TOP HAUSA NOVELS atOptions = { 'key' : '20e08520dad54dbf6d9e963271

DABI'AR ZUCIYA ❤ page: 55 - 56

 55

Dz



      A hankali cikin kasala da mutuwar jiki take takowa zuwa kitchen din gidan,kitchen din data jima rabonta dashi,saiko yau,tun bayan wayar da samir din yayi,ya umarci hajiya qarama ta baro gidanta su tattaro su dawo cikin gidan professor rashid din,bayan nan dinma ya sanya an qara securiy,wanda gaba dayansu babu wanda yasan abinda hakan yake nufi,don babu wanda ya yiwa bayani a cikinsu.


        Baccin daya yanke mata tun cikin dare ne cike a idanuwanta,tun daga sanda tayi mafarkin matar bata sake rintsawa ba,don haka ta yanke shawarar fitowa zuwa kitchen din ta kama wani aikin ko hakan xai debe mata kewa,ya kuma qwarara jikinta.


       Tun daga nesa ta hangi biba tsaye cikin kitchen din tana feraye dankali,sai tayi sallama,biban ta waiwayo fuskarta dauke da fara'a tana amsa mata.


    "Ina kwana" kaltum ta gaidata tana zaro wuqa a ma'ajiyarsu,ta fara tayata firar dankalin,amsa mata tayi kamar kullum cikin sakewa,sai suka fara taba hira sama sama,duka hirar tasu akan ciwon daddy ne da makamantansu,saidai can qasan ran kaltum maganar da takeson yi mata tana tsunkulinta,bata samu damar yi mata ba har sai sanda suka gama gyara komai suka dora kan wuta.


      "Ashe hotonki maman yaya saraki ce a jiki?,kuna da alaqa daman?" A birkice ta dago kanta ta dubi kaltum,razana da firgici suka bayyana baro baro saman fuskar biba,ta soma waige waige da hanzari,ta tabbatar babu kowa sai kawai ta wafci hannun kaltum ta tura qofar baya ta kitchen din ta jata ciki.


     Idanuwa ta tsare kaltum dasu,kafin hawaye ya soma wanke mata fuska,cikin muryar kuka,kans murya can qasa ta fara magana


   "Duk yadda nayi dake karki tona wannan maganar kaltume saida kika tono ta?,shin bakyason lafiyarki ne?,ko bakison ranki dana iyayenki?,to bari na buda miki komai ko hakan xaisa ki janye kika ki kuma yiwa kanki da yan uwanki gata.......tabbas mamar samir ce a jikin hoton,raihana......wadda ni ba kowa bace face 'yar aikinta shekaru masu dama,yar aikin data dauketa kamar 'ya uwa,ta yimin dukkan wani gata,ta bani kulawa da dan uwa zai baiwa dan uwansa,hakan yasa nima na dauketa kamar yar uwata,na kuma riqi samir kamar d'ana.....mutum ce iya mutum,wadda duk yadda za'a kwatanta miki kirkinta ba zaki fahimta ba sai zama ya hadaku da ita.....kwatsam dare daya hajiya jidda ta shigo rayuwar professor rashid.....ta zama matarsa,abinda babu wanda ya taba zato ko tsammanin zai faru,duk da cewa kusan auren cin amana ne jidda tayi da professor amma haka hajiya raihana ta karbi qaddararta....." Dubanta kaltum tayi tana mamakin kalmar auren cin amana,kamar biba zuwaira tasan me take rayawa saita gyada kai


    

     "Eh.....auren cin amana,domin kuwa jidda 'yar aikin hajiya raihana ce" idanuwa kaltum tadan bude kadan alamun mamaki,wannan wanne irin labarine haka a birkice?



      "Karki dauka gama garin me aiki" biba ta fada tana sake matsawa kusa da kaltum muryata a kwance


     "A'ah,irin masu aikin da basu da kowa,suke da matuqar buqatar taimako,ta daukota ta kawota cikin gidanta,ta nuna mata dukkan gata da rufin asiri,ta sanyata taci gaba da karatun jami'a,bayan ta kammala,tasa Daddy ya bata aiki a wani kamfani nasa da alokacin yake gudanar dashi,duk da hankalinsa a sannan ya fara karkata ga siyasa.....amma jidda ta aure mata miji,ta kuma janye hankalinsa gareta ita daya qwallin qwal,munyi imani bata asiri bata kuma aiki dashi,bamusan da wanne siddabaru take amfani ba,amma ta juya tunanin professor gaba daya,bashi da cewa sai tata,kullum kwanan duniya akwai fada ko tashin hankalin da zai saukewa hajiya raihana,tun bata damuwa harta shiga damuwa,kwata kwata ta zama kamar 'yar kallo cikin gidan,qalilanne cikin 'yan uwan professor suka koma suna ta tata,kamar irinsu hajiya qarama,jidda ta janye komai ta kuma janye kowa......,lokaci mai tsaho ana a haka,har zuwa sanda jidda haihu yara mata guda biyu,tazararsu shekara biyu kacal,ba jimawa hajiya raihana ta samu ciki itama,wanda tunda ta sameshi babu zaman lpy,cikin da ta fita dashi kenan,rana daya muka tashi cikin gidan nan da maganar bacewarta,qaura wambai babu ita babu dalilinta,sai samir data bar mana,duba na duniya ba'a samu hajiya raihana ba,a sannan jikina ya bani ba mutuwa tayi ba kamar yadda mutane keta fada,saboda ganin girman cigiyar da akayi amma babu labari ko motsinta.


       Zuciyata ta sake yarda da abinda take raya min ne na cewa ba bata tayi ba,akwai abinda ya faru da ita,saboda wasiqa dana samu saman gadonta,kuma bisa dukkan alamu tana tsaka da rubutata ne abinda ya sameta ya faru da itan,sirrine tsakanina da ita,bazan iya gaya miki ba.....a lokacin jidda ta shigo dakin kawomin samir daketa rigima akan na lallasheshi,taga wasiqar,ta karanta,a gabana ta duqunqune wasiqar ta kuma sakata a toilet tayi fuloshing dinta


      "Dukkan abinda ta rubuta ki daukeshi ki watsar dashi gefe.....bari na gaya miki,yau ba watan raihana uku ba bata nan?,to ki sanya a ranki watanta uku cikin kabarinta.....domin ba zaku sake ji ko ganinta ba,wannan maganar ina gaya miki itane tamkar kana tona sirrinka ga wanda yake kan gargarar mutuwa,kinga ba wanda zaiji saidai ko qasar kabarinsa.......fitar wannan maganar dai da take rasa ranki,hakanan dukkan wanda kika shaidawa shima kin sakashi cikin babban hadari,babbar soyayyar da zaki nunawa dukkan wanda ke tare dake shine,ki kiyaye kunnuwansa daga sauraren wannan batun" maganar data gaya min kenan cikin kakkausar murya da yanayi me ban tsoro.


.


"Na tsorata sosai,don haka a sannan na roqeta kan zan ajjiye aiki,zan koma gida"


"Bismillah,kina iyawa indai kin shirya mutuwa keda duk wanda yake rayuwa tare dake" wannan maganar tasa nayi shuru ina tsuma saboda tsabar tsorata,ta jefeni da wani kallo,sannan ta matso gabana


"Bari na gaya miki wani abu....keda duk wanda yasan qamshi qamshin abinda ya faru bashi ba fita daga gidan nan,aiki kuma yanzu kuka fara har zuwa .lokacin mutuwarku,bance ba zaku dinga zuwa gida ba,amma babu tabbaci har sai abinda na gani" da wannan maganar ta fita ta bani waje......haka na rayu dukka shekarun nan ina kuka a boye na rashin raihana,ina addu'ar Allah ya bayyanata idan tana raye,idan kuma da gasken ta rasu.....to ina mata fatan samun rahamar Allah da dacewarsa,ina kallo take nunawa samir soyayyar da nasan bata gaskiya bace amma bani da abinda zan iya aikatawa.....sai taso sangartashi da lalatashi amma haqarta bai cimma ruwa ba,ban sani ba ko qarfin addu'ar mahaifiyarsa ke bibiyarsa,da kuma alkharin da tayi a rayuwarta ne yayi masa tasiri?......da wannan bata yiwu ba saita canza salo,ta sanya samir yana sabawa dukkan muradi ko buri da abinda mahaifinsa keso,ta wannan hanyar ta kauda dukkan wata jituwa da qauna da yakewa samir din,ya koma kallonsa a matsayin bijirarren da mara biyayya,a fakaice takeson ture samir daga zuciyarsa ta cusa najwa ta qarfi da yaji,taso hadawa da jawahir....amma yarinyar sai Allah ya halicceta daban,kusan ta debo dabi'un samir din,wannan yasa sukafi jituwa qwarai da gaske......abu daya ne yasa naqi shiga wannan yaqin kan rayuwar samir...." Shuru ta danyi,murmushi kuma ya subuce daga fuskarta ta tsakiyar hawayenta


"Duk abinda takeyi tana yine saboda ta raba samir da mahaifinsa.....tana qarfafa samir yayi abinda ya tsarawa ransa kar ya damu da abinda mahaifinsa yakeso......sai Allah ya bashi wata kariya,ya bashi wata zuciya ta alkhairi,wata zuciya ta hangen nesa,zuciya meson taimako......ya zamana dukkan abinda ya dage zaiyi din me kyau ne,tayi hakan don ta nisanta shi da ubansa,sai kuma hakan ya zame masa alkhairi ba tare data farga ba,samir.....bai manta ni ba,bai manta wacece ni a wajen mahaifiyarsa ba,duk sanda zai aiwatar da wani abu yana tambayata shawara koda aboye ne ba'a gaban idanun kowa ba,ina kuma bashi shawara dai dai gwargwado,duk da cewa....a wasu abubuwan hajiya jidda ta riga tayi tasiri a tunaninsa,misali,yabar zancan mahaifiyarsa sam ya daina daukoshi,ya daina yinsa,na rasa ta yadda zan dauko masa wannan tunanin na dawo dashi cikin kwanyarsa,na rasa yadda zan fahimtar dashi cewa hajiya jidda ba masoyiyarsa bace,hajiya jidda maqiyaya ce gashi da rayuwarsa........" tana kaiwa nan wani kuka me nauyi ya taso mata,kukan daya sanyata komawa ta qofar kitchen da sauri.


      Sulalewa kaltum tayi a hankali ta zauna sosai a qasa,yau tana ganin wata rayuwar bayan rayuwar ta data sani,ashe kowacce rayuwa da irin nata qalubalen?,tayi tunanin cewa matuqar kana cikin wadata baka da wani sauran qalubale,ashe karatun ba haka yake ba.


      Amma wacece a gidan masu tabin hankali?,wacece ita?,anya sunsan da zamanta?,meye dangantakarta da raihana maman samir?,mahaifiya?,qanwa ce ko 'yar uwa?,jikinta yana bata tabbas akwai wani abu a qasa,saidai kunnuwanta suna mata amsa kuwwa,tare da tuna mata maganar mummy a ranar da sukaje gidan,jan kunne da gargadi da kakkausar murya


"Ko 'yar cikina ban yarda naxo da ita wajen nan ba,waje ne dake cike da sirri,waje ne kuma me hadari,kisa a ranki baki taba zuwa wajen ba,hakan shi xaisa ba zaki gayawa kowa kinxo din ba kinji kaltume?" Bata dauki komai ba a wannan lokacin,ta dai gyada mata kai a ladabce,ba tare data fahimci ko hasaso komai a kanta ba.


******Tun daga wannan ranar kaltum bata sake samun nutsuwa kan maganar ba,kullum maganar ke yawo cikin kwanyarta,gefe daya kuma hankalinta ya dauku ga mummy,haka kawai ta samu kanta da nazarin mummy,cikin nutsuwa da ankarewa ta dinga fuskantar wasu abubuwa da dacan hankalinta bai kai ba,yanayinta daban kam ciwon daddy a gaban samir da kuma sanda baya nan,yadda take mu'amala da masu aikin gidan daban da yadda take mu'amala da biba,mu'amalarta da qawayenta da sauransu.


     A kwanakin duk sanda ta kalli Samir wani tausayinsa yake lullubeta,gaba daya ya fada yadan rame,saidai hakan bai fiddashi daga nutsuwarsa ba,nutsuwar nan tana nan,amma akwai tarin damuwa saman fuskarsa da ta gaza bayyanuwa,hankalinsa gaba daya ya tattara kan shirye shiryen fitar da daddy waje.


*******Karfe biyu na rana ta gama shirya abincin da zata tafi asibiti dashi,duk da cewa wadanda takeyi dominsu basa samun damar sanya koda loma guda a bakinsu,tanayin komai ne saboda jawahir samir hajiya qarama dama daddyn dake kwance,wanda zuwa yanzu am fitar dashi daga icu,saidai yana wani dakin daban na musamman.


       Tsaf ta shirya cikin atamfa maroon colour,me torches na blue black,da hijab tayi amfani,wanda ya dace da kayan jikinta,ya kuma haskata sosai.


      Fuskarta ta kalla a a mudubi sanda zafa gotashi,kullum kwanan duniya wani sake gogewa take gami da sajewa da al'ummar gidan,a yau sai taga abun har yafi na kwanakin baya,don tunda aka shiga wannan rudanin na ciwon daddyn rabon data tsaya cikin nutsuwarta haka,gefe daya ga tunanunnuka iri daban daban,fatarta sake fresh take tana bada color me masifar tafiya da hankali,a chocolate color din ma tasu skin din ba kowa ke samun irinta ba,saita qara gaba da sauri,saboda tuna inda zata je da tayi,ta kuma tabbatar driver na nan yana jiranta,hajiya qarama ma na can na xuba idon zuwanta,ko yaya taga batazo din ba saita damu,matsalar gabanta ta daddy baisa ta manta da ita ba,tana mamakin yadda take treating dinta kamar diyar cikinta.


   Suna tafe a motar zuciyarta da qwaqwalwarta na nutso a duniyar tunani,tunanin daya zame mata qa'ida,har zuwa sanda zasu gifta ta gaban gidan,ta bishi da kallo kamar yadda ta saba,a wannan ranar......sai taji zuciyarta na tsananin bugawa,kamar xafa fasa qirjinta,ta lumshe ido sanda suka gota gidan tana furta


      "La haula wala quwwata illa billah" saita maida idanun nata ta rufe,har zuwa sanda suka qarasa asibitin.


        Sai data gaida dukkan wanda ya kamata ta gaida,suka hada idanu da wata baquwar fuska,tana zaune dare dare saman kujera tana danna waya,saita zare idanun nata kaltum din tana miqewa,ta isa gaban hajiya wadda suke zaune tare da jawahir ta zauna ta fara fiddo abincin tana zuba mata.


      Sai data kammala zubawar hajiya tace


     "Kinga kaltum,dauki abincin nan ki xagaya ta bayan dakunan can,samir yana can ki miqa masa,na jima rabon da naga ya sanya wani abu a bakinsa,dole yaci abinci ko yaya ne ai" kai ta gyada kana ta miqe tana sake daukan wani plate din abincin


      "I wanna see him...muje na gani" jauhar ta fada tana sauke wayar dake hannunta,bata waiwayo ba hakanan bata tsaya ba,ta fara tafiya zuwa direction din da hajiya qaraman tace takai masan,haka kawai gaba daya yau takejin zuciyarta a rikice,bugun da take ya zarta qa'ida.


       Su biyune xaune kan kujeru gufa ukun dake wajen,tun bayan fitowarsa daga wajen likita suka hadu da amiru a wajen


      "Zuciyata tana gayamin akwai wata a qasa tabbas ba shakka,kuma zargina yafi karkata kan abokan siyasar daddy,kamar sun kutso cikin lamaransa da shirin kau dashi,sannan sun nema hadin kai da taimakon wasu nasa na jikinsa,saidai na rasa gano ko su waye?,amma ba shakka......tabbas bala suspect ne a wajena,duk da cewa bani da gamsassu da qwararan hujjoji.....amma inaji a jikina" ya fada yana kallon amiru da idanuwansa wadanda sukayi laushi,saboda qalubalen daya soma tunkaro rayuwarsu ba tare da shiri ba.


       Kai amiru ya jinjina cikin dogon nazari,mamaki fal zuciyarsa da kuma shakku,bai bar abun a ransa ba ya dubi samir shima


      "Dukka bayananka na gane na kuma gamsu,but samir.....bala fa tsohon drivern daddy ne,kuma amintaccensa,ka manta?" Miqewa samir yayi a hankali,ya sanya hannayensa duka a aljihun wandonsa,yayi taku hudu daga inda suke zaune,kana ya baiwa amiru baya


      "Koya yana iya zama suspect amiru.....idan nace kowa ina nufin harda mommy.....zan sanya idanu akan kowa,zargina kuma zaibi takan kowa" miqewa yayi a hankali,ya taka shima zuwa inda samir din yake,ya tsaya dab da bayansa,sannan ya dora hannunsa saman kafadrsa


       "Zaka samu dukkan wani gudunmawa da kake da buqata daga gareni,zamu fuskanci wannan challenge din tare kamar yadda muka saba,na maka alqawarin rufe sirri,da kuma dafawarka har sai mun cimma gaci" kai samir ke jinjinawa,baikai ga cewa komai ba ya hangi bullowarsu,tana gaba jauhar na bayanta.


      A hankali ya zubawa kaltum din idanu,fuskarta sam babu alamu na fara'a ko walwala,duk da cewa tunda daddy ya gamu da wannan tsautsayin yadda walwala da farinciki ya yiwa familyn qaranci ita dinma haka,abinda ya sake daga daraja da qimarta gami da martabarta cikin idanu da zuciyarsa,hidima take bilhaqqi,zaka rantse mahaifin daya haifeta ne.


A hankali ya maida idanunsa ga jauhar,wadda take tafe tana latse latsen waya,baya ga earphone dake kunnenta,nazarinta itama yayi na wasu sakanni,yanason tantance wane interest ne dashi a kanta?,ya dauke idanunsa a hankali yana juyawa baya,sai suka kusa karo da amiru dake tsaye bayansa,da alama shima sashen da suka taho din yake kalla,hada idanu sukayi,kowa sai ya dauke idonsa,da alama akwai abinda ke zuciyar kowa,saidai kuma ba muhallin magana bane nan din.


       Sallamarta ta mamaye wajen a zazzaqar muryar nan tata,wadda ta cika da sanyi da taushi fiye da lokutan baya,amiru ne ya amsa,samir kuma ya sauke mata idanunsa,bata kalleshi ba har ta gaidashi bayan ta ajjiye kayan abincin a gabansa.


       "Sweet baby......kana ta nan ashe,hajiya tace ga abinci nan kaci.....ayi serving naka?" Jauhar ta fada sanda ta iso kujerar daya koma kai ya zauna,ta dafe bayan kujerar dab da bayansa tana kallonsa.


      Idanunsa ya maida ga kaltum,wadda tuni tayi nisa wajen zuba masa abincin ba tare da taji da bakinsa ba


       "Kadan.....hakama is ok" ya fada a tausashe ganin yadda kaltum din ke loda masa abincin bata ko kalleshi ba,daga isowarsu wajen kawo yanzu ta gane dawa suka taho,jauhar....sunan data riqeshi tsaf a kanta,tun wancan lokacin da jawahir ke yawan bata labarinta,a lokacin da batasan ciwon kanta ba,a lokacin da batajin komai don an ambaceta a gabanta.


     Tura masa gabansa tayi ta miqe


       "Ni ba za'a sanmin ba?,ko yayan naki kawai kika sani?" Amiru ya fada yana dan murmushi sanda ta miqe zata bar wajen,juyowa tayi,tadan saki murmushi,kana ta dawo a hankali shima ta soma zuba mishin.


      "Kaci mana please sweet baby,ko sai na baka da kaina,bakaga yadda ka zama bane?" Kaltum ta tsinci muryar jauhar tana fada a wani mugun shagwabe,kamar zata saki kuka,abinda ya sanya hannunta kakkarwa kenan ba tare data ankara ba,ta ajjiyema amiru abincin ta miqe da hanzari ta soma barin wajen.



Haka kawai taji batason ma komawa wajensu hajiya qarama,saita nufi qofar fita daga asibitin,tana jin zuciyarta a matse,tare da wani irin nauyi,taci gaba da takawa a hankali tana barin harabar asibitin.


      Batasan tayi tafiya me nisa ba sai data ga tana hango asibitin masu rangwamen hankalin,haka nan kawai taji kamar ana mata umarnin tafiya zuwa wajen asibitin,sannu a hankali sai gata a bakin gate din asibitin.


      Idanun masu tsaron qofar a kanta


     "Hajiya ina zaki?" Murmushi tayi qoqarin qirqirowa


       "Akwai wanda nakeson gani cikin ma'aikatan?"


"Wa kenan?" Daya daga cikinsu ya tambayeta,shuru tayi na sakannin da basu wuce uku ba,tana laluben qwaqwalwarta ko zata iya tuna sunan daya daga cikin ma'aikatan da taji mummy ta kira sanda suka shigo


     Idanunta suka sauka kan kyauron dake daure a hannun daya daga cikinau

"Kyauro" tayi caraf ta ambata


      "Shiga,yana ciki" ya fada yana bude mata gidan,ta sanya qafarta a hankali,gabanta yana tsananta faduwa,zuciyarta nason raurawa,amma taci gaba da kutsawa zuwa ciki.


       Kai tsaye taci gaba da sanya kanta,bata tsaya ko ina ba sai office din da aka saukesu wancan karan.


      A hankali ta tura qofar ta shige zuciyarta na bugawa,babu kowa cikin office din,sai take ji a zuciyarta kamar wata dama aka bata,don haka cikin hanzari ta soma laluben qofar da aka bude musu suka shige wancan karon.


        Tana kusantar dakin bugun zuciyarta na qaruwa,duhu ne sosai a wajen,da alama duk dakin dake wajen dakuna ne na wadanda ciwonsu yayo worst,aka kuma fitar da ra da samun lafiyar wasunsu,waje ne tsit mai rashin wadatar haske,kai kace maqabarta ne,tana kutsa kai zuciyarta na gargadarta,amma ta wani sashen kamar ana qara mata qaimi da kuma qwarin gwiwa,da haka har ta isa qofar dakin,saidai a kulle yake da kwado,hakan yasa ta matsa kadan zuwa bakin window din,a bude yake,saidai tsaho daya danyi mata kamar wancan karon,ta waiga kadan,saita hango wani dan katako,ta tabbatar zai qara mata tsaho yadda takeso,don haka ra daukoshi cak,ta ajiyeshi saitin window din,ta taka a hankali tana sanya idanuwanta zuwa cikin dakin.



Daga can take hangenta,xaune a daya daga cikij corners din dake dakin,a takure kamar wadda ke jin sanyi,habarta na saman gwiwoyinta,idanunta kuma alumshe suke,saidai tana hangen yadda take tattaba yatsun hannunta,kamar wadda ke irga tasbihi da su,hakan yasa kaltum din taji kamar ta sauka ta juya,saboda zuciyarta na tunasar da ita inda take,da kuma wajen wadda take tsaye.


       "Salamu alaikum" bakinta ya subuce ta furta da sautin da dukka wanda ke cikin dakin xai iya jin abinda tace

"Subhanallah" taji ta furta tana daga kanta da sauri ta saukesu ga kaltum dake riqe da qarfe window din tana kallonta.


     Idanu ta zubawa kaltum din tana kallonta,karo na farko data ga wata baquwar fuska haka tsaye a gabanta,yayin da kaltum ke kallonta tana karantar tsantsar kamanni da suke sake bayyana kansu a yanzun da suke kallon juna kallo irin na qurilla,yayin da wani gefe na zuciyarta ke cike fal da mamakin ambaton subhanallah din da taji tayi.


      Zuciyarta ta sake raya mata ta aikata wani abu,cikin buguwar qirji ta buda bakinta a hankali


"Samir yana gaisheki" zumbur taga ta miqe kamar wadda wani abu ya tsikara,lamarin da yayi matuqar razana kaltum,har ta dan ja da baya,saboda tana ganin kamar zata rugo da gudu ta cafketa,saidai bata qara wani motsi ba illa zuba mata idanun data sakeyi


"Muhammad samir rashid azare?" Kunnuwanta suka tsinto kalaman da suke fitowa daga bakinta a sanda take ci gaba da tsaiwar.


      Ta riga da tasan cikakken sunan daddy,ta kuma tabbatar cikakken sunan samir kenan,saboda haka saita gyada kanta suna ci gaba da kallon juna.


        Jikinta yayi matuqar sanyi lokacin da taga hawaye yana saukowa daga fuskar matar daya bayan daya,wani busashen murmushi yana son mamaye fuskarta


"Ke wace?" Ta sake jifanta da tambayar da batasan amsar da zata bata ba,saidai kafin ta amsa din taji takun tafiya,abinda ya sanyata waiwaya da hanxari cike da tsoro da fargaba tana duban hanya.




56


    Sake maida kallonta tayi ga qofar dakin bayan ta dauke idanunta daga doguwar hanyar da har yau wanda ke tafiyar baikai ga bayyana zuwa inda take ba,ga mamakinta sai taga qofar na bude,sabanin daxu da ta ganta kamar a rufe,kafin ta kammala tunanin da zatayi taga anja qofar an bude mata,saita sauka da sauri ta sanya kai cikin dakin.


     Hannunta taji an fincika,data duba sai taga matar ce,kafin ta gama tantance komai ta isa da ita bakin dan duqurqushin gadonta ta dage mata,ta gane me take nufi,don haka ta shige,ta sauke xanin gadon da ya sauka ya lullube har qasan gadon,tana iya hangenta ta tsakanin labulen ta koma ta zauna kamar yadda take daxun,wanda da zamanta da qarasowar wanda taji takun nasa duka bai wuce second biyar ba.


     Yana mita ya shigo,kamar wanda yake magana da mutum me hankali

"Lalle sabi'u yana wasa da aikin nan,baisan girman aikin dana bashi ba,baisan kuma wace hajiya jidda ba,banda guntun iskanci ya za'ayi ya barwa mutane daki a bude?,salon ki fita ya jawo mana jidali?,dole nayi masa jan kunne me qarfi,idan bazai iya ba ya ajiye a bawa wani".


      Abinci taga ya ajjiye mata,ya dan tsaya kadan a kanta na wasu daqiqu,ba jimawa wayarsa tayi qara,yayi hanzarin dagawa ya soma amsawa,saiya juya yana ficewa daga dakina da alama wayar da yakeyi ta shagaltar dashi bai rufe dakin ba yadda suka saba ya fice da sauri.


      Kaltum dake qasan gadon gaba daya jikinta ya jiqa da gumi,gaba kura baya sayaki,gata a cikin dakin me lalurar tabin hankali,wanda har sarqa aka tanada cikin dakin,da alama ana sanyata lokaci bayan lokaci idan buqatar hakan ta taso,na biyu ta ratso ta shigo wani shinge da aka jima ana mata gargadi kan furta koda kalma daya a kanshi,yau sai gashi,bama zancan muhallin ba,ta keta duk wani gurbi ta dangana da tsakiyar shingen tsundum


      "Fito,ba zasu dawo ba sai tsakiyar dare ko kuma gobe....." Taji ta furta da muryarta a sarqe kamar daxun bayan ta yaye xanin gadon.


     Mamaki ya sanya kaltum ta xuba mata idanu,ta yaya take magana sak irin ta masu hankali,muryarta ras a kuma nutse?,banda yanayinta babu abinda zai sanyaka kayi tunanin ba lafiyayya bace,kamar tasan tunani da mamakin da takeyi sai ta sake jin muryarta


       "Cikin hayyacina nake,kar kiji tsoron komai,fito....ina jin kece addu'ata dana jima inayi" wadannan kalaman nata su suka bata qwarin gwiwar fitowar kamar yadda ta buqata.


      Zama tayi dandaryar qasa kamar yadda take daxun,saita yiwa kaltum nuni da wajen xama da hannunta,ta qaraso a hankali har yanzu da ragowar fargaba cikin ranta,saidai kuma ta samu qwarin gwiwa,ta zauna tana fuskantar kaltum din,a hankali ta buda baki



     "Duk da bandan wacece ke ba,aiken jidda ce ke ko kuma ubangiji ne ya jeho min ke ki xame min haske kamar yadda na dauki tsayin shekaru ina roqa.......inason insan wacece ke" qas kaltum tayi da kanta,taga abubuwa masu tarin yawa suna kai kawo


"Ni ba kowa bace,face wata mara gata da galihu da samir ya dauko daga qauyensu,ya dawo da ita cikin gidansu,ya bata gata da galihu da kuma dukkanin kulawa"


      "Samir dina?,ya zama mai tausayi da taimako kenan kamar yadda nake roqon ubangijina?" Ta fada muryarta na rawa,da alama zuciyarta fa tsinke,kuka na dab da zuwa mata kowanne lokaci.


      Kai kaltum ta gyada mata tana dubanta


"Amma ya akayi kika sake dawo kanki cikin wannan hatsarin?,bayan na tabbatar zuwanki na farko qaddara tasa jidda zuwa dake?,kuma ina da yaqinin kin samu kyakkyawan jan kunne daga gareta?kinsan wacece ni ne?" Shuru tayi zuciyarta na raunana,batasan amsar da zata bata ba.


       "Zuciyata ce ta kasa nutsuwa,tana ta gayamin na dawo gareki,bayaga tarin mafarkan da suka cika barcina" kai ta gyada tana kallonta,cike da yabawa da jarumtar yarinyar,tunda har tasan jidda,amma ta yadda ta fuskanci kowanne qalubale ta dawo gareta,ba tare da tasan ainihin wacece ita ba.


      "Nice mahaifiyar samir.....samir dana ne" maganar data sanya kaltum ta kusa shidewa bayan ta dago da kanta,tabbas ta jima tana qiyasta haka,ta dade tana jin kamar hakane,ashe hakanne da gaske?.



Dauke idanunsa yayi daga kanta sanda take bacew ganinsa,ya sauke wata boyayyar ajiyar zuciya,idanunsa suka sauka kan amiru,sam baisan ya xuba masa ido yana kallonsa bane sai yanzu,wani qaramin murmushi amirun yayi ya dauke kansa,shima sai ya janye idanunsa,ya maida ga jauhar daketa fama da chart,amma rabin hankalinta na ga samir da takeja da hira,saiya miqe a hankali,a sannan ta daga idanunta daga kan waya tana dubansa


"Bakaci ko spoon daya bafa" kai ya girgiza yana zuba hannayensa cikin aljihun wandonsa,a daqiqun da suka dan shude lokaci kadan yana jin kamar akwai wani dan waje da zai iya koda loma biyar ne,to amma bayan barin kaltum wajen.....sai yaji kamar ta tafi da dukkan wani sauran waje daya rage da zai iya zuba abincin


"Am coming"ya fada yana takawa a nutse yana barin wajen,gaba daya hankalinsa yaji ya dauku xuwa wajen daddy,mintunan da likitocin suka bashi zasu duba daddyn yana da tabbacin kafin qarasawarsa dakin sun cika.



A nutse yake takawa zuwa cikin dakin,bayan likitoci sun kammala aikinsu,sun kuma gama masa dukkanin bayanai kan cewa akwai ci gaba a ciwon nasa,su qara haqurin fitar dashi a basu kwana uku,idan hakan yaci tura saisu daukeshin.


      Duk duniya baya jin akwai wanda yakejin abinda yakeji a qirjinsa,yana jin wata muguwar kewa tare da fargaba tana shigarsa,idan ya rasa daddyn ya tabbata bashi da kowa kenan,tunda har yau baisan duniyar da MAHAIFIYAR DATA GUDU TA BARSHI TAKE BA,abinda ya kasa goguwa cikin idanunsa,yana iya tuna sanda ta fice daga gidan ta gaban idanunsa,yana kuka yana daga mata hannu,amma ko sau daya bata waiwayo ta kalleshi ba.


     Runtse idanunsa yayi,a hankali ya taka zuwa gaban gadon,ya sake janyo kujerarsa da kusan kowanne lokaci take ajjiye a wajen ya zauna gaban daddyn yana ci gaba da kallonsa.


       Ya jima yana karanta addu'o'i yana tofa masa saman kansa,kafin ya sanya hannunsa cikin tafin hannun daddyn ya runtse a nasa,sannan a hankali ya saukar da kansa yana kallon hannuwan nasu dake sarqafe da juna.


     Motsawa kadan yaga sunyi,abinda yasashi sake qura musu idanu ba qaqqautawa,still ya sake ji da ganin sun motsa din,sai kuma ya damqe hannun nasa gaba daya,abinda ya saka samir daga kansa da hanzari kenan zuwa fuskar daddyn.


      Kamar numfashinsa zai dauke saboda farinciki sanda sukayi ido hudu da daddy yana kallonsa,bakinsa ya sarqafe,ya kasa furta kowacce kalma


       "Allah yayi maka albarka" yaji kalmar ta fita daga bakin daddyn,saiya sake qura masa ido yana mamakin furucin daga bakinsa,sake maimaitawa daddyn yayi,bakin samir yana rawa yace


       "Am....een.....ameen daddy,sannu"saiya gyada masa kai


       "Dagani na zauna" ya fada a hankali muryarsa na sarqewa


       "Bari a yiwa likita magana" ya fada da sauri yana miqewa


        "Fara daga nin tukunna,ba abinda zai faru da izinin Allah,akwai maganar da nakeson gaya maka kafin shigowar kowa" cikin hikima ya dagashin ya jinginar dashi,yana fatan basuyi kuskuren aikata hakan ba,saidai yana zama yadan fara haki


        "Daddy....ka bari a kirasun" qaramin murmushi ya saki yana dafa kafadar samir din,cikin hakin ya sake cewa


       "Nayita roqon Allah......ya bani aron......rai da lokacin da zanta ce maka......Allah.....yayi maka albarka.....na....godewa Allah da.... .ya aramin din.....,abu na biyu......banason kace komai akan ciwona.....koda kuwa akwai wani abu da kake zato......ina bala?"


      

          Cikin mamakin kalaman daddyn yace



"Yana dakin da aka kwantar dashi,amma da gobe zasu sallameshi" sai daddyn ya gyada kai,yana son cewa wani abun amma hakin ya qara yawa,abinda ya tilastawa samir din fita da hanzari kenan,saidai wani sashe na zuciyarsa ya cika da farincikin da zai iya cewa tunda yake rayuwa a duniya bai taba jin irinsa ba.



       "Ni din mahaifiya ce ga samir,yaro daya tilo nawa dake raye a duniya....haifaffiyar qasar sudan ce,birnin Khartoum,munyi auren saurayi da budurwa da rashid a lokacin da yake University of Khartoum wato U of K,bayan ya kammala karatunsa muka tattaro muka dawo qasar nan da zama bisa amincewar dangina da kuma yarda da nagartar halaye da dabi'unsa.


       Muna zaune cikin lumana da rufin asiri,da amintattun masu aikina guda biyar,saidai biyu daga cikinsu sunfi shiga raina,kuma minfi shaquwa dasu,zuwaira da kuma harira.


       Muna zaune da kowa lafiya a dangin rashid,saidai bani da 'yar uwa qawa kuma aminiyar da nake jinta a raina kamar hafsat,ta daukeni kamar ciki daya muka fito da ita,kamar yadda nima na dauketa hakan.



       Mun samu zama na fahimtar juna da qauna,har zuwa lokacin da rashid ya shiga siyasa bayan na haifi samir da wasu 'yan watanni,siyasar data dauke hankalinsa matuqa fiye da yadda yake a da,duk da cewa dukkan wani haqqinmu babu abinda ya sauke ko ya fasa bamu,saidai mun rage samun lokacinsa kamar da,saboda harkokinsa na siyasar da kuma kasuwancinsa da Allah ya sawa albarka yaketa habaka.


        Kowacce rana a rayuwar dan adam tafe take da qaddararta,muna cikin wannan xaman namu na aminci,kwatsam jidda ta shigo rayuwarmu,shigar data sauya qaddarata izuwa bigiren da muke kai a yanzu.


       A wata rana bayan mun fito daga asibiti,nakai samir dake fama da zazzabi,nida zuwaira,zuwaira na gaban mota ita da driver ni ina baya muna hira kadan kadan sanda driver zai fito daga cikin asibitin,daga gefe a rakube na hangi wata yarinya,wadda a qalla zan bata shekara uku ko hudu,kuka take sosai tana kakkarwa,har zamu gota tausayinta ya tsargamin saboda irun kukan da take,na saka driver yayi parking,na fita na sameta.


      Ta dan tsorata da farko da ganina,amma daga baya saita saki jiki,na tambayeta ta gayamin labarinta kan cewa,su ba 'yan garin nan bane,bata da kowa a duniya,saida kakarta ta rage mata,ita ke riqonta,to itama kakar tata sai Allah yayi mata rasuwa,sai wata mata dake siyan quli da daddawa wajen matar ta dauki riqonta,ashe matar magajiyar karuwai,data kaita gidanta tayi tayi da ita kan ta shiga harkar neman maza amma taqi,dalilin da yasa ta dinga gana mata azaba kenan,data gaji shine ra gudo.


      Sanda na dauketa zuwa gidana banji komai a raina ba,hakanan ban kawo komai ba,kawai na saka a raina cewa,duk wanda ya taimaki wani Allah zai taimakeshi.


      Amma tunda muka zo gidan muka tattauna da xuwaira naga rashin gamsuwarta da lamarin,abun ya dan bani mamaki,saboda nasan cewa ba halayyar zuwaira bace,tana da kirki tana da tausayi,abinda yasa muka jitu kenan tamu tazo daya,saidai duk da na karanci hakan ga fuskarta,bata fito fili ta gayamin ba,har sai dana tuntubeta da cewa


       "Naga kamar xaman hauwa dana yanke tare da mu baiyi miki ba ko?" Murmushi kawai tayi sannan tace


       "Ba haka bane,rayuwa ce yanxu ta canza,duniya ta zama abar tsoro,taimako ya zama shima abun tsoro,kawai dai inaga ya kamata kisan ainihin wacece ita kafin ki xauna da ita" a lokacin murmushi nayi


"Banda abinki zuwaira.....ta yaya zansan wacece ita?,bayan bata da kowa?" Kai zuwaira ta kada


"Bazaiyu mutum ace kaf danginsa babu mutum ko daya ba,ba'a rasa saura,idanma babun,can inda ta zauna ita da kakarta kafin rasuwarta ya kamata ki tambayi halayyarsu kiji" a lokacin gani nake kawai hasashe ne irin na zuwaira,amma kamannin jidda basuyimin kama dana wata mai mummunar dabi'a ko halayya ba,don haka nabi zuwaira da cewa zan bincika na share zancan kawai,jidda taci gaba da rayuwa damu.


        Abun kamar hadin baki haka hafsa tace min,da yake tana da zafi ma har sabani mukaso samu da ita,tace nikam bani da wayo ne ko bansan ciwon kaina ba,da zan dauka mutum rana tsaka na kawoshi rayuwata ban bincika ainihin wayeshi ba,nace mata babu komai,Allah na nufa,kuma ina fatan ya sanyawa nufina albarka,tun tana mita da qananun maganganu har ta haqura ta zuba idanu,saidai a yadda take kallon jidda da yadda take mu'amala da ita zakasan kwata kwata bata kwanta mata a rai ba,don ba haka take mu'amala da sauran masu aikin gidan ba.


     Ta bangaren rashid ban samu matsala ba,saboda a sannan din jiddan da girmanta,budurwa ce,ta haura shekara ashirin ma,saboda haka ta haura shekarun da baya daukar masu aiki a cikinsu,yace dai kawai idan ina ganin dai daine shikenan,ta zauna din tare damu.


     Maganganun zuwaira da hafsa suka sanya naqi sakin jiki lokaci daya da jidda,na dinga karantarta a nutse,amma banga wani aibu ko mummunan hali tattare da ita ba,sai hidima da soyayya da take nunawa samir,fiye d wadda ni uwarsa nake nuna masa,hakanan fiye da wadda su zuwaira ke nuna masa,idan tana gidan samir baya kuka,babu me tabashi,babu me masa fada,baya neman abu ya rasa,kai hasalima idan kaga samir a wajena tun a lokacin nono kawai zai sha ya koma wajenta,ko yaye dana tashi ita ta karbeshi ta yayeshi,a lokacin hafsa ta tada ballin bala'i kan ita tace zata yayeshi ai,zata hadashi da yaronta amiru,wanda suke sa'anni,tsiran kwana biyu ne haihuwarsu,jidda na kuka tana bata haquri ra tattara samir ta kai mata,don ko sau daya bata taba nuna ta gane hafsa bata qaunarta ba,hakanan bata taba nuna damuwa kan rashin qaunar dake idanun hafsa ba,kullum girmamata take da nuna mata qauna.


       Kowa sai daya tausaya mata sanda samir ya tafi yaye wajen hafsa,ta koma sukuku babu wani walwala,har rashid ya gane,a sanna magana ta soma hadasu,ya tsokaneta da maman samir,yace kuma zai lallaba hafsan ta dawo mata dashi.


      Wannan shine silar fara magana tsakaninsu,saboda mahaukacin son da rashid yake nunawa samir,kamar an gaya masa cewa shi kadaine abinda zai haifa a duniya.


       Na riqe jidda cikin martabawa da girmamawa,na bata suttura irin wadda nake sawa,na bata irin abincin da muke ci,na bata makwanci tamkar na matar gida,na kula da buqatunta fiye dana kowa,saboda a lokacin ina ganin tafi sauran ma'aikatana quruciya,inaso ta tsare kanta da mutuncinta har tayi aure.


       Cikin hakan na duba certificate na secondary dinta,banyi qasa a gwiwa ba na samar mata gurbin karatu cikin jami'ar da nake koyarwa,ba matsala ko wahala ta samu saboda muqamin da nake dashi a sannan, course me kyau na samar mata,saboda dukka ina duba gobenta.


         Tafi tafi jiddan ta soma sakewa damu,ba jimawa ta koma kamar 'yar gida,a hankali sai duk wata sabga ta gidan ta fara komawa wuyanta,bayan tsantsar kulawa da samir,wanda wani lokaci tare suke zuwa lactures su dawo,har wasu ma na tsammatar danta ne,wanda sukasan bata da aure kuma sun dauka qanwata ce,dukka ina ce musu eh,saboda nima inajin dadin zama da hauwa,tana da matuqar ladabi da biyayya,hakanan tana yabawa sosai da dukka hidimar da nake mata,saboda babu abinda zan siya ban siya mata ba,don a lokacin dan dai Allah ya hadani da mutane masu tsarkakakkiyar zuciya ne,daba shakka a sannan babu abinda zai hana hassada da qyashi shiga zukatan su zuwaira akan jidda,amma Allah baisa sun nuna komai ko sun damu ba.


      Cikin qanqanin lokaci ban farga ba na fara ganin wasa da dariya sun fara shiga tsanin rashid da jidda,na danju kishi kadan,amma abun ban wani bari yayi tasiri sosai a raina ba,saboda naga dukka akan samir ne,fiye da rabin hirar tasu ma duk kan samir ne da abinda zasuyi yaji dadi,rayuwarsa ta inganta,don haka sai na saki raina,da zuciyata daya naci gaba da sabgata.


      Kwatsam ban ankara ba sai sabo da shaquwa ya fara gittawa a tsakaninsu,hira raha da wasa da dariya,tun ban damuwa har na fara jin kishi sosai a raina,amma na rasa ta yadda zan yiwa rashid qorafi,saboda yadda jidda ke bani girma tana kuma sake bada himma wajen kula da samir da nuna masa soyayya da kulawa.


       Wasa wasa abu yaci tura,har takai ta kawo rashid zai dauki jidda da samir su fita shopping ni ina zaune,koda abu ne wani lokacin idan bana kusa saidai ya bawa jidda ta riqemin kota ajjiyemin,idan nayi magana sai yace,ai yaga na aminta da jiddan ne,kuma yarinyar nan tana da hazaqa da qoqari,komai.naki dana yaron nan ita ke muku shi,haushi ya cikani,na tsuke fuska nace


"Ai ba gazawa taga nayi ba ko bare ka gayamin haka" dariya ya fashe da ita


"Kai raihana,ban sanki da wannan ba,kishine kawai yake damunki hala,amma jidda ai hutu ce a wajenki,kaf masu aikin gidan nan babu wanda yake aikatuwa irinta" gaskiya ne abinda ya fada,amma abinda na gani shine,babu wata sabga data zama wajibina dana gaza,komai na kula da mijina ban fasa ba,aikina bai sanya na rageshi da komai ba,kuma shi dinma harkokinsa sun sanya ba mazaunin gida bane.


     Abu daya ne da ban ankara dashi ba sai sannan,jiddan tana da azarbabi,wasu abubuwan na rashid ko na samir duk sanda na tashi xanyi saina tarar tayi wuf tayishi,koda baqi nayi kafin nace ayi musu kaza tayi,duk wanda yazo gidan saiya tafi da kirkin jidda a bakinsa,duk sanda muka hadu ya dinga tambayar ina jidda?,yarinya me kirki,musamman dangin rashid,cewa suke nayi dace da yarinya me kirki,ranar da family na daga sudan sukazo kuwa,zaka ce wajenta suka zo,duk wata hidima tasu a wuyanta take har suka tafi,da na dan motsa zatace aa na zauna miyi hira da baqina.


    Randa na hada undies din rashid xan wanke a toilet dina,nayi baqi na fito muna gaisawa bayan ta saukesu a wannan lokacin na fara taka mata burki kan ta daina shiga hurumin daba nata ba,tana hawaye ta bani haquri,idan raina ga baci nayi haquri,ita batayi don wani abu ba,tayi ne saboda taga jiya iwar haka ina kwance bani da lpy ina fama da zazzabi,yadda naga tanata kuka tana bani haquri sai naji babu dadi,naga kamar ban kyauta mata ba,tunda kulawa ce tasa haka,amma komai kulawa bai kamata ta taba kayan da suke sirrin mijina ne,nace mata ya wuce amma ta kula.


       Kwana biyu haka ta dinga rayuwa sukuku a gidan,har samir sai daya koka saboda yadda ta koma ba kuzari,rashid ma ya fuskanci haka,ya kuma sameni da maganar.


     Fada sosai na dinga yi,ta inda nake shiga ba ta nan nake fita ba,saboda raina haka kawai naji yana quna,bugu da qari kima yaron cikin dake jikina,wanda ya qaramin zafi,baice komai ba harna gama,sannan ne ya amsa min da


"Kada dai kije kishi ya rufe miki ido ki batawa wanda yake qoqarin kyautata miki" lafazin da ya sanya jikina yayi sanyi kenan,na rage daurewar dana fara yi mata.


       Yan kwanaki tsakani laulayi ya sakani a gaba,sai komai ya sake komawa hannun jidda,ni kaina a sannan na yaba mata,yadda take hidima damu kan jiki kan qarfi,bata xama ta huta kona minti daya,ga makaranta tata data samir wanda ya fara zuwa ba jimawa,ban samu kaina ba har sai da nayi barin cikin,taci gaba da hidima da ni har na warke na koma kan harkokina.


      Ban jima ba na sake samun wani,shima dai itace komai.namu,wannan ya qara kusanci me qarfi tsakaninta da samir dama rashid,shima dai cikin sai da ya fita na samu sauqi,bayan na warke saina sake ganin canji sosai tsakanin rashid da jidda,idan nayi magana yahau fada,yace duk kyautatawar da takemin bana gani?,sai shi don ya kyautata mata?.


        A wannan lokacinne rigima kusan taso barkewa tsakanin hafsat dashi,ta shiga maganar,ya hadamu duka yace bamu da kirki kuma bamu da halacci,kamar yadda na gaya miki,hafsat tana da zafi,saita qyaleshi kamar anbar maganar,tafiya tana kamashi tazo ta sanya jidda tattara kayanta tace lallai sai tabar gidan.


      Yadda jidda ke kuka tana roqon tayi haquri ya karyarmin da xuciya,ina qoqarin cewa ta barta,amma hafsa ta hada harda ni,haka nan tasa jidda ta tattara tabar gidan,ta gama kin bambamin fadan na zauna lusaranci,idan baiyi wasa ba zafa qwace rashid a hannuna,tayi ta gama ta fita.


     Tunda jidda ta fita duka sai tausayinta ya kamani,na kasa nutsuwa,musamman idan na tuna cewa bata da kowa,to ina zataje?,itace tambayar data dinga damuna,na tsaya gaban madubi na dubi kaina,sai naji bana ji sam bana tsoron zama da jidda,banjin zata iya qwacemin rashid,duba da irin halaccin da na yiwa rayuwarta,halaccin da nakejin ya isa yasa jidda taji kunya da nauyin aikata min ba dai dai ba,uwa uba bata ko kama qafata wajen kyau da diri ba?,to meye zanji tsoro?,wannan tunanin ya sanyani fita neman inda jiddan tayi.


Post a Comment

0 Comments