TOP HAUSA NOVELS atOptions = { 'key' : '20e08520dad54dbf6d9e963271

DABI'AR ZUCIYA ❤ page: 61 - 62

 61


      Cikin kwanakin da suka biyo baya gaba daya gidan ya canza ya koma wani iri,tamkar gidan da ake zaman makoki,duk da wani ɓarayi na farinciki da ya samu cikin zukatansu,to amma mummy ta bar musu babban tabo a rayuwarsu.


       Mummy tana kwance a asibiti,ta samu mummuna yanka wanda ta illata qodarta,najwa na hannun 'yan sanda,saboda asibiti da suka qi amsar mummy lokacin da aka kaita,suka dage kai da fata sai an nemo 'yan sanda,drivern gidan professor da yaga zai shiga ciki bayan bashi yayi aika aika ba yayi musu bayanin komai,take suka garzaya,suka kuma damqe najwa sukayi ram da ita,baiwar Allah jawahir na azare tana ta tambayar kanta abinda ya faru amma bataji komai ba hakanan bata ga komai ba,don haka sai tadan kwantar da hankalinta,sukaci gaba da zama da tsohuwa yadikko tana kula da ita da ciwon suger dinta daya tashi,ta ta'allaqa zuwan nata ma da ciwon nata da ya motsa.


      Ta gefen dadday gaba daya tunda al'amarin ya faru yana dakinsa ya kulle kansa,babu wanda yake bari ya shiga kamar yadda shima baya fitowa,yayi kuka yayi kuka har baisan adadinsa,yayi nadamar da yace baiga amfaninta ba,yaji gaba daua siyasa ta fice masa fit a ka,ya tabbatar abinda ya sake kawo wannan matsalolin da gidansa ya fuskanta shine rashin samun wadataccen lokacin zama da iyalinsa da ya fara samu sanadin siyasa,ya tuna yadda rayuwar gidansa take a baya,ya tuna irin soyayya qauna da kulawa da yake samu daga raihana,yayi kukan da tunda mahaifiyarsa ta haifeshi bai taba irinsa ba,har sai da idanunsa suka soma rauni.


yayin da saraki ya duqufa wajen ganin an duba lafiyar mommansa an tabbatar da ingancinta.


      Cikin hikima da isa irin ta ubangiji treatment kadam take da buqata,sai kuma idanunta da ya samu raunin gani saboda zama a duhu data jima tana yi,so ko yaya ta shiga haske sai yayita damunta,wannan dalilin ya sanya aka yi mata glass da zata dinga amfaji dashi sanda zafa fita ga haske har zuwa sanda ganinta zai dai daita.


       Sai da yaga yadda jikinta ya fara kyau,ta fara dawowa cikin hayyacinta sannan ya karkata zuwa ga gyaran dukkan abubuwan da suka wakana.


        Da farko bai sanya an kama bala ba,saboda bisa dukkan binciken da yayi ya tabbatar masa da cewa tursasashi akayi ya aikata abinda yayi din,saidai kuma ta yaya zaka yarda kaci amanar mutumin daka jima kana aiki qarqashinsa yana hidimta maka?,wannan shike nuna babu aminta ko kadan tattare dashi,wannan dalilin yasa ya sallami bala daga bakin aiki,abunda ya sanyashi cikin tashin hankali da baqinciki me yawa,haka nan ya kori fawwwaz shima,sa'an nan yana jiran samun lafiyar mummy ya hada ita da hajiya shuwa ya shigar da qara akansu,saboda lallai ba shakka akwai abinda yasa hajiya shuwa yin wannab tonon sililin,ya tabbatar ba banza ba,da ita kuma da mummy shi a wajensa dukka masu laifi ne,laifinsu daya.


       Abu na gaba ya sanya an tattarewa mummy dukka wasu kaya da suka shafeta an kai Warehouse na kamfaninsa an jibge,bayan ya samu Tex daga daddyn kan ya aiwatar da hakan,saidai abu daya ya kasa tabawa ya kuma kasa magana akai shine najwa,sosai jikinsa ke sanyi idan ya tuna waye mahaifinta?,meta aikata?,don jawahir ko sama da qasa zasu hadu baya jin zai bari sunanta ko rayuwarta su baci,kuma bayajin zai bari ta kufce daga hannunsa ko a cire mata sunan 'yar uwa kuma autarsu,saidai kuma ta yaya zai binne abun?,bayan idan ta dawo zata tambayi mahaifiyarta da 'yaruwarta?,ba shakka yaqi ne babba a gabansu.


        Baiyi qasa a gwiwa ba wajen sawa a cafko dukka ma'aikatan da mummy tayi amfani dasu wajen tsarewa da cutar da momma,daga nan aka miqa su kotu aka kuma fara shari'a dasu,bayan ya dora umar kan case din,cikin qaramin lokaci saiga batun ya yadu,cikin manyan shafukan jarida,labarai na gidan radio da television,kafofin sada zumunta,ko ina ka leqa zancan ake tattaunawa

"MATAR BABBAN SIYASA KUMA DAN KASUWA PROFESSOR RASHID AZARE TA BAYYANA A GIDAN MASU TABIN HANKALI,BAYAN DA ABOKIYAR ZAMANTA KUMA 'YAR AIKINTA DATA AURE MATA MIJI TAYI MATA QULUMBOTO TA BADDA ITA TSAHON SHEKARU ASHIRIN DA DORIYA SABODA KISHI KAWAI" topic ne daya dauki hankula matuqa da gaske,aka dinga tattaunashi ana yamadidi dashi.


        Koda batun yakai kunnen samir sai yaji dadi da ya karbi wayar jawahir babbar ya hadata da keypad kan zai sauya mata wata,gidan yadikko kuwa ba wani kallo ta cikayi ba,yasan ba lallai labarin yakai kunneta ba,idan ba takanas wani zaiyi ya gaya mata ba.


         Cikin qanqanin lokaci al'umma da dangi makusanta suka fara tururuwar zuwa yiwa momma barka da fitowa da kuma jajen abinda ya faru,abinda ya sanya samir ya bada umarnin duk wanda yazo ace momma din bata gidan,badon komai ba,sai don yana buqatar ta samu hutun daya dace,ta sake komawa hayyacinta,don har a sannan tana samun kulawar lafiya daga wajen qwararren likita da samir din yayo haya takanas aka ware daki guda ya zuba duk abinda ya kamata kamar dakin asibiti yake kula da ita.


         Cikon sati na uku momma ta fara komawa nutsuwarta,da taimakon bibi da kuma kaltum da take qoqari wajen girka dukka kalar abincin da tasan zai maida ma momman lafiyarta cikin sauri,takan dafa mata dawa kamar shinkafa,tasa mata manja da gishiri,kuma momm din bata qi,tana amsa taci,hakan tasa qashinta ya fara samun qwari nan da nan,kuzarinta ya dawo,abinda zai baka mamaki,tamkar ba itace ta rayu tsahon wannan lokacin tana azabtuwa a rufe ba,saidai idan kayi duba da kasancewarta mace mai tsananun ruqo da ibada tun da can ba abun mamaki bane,to sai kuma zamanta a wancan wajen ya sake sawa ta kusanta kanta da Allah sosai,yawan ambaton Allahnta yafi na baya kafin wannan musibar ta sameta,lalllai ba shakka ambaton Allah kat ne!,dashi kadai kuma zukata suke samun nutsuwa.


      Amiru shine ya ankarar da samir rashin fitowar daddy kwata kwata,sanda yaje gareshi ba yadda baiyi ya fito din ba amma daddyn yace yayi tafiyarsa,ya shiga damuwa samir,saboda yasan abinda daddyn ke dubawa da abinda ke damunsa,saidai yadda ya roqeshin ya tafin hakanan ya tafin kamar yadda ya buqata.


        Wata sabuwa......sanda yake gayawa momma matakin da daddyn ya daukarwa kansa saita kauda kai


"Ka rabu dashi,qila wannan shine abinda yafi dacewa da shi,saidai a gobe inason ka hadani dashi,ina buqatar takardar sakina,don inason nan da rana ita yau na wuce gaban dangina,wadanda basu da labarin fitowa ta" kai samir ya daga,fuskarsa cike fal da damuwa gami da tarin fargaba,da gaske momma take tafiya zata sakeyi a karo na biyu ta barsu?,idan ta tafin to ya zasuyi su rayu?,waye zai zauna dasu?,wacce rayuwa daddyn zai fuskanta a nan gaba?.


"Momma....idan kika tafi kuma?....." Hannu ta daga masa

"Bance kace komai ba" sai yayi shuru yana sadda kansa,kafin ya miqe a hankali,yana jin maqogoransa a bushe,don haka yayi hanyar kitchen don ya samu ruwan da xai sanya masa ko xai dawo dai dai.



        Tarin ganyayyaki ne gefe guda a kitchen din,wanda dukka tayi amfani dasu,wasu cikin girkin da a yanzu takewa momma din,wasu kuma ta zuba cikun kunun ganye data kammala ta sauke,tana ta kiciniyar bude flask don xubawa a ciki kada ya huce.


        Daga bakin qofar kitchen din ya dakata,duk kuwa da tarin qishirwar daya kwaso,ya zuba mata idanu yadda taketa bata fuska da yarfa hannu saboda yadda murfin flask din yayi mata tauri yaqi buduwa,sake gwadawa tayi still yaqi,sai ta sake yamutsa fuska taja ta zauna kan kujerar plastic din dake kitchen din tana tura baki,kamar wani ne yayi mata laifin.


       Idanunsa ya lumshe a hankali,murmushin da baiyi zato ba ya kufce masa,yana jin wata qauna da soyayyarta mai qarfi tana zarmewa gami da kwarara cikin zuciyarsa,tana hawa kuma wani mataki da matsayi mafi qololuwar daraja cikin ransa,matsayin da mahaifiyarsa kadai yakejin ta wuce nan.


        Bai taba zato ku tunanin yarinyar tana da dakiyar da zata aikata abinda ta aikata din ba,bai taba kawowa tsayayyar zuciyarta takai haka ba,abu mafi burgewa tattare da ita tausayi da imani irin nata,da son tsage gaskiya komai dacinta.....wanda dama wannan halayyarta ce tun dadewa.


      Sake dubanta yayi,ta dan fada ita kanta,tunda momma ta shigo gidan bata huta ba itama,bayan ta gama dawainiya da lalurar daddy,shikam a duniya me zaiyi mata ya saka mata?,bayan tsaftatacciyar soyayyarsa da yakejin kaf duniya babu matar data cancanci ta mallaketa irin ita?,UMMANTA ta fado masa a rai,dukka jiki da zuciyarsa sun masa amannar cewa za'a samar da mace kuma uwa ta gari a wajen,haqiqa ta canci dukkan wata soyayya da qauna gami da kulawa.


      Hannayensa ya sauke ya saka kai zuwa cikin kitchen din ahankali,idanunsa na akanta,cinyoyinta sun fito sosai ta cikin wandon rigar baccin jikinta,hakan ya bawa hips dinta damae fitowa sosai,sai ya maida hankalinsa ga qirjinta,wajen da akoda yaushe yake tsole masa ido .


      Sun fita sosai sun kuma tsaya car a jikinta,hakan ya sake baiwa structure na jikinta fita,yabi santala santala hannayenta da a baya suka cika sirantaka,wanda a yanzu sun cika sosai.


       Gab da zai isa gareta ta miqe,ta dan qara gaba kadan zuwa gaban famfo ta tara,ta kunna ta tara saman flask din,wai ko saukar ruwan zai sa flask din ya saki ta samu damar budeshi.


      Ba zato taji an kama dukka qugunta an riqe,amma sai qamshin turarensa ya bata amsar waye,take jikinta ya amsa gaba daya sanda yake sake matso da ita cikin jikinsa,rungumeta yayi sosai sannan ya miqa dogayen hannuwansa ya gefe da gefanta ya jawo flask din yaa bude mata shi,ya daurayeshi sosai sannan ya ajjiye a gabanta


"Gashi nan,me aka dafa mana ne?,saboda rowa gaba daya mu ba'a taba yi mana tayi ba ko?" 


"Subhanallah" ta fada cikin zuciyarta tana qanqame jikinta waje daya,saboda yayi maganar cikin kunneta,hucin numfashinsa da na bakinsa wanda ke bada qamshin mint ya shige kunnenta,ya tada duk wata tsiga ta jikinta,yayin da shi kuma yaci gaba da sansanar wuyanta,sassanyan qamshin turaren data shafa daren jiya na shiga hancinsa,yana aikawa da wani rikitaccen saqo zuwa qwaqwalwarsa,a nutse ya shinfide tafukan hannayensa saman mararta,idanunsa a rufe yana ci gaba da sansanar wuyanta zuwa gashinta dake qamshin man kitson da tayi oiling dashi.


       Idanunta ta mayar ta lumshe itama,saboda yadda gaba daya kowacce gaba ta jikinta lakarta ke mutuwa,ta dora hannuwanta saman nashi hannun tana son zamesu daga mararta,saboda yadda ya tsayar qara gudun zuciyarta


"Karki cire......baki qara wani period din ba?" Ya tambayeta muryarsa qasan maqoshi,kamar wanda ke mata rada,fitar furucin ya qara rudata,saita girgixa masa kai da sauri alamun a'ah


"But....me yasa baki gaya min ba sanda ya dawo?,ko baki shirya karbata a matsayin mijinki ba?" Gaba daya ya sake rudata dajin abinda ya fada din,miji?,ita a yanzu har isarta takai yayi matar aure da ita?,kamar yasan me take tunani,saiya saketa,yaja baya kadan,sannan ya juyo da ita tana fuskantarshi,ya zuba mata idanu da birkitattun idanuwansa da suka sauya launu,tun tun tuntuni......baisan wane baiwa ne da ita haka ba,da yakan samu kansa cikin burkicewa duk sanda jikkunansu xasu hadu waje guda,ko don bai saba hakan ba sai a kanta?.


       Dukka tafukan hannayensa biyu ya saka a kuncinta na dama dana hagu,ya dago fuskarta sosai ta yadda zai iya kallon qwayar idanunta


"Bansan ke alheri bace a rayuwata sai a yanzu,ban kuma sani ba.....ko zai iya karbar wannan samir din a matsayin mijinki?" Idanunta ta runtse,tambayar tayi mata tsauri sosai,yana kasheta ne da wannan tsaiwar tasa cikin jikinta ba tare daya sani ba,muryarsa kadai matuqar dab da ita take hautsina mata tunani take,tasa ta manta abinda takeyi


"Bansan wanne irin tukuici kike da buqata daga wajena ba"


"Ka kaini gida,inason naga ummata" ta samu kanta da fada,hawaye kuma ya biyo bayan maganar tata.


       Kai ya fara girgizawa

"No....no, stop it please" ya fada yana sanya yatsansa yana dauke mata hawayen saman fuskar tata,ido ya tsura mata sosai yana kallon zanen fuskarta,komai yana zaune bisa muhallinsa bisa tsari da halitta me kyau,wannan shine kallo mafi kurkusa daya taba yiwa kaltum din,dan madaidaicin bakinta idanunsa yakai kai,ya zarto da hannunsa wajen zuwa daidai hancinta,ya dora yatsansa guda biyu ya soma zagaye tattausan lips dinta.


       Da hanzari ta qwace fuskarta ta hanyar ja da baya saboda jin wani shock da tayi kamar an jata,tun daga yatsun qafarta har zuwa qwaqwalwarta,sai ya harde hannayensa yana fidda murmushi yadda ta juya baya ta kasa hada ido dashi,idanunta na nuna zallar kunyarsa data kamata.


     Qarasawa yayi inda flask din yake ya dauko ya biyota dashi,ya ajiye kusa da ita yana cewa


"Zan dauki lokaci me tsaho ina koya miki yadda zaki rayu dani,babu abinda kika sani dangane dani illa kamannin fuskata......a yau na shiryawa shaidawa dukkan wanda ya kamata cewa KE MATATA CE" Haka kawai taji gabanta yayi mugun bugawa,tsoro ya kamata,saita daga fararen idaunta ta kalleshi kafin ta janyesu,ta koma qoqarin sauke tukunyar kunu.


       Duk sanda ta kalleshi da fararen idanun nan nata yakanji wani abu ya tsarga masa,ba tun yau ba,ba tun wannan lokacin ba....yakejin hakan,kusan tun ganin farko da yayi mata,ya manta rabon da yaga mace mai fararen idanu kar haka irin nata,sai ya dauka wannan banbancin ne.


       "Bakya sona ne?,ko ban miki ba?" Ya fada yana ware hannayensa gaba daya bayan ya zagayo gabanta ya tsaya,a sace ta kalleshi ta dauke kai,cikin ranta tana fadin,komai kyau isa mulki dukiya ko nasabar mace,bata isa ta kalli samir yace baiyi mata ba.....indai ba irin mazan aljanna takeso a kawo mata duniya ba


"Kalleni sosai....." Ya fada yana sake matsota,sai tayi saurin ja da baya,sannan ta take ta fice daga kitchen din da gaggawa,don tabbas ta bari yaci gaba da hada jikinsa da nata.....batasan iya yadda adadin sonsa zaikai cikin zuciyarta ba.


******Qarfe bakwai na dare ne,cikin shigar laffaya mai azabar kyau butter colour ta nannade jikinta,kamar yadda take kusan rabin shigarta kenan a shekarun baya tun duniya tana kwance.


       Samir ne ya sake knocking qofar,wanda cikim jagulewar rai da zuciya dama yayo rakiyar,don kawai bazai iya saba umarnin momman tasa ba.


       Karo na kusan biyar ya sake bugawa kafin ya iya jiyo maganar daddyn can qasa


"Waye?"


"Samir ne....momma keson magana da kai" daga nan inda yake tsaye,yana iya jiyo qarar saukowarsa da qarfi,da alama amsar da samir din ya bashi tayi masa ba zata,ba'a kuma cika minti daya ba qofar ta bude,karo na farko tun bayan satittikan da suka shude daya rufe da kansa.


      Kallo daya samir yayi masa tausayinsa ya sauko masa,gaba daya ya hada wata qasumba a fuskarsa da kansa,wadda ta cika da furfura,ramar da yayi ta bayyana har saman fuskarsa,wasu qashi dukka sun bayyanar masa.


      Idanunsa nakan momma din a sanda ya bude qofar,sannan ya matsa yana basu damar shigowa.


       Samir yana iya ganin yadda ya saka wani qyalle yana kadewa momma kujerar tare da gaya mata ta zauna,saidai a maimakon hakan saita koma can wani waje nesa kadan ta jingina,fuskarta kuma babu alamun annuri ko fara'a ta fara magana


"Na riga dana hada kayana,inason komawa qasata cikin dangina,nazo ne domin karbar shaidar sakina.....saboda al'adarmu saikin nuna ta koda wani auren naki na gaba zai taso,ina fatan ba zamu tsawaita magana ko bata lokaci ba" sosai tashin hankali ya bayyana kan daddyn,sai samir ya kauda kansa,saboda tausayin daddyn nasa,ya dade da yi.masa uzuri,saboda yasan dukkan abinda ya faru MAKIRCI DA KISSA ne sukayi aikinsu,mummunar kissa abar qyamata.


       Muryar daddyn a dakushe ya fara magana

"Raihana....kiyimin rai don Allah......karki ce zaki tafi ki barni,kunyar ki da kunyar yadda zan tunkareki ya sanya na kulle kaina tsahon wadan nan kwanakin,saboda bani da wani abu da zan gaya miki wanda zan wanke kaina,nasan cewa na rusa dukkan wata yarda da aminci dake tsakaninmu"


"Kayi haquri na roqeka nima,komai da ka yimin na yafe maka albarkacin danka,amma a yanzu ina buqatar shaida ta,saboda inason na koma qasata cikin ahalina na qarasa rayuwata"


"Har yanzu da aurena a kanki raihana......saboda bayan na rubuta saki guda daya......munyi rigima sosai da hafsa a sannan duk da ba'a ganki ba bakya nan,ganin yadda ran hafsa ya baci sai nace na maidaki,kuma daga ranar har kawo yau a yanzun ban janye ba......saidai in sake jadda miki cewa ke matata ce,hafsa itace shaidata"


     Wani nannauyan numfashi samir ya sauke,yanajin wani sanyi yana ratsa zuciyarsa,saidai cikin lokaci kadan momma ta kafe kan batasan wannan ba,don haka samir ya zare jikinsa daga dakin,bai kuma tsaya ako ina ba sai dakin hajiya qarama.


      Baiyi qasa a gwiwa ba ya gaya mata abinda ke faruwa a sashen daddyn,daquwa ta watsa masa

"Don qaniyarka me yasa zaka rakatan?,me yasa baka zo ka sameni ba tukunna" kanshi ya shafa,yadda yaga hajiya qaraman ta miqe cikin gaggawa yasan komai zai dai daita,mayafinta taja kuwa ta fice,shi kuma ya koma ya zauna cikin kujerun dake dakin yana sauraron dawowarta.


      Kusa awa guda hajiya qaraman ta sake dawowa,da alama ansha fama ansha gwagwarmaya,saidai yanayin fuskarta kawai ya tabbatar masa komai ya dai daita


"Kaje yaya yanason ganinka" tsam ya miqe yabi bayanta har zuwa sashen daddyn.


      Kallo daya yayi musu dariya taso kubce masa,fuskar daddyn wasai ,saidai momma da har yanzu a cunkushe take,fuskarta na nuna fushi,amma kuma idan kayi mata kallon tsanaki zakasan cewa fushi ne akeyi irin na masoya.


       Gaban daddyn ya qarasa ya duqa

"Gani daddy" gyara zamansa yayi sosai yana kallonsa


"Samir....inason in sake neman afuwarku ne gaba daya kan dukkan wani abu da ya faru"


"Daddy.....kasa a ranka nidai a wajena.....kamar komai bai faru ba......saidai.....inason dukkaninku kuyimin afuwa,saboda na aikata wani babban kuskure watanni masu yawa da suka shude,kuma na kasa gayawa kowa a cikinku" dif sukayi,kowa yana dubansa,kowa kuma da abinda zucuyarsa take ayyana masa,aka rasa me magana,sai daddy


"Na yadda dakai samir,kome zaka aikata ina da kyakkyawan fatan da zaton bazai zama mai munin da zai cutar da al'umma addini ko mutuncinka ba,kada kaji komai,sanar dani" zama yayi sosai,cikin nutsuwa ya shiga shaida musu dukkan abinda ya faru,tun daga lokacin da ya fara sanin bilal,rayuwar kaltum har zuwa yadda auren ya dauru.


       "Alhamdulillah" hajiya qarama ta furta tare da wata ajiyar zuciya mai qarfi


"Mun godewa Allah da ya sanya iya haka ce ta faru.....hankalina har ya kwanta" to ga momma da daddy ma kusan abinda ya faru kenan,saboda ya sanya kowa a cikin taraddadi,saidai amsar daddy ta sake kwantar masa da hankali


"koda kaltum bata zauna damu ba....koda ita ke da buqatar ta aureka tabbas zamu aura mata kai.....barema tun zuwanta.....babu wanda bai yaba da dabi'u da halayenta ba"


"Banajin a duniya akwai yarinyar da zanso banda kai bayan ita" amsar da ta fito daga bakin momma kenan,sai ya runtse idanu yana tasbihi ga ubangijinsa,lallai duk wanda ya nufaci ubangiji wajen aikata wani aiki.....to babu makawa zai shige masa gaba,zai share masa hawayensa,hakanan duk wanda yaji tsoron Allah xai samar masa mafita......zai kuma azurtashi ta inda baya zato.


🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥


*_DA ZAFINSU_*


*_A TSARE SUKE_*


*_SUN TANADESU_*


*_CIKIN SALO NA HIKIMA DA BAN SHA'AWA_*


*_ƘAWATATTU kuma ZAFAFAN DOCUMENTS HAR GUDA 25 na ZAFAFAN MARUBUTA GUDA BIYAR da aka tanadar muku dasu_*


*_tun daga batch 01 har batch 05,duka bisa farashin rangwame_*


*_MAZA TUNTUBESU TA WADANNAN LAMBOBIN WAYAR KAMAR HAKA_*


_WADANDA SUKESON TURAWA TA ACCOUNT SU YIWA WANNAN NUMBER WAYAR MAGANA_


08184017082


_MASU TURA KATIN WAYA KO VTU KUMA_

09134848107


*_TARON GAMAYYAR ZAFAFAN MARUBUTA.....MASU ZAFAFAN ALQALUMMA_*




62


*10:48*


      Yana tsaye gaba mudubi yana sharce ruwan kansa,yana kuma kallon kansa a madubin,sosai fuskarsa ta wadatu da murmushi,musamman idan ya tuna abubuwan da suka faru a wunin yau din,gaba daya dukkan wata matsala tasa ta warware cikin ikon Allah,abinda ya rage masa a yanzu kawai shine yadda zaiyi da jawahir ya badda mummunan labari a kanta,don ko shari'ar gidan masu tabin hankali a dazu da safe aka qareta,kyauro da sauran mutum uku da suka taimaka masa wajen ajiyar momma na wadan nan shekarun,an yanke musu hukuncin daurin rai da rai.


       Sake murmusawa yayi da ya tuna yadda hajiya qarama ta tubure haiqan da gaskiya aka baro momma sashen daddy,duk da kuwa itama tuburewar da taso yi,saidai rigimar hafsatun tata tafi tata girma.


     A yau komai ya kawo qarshe,ya tabbata kaltum ta zama tasa,wadanda ya kamata su sani sun riga da sun sani,sun karba su lamunce masa,iya wannan kadai idan ya tuna yana sanyashi nishadi.


        Da fari tausayin kaltum ya fara,bai sani ba so ashe yana farawa daga tausayi,ya fara sonta ne ba tare da yasan sonta yake ba,ya aza cewa tausayinta da tausayin rayuwar da suke ciki yake yi,da kuma sabo da sukayi da da uwanta bilal.


     Ja da baya yayi,hakanan yaji a daren nan gangar jikinsa tana buqatar jin duminta,sai ya bude ma'ajiyar kayansa,wadda taci cupboard guda,ya lalubo wasu pyjamas farare qal masu budadden qirji ya sanya,ya feshi jikinsa da lallausan turarensa na bacci,sanna ya zura wasu slippers na fata ya dauki wayarsa ya baro sashen.



        A hankali ya tura qofar dakin nata,babu haske kwata kwata sia qamshin dake tashi,da alama ta jima da kwanciya,don lokacin da ya kunna fitilar wayarshi ya hangeta ne duqunqune cikin bargo,kyakkyawar fuskarta ta haska tarwai cikin milk din duvet din da take ciki,sai ya maida qofar,ya taka har zuwa bakin gadon.


        Da qaramin haske yayi amfani ya kalli fuskarta son ranshi,murmushi kwance saman fuskar tasa,saboda tunawa da wasu abubuwa daya dinga yi a kanta,wamcan lokacin da ya fara ganinta,cikin qauyensu,a yanzun sai yake ganin kamar ba ita ba,komai dake tattare da ita ya canza.


       Jan bargon yayi a hankali ya sauko zuwa saman cikinta,ta sake bayyana sosai cikin kayan baccin da suka kwantawa fatarta,sai ya kasa daurewa,ya raba ta bayanta ya kwanta a jikinta tare da sake jawota cikin jikinsa sosai yana sauke numfashi,abinda ya farkar da ita kenan a tsorace


"Shshshsh..... mijinki ne, keep calm sai tayi shuru tana sauraren bugun zuciyarss dake fita da sauri da sauri.


        A hankali ya zura hannunsa saman fatar cikinta ta qasan rigarta,ya fara yawo dashi,abinda yaso tafiya da numfashinta kenan,ya kuma qara bugun zuciyarta,saita riqe hannun nasa jin yana son zarcewa zuwa sama,bayan ta tabbatar babu bra a jikinta,da ya gota din kuwa tasan koma meye zayaji shi.


       Cikin kasala ya girgiza kansa


"No....dan kadan please....nima na dana,karki hanani,nafa yi qoqari,ba wani abu bane me yawa.... please" ga tsoro ga kunya,saidai cikij wani salo dake nuna qwarewa a iya tafiyar da tattausar soyayya mai narkar da xukata,ya dinga karantar da ita wasu darussa masu wuyar mantawa,ya kaita duniyoyi da babu komai cikinsu face zallar farinciki da masoya ke tsinta a cikinsa,sunyi musayar kalamai,yadda ya fallasa a sirin zuciyarsa a gareta,hakanan bai qyaleta ba itama sai da ta fidda masa dukkan wani sirri dake ranta,ya jita a jiki da zuciyarsa sosai a ranar,da quar ya iya qyaleta bau zarme ba zuwa next level ba,saidai kuma ya qare da ciwon mara sosai,wanda bai sakeshi ba sai gab da asuba.


      Tunda ya fito daga wanka yake son su hada ido amma taqi,sbaoda wani nauyinsa da ya dora mata,ya kaita makarantar da bata taba leqawa ba,saidai ta samu tarin karatu da ilimi,ya kuma sake loda mata soyayyarsa ninkin baninkin.


      Allah Allah take kawai ya fice daga dakin,kada wani cikin jama'ar gidan ya ganshi ya gane a nan ya kwana,amma sai ta lura shi kam ko a jikinsa,sabgarsa yake hankalinsa kwance


"Ki daura alwala muyi sallah" ya fada yana shimfida abun salla tare da cije dariyarsa,saboda yana son yaga qarshen pretending dinta.


      Baki tadan turo gaba,ta tsammaci xai fita ne ya barta,saboda maganar Allah tana kunya yaga tayi wanka a gabansa.


       Daga kai yayi yana dubanta,sai tayi maza ra runtse idanunta,ya saki lallausan murmushin nan nasa,sai ya miqe daga sunkuyon da yayi,ya soma takawa zuwa inda take zaune ta nade dukka jikinta da duvet,saboda yadda ya yamutsa gaba daya kayanta.


      Dan zabura tayi sanda ta jishi gab da ita,a dole ta juyo ta fuskanceshi,gashinta daya gama yamutsewa ya rufe fiye da rabin fuskarta


"Don Allah.....zan tashi,amma kaje......momma fa?" Murmushi ya sake,tana qara yi masa kyau,sai yakai hannunsa a hankali yana janye gashin nata zuwa baya,hakan ya baiwa fuskarta damar bayyana sosai,yakai idanunsa kan lips dinta wadanda suka danyi ja,yasan kuma hakan xafa faru,saboda ya tsotsesu son ransa


"Momma ma wajen daddy ta kwana,so kada ki wani damu.....ya kamata ki cire wannan kunyar kwata kwata idan kina tare dani,ni mijinki ne kamar yadda kike matata,halal muke ga juna,amma ban sani ba,ko sai ni da kaina na qarasa cire miki ita gaba daya a wuce wajen ne?" Yayi maganar yana sake matsota,abinda yasa taja baya da sauri,ba shire ta sauka daga gadon sai bandaki.


     Bin bayanta yayi da kallo kamar wani zautacce,sai kuma murmushi ya subuce masa,yasa hannu saman kansa yana shafa sumarsa,idanunsa a lumshe yana tuna daren jiya,yana kuma jin yadda alwalarsa ke karyewa,saiya daura sabuwa kenan.


       Tun bayan futarsa ya barta kwance cikin bargo bacci ya qauracewa idanunta,kamar yadda murmushi yaqi barin fuskarta,ashe haka soyayyar miji da mata take da dadi da kuma gardi?,duk inda ta juya a kaf fadin gadon qamshinsa ke tashi,ta rasa da wanne irin maye turare yake amfani,ya tafi ya bar mata qamshinsa,tasan kuma shine zai hanata sakewa.


      Ajiyan ya dasa abubuwa masu matuqar qarfi cikin zuciyarta,saidai wasu guraren a jikinta radadi suke mata,saboda saqonnin data karba masu zafin gaske daga wajen sarakin,ashe a baya yadda take jinsa a ranta wasa ne farin girki inji hausawa.


       Gyara kwanciyarta ta sakeyi a karo na barkatai,saidai saukar sautin kuka daga can waje ya sanyata tsaiwa cak,kafin ta samu kanta tana dirowa daga gadon ba tare data shirya ba,bata tsaya neman dankwali ko hijabi ba,daga ita sai doguwar rigar atamafar da sarakin ne ya zabo mata ita kafin ya fita tayo waje,saboda muryar jawahir takeji.


        Kafin ta isa har samir hajiya qarama da momma sun rigata isa wajen,sai securities su biyu dake tsaye a can bakin qofa,daga gefe kuma yadikko ce da amiru.


       Momma da hajiya qarama ke riqe jawahir din,wani irin kuka take mai ban tausayi,tana sulalewa qasa suna dagota,jiki da qafafuwan kaltum sukayi sanyi,hawaye ya balle mata,bisa dukkan alamu labari yaje kunnnesu,dama kuma zancan duniya baya buya,duk kuwa yadda kakai ga son boyeshi,sai ta kasa tsaiwa,ta nufi jawahir din da hanzari,tana ganinta itama ta nufota suka rungume juna,suka sake sakin sabon kuka.


       Samir ne ya qaraso wajen a hankali ya rabasu,sannan ya kama hannun kaltum,zai kama na jawahir ya tuna a yanzun haramunne aikata hakan,sa ya yiwa hajiya qarama alama da ido,ta kamo jawahir din suka nufi falon gidan gaba daya,banda securities da sukaci gaba da kula da gidan.


         Sun jima zaune cikin falon wanda yake shuru,bakajin sautin komai sai na kukan jawahir,babu wanda ya hanata kuka kamar yadda babu wanda ya hanata fadar dukkan abinda ke ranta,kalamai ne da suka sanya kowa kuka a wajen sosai,har da daddy da ya fito daga baya


"Ashe ni din ba kowa bace face wulaqantacciya wadda ta fito ta qazamar hanya,ashe bani da wani cikakken asali?,ashe ni da najwa ba mahaifinmu daya ba?,ashe ya saraki bamu hada alaqar komai dashi ba?,me yasa mommy bata tsaya ta haifemu wajen nagartaccen mutum irin daddy ba?,me yasa ta yiwa Allah shishshigi?,bata tsaya mun fito ta tsatson daddy ba?,tayi gaggawa taje ta haifemu daga wani tsatson na daban?,yanzu ace har bushewar zuciyar ya najwa yakai ta cakawa mahaifiyarta wuqa?,wannan wanne irin bala'i ne?" Sosai tausayinta ya cika zuciyar momma,ta matsa kusa da ita ta rungumeta sosai cikin jikinta,tana bata kalamai na ban haquri da yarda da qaddara


"Ni din ki daukeni tamkar mahaifiyarki,daddynku kuma har abada daddynku ne,babu me canza muku wannan" cike da mamaki ta daga ka daga jikin momma din ta dubeta


"Yanzu bayan dukka abinda mummy tayi miki har zaku iya ci gaba da riqeni?" Murmushi momma tayi,tausayin yarinyar na sake ratsata,saboda ta tabbatar nagartacciya ce saboda yadda kowa ke yabonta,tare da kaffa kaffar kada taji al'amarin


"Qwarai kuwa,ke din diyarmu ce halak malak" saita sake fashewa da kuka,wanda daga baya ta sassauta saboda kalaman ban baki data dinga samu daga wajen kowa,kukanta ya koma ajiyar zuciya.


        A sannan samir ya miqa hannunsa ya matsa hannuwan kaltum,tadan dubeshi kadan,qasa qasa yace da ita


"Ya isa....kukan ya isa haka,ki adanashi,kada ki rasa na first night" kamar qasa ta tsage ta shige haka taji.


        Ido suka hada da amiru,sai ya sakar masa wani kallon tsokana,dauke kansa yayi bayan ya maida masa da harara


"Idan kina fitowa irin haka,zuciyata zata iya bugawa" da sauri ta daga kai ta kalleshi,saiya wara mata idanunsa sosai yana gyada kai alamun tabbatar mata


"U have no idea how much I love you.....but the time will reveal,jeki nemo hijabi" abinda ya sanyata miqewa a kunyace zuwa daki,sai ya dubi jawahir


"Auta bita kuje,karki sake kuka,ki dauka kamar komai bai taba faruwa ba" 

"To" ta amsa a matuqar karye


"Promise?" Ya sake cewa da ita,saita gyada kai tana qoqarin maida qwallarta,fuska yadan bata


"No,ki bude baki ki amsa min" murmushi ne ya taho mata mai hade da hawaye,har yanzu da gaske yana nan a matsayin yaya sarakinta,babu abinda ya canza


"Yes yaayaaa" ta amsa masa da yanayin da aca baya take amsa masa,abinda ya taba zukatansu gaba daya


"Good girl" ya fada yana qoqarin boye rauninsa,suka bita da kallo gaba daya sanda take tafiya zuwa dakin kaltum.


      A nutse ya faka motarsa a harabar asibitin,wanda suka dauko jawahir da dukkansu sukayi amannar taje taga mahaifiyarta,shi da kaltum ne zaune a gaban,yayin da amiru da jawahir din suke baya.


        Sai da yakashe motar sannan ya waiwaya yada dubeta


"Duk abinda ta aikata miki mahaifiyarki ce,she need your respect,sannan idan kika shiga kika zauna kina kuka?,ki tabbatar bazan sake barinki zuwa ba, understand?" Kai ta jinjina tana boye qwallarta


"Ok" ya fada,abinda yasa amiru bude side dinshi ya fito,itama jawahir din haka.


       Caraf ya kama hannun kaltum itama dake qoqarin bude nata side ta fita,ya manne tafukan hannuwan nasu waje guda,dumin jikin kowannensu yana ratsa jikin dan uwansa


"Ina zaki madam?"


"Zan raka jawahir" wani narke mata yayi,tamkar dan yaye


"Haba madam.....wannan wata dama ce fa,da mun koma gida shikenan za'a sanya mana ido,don naji hajiya qarama daxun ta fara wasu maganganu....." Qasa yayi da muryarsa


"Please,abun jiya za'a dan sanmu na qara ɗanawa" idanu ta fitar waje gaba daya,amma ganin yadda ya tsareta da nasa idanun masu tsananin kaifi saita sauke nata qasa


"A waje muke fa" tana rufe baki taga motar ta soma duhu,saita daga kai da sauri,ashe danne madagar gilasan motar yayi gaba daya,saidai bai juya ba still ya tsareta da idanuwa ne,gilasan kuma sunayin sama har suka gama rufewa ruffff.


       "Yanzu fa?" Ya jefe mata tambayar yana sake jifanta da wani tsumammen kallo,saidai kafin takai ga bashi amsa ma tuni ya hade tazarar dake tsakaninsu.


        Da zafi zafi yaji ana knocking glass din motar,ya zare jikinsa a galabaice yana duban wanda ke bugun glass din,amiru ne,bai sauke ba sai daya tabbatar ta gyara daurin da kwalinta,ya gyara xaman rigar jikinsa,sannan ya dauki ruwan dake ajjiye kusa dasu ya bude ya kafa kai ya fara kwankwada,zuwa sannan amirun harya qagauta,ya zagayo ta gaban glass din motar yana duban samir,wanda baiyo ko darr ba sai daya gama shan iya yadda zai iya ya miqawa kaltum sauran sannan ya sauke glass din


"Kaima fa dan iska ne da alama inda ka samu waje....ka fito mummy nason ganinka urgently, she's in serious condition,da gaske nake,jawahir ta kasa riqe kukanta,ni kaina na kasa controlling nata please......" Da sauri ya buda murfin motar ya fito,sannan ya zagaya ya budewa kaltum,ya riqeta sosai cikin hannunsa suka fara takawa zuwa cikin asibitin,kome zaiyi zaiyi ne saboda jawahir badon mummy ba,don ko sau daya a rayuwarsa baya buqatar sake ganin fuskarta indan ta shine.


     Duk wanda yaga mummyn yasa a gargara take,banda gursheqen kuka babu abinda jawahir keyi,shigowar samir gaba daya hankalin mommy ya karkata a kansa,saidai duk yadda taso bude baki tayi masa magana abun ya gagara,'yan maganar sun tafi,kalamanta na duniya sun gama qarewa,sai jawahir ta hau girgizata


"Mommy na yafe miki,ga ya sarakin,kice su yafe mikin.....ki fada musu" gaba daya jikinta ne ya saki cikin yan qananun daqiqu,taja wata qatuwar shaquwa me qarfi,abinda ke alamtawa duk wanda ke dakin cikawarta,bayan likitoci sun duddubata suka tabbatar masu da hakan.



      Kuka sosai kaltum itama ta saki,mutuwar bilalunta ta zamar mata sabuwa,mikin dake zuciyarta ya dawo sabo,kama hannun samir yayi ya maidata mota ya zaunar ita da jawahir,ya bar amiru ya kula dasu,ya koma cikin asibitin,ya biya dukka wani bill nata dana sauran jama'ar dake dakin,wanda dama ya saba hakan,kusan dabi'arsa ce,bawai yayi ne kawai don ita kadai ba,yayi ne saboda Allah,yayi ne kuma saboda ranar gobe.


********Cike da farinciki take hada kayanta cikin wani qawataccen akwati,duk da cewa tana qoqarin danne farincikin nata saboda ta yiwa jawahir dake zaune a gefanta kara,wadda a jiya akayi addu'ar bakwai na rasuwar mummy.


      Bayan shafe watanni masu tsaho da yawa,sai gashi a safiyar gobe zata sauka garinsu na dinya,zata yi tozali da ummanta,zataga habiban ta,yakumbo indo kawu ado umma suwaiba sai kuma lantana,wadan nan kusa sune mutanen da take muradin gani kaf fadin qauyen dinya,masoyan da bata da tamkarsu,ji take a goben kamar zata tafi saudiyya ne aikin hajji.


     "Nayi mamakin yadda kika iya jarumta da qarfin hali.....wadda keda miji kamar ya saraki.....amma kika zauna a wancan lokacin 'yammata na miki farautarsa?,bansan baki da wayo bafa sai da nasan cewa yaya saraki mijinki ne" ta tsinci dakusashshiyar muryar jawahir na fada sanda take zuge jakarta.


      sakin aikin tayi,ta juyi fuskarta dauke da fara'a tana kallon jawahir dake zaune saman abun sallah,sanye da hijabi,gefanta alqur'ani ne data gama karantawa,tayi matuqar jinjinawa gami da sarawa dauriyar da jawahir ta nuna,idan ka ganta a yanzu,zaka tsammaci ba itace wadda abubuwan nan suka faru da ita ba,saidai tayi imani da cewa QUR'ANI WARAKA NE kuma ambaton Allah shike sanyawa zukata nutsuwa,tun daga ranar kullum sai kaltum ta yiwa jawahir tofi a ruwa ta bata tasha,daga qarshe sai ya zama ma tofin ne ruwan shanta,bugu da qari da qur'ani take wuni a hannunta,tunda ta samu izifi me yawa a wajen kaltum din,sanda suke musayar karatu da ita,sannan idan xasu kwanta dashi suke kwana cikin wayar jawahir din.


      Gefan jawahir ta dawo ta zauna tana murmushi


"Ban taba kawowa cewa akwai randa zatazo da zaya soni ba,ban taba hada kaina dashi ba,saboda nasan akwai tazara me tarin yawa a tsakaninmu,nafi kowa sanin cewa ceto ne yasa ya aureni bawai soyayya ba,amma a yanzu.....banajin akwai wadda zan iya barwa shi" murmushi jawahir ta saki


"Koni bazan bari ki barwa kowacce mace shi ba,saboda ke kikafi cancanta....." Tsagaitawa kadan jawahir din tayi


"Inaji a raina inama ace nice ke?,inama ace cikin tsanani irin naki na taso?,a yanzu rayuwa tayimin kyau kamar haka?" Qwalla ta cika idanunta sanda takai qarshen maganar.


     A tausashe kaltum ta dafa kafadarta

"Ki godewa Allah da yayoki musulma,cikin al'ummar annabi muhammad.....ya kuma barki da imaninki.....sannan ya hadaki da mutane irinsu daddyn,da Allah yaso sai ya halicceki akuya ko tunkiya ko kuma zaki,ko ya halicceki kafura,kinga ko iya wannan ni'imace,duk wani yanayi da dan adam yake ciki mai gushewa ne watarana,a shekarun baya sanda nake cikin tsanani nida mahaifiyata da dan uwana,ban taba kawo cewa watarana komai zai wuce ba,to kamar hakane....kema wataran zakiga kamar komai bai faru ba"


"In sha Allah" ta amsa tana dauke qwallarta,sannan ta miqe ta ciro wata jakarta,ta dawo ta zazzageta,kudadene suka fado masu yawa,kusan dukka sababbi ne,saita tura gaban kaltum


"Kudaden break dinki ne da yaya saraki yake bani na baki,tun sanda kika fara zuwa makaranta wadanda baki taba amsa ba,dama ya gayamin gasunan na baki,amma bai sani ba.....ba lallai bane ki amsa,saboda bakison sababbin kudi bakya amsarsu....." Ta qarashe maganar qaramar dariya na kubce mata,tayata kaltum din tayi sannan tace


"Bari na baki labarin abinda ya sanya yake tsokanata har yau" tiryan tiryan ta gaya mata,abun da ya sanya jawahir din dariya sosai,ganin labarin ya sanyata nishadi,sai taci gaba da bata wasu labarai na wautarta sanda take a matsayin kattume,har zuwa sanda wayar jawahir tayi qara ta daga tayi magana ta sakanni sannan ta sauke


"Kije ya samir yana kiranki" miqewa tayi tana laluben hijabinta


"Bari naje na dawo na qarasa baki labaran" harara jawahir ta jefa mata


"A haka ake zuwa turakar mijin?" Saita miqe tana qwace mayafin,ta kama hannunta zuwa gaban madubi,duk da jikinta tashin qamshi yake,don bata jima da fitowa a wanka ba,amma sai da jawahir ta sakeyi mata wankan turare tun daga gashinta har qafafunta


"Duk inda zai shanshana yaji qamshi.....kuma karki dawo min,kawai kice min sai da safe" ta fada tana jefa mata wani farin mayafi mara kauri instead of hijabin data saka dazu.


      Sakato tayi tana duban jawahir sanda take komawa saman abun sallarta tana zama


"Amma qamshin nan yayi yawa,zan keta ta falo ne fa,yanzu idan na hadu da daddy ko momma fa nace meye?"


"Haram ne?,wurin mijinki zaki fa,lada zaki samo...."kafin takai qarshe wayarta ta sake tsuwwa


"Ki rufan asiri ki tafi,Allah shine yake sake kira" dariya ma jawahir din ta bata,yadda ta hade hannayenta waje daya tana roqarta,saita yi gaba a hankali ta fice,tausayin jawahir din na sake cikata,ta samu zuciyarta da yi.mata addu'ar samun miji nan kusa da zai zame mata sanyin idaniya itama.


🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥


*_DA ZAFINSU_*


*_A TSARE SUKE_*


*_SUN TANADESU_*


*_CIKIN SALO NA HIKIMA DA BAN SHA'AWA_*


*_ƘAWATATTU kuma ZAFAFAN DOCUMENTS HAR GUDA 25 na ZAFAFAN MARUBUTA GUDA BIYAR da aka tanadar muku dasu_*


*_tun daga batch 01 har batch 05,duka bisa farashin rangwame_*


*_MAZA TUNTUBESU TA WADANNAN LAMBOBIN WAYAR KAMAR HAKA_*


_WADANDA SUKESON TURAWA TA ACCOUNT SU YIWA WANNAN NUMBER WAYAR MAGANA_


08184017082


_MASU TURA KATIN WAYA KO VTU KUMA_

09134848107


*_TARON GAMAYYAR ZAFAFAN MARUBUTA.....MASU ZAFAFAN ALQALUMMA_*


Post a Comment

0 Comments