TOP HAUSA NOVELS atOptions = { 'key' : '20e08520dad54dbf6d9e963271

'Yar Tsakar Gida 1-2 page 45-50

 Da ta rufe Ƙirjin ta tana bin sa da Kallo tamkar taga Abun tsoro . Janye hannun nata yayi yana kafe breast ɗin ta da kallo . Noory Meye haka ? Wannan fa Ƙwartonci ne ?. Kallon ta yayi yana duban idanun ta yanda suka fara kawo Ruwa , cike da basarwa hade da Ɗan dawowa hayyacin sa yace “ Don Noory ya gyara miki Towel laifi ne Amrah ? Ai ba ƙwarton ci bane , Kawai dai gyara Miki shi zanyi naga baki daura dai dai ba . Kallon sa tayi kaman Wata mai wayo tana cewa “ Ohho na gane yanzu to ya zan yi ya sauka . Ɗan murmushi yayi yana kai hannun sa tare da warware Towel ɗin daga jikin ta , Saurin kallon sa tayi nan taga shima idanun sa na akan fuskar ta . Nauyin haɗa ido dashi taji a wannan sa'ilin ta rasa Fahimtar inda Manufar sa yake . Wannan yasa ta Yin ƙasa da idanun ta tana zuba ma Sarautar ALLAH ido . Sai da ya raba towel ɗin da jikin ta sannan ya fara Ɗaura mata da kan shi , gaba ɗaya jikin sa yayi sanyi baya da wani kuzari, Ji yake tamkar ya rungume ta a haka su kasance har Abada . Amrah na gama Miki Kinga yanzu sauka ko.? Kallon shi tayi kana ta kalli Jikin ta inda ya daura mata towel ɗin . Ya sauka ba kaman nata ba . Yauwa Noory ya sauka ,amma dai har yanzu ƙarami ne.  Ta ƙare maganan tana kallon sa tana kuma cigaba da cewa “ Noory kaine lokacin nan fa kace babu kyau cire kaya a gaban mutane ,amma me yasa yanzu kuma ka cire mun towel a gaban ka .? . Kallon ta yayi yana kai hannun sa tare da Sosa ƙyar sa yana shafa Sumar kan sa don ya rasa me zaice mata.  Noory baka ce komai ba . Ta kuma katse shi har da riƙo hannun sa .  Amaimakon taga ya bata Amsa sai gani tayi ya kai bakin sa yana ɗan rage tsawon sa tare da kissing din saman Goshin ta . I luv You Amrah . Ya furta yana mata  Sanyayyar kissing 😘 . Muje ki saka Sleeping drees sai muyi dinner . Ohk Noory muje . Ta furta tana kallon sa . Murmushi Nurayn yayi yana riƙe Hannun ta tare da nufar Inda kayan ta yake . Buɗe Waldrop ɗin yayi yana fara fiddo mata da Wasu irin tsadaddun kayan barci masu kyaun gaske . Wanne zaki saka a ciki .? Hannun ta takai tana Ɗaukar daya daga ciki mai laushi mai jikin mage , kalon Milk da Red.  Noory Wannan sunyi kyau sosai , Amma ya akayi ka saya wannan yaushe kasaye su. ? 


Tun ranan dana ga Amrah nasa akayi mun ordern su , saboda nasan zaki so su sosai . Thank you ta furta tana buɗe Kayan , Riga ce da Wando . Wandon dogo sai rigar iya Ƙugu.  Ba tare da ta ji komai ba ta saka su a gaban sa.  Dan shiru yayi yana ƙare mata kallo don sai a sannan ya tuna babu braziya kwata² bai sa an kawo masa ba . Hannun ta ya kama yana nufar inda mirror yake don ya kimtsa ta . Yanda yake yi mata tamkar yarinyar goye.  Matsawa yayi da wani kujera na gaban madubin yana mata Alamun ta zauna , babu musu ta zauna tana kallon kanta a madubin Fuskar ta na fidda Annuri . Noory baka ce nayi kyau fa .? Tayi maganan tana kallon kan ta ta madubin Fara'ar fuskar ta ya gagara ɓoyuwa. Kin wuce ƙyau ai . Yayi maganan yana murmushi . Ɗan cuno baki tayi tana furta “ Ban fahimta ba ?. Ohk . Ya furta yana ɗaukar hand dryer tare da fara tsane mata Ruwan kan ta.  Kallon sa take tayi masa ƙurrr ta jikin madubin yanda yake busar da gashin nan nata  tare da bin sa da Mayika masu ƙamshi da daɗi . Hannun sa yasa yana tattare Gashin nata da Red ribom . Sosai tayi kyau na karshe ita kan ta kallon kanta take tamkar ba ita Bace Amratun da ta sani . Kafesa tayi da ido ta jikin madubin Yayin da Wasu irin hawaye suka fara sauko mata , sam bata shirya zuwan su ba ,amma sun gagara ƙin sauka mata . Amrah na .! Kukan mene kike yi ? Da zafi ne .? Nurayn yayi maganan lokaci guda cike da kulawa yana kallon fuskar ta . Miƙewa tayi daga zaunen da take tana juyowa tare da saurin Rungume sa tana shigewa jikin sa sosai tare da cigaba da rera kukan ta a hankali . Lumshe idanun sa yayi yana shafa bayan ta tare da rarrashin ta da hannun sa .  Noory Mama na na tuna da ita . Ta furta maganan tana cigaba da rera masa Sabon kuka . Humm Sauke Numfashi yayi a hankali kana ya Matsar da jikin sa da nata . Hannayen sa biyu ya saka yana tallabo Kuncin ta tare da kafe ta da Sexxy eyes ɗin sa. Sorry It's Ohk ...Ya isa haka ki daina kuka kinji, Baga Nooryn ki ba ? , Zai zauna dake har Abada . Saurin Ware manyan idanun ta tayi tana kallon sa , Hawayen na sauka mata a hankali tana motsa bakin ta tare da cewa “ You promise.? Gyaɗa mata Kai yayi yana Lumshe idanun sa tare da cewa “ Yes i promise Amrah . Sakin masa murmushi tayi sosai tana kara riƙe hannun sa . Ina son ka sosai Noory na . Daga Aunty Ikilima sai kai nake so sai Baba Adamu , shima yana Sosai Noory . Girgiza Kai yayi yana jin wani irin tausayin ta tare da narkakkiyar soyayyar ta dake tsuma zuciyar sa . Hannun sa yakai yana Matsar lotion tare da fara shafa hannun ta zuwa fuskar ta dashi . A haka har ƙafa ya sunkuya yana shafa mata . Kallon sa Amrah tayi tana cewa “ Noory Kace zaka Zauna dani har  Abada .? Eh mana Amrah . Ya furta maganan ba tare da ya kalli fuskar ta ba , yana bin ƙafarta da lotion🧴ɗin . Noory Zaid da gaske yake zai Aure Ni .? Wani irin ɗauke Nurayn yayi kansa yaji ya sara masa da Ƙarfi . Wani irin zuciya ne ya harniƙo sa . Ji yake yana sauke wani irin numfashi da sauri da sauri na tsaban kishin sunan Zaid da ta Ambata . Wani Abu ya danne kamin ya ce “ Me yasa kika tambaya ni .? 


Uhmm kace zamu rayu tare , Amma idan Zaid ya Aure Ni ai gidan sa zan koma kasani , Sannan kuma kai Naana ce zaka Aura bani ba . Aje ƙafarta yayi yana miƙewe kana yace “ Idan nace zan rayu dake har Abada , ina nufin zan kasance miji ne a gare ki . Tun daga yau zamu fara rayuwa har zuwa numfashi na na ƙarshe babu Rabuwa . Kallon sa take yi bakin ta ɗauke da tambayoyi hakan yasa ka shi cewa “ Ni mijin ki ne Amrah ba Kaman yanda Ɗauke Ni a baya ba , yanzu ke matata ce . Saurin miƙewa Amrah tayi daga Zaunen da take bakin ta na Rawa cikin Muryar kuka ta furta “ Noory Daddy ,Daddy ...saurin daura yatsar sa yayi bisa laɓɓan ta kana yace “ And so what .? Daddy shine zai zauna mun dake ? Nine mijin ki , Ni kuma nake Son ki ba Daddy  Ni mijin ki ne Amrah . Hawayen idanun ta ne suka ƙara gudu . Muryar ta na rawa ta fara cewa “aa Noory , Naana Daddy mommy zamu saka su a tension, zasu shiga cikin wani hali , ga kuma Zaid ya shirya rayuwar Aure dani shine ya faɗa mun haka. ? Wani irin Tsawa Taji Nurayn ya daka mata wanda sai da Wurin ya amsa . Idan kika ƙara mun maganan Zaid .......wani dauke wuta yayi jijiya na masifa na ratsa saman Wuyar sa. Kasa ƙare maganan yayi yana juyawa tare da kaiwa da komowa . Ƙyaam Amrah tayi ta kasa motsa ko dan yatsa saboda Tsoro . Oya go . Tafi kije ki Auri Zaid Ɗin , ki barni Ni bakya so na ko ? Humm ya sauke wani irin zazzafan numfashi kana ya cigaba da cewa “ Tafi Amrah fita ki tafi kije kiyi Rayuwa da Zaid , nasan kina Son shi ba , Ni kuma bakya buƙata na , dashi kike son kiyi Rayuwa bani ba ? , Eh Amrah , zan iya rayuwa Ni kaɗai koda babu wata a rayuwa ta , zan rayu a haka har Mutuwa na ya riskeni . Dama na iya Rayuwar rashin ki na tsawon shekaru fiye da Goma duk da na shiga Wani hali mai wuyar Misaltuwa , so I can stay alive even without yhu . Just Go.....! Kasa motsi Amrah tayi tsoron sa take ji tunda take bata taɓa ganin sa a irin wannan yanayi ba .  A hankali ta silale a ƙasan tiles ɗin tana fashewa da Kuka mai tsuma zuciya da ban tausayi . Noory na kai nake so , Daddy nake Tsoro ....ta furta Maganan kuka na cin ƙarfin ta .  Dafe kan sa yayi yana jin yanda yayi masa Nauyi sosai . Rintse idanun sa yayi yana jin Babu Dadi yanda idanun sa suka rufe amma a haka soyayyar Ta azazzalan Zuciyar sa take . Amrah komai ina yi Miki ne saboda ina Son ki , a da baya idan na rasa ki na jura hakan saboda zuciya tana da yakinin ganin ki a wata rana . Amma kuma a yanzu ba na jin zan iya dannar zuciya ta akan na hakura na rasa ki a karo na biyu . Idan ba Zaid ke to ki sani na bashi ke ne ba har Abada . Mun rabu kenan , ba zan iya jura ba ,dake nake so nayi rayuwa . Bayan ke kuma babu kowa . I Change all my self my life because of you Amrah , ba haka nake ba . Tun ranan da na dawo Nigeria nake jina I'm  completely different daga rayuwa ta na America dana yanzu . Sai na fahimce kece gyaruwa ta i lab you always Amrah . 


Yana maganan ne tamkar mai gushewar hankali sam baya Fahimtar ma abun da yake faɗi . Tausayin kan su ne ya kamata. Cikin Sauri ta miƙe tana nufar inda yake . Hannunta ta Ware tare da Rungume sa tana cigaba da rera kukan ta a hankali . Ina son ka sosai Noory na ” . Wani irin ajiyar zuciya ya sauke yana ƙara Hugging din ta sosai . Kin kyau Amrah , Amma kin san menene.? Taji Muryar sa ya katse ta tamkar babu Abin da ya faru tsakanin su yanzu . Ɗago da Lulun idanun ta tayi tana kallon sa kana ta Girgiza masa kai . Motsa laɓban sa yayi Hushiryar sa na bayyana kana yace “ Idan kika yi Dariya sai kin fi haka kyau . Dariyar tayi wanda bata shirya ba hakan yasa shima sakin Murmushi yana cewa " Ko kefa . Muje muyi dinner dare yayi sosai yanzu fa Ƙarfe 8:45pm . A tare suka fice daga Bedroom din suna nufar Dinning room . 

**

9:30pm.

Juyowa Mom Sa'adah tayi tana kallon Daddy da Nusaiba wacce take gyefe ta rafka tagumi, cikin Muryar damuwa Mommy ta furta “ Ina tsoro , wallahi na fara tsorata zuciya ta tana mun hasashen Wani Abu na daban . Nurayn har yanzu fa bai dawo Gida ba . Shi ƙaramin yaro ne da zaki damu don bai dawo Gida ba . ? Idan yayi fushi ne akan Wancen Yar talakawan to ya haɗiye ran sa ya mutu ba zan Aura masa ita ba , Sannan kuma duk inda yake kiyi gaggawar neman sa don ki sanar masa nan da kwana ki biyar ya rage Auren sa da Naana Fiddausi . Duk inda yake ya dawo kamin ransa ya ɓaci . Daddy ya katse Mommy cike da banbami don Sam baiyi tunanin Nurayn zai iya yanke wani hukunci akan Abun da suka gindaya masa ba . Juyawa yayi yana nufar Under ground ɗin sa , yayin da Nusaiba ta kalli Mommy tana cewa “ Mommy wai Meye Ya Nurayn zai yi da Wancen Yar matsiyatan .? Haba Wallahi Abin kunyar sa ce ma ace ya Auri wannan yarinyar ai sai Abokanan sa suyi masa Dariya , ki kalla fa Nana deegre holder ce , Amma a hakan .....Saurin Ɗaga mata Hannu Mommy tayi tana juyawa tare da wuce ta tana nufar Bedroom.......!

Wani irin takaici ne da baƙin ciki ya rufe Nusaiba kama kan ta tayi tana fashewa da Wani irin kuka na takaici da baƙin ciki , babu fuskar wacce take Hangowa a halin yanzu fache na Amrah.  I hate yhu ...na tsane ki na tsani ganin Wannan Jakar dabban yar talakar a rayuwar mu . Kin hana Rayuwa ta dana Ya Nurayn sukuni ,tun da kika shigo cikin rayuwar mu kika sauya mana shi . Na tsaneki a rayuwar mu ke Guba ce . Bayan Nurayn yanzu har Zuciyar Mummy ta siye , Wallahi Mommy son Yarinyar nan take , ko ta faɗi ko bata faɗi i understand that . Ni na fahimci Hakan . Kuma wallahi ba kan ki kika jawo ma masifa har dangin ki sun shiga uku . Miƙewa Nusaiba tayi tana nufar Bedroom ɗin ta cike da Ɓacin Rai . 

Kwance yake a ƙayataccen Gadon nasa haka zalika idanun sa suna rufe tamkar mai barci amma kuma a zahiri ba barcin yake yi ba . Me yasa Nurayn zai yaudare ni .? Me yasa Bai taɓa faɗa mun cewar Amrah itace Wannan Amran tasa da yake bani labari ba .? Tabbas ba zan iya haƙuri ba , dole ya bar mun matata . Rintse idanun sa yayi da ƙarfi yana tuno da abubuwan da suka faru a zauren Gidan canonel Ɓaidu . Wani dafe kan sa yayi yana miƙewa tamkar Wanda aka tsikara . Kasan Waye Ni Nurayn sannan kasan Bana taɓa Son Abu Ban same shi ba . Dole ka bar mun Amrah itace matar da nake fatan Aure indai ina raye babu mijin da Amrah zata Aura bayan Ni Zaid . 
**
Zaunar da ita yayi a bakin gadon nasa yana gyara Rigar barcin sa , fuskar Nurayn ɗauke da murmushi ya kalli Amrah yana cewa “ Na kira Baba yanzu kiji Muryar sa ,sai muyi barci ko .? Ƙirjin Amrah ne ya buga Da ƙarfi wani irin zullumi na shigar ta . Idanun ta ne tayi narai narai dasu tana kallon Nurayn . Noory idan ka kira Baba bazai ce ka dawo dani ba ko .? Lumshe idanun sa yayi kana ya ware su akan fuskar ta yana Girgiza mata kai Alamun a'a. Shiru tayi tana ɗan tunani kamin ta tsinkayi Muryar sa yana cewa “ kina jin barci ne ? , Taho ki ƙwanta ” . A'a ka kira baba na ina son jin Muryar sa . Kafe ta yayi da Wannan sexy eyes ɗin Nashi kana yace “ Ohk ” . Takawa yayi yana nufar side ɗin da Wayoyin sa suke yana kai hannun sa tare da Ɗaukar daya daga cikin wayoyin nasa . Cike da kuzari irin nasa da zafin nama ya fara latsa kiran numbern Baba Adamu . Unfortunately kiran ne ya yanke Dai dai na Mommy na shigowa . Kallon Sunan Mommy yayi yana takawa tare da zama gyefen Amrah . Hannun sa yakai yana Rungumo ta jikin sa yayi yana kwantar da ita bisa kafaɗan sa . Daukar kiran yayi yana furta “ Mummy ” . Wani irin Ajiyar zuciya Mom Sa'adah ta sauke cikin ƙasa da murya ta furta “ Nurayn kana ina ne? Hello Nurayn? ” . Ta ƙara maganan cike da Ɗan daga murya jin yayi mata shiru . Mommy ina lafiya fatan kuma haka ?. Nurayn ina kaje ne ? Daddy yana faɗa sosai sannan kuma kasan Auren ka da Naana Fiddausi saura ƙwana ki biyar ...Ɗagowa Amrah tayi tana kallon Nurayn Wanda shima ita yake kallo , Tana jin maganan da Mom Sa'adah keyi nan take Zuciyar ta ya tsinke Hawaye ne suka fara biyo Kuncin ta . A hankali ta fara tunanin Dole Nurayn zai kuma barin ta a karo na biyu . Lumshe idanun sa yayi yana buɗe su tare da kai hannun sa yana ɗaurawa bisa Kuncin Amrah a hankali yake goge mata hawayen dake gangaro mata , Mommy a yanzu ba zan Auri Naana ba , Cox ina da mata .! What ..? Mummy ta katse shi tana gyara zaman Wayar kunnen nata , Nurayn me kake cewa haka ? Baka fahimce me nake faɗa maka bane .? Cike da Wannan Arrogant Muryar nasa babu tsoro ko jin ɗar bisa Abin da zai kai ya komo ya furta “ Mummy kuyi hakuri bisa Abin da zana faɗa Miki , but I'm serious ni a yanzu inda Mata , kuma ba kowa Bace Fache Amrah ta da kika sani . An daura mun Aure da ita  tsawon kwana ki uku baya , Sannan a yanzu ina tare da matata . Ku dakatar da Wannan Auren don ko an daura shi to daga lokacin da yazo kunne na zan yi mata saki uku . Cox bana ra'ayi . 

Nurayn ..Nurayn mune fa iyayen ka . Mummy ta furta kalmar cike da rashin sanin me ma zata faɗa masa ,sosai ta gama rudewa bisa jin wannan maganan tasa . Jin al'amarin take tamkar wasa ko a mafarki . Mummy  love good night . Nurayn yayi maganan yana Datse kiran yayin da mummy ta tsaya sai tana furta “ Nurayn Hello Nurayn. 

Juyawa Nurayn yayi yana kallon Amrah Wacce ta miƙe tana nufar Mirror side ɗin shi . Kallon Wani babban elargement take yi mai dauke da hoton wata ƙosasshiyar Hajiya Tayi shiga irin ta larabawa . Fuskar ta bayyane da Annuri . Sunan idanun Amrah a bisa Hoton yake amma sam Hankalin ta da tunanin ta ba anan yake ba . Kuka sosai take yi har da cira . Amrah  .! Muryar Nurayn ya katse ta wanda ya tako Izuwa gare ta . A hankali ta Juyo tana kallon sa kana tace “ Noory Ka maida Ni Gida ” . Kallon ta yayi kana cike da Miskilanci kaman maganan bai doke sa ba ya juya yana kallon Hoton Ammie Hafsat.  Kin ga Ammie ce Wannan Ina Son ta sosai tamkar yanda nake son Mummy Babu banbanci . Tun ina ƙaramin yaro ita ce support ɗina , ko nayi laifi bata cewa nayi sai dai tace “ You Are right my Son.  A yanzu ma itace kadai ta nuna mun goyon baya akan Auren mu . Yaushe ka Aure Ni Noory ?.  Ɗan murmushi Nurayn yayi kana ya kalli idanun Amrah cike da kulawa yace “ Baba ya ɗaura mana aure ,a yanzu zamu kasance tare har Abada ki ƙwantar da hankalin ki kinji Amrah ta .
[8/18, 8:33 PM] Anty Aisha Mmn Teddy Marubuciya: *🛖ƳAR TSAAKAR GIDAA🛖*
Romance love and Sympathetic Story.
Lulun idanun ta ta zuba masa kaman mai tunanin Wani Abu na daban ,kana daga bisani ta ɗan gyada masa kai Alamun to . Kallon idanun ta tayi wanda ta juya tana kallon Hoton Wacce ya kira da Anmie kana tace “ Ita Ammie tana ina ne ? . Hannun sa yana ɗan haɗa ta da jikin sa , ganin hakan yasa Amrah Rungume sa duka idanun su na akan Hoton Ammie Hafsat . Tana Egypt da zama a yanzu. Oh Noory itama tana zaune ne kaman Yanda kukayi zaman America da Daddy da Mummy? . Ba tare da ya kalli Amrah ba yasa hannun sa yana kama laɓɓan ta na ƙasa tare da matsawa yana furta “ Surutu...” . Janye laɓɓan nata tayi tana dariya kana tace “ Sorry noory na daina ” . Ina son ki a hakan , yayi maganan yana kallon fuskar ta kana ya cigaba da cewa “ Ammie Hafsat ita kaɗai take rayuwa a can , bata da miji , Ɗan kumshe idanun sa yayi yana kai hannun sa tare da yamutsa Sumar kan sa yana cewa “  labari ne mai tsayi , bamu da lokacin yin sa a yanzu . Hummmm Amrah ta sauke Ajiyar zuciya kana ta juya tana faɗin “ Noory Good Night ,na tafi Bedroom ɗina sai da Safe . Kasa mata magana yayi domin kuwa jin laɓɓan sa yayi sun masa nauyi Ainun, so yake ya Dakatar da ita amma ya kasa . Har ta kai bakin ƙofa ta juyo tana kallon sa tare da sakin masa murmushi. Hannun sa ya daura a saman laɓɓan sa yana hura mata sumba tare da furta “ Good Night ” . Juyawa tayi tana ficewa cike da jin Dadi ta nufi Izuwa Bedroom din ta . 

Tun da Amrah ta shiga Bedroom ɗin nata ta kasa zama , bin ko ina take da kallo . Noory na miji na , ta furta a sarari cike da ganin Abin tamkar a mafarki. Wasu irin hawaye ne ke bin Ƙwarmin idanun ta . Lumshe Idanu tayi tana tuno da Furucin Daddyn Nurayn akan Ƙiyayyar sa ga Talaka irin ta . Wasu irin marayun hawaye ne suka fara bin Kuncin ta , tausayin kan su take ji , A hankali ta furta “ Noory ya zaɓi yayi Rayuwa dani fiye da iyayen sa ? Anya ban zalunce shi ba ? , A kullum sai nayi kewa da jin soyayyar Umma ta , Amma shi ba zai yi na iyayen sa ba kuwa ?.. Dafe Kuncin ta tayi a hankali tana takawa tare da nufar Resting room ɗin Wurin tana tallabo Kuncin ta tare da cigaba da tsiyayar  Hawaye . 
**
Ƙasa motsi Nurayn yayi tun da Amrah ta fita , Kusan mintuna Uku yayi yana tsaye ,kana ya juya yana nufar ƙayataccen Gadon sa . Ƙwanciya yayi idanun sa na kallon sama , sam ya gagara Lumshe su don baya jin barci zai iya ɗaukar sa a wannan lokacin ba tare da Amrah a gyefen sa ba . Kusan mintuna Goma sha yana kwance sam ƙwaƙwalwar sa ta gagara fidda masa da mafita , saurin miƙewa yayi yana maida Room silipers ɗin sa tare da ficewa daga Bedroom din . Bedroom ɗin Amrah ya nufa inda tana zaune tana sharɓan kuka har da shashaƙa taji shigowan sa . Wani saurin juyowa tayi tana miƙewa tare da kallon sa , inda shima ya tsaya cak yana kallon ta . Bakin sa na son tambayar ba'asin kukan nata ,amma kuma miskilancin sa na dannar sa . Ɗan jan numfashi Amrah tayi tare da komawa tana zama a kujeran tana tallabo Kuncin ta . A hankali ya ɗaga ƙafarsa yana kusantar inda take yana zama a gyefen ta . Ɗan kallon sa Amrah tayi da gyefen ido ,sosai ta fahimci yana son tambayar ta me yasa take kukan ,amma ya gagara hakan ,wannan yasa ta juyowa tana fuskantar shi , hannun sa ta riƙo guda ɗaya tana cewa “ Noory ina Son ka Sosai ” . Sexy eyes din sa ya zuba mata wani irin tausayin ta yake ji na Ratsa ko wani bargo da jini da tsoka na jikin sa . Ina son ki fiye da yanda kike so na Amrah . Kin yarda ? Ya furta kalmar yana ɗan sakin mata Murmushi tare da kai dayan hannun sa yana goge Hawayen fuskar nata . Na yarda Noory ,na yarda da kai fiye da yanda na yarda da Kaina . Haka ina son ka fiye da kaina . Amma ina jin tsoro sai nake ji kaman zaka kara tafiya ka barnnnnnniiii kuka ne ya ƙwace mata da sauri ta shige jikin sa tana Rungume shi ƙaaam tare da cigaba da rera sabon kukan ta . Wasu irin zafafan Ƙwallah ne suka ciko idanun sa . Yasan Sabon raɗaɗin tafiyar da yayi a baya ne yake dawo mata . Cike da mazantaka irin nasa ya danne yana maida ƙwallahn idanun sa , don kuwa a yanzu ya fita jin raɗaɗin da kuma jin zafi a zuciyar sa . Hannun sa yasa yana shafa bayan ta a hankali tare da kai bakin sa dai dai kunnen ta yana hura mata iska mai daɗi , wani irin Ajiyar zuciya take ja a hankali tana tsagaitawa da kukan nata , har a lokacin bata ɗago daga Kirjin sa ba tana nan kwance lamo . Cigaba yayi da Rarrashin ta da hannun sa har Barci ya fara Ɗaukar ta don wani irin ɗumin jikin sa take ji tamkar tana kwance jikin Mahaifiyar ta . Fiye da Mintuna talatin suna a haka har barci ya Ɗauke ta kana Nurayn ya ɗan gyara zaman ta yana saka hannayen sa biyu cike da kulawa yana Ɗaukar ta cak tare da nufa da ita Saman Gadon ta .  Dai dai ya ƙwantar da ita ne yaji saukar ruwa duba ga weather din da ake ciki yasa shi jan nata Blanket mai laushi yana rufe ta dashi .  Fuskar ta ya tsaya yana kallo yana ɗan Murmushi kana ya miƙa hannun sa yana rage masu hasken Fitilun zuwa Dumb light . 

Ƙwantawa yayi yana rungume ta ta baya tare da rufe su da bargon , Mutsu² Amrah ta fara yi jin mutum a bayan ta . A hankali ta ware manyan idanun ta cikin sauri tana miƙewa daga Ƙwancen da take tare da yin zaman tijajan. Noory ta furta cike da mamakin ganin sa tare da ita ... Bai tanka ta ba haka idanun sa suna tsaye akan ta . Dan Lumshe idanun ta tayi tana ƙara buɗe su ,kana a zuciyar ta tace “ Me ya kawo sa nan kuma ? Baga Bedroom ɗin sa can ba ? . To amma ya yake mun wannan kallon ? , Na fara Tunanin Noory fa anya ba irin Doctor Zaid bane .? Tunanin me kike yi.? Muryar sa ya katse ta wanda yake nuni da ganin baiyi wani Abu bako ba . Noory zan iya barci Ni kadai ai , ka tafi Bedroom ɗin ka . 

Kauda kan sa yayi Gyefe yana kallon can wani ɓarayi daban . Kallon sa Amrah keyi don mamaki yasa bakin ta yaki rufuwa , wani irin halin Boss taga yana mata , Don alamu ma ya nuna baya da lokacin ɓata Yawun bakin sa akan ta . I beg sleep . Ya furta yana miƙa hannun sa tare da ƙwantar da ita jikin sa yana ƙoƙarin Rungume ta ne tayi Saurin cewa “ A'a Wallahi ba zan kwanta da kai ba . Kika ce Wallahi .? Ya furta kalmar yana daure fuskar sa babu Wasa . Humm Zaki kuwa kwana dani har muyi tarayyar ma'aurata . Noory ban gane ba ?. Uhmm miji da mata ba'a the same bed suke barci ba , so mu ma yanzu a tare zamuyi barci . Kasa masa magana tayi a hankali ta rufe idanun ta tana motsa labɓan ta tare da fara addu'ar yin barci . Wani Murmushin ya saki mai karamin sauti kana yace “ Amrah yau fa ba barci , Ki dakata da Addu'ar barci 😳 , sai munyi romance sannan daga bisani sai kiyi barcin . Jikin Amrah ne ya hau kyarma kar ³ don dai ta fahimci inda yanzu al'amuran suka nufa . Noory Meye haka ? Wasa kake yi .? No ba wasa nake ba Amrah. Bari mu fara . Taji ya katse ta cike da tsantsan ya shahara taji hannun sa a tsakiyar Breast ɗin ta yana Wani shafa su tare da fara murzasu su da duka hannayen sa . Kokarin Miƙewa take yi kawai taji ya Mirgino ta yana haye ta tare da sakin wani irin Nannauyan Ajiyar zuciya . Cikin wani irin Muryar da bata taɓa sanin shi da ita ba cike da Rarrashi da Muryar ficewa a hayyaci Feelings ɗin sa yakai 99%😹 ya furta “ Please Amrah ina son su , ina son naji hannu na a kullum ina taɓa ko ina na jikin ki , You are my Taste my Life my everything . Sau Ɗaya daga yau ba zan sake ba . Idanun Amrah ne suka fito waje Cikin shagwaɓen murya tace “ Noory..... wani irin Abu ne yaji ya tsira nasa nan take ya sauke wani irin huci yana furta “ Ashhhh Amrah please stop it . Amrah kiyi shiru bana son nayi komai dake duka a yau . But idan kina magana zan wuce ko ina . Kiyi shiru just for 30 minutes . 

Lumshe idanun Amrah tayi gaba ɗaya tsoron sa ma take ji . Muryar ta na rawa na son yin kuka ta kuma cewa “ Noory ka daga Ni to . Ba zan yi kukan ba . A hankali ya muskuta yana ɗaga ta amma hannayen sa still suna saman breast ɗin ta yana Wani irin murzar su laushin su yafi komai shiɗar dashi . Fuskan ta taji ya juyo dashi yana fuskantar nata , a hankali ya matsa kusa da ita yana kai bakin sa tare da kama laɓɓan ta yana tsotsa cikin wani irin salo yana lasar laɓɓan ta tamkar wanda ya samu sabon zuma .....!

Post a Comment

0 Comments