dawo ta same Ni.... Assalamu alaikum Muryar Amrah ya katse su cikin sanyin nan nata . Kasa magana duka suka yi ,ganin ta da Sabon kaya a jikin ta , sai Farantin gyaɗan data dora wankakkun uniform din ta akai . Ehhhhh...??? Larai ta furta tana kallon su Baba Zuwai . Ke gantali kika fara ko kuwa mene ? Wane ne ya baki kaya har da chanja Miki . Mun shiga Uku mu , kin san fa yanzu a lungu ake lalube yara a ƙwaƙule su tasss . Babban magana dama an haife ta akwararo yanzu itama zata haifo mana dan kwararo .............!
 

Kallon su Amrah keyi sam ta rasa fahimtar inda maganan su ya nufa , abun ka ga karamin yaro Hausan har a lokacin koyan ta ake yi,wannan yasa ta kallon Baba Zuwai tana cewa " Wallahi Baba.....yi mun shiru...!! Ta daka mata Wani irin gigitaccen Tsawa tana mai Cigaba da cewa " Nawa Ɗaya shine ki bani Kuɗi na casss Don Ƙwandala ya ɓata sai na sauya Miki kamanni da Duka a cikin gidan nan . Cikin Rawar Jiki Amrah ta miƙa ma Baba Zuwai kudin ,jikin ta ko ina Rawa yake yi ,tsoron ta ɗaya kar yazo kudin bai kai ba . Muryar Baba Zuwai ne y katse ta tana faɗin " Allah ya cece ki sun cika , wuce Ki Dauki bokiti ke debo ruwa ki zo ga kwanuka can ki Wanke su . Tom Baaba . Amrah tace tana Saurin wucewa ɗakin Ikilima don anan yanzu Amrah ke kwana ita Ɗaya ,don ikiliman bata nan . Duk da A wannan shekaran zata dawo Gida Shikenan kuma an gama Sakandire . Aje uniform din nata tayi tana saurin fitowa tare da Ɗaukar Bokiti da Wannan yammacin tana nufar makoton su inda suke da rijiya don ta debo Ruwan wanke wanken  .
**
Akwana a tashi babu Wuya shakuwa da soyayya tamkar yaya da Kanwa ya shiga tsakanin Nurain da Amrah ,wacce a yanzu take cikin zakukwuran yaran Ajin nasu . A farkon Term din tayi na Goma wanda a jarabawa na gaba tazo na Uku . Sam a yanzu bata damuwa da Fitinan cikin gidan su da tsangwaman da take sha , Don idan sun ɓata mata tana fitowa zata shige Gidan Su Nurain , Anan zai Amsa kayan tallahn ta ya rabar suyi hira tayi barci idan ta huta sai suyi karatu . Sosai kokarin Amrah ke basa mamaki don kullum a zuciyar sa cewa yake " An kashe product anan , Don bata yi sa'an Iyaye ba ,duk da a yanzu ya san ita marainiya ce . Wannan yasa shi sosai yake bata kulawa ,ya zama mata tamkar uwa uba bango majingina . A yanzu har yakai ya kawo sunan ta a makarantar ƙanwar Nurain ,don da yawa wasu suna mata kallon ƙanwar sa ce . 
Ihun Ɗaliban ne yasa Nurain Wanda a yanzu suke SS 3 kuma yana da muƙamin Headboy saurin juyowa shi da duka abokanan nasa suna kallon inda Yaran primary din suke a layi . Sunan Amrah ne ashe da aka kira a matsayin wacce tazo na uku yasa Ɗaliban ihu suna kiran sunan ta Da Fine Girl fine girl don sunan da suke kiran ta dashi kenan . Tsayawa yayi yana murmushin nan nasa yana gani Amrah ta fita cike da karsashi da gwarin Gwiwa ta ta amsa Kyautar nata tana juyawa tare da kallon Ɗaliban tana mai ɗaga masu cike da fara'a . Juyawa Nurain yayi yana kallon Abokanan nasa suna barin Wurin don ita Amrah bata Gansu ba ma .  A cikin Ajin su babu wacce Amrah ke shan Wuyan ta irin Naana bata da kirki ,kullum aikin ta kenan bin ajijuwan tana cewa " Ai Amrah yar talakawa ce har tallah take yi , basu hada komai da Nurain ba . Duk tana faɗin Wannan maganan ne saboda Tasan Familyn Nurain . Don da mahaifiyar ta da Momyn Nurain ƙawaye ne sosai . Don a bakin Naana Mommyn Nurain ta fara jin sunan Amrah da Halakar su da Nurain . Kallon Marian tayi tana dalla mata harara tare da kallon Amrah wacce ta dawo inda suke tsaye . Bakin ciki ya ishi Nana do mun kuwa ita ce ke daukar positon din da A yau Amrah ta dauka , ita kuma tayi baya don na Huɗu tazo . Humm Wacce kike ne ? Amrah Ko? , Kar ki manta Wacece ke , Haka zalika kullum talaka a kasan mai Arziki yake , Ki daina farin ciki don a yau kin zo na Uku a gobe ina nufin a kwana a tashi Ni zan zama ta gaba dake , sannan ke matsayin ki ba zai wuce mai mun shara da goge goge ba .  Mtswwwww...! Saurin buɗe baki Marian tayi zata yi mata magana sai Amrah ta riƙe ta tana Girgiza mata kai Alamun ta rabu da Naana don ita bata son tashin hankali gaba Ɗayan ta ,sannan kuma sam bata ji zafin maganan Nana ba ,don dama tasan Naana ba tsaran ta bane . Duk Hutu suna Abroad kin ga ba zata hada kan ta da ita ba . Idanun ta sun ciko da ƙwallah sosai Amma sai ta maidasu tana lallashin Zuciyar ta daba kan ta Haƙuri .
**
A hankali take kutsa kan ta Izuwa Falon Gidan ,cike da Sanɗa wai a dole tana so tayi surprising din sa . Yanda taji Muryar nasa ne yasa ta saurin ƙarikawa inda yake , Sakin Takardar da kyautan nata tayi a ƙasa Ganin Hawaye na bin Kuncin Nurain , Jarumin Namiji wanda ko karaya bata taɓa Gani a idanun sa ba ,amma a yau taga Hawaye . Cikin nuna damuwa ya furta " Please Mommy ki bari na kammala SS 3 ɗin After all sai na dawo America, idan na tafi Wane zai kula da Amrah.? . Wacece Amrah ? , Muryar Daddyn shi ya katse shi cikin zafi ,wanda da'alama mutum ne mai zafi , gobe zan sa a zo dauke ka , jirgin 11am zaku biyo zuwa America. Tare aka haife ku da ita yarinyar ne ? , Ƙanwar Nusaiba tana SO ta ganka duk ta damu , yau ne fa karin Shekarun haihuwar ka ,amma baka sai dai muyi ta kallon hoton ka . Shiru Nurain yayi a zuciye cike da sangarci irin na yaran Hutu ya Datse kiran yana cilli da Wayar can Gyefe . Kallon sa Amrah tayi a hankali ta kira sunan sa da " Nurain ...! Ɗago da sexy eyes din sa yayi yana kallon ta kamin yace " Na'am Amrah . Meke faruwa ? Tafiya zaka yi ? Zaka koma America ne inda Mommy da Nusaiba suke kaima?.  Duka a lokaci daya take jero masa tambayoyin nata . Cike da son kawar da damuwan sa ya kalle ta yana kafe ta da idanu,kawai sai taga ya zaro mata idanun sa yana tsora ta ,saurin bata tayi ,nan take ya hau yin mata Dariya yana faɗin " Matsoraciya . Taho muje kasa palour . Bin bayan sa tayi tana faɗin " Nurry ka daina tsorata Ni da yawa haka . 

Me hoto ta gani a tsakiyar falon , yayin da Nurain ta kalle ta yana cewa " Amrah today I'm + 1 . Wow Happy birthday Nurry . Murmushi yayi yana rike hannun ta tare da furta " Thank you Amrah . Cake din da Mama Nanny ta kawo masu ne Amrah ta kallah kamin ta tsinkayi Muryar sa yana cewa " Mama Shigo Mai Photograph yana jira a dauke mu duka . Rungume Nurain Amrah tayi a tare suka dau hoton wanda yawan su yafi talatin fiye da Ashirin suna tare daga ita sai shi suka yi shi . A wannan rana sun wuni cikin nishaɗi har wuraren yammaci . A farfajiyar Gidan ne ta kalli Nurain tana cewa " Nurry ina keken ka yake.? Juyawa Nurain yayi yana kallon Can Gyefen Garden kamin yace muje can ki gani . Kai tsaye suka nufa Garden din Nurain na fiddo da keken sa Taho ki hau . Yayi maganan yana kallon Amrah don yasan Abun da take so kenan . Kallon sa Amrah ta tana masa dariya tare da cewa " yeeee tana saurin hayewa ta gaban shi yana fara juyi da ita a keken suna kaiwa da komowa a tare . Su kan su basu san mintunan da suka ɗiba a hakan  Amrah ..... Taji Muryar sa ya kira sunan ta. Ɗaga idanun ta Tayi tana kallon sa fuskar ta cikin matsanancin fara'a ,Kiyi Haƙuri kinji..." Uhmm mene kayi mun Noory.? Murmushi taga yayi mata yana Girgiza kan sa tare da cewa " ba komai . Kallon sa Tayi tana jin akwai wani Abu kamin tayi masa magana Muryar Mama Nanny ya katse su tana faɗin " Dare fa ya fara yi , Amrah ta tafi Gida haka . Sauka Amrah tayi daga keken tana kallon Sa tare da daga masa hannu tana faɗin " Sai da safe.  Ba zan jira ka ba gobe makaranta xan tafi ,idan ina jiran ka Zango daya ke wuce ku kullum . Idan kazo school ma haɗu . Juyawa tayi da gudu tana barin Wurin . A hankali Nurain ke sauke Numfashi don ji yake tamkar zuciyar sa zata tarwatse.  Idanun sa na fidda Hawaye masu zafi da raɗaɗi . 

Kama hannun sa Mama Nanny tayi tana nufar palour dashi . Nurain kayi hakuri Kabi maganan iyayen ka , ko mun daɗewa wata rana zaku hadu da Amrah . Tafiya ba mutuwa bace ba . Mama yanzu ba yanda za'a yi Amrah tabi Ni mu tafi America,ko na roƙi Baba Adamu ?. Cikin Sauri Mama Nanny tace " A'a Ba zai yiwu ba ,ko itama Amrah ba zata bika ba . Rintse idanun sa yayi yana cewa " ki haɗa mun kayan da zan tafi dasu . Gyada masa kai Mama tayi kurum tana gani ya wuce ciki ,a zuciyar ta hamdala take yi daya amince da tafiyar nasa do mun kuwa bakaramun fada ta sha ba a gurin mahaifin sa , a cewan sa tayaya ta bari har Wata mu'amala ta shiga tsakanin sa da yar talaka...? 
**
Zama yayi a kasan tiles din yana bin gift din Amrah da sakamakon jarabawar nata da kallo . A hankali ya kankafe yana yo kasa dasu tare don yaba Mama ta sanya masa a jakar tafiyan sa .

Safiyar Alhamis . 
Zaune Amrah take a cikin Ajin suna fira da ƙawayen ta . Kaman Ance ta juya idanun ta ya sauka akan Naana dake mata wani irin Dariya . Humm sauke Numfashi tayi a hankali tana Cigaba da Rubutun ta a haka har aka Tashi break . Marian ina zuwa ko zaki rakani Secondary Section . Hahaha....Uban me zakiyi a secondary section din.? Muryar Naana ya katse ta , takowa tayi gaban Amrah tana faɗin " Nasan Wurin Nurain Zaki je ? Shin baki da labarin Nurain ya koma America da zama. ? Kirjin Amrah ne ya buga daaam . Ai ba zaki ƙara ganin Nurain ba ya Miki nisa nisan da ba zaki taba iya cimmasa ba . Kallon Naana Amrah tayi kawai sai ta juya da Gudu tana nufar Section din su . Voting ta tadda Sunayi na sabon Headboy wanda Ganin haka yasa Zuciyar ta kare karyewa . Juyawa tayi tana ware ware tare da kallon Yan Class din nasu . Amrah ...! Taji Muryar saif ya katse ta . Cikin sauri ta Juyo tana kallon saif tare da cewa " Ina Nurry yake ? Don Allah ka faɗa mun yana ina..? . 

Kallon Amrah saif yayi cike da daurewar kai yace " A'a bai faɗa Miki zai koma America da zama ba ? , Ai yanzu ma haka jirgin su ya Ɗaga nake tunan.... Kamin ya ƙarike Maganan ta juya da Gudu tana nufar Hanyar Gate . Me Gadi dai yaga yarinya ta felle ne ta gudu wannan yasa shi kiran sunan ta da Ƙarfi Amma ko waiwayowa ba tayi ba . Gudu take yi iya ƙarfin ta wanda sam bata tsaya ba sai a bakin Gate ɗin Gidan su Nurain.  Baba mai Gadi ta gani a kofar gidan ,Wannan yasata ƙarisowa cikin haki take fadin " Ina Noory.? . Kallon ta ya tsaya yana yi wanda Ganin irin kallon da yake mata yasa ta fara zubda Hawaye . Da gaske ne kenan ya tafi.? . Girgiza Kai Baba mai Gadi yayi cike da Tausayin Amrah kana yace " Kiyi Haƙuri Amrah , kuskuren naki ne tun farko kin shiga jikin wanda yafi ƙarfin ki , sanadin ki mahaifin sa yasa shi don dole sai ya koma America, Saboda baya son hulda da talaka . Yaji labarin ki , kuma ko da kika ga Nurain a nan layin mahaifiyar sa ce taso hakan ,ba tare da mahaifin sa yasan a cikin talakawa yake zaune ba . A yanzu ina so ki manta da Nurain domin gidan nan ko kin shiga babu kowa cikin ta ya sallami kowa,sannan Nima yanzu ina hada kaya na ne xan koma Garin mu ta buzaye . Karan motocin da Amrah taji ne yasa ta Saurin juyawa tana kallon Wasu irin manyan motaci irin na rusau din nan . Hawayen idanun ta karuwa suka yi . Baba mai Gadi Nurain ya tafi kenan . Amrah kalli kiga wannan motocin sun zo ne don rushe Gidan nan , saboda Mahaifin sa baya son alakar ku Dawowan Nurain ba yanzu ba . Kuma ko ya dawo Nigeria ba lallai ya gane inda kike ba . Saboda rushe gidan nan za'a yi inda ya zauna ma ba zai gane ba . Idan kuwa aka rushe nan da shekaru uku Ba za'a gane komai ba ,bare kuma ya kai ga Shekaru goma . Kiyi Haƙuri ki manta da komai ,ki manta da kin san Nurain .!  Ɗauke Wuta tayi tana kasa ce masa komai ya juya yana barin ta anan tsaye don baya da bakin da zai Fahimtar da ita .

A hankali take daga ƙafan ta tare da Nufar can Gyefe tana gani aka fara rushe gidan yayin da bata motsa ba har aka maida wurin flat .zama tayi a bakin hanyar tana wani irin kuka mai ban tausayi da raunana zuciya . 
**
Akwana ta a tashi Wahalan nata na karuwa amma a haka take girma ,tana manta komai a rayuwar ta amma ta kasa mantawa da Nurain wanda a yanzu gidan su ya zama Wani karamin kasuwar layin don fili ne aka maida shi na Al'umma ,wannan ya tabbatar mata da cewa " Mahaifin Nurain wani babban ne a Nigeria.  A yanzu sun kai Primary 5 inda a yanzu hanya ta biyo don an ce tazo da kuɗin zana jarabawar shiga Js 1 . Sannan scholarship ɗin nata ya ƙare yanzu sai dai ta biya kuɗi idan tana son tafiya Ajin gaba ko ta sauya makaranta . A Tsakar gidan taci karo da Baba Adamu wanda shima a yanzu yana jin jikin sa halin rayuwa kudin ma babu kwatakwata . Sannu da Jiki baba . Yauwa Amratu ,yayi maganan yana kokarin ficewa . Nufar dakin Baba Zuwai tayi sam ta kasa tambayar baba Adamu . 

To maza a sauya kaya azo a dauki tallann Awara . Kallon Baba Zuwai tayi kana tace " Tom Baba , Baaba An Koro ni kudin jarabawa Zamiyi exam . Don Allah Baaba ki biya mun ,idan banyi ba ba Zanje Matakin gaba ba . 

Wani irin Kallo Baba Zuwai tayi mata kamin tace " Alhamdulillah, Na huta da Wannan shegen karatun naki , Ni asara ta haife Ni na biya Miki kudin makaranta,koda kuwa kudi na zuba mun ai ba zan baki ba . Don haka Shikenan . Daga nan kin gama karatu har Abada kuwa.  Wasu irin Zafafan ƙwallah ne suka zubo mata . A hankali take tunawa da maganan Nurain . Ki mun Alƙawari ko dani ko bani Zakiyi karatu . Me kike so ki zama for your future life.? Rintse ido tayi tana tunano da maganan tasu . Ina so na zama babban mutum kaman kai . Dallah dauki Awara ki fita ki zaga mun makota . Saurin daukar Roban awaran tayi tana ficewa daga Dakin . Tun daga nan Amratu bata ƙara karatu ba ta hakura ta aje komai da ya shafi karatu sai Wahala na cikin gidan kawai . Kamin nan kowa yasan ta a ƳAR TSAKAR GIDA.

*2023................*
Amrah......! Amrah.....!! Baba Zuwai ke kwaɗa kiran sunan Amrah tana Fitowa da Dakin Inna Larai . A hankali ta sako kafanta tana fitowa daga Dakin Yaya Ikilima . Kara murje idanu na nake yi ko dai sune basa Ganin mun dakyau . Wow...wow wow . Amrah ce ta zama Wata irin kyaƙyƙyawar Karshe kyawunta ta ko ina ya bayyana. Farin ta ya Fito Tassss. Idanun ta kuwa sun kara yin dulu².  Smiling face din nan nata yana nan , don ta haka ne na hango simple din ta da suka loɓa daga tsakiyar Kuncin ta . Doguwa ce amma matsakaiciya  . Tana da dan dogon hanci sannan siriri,bakin ta kuwa baka ce spoon yana shiga ba . Ga cikar gashin ido dana Gira. Komai sai dai muce Mashaallh, Yanda ta cika ka rantse ta kai shekaru Ashirin , Ga Albarkatun sama da ƙasa.Harara Baba Zuwai ta Watsa mata tana watso mata dubu takwas din Aikin nata kamin tace " Ba kin ce za'a kara maku Kudi a wurin aikin naku ba? Ya nake ganin dubu Takwas...........!

A sanyaye Amrah tace " Baaba Kiyi Haƙuri,Basu ƙara mana ba ,a da baya sunce zasu kara Amma har yanzu shiru , Wasu sunce sai mai Asibitin ya dawo Ƙasan shine ake sa mana Ran ƙarin Albashi .kallon ta Baaba Zuwai tayi tana jan dogon Tsaki... Mtswww" . Shashancin Banza To zaki shirya ki tafi Aikin ne ko kuwa zama zaki yi a Ɗaki ,idan an Kore ki mu koma cin ƙasa kike so? . Yi Haƙuri Baaba yanzu xan shirya dama . Tayi maganan tana kokarin juyawa . Keee Shegiya Ƴar Tsakar gida dakata daga nan ki ji Ni . Cak Amrah ta tsaya ba tare da ta Juyo ba , idanun ta na fara Saukar da Hawayen da suka zama mata jiki a yanzu . Kin san Allah wannan Albashin aikin Asibitin naku yayi mun kaɗan ,duk da dama Aikin kaskanci kuke yi ai , to bai dame Ni ba , daga Safe ne zuwa karfe biyu kuke gama Aikin , a yau kar ki shigo mun cikin gidan nan ba tare da kin ƙara samun Aiki bane ,ki bi layin masu kuɗi ki nemo inda zaki rinƙa masu Aikatau Daga Rana zuwa Dare . Ga GRA nan ga sauran Wurare nan ai ba sai na ɓata Yawun baki na Wurin faɗa Miki Abin da ya dace da abun da zakiyi ba . Gyaɗa mata Kai Amrah tayi kana tace " Tom Mama.  A'a ina Ni ban haife ki ba , Kinga yayana can , Baaba Zuwai ta katse Amrah tare da nuna mata inda su Zulai suke gata nan fa tayi kirɓeɓiya amma babu mijin Aure saboda babu hali . Ƙasa Amrah tayi da idanun ta ,kana ta Cigaba da jin Muryar Baaba Zuwai tana cewa " Don haka kar ki ƙara kirana da sunan Mama , ki rani da Baaba Zuwai yanda duniya ke kirana don Kema a Duniyar na ganki ,har gwara wasu na duniyar dake da ba'a san Asalin ki ba . Lumshe manyan idanun ta Amratu tayi wasu narkakkun Hawayen na zubo mata . Ba tare da ta iya magana ba ta juya tana shigewa ɗaki yayin da su Zulai da Sauran Ƴammatan Gidan suka kece da Dariya har da masu buga Ƙafa . Suna fadin " Baaba Zuwai tamu ,Allah ya bar mana ke . Dadin mu dake tsage Gaskiya ko mun Ɗacin ta . 
A'a To ai Gaskiya ce kuma ban ga Abun tsoro ba , to wa ma zanji tsoron faɗa mawa wannan yarinyar da bata fi cikin hannu ba .  Lanti ce tazo Wuce su data fito daga Banɗaki nan Cike da Tsiwa Zulai ta fara magana tana yin fadan yar hannun ka mai Sanda . Eh Baaba Ai irin Wannan Gaskiyar ne Wasu basa iya faɗi.
Suna tsaka da Wannan maganganun nasu ne Amrah ta fito sanye cikin Uniform din masu Aikin cleaning Dark blue sai farin hijab ƙarami iya kafaɗa . Nufar Igiyar Shanyan tsakar Gidan tayi tana kai hannun ta tare da Ɗaukar Hijabin ta dogo tana sakawa . A hankali ta kalli Baaba Zuwai wacce har a lokacin take bin ta da Wani irin kallo mai tattare da nuna tsana da kiyayya . Baaba na tafi Sai na dawo . Ki tabbatar kin sami gidan Aikatau din da zaki rinƙa yi ,don ina so na ringa ganin Kudin duk wata yana wuce haka . Tom sai na dawo . Banza tayi mata a haka ta fice tana masu sai ta Dawo amma babu Wanda ya kalleta ko ya tanka mata . 
**
*ZAID SPECIAL HOSPITAL*
Shugaban masu goge gogen ne ta kalle su Amrah wacce ta tara a ɓarayin masu cleaning ɗin.  Cike da jaraba da masifa take fadin " Duk Wanda na kama da Kuskure ko ƙalilan ne Koran sa zanyi ,do mun kuwa nima idan an kamu da kuskure nice za'a sallama . Duka idanun su a ƙasa yake ,yayin da Mom Cruzita ta Cigaba da kallon su tana bin Amrah da Wani irin kallo kamin tace " Ke Wacce kike? . Saurin Ɗagowa Amrah tayi tana furta " Amrah . Oh...! Kar na sake ganin ki da Wannan shegen Hajibin naki duk faci da ɗinki ,nan wuri ne na tsafta . Yanda kike tsaye a haka ,haka nake so na Ganki kullum . Kuma dole kuna yin guga don bana son ganin ko wacce ma'aikaciya da Squzing .  Ok Ma. Suka furta a tare . Kowa zata iya Komawa bakin Aikin ta . A hankali Amrah ta juya tana kokarin barin wurin ne taji kiran Mom Cruzita . Cikin sauri ta dawo kusa tana faɗin ' Gani . 

Kiyi maza Office Din Doctor Zaid kiyi aikin ki . Cike da Rashin fahimtar Waye Doctor Zaid ta juya tana faɗin " Ok ma . A farfajiyar Asibitin ne ta kalli Sauran yan Uwan ta masu aiki irin nata kana tace " Hajara Don Allah waye Doctor Zaid? . Wani irin kallo Hajara tayi mata kamin tace " Au Bama kisan Mai Asibitin ba kike so kice? , To me zaki yi masa ?. Hannatu ne ta katse su tana cewa" Haba Hajara ai ba lallai Amrah tasan shi ba ,tun da ba wani dadewa tayi anan ba ,kuma ai shima a satin nan fa ya dawo Nigeria bayani ya kamata kiyi mata . Ohh Haƙa ne ? , To bani da wannan lokacin . Hajara tayi maganan tana Wuce su tare da ɗaukar Roban zuba shaharan su . Humm Kinji Amrah me Asibitin ne ya dawo , jiya da yake da wuri kika tashi shiyasa baki sani ba.  Office din shi sai kin hau benan can . Kin bi kaman zaki operation to hannun dama Office din sa yake . Tom Na gode sosai . Bakomai . Juyawa Amrah tayi tana nufar benen Asibitin tare da Hayewa ,kwatancen Amrah tabi tana nufar hannun daman ta . Idanun ta ne ya sauka akan ƙofan Da bata taɓa lura dashi ba sai a yau .  Gyara Hijabin ta tayi tana kai hannun ta kai tsaye tare da murɗa Handle Door ɗin ,don a tunanin ta babu kowa a ciki ,kuma kaman yanda ta saba zata yi aikin ta ne ta fito . Yanda tayi tunani haka kuwa ya kasance don bata ga kowa ba . Nan ta fara kakkaɓe kakkaɓen ta tare da goge goge tana fashe Wurin da turare kaman yanda suka saba . Wani wuri ta gani kaman Corridor abun ya ɗan bata mamaki amma sai ta dauki bokitin ta tana nufa cikin wurin . A sarari ne ta furta " Me yakawo Gado kuma nan ,kaman Ɗaki,can dai nasan bai wuce consulting room ne to nan kuma fa ? . A yamutse ta ga Gadon nan take ta fara Gyara wurin da Bed ɗin . Waigawa gyefe tayi idanun ta na sauka a Privacy Wanda Tasan toilet ne . Idanun ta a ƙasa ta nufi Toilet din tana murɗa Handle din tare da shiga . 

A zaune ta gansu wanda  da'alama shine Doctor Zaid din , Gyefen sa Wata budurwa ce kosashiya xigidir a cikin baf din Wanka yana zaune hannun sa na saman Nonuwan ta yana shafa su tare da kumshe idanun sa . Ita kuwa Gwanar Tana tsugunne Gwiwowin ta kasa kaman mai rokon tuba tana shafa Madam joy din sa tare kissing din sa da bakin ta . Sakin Bokitin Amrah tayi tana rufe ido tare da yanka wani irin uban ihu gaba ɗaya ta urince ta kasa gudu ta kuma ki daina Ihun . Duk da Ihun nata ya ba Zaid Tsoro ,amma hakan bai hanasa Bude idanun sa a Miskilance ba . Ware tsayayyun idanun sa yayi akan Amrah Wacce ko ina na jikin ta rawa yake , sai ihu da take yi ta zubar da Roban mopping din nata a ƙasa . Sakin baki da Idanu yayi yana kallon Amrah yana haɗiye wani irin yawu...cike da masifa Budurwan masha'an nasa ta dago tana buɗe baki zata yi ma Amrah Tijara ,kawai sai taga ya yi kasa da kanta yana tasa mata Kayan Dadin sa nan take ta cigaba da aikin lashe sa kaman mayya tana tsotsewa . Har a wannan lokacin idanun sa bai dauke su daga kallon Amrah ba . Lasan Laɓɓan sa yayi na ƙasa yana ƙoƙarin mata magana kawai tayi wani irin huruji da gudu ta fice daga Bathroom din ,ko kallon Gaban ta bata yi .  Lumshe idanun sa yayi yana Cigaba da Shafa kan Labiba kana yafara sauke Numfashi da sauri da sauri . Abun nasa tana yo sama tare dayin tsaiiiii tana haniniya . Hannu Labiba tasa tana shafa ta tare da Dannata Izuwa cikin bakin ta tana shafa Twins ɗin sa da hannun ta , aaaahh ashhh aaahh Aaaahhh ya hau jan iska da ƙarfi yana daɗa Zura mata a bakin ta kaman wanda yake cikin Virgina ɗin ta yana sex da ita haka yake ji . Mintuna biyu tsakani ya fara Mata ɓarin madaran sa yana jan numfashi kaman na mintuna uku yayi ƙasan baf din yana sakar ma kanshi shower . Tana cikin ruwan yana wanke Sumar kan sa ,amma har a lokacin hannun ta na ƙasan shi tana ja masa Madam Din nasa tare da Lumshe idon ta alamun bata ƙi sukai dare a haka ba . A Miskilance ya miƙe yana jan Rigar Wankan sa dake saƙale yana gyarawa tare da zuro ƙafafun sa yana saka Toilet siliper ɗin sa . Ɗaga idanun sa yayi yana kallon kansa a madubin Bathroom ɗin , fuskar Wannan yarinyar data shigo yanzu ya gani Wato Amrah ,wannan yasa shi saurin juyawa Yana kallon Bayan sa ,amma sai yaga bata nan , murmushi yayi yana shafa Sajen fuskar sa tare da gyara rigar jikin sa ,inda faffaɗan ƙirjin sa ya bayyana ,ga suma ya rufe luff....Huhhhh Ya furzar da iska yana  ƙare ma kan sa kallo tare da ɗan faɗawa tunanin Wannan yarinyar da ya fahimci babu shakka cleaner ce . Ni kuwa ƙare masa kallo nayi kyaƙykyawa ne sosai kaman balarabe don idan a ƙasar can na gansa to babu shakka zance masa Balarabe saboda kyau sa . Yana da yan matsakaitan Idanu amma a ƙaƙƙafe suke dagani kasan babu kunya a cikin su . Dogo ne sosai tsayayyen ingarman Namiji wato Sexy . 
** 
Mom Cruzita ne suka haɗu da Amrah Wacce take haki gaba ɗaya ta Fita a hayyacin ta . Wani irin kallo Mom Cruzita tayi mata cike da Tsawa take fadin " Kin kammala Aikin naki ne?. Jikin Amrah na rawa tayi saurin Girgiza mata kai Tare da cewa " Eh. Tana saurin wuce ta don Hankalin ta ya tashi kai tsaye nufar ɓangaren su tayi tana ɗaukar Hijabin ta tare da ficewa daga Asibitin ba tare da kowa ya sani ba .
Shiga Office din nasa tayi ,ganin komai ƙal yasa ta kokarin juyawa . Amma sai taji motsin sa daga ciki wannan yasata dan dakatawa har ya fito yana gyara Necktie ɗin sa .  Good morning Sir . Tayi maganan tana dan risinawa . Morning mam Cruzita . Aammm Wannan yarinyar ahmmm .... Dan kame² ya tsaya yi mata a Miskilance,wannan yasa Mom Cruzita saurin cewa ' Sir cleaner ce ,Fatan batayi maka Wani shirmen ba ,don akwai ta da shauni . No jeki kawai idan ina bukata wani abu i Will let you know . Ohk Sir . Tayi maganan tana barin Office din . 

Nufar Table din sa yayi yana ɗaukar Wayan sa tare da fara kiran numbern Aminin nasa dake Abroad....
**
Bayan Fitan Amrah kai tsaye GRA ta nufa gida na biyu ta shiga inda zata roƙe su tana masu Aikatau . Cikin ikon Allah Shamakin Hajiyar Gidan ta amince da ita ,ganin yanda taga Amrah yasa ta yaba da natsuwar ta nan take ,kuma ta shaida mata Albashin ta a wata dubu goma . Sosai Amrah tayi farin ciki da hakan ,don a washe gari suka ce ta fara zuwa aikin ta . 

A washe gari Asibitin Zaid ta fara zuwa ,inda Mom Cruzita tace taje Office din sa ta Yi cleaning,amma sai ta nuna kaman bata Fahimce ta ba , wani Office din taje tayi ,tana gamawa ta lafe ta buya tana ji ana neman ta amma ta gudu wani reception din na majinyata tana aikin a can . Ƙarfe biyu tana fitowa ta nufi Gidan Data samu Aikin . Kai tsaye Falon Hajiya Sa'adah aka nufa da ita .  A ƙasa ta zauna kaman yanda taga shugaban nasu tayi . Ƙamshin turaren Hajiya Sa'adah ne ya mamaye palourn wacce take saukowa daga Upstairs din tsakiyar falon . Fuskar ta ɗauke da fara'a take kallon su , don ita Amrah bata Ɗago ta kalle ta ba . A'a Hadiza Wannan itace Yarinyar.? Eh Hajiya itace . Jin haka yasa Amrah Ɗagowa tana kallon Hajiya Sa'adah dake zama a daya daga cikin kosassun Kujerun palourn . Kasa motsa bakin ta tayi tana kafe Hajiya Sa'adah da ido kyaƙyƙyawar Hausa Fulani ce ,baƙa mai kyau . Ƙwaƙwalwar Amrah ne ke juya mata ina nasan Wannan fuskar . Ganin haka yasa Hajiya Sa'adah cike da fara'a cewa " ya Sunan ki.? A hankali Amrah tace " Barka da Warhaka Hajiya . Yauwa ya sunan ki ne?. Sunana Amrah . Kallon ta Hajiya Sa'adah tayi tana dan yin shiru kana daga bisani tace " Kin san dai Aikin naki ko ? Zaki rinƙa yin Abincin Dare ko wani lokaci , sai dai ki tabbatar karfe 7:pm kin tanadar mana dishes din mu a Dinning . Ok Inshallah Hajiya . Yauwa Hadiza kuje ki sanar mata sauran Aikin ta ,sannan a fara bata Girkin a yau mu ji kalon nata dandanon . Ok inshallah Hajiya . Hadiza tayi maganan tana kallon Amrah suna Miƙewa tare da nufa babban kitchen din gidan .  A zuciyar Amrah cewa take waye Alhajin gidan nan ne ? Kila soja ne , don taga Sojoji dake yawo ko ina a gidan ,sune masu tsaron Gidan . 

...7:00pm ...
Komai na Dinning ya kammala don a dai dai Wannan lokacin Kunun Aya take Aje masu a Dinning ɗin don time table ake bi ,yau suna da jaloap Rice da farfesun Kaza sai kunun Aya da Salad dasu waken Gwangani daga gyefe . Bin kujerun wurin tayi da kallo guda kusan takwas . Amma Babu mutum ko ɗaya da ya fito . A hankali take jin motsin Isowa ana dan dariya cikin Muryar ta tana furta " Ok dear miss youuuu uhmmm 💋 .  Saurin juyawa Amrah tayi suna yin ido Huɗu da fuskar da ta sani farin sani . Wato Naana . Sauke Wayar Naana tayi tana nuna Amrah da Hannu tare da cewa " You....? Kece anann.? Kawai sai ta sheƙe da wani irin Dariya tana tafa hannu tare da ƙarikowa gaban Amrah tana gyara Top din rigar ta ,don English wears ne a jikin ta riga da Wando . Didn't I told you ? , Ban faɗa Miki ba Amrah ? Yau ina postion din Naki ,kar ki manta a Class ni kika doke nazo na hudu kina yar talaka kika zo na Uku . Na faɗa Miki dama Wata rana kece zaki mun shara da wanke² yo gashi,yanzu kece mai girka mana Abinci da Sharan ma duk Abin da muka so shi Zakiyi mu biya ki yar talaka . Shiru Amrah tayi idanun ta na kallon ƙasa . 

Dafa ta Naana tayi tana cewa " Zan baki Albishir Uku zuwa Hudu wanda nasan zai shiga Kwanyar ki da kyau tilent Class . Humm Numfasawa tayi kana tace " Na farko A yanzu ina da takardan Digiri a hanyar nursing a yanzu ina basic nursing wato masters . Kefa? Hahaha nasan Ina ko secondary ba'a gama ba . Na biyu kin san dai yanda mutanen Gidan suka tsani talaka musamman Daddy baya son ido biyu da talaka.  And na uku Humm kina da labarin Nurain ya manta dake da Rayuwar ki ma, don kuwa tun da ya bar kasar nan shekara fiye da goma sha bai dawo ,saboda ya manta dake da Rayuwar ki , Sannan na hudu nan da Watanni Biyu zan Zama matar Nurain.....! 

Saurin Ɗagowa Amrah tayi tana kallon Naana kamin a sanyaye tace " Ina Noory yake ?. Kaji dabba ... Naana ta katse ta , ina zaki ga Nurain har yau bai dawo ba ,sai dai a satin nan zai dawo amma yayi Miki nisa mutumin da securities din sa Sojoji ne ta ina zaki tunkare sa . To yanzu dashi na gama waya , Sannan nan Gidan ba gidan kowa bane Fache Gidan iyayen Nurain..... Hajiya Sa'adah itace Mommyn Nurain....ke Da'allah zo ki zuba mun abinci naci na tashi...................

Post a Comment

0 Comments