TOP HAUSA NOVELS atOptions = { 'key' : '20e08520dad54dbf6d9e963271

Abokin Aikina cmplt txt

  *ABOKIN AIKINA*

          


*@HADIZA D. AUTA*



*LAMBA TA ƊAYA.*


*_True life story_*


Tun da na shiga cikin motar shi, zuciyata ta fara dakan luguden uku-uku. Saboda tsananin tashin hankalin da ya kawo mini ziyara, domin ni kaina na san illar da hakan zai haifar mini. Na yi hanzarin dafe goshina tare da faɗin wash! Saboda mugun saran da na ji a tsakiyar kaina. "Subhanallah! Me ya faru?" Ita ce maganar da ta fito a bakin MD cikin kulawa, tare da damuwar da ta kasa ɓoyuwa a kan fuskar shi. Kafin daga baya ya ci gaba da ce wa "Ki daina saka kanki a damuwar da ke haifar miki da ciwon kan nan naki. Saboda lafiyarki tana da matuƙar amfani a wurina..."  ƙarshen maganar shi ba ƙaramin duka ta yi wa zuciyata ba, babu shiri na yi hanzarin kai kallona a kan fuskar shi.. "I, kina da matsayin da ciwonki ya dace mu shiga damuwa sosai a cikin ma'aikatarmu" ba shiri na sauke ajiyar zuciya mai ƙarfi, fargabar da ta tokare mini maƙoshi tana ƙoƙarin toshe numfashina ta faɗa. Sannan ya ɗora sharhi a kan maganar shi da ce wa "Dalilin hakan ya sa muke takaicin sabuwar lalurar nan da ta same ki. Wadda take ƙoƙarin kawo mana tawaya a cikin cigaban da muke samu ta ɓangaren jajircewarki. Ki daure ki sha magungunanki kamar yadda likitan ya umurta.  Sannan ki samu relief na tsawon kwana uku kafin ki koma wa aikinki. Ubangiji ya ƙara lafiya" "Amin" na amsa cikin maƙoshi saboda har lokacin ban daina jin saran gudumar da ake yi mini a tsakiyar kai ba. A sakamakon somewar wuccin-gadin da na yi ina tsaka da aiki a cikin Offishina.


Har ƙofar gidan ya ajiye ni ba tare da ya damu da matsalar da hakan za ta haifar mana ba daga ni har shi. Na fito motar jiki babu kuzari ina ƙoƙarin yi masa godiya ya miƙo mini ledar magungunan, da ya tsayu kai da fata jikin shi da aljihun shi har na farfaɗo na samu kaina.  Na zura hannu da nufin karɓar ledar babu zato muka zabura dukanmu, saboda dukan da muka ji an yi wa gilashin motar shi na gaba. Wanda a lokaci ɗaya ya tarwatse har yana barazanar bugun fuskokinmu. Da sauri na yi baya cike ƙoƙarin janyewa daga jikin motar, shi ma MD ya fito daga motar cikin zafin nama. Ƙirjina ya shiga bugawa a dalilin ido biyun da na yi da curarriyar fuskar Mukhtar. Wanda ke tsaye riƙe da ƙaton ice yana huci tare da aika mini mugun kallon da fitsari ya so suɓuce mini.  Kafin na yi wani yunƙuri ya fara ɗaga gandamin icen ya ci gaba da dukan gilasan motar MD babu-ji-babu- gani. Ɗaga icen yake yi yana sauke shi a kan motar iya ƙarfin shi gabaɗaya ya canza mata kamanni. Cikin tsananin tashin hankali na kai kallona ga MD da ke tsaye rungume da hannuwansa a ƙirji, yana ƙare wa Mukhtar kallon da na rasa gane ainahin abin da yake nufi da hakan. Cikin azama na nufi Mukhtar jiri yana kwasa ta da nufin hana shi aika-aikar da yake yi, sai dai kafin na isa wurin shi na yi azamar duƙewa ƙasa saboda hango icen da na yi dishi-dishi a sama yana ƙoƙarin faɗowa kaina. Shirun da na ji ya sa na ɗago kaina na gani da zummar ko dai idanuwana ne bai hango daidai ba. A kiɗime na miƙe jikina ya hau rawa saboda hango Mukhtar a yashe ɗan nesa da ni, icen kuma a hannun MD yana huci cikin matsanancin ɓacin ran da ya bayyana kan shi a kan fuskar shi. Hannu ya shiga nuna Mukhtar da shi cikin wata kausasshiyar murya ya ce "Zan haƙura da rasa komai amma ban da Zaituna. Ka yi duk abin da kake so zan kawar da kai amma kada ka yi gangancin taɓa martabarta balle lafiyarta. Wawa kawai soko wanda bai san darajar aure ba". 


Kafin na gama tantance abin da ƙwaƙwalwata take son sanar da ni, tafin Mukhtar ya fara sauka a cikin dodon kunnuwana, sosai ya so ƙara zautar  da tunanina ya hautsine mini kuzarin jiki da guntun tunanin da ke cikin kaina. Musamman maganganun da ya fara faɗa waɗanda suka zamo tamkar ɗigar ruwan dalma a jikina. "Rana ba ta ƙarya sai dai uwar ɗiya ta ji kunya. Haka ma rana dubu ta ɓarawo ɗaya tak! Ta mai kaya ce. A yau ka fasa ruɓaɓɓen ƙwan da kuka daɗe kuna ɓoyewa a tsakaninku. Da kanka ka yaye labulen sirrinku, ka fallasa asirinku saboda girman haƙƙin aure da ke bibiyar rayuwarku. To ka sani ka yi kuskure kuma ka yi gangancin shiga gonar da ba taka ba. Kuma ko za ka mutu a kanta wallahi ba zan taɓa sakinta ba balle ka aure ta. Ke kuma sai na nuna miki ba irina ake cin amana a zauna lafiya ba..".


Ƙare maganar shi ta yi daidai da fisgar da ya yi wa hannuna tamkar zai raba shi da gangar jikina, ina tirjiya tare da kai wa hannun shi duka da ɗan ƙarfin da ya rage mini. Amma hakan bai hana shi jefa ni cikin gidan ya wullar tsakiyar ɗakina ba. Ina ji ina gani ya saka mini key ya rufe ni ruf a cikin ɗakin ba tare da ya jira jin komai daga bakina ba. Na fara dukan ƙofar ɗakin ina kuka cikin disasshiyar muryata tare da ƙwala masa kira cikin ƙarfi ina faɗin; ya tsaya ya fahimci yadda abin yake, saɓanin abin da ya zata kuma ya yi tsammani tsakanina da MD. Amma hakan bai sa ya buɗe ni ba balle ya yi lokacin jin ta bakina kamar yadda na sha sanar da shi koyaushe.



ABOKIN AIKINA. Zai zo da zafin shi a cikin wannan shekarar. Free ne ga kowa saboda darussan da ke cikin littafin abin tausayi abin takaici abin koyi ga wasu nagartattun halaye. Abin gudu abin ƙyama daga wasu gurɓatattun halayen da za su zo a cikin littafin ABOKIN AIKINA.


 *ABOKIN AIKINA*



*@HADIZA D. AUTA*



*SADAUKARWA GA DAUGHTER ANUP😘*



*LAMBA TA BIYU.*



Ban san ya rigumar ta ƙare ba, domin shi kan shi tun da ya fita bai dawo gidan ba sai da dare ya ɗauke sawu kamar yadda ya ba. Na ci kuka har idanuwana suka kumbure babu mai rarrashina. Mutum ɗaya ce nake da tabbacin za ta kwantar mini da hankali, sai dai ba zan so ɓata mata farinciki ba kamar yadda nawa ya gurɓace. Ƙarin takaicin kuma yaran duka ba su dawo gidan ba, wanda alamu ya nuna a can za su kwana wurin Ummata. Amma mamakina ba ta kira ta sanar da ni ba kamar yadda ta saba idan sun yi marmarin kwana gidan. 


    Ajiyar zuciya na sauke a lokacin da na juya kwanciyata, wadda nake jin suka cikin haƙarƙarina tamkar a kan ƙayoyi nake kwance. Sanin kuka ba zai yi mini ranar komai ba domin ba yau na saba yin irin shi ba, kuma har yanzu bai warkar mini da mikin da ke cikin zuciyata ba balle ya kawo mini waraka, daga ƙangin rayuwar da nake ciki. Wanda a kullum na tuna ina jin kaina tamkar wata marainiyar da ta rasa komai da kowa nata a cikin duniya.  Saran da kaina ya yi ya sa na yi hanzarin dafe goshina ina faɗin "Wash! Allah!" Saboda wani zafin da nake ji yana bi cikin jijiyoyin idona, wanda ya haifar mini da zugin da ya hana ni buɗe idanuwan har sai da ciwon ya lafa mini. Shiru na ɗan lokaci ina sauraren azabtuwar da nake fuskanta a cikin kaina har ma da zuciyata da ta karɓi nata kason, tana yi mini wani irin ciwo tamkar za ta tarwatse a cikin ƙirjina.


Daren ranar haka na yi bacci cikin rashin natsuwar zuciya da ciwon da ya ƙi bari na na huta. Da ƙyar na samu ƙarfin halin yin sallah sannan na lallaɓa na koma kan gado na ƙudundune cikin bargo. Daga tunanin da zuciyata ta lula ban san lokacin da bacci ya yi awon gaba da ni ba. A cikin baccin na ji muryar Ummata tana faɗa a sama tamkar a mafarki, sai dai buɗe idanuwan da na yi na gan ta tsaye saman kaina fuskarta a haɗe ya tabbatar mini gaske ne ba mafarki ba. Na yi ƙoƙarin tashi zaune cikin disasshiyar muryar da ta gaji da kuka na fara gaishe ta, ba tare da ta amsa ba ta fara feso mini abin da ke cikin bakinta, "Me kike so ki mayar da kanki Zaituna? Har yaushe kika yi girman da za ki fara bin wasu mazan waje bayan da auren wani a kanki. A zatona ko babu igiyar aure kanki za ki tsare mutuncinki ko don ki hana zagin da mutane za su yi mini, a kan riƙon sakainar kashin da ake ganin ni ce na yi silar mayar da ke abin da kika zama yanzu. Shin ba kya ganin rashin zaman lafiyar aurenki zai taɓa mini ɗan guntun mutuncin da ya yi mini saura a idon mutane? Kina buƙatar ki kashe aurenki ki zo mu jeru gida ɗaya ni da ke mu dinga haɗa kafaɗa babu mai aure a cikinmu?. Sau nawa zan ce ki yi haƙuri da halin Mukhtar ko don yaranki? To bari ki ji; Idan ma kin kashe auren gidan wani za ki sake zuwa, kuma bai zama lalle ki samu marar mata ko wanda bai da 'ya'ya ba. Kin ga idan kin ƙi sharar masallaci sai ki je ki yi ta kasuwa, domin kuwa dole ne ki yi wa 'ya'yan wasu bauta bayan kin watsar da naki a wulaƙance..." Kukan da ta fara yi ya ƙara damalmala mini komaina. Ban tsaya rarrashinta ba ni ma na fashe da nawa kukan cikin ƙunar zuciya saboda na kasa furta kalma ɗaya da zan kare kaina, wanda na sani ita kanta shaida ce a kan tsare mutuncin aurena da nake yi duk da bai zama ingantaccen aure kamar sauran aurarraki ba. Daga ni har ita kuka muke yi mun kasa rarrashin juna balle mu samu wanda zai rarrashe mu. 


Ita ce ta fara jarumtar tsayar da ruwan hawayen da take yi ta shiga fyace majinar kukan da ta sha, ta janyo ƙafafuwanta ta zauna a bakin gado cikin sigar rarrashi ta ce "Idan ban da tausayin yaran nan da nake yi, me zai sa mu fuskanci baƙincikin rayuwa irin wannan? Ki yi haƙuri Zaituna na san ina sara miki ko babu gaɓa. Amma ki sani ni na san abin da ya sa ba na fatan ki kashe aurenki. Kuma ina roƙon Allah ya hana ki zama bazawara, domin ni kaɗai na san duhun baƙincikin da ke damfare cikin hakan. Ubangiji ya yi miki albarka, yadda kike yi mini biyayya ke ma Allah ya sa 'ya'yanki su yi miki fiye da hakan". Tana ƙare faɗar maganar ta miƙe tana ƙoƙarin ficewa daga ɗakin, na bi bayanta da kallo ina goge hawayen da suka kasa tsayawa cikin kwarmin idona.  Kiciɓis suka yi da Mukhtar wanda yake ƙoƙarin shigowa ɗakin fuskarsa a haɗe tamkar bai taɓa dariya ba. Ganin ta ya sa shi sakin fuskar shi kaɗan ya rusuna har ƙasa yana sosa ƙeya cike da girmama ya ce "Umma daman magana nake so mu yi dangane da aikin nan da take zuwa. Ni dai gaskiya ban lamunta da shi ba, idan akwai yiyuwar ta daina zuwa duka a duba mini. Saboda zuwa aikin ne yanzu duk wata matsala take kunno kai tsakanina da ita, amma idan aka jingine shi kamar an yi maganin rabin matsalolin da ke faruwa daga wannan sai wannan".  Shiru ya ratsa tsakani idona a kanta ina jiran amsar da za ta ba shi kafin na yi magana, domin na fuskanci nazarin maganganun shi da amsar da za ta bayar take yi.  "A gaskiya Mukhtar sai dai ka yi haƙuri da zancen aikin nan, domin ka sani ban da wani iko a kan hana mata zuwa aikin nan. Amma tun da ba ka so kana da ikon da ya fi na kowa a kanta. Ka je ka samu Alhaji Ali domin ka sanar da shi a kai ƙarshen maganar, saboda shigar da kaina cikin maganar yanzu zai sake janyo wata sabuwar rigima tsakanina da shi. Wanda ba na fatar hakan an yi na baya ina fatar kuma ba za a yi maimaici ba". ajiyar zuciya na sauke mai ƙarfi ina aika masa harara da jajayen idanuwana tamkar su fito su manne jikin shi. Saboda tsabar takaicin da yake ba ni ji nake kamar na taso na rufe shi da duka. "Ba sai na je ba, a bar zancen kawai. Umma amma a sanar da ita babu ita babu wannan mayaudarin mutumin. Domin wallahi yanzu haka mutane har sun fara zunɗena a kan na zama mijin ho-ti-ho, saboda ganin yadda na kasa raba ta da mutumin da yake ƙoƙarin keta mata haddin aure..." "Wane aure kake zance? Kai har kana da bakin faɗar kana aurena? Na rantse da Allah darajar Umma kake ci, da tuni na watsa maka fetur na ƙone ka..." 


"Innalillahi wa inna ilaihirraji'uun!" Ita ce kalmar da Ummata ta furta cikin kiɗimewa da tashin hankalin da ya bayyana kan shi cikin fuskarta. "Gara da ta yi gabanki kika gani Umma, haka take yi mini ko a gaban su Haidar. Ba ta jin kunyar faɗa mini magana domin ta wulaƙanta ni a gabansu. Ban san wace irin tsana ce take yi mini ba da ba ta iya ɓoyewa ko a gaban waye..." "Ban ji daɗin maganar nan ba Zaituna, ki san me za ki faɗa wa mijinki saboda gudun shiga matsala da fushin Ubangiji".  Nasiha ta shiga yi mini ina sharar hawaye, shi ma tana yi masa faɗan so-kanka a fakaice. Saboda har kullum tana jin nauyin shi da kunyar surukuntakar da ke tsakaninta da shi. Wadda ya dace a ce tuni ta watsar da ita ta huta, ko don kalolin cin amanar da yake yi mini.  A gabana suka yi sallama ta fice ya dawo kaina yana ƙare mini kallon wulaƙanci sama da ƙasa, sannan ya yi ƙwafa ya fice tare da buga mini ƙofar ɗakin da ƙarfi kamar zai ɓalla ta. 





Shin ya wannan rikicin yake ne? Kun hasko wani abu cikin labarin ko sai mun ƙara nutso a cikin tafiyar?. 





D AUTA CE🚶



*ABOKIN AIKINA*



*@HADIZA D. AUTA*



*SADAUKARWA: DAUGHTER ANUP*



*LAMBA TA UKU.*


Ajiyar zuciya na sauke, sannan na yunƙura cikin rashin kuzari na sauko daga gadon. Ina layi na fice ɗakin saboda yunwar da ke ƙwaƙular cikina, kitchen na nufa kai-tsaye don jirin da nake ji ya tabbatar mini da ban samu waraka daga ciwon da ke damuna kwana biyu ba, wanda yake hana ni sukuni a duk lokacin da babu komai a cikina. Turus na yi na ja na tsaya gaban kayan shayinmu. Domin a take na gano Mukhtar ya yi abin da ya saba, saboda kofin da ya yi amfani da shi ma a nan ya bar shi bai ɗauke ba, kamar yadda ya bar gwangwanin madarar a buɗe bai rufe ba, bayan milon da ya barbazar a ƙasan tiles har ya yi danƙo, domin ba na tamtama a kan lokacin da zai zuba ya sha shayin ne ya zubar da shi, saboda halin shi da sani na sakankance komai ba ya yin sa a nutse sai ya yi hargitsi. Sau tari idan zai ci tuwo kafin ya tashi daga cin tuwon nan sai ya zubar da miyar. Idan fura ce kuma da wuya ya gama sha a kofi bai zubar da rabi ba.


 Numfashi na ja tare da sauke ajiyar zuciya cikin ƙunar rai, a gurguje na ɗan gyara wurin sannan na ɗora ruwan zafi na haɗa tea. Saboda a yadda nake ji ba zan iya cin komai ba idan ba shi ba. Fitowa ta daga kitchen kenan ina ƙoƙarin komawa ɗaki, na ji muryar maƙociyata tana sallama, hakan ya tabbatar mini da Mukhtar ba ya cikin unguwar, domin a bin da na sani ne ba ta shigowa gidan sai ta tabbatar da ba ya nan, saboda tana cikin mutanen da yake zargin suna kawo mini tsegumin da yake haɗa mu rikici da shi a wasu lokutan. Na amsa mata sallama da disasshiyar muryata irin ta marasa lafiya. Tare muka nemi wurin zama a kan kujerun falon muka zauna, ina kurɓar shayin muka fara gaisawa babu yabo babu fallasa. Yanayin kallon da naga tana yi mini ya tabbatar min da akwai dalilin da ya kawo ta wurina, wanda ba na raba ɗaya biyu a kan rikicin da ya auku ne jiya. Wanda nake da tabbacin zuwa lokacin ya karaɗe ko'ina cikin unguwar da kewaye. Nan take na ji hawaye ya cika idanuwana, na ajiye ɗan sauran shayin da rage kan tebur, saboda zuciyata ta yi duhun da ba zan iya shanye shi ba. 

"Ban samu wayarki ba, shi ya sa na kasa haƙuri sai da na yi wanann tattakin. Saboda ba na so Mukhtar ya gan ni ya yi mini abin da raina zai ɓaci a banza..." "Me ke tafe da ke?" Ita ce tambayar da na jefo mata tun kafin ta dire zancenta. Sai da ta sauke ajiyar zuciya sannan ta ce "Ban ji daɗin abin da ya faru ba, kuma ban ji daɗin irin zantukan da ake yi a kanki cikin unguwar nan ba" Ta ƙare maganar fuskarta ɗauke da damuwa, shiru na yi na ɗan lokaci sannan cikin muryar kuka na ce "Ban ga laifin duk wanda ya zage ni ba, domin abin zagin ya ji ko kuma ya gani shi ya sa ya zage ni. Idan akwai mai alhakin laifin hakan to ni ce nan. Domin da ban yi biyayyar da nake yi a yanzu ba, da duk hakan bai faru ba. Na sani babu biyayya wurin saɓa wa mahalicci, amma na zaɓi tauye kaina na ci amanar kaina saboda farincikin mahaifiyata. Na sani kuma Allah ma ya sani babu wani abu na assha tsakanina da MD illa gaisuwar mutuncin da muke yi. Amma ban san miye a cikin zuciyar shi dangane da ni ba, domin da ban ji abin da ya faɗa ba kai-tsaye zan ce da kowa sharri Mukhtar yake ƙoƙarin yi masa, sai dai kuma idan na yi duba da sanin darajar ɗan'adam irin na shi. Zan daki ƙirji na ce sai Allah ya isar masa a kan duk wanda ya zarge shi a kaina. Ban ji daɗin kashin kajin da ya shafa wa kansa ta dalilina, duba da mutumtakar shi ta fi ƙarfin kwatar ɗan sauran mutuncin da ya rage, wanda Mukhtar bai gama watsar mini ba. Ban taɓa ganin aure irin nawa ba a duniya, ina ma ban rayu ba har zuwa wannan lokacin da nake wannan maganar. Na tsani kaina kuma na tsani kowa ma a duniyar nan..."  

Kuka na fashe da shi mai ƙarfi saboda ƙololon baƙincikin da ya tsaya mini a ƙahon zuci. Haƙuri ta fara ba ni, tana goge hawayen da na kula suna fareti saman fuskarta tun lokacin da na fara magana, sannan ta ce, "Idan ɓera da sata daddawa ma da warinta. Me ya kai ki shiga motarsa har ki bari ya kawo ki gida? A gaskiya dole Mukhtar ya ji haushin hakan, don ko ke ce kika gan shi da wata a mota za ki ji babu daɗi, shi ma da Allah ya halassta wa ya yi huɗu. Me ya sa ba ki hana kanki shiga motar ba tun a farkon tayin da ya yi miki? Ina da tabbacin da kin kauce wa wannan alfarma ta shi da kin tsira daga yamaɗiɗin da ake yi da ke. Yanzu wa gari ya waya? Ko fita kika yi za a nuna ki a ce ke ce, shin kin manta abin da ya faru baya kafin wannan? Haka za ki yi ta maimata laifi iri ɗaya wane kallo kike ganin mutane za su yi miki? Idan wancan gaskiyarki ta wanke ki, wannan kuma fa?" 


Shiru na yi kawai ina ci gaba da tsiyayar ruwan hawayen da suka kasa tsaya mini tamkar burgaggen famfo. Na sani ita mai tausayin halin da nake ciki ce, amma wani lokaci ina jin haushin yadda take ganin ban iya zaman aure ba ne, shi ya sa Mukhtar yake shuka mini tsiyar da ya ga dama. Duk da ina jin takaicin kallon da take yi mini, ina yi mata uzuri saboda ba ta haɗu da rabin kwatar matsalar da nake ciki ba ne. Na san da ta shiga makamancin halin da nake ciki, wataƙila za ta fahimci yadda abin yake. 


"A tara mata dubu ba za su iya haƙurin da nake yi gidan Mukhtar ba, a cikin matan dubu kuma har ke kanki Maman Taufiƙ ba za ki iya wata ɗaya da Mukhtar ba, a yadda na san halinki da tsattsauran ra'ayinki. Don haka ki bar kowa ya kalle ni a yadda ya fassara ni, ki bar kowa ya zage ni a yadda yake so. Na yafe wa duk wanda ya zage ni a cikin rashin sanin ba bisa haƙƙina ba, amma Mukhtar ba zan iya yafe masa ba ko da zan janyo wuta tana ƙona jikin shi..." 

     "Innalillahi wa inna ilaihirraji'uun! Sau nawa zan ce ki san abin da kike faɗa Zaituna? Yanzu ribar me za ki ci idan kin yi wa mijinki uban 'ya'yanki Allah ya isa? Ba kya gudun wani abu ya same shi ta sanadin hakan?" Tambayoyin da ta jero mini kenan a ruɗe, saboda firgicin abin da ta ji a bakina, wanda inda da sabo ta saba ji amma ta kasa shanye wa kunnuwanta a duk lokacin da irin haka ta kama. 


"Gaskiya ki gyara furutan da kike furzarwa ga mijinki..." "Duk abin da ta yi mini ke kika janyo. Don ke kika shigo zuga ta kina fakewa da ban haƙuri" zancen Mukhtar kenan a tsakiyar kanmu, zumbur ta miƙe tana faɗin "Allah dai shi ne masani a kan komai. Domin yadda nake fatar na zauna da mijina lafiya  ita ma ina mata fatar hakan..." Idona a kanta ta fice ranta a ɓace, hakan ya sa na fara girgizar ƙafafuwana cikin matsanancin fushi na ce "Ranar da duk haƙƙin matar nan ya kama ka, wallahi ba za ka ji daɗin rayuwarka ba. Ka ji da haƙƙoƙan da ka ɗauka ka daina ƙoƙarin ɗora wa kanka wasu. Domin zargin da ke cin zuciyarka zai yi ta janyo maka musibar da ba ka san ina za ka shiga ba ranar lahira..." "Daman ai ke ba ki mini fatar na gama lafiya balle na shiga aljanna..." "Duk abin da za ka faɗa ka faɗa kanka tsaye, ni dai na sani haƙƙi bala'i ne mitsssss! Aikin kawai" 

   A fusace na miƙe na shige ɗakina tare da rufo ƙofa. Gado na faɗa ina rera kukan da na kasa tantance ainahin na mene ne nake yi. Shin tausayin kaina da ban yi sa'ar miji ba? Ko tausayin 'ya'yana da ban zaɓar musu uba nagari ba? Ko kuma tausayin MD da ya rufta rayuwar shi cikin bahagon auren da bai san lokacin haɗuwar shi da sanadin lalacewar shi ba? Ta ya zan fassara mafarin matsalata? Ta ya zan warware wa kaina baƙin ƙullin da ya hana ni jin daɗin aure? 'Allah kana gani ba ni da kowa sai kai. Ka kawo mini waraka daga matsalolin da ban san ya zan yi na shawo kansu ba'. Abin da na faɗa kenan a zuciyata cikin ƙanƙan da kai ga Ubangijina.




Hmmmm! Yanzu aka fara 😅



 *ABOKIN AIKINA*



*@HADIZA D. AUTA*



*SADAUKARWA: DAUGHTER ANUP*



*LAMBA TA HUƊU.*


Kiran sallar zuhur ya sa na miƙe jiri yana kwasa ta na ɗoro arwala. A zaune na yi sallah saboda ƙafafuwana da na jin ba za su iya ɗauka ta ba. Bayan na gama a nan kan sallaya na kwanta ina sharɓar hawaye, ban san lokacin da bacci mai nauyi ya yi awon gaba da ni ba. Azababben ciwon kai ya farkar da ni babu shiri, saboda luguden da ake yi mini cikin kai ya linka yadda na saba ji, dafe kan na yi ina ta faɗin sunayen Allah a zuci da bakina. Kukan da cikina yake yi ya sa na yunƙura zan miƙe jiri ya kwashe ni na koma na zauna. Shiru na ɗan lokaci ina sauraron daddaƙar da ake yi mini cikin kan, sannan ina jin tashin ƙarar tv'nmu cikin kunnuwana daga nan inda nake, ƙarfin halin miƙewa na yi ina layi na fito daga ɗakin domin na samar wa kaina abin da zan iya ci. Ganin Mukhtar zaune a falon yana kallon waƙar Indiya, hakan ya sa na ji wani tuƙuƙin baƙinciki ya rufe mini zuciyata, don har ga Allah na tsani jin muryar shi ma balle na yi ido biyu da shi. Hakan ya sa duba ɗaya na yi masa na kawar da kai na shige kitchen, duk da raina ya ɓaci da ganin garar da yake ci shi kaɗai ba tare da ya neme ni ba. Duba da yadda ya san ban da lafiya tsawon kwanaki kuma ban ci komai ba.  Sai maganin Chemist da yake siyo mini don bai yarda da zuwa asibiti ba. Ganin yake yi na cika jaye-jayen abin da zan ɗora masa wahala, ko yara ke ciwo sai an yi da ƙyar yake bari a je asibiti. Wani lokaci ma sai mun yi rigima sosai sannan yake jan yaro ya je da shi da kan shi, a ƙoƙarin shi na nuna jin haushin matsin lambar da nake yi masa. Ba zai je da ni ba ko ya ba ni damar zuwa da su ba, sai dai idan sun dawo na ga magungunan da aka siyo ban isa na ce komai ba.

   

   A wannan karon ma tea kawai na iya haɗawa na fito. Ina ƙoƙarin shigewa ɗaki ƙamshin naman da yake ci ya cika mini hanci, amma hakan bai sa na waigo ba balle na yi masa ƙorafi. Zaune na  yi bakin gadon na zuƙe shayin sannan na yi shiru ina nazarin yadda aka yi na rasa wayata. Domin hankalina duka ya dawo kanta saboda ita ce abokiyar hira ta, kuma ita ke ɗebe mini damuwa a duk lokacin da nake cikin ɓacin rai ko kaɗaici. Mintuna kaɗan da shan shayin na jiyo muryar wata tana sallama, kamar na share amma na kasa haƙuri na miƙe ina taku a hankali na fito domin, na ga wake sallamar.  Firdausi ƙawata ce na gani ta nufo ni cikin fara'a tana faɗin "Ashe kina ɗaki?" "E, mu je daga ciki" Sai da ta yi gaba sannan na bi bayanta, bayan na aika wa Mukhtar mugun kallon da nake ji kamar na shaƙe masa wuya, saboda kallon da na ga yana yi muna ta gefen ido. 


"Zaituna kin rame da yawa, har yanzu jikin ne?" Sai da na yi murmushin ƙarfin hali sannan na ce "Jikin ne, tare da baƙincikin Mukhtar da ya addabi zuciyata.."  "Mu yi zancen ciwon, don ita matsalar Mukhtar idan da sabo kin saba da ita. Gaskiya ya dace ki je asibiti a bincika a ji me ke damunki, zama da ciwo cikin gida ana shan magani ba ya kawo waraka. Don wani lokaci ciwo daban maganin da ake sha ma daban.." "MD ya kai ni asibiti, a lokacin da na faɗi na some a wurin aikinmu. Amma masifar Mukhtar ba ta bari na karɓi magungunan ba..." "Ban gane ba!" Sai da na zuƙe majinar kukan da ya zo mini sannan na ce "Shi ya kai ni asibiti daga can wurin aikin, bayan na samu kaina ya ɗauko ni a motar shi ya kawo ni gida. Shi ne fa Mukhtar ya farfasa masa gilassan mota sannan ya tara mana mutane yana jifar mu da miyagun maganganun da babu komai a cikinsu face ƙazafi da zargi..." "Innalillahi wa inna ilaihirraji'uun! Wai shi Mukhtar me ya sa ba ya hangen nesa kafin ya aiwatar da abu? Meye laifin MD a nan don ya taimaka miki a matsayin shi na babba a wurin aikinku? Wani lokaci rashin fahimta da zargi shi yake kawo duk wata matsala da ke faruwa ke da shi, sannan abin haushin ma Mukhtar ba ya jin maganar kowa kuma ba ya jin shawara ko an ba shi. Tabbas! Zai ji zafi idan ya ga wani ya kawo ki gida a cikin motar shi. Amma kuma yana da kyau ya yi bincike ya ji wane dalili ne ya kawo hakan? Saboda ya fi kowa sanin halinki, abin da za ki iya yi da wanda ba kya iyawa, duk da ba a shaidar mutum amma ana gane zurfin ruwa a cikin ido. Duba da tsawon lokacin da kuka kwashe tare ya dace a ce akwai fahimtar juna tsakaninku. Ni fa wallahi ban ga amfanin irin wannan zaman da kuke yi ba. Idan shi ya hau ke ki sauko mana, duk da na san zuciya ba ta da ƙashi, amma ya dace ku zauna ke da shi ku samu maslaha a cikin zamanku. Yaranku girma suke yi, kuma suna fahimtar duk abin da ke wakana a tsakaninku. Wanda hakan kwata-kwata bai dace ba. To ni zan tafi, amma ki daure ki je Asibiti gaskiya, zama da ciwo da ba zai yiyu ba. Saboda lafiya 'yar tattali ce idan ta suɓuce komai zai iya lalacewa, sannan ki daina saka wa kanki damuwa a kan matsalar shi. Don da lafiyarki ma ya mayar da ke juji balle kin rasa lafiyar da kowa yake tinƙaho? Allah dai ya kyauta..." Cikin matsanancin ɓacin rai kwance a kan fuskarta ta fice, domin a kaf faɗin garin babu wadda ta san matsalata ciki da baya sai Firdausi. Domin akwai abubuwan da ko Ummata ba ta san da su ba, amma ita amincina da ita da zamanta mace mai sirri ya sa ba na shayin sanar da ita damuwata. Tare muka fito tana faɗin "Ki daure ki je asibiti gaskiya" "In Sha Allah" na ce da ita, ko da muka fito Mukhtar ba ya falon. Har ƙofar gida na raka ta, bayan mun ɗan taɓa hira sannan muka yi sallama ta tafi. Ko da na dawo falon na hango Mukhtar yana fitowa daga ɗakin shi, ba ƙaramar jarumta na yi ba wurin tsayawa na fuskance shi na ce "Gobe ina so na je asibiti..." "Ko ba ki faɗa ba ai na ji komai da kunnuwana..." "Daman ina sane da laɓen da kake yi mini idan na yi baƙi. Shi ya sa ba na shayin faɗar komai domin ka ji da kunnuwanka" Shiru ya yi yana kallo na saboda na kamo tashar shi da kyau, domin abu ne wanda na kiyaya gare shi duk lokacin da na yi baƙi sai ya laɓe ya ji me muke faɗa, ko da gidan ya dawo ya fahimci akwai wasu saɗaf-saɗaf yake yi ya laɓe ya dinga sauraron hirar da ake yi. 

      "Yana da kyau da ki koyi ɓoye sirrinki, don ba ke kaɗai ce mai matsala a gidan aure ba..." "Kowa ta shi ya sani, don haka kowa karatun sallah yake yi da kumfan bakin shi. Asibiti nake so ka kai ni gobe, saboda haka na yi maka magana. Domin duk abin da zai sa na haɗa yawu da kai ma ba son shi nake yi ba, matuƙar bai kama dole ba.." amsar da na jefo masa kenan a  ƙufule, shi ma bai bari na dire zancena ba ya ce "To ni gaskiya ban da kuɗin kaiki asibiti. Yanzu haka ko kuɗin da zan je aiki Boɗinga ban da su balle na kai ki asibiti". Shiru kawai na yi ina kallon shi sannan na ce "Ba ka da kuɗi ka ci kaza ɗazu?" "E, wannan daban, don ba ki san yadda aka yi na same ta ba. Amma gaskiya ban da kuɗin kai ki asibiti, wurin aikin ma da wuya idan zan je goben saboda ban da kuɗin mota..." "Ni ina da, kuma ina roƙon Ubangiji ya ƙara mini.." A harzuƙe na tari numfashin shi na yi maganar, sannan na wuce kan kujera na zauna ina nishi saboda zuciyata da ke ta bugawa da sauri da sauri. Raka ni da "Amin" ya yi sannan ya fice abin shi. 

      Kuka na shiga yi ina nazarin rayuwata ta baya da yanzu, da badaƙalar da aka sha farkon auren har zuwa yanzu ba tare da an gama ba. Tiryan-tiryan komai ya shiga dawo mini cikin kwanyar kai. Hawaye ya ɓalle mini tamkar burgaggen famfo mai bori, sai da na gaji da kukan don kaina sannan na miƙe na yi wanka na yi sallah. 


Rashin wayata da rashin jin motsin yarana kusa da ni, ya haifar mini da wata sabuwar damuwar da ta janyo mini Zazzaɓi. Nan take na fara jin sanyi na nemo paracetamol,  ƙwara biyu na afa na dunƙule ina rawar sanyi. Cikin ikon Allah mintuna a tsakani na fara jiɓi a daidai lokacin da na fara jin ihun murnar yarana, wanda hakan yake tabbar mini da alamun sun dawo. Farinciki fal raina na fara ƙoƙarin saukowa daga kan gadon da nufin tarbon su. Sai ga su sun shigo da gudu sun rungume ni suna faɗin "Oyoyo Mama" tsananin daɗi ya sa na maƙalƙale su duka su ukun ina faɗin "Sannun ku da zuwa". Ummu Salma babbar 'yata ta taɓa wuyana ta ce "Mama jikinki da zafi har yanzu ciwon kan kike ji?" Hawayen kuka ya zo mini na yi ƙoƙarin mayar da su ina faɗin "Ai na ji sauƙi, amma gobe zan je asibiti a duba ni..." "Mama duk na girma na zama babba, sai na gina miki ƙatuwar asibiti a cire miki ciwon kan nan ki huta" Abin da Haidar ya faɗa kenan yana share mini hawayen da ban san lokacin da suka zubo kan fuskata ba. Iman na kalla wadda ta yi tagumi tun da suka shigo ba ta ce komai ba tana kallona. Sanyin halinta da na sani ya sa na dafa kanta cikin ƙaunar uwa zuwa 'yarta na ce "Ke kuma me za ki yi mini idan kika girma". Sai da ta share hawayenta sannan ta ce "Zan saka ki farinciki ki daina kuka ba na son ganin hawsyenki..." Kukan da ta fashe da shi ya sa ni ma nawa ya ƙara ambaliya. Hannunta na riƙo cike da jarumta na goge hawayen da ke ta sauko mini kan fuska na ce "Ki daina kuka kin manta za ki zamo likitaa!?" Na ja kalmar ƙarshe cike da jan zaren wasa domin na tsayar da kukanta. Kai ta ɗaga mini alamun "e" Ina murmushin ƙarfin hali na ce "To ai da kin yi mini  allura cikin baki shi kenan ruwan hawayen zai ɗauke" cikin sauri ta rufe bakinta tana dariya ta ce "A baki kuma..?" Kafin na ba ta amsa Haidar ya ce "Ai Mama har cikin ido ana allura ko?" Tambayar shi ta ba ni dariya na ce "Har cikin kunne ma.." Gabaɗaya daga ni har su muka fashe da dariya. Cikin dariyar na kalli Ummu Salma na ce "Ki je ki dafa muku Indomie.." "Umma fa ta ba da abinci a kawo muku ke da Abbanmu. Mu ma ta ba mu namu ta ce mu zo da shi mu ci a nan" Annurin fuskata ya ɗauke a dalilin Abbansu da na ji ta ambata, saboda har ga Allah ba na son maganar Mukhtar da duk abin da ya shafe shi, har cikin zuciyata. 


Haɗe fuska na yi na ce "Oya ku je ku yi shirin sallar magrib ga ta can an fara kira. Kai kuma Haidar ka wuce masallaci kada ka bari a fara sallah ba ka fita gidan nan ba" Suka fice ɗakin cikin sauri na sauke ajiyar zuciya. Raina a jagule na sauko gadon na fito falo, kulolin Ummata da na hango saman table ɗin tsakiyar falona. Hakan ya sa na isa da sassarfa na fara buɗe babbar kulolin da ke gabana. Tuwon masara ne da miyar ganye sai ƙamshin man shanu ke tashi. Sai ɗaya kular da na buɗe na hango ɗanwake maƙil a ciki da man ja a leda tare da yajinsu a leda. Hakan ya tabbatar mini tuwon ne namu su ne da ɗanwake. Wuri na samu na zauna cikin tagumi ina nazarin har yaushe Umma za ta dawo daga rakiyar Mukhtar, duk da abin da yake yi mini ita har kullum girmansa take gani a idonta. 'Shin ta ya ya zan fahimtar da Umma illar ɗaure wa Mukhtar ƙugun da take yi? Kuma har zuwa yaushe zan fita daga wannan ƙangin rayuwar da nake ciki?'





Hmmmm!😰




D. AUTA CE✍🏼



D. AUTA CE🫰🏻



*ABOKIN AIKINA*



*@HADIZA D. AUTA*



*SADAUKARWA: DAUGHTER ANUP*



*LAMBA TA BIYAR.*


Hawayen da suka gangaro mini na share, sannan na miƙe na yi ɗaki domin na yi sallah. Na daɗe kan sallaya ina addu'o'in waraka daga halin da nake ciki. Shigowar yaran ya sa na ɗaga kai ina kallon su, rige-rigen gaishe ni suke yi ina amsawa cikin sakin fuska, Ummu Salma ta ajiye abincin da ta zubo mini shaƙe da plate. Sai da na yi murmushi sannan na ce "Wannan abinci ina zan kai shi ni kaɗai...?"

    "Ki ci ki ƙoshi Mama. Umma ta ce mu dinga saka ki kina cin abinci mai yawa, kuma mu dinga ba ki haƙuri kada mu bari ki yi kuka".

    Abin da Haidar ya faɗa kenan tare da ɗebo tuwon yana ƙoƙarin kai mini lomar a bakina. Baki na buɗe ya saka mini murmushi ɗauke a kan fuskar shi yana jin daɗi. Ganin hakan ya sa dukansu suka dinga ɗebo tuwon suna ba ni, ban hana su ba kuma ban ƙi karɓa ba. Sai da na fara jin amai sannan na dakatar su. Ruwa Ummu Salma ta kawo mini na Sha, cike da jin daɗi har cikin raina na yi musu godiya kuma na saka musu albarka. 

    Na ba su umurnin canye sauran tuwon sannan na ce da su mu je falo, a can ma tare muka ci ɗan waken kuma sosai na ji daɗin shi a bakina. 


***

Daren ranar na yi bacci sosai kuma na ji sauƙi dangane da ciwon kan da ya addabe ni. Mukhtar kuma bai dawo gidan ba sai sha biyu da rabi, kamar yadda ya saba yin daren shi a waje koyaushe. Ina jin lokacin da yake rufe gida tare da rufewar ɗakin shi, ajiyar zuciya na sauke a raina na ce, 

'Ni kam dai ba ni da bambanci da bazawara. Wai me ya sa wasu mazan suke kasa gane abin da mata suka fi so a wurinsu? Shin ta ya ya mace za ta ji daɗin kyautata wa mijinta bayan shi ba ita ce a gaban shi ba..?'  

Katsar da marata ta yi na yi hanzarin dafe wurin ina faɗin,

 "Wash! Allah!"

Gumi ya fara karyo mini saboda kartar da marar take yi mini, bayan ta dunƙule wuri ɗaya tana zugi. Saboda wani feeling da nake ji wanda nake da tabbacin sha'awa ce ta janyo mini ciwon marar. Na jima cikin halin kafin ta lafa bayan na samar wa kaina waraka, ta hanyar da na saba a duk lokacin da na shiga irin wannan halin. Kuka na fashe da shi cike da ƙyamar abin da nake yi, wanda nake jin takaicin abin a raina amma kuma na kasa dainawa.

        Saboda ganin ba ni da wata mafita mai sauƙi idan ba ta wannan hanyar ba. Duk da na san hakan laifi ne kuma illa ne gare ni ga lafiyata, amma na zaɓi bai wa kaina natsuwa ta wannan hanyar domin ba zan iya aikata zina ba, haka ma ba zan iya zuwa wurin Mukhtar ba. Sanin ko na je babu abin da zai iya tsinana mini balle ya warkar mini da ciwon, illa ya ƙara mini damuwa da takaicin da zan kwana ina tsaki tare da jin haushin kaina. Ban bari na kwana da najasa ba, na tashi na yi wankan tsarki sannan na dawo na kwanta raina a cunkushe kamar ko yaushe. Amma na yi bacci mai daɗi saboda samun natsuwar da na yi ta hanyar gamsar da kaina.


    Tun da safe na miƙe na taimaka wa Ummu Salma suka shirya cikin kayansu na makaranta, sannan suka karya agurguje suka nufi ɗakin shi ya ba su kuɗin tara da na abin hawa. 

     Daga nan inda nake ina jiyo sautin shi yana yi musu faɗa.  "Ni fa wallahi ban da kuɗin da zan ba ku yau. Don ko wurin aiki ba zan je balle na ba ku kuɗin tara, karɓi ɗari ku yi maneji da ita idan za a kai ku hakan.."

   Suka fito fuskokinsu a haɗe suka yi mini tsaye, cikin ƙunar rai na miƙe na ɗauko musu kuɗin tara sannan na ƙara musu kuɗin da zai kai su ya dawo da su. Don daman can kuɗin zuwa kawai yake ba su idan an tashi su dawo ƙasa. Sannan na ja kunnuwansu sosai a kan kada su je ko'ina idan sun dawo ba ba nan, matuƙar ba lokacin islamiya ya yi ba su tafi. Saboda asibitin da zan je ganin likita, kuma ban san lokacin da zan dawo ba.  

    Na raka su har ƙofar gida suka tafi suna ɗaga mini hannu sannan na dawo na nufi ɗakina rai a ɓace. Saboda matuƙar haushin da na shiga dangane da riƙon sakainar kashin da yake yi muna ni da yarana. Wanda hakan ya ƙara saka mini haƙuri da juriya a kan zaman da Umma take so na yi ko don yarana. Domin Mukhtar ko dabba aka bar masa tsaro sai ta mutu bai san ta mutu ba, saboda rashin kula da ko-in-kula irin na shi ta kowane ɓangare. Haƙƙin kan shi ma bai sauke ba balle haƙƙin waɗanda ke tare da shi.


    A gurguje na shirya ba tare da na sake bi ta kan shi ba na fice abina. Kai-tsaye gidan Firdausi na nufa, domin ta raka ni asibitin saboda babu waya a hannuna balle na kira ta. 

       Da murna ta tarye ni muka yi ɗakinta cike da jin daɗin ganin juna, zama na yi a kan gadonta ina faɗin "Wash!" Saboda tafiyar da na yi gabaɗaya jikina ciwo yake yi, domin har lokacin ba na jin ƙarfin jikina. 

    Bayan mun gaisa na sanar da ita abin da ya kawo ni wurinta, shiru ta yi na ɗan lokaci sannan ta ce "Bari na faɗa wa Baban su Mujahida tun kafin ya fita". 

     Da sauri ta fice na bi bayanta da kallo cike da burgewa, saboda suna zaman lafiya sosai ita da maigidanta da yaransu cikin farinciki. Tagumi na yi ina zancen zuci, 

'Ke kam kin yi sa'ar aure, ba irina ba da na rako matan auren duniya'.

     Har raina idan na ga mace da mijinta suna ƙaunar junansu, burge ni suke yi matuƙa gaya. Saboda ni ban ƙaradda komai a cikin aure ba face wahala da tsunduma kai a cikin masifa. Bayan zubewar ƙimar da mijin ya yi mini a idon mutane, tare da janyo mini zagin da ban ji ban gani ba...


    "Yawwa! Ya ce mu je amma fa wallahi ya yi faɗa..."

     "Faɗan me?" Ita ce tambayar da na jefo mata saboda faɗuwar da gabana ya yi babu shiri. 

   "Ya ce ina mijinki da ba zai kai ki asibitin ba sai ni zan kai ki?" 

     Ajiyar zuciya na sauke tare da yin tagumi nan take na ji wani ɗaci ya ziyarci maƙoshina. Cikin sanyin muryar da ke gaf da kuka na ce "Idan kin ga zan takura kawai na tafi ni kaɗai..."

    "Ba fa hana ni ya yi ba, kawai dai haushi abin ya ba shi a ce ni zan raka ki asibiti bayan mijinki ne ya dace ya ɗauki alhakin hakan. Bari na shirya mu je kada mu yi latti da yawa mu tarad da jira" 


     Bayan ta shirya muka fito gidan, abin hawa muka samu muka hau. Muna tafe ina yi mata bitar yadda muka yi da shi a kan zuwa Asibitin. Girgiza kai kawai ta yi cike da takaici ta ce "Ni na rasa wane irin mutum ne Mukhtar! Shi kullum idan bai janyo abin magana ba ba ya jin daɗi. Tsakani da Allah kwata-kwata ba ya kyautawa, domin ita lafiya gaba take da komai".  Shiru kawai na yi ban ce komai ba, saboda tsabar ɓacin ran da na shiga.


    Ko da muka je Asibitin mun taradda jira muka bi sahun masu bin layi. Muna ta hirar matsalolin ma'aurata ni da Firdausi har layin ya kawo kaina, na shiga ofishin likitan cikin sanyin jiki na zauna kujerar da ke gaban shi. Bayani na fara yi masa bayanin abin da nake ji, shiru ya yi mini na ɗan lokaci yana rubuce-rubuce sannan ya ɗago kai yana ƙare mini kallo ya ce 

"Kina da aure?" 

Na ce masa "I" 

Ya sake yin rubutu jikin wata takarda sannan ya miƙo mini ya ce 

"Je ki a yi miki awon, idan aka gama ki kawo mini result". 

    Na miƙe cikin hanzari na fice, wanda nake ji a jikina kallona yake yi ta bayana. Takardar na miƙa wa Firdausi muka nufi ɓangaren da za a yi mini awon. A nan ma jira muka yi har layi ya kawo kanmu, tare da ita muka shiga. Aka ɗibi jinina da fitsari sannan muka dawo muna jiran sakamako. Mintuna a tsakani aka kira ni na karɓi takardar gwajin muka koma wurin Likitan. Na miƙa masa takardar ya duba tsawon minti biyu sannan ya kalle ni ya ce,

 "Kina da ulcer, kuma sannan kina fama da matsananciyar sha'awa a jikinki. Ki yi ƙoƙarin shawo kan matsalar tun kafin ta yi ƙarfi".  

   Kunya ta rufe ni na haɗe fuska ban ce komai ba. Takardar ya miƙo mini ta magungunan da zan saya sannan ya raka ni da addu'ar samun lafiya, na fito offishin cikin sauri saboda kunyar da ta yi mini lulluɓi. 


    Ban sanar da Firdausi zancen ba, amma na yi mata bayanin ulcer da aka ce ina ɗauke da ita. Chemist ɗin da ke bakin Asibitin Firdausi ta sa muka je, magungunan aka duba mana sannan aka saka leda bayan an yi total. Kuɗin da ke hannuna ba su isa ba sai da ta cika mini, sannan na karɓi maganin muka tafi.  


Abin hawa muka fara nema a bakin titi, kamar an ce na kalli gefena. Sai ga MD da gudu zai wuce ta gabanmu karaf idanuwana suka sauka cikin na shi. Gabana ya ƙire ya faɗi saboda tozalin da na yi da shi ya tuna mini ɓarnar da Mukhtar ya yi masa. Nan take na shiga sunkuyar da kai har ya dawo ya tsaya gabanmu, cikin fara'a yake tambayar inda za mu je. Firdausi ce kawai ta amsa masa da cewa, "Gida za mu je..?" 

Gaishe shi na shiga yi cike da jin nauyin shi a idona, buɗe motar ya yi ya fito idanuwan shi a kaina yana faɗin 

"Ya jikin naki?" 

Kaina a duƙe na ce "Da sauƙi".

"Allah ya ƙara lafiya"

"Amin" Firdausi ta amsa, ni dai kaina a duƙe zuciyata cike da son ba shi haƙuri dangane da abin da ya faru. Motar shi ya koma ya fito da wata leda a hannun shi ya miƙo mini yana faɗin

"Ga wayarki nan da na manta ban ba ki ba ranar. Tsoron wata rigimar ya hana na bai wa kowa ya kai miki gida. Sannan ki yi haƙuri dangane da abin da na janyo miki ranar, ban san hakan zai faru ba da ban je ba..." 

"Babu komai ni ce ya dace na ba ka haƙuri..." Maganar da na yi kenan cikin sanyin jiki, kafin ya katse ni da faɗin,

"No! Kada ki damu. Allah ya ƙara lafiya".


Yana ƙare faɗar hakan ya shige motar shi ya wuce, ajiyar zuciya na sauke sannan na ce da Firdausi. "MD yana da kirki wallahi. Kuma ko a offis ba ya shiga shirgin mata, shi ya sa ban ji daɗin abin da Mukhtar ya yi masa ba..." 

"Allah dai ya kyauta! Amma zargi ba zai bar Mukhtar zama lafiya da ke ba, matuƙar bai sauya hali ba". 


    Abin hawa muka samu, bayan mun miƙa tafiya na buɗe ledar da MD ya ba ni da zummar ciro wayata, kawai sai ga sabon kwalin waya na hango. Baki buɗe na yi hanzarin faɗin,

 "Na shige su!"

Firdausi ma ta kai kallonta ga kwalin wayar tana faɗin "Sabuwa ce!" 

Cikin sauri na fito da wayar a kwalinta har wani sheƙi take yi, sai kuma ga asalin wayata ƙasan kwalin na gani. Jikina ya hau rawa cike da tsoron abin da zai je ya dawo, saboda har ga Allah na gaji da tashin hankali. Musamman irin wanda zai janyo rikicin da za a ji tsakanina da Mukhtar, sannan ba na son zargin da yake jifa ta da shi a banza mutane suna zagi na. 


 "Damuwar mi za ki yi a kan abin da ba ki roƙa ba?" Firdausi ta jefo mini tambayar ganin yanayina ya sauya a lokaci ɗaya.

   "Halin Mukhtar na sani, a kan wayar nan zai iya janyo mini zagin mutane da ɓacin ran Umma". Na ƙare maganar kamar wata doluwa. 

   "To ke faɗa masa za ki yi yadda aka yi kika same ta kenan? To bari ki ji, na rantse da Allah muddin ba ki taimaki kanki da kanki ba babu wanda zai ƙwatar miki 'yancinki wurin Mukhtar. Ban ce kada ki mayar wa MD wayar shi ba idan hankalinki bai kwanta ba, amma ki daina ba da ƙofar da zai dinga ɓata miki suna a banza. Haka kawai don shi laifi yana tudu sai ya dinga tsallake na shi yana hango naki domin ya baza wa a faifai yana rabar wa mutane!?"  

Ta ƙare maganar cikin ɗaga murya cike da jin haushi. Shiru kawai na yi ina nazarin maganganunta, cikin sanyin murya na ce,     

      "Zan mayar masa da wayar shi gaskiya. Saboda ba na son zargin Mukhtar ya tabbata a kanmu..."




Sannu matar Mukhtar🥲






D. AUTA CE✍🏼



*ABOKIN AIKINA*



*@HADIZA D. AUTA*



*SADAUKARWA: DAUGHTER ANUP*



*LAMBA TA SHIDA.*


Shiru kawai Firdausi ta yi mini bà tare da ta ce da ni komai ba, har sai da muka je unguwarmu aka ajiye ni sannan muka yi sallama. Fatan samun sauƙi ta yi mini sannan mai adaidaitan ya juya da ita suka wuce. Da tunanin yadda zan mayar wa MD wayar shi a zuciyata na isa bakin ƙofar gidanmu, dole na yi turus ina kallon ƙofar da kwaɗon da ke jiki. Juyawa na yi cike da gajiya na yi gidan Maman Taufiƙ, saboda tabbacin da nake da shi wurinta yara suka kai mini makulli idan na zo na karɓa. 

    Da sallama na shiga gidan, tsaitsaye muka gaisa na karɓi makullin na fice. Saboda ba na son tsawaita zance a lokacin saboda burin da nake da shi a cikin raina, wanda nake buƙatar sirri ba tare da kowa ya ji ko ya gani ba. 

   Ban tsaya falo ba kai-tsaye ɗakina na wuce na zauna kan gado. Ajiye jakar da ke hannuna na yi sannan na fito da ledar wayar da MD ya ba ni, wayata na fara cirowa cikin sauri na kunna. A gaggauce na nemo wayar MD ina ƙoƙarin danna masa kira wani kiran ya shigo wayata. Ganin sunan mai kiran ya sa na yi hanzarin ɗaga wayar, 

     "Ke matar nan ina kika shige kwana biyu babu ke babu wayarki?" Murmushi na yi kamar a gabanta sannan na ce, "Kwana biyu ina ta fama da jiki, sai yau na samu sararin buɗe wayar..." 

    "Allah Sarki! Ɗazu na zo gidanki domin na duba ki ba kya nan" Ta ƙare maganar muryarta ɗauke da damuwa. 

    "Ayya! Na je asibiti ne yanzu na dawo gidan". Na ba ta amsa cike da kulawa saboda tuno wace ce ita da matsayin da ta ɗauke ni. "Na so na tarad da ke, saboda akwai maganar da nake so mu yi. Amma dai yaushe za ki dawo wurin aiki?"  

   

"Ranar Laraba in Sha Allah zan shigo. Amma idan babu damuwa ki faɗa mini yanzu mana". Na ba ta amsa cikin ƙosawa da son jin abin da za ta faɗa mini, duk da jikina ya ba ni tatsuniyar gizo ba ta wuce ta ƙoƙi. Domin ni da ita kusan duk kanwar ja ce sai dai matsalarta ta fi tawa sauƙi linkin. 

    "Hmmmmm! Na gaji da matsalar Mama, kuma ba na so na yi abin da zai janyo mini wata rigima..." 

     "Ki yi haƙuri kamar yadda kika saba.Saboda mai haƙuri yana tare da Allah komai daɗewar lokaci, zai kawo miki waraka ta gano gaskiya gaskiya ce da yardar Allah..."

     "Mama ta yi nisan da ba ta jin kira, yanzu haka dawowar da na yi na iske ana damun fura a tsakar gidan nan. Amma har aka sha aka shanye daga ni har Yusuf babu wanda aka bai wa. A ganina ko ba mu da haƙƙi za a ba mu ladar ganin ido, sannan abin da kowa ya sani ne ina son fura amma ba su ji kunyar hana muna ita ba, daga ita Mamar har Sadiyar duka. Sannan ko ya dawo na faɗa masa haƙuri kawai zai ba ni. Ƙarshe ma ya bi ni da dogon sharhin ƙarya domin ya kare Mama kada a ga laifinta..." Cikin muryar kuka take magana, kafin na sauke ajiyar zuciya na ce, 

     "Ki yi haƙuri Amina ki bar su da girman haƙƙin da ke kansu, idan kina buƙatar furar ki saya ki sha ai ba faɗuwa ba ce". 

    Sautin sharar kukan da take yi a cikin wayar ya kashe mini jiki matuƙa, da lallami na kwantar mata da hankali har ta fahimta, kuma ta sauko daga dokin fushin da ta hau. Sannan muka yi sallama na kashe wayar bayan na tabbatar mata da zan fito aiki ranar Laraba.

     

     Shiru na yi na ɗan lokaci sannan na furzar da iska a bakina, na ƙara lalubo wayar MD na danna masa kira. Sai dai har ta tsinke ba a ɗaga ba, ban gaji ba na sake danna wani kiran, ringing ɗaya biyu aka ɗauka.


     "Assalamu alaikum" ita ce sallamar da na yi cikin karyayyar murya.

      "Wace ce ke?" Tambayar da aka jefo mini kenan a fusace cikin ɗaga murya, ƙirjina ya buga babu shiri cikin sauri na katse kiran. Saboda muryar macen da na ji hakan ya tabbatar mini da matar shi ta ɗauki wayar. Jikina ya hau rawa musamman kiran da na ga ya shigo wayata ɗauke da sunan MD. Kamar kada na ɗauka, sai dai na yi jarumtar ɗagawa cikin ɗar-ɗar saboda tsoron abin da za ta faɗa mini. 

     "Me ya haɗa ki da mijina har kike kiran shi a waya?" Shiru na yi saboda ban san me zan ce da ita ba. "Wannan kiran ya zamo na ƙarshe tsakaninki da shi matuƙar kina da sauran son kanki. Domin a kan mijina wallahi babu abin da ba zan yi wa duk 'yar iskar da ta raɓe shi ba. Idan kuma kina ganin faɗa ce kawai nake yi, to ki sake kula shi ki ga yadda zan sa a nemo mini ke a duk inda kike cikin faɗin duniyar nan.."  ƙitt ta datse kiran ta bar ni riƙe da waya a hannu na kasa motsin kirki tamkar wadda aka zare wa laka. 

    Cikin sanyin jiki da na gaɓɓai, na sauke wayar daga kunnena tare da sauke wata ƙaƙƙarfar ajiyar zuciya. 'Gaba kura baya siyaƙi' zancen da na faɗa kenan cikin raina. Saran da na ji kaina ya yi ya sa na miƙe da nufin ɓoye wayar na ci abinci. Saboda masifaffiyar yunwar da nake ji, na yunƙura kenan saƙo ya shigo wayata. Da sauri na duba saƙon ƙirjina yana bugawa saboda fargaban kada a ce matar MD ce, sai dai na kasa ɗauke idona daga kan allon wayar saboda saƙon da nake ta maimaicin karatun shi a zuciyata. 

     'Ki yi haƙuri Zaituna. Na shiga wanka ne ban san kin kira ba. Me ke faruwa ne?'


     Ajiye wayar kawai na yi saboda ban san me zan ce da shi ba a lokacin, domin kwanyata babu komai a cikinta kamar an goge mini komai. Fita ɗakin na yi na nufi kitchen, cike da tabbacin ganin abin da zan jefa wa cikina don na san Ummu Salma ta yi mana girki. 

      Shinkafa da wake na gani, cikin sauri na zuba na dawo falo na zauna ina ci ina tunanin  kashedin da matar MD ta yi mini, wanda nake jin sautinta yana amsa-kuwa cikin kunnuwana tamkar a lokacin take magana. Ban san lokacin da na canye abincin ba saboda dogon nazarin da na lula.


    A gurguje na gama sallah, saboda kiran da ake ta yi mini wani bayan wani ga wayata da ƙara. Zabura na yi cikin zafin nama na ɗauki wayar a daidai lokacin da wani kiran ya sake shigowa. Da hanzari na danna kore saboda ganin sunan MD ɓaro-ɓaro a jikin wayar, kuma zuciyata ta tabbatar mini da shi ne ba matar shi ba. 


     "Don Allah ki yi haƙuri, kada ki ga na takura ki. Me ya faru ne na ga kiranki..." 

     "Daman wayar da na gani ce a cikin ledar da ka ba ni. Shi ne na ce ko ka manta ne ka sako ta a ledar..." katse ni ya yi da faɗin,

     "No! Taki ce ba mantuwa na yi ba. Kuma kada ki ɗauki ce wa na ba ki ita ne da wata manufa. Na ba ki ne a matsayin kyauta saboda ci gaban da kika kawo mana a cikin ma'aikatarmu. Muna alfahari da samun zaƙaƙurar ma'aikaciya irinki, fatan za ki karɓa hannu bibbiyu domin ki ji daɗin ƙara jajircewa a kan aikinki".


     Girmansa da mutuncin shi ya sa na ce da shi na gode "Na gode sosai Sir. Allah ya ƙara rufa asiri" Muka yi sallama a mutumce, amma a raina na so ya karɓi wayar shi. Ko ba komai zan yi nesa da rashin mutuncin matar shi, duk da ba na zaton ta san da wayar balle zancenta...

      

   "Da wa kike waya?" Ita ce tambayar da Mukhtar ya jefo mini ba tare da na ji motsin shigowar shi ba. Fuska na haɗe alamun babu sassauci ga duk abin da zan furta cikin bakina a lokacin. 

     "Ina ruwanka da wanda nake waya da shi. Ko kana da ikon duk wani motsin da zan yi sai ka san da zaman shi?" A fusace na yi maganar cikin ɗaga murya. Bai kula ni ba ya nufi wurin  wayar da ke kan gado har lokacin, ya fiddo ta a leda yana jujjuya kwalin yana girgiza kai. Ban hana shi ba har ya gama tsugudidin shi ya ajiye tare da rugume a hannu a ƙirji ya ce,


     "Wai me kike son mayar da kanki ne? A tunaninki Allah ba zai kama ki a kan cin amanar auren da kike yi ba...?"

      "Kafin ya kama ni kai ne mutum na farko da haƙƙi zai rataye maka wuya ka mutu a wulaƙance. Yanzu kai har kana da bakin faɗar ana cin amanar aure? Kai nawa ka yi kafin ni na fara? Ko ka manta bala'in da kake yi na tuna maka yanzun nan? Ka san darajar aure kake shiga hurumin wasu matan auren? To bari ka ji abin da ba ka sani ba, a yau duk abin da na zama wallahi kai ne ka ɗora ni a kan hanyar na miƙe ɗoɗar. Saboda matan auren da ka yi rayuwa da su haƙƙinsu ne ke ƙoƙarin fita a saman kaina..." 

     Jikina yana rawa nake faɗar maganar saboda tsananin ɓacin ran da maganar shi ta saka ni. Kafin shi ma ya katse ni da faɗar, 

     "Babu inda aka ce wai don wani ya yi abu kai ma sai ka yi. Ki bar ni da haƙƙinki da kika ce na ɗauka, ke kuma ki sauke wanda yake kanki ki huta. Amma wayar nan ko ki mayar wa ɗan iskan da ya ba ki ita. Ko kuma na sanar wa Umma tun da ni kin raina ni ba kya jin maganata..." 


A harzuƙe na ce "Duk inda za ka je ka faɗa ka je ka faɗa, amma wallahi ba zan mayar da wayar nan ba. Idan ka isa kai namiji ne ɗan halak, ka haɗa ni da takardar sakina uku yanzun nan ba sai anjima ba..."


     "Allah ya ba ki haƙuri. Tun da ke ba ki da wani zance a rayuwarki sai na saki".

      "Aurenka auren tsiya miye amfanin shi? Wallahi da irin wannan auren naka gara zawarcin mace dubu. Don kai ba mijin aure ba ne kuma ba ka kai namiji ba har yanzu..."

     "Ya isa! Kada ki nemi faɗa mini babu daɗi. Waya dai ce ki je ga ki ga ta nan. Idan wadda ta isa da ke ta zo ai sai ku yi maganar tun da ni kin mayar da wani shashasha". 

   

Daga haka ya fice fuu tamkar ya tashi sama, kallon banza na bi shi da shi sannan na yi tsaki. Wayar na mayar a leda sannan na ɓoye ta, don na san tsaf zai iya dawowa ya ɗauke ta ba tare da na sani ba. Zuciyata cike da alwashin ko Ummata ta ce na mayar da ita ba zan mayar ba balle shi.




Ku ci gaba da bi sannu a hankali za mu je inda warwarar ƙullin da ya wargaza zaman lafiyar auren Zaituna da Mukhtar 😅




D. AUTA CE ✍🏼


*ABOKIN AIKINA*



*@HADIZA D. AUTA*



*SADAUKARWA: DAUGHTER ANUP*



*LAMBA TA BAKWAI.*


        Raina a ɓace na fito falo saboda sautin maganar shi da nake ji a sama, yana bayanin rikicin da muka yi da shi. Wanda nake da tabbacin waya ce yake yi kuma Ummata ce yake faɗa wa. Bakin ƙofar shi na nufa saboda baƙincikin makircin da na ji yana yi a cikin wayar, don bayan abin da ya haɗa mu har da ƙarin gishiri da mai, yana ta ƙoƙarin dole sai ya ɗora mini laifukan da ya saba ya wanke kan shi. Saboda komai na yi a wurin shi laifi ne shi kaɗai ne mai yin daidai.

     "Wallahi Umma har yanzu suna tare, a kan shi yau babu abin da ba ta faɗa mini ba. Babban baƙincikina mutane har sun fara yamaɗiɗi da ita a cikin unguwar nan saboda tarayyar da take yi da shi..."

       "Hakiƙa duk mai irin halinka a rayuwa ba ƙaramar asara ya yi ba wallahi. Ina takaicin zama wuri ɗaya da kai, ina da-na-sanin auren da na yi maka tsawon shekaru. Haka ma ina tausaya wa yarana da na yi zaɓen tumun dare wurin zaɓar musu uba kamar ka..." Abin da na faɗa kenan a bakin ƙofar ɗakin shi, cikin ɗaga murya bakina yana kumfa, domin ya tabbatar da na ji abin da yake faɗa. 

     "Ai kin saba faɗa ba tun yau ba, don haka yanzu ko kin maimaita ba abin mamaki ba ne..." Na katse shi cikin hanzari ina faɗin, 

      "Tir! Da rayuwarka Mukhtar! Ka ji haushi iya haushi a kan rayuwar azuzancin da kake yi. Idan burinka haɗa ni da mahaifiyata ne, to ka je ka ci gaba ga gani idan Allah zai bar ka..."


      Ƙarar da wayata take yi cikin sautin kiɗan da na saka mai daɗi, hakan ya tabbatar mini da Umma ce take kira na. Ban bi ta kan wayar ba na ci gaba da aika masa baƙaƙen maganganu yana mayar mini da raddi cikin rainin hankali, domin duk na faɗa sai ya mayar mini ɗaga can cikin ɗakin shi. 

        Shigowar yara aguje bai sa na daina abin da nake yi ba, saboda na riga da na zo wuya. Kamar yadda har lokacin wayata take ta ɓurarin neman agaji. Kallo kawai yaran suka bi ni da shi bayan kowanensu ya sha jinin jikin shi, domin in da sabo sun saba gani amma sun kasa cire damuwar hakan a ransu. Saboda su na koma kan kujerar falo na zauna ina sauke numfashi, Haidar ya zo ya zauna kusa da ni yana riƙe mini hannu cikin nuna kulawa. Ummu Salma ta yi ɗaki da sauri ta ɗauko wayar ta kawo mini, Iman ta rakuɓe tana kallona tana sharar ƙwalla. 


     "Mukhtar ƙarya yake yi Umma, kuma ƙazafin da ya saba ne ya sake yi mini..." Na faɗa raina a ɓace ba tare da na jira cewarta ba. 

       "To me ya haɗa ki da mutumin har ya ba ki waya?" 

     Ajiyar zuciya na sauke sannan na ce "Waya ce aka rarraba a ma'aikatar kowa aka ba shi ba ni kaɗai aka bai wa ba. Shi ne fa daga ganin ta ya fara jifa ta da ƙazafin da ya saba, tun da ni babu ranar da zan yi abin kirki kullum sai ya kawo ƙara ta. Saboda ganin yake yi ya fi ni iya faɗar zance, da daɗin bakin ƙarya domin kawai ya sa ki ga laifina.."

     Na katse maganar saboda kukan da ya zo mini. Umma ta yi shiru na ɗan lokaci sannan ta ce, "Daina kuka ba na son jin kukan nan raina ƙara ɓaci yake yi. Ki yi haƙuri zan fahimtar da shi domin ya daina tunanin da yake yi a ran shi..."

      "Na gaji da zama da Mukhtar Umma, na kai matuƙar ƙololuwa a kan zaman nan da nake yi.." Ƙit! Ta kashe wayar, saboda abin da ta tsana kenan a ranta ta ji ire-iren waɗannan maganganun suna fita daga bakina. 

      Kuka na ci gaba da yi Haidar yana goge mini hawaye cikin fuskar tausayi. Ummu Salma da Iman suka shiga sharɓar kukan su ma, kafin Ummu Salma ta miƙe cikin ɓacin rai ta shige ɗakinsu.


   Na kai kallona ga Iman cikin muryar kuka na ce "Tashi ki cire kayan Makarantarki. In dai wannan ƙaddararren uban naku ne, kuna da aiki idan kuka ce za ku dinga kuka a kan mugun halin shi. Kai ma ta shi ka je ku cire kayan ka fito ka yi shirin zuwa masallaci".

     Suka miƙe tare da jan jakar islamiyarsu suka yi ɗakinsu. Na daɗe zaune a wurin ina karanta wasiƙar jakin da na saba, a kan wace hanya zan rabu da wannan baƙin zaman da nake yi. Sai dai duk hanyar da na zura kai cikinta sai na hango tarnaƙin da ke gabana idan na ce ita zan kama.

      'Ni shi kenan a haka zan ƙare rayuwata da mijin da ba zai share mini hanyar shiga aljanna ba?' 

      Tambayar da na jefi kaina da ita kenan wadda ban da cikakkiyar amsarta, kiran sallar magrib ya sa na miƙe na yi ɗaki. Ina kan sallaya har aka yi isha, sannan na miƙe na fito falo na zauna, ɗauke da wayata ina chat su Ummu Salma suna kallo. Jiki na saki a cikinsu muka ci abinci tare na sha magani kamar ba ni da damuwar komai, domin Allah ya saka ni cikin mutanen da damuwa ba ta zauna mini a zuciya duk girmanta. Daga na yi masifata na gama shi kenan nake jin komai ya wuce a wurina, amma duk lokacin da ban samu damar furzar da abin da ke bakina ba, abin ya fi tsaya mini a zuciya har ya haifar mini da damuwa. 

     Mun ja lokaci a falon har suka yi bacci. Sai da na tayar da su suka shiga ɗakinsu, sannan na tofe su addu'o'i na rufe musu ƙofa na nufi ɗakina. 

    

        MD na hango online bayan na kwanta na sake buɗe datata, saboda Gb WhatsApp ne gare ni duk wanda ke online sai ya nuno mini yana nan. Haka kawai na tsinci murmushi a kan fuskata, domin har cikin raina na ji daɗin ganin shi ko da ba za mu yi magana ba. Na shiga duba status ɗin mutane idan na fita wannan na faɗa wancan har na isa ga na MD. Shiru na yi ina nazarin maganganun da na ga ya rubuta a status ɗin shi, domin kai-tsaye na alaƙanta rubutun da ni. 

    'Mu yi haƙuri da yanayinmu na yau idan bai yi daɗi ba. Domin komai wucewa yake yi kamar ba a yi ba. Babu abin da yake tabbatacce idan ba wanda Allah ya tsara ba! Ubangiji ya kawo mana farincikinmu a kusa da mu'. 

     Ajiyar zuciya na sauke, tare da goge ruwan hawayen da ya ziraro mini a gefen fuska. Saboda ina ji a raina kamar ya shiga zuciyata ya hango abin ke cikinta. Ina ji kamar ya haska wani madubin da ke hango masa hoton abin da ke damuna. 

     "Tabbas!" 

Comment ɗin da na yi masa kenan a jikin status ɗin. Babu jimawa ya buɗe saƙon tare da fara typing a lokaci ɗaya. Kasaƙe na yi ina jiran ganin me zai ce, saboda sanyin da jikina ya yi a lokacin ɗaya bayan na fito daga akwatin sirrin shi.

     'Barka da dare!'

    "Barka dai sir!"

Maganar shi da amsata kenan bayan na ɗan ja lokaci kafin na buɗe saƙon, gudun ya gano zumuɗin da nake yi da ganin maganar shi. 

 "Ba ki yi bacci ba ashe?"

"I, yanzu dai zan shige"

     Na ba shi amsa daidai da tambayar shi, kafin ya sake jefo mini wata tambayar na amsa masa. 

  "Ya jikinki?"

"Alhmadullilah! Na ji sauƙi sosai."

"Allah ya ƙara lafiya"

"Amin Ya Rahman!"


Shiru ya ratsa tsakanin maganganun. Har na bar akwatin sirrin shi na koma status ina kallo sai ga wani saƙon ya jefo mini, wanda na hango abin da ya ce tun a saman sanarwar da ake yi mini ta shigowar saƙon.

   "Yaushe za ki koma aiki?" 

   Ɗan jim na yi kafin na ba shi amsa da cewa, "Laraba in Sha Allah!"

"Allah ya kai mu". Ita ce amsar da ya ba ni kafin ya sauka. A gaban idona ya sauka online ba tare da ya jira mun yi sallama ba, haka kawai na tsinci zuciyata da ɓacin rai, saboda rashin jin daɗin hakan a raina. Shiru kawai na yi ina tunanin me ya sa bai jira mun yi sallama ba, a ƙarshe ni ma kashe wayar na yi na gyara kwanciya. Da tunanin shi na kwana a raina, tare da guntayen mafarkan da na yi da shi a cikin baccina. Waɗanda ba zan iya kawo ya ya na yi su ba, amma dai tabbas na gan shi a cikin mafarkina kuma a yanayi mai daɗi. 


    Abu kamar wasa wunin ranar zungur MD yana maƙale a zuciyata, domin ko na so kawar da tunanin shi sai ya dawo mini sabo. Ta kai minti ɗaya biyu sai na buɗe data domin kawai na yi katarin hango shi online, sai dai abin haushi tun daga saukar da ya yi bai sake hawa ba sai dare. A galabaice na ga daren saboda matsuwar ganin shi da na yi.

       Cikin sa'a bayan Isha ina hawa na hango shi, farincikin da ya lulluɓe ni ya sa na kasa ɗauke idanuwana daga kan lambar shi. Sannan tunatarwar da ake ta yi mini ta MD online ta ƙara rura wutar murna ta. Haka kawai na tsinci kaina da shiga Gallery na ɗauko hotona da nake ji da shi na ɗora a status, duk da hakan ba halina ba ne ɗora hoto a status. Amma zuciyata ta ƙawatu da saka shi cikin ɗoki da zumuɗi, mintuna a tsakani da ɗora shi na shiga duba saƙunan da ke ta shigo mini har lokacin tsakanin groups da private. 

     "Ma Sha Allah!"

Ita ce kalmar da ya yi mini comment da ita a jikin hoton. Murmushi na yi a raina ina faɗin 'Dama ta samu' Sannan na yi reply da "Na gode Sir"


    Shiru bai sake cewa da ni komai ba bayan ya duba saƙon, kawai sai na ji ina sha'awar gaishe shi. 

"Ina wuni?" Ita ce tambayar da na yi masa ƙirjina yana bugawa, saboda har raina ina jin kaina tamkar wata mara gaskiya.


 "Lafiya lau ya ƙarfin jikin?"

"Alhmdulillah!"


Daga haka kamar ba zai sake ce mini komai ba, sai na hango ya sake cewa, "Gobe sai offis ko?"

      Cike da jin daɗi na amsa da, "In Sha Allah!" 


     "Your welcome!"


Yana gama faɗar hakan ya sauka, na yi reply da "Thanks!" Amma har sha biyun dare ta wuce bai dawo online ba balle ya ga godiyar da na yi masa, na ji matuƙar haushin hakan, a raina na ce,

     'Wai shi bai san babu kyau ana tsaka da magana a sauka ba a sanar ba?' 

 Tsaki kawai na yi saboda ya ɓata mini rai ba kaɗan ba, sai da na nutsa cikin tunani na hango rashin yi wa kai adalcin da nake ƙoƙarin yi. Sai kuma na dawo faɗin, "To ma ni ina ruwana da shi wai? Ummh!" Shiru na yi kawai ina ta bai wa kaina laifi, a kan damuwa da wanda bai dace na damu da shi ba, har bacci ya yi awon gaba da ni. A cikin baccin ma na yi ta ganin fuskar shi yana mini murmushi. 


     Safiyar Laraba na tashi cikin kuzari da ƙarfin jiki, saboda magungunan da na sha sun taimaka mini wurin rage mini ciwon da nake yi. Sannan a gefe ɗaya kewar ofishina da ɗokin ganin MD ya saka ni gaba, saboda ina ji a raina tamkar wannan ne karo na farko da zan fara zuwa wurin aiki. 

      Kwalliya na yi sosai cikin shiga mai fisgar zuciya, sannan na feshe jikina da turaruka masu ƙamshin daɗi. Jakata na saƙala a kafaɗa, sannan na saka yarana gaba muka fito gidan suna ta yaba kyawun da na yi musu a ido. Inda Haidar yake wasar baki ya ce, 

     "Kin yi kyau sosai Mama. Ko wurin biki za ki je idan kika dawo aiki?" 

    Murmushi kawai na yi masa sannan na ce, "Kai na yi wa kwalliyar nan duka domin ka ji daɗi Yarona" Haidar ya yi tsalle yana faɗin "Gobe ki yi wata Mama, zan siyo miki yalo da kuɗin tarata". 


Ummu Salma ta maka masa harara tana faɗin, "Daina murna yaro ba don kai kaɗai aka yi ba har da mu". Yana yi mata yelum muka shiga adaidaita sahu, Iman ta riƙo hannuna tana murmushi ta ce "Kin yi kyau Mama" Cike da jin daɗi a zuciyata na rungume su duka ina faɗin, 


"Na gode yarana! Ubangiji ya yi wa rayuwarku albarka, kuma ya ƙara shirya mini ku..." Nan take muryata ta fara rawa saboda ƙwallar da ta cika idanuwana.

 

"Amin" suka ce, sannan  suka dinga yi mini surutu kala-kala, tare da ba ni labarin bulalar da za a yi wa 'yan latti a makantarsu, har muka je bakin gate ɗinsu aka ajiye su. Kuɗi na ƙara musu domin su dawo gida saman abin hawa, kada su biyo sayyada kamar yadda suke yi kullum. Godiya suka yi mini dukansu suna mini bye-bye har suka shige, sannan mai adaidaitan ya juya da ni zuwa ma'aikatarmu. Inda nake ji a raina tamkar wannan ne zuwan farko da na fara yi a wurin aikin nawa. Saboda sauyin da na samu tsakanin wancan zuwan da nake yi da wanda zan yi a yanzu. 





Shin me zai faru a gaba a kan wannan canjin na Zaituna?🥲 Ni dai ba za a ji mutuwar Sarki bakina ba🏃🏻‍♀️





D. AUTA CE✍🏼


 *ABOKIN AIKINA*



*@HADIZA D. AUTA*



*SADAUKARWA: DAUGHTER ANUP*



*LAMBA TA TAKWAS.*


    

       Har cikin harabar ma'aikatar ya shigar da ni, bayan ya ɗan tsaya na gaisa da maigadin wurin. Saboda zaman shi dattijo kuma yarena waton Hausa Fulani, hakan ya sa a duk lokacin da ya gan ni yake ba ni girma sosai ni ma ina ganin mutuncin shi a idona.

     Mai adaidaita na biya kuɗin shi sannan na rataya jakata a kafaɗa, taku na fara yi cikin taƙama irin wanda nake jin sauyin tafiyar a jikina.

     Gaisawa na fara yi da mutane kamar yadda na saba cikin sakin fuska da babu yabo balle fallasa. Kai-tsaye ofishina na nufa ina baza ƙamshin da ya janyo mini kallo a wurin mutane. Domin ina hankalce da ɗaiɗaikun da suke bi na da kallo ta gefen idona. Murmushi na yi mai bayyana jerarrun haƙorana farare tas da ke cikin ɗan ƙaramin bakina, saboda tsintar kaina da na yi a cikin mayalwacin farinciki.


    'Da alamu kwalliya za ta biya kuɗin sabulu'.


     Zancen da na yi a zucina kenan, bayan na buɗe ofishina na shiga. Zama na yi a kan kujera bakina ya ƙi rufuwa saboda ina ji a jikina zan yi bankwana da damuwar Mukhtar, matuƙar haƙa ta ta cim ma ruwa.

      Zamana ba da jimawa ba wani ɗaya daga cikin ma'aikatanmu ya shigo yana faɗin. Akwai waɗanda suke jiran zuwan ki tun ɗazu, amma Oga ya ce ki je yana son ganin ki yanzun nan kafin ki fara ganin su. 

     "Ok" Kawai na faɗa cikin tsare gida ya fice, saboda abu ne wanda kowa ya sani ba na sakin jiki da kowa cikin ma'aikatar idan aka cire Amina. Ita ma sai da na gama tantance halinta sannan na fara sabawa da ita a farkon zuwana. 

       Turare na fito da shi na ɗan goga a hannu sannan na shafe a jikina, nan take ƙamshin ya ƙara kama ni na nufi offis ɗin MD kai-tsaye. Zuciyata a sake kuma cike da zumuɗin yin ido biyu da shi, duk da ina ji a raina babu kyautuwa a cikin abin da nake ƙoƙarin yi. Amma na kasa hana wa zuciyata muradinta.

      

      Ƙofar na tura a hankali bakina ɗauke da siririyar sallamar da harshena ya karye a lokaci ɗaya yayin furzo ta. Kan shi a duƙe yana ta rubuce-rubuce a cikin wasu files, ya ɗago babu shiri tare da jefa idanuwan shi a kan fuskata. Kallo ya fara bi na da shi amma ban san me ya tuna ba ya ɗauke kan shi daga kaina cikin sauri,  mayar da idanuwan shi ya yi a kan files ɗin yana ci gaba da rubutun shi.  

        Shiru ya ɗan ratsa tsakani ina tsaye cikin sanyi jiki, sannan na yi ƙarfin halin furta masa, "Barka da safiya". Daga duƙen ya amsa mini da,

  "Barka dai! Ya ƙarfin jikin?" 


    Ina wasa da yatsun hannuna na ce "Alhmdulillah!" Bai sake cewa komai ba ya fara tattara files ɗin wuri ɗaya sannan ya miƙo mini, kan shi a duƙe ya ce "Akwai mutanen da suke jiran ki, file ɗinsu ne duk wanda ya bayar da kuɗin sai ki cike masa idan kin gama ki dawo mini da su". 

       Karɓa kawai na yi ina ƙoƙarin juyawa, sai dai kafin na yi wani dogon motsi na tsinkayo muryar shi cikin kunnuwana a sarƙe yana cewa, "Ki daina amfani da turare mai ƙarfi idan za ki zo offis". 

       Daga haka bai sake cewa komai ba ya janyo wasu takardun yana rubutu, nan take ƙirjina ya buga jikina ya fara rawa cikin saurin murya na ce "In Sha Allah zan kiyaye".

     Ina gama faɗar hakan na fice cikin sauri, saboda har cikin raina na ji kunyar abin kuma na ji daɗin kulawar da ya yi a kan hakan. Duk da bai yaba turaren a zahiri ba, amma Hausawa sun ce,


 'Tankawa yabawa ne'.


       Cike da tsantsar farinciki na fara aikin da ya saka ni, domin har wani ƙarfi na samu da kuzarin yin aikin cikin nishaɗi. Kuɗin haraji na shiga karɓa ina haɗa kansu bayan na cike takardun shaidar an biya.

    Ban samu kaina ba har sha biyun rana, sannan na tattara kuɗin da files ɗin na nufi ofishin shi. Sai dai ko da na shiga da sallamata a baki dole na yi turus, saboda ban hango shi a kan kujerar shi ba kamar yadda na tsammata. Nufar teburin shi na yi da nufin ajiye masa takardun da kuɗin na juya, sai ga muryar shi na ji tana tashi a cikin toilet ɗin da ke Offishin kamar yana faɗa. 

   "Wai ke Fatima har yaushe za ki yi hankali ne? Yanzu abincin da zan ci ma kin kasa tashi ki girka sannan ki zo da zancen fita? To babu inda za ki je, kuma na dawo na tarad da ba kya gidan sai kin gane kin yi wauta, mitsssss! Aikin banza kawai. Mace har ma mace amma ta kasa sanin yadda ake tattalin miji. Sai baƙin yawon masifa daga wannan biki sai wancan..."


     Da sauri na ajiye masa takardun da kuɗin na nufi hanyar ficewa offis ɗin, saboda na ji takun shi alamun zai fitowa kuma ba na so ya same ni. Har na riƙe handle ɗin ƙofar da nufin ficewa a ƙoƙarina na son arcewa kafin ya fito. Cikin sauri na juyo jikina yana rawa na yi jarumtar ɓoye tsoro kada ya bayyane a kan fuskata, saboda ba na so ya zargi na yi masa laɓe domin na ji wani abu daga cikin sirrin shi. 

     A take ya musa tunanina ta hanyar faɗar, "Karɓi waɗannan ki haɗa list ɗin wuri ɗaya. Amma ki bar su a hannunki har zuwa gobe, don na san ba lalle ne ki kammala su a yau ba".


    Karɓar takardun na yi na fice, zuciyata a cunkushe na nufi offis ɗina. Saboda muryar da na ji ya yi amfani da ita wurin yi mini maganar ƙumshe take da damuwa. Haka kawai na ji ina jin haushin matar shi a raina, domin ganin Allah ya ba ta dama amma tana wasa da ita cikin izgilanci. 

     Shiga ta offis ke da wuya na hango Amina zaune a kan kujerar baƙi ta yi tagumi. Murmushi na yi babu shiri maimakon na ji tausayin halin da na gan ta, kuma na san tana ciki. Amma sai na ji dariya ta zo mini, saboda kallon da nake yi mata har yanzu ba ta san komai a cikin ƙalubalen aure ba, idan na auna shekarun aurenta da ta sanar da ni, da shekarun aurena da kuma matsalolin da nake ciki. Waɗanda nake hangen ko rabin kwatar ba ta kai ba balle ta kamo ƙafata.


   Zama na yi tare da faɗin "Wash Allah!" Ta ɗago da kanta tana kallo na hawaye kwance a kan fuskarta. Mamaki ya so kama ni saboda tunanin me ya saka ta kuka a lokacin...

      "Ina cikin tashin hankali Zaituna. Wallahi zuciyata gaf take da bugawa matuƙar Mama ba ta canza tsarin da ta yi ba.."

 Zancen da ta tarye ni da shi kenan cikin rawar murya hawaye suna kwarara a kan fuskarta. Kafin ni ma na tari hanzarinta da cewa "Haba Amina! Har zuwa yaushe ne za ki saba wa zuciyarki shanye damuwa a kan halin Mama...?" 

      "Wannan karon daban yake da sauran abubuwan da take yi mini. Ta ya za a ce ta ɗauki kwanana ta bai wa kishiyata? Na rantse da Allah ba zan iya jurar ganin wannan kayan baƙincikin ba. Na fi so na je gidanmu da dai a ce na zuba ido Sanusi ya kwana ɗakin Sadiya".


    Ajiyar zuciya na sauke mai ƙarfi, sannan na kira sunanta cikin sanyin murya na ce "Amina! Idan na tambaye ki za ki ba ni amsa?"

"Me zai hana idan na sani?". Ta ba ni amsa a gatsali kuma ta da dawo mini da tambayar kaina. 


"Don me Mama ta nemi yi miki haka.."

"Saboda ta ƙuntata rayuwata ta ɓata mini rai. Idan ma mutuwa zan yi na je na yi ita babu ruwanta". 

 Ta ƙare maganar cikin kuka wanda ya ƙara tona asirin ƙunar da zuciyarta take yi. Gajeren murmushi na yi sannan na ce,

       "Kin san da hakan kuma kike ta wahalar da kanki a banza? A tunanina tun da har kin gano da gayya ta yi don ta ɓata miki rai. To ya dace ke ma ki ci maganin abin ki nuna mata hakan bai dame ki ba..."


      "Ta ya zan iya jure wannan cin kashin Zaituna? A gaban idona ya kwana ɗakin Sadiya kuma a ranar kwanana a ce ba zan damu ba? Wace irin juriya ce zan yi a kan dokarta? Bayan ita ta saka ƙafa ta yi fatali da faɗar Allah Manzonsa, ta halasta haram ta haramta halas. Sai dai ana so na yi juriyar zuwan mala'ikan ɗaukar rai, domin ya zo ya karɓi raina cikin gaggawa na huta da wannan rayuwar baƙincikin ba.  To ni wallahi ba zan iya ganin wannan kayan takaicin ba gidanmu zan je..." 

      

        Maganar da katse ni da ita kenan cikin matsanancin fushi na zahiri da ya tona asirin zaman shi a kan fuskarta. Da kai wa ƙololuwar ɓacin ran da ya fito har a cikin lafuzzan bakinta. A fusace ta miƙe ta ja jakarta da nufin ficewa, sanin idan ta fita a irin wannan halin da take ciki komai za ta iya aikatawa. Na yi hanzarin miƙewa na sha gabanta sannan na rufe offis ɗin da key na zare. Ƙasa ta durƙushe tana gunjin kuka mara sauti, na yi saurin isa inda take cikin tausayawa na fara rarrashinta. 

     Ganin da gaske take ba za ta iya juriya a kan shanye damuwarta ba. Na miƙe cikin tsananin ɓacin rai tare da rugume  hannuwana a ƙirji, cikin wata kausasshiyar murya na ce  "Da a ce zan iya, da na sanar da ke labarina. Wanda nake da tabbacin ya linka naki baƙinciki sau goma, wataƙila ki gano ba ke kaɗai ce igiyar aure take wahalarwa ba. Domin ina da tabbacin taki matsala tamkar shafin mai take idan kika ji tarihina".


    Sai da ta rage sautin kukanta sannan ta ce, "Kina nufin ke ɗin nan da nake gani kin taɓa shiga matsalar aure a baya kafin yanzu?"

     "Yanzu haka ina cikin matsalar, kuma har yanzu ban shaƙi iskan 'yanci ba". 


Kallon mamaki ta bi ni da shi kafin ta sake cewa, "Kina da damuwa amma ban taɓa gani a kan fuskarki ba? Kina da damuwa amma ba ki taɓa nuna alamun hakan ko a cikin furucinki ba? Kina da damuwar da ta fi tawa kuma kika iya haɗiye ta cikin cikinki, ba tare da kin yi aman jinin fitar da baƙincikinki a fili kin huta ba? Ta ya zan gamsu da hakan bayan ni na kasa shanye rabin kwatar damuwar da kika ce kina da ita? Kaico Zaituna, ni na kasa farinciki balle wanda zai linka ni fuskantar matsalar a rayuwar aure?"


    Murmushi na yi mata sannan na fara safa da marwa a tsakiyar offis ɗin, kaina a duƙe hannuwana a baya ina furzar da iska mai zafi daga bakina. Saboda tuno majaujwar tashin hankalin da ta yi ta juyawa da ni a baya har zuwa yanzu. 

    Hawayen da suka fara gangara a kan fuskata na share da gefen hannuna, sannan na yi jarumtar ba ta amsa a gajarce.

      "Ta hanyar sanar da ke labarina" 

Ban jira cewarta ba na fara jero mata  tambayoyina kamar haka;  

       "Kin taɓa kama mijinki yana hulɗa da matar aure?"

     "Mijinki ya taɓa faɗa wa duniya kin ce sai kin kashe shi?"

      "Mijinki ya taɓa damfarar Iyayenki?"

        "Mijinki ya taɓa yi wa 'yar aikinki ciki?"

       "Mijinki ya taɓa neman auren ƙawayenki na ƙud-da-ƙud waɗanda kuka tashi tun kuna ƙurciya?"

       "Mijinki ya taɓa bai wa ɗanki matsayin da ya yi kamanceceniya da zama kishiyarki?"

       "Mijinki ya taɓa sayar miki da kayan ɗaki? Ko ya taɓa satar miki kuɗi ko wani abin amfani?"

       "Mijinki ya taɓa fallasa ki a bisa ƙazafi cikin dangin shi da naki bayan 'yan'uwa da abokan arziƙi masu ganin girmanki?"

        "Mijinki ya taɓa zuwa wurin mutanen da kike jin kunya aron kuɗi ko roƙo?"

       "Mijinki ya taɓa yi miki ƙazafin kina tare da wasu mazan waje a gaban 'ya'yanki?"

       "Kin taɓa neman haƙƙinki wurin mijinki bai sauke ba?"

         "Kin taɓa shekara huɗu ba tare da mijinki ya kasance ki ba...?"


      "Dakata Zaituna. Kada ki sanar da ni cewa duk waɗannan abubuwan da ke suka faru?" Hanzarin katse ni ta yi saboda mamakin maganganun da ta ji suna fita bakina. Kafin na ba ta amsa cikin muryar kukan da ya kasa tsaya mini, saboda ta sa na fama mikin baƙinckin da ya daskare mini zuciya. 


      "Tabbas da ni waɗannan abubuwan duka suka faru, har ma da sauran wasu tambayoyin da kika katse ni ban samu sararin furzowa ba..." 

      "Innalillahi wa inna ilaihirraji'uun! Ke kam wace irin zuciya ce da ke haka mai shanye baƙƙan ciki manyan kashi kashi irin haka? Ni ko zan so na ji waɗannan abubu ɗaya bayan ɗaya, don na san tabbas akwai karatun da zan kwashe a cikin tarihin rayuwarki. Kuma zan ɗauki darussa a ciki ko don na magance matsalar da ta addabe ni. Cabɗijam! Ashe daman akwai wadda ta fi ni shiga matsala a rayuwar gidan aure?"






Akwai Amina. Domin kuwa kafin a je ko'ina ga Zaituna nan a kusa da ke🥲






D. AUTA CE✍🏼


 *ABOKIN AIKINA*



*@HADIZA D. AUTA*



*SADAUKARWA: DAUGHTER ANUP*



*LAMBA TA TARA.*


       "Tabbas! Akwai wadda ta linka ki fuskantar baƙƙan cikin aure. Kuma ba wata ba ce face ni nan Zaituna" 

       Kallon mamaki na ga ta bi ni da shi tana jinjina kai, kafin ta yi tagumi tana kallo na tamkar wata sabuwar halitta a gabanta. A hankali na tako na zo wurinta na dafa kafaɗarta fuskata ɗauke da murmushin ƙarfin hali, wanda na yi amfani da shi ne kawai domin na kore rabin damuwata, kuma na ƙarfafa mata zuciya ta zamo jaruma a fagen shanye takaici, jajirtacciya a wurin kawar da kai da hangen nesa.


      "Akwai mata da yawa waɗanda suke fuskantar matsalolin aure a wannan lokacin da muke ciki. Saboda sauyin da zamani ya zo mana da shi, da kuma tsarin yadda ake gina tubalin auren tun tushen shi. Ba tare da an yi duba da nagartar mutum ko asalin shi ba". 


     Zancen da na yi kenan a lokacin da nake duƙe wurin Amina domin na tunatar da ita mutuwar yawa kaka ce. Sannan na miƙe na nufi kujerata na zauna, idonta a kaina wanda alamu ya nuna mamakina da ke kwance a kan fuskarta.

       Daga can inda take zaune ta jefo mini tambaya cikin sanyin murya. "Ina mamakin yadda kika iya shanye waɗannan abubuwan duka a cikin zuciyarki. A rayuwata ban taɓa sanin akwai mai ƙarfin zuciya irinki ba, domin ina da yaƙinin da ni ce ke da tuni na mutu har an manta da ni. Amma ke ga ki sharr da ke ma sha Allah tamkar ba ki san wani abu damuwa ko ɓacin rai ba.."

      "Ni ma ɗin ba yin kaina ba ne daga Allah ne. Saboda na yi kuka tamkar zan ƙarar da ruwan hawayena, haka ma na shiga ƙunci da damuwa tamkar ba zan sake shaƙar iskan numfashi ba. Amma duk da hakan Allah ya inganta mini lafiya har yanzu ba a ce ina ɗauke da hawan jinin ba. Don haka ke ma ki mayar da komai ba komai ba, ki kalli komai ki kawar da kai kamar ba ki hango komai ba. Ina tabbatar miki sannu a hankali komai zai zo miki fiye da tsammanin ki. Abin da ya saka ki kuka a yau zai dawo yana ba ki dariya, abin da ya ba ki takaici zai dawo hannunki kina juya shi ta yadda kika ga dama. Amma duk wannan ba zai samu ba har sai kin cusa wa zuciyarki haƙuri, haƙurin ma na gasken gaske".


    Shiru ya ratsa tsakani kafin na ji ta sauke ajiyar zuciya cikin sanyi ta ce, "Ke mutum ce har da rabi Zaituna. Na gode wa Allah da ya kawo ki ma'aikatar nan kuma ya haɗa ni zama da ke. Saboda kina da zuciya mai kyau tare da hangen nesa. Na gode sosai Allah ya ƙara mana haƙuri gabaɗaya".


    Murmushi kawai na yi cike da jin daɗin yabon da ta yi mini, duk da wani sashe na zuciyata yana tunatar mini da ɓoyayyen laifina, tare da wannan da nake ƙoƙarin aikatawa a sirrance. 

     Agogon hannuna na duba cikin sauri na fara haɗa takardu ina sakawa jakata, saboda ganin har ƙarfe biyu ta wuce uku ta doso. Miƙewa na yi na nufi ƙofa da nufin zuwa gida, Amina ma ta tashi daga zaman dirsham ɗin da ta yi a dandamalin siminti tana gyara zaman zaninta. Ina ƙoƙarin ficewa ta yi hanzarin dafa kafaɗata ta ce "Ina sha'awar jin labarin tarihin rayuwarki. Idan babu damuwa ki ba ni lokacin da zan zo har gida, domin na ji wannan badaƙalar da kika fara yi mini tsokaci. Saboda jikina ya ba ni zan ƙaru da wasu abubuwa fiye da na yanzu".


"Idan kuma mijina bai aminta da hakan ba fa?" 

 "Sai na haƙura".

      Ta ƙare maganar cikin kwantar da kai da muryar tausayi. Murmushi a kan fuskata na ce, "Zan sanar da ke amma ba gidana ba. Saboda ba na so na yi sara da mutum sama". 

     Ita ma fuskarta ta faɗaɗa da murmushin alamun ta hasko abin da nake nufi.


     Tare muka fito inda muka tarad da mutane da yawa sun yi gida, saboda a ƙa'ida ƙarfe biyu dam muke tashi. Amma yau ga mu har ƙarfe uku saboda batutuwan da muka tattauna sun janyo lokaci ya tafi ba mu sani ba. 


    Cike da damuwa muka doshi bakin gate ɗin ma'aikatar, saboda haushin rashin ganin motar MD, wanda alamu ya nuna shi ma ya yi gida. Muna ƙoƙarin fita gate sai ga motar shi ta doso babu shiri muka yi gefe ya shige. Kamar na tsaya na yi masa sai gobe, amma na dake na fice muka ja tunga a bakin titi. Abin hawa muka samu dukanmu, ni na fara shiga tawa na zauna har muna ƙoƙarin barin wurin. Sai ga muryar Baba maigadi yana ƙwala mana kira ni da Amina, da sauri na leƙo kai bayan na dakatar da mai adaidaitan ya tsaya. Baba maigadi ya iso wurinmu da ledodi biyu a hannun shi ya miƙo mini ɗaya ya bai wa Amina ɗaya. Kafin mu tambaye shi ya riga mu da faɗar, 

     

     "Ranka ya daɗe ne ya ce na kawo muku". 


    Baki sake na kai kallona cikin ma'aikatar, sannan na dawo da kallon a kan Baba maigadin na ce, "Kuma mu ya ce a bai wa?"


   Kai-tsaye ya amsa mini da "Tabbas! Ko tantama babu Hajiya". 

    "Ka ce masa mun gode. Allah ya ƙara rufa asiri". Cewar Amina kenan cike da jin daɗin da ya bayyana kan fuskarta. 

     "Hajiya mu je kawai Allah ne ya tsaga da rabonmu". 

      Abin da ta sake faɗa mini kenan ta shige adaidaita suka wuce, ganin hakan ya sa ni ma na yi godiyar cikin sanyin jiki muka tafi. 

     

    Tafe nake cike da mamakin wannan kyauta da MD ya yi mana ni da Amina. Duk da ba wannan ne karo na farko da yake yi wa mutanen wurinmu alheri ba, amma dai ni kam na ji abin har cikin raina. 

     Ban san lokacin da muka isa unguwar ba, sai da mai adaidaitan ya tambayi wani layi zai shiga. A nan na dawo natsuwata na yi masa kwatance muka doshi ƙofar gidanmu.  

    

     Tun daga nesa na hango Mukhtar zaune a kan dakalin ƙofar gidan, tare da wata mai tallar masara bakin shi har kunne suna hira. Haushi ya turnuƙe ni cikin sauri na miƙa wa mai adaidaita kuɗin shi na ja ledata. Ban kalli inda yake ba balle na tsaya sauraron borin kunyar da yake yi. 

   "Tashi ki je malama, tun da na biya ki kuɗin masararki zaman me kike yi a nan kuma? Salon ki janyo mini zargi..." 

     Iya abin da kunnuwana suka ji kenan na shige ciki. Da gudu yarana suka tarye ni suna ihun murnar gani na, da masara a hannunsu suna ci. Ban yi mamakin ganin su da masarar ba don na san Mukhtar ne ya saya musu. 

     Zama na yi a falon ina faɗin "Wash! Allah!" Iman da Haidar suka fara yi mini sannu da zuwa cikin farinciki. Sai ga Ummu Salma da plate ɗin taliya shaƙe ta dire a kan teburin tsakiyar falon. Sannan ta ɗauko ruwa biyu a firij ta dire mini tana wasar bakin faɗin,


 "Sannu da zuwa Mama". 


    Na amsa cike da jin daɗin kulawar da yarana suke ba ni, ledar da MD ya ba mu na buɗe cikin sauri na fito da robar takeaway ɗin da ke ciki guda biyu. Na buɗe nan take ƙamshin jallof ɗin da ke ciki ya gauraye falon, sannan na buɗe ɗayar robar sai ga peppe chicken a shaƙe ya sha jar suya. 

     Murmushi na shimfiɗa a kan fuskata, cike da jin daɗin wannan kyauta ta musamman. Tire na sa Ummu Salma ta miƙo na juye jallof ɗin da naman duka, sannan na ɗebo taliyar na zuba. Na ce duk su zauna mu ci tare, murna ɗauke a kan fuskokinsu muka fara cin abincin. 

    Muna tsaka da ci Mukhtar ya shigo ya yi mana tsaye a kai yana ƙallon mu. Ni dai ƙanzil ban ce da shi ba ina ta cin abincina, saboda ban san ina jin yunwa ba har sai da na fara kai loma.  Haidar ne ya kula shi ta hanyar faɗin "Abba ka zo mu ci..." 

     "Rufa mini asiri kada a fasa mini kai Haidar. Wannan abincin ai na manyan ma'aikata ne ba irinmu ba". 

      Sarai na fahimci bugun gorar da yake yi mini, amma kallo ma bai ishe ni balle na tanka shi. Yana tsaye na gama ci na miƙe na wanko hannuna, sannan na sha ruwa tare da jan jakata na yi ɗaƙina. A jikina nake jin kallon da ya bi ni da shi, hakan ya tabbatar mini da kallon tuhuma ko zargi yake yi mini. 


    Har zan shiga toilet na fito domin na tunatar da yaran zuwa islamiya. Karaf na ji maganar Haidar yana faɗin "Abba mai masarar ta tafi ko? Har na so na je ta canza mini tawa na fasa, saboda tsoron ka yi mini faɗa tun da ka ce kada mu sake fitowa sai ta tafi..."


    "Kai Haidar! Tashi ka je ku yi shirin makaranta lokaci yana ƙurewa". Ina ƙare faɗar hakan na juya zuciyata cike da ƙuna, domin zancen shi ya hasko mini korar da ya yi musu domin ya ji daɗin hira da mai masarar. 


     Har na gama sallah ban daina jin zafin abin a raina ba, waton shi bai hangen bayan shi kullum gaba kawai yake kallo. Ba ya gudun abin kunyar da zai janyo wa 'ya'yan shi gori musamman yanzu da suka fara girma. 


  "Allah wadaran naka ya lalace!" 

  

   Abin da na faɗa kenan bayan na sauke ƙatuwar ajiyar zuciya. Ina nan zaune kan sallaya suka shigo suna yi mini sallama za su je makaranta. Na yi musu fatan dawowa lafiya tare da addu'ar tsarin da na saba yi musu idan za su fita. Ficewarsu ya sa na goge ƙwallar da ta zubo mini a gefen ido, sannan na miƙe na yi sallar Asr, saboda an fara kiran sallah a masallatan da ke cikin unguwar. 


     Wanka na yi sannan na dawo falo na zauna ina aikin takardun da MD ya ba ni, zuciyata a cunkushe da damuwar rashin sanin ciwon kai irin na Mukhtar. 

       Tunanin yi wa MD godiya ya faɗo mini a rai, na ajiye biron da ke hannuna na ɗauki wayata da ke kusa da ni. Data na buɗe na saƙuna suka gama shigowa, sannan na nemo shi aka yi dace yana online. Na tura masa saƙo kamar haka,

      "Baba Maigadi ya ba mu saƙonka, mun gode sosai Allah ya ƙara rufa asiri ya saka da alheri."


     Sai da saƙon ya tafi sannan na fara dudduba sauran saƙonnin mutane ina bayar da amsa. Karaf na ji muryar Mukhtar a tsakiyar kaina. 

       "Na san za ki yi zargin wani abu dangane da abin da kika ji Haidar ya faɗa. To wallahi ni babu komai tsakanina da mai masara. Amma fa idan kin yarda don na san halinki da mugun zargin tsiya, mutum bai isa ya yi abu ba sai kin saka mai ido".


     Ban kula shi ba balle na tanka, dannar wayata kawai nake yi ba tare da na ɗago kai ba, saboda hankalina yana kan wayar don na hango MD yana typing. Saƙon ya shigo kenan ina ƙoƙarin buɗewa, babu zato na ji Mukhtar ya fisge wayar daga hannuna. 


   Zumbur na miƙe cikin zafin nama na yi kan shi a fusace, saboda ƙoƙarin duba wayar da yake yi...





Mu haɗu a next page😛




D. AUTA CE✍🏼


 *ABOKIN AIKINA*


*@HADIZA D. AUTA*


*SADAUKARWA: DAUGHTER ANUP*


_*Ban yarda ba! Kuma ban amince a juya mini littafi ba, ko a yi amfani da shi ta kowace fuska ba tare da izini na ba. Saɓanin hakan zan ɗauki matakin gaggawa wanda babu sani balle sabo😼*_


*LAMBA TA GOMA.*


       Cikin sauri ya yi gefe wayar a hannun shi yana dubawa, haushi ya sa na bar shi da wayar na dawo na zauna ina ci gaba aikina. Sai da ya gama binciken abin da yake son gani, sannan na fara jin maganganun da suka ƙara tunzura ni daga bakin shi. 

      "Wai ke har yaushe za ki gano aure yana da muhimmanci? To wallahi a wannan karon zan ɗauki mummunan mataki a kan wannan munafukin mutumin..."

      "Kafin ka ɗauki mataki a kan shi, ka fara ɗauka a kanka domin abin kunya da Allah wadai ba halin shi ba ne shi. Don haka ka yi duk abin da ka ga za ka iya tun da shi kwando yana iya ce wa rariya na yoyo". 


     A fusace na ba shi amsa, shiru ya ratsa a tsakani ba tare da ya ce komai ba. Ban ɗago ba balle na ga yanayin shi, amma jikina ya ba ni kallo na yake. 

         "Yanzu don Allah ke ba za ki mutunta auren da ke kanki? Babu hujjar da za ki riƙa balle ki halasta tarayyar da kike yi da wannan ƙaton mutumin. To bari ki ji abin da ba ki sani ba, wallahi idan na lamunci komai ba zan yarda da irin wannan cin kashin ba. Don haka zan ɗauki mataki a wannan karon tun da ke ba ki san zurum ba..."

       "Ka riga da ka yi sake ɗan zaki ya girma, a yanzu na riga da na ƙuna ba na tarar ƙauri. Duk abin da za ka yi wallahi a jiraye nake domin babu abin da zai razana ni..."

 "Haka kika ce?"

 "Haka na faɗa!"

        Fuu! Na ji ya wuce ba tare da ya ba ni wayar ba,  na yi hanzarin ajiye rubutun na sha gaban shi cikin matsanancin fushi na ce, "Ba ni wayata!" 

"Ba zan bayar ba...!"

     Amsar da ya ba ni kenan bai gama rufe bakin shi ba, cikin azama na fara ƙwatar wayar ta ƙarfi a hannunshi. Kokawa muka fara yi da shi ina ƙoƙarin ƙwata yana hana ni, a bisa tsautsayi ya ɗaga wayar sama na yi zillo na bugo hannun shi ta suɓuce masa. Cikin zafin nama na yi ƙoƙarin cafko ta amma ban yi dacen hana ta kai wa ƙasa ba.  Kife ta faɗi na duƙa zan ɗauka ya saka ƙafa ya shura ta ta daki bango gabaɗaya ta tarwatse.

      Layina na kawai na duƙa na zare daga jikin kwankwatsattiyar wayar, sannan na juya ba tare da na ce da shi komai ba. Domin a lokacin komai zan iya yi masa ɓangaren aika-aikar da zan illata shi matuƙar na biye zuciyata, gudun aikin da-na-sani a zuci na yi jarumtar faɗar 'Innalillahi wa inn ilairraji'un' Allah ya taimaka na yi controlling temper ta cikin ɗan lokaci. 


     Takardun na kwashe na yi saurin shigewa ɗakina na rufe. Sannan na janyo sabuwar wayar da MD ya ba ni na saka layina da memoryna. Kasancewar akwai nefa a lokacin na jona caji na kwanta ina sauke numfashi a wahale, saboda yadda nake ji tamkar zuciyata za ta ɓalle ta fito a kan matsanancin bugun da take yi. 

        Tsawon lokaci ina cikin mawuyacin halin kafin zuciyar ta lafa numfashina ya daidaita. Ihun yara da bugun da ake yi wa ƙofar ɗakina hakan ya tabbatar mini da yara sun dawo. Daga nan inda nake na yi musu magana cikin ɗaga murya, 

       "Ku je ku yi shirin sallah!" 

       Shirun da na ji ya gasgata sun ji abin da na ce. Ko da aka yi kiran sallar magrib ban tashi ba har sai da aka fara tayar da Sallah. Sannan na miƙa cikin rashin kuzari na yi toilet na ɗoro arwala na yi sallah, na daɗe ina jera addu'o'i a kan Ubangiji ya kawo ƙarshen zamana da Mukhtar lafiya. Domin ba na fatar zuciya ta ɗebe ni na aikata abin da zai shafi mutuncin 'ya'yana na janyo wa Ummata da 'yan'uwana gori.


     Daren ranar ban fita falo ba, a nan na ƙarasa aikin takardun sai da goman dare ta buga, sannan na gama na fito domin na ga a wani hali yarana suke. Addu'a na tofe su da ita sannan rufo musu ƙofa ina goge ƙwallar tausayinsu da ta gangaro mini. 


    Kasancewar ba na cikin walwalar zuciya setting ɗin WhatsApp kawai na yi, sai facebook da na ɗan leƙa bayan na buɗe. Ban wani jima ba na ajiye wayar saboda komai ya gundure ni, idan aka cire MD da ke gefen zuciyata motsi kaɗan sai na tuno shi a raina.


     Da safe ma sai da na canye cikin shigar doguwar rigar atamfa ɗinkin A.shape. Na yafa mayafina mahaɗin atamfar da takalmin da suka yi shige da kalar atamfar. Na feshe jikina da turaruka ba tare da na damu da huduɓar MD ba. domin burin da nake da shi, a kan wani dalili ya yi tsanin haɗa numfashina da na shi ko da tazara ta ratsa tsakaninmu. 

     Kamar jiya har na saukar da yara makaranta ba su daina yabon kwalliyata ba. Duk da ban shafa komai a fuskata ba face powder da lips, sai ɗan kwallin da na zirara wanda sai an kula da gaske ake hango shi idona. 

         Tun a lokacin da na shiga ma'aikatar na fara cin karo da MD ya fito zai nufi motar shi. Ina hankalce da shi kallo ɗaya ya yi mini ya kawar da kai, murmushia a kan fuskata na gaishe shi ƙirjina yana bugawa. Saboda kwarjinin shi ya sa na manta da komai ta yadda ban san lokacin da na saki fuskata ba. 

       Haka na yi ta gaisawa da mutane fuska a sake, duk da kallon hadarin kajin da na ga wata ma'aikaciya tana yi mini. Ban damu ba kuma ban ji haushi ba, domin ba ta gabana tun asali balle na saka ta cikin abubuwa masu muhimmanci. Saboda tun zuwana wurin na fahimci akwai hassadata a cikin zuciyarta, sai ga shi na ji komai a bakin Amina. Ashe mijinta ne aka karɓe wa matsayi aka ba ni, asali ma aka kore shi gabaɗaya cikin ma'aikatar. Dalilin zanba zamba cikin aminci bayan ruf-da-ciki da sama-da-faɗin da yake yi wa kuɗin wurin. Wanɗanda yake wadaƙa son ran shi daga shi har matar shi wadda take matsayin mataimakiyar shi. 


     Ni da ban san lokacin da aka yi ba, amma hakan bai wanke ni daga shiga komarsu ba. Duk inda ta gan ni kallon banza ne ke raba mu, tun ina kula ta sama-sama har na tattara ta na watsar domin ba ta gabana. Surutan da take yi a kaina ma ban taɓa bi ta kai ba, domin ina ji a raina ba ta kai wadda zan ɓata lokacina a kanta ba. 


    Zama na yi a kan kujerar offis ɗina, ina dudduba aikin da na yi ina gyara inda ya dace. Kira ya shigo wayata na yi hanzarin fito da wayar a jaka babu shiri ƙirjina ya buga. Cikin sauri na ɗauka,

       "Ki kawo takardun idan kin kammala aikinsu".


     Zancen MD kenan bai ƙara da komai ba ya katse, cikin sauri na tattara takardun na yi offis ɗin shi. Da siririyar sallama na tura ƙofar na shiga, kaina a ƙasa na ajiye masa takardun zan juya. 

"Shi dai wannan turaren ba za a daina saka shi ba kenan?" 

      Maganar da ya jefo mini kenan cikin ƙasan maƙoshi, shiru kawai na yi masa ina wasa da yatsun hannuna. "A matsayinki na matar aure, bai dace kina bari wani yana shaƙar ƙamshinki ba, wanda na san kin sani ko wadda babu aure kanta ba a halasta mata shafa turare dan za ta fita ba..." 

     "Sai bayan na saka na tuna, amma in Sha Allah zan kiyaye daga wannan". 

       Na ƙare zancen cikin sanyin murya da ƙara mata zaƙi. Bai ce da ni komai ba har na kai ƙofa zan fita na tuno saƙon shi na jiya da ban ga me  ya rubuta ba. Juyowa na yi riƙe da handle ɗin ƙofar cikin ɗakiya na ce,

     "Jiya ban ga saƙon ka ba wayar ta fashe. Ina ƙara godiya Allah ya ƙara buɗi". 

     "Amin" Ita kaɗai ya faɗa ya ci gaba da aikin da yake yi, na fito zuciyata fes saboda kulawar ta shi gare ni.  Hakan ya tabbatar mini da fatsata ta fara kamo mini kifi.


     Ranar ban yi aiki da yawa ba, ina tsaka da chatting Amina ta shigo, muka gaisa fuskarta babu yabo babu fallasa domin na kasa tantance yanayinta.

     Zama ta yi tana sauke ajiyar zuciya ta ce "Jiya da tunaninki na kwana, ta yadda na matsu safiya ta waye na zo domin na ji tarihinki..." 

     "Ina Mama fatan tana lafiya?"

    Tambayar da na yi mata kenan domin na ji yadda suka ƙare da rikicin kwanan. "Ina kwana ce kawai ta haɗa mu yau. Ita ma ba ta amsa ni ba, na ƙara yi mata duk da na san ta ji ni a farko. A masifance ta katsa mini tsawa tana faɗin na bar mata ɗakinta ba ta son gani na. Da na ƙi tashi ta yi kaina da duka na fice, a bisa tsautsayi ta rufo ƙofar ɗakinta cikin fushi ta dantse mini yatsun hannu na. Na jima ina jinyarsu kafin su rage mini zugi na samu ƙarfin fitowa". 


     ""Hmmmmm! Batun kwanan fa a can ya kwana ko a wurinki?" 

     Shiru ta yi tana goge hawaye tsawon mintuna sannan ta ce, "A can ya kwana". 

      "Ki yi haƙuri komai yana da farko kuma yana da ƙarshe. In Sha Allah komai zai zamo tarihi watarana". 


     Daga ni har ita muka yi shiru, na shiga dogon tunanin cutarwar da mata suke fuskanta a gidajen aurensu. Tare da tambayar kaina 'Yaushe ne mata za su daina fuskantar ƙalubalen aure?' 

        'Babu rana' amsar da wata zuciyar ta ba ni kenan cike da tabbacin matuƙar ba a ɗinke ɓarakar ba, to ba za a taɓa daidaituwa tsakanin ma'aurata ba.

 'Ta wace hanya?'

      Tambayar da na sake yi wa kaina a zuciyata kenan, kafin Amina ta katse mini zancen zucin da nake yi, "Ina so ki sanar da ni abubuwan da kika fara faɗa mini jiya, wanda asali dalilin hakan ya sa na fito aiki yau. Domin ba na so na ƙi  zuwa na yi missing wannan babban Flight'".

'Yar dariya na yi saboda ƙarshen zancenta, shiru na yi ina nazarin ta inda zan fara ba ta labarin kaina. 


        _"Kamar yadda kika sani sunana Zaituna Aliyu, amma Aliyu Yayan mahaifina ne ba shi ne asalin wanda ya haife ni ba. Sunan mahaifina Alhaji Sani. Na samo asalin sunan tun a ranar da Baba Ali ya saka ni makaranta tare da 'ya'yan shi. "_

      _"Haifaffiyar Jahar Kebbi kuma 'yar asalin garin Fulani, waton ƙauyen Ɗakin Gari. Na taso a garin Kebbi tare da mahaifina kafin Allah ya yi masa rasuwa. Na ci gaba da zama a garin Kebbi hannun Baba Ali cikin unguwar Aleru Quarters har na kammala karatuna a matakin digiri. Inda na yi Federal staff school nursery, primary and secondary. Sannan na ci gaba da karatun jami'a a Federal University Birnin Kebbi "_

           _"Mahaifiyata 'yar asalin jahar Sokoto ce. A ƙaramar hukumar wamakko lokal government. Jefi-jefi ina kai mata ziyara a duk lokacin da na samu sarari, sai dai ba na daɗewa idan ba babban hutu aka samu a makaranta ba."_

        _"A irin wannan ziyarar da nake kai wa Ummata a garin Sokoto na haɗu da Mukhtar har Allah ya ƙaddara aure tsakanina da shi. Sai dai kafin auren ya tabbata sai da aka yi ɗan ƙaramin gumurzu."_




Ni ma dai a matse nake da na ji tarihin aurenki da Mukhtar da wannan gumurzun😅




D. AUTA CE✍🏼


*ABOKIN AIKINA*


*@HADIZA D. AUTA*


*SADAUKARWA: DAUGHTER ANUP*


_*Ban yarda ba, ban amince a juya mini littafi, ko a yi amfani da shi ta kowace fuska ba tare da izinina ba. Saɓanin haka zan ɗauki matakin gaggawa wanda babu sani balle sabo😼*_



*LAMBA SHA ƊAYA.*


         _A ranar da na fara haɗuwa da shi, ina kan hanyar zuwa Bafarawa estate na fito Line G. Inda na kai wa wata ƙawar mahaifiyata ziyara a bisa umurnin ta. Domin ɓeran masallaci ce ni babu inda nake zuwa kullum ina gida, wannan fitar ma ta matsa ne sai na je na gayar da danginta da ke Dunguza, saboda babu tazara tsakanin su da Line G . Kullum suna ƙorafin ba ta bari na yi zumunci, idan na zo har na koma ba su sani ba. Su yi ta mita bayan sun juye laifin da nufin ita ce ba ta so na yi zumunci da su._

        _Kasancewar ba wata tazara ce mai yawa ba, na zaɓi komawa ƙasa domin na miƙa ƙafafuwana. Na fito Line G. Kenan daidai polo na ji magana a bayana, cikin sauri na waiga na yi tolazi da fuskar shi ɗauke da murmushi. Amma tun daga kallo ɗayan da na yi masa ban sake bi ta kan shi ba, tafiya nake yi yana bi na a baya yana faɗin,"_

       "Don Allah ki tsaya ki saurare ni, unguwarku kawai nake so ki sanar da ni sai lambar wayarki".

         _Na ci gaba da tafiyata ban tsaya ba balle na tanka shi kamar yadda yake so. Tun yana yi mini magiya ina jin haushin takurar da ya yi mini har ta kai ya fara ba ni tausayi. Saboda muryar kukan da na ji ya koma yi cikin marairaitar da ya yi nasarar saka ni tsayawa na ce da shi,_

       _"Ka yi haƙuri ba na magana a kan hanya..."_


       "Lambar wayarki kawai nake so ki ba ni. Sannan ki sanar da ni a ina zan same ki?"


     _Tafiya na ci gaba da yi ya biyo ni yana ci gaba da roƙon lambata amma ban sake bi ta kan shi ba, har na isa gidansu Ummata da ke Bafarawa estate._

        _Kwana biyu tsakani ina tsaka da aiki aka aiko wani yaro ana kira na, ina gunguni haɗi da tsaki na fito. Saboda takurar da Umma ta yi mini a kan dole sai na je na ga wanda ke nema na. Da mamaki na bi shi da kallo saboda tunanin wa ya sanar da shi unguwar balle gidan da nake. Murmushi ya bi ni da shi hannun shi a aljihu ya ce,_

           "Kin yi mamakin gani na ko? To Hausawa sun ce mai son ɗan tsuntsu shi yake bin shi da jifa, shi ya sa na biyo sawunki sau da ƙafa har na ga gidan. Saboda na gani kuma na yaba da kalar tarbiyyarki. Hakan da kika ya ƙara miki matsayi a zuciyata da ƙima a cikin idanuwana. Don haka ga Muhammadu Mukhtar da fatar ya yi miki a matsayin mijin auren ki!".


     _Shiru kawai na yi domin har zucina natsuwar shi ta burge ni, sai dai a lokacin ba aure ne a gabana ba domin farkon shiga ta Jami'a kenan. Kuma ina da burin karatun shi ya sa ba na kula samari ko a Kebbi duk da takurar da suke yi mini. Don asali ma akwai wani da muke soyayya da shi sai dai Baba Ali bai yi na'am da shi ba. Hakan ya sa duk nacin da yake yi a kan ya turo Iyayen shi a tsayar da magana bai amince da hakan ba. Dalilin da ya sa na fuskanci karatun da kyau domin na samu abin da na je nema._


     _Ajiyar zuciya na sauke sannan na ce,_ "Ka yi haƙuri da abin da na yi, saboda ba na tsayawa magana a titi. Musamman irin Polo club da ta zamo mahaɗar kasuwanci da dandazon mutane..."

       "Hakan ma ya tabbatar mini na yi zaɓen matar aure a inda ya dace. Amsar ki kawai nake buƙata yanzu domin ita ce abu ma fi muhimmanci a wurina". 


     _Shiru muka yi daga ni har shi ina wasa da gefen hijabina amma jikina a mace saboda daburcewar da na yi na rasa me zan ce. Ga kuma jikina ya ba ni idon shi duka a kaina suke, na yi jarumtar ɗagowa domin na saci kallon shi. Caraf muka haɗa idanuwa na yi saurin janye nawa ina masa kallon gefen ido, amma shi kafe ni ya yi da kallo ko ƙyaftawa ba ya yi. Na kawar da kaina gefe tare da rungume hannu a ƙirji na ce,_ 

      "Ka ba ni lokaci zan sanar da kai idan na gama shawara". 

       Shiru ya yi na ɗan lokaci sannan cikin sanyin murya ya ce, "Kamar zuwa yaushe za ki gama shawarar?"

"Sati ɗaya"

Na ba shi amsa ina ɗan murmushi, ya maraice murya yana faɗin "Kafin lokacin na zama gawa ai". 


     _Dariya ta suɓuce minu saboda sosai zancen shi ya ba ni dariya, domin yanayin da ya yi maganar yana karye wuya tamkar yaron da aka ƙwace wa alawa yana tsaka da jin zaƙinta._

      "Kwana uku ai ya yi ko?"


"Kwana ɗaya tak zan iya juriya, ko shi zan kasance cikin wasiwasi da ƙididdigar lokaci. Don haka ki taimake ni ki sanar da ni yanzun nan ko don na fita fargabar da nake ciki..."

     "Ka kwantar da hankalinka in Sha Allah alheri ne". 


_Daga haka ya ci gaba da ja na da hira har duhun magrib ya kawo jiki. Sallama muka yi da shi bayan na ba shi lambar wayata, domin ya kira ya ji amsar shi gare ni._


***

      _Abu kamar wasa soyayya mai ƙarfi ta shiga tsakanina da Mukhtar. Saboda ƙarfin da Umma take ƙara wa abin a ƙoƙarinta na son na yi aure Sokoto ko don na dawo kusa da ita. Amma Baba Ali bai karɓi abin kamar yadda Umma ta ɗauke shi da muhimmanci ba. 

Familyn su Mukhtar sananne a cikin garin Sokoto, shi ya sa ba a sha wuya ba yayin binciken asalin shi, wane ne shi a idon mutane._


      _An ɗauki lokaci muna soyayya da Mukhtar, kuma Baba Ali bai hana shi zuwa wurina ba kamar yadda ya yi mini iyaka da Jafar. Saboda ya nuna ƙarara ba zai ba shi ni ba, saboda asalin tushen shi Rundawa ne su. Kuma a cewar shi abin kunya ne da Allah-wadai ga Bafulatanin da ya haɗa zuri'ar shi da masu Fawa. Duk da wasu daga cikin 'yan'uwanmu sun tunatar da shi Allah bai haramta ba, amma ko kaɗan bai yi amanna da hakan ba. A ƙarshe ma fitowa ya yi a fili ya sanar shi ya yi mini miji ya yi haƙuri._

     _Sosai na ji tausayin Jafar saboda na san kalar son da yake yi mini marar algus. Duk da a lokacin ni kaina zuciyata ta fi karkata da son Mukhtar fiye da shi. Dalilin hakan na tattara shi gabaɗaya na ajiye gefe, na bai wa Mukhtar matsayi mai girma a raina. Bayan lokacina da na sadaukar masa, amma ban bari ƙaunar da nake yi masa ta shafi karatuna ba. Kasancewar doka ce ta musamman Baba Ali ya gindaya mini, duba da yadda na yi nisan kiwon da ba na jin kira a kan soyayyar Mukhtar._


***

    _Zancen aure na da Mukhtar ya kankama har an kawo sadakina. Domin ƙa'ida ce a wurin Baba Ali ba ya bari a yi wa 'ya'yan shi lefe, duk da yake ɗan boko kayan fitar biki kawai yake ɗora wa wanda zai auri 'yar shi. Saboda ba a kaina aka fara ba shi ya sa ban wani damu ba. Amma Ummata ta ji haushin hakan kasancewar ni kaɗai ce gare ta har lokacin. Duk da ta yi aure biyu bayan mutuwar Babana amma babu inda ta haifu._

 _Mukhtar ya nuna mini jin haushin shi sosai dangane da soke lefen da Baba Ali ya yi. Domin ya sanar da ni har ya gama haɗa komai lokacin kawo mini kawai ya rage a saka, amma hakan ba zai hana shi ajiye mini ba idan na zo sai ya ba ni. Na yi farinciki sosai da maganar ta shi, kuma zuciyata ta ƙara tabbatar mini ƙololuwar ƙaunar da yake yi mini. Ummata ma ta ji daɗi a lokacin da ta ji labarin lefe na zai tarbe ni a gidan Mukhtar._


    _Ba a yi bikin ba sai da na kammala digirina, amma tun a lokacin ya nuna mini ba zai bari na yi aiki ba. Kasancewar ina son shi ban kalli hakan a matsayin wani abu ba. Baba Ali ma da ya yi masa zancen aikin ni na ba shi shawarar ya ce masa ya amince. Saboda gudun matsala ta biyo baya ga shi a lokacin ba zan iya juriyar rashin shi ba. Kuma hakan ta kasance a lokacin da ya kira shi takanas domin su yi magana a kan aikin nawa. Baba Ali ya ji daɗin hakan kuma ya ƙara nuna farincikin shi a kan halin yakamatan da ya hango ga Mukhtar._


      _Sadaki sai kayan fitar biki kala biyar Mukhtar ya gabatar a yayin neman aurena. Aka yi bikinmu cikin mutunta juna aka kai ni gidan su Mukhtar da ke unguwar Sokoto Silma. 'Yan'uwan shi da abokan arziƙi duk wanda ya gan ni sai ya ce ma sha Allah, saboda kyakkyawar halittar da Allah ya mallaka mini. Kasancewa ta farar bafulatana mai dirarren jiki da yalwar faffaɗan ƙugu ga cikar ƙirji._ 

    

***

_Daren ranar babu komai da ya shiga tsakanina da shi, kasancewar wasu daga cikin ƙawayena da danginmu na Kebbi a nan suka kwana. Sai ta ta biyu ya karɓi budurcina ba tare da na san me ya faru a lokacin ba. Domin har yanzu da nake bayar da labari ba zan iya kawo me ya faru a darena na farko da Mukhtar ba. Da asuba na farka na tsinci kaina cikin sabon sauyi, tuna abin da ya faru ni da ni kafin ya shiga jikina. Ya sa na rufe fuskata cike da jin kunyar kaina a cikin idanuwana. Na miƙe ban gan shi a ɗakin ba na yi toilet ɗinmu da ke cikin ɗakin, tsarkake jikina na yi sannan na yi wankan tsarki na fito. Sallaya na shimfiɗa na yi sallah na yi addu'o'in zaman lafiya ni da angona Mukhtar. Sannan na yi karatun Qur'ani da na gama na yi azkar ɗina kamar yadda na saba. Domin gidan Baba Ali ba a wasa da sallah sosai ake riƙo da addinin Islama. Mun samu ilimin muhammadiyya daidai gwargwado, mun yi saukar Qur'ani kuma mun haddace littafai da dama._ 


     _Rayuwar amarcina da Mukhtar gwanin ban daɗi, duk da ina shan mamakin yadda ba ya barin kuɗi a hannuna. Duk abin da aka ba ni shi yake karɓewa, kuma ba na jin ko ɗar haka zan miƙa masa. Saboda ina tunani tara mini yake yi gudun a sace, duba da yadda gidan yake cika da mutane koyaushe ana zaryar zuwa ganin amarya da muhallinta. Domin babu abin da ba a yi mini na 'ya'yan gata ba, kayan ɗakina ma abin kallo ne bayan ƙattin kujeruna da suka canye filin falon. Bayan firij da sabuwar telar da aka haɗo ni da ita, domin na nemi na kaina kafin na fara aiki._

   _Har a raina ina so na yi alheri ko da kuɗin abin hawa ne idan dangin Ummata suka zo wurina, amma babu ko ficika a hannuna. Sai idan an yi katari yana gidan na tambaye shi ya ba ni na ba su._


      _Ashanar da nake tsinta a cikin ɗakina ko falo lokaci bayan lokaci, ita ce abu na farko da ya fara ɗaure mini kai a gidan Mukhtar. Tun ba na kula har na fara tambayar shi ko shi yake ajiye ta, amma ya nuna mini shi ma bai san da ita ba. Cikin tsoro nake tofe ashanar da addu'a sannan na ɗauke ta na kai na ajiye, abin mamaki kuma sai na nemi ashanar inda na ajiye na rasa. Idan na tambaye shi shi ya ɗauka ya ce da ni a'a, tun ina bi ta kai har na watsar ina ci gaba da addu'o'in tsari saboda ina da tsoro sosai._


    _Matsala ta farko da na fara cin karo da ita a wurin Mukhtar ita ce rashin tashi sallar asuba. Ba ya yin salla sai ya yi wanka idan zai fita wurin aiki, wani lokaci har ƙarfe takwas da rabi yana kai wa bai yi sallar asuba ba. Abin ya fara damuna na fara yi masa ƙorafi a kan hakan, saboda duk na tashi sallar asuba sai na tayar da shi amma ya ƙi tashi. Wani lokaci ma tsaki yake yi ya juya kwanciyar shi ba tare da ya tashi ba._

       _Tun yana jin haushin takurar da nake yi masa har ya fara tashi yana yi ba don yana so ba, don wani lokaci ma har ya tafi wurin aikin shi yana fushi ba ya sake mini fuska. Abin yana ba ni mamaki sosai duba da masallacin da ke ƙofar gidansu, wanda kira da Sallar shi duka ina ji tar-tar har cikin ɗakina._


  ***

_Watana ɗaya da sati biyu gidan Ummata da matar Yayanta suka zo ganin ɗakina. Saboda tsabar murnar ganin su bakina har kunnena, na tarye su da abin da nake da shi sannan na kira shi na sanar da shi zuwan su. Mintuna a tsakani ya zo da kayan marmari da jiƙa maƙoshi, na saka musu a tire na ajiye gabansu suna gaisawa da shi. Kan shi a duƙe cikin tsantsar ladabi har suka gama ya fice, na gabatar musu da abin taɓa bakin muka fara hira. Matar Kawuna ta shiga binciken zamanmu a fakaice na sanar da su komai lafiya, domin su tabbatar da abin da suka ce sun ji a bakin mutane. Dangane da zaman lafiyar da ke tsakanina da Mukhtar. Domin duk wanda ya zo ba ya gani na cikin baƙar fuska balle rashin walwala, hakan ne yake nuna zaman lafiya da jin daɗin aurena a zahiri._ 

       "Zaituna ya zancen lefenki! Mun yi ta jira mu ji kin kira mu zo mu gani amma har yanzu babu labari. Ko dai ya ba ki mu ne ba ki faɗa ma ba?" 

      _Maganar Inna Kulu kenan domin ta ji ba'asi a kan lefen da ni ma nake bitar zancen shi cikin raina koyaushe. Domin na kasa yi wa Mukhtar tuni a kan lefen, saboda ba na so ya ga na cika zalama. Shi ya sa na dakata domin na ga zurfin gudun ruwan shi. Tambayar da Inna Kulu ta yi ta fama mini damuwar abin a raina, amma na bagayar da faɗar,_

        "Ko jiya mun yi zancen ya ce na ƙara haƙuri kwanan nan Iyayen shi za su kawo mini".

      "Ma Sha Allah! To Ubangiji ya ƙara muku zaman lafiya da fahimtar juna. Idan suka kawo ki  sanar da mu cikin lokaci domin a san me za a bayar tukuici". 


_Dariyar yaƙe kawai na yi tare da ɗaga kai, cike da fargaban kada Mukhtar ya sa na ji kunya a kan ƙaryar da na yi musu, domin na ƙare masa martabar shi a idanuwansu. Lokacin da za su tafi na kira shi ya ba ni ɗari biyar na ba su, shi kuma ya ba su dubu biyu suka ce ba za su karɓa ba. Da ƙyar na matsa suka karɓa ko shi sai da ya fice sannan suka karɓa a hannuna._ 


      _Da dare lokacin da muka kwanta bacci yana wasa da jikina nake yi masa tambaya a kan lefen, nesa da ni ya koma ya juya mini baya bai ce da ni komai ba. Shiru ya ratsa tsakani sai tashin minsharin shi na ji alamun ya yi bacci. Na ɗauki lokaci ina tunanin abin da ya sa ya yi mini haka daga tambaya, ban san lokacin da bacci ya yi awon gaba da ni ba._

     



   Hmmmm! Labari ya soma😅




D. AUTA CE✍🏼


*ABOKIN AIKINA*



*@HADIZA D. AUTA*



*SADAUKARWA: DAUGHTER ANUP*



_*Littafina free ne ban yarda a sayar da shi ba, ko a juya shi ta wani ɓangare ba tare da izina na ba😒*_



*LAMBA SHA BIYU.*


          _Da safe ma haka muka tashi yana haɗe fuska, shirin fita ofis ya yi yana ƙoƙarin ficewa na sha gaban shi tare da riƙo hannun shi. Cikin damuwar da ta bayyana kanta a saman fuskata na ce da shi,_

          "Wai me hakan yake nufi ne? Ban san me na yi maka ba jiya daga magana ka yi fushi da ni. Yanzu ma ga shi kana ƙoƙarin ficewa babu walwala. Don haka don Allah ka yi haƙuri idan har akwai abin da na yi maka ban sani ba"

       _Bai ce da ni komai ba, ya zare hannuna daga riƙon da na yi masa ya fice. Zama na yi cikin sanyin jiki tare da yin tagumi hannu biyu ina tunani, da zancen zucin da na shiga yi ni kaɗai ina bai wa kaina amsa. Domin jikina ya ba ni kamar akwai wata matsala dangane da lefen, shi ya sa ba ya son maganar kuma ba ya son tattauna maganar da ni. Ajiyar zuciya na sauke tare da cin alwashi a raina, ba zan sake yi masa maganar lefen ba._

_Domin matuƙar tayar da zancen zai kawo mana rashin jituwa to babu amfanin dawo da hannun agogo baya.Tun daga lokacin ban sake yi masa maganar ba, shi ma bai ce da ni komai a kan hakan ba. Ummata ma tun tana tambaya ta har ta daina, wataƙila kame-kamen da nake yi wurin kare Mukhtar, ya sa ta gano abin da nake ƙoƙarin ɓoye mata._


      _Wata uku da aurenmu na samu ciki, wanda ni ban ma san da shi ba, har sai da Mamar shi ta turo mini abokiyar zamanta tana tambayar, yaushe rabon da na ga al'adata. Shiru kawai na yi ina tunani kafin na yi mata bayanin wata ɗaya ne kawai ban gani ba. Farinciki kwance a kan fuskarta ta fice, na bi ta da kallon mamaki domin kaina ya ƙulle da tambayar. Saboda na manta shaf da wani zancen ciki."

       _A lokacin da Mukhtar ya dawo gidan da yamma, na fahimci kamar yana cikin damuwa duba da yadda ya yi zaune shiru yana tunani. Domin ko abincin da na kawo masa bai ci ba sai cizon haƙoran shi yake yi. Zama na yi kusa da shi cikin kulawa na ce da shi,_

       "Fatan dai lafiya?"

_Shiru ya yi mini ba tare da ya ce da ni komai ba, ya duƙar da kan shi ƙasa yana kallon ledar da ke malale cikin falon nawa. Ni ma ganin haka ban sake cewa da shi komai ba na yi shiru ina tunanin wa ya taɓo shi._


       "Yanzu ke kin shirya haihuwa a wannan lokacin da muke ciki?"

     

      _Tambayar da ya jefo mini kenan cikin kaushin muryar da ta tona asirin ɓacin ran da yake ciki. Mamaki fal raina na bi shi da kallo cike da rashin fahimtar inda ya dosa._ 


   "Haihuwa ai ba a shirya mata, domin idan lokacin yin ta ya zo ko ana so ko ba a so sai an..." Zancena kenan wanda bai bari na dire ba ya katse ni da cewa, 

      "Dakata Malama! Ba wa'azi na ce ki yi mini ba! Kawai amsa nake so ki ba ni."


     "Idan har amsata kake son ji a nan, to ni ban da zaɓi ko jayayya da hukuncin Allah. Ko yanzu na samu ciki zan yi godiya ga Ubangiji, idan kuma ban samu ba zan jira lokacin da zai zo, ai abin farinciki ne gare mu duka." _Amsar da na ba shi kenan cikin ɓacin rai, domin na fara fuskantar abin da yake nufi da tambayar, wanda nake ji a raina ba zan lamunci hakan ba._


    "To cikin ya zo, kuma ya ba ki ki yi ta farinciki."


     _Yana gama faɗar maganar ya miƙe fuu ya fice falon, tare da shura takalmin shi ya bar gidan. Idanuwana a kan kulolin abincin da na kawo masa bai taɓa ba, haka kawai na ji hawaye yana bin kumatuna ba tare da na san lokacin da ya fito ba. Bayana na jingina da kujerar da nake zaune, kaina a sama ina tunanin daman haka auren yake. Domin zuwa lokacin na fara fahimtar farincikin da ke cikin aure kaɗan ne, saboda damuwar da na fuskanta a cikin shi ta fi jin daɗin shi yawa._


     _Tun daga wannan maganar ya shiga fushi da ni tsawon kwanaki. Domin bayan abincin da ya daina ci har da ƙaurace mini ya yi a shimfiɗa. Amma damuwar rashin cin abincin da ya haifar wa zuciya, ya fi na haɗa shimfiɗar yawa. Saboda ko kaɗan wannan lamarin bai dame ni ba a lokacin, asali ma ji nake yi kamar an takura ni a duk lokacin da ya nemi haƙƙin shi wurina. Sai dai ba na musa masa balle na yi ƙorafin da zai gano ba na maraba da shi. Mun ja lokaci kafin ya saki fushin mu dawo kamar yadda muke, amma ko kaɗan ba ya zancen cikin. Ni ma ba na yi masa don na gama gano inda ya dosa._


     _Na fara fuskantar matsalolin cikin tsakanin ƙyanƙyami da aman da nake sha, a wasu lokutan da idan na ci wani abu zuciyata ta kasa kwanciya. Alhmdulillah! Mahaifiyar shi da 'yan gidansu suna ba ni kulawa, domin duk abin da nake so ko ban nema ba za su kawo mini na ci ko na sha. Ɓangaren shi ne kawai babu gamsasshiyar kulawa, musamman irin wadda masu ciki suke buƙata a yayin laulayi. Duk da ina jin haushin ko-in-kular da yake yi wa cikin, amma ba na nuna masa saboda ko kaɗan ba na son abin da zai haɗa mu rikici._


    _Cikina yana wata huɗu ya yi bulaguro zuwa Abuja, ya bar ni daga ni sai cikina sai Mahaifiyar shi da dangin shi. Waɗanda suke faɗi-tashi a kaina domin su ɗebe mini kewar shi, kuma su faranta mini. Takanas Yayar shi ta kawo mini babbar 'yarta domin ta taya ni zama har ya dawo. Duk da wani lokaci a cikin gidansu nake wuni sai dare ya yi na dawo gidan na kwanta._ 

      _Sai da ya shafe sati biyu har da kwanaki sannan ya dawo. Duk da ina jin haushin daɗewar da ya yi, saboda babu wani uzurin dolen da ya kai shi, amma hakan bai hana ni nuna masa farincikin dawowar shi ba. A daren ranar ya kashe ƙwalamar shi a kaina, amma ni ya janyo mini amaye-amaye a tsakiyar daren zuwa safiya. Saboda turaren jikin shi kwata-kwata bai yi mini daɗi ba, haka ma warin tabar da na ji bakin shi yana yi ya saka ni aman dole. Sai dai tun da ya yi mini sannu sau ɗaya ya juya kwanciyar shi yana ta minshari, jiki na ja na yi falo. A kan kujera na kwana a ranar ina ta tofar da yawu saboda tashin zuciyar da nake ji a duk lokacin da na tuna da warin tabar._

      _A rayuwata na tsani taba, domin ko warinta na ji sai kaina ya juya. Dalilin hakan duk mutumin da na gani yana shan taba har raina nake jin ƙyamar shi, kuma ba na zuwa kusa da shi balle warin ya dame ni. Kwana na yi ina juyi da tunanin ina Mukhtar ya haɗu da taba har ya sha, saboda tun da nake da shi ban taɓa sanin yana shan taba ba balle na gani. Hakan ya sa na shiga kokwanto a kan ita ce ko dai ni ce kawai na ji kamar ita._

     _A lokacin mun cinye abincin gara har mun fara aune, dalilin haka na fara shiga wata sabuwar matsala. Duba da yadda na saba dafa abinci wadatacce na kai gidansu, bayan wanda 'yan'uwan shi suke shigowa su ci ko kuma su tafi da shi. Ga shi idan ma na dafa ni ba na iya cin nawa sai na gidansu idan an ba ni. Haka zan dafa iya konon da ya kawo, idan na cire masa na shi sai na juye musu saura a kula na kai musu. Hakan ya janyo suka fara haure mini kai, tunanin su ni ce kawai na tsiro da abin don ba na son ba su._

      _Saboda ba su san daga shi ne ba, idan ya shigo da konon shinkafar ya ga da mutane a gidan sai ya je Kitchen ko wani wuri ya ɓoye ta. Sai dai ya kira ni gefe ya sanar da ni ga inda ya ajiye idan na tashi dafawa._

      _Sannu a hankali suka canza mini gabaɗaya, abincin da nake kai musu ma suka daina karɓa, ni ma wanda suke ba ni suka daina aiko mini. Na shiga damuwa da neman dalilin sauyin su, na samu amsar a bakin 'yar Yayar shi wadda ta yi taya ni bacci. A lokacin da ta ga na shiga damuwa, a kan na ba ta abincin ta kai musu suka dawo mini da kayana._


      "Wallahi Aunty dama kin daina ba su, don na ji suna faɗar tun da ba ki yi niyyar ba su ba gara su hutar da ke. Domin wai a lokacin da kike son ba su sai kin cika kula ki kai musu, kuma duk wanda ya shigo kina ba shi saɓanin yanzu da kika daina."


"Ikon Allah!"


     _Ita ce kalmar da ta fito bakina ban shirya ba, saboda mamakin zancen da kuma rashin adalcin da suke ƙoƙarin yi mini. Sai da na sauke ajiyar zuciya sannan na ce,_

      "To wallahi Sajida ba daga ni ba ne. Shi yake siyo shinkafar kaɗan shi ya sa nake ba su kaɗan. Amma da a ce zai siyo wadatacciya zan ba su kamar yadda na saba, wataƙila ma a fi haka musamman yanzu da ba komai nake iya ci ba." Na ƙare maganar cikin damuwar da ta bayyana kan fuskata.


"Ki ƙyale su Aunty kowa ya yi nagari don kan shi."


   _Amsar da ta ba ni kenan a ƙoƙarin ta na kwantar mini da hankali, kuma sosai ta shiga jikina. Saboda zallar gaskiyar da ke ciki tare da jin daɗin fahimtar da ta yi mini._

      _Da ya dawo ban ɓoye masa komai ba na sanar da shi, saboda ya yi wa abin tufƙar hanci ta hanyar sauya awon da yake yi domin a samu zaman lafiya. Amma fitittike wa ya yi ya shafa wa idonsa kwalli, a kan cewa; konon shinkafar shi ne daidai ƙarfin shi. Na yi ta so na nuna masa illar ƙaramin awon da matsalolin da zai haifar mana a nan gaba, amma ya nuna mini ya fi ni sanin komai da tsarin rayuwa. Dole na ƙyale shi a yadda yake so don ba ni da ikon saka shi dole, musamman da na ga ya fi ni son dangin shi amma bai ji kunyar yin abin da yake so ba._ 

       

     _Haka muka ci gaba da tafiya babu jituwa tsakanina da mahaifiyar shi da ƙannen shi, har zuwa lokacin da cikina ya yi wata tara haihuwa yau ko gobe. Wanda a lokacin ya karta mini wani gagarumin laifin da ya so katse igiyoyin au..._


      Zuuuu! Shi ne sautin virbration kiran da ke fitowa a cikin wayata saboda tana silent. Wanda ya dawo da mu daga duniyar waiwayen bayan da muka lula daga ni har Amina, wadda ta yi luf tana sauraro na ko motsin kirki ta kasa yi. 

      Da hanzari na ɗauki wayar saboda ganin sunan Baba Ali ɓaro-ɓaro a jikin fuskar wayar. Gaishe shi na fara yi cikin mutuwar jiki da sanyin murya, bayan fargaban da nake ciki a kan kiran na shi. Wanda ya haifar mini da bugun zuciya da sauri da sauri, kafin na fara jin maƙasudin kiran cikin faɗa da ɗaga murya. 

      

       "Mijinki ya kawo ƙarar ki wurina, a kan abubuwan da kike yi a wurin aiki. Waɗanda bai kamata gare ki ba, a matsayinki na matar au..."

       "Wallahi Baba ƙazafin da ya saba ne kawai babu gaskiya a ciki. Burin shi kawai na daina aikin nan bayan kuma shi ma  yana rufa masa asi..." 

      Amsar da na ba shi kenan cikin muryar kuka saboda tsabar jin haushin abin da Mukhtar yake yi mini. Shi ma ya tare hanzarina yana faɗin,

         "Ko ma dai mene ne ki ji tsoron Allah a matsayinki na matar aure. Don kin san hukuncin matar da ke cin amanar aure, don haka ki kiyaye. Allah ya ƙara miki haƙurin zama da shi tun da Habi ta zaɓar miki zaman. A tunaninta irin wannan zaman ya fi alheri da zaman ki bazawara."


      Hawaye na goge a kan fuskata sannan na ce, "Don Allah Baba ka yi haƙuri. Wallahi ba na ƙaunar Mukhtar a rayuwata kuma na tsane shi."

        "Ki yi haƙuri Allah yana tare da ke."

Daga wannan maganar da ya katse kiran, sauke wayar na yi daga kunnena ina zuƙar majinar kuka. Kayana kawai na haɗa a jaka na miƙe na fice daga offis ɗin, ba tare da na yi wa Amina sallama ba saboda ƙunar da zuciyata ke yi.






Hmmmm! ABOKIN AIKINA fa rikici ne daddale a cikin shi yasin😅




D. AUTA CE✍🏼


*ABOKIN AIKINA*



*@HADIZA D. AUTA*



*SADAUKARWA: DAUGHTER ANUP*



_*Littafina free ne ban yarda a sayar da shi ba, ko a juya shi ta wani ɓangare ba tare da izina na ba😒*_



*LAMBA SHA UKU.*


         Karaf na ci karo da mutum ba tare da na tantance wane ne ba. Amma duk da hakan ban jira komai ba na yi gaba, balle na bai wa wanda muka yi karon da shi haƙuri.

     Idona a rufe na fice ma'aikatar tamkar na kifa. Jefa ƙafafuwana kawai nake yi, a dalilin duhun baƙincikin da ya yi mini rumfar da ta lulluɓe mini zuciya.

     Ban yi tsayuwar jiran adaidaita ba na ci gaba da jefa ƙafafuwa cikin sauri, har na yi katarin ganin wata za ta wuce babu kowa a ciki na tare. Luf na yi bayan na zauna  ina sauraron waƙar da ke tashi a cikin daidaitar. Wadda nake jin ta har tsakiyar zuciyata, domin ta ƙara rura wutar tsanar Mukhtar a cikin zuciyata. Saboda duk wani  baiti da ke fita a cikin waƙar, ina alaƙanta shi da ni kuma ina ji a raina tamkar ni ce nake furzo su daga bakina zuwa kunnen Mukhtar. 

 

'Ka rusa soyayyar da zuciya ke ma.'

'Na daina ƙaunar ka zan iya rantse ma.'

'Ba wata alfarmar da za na iya yai ma.'

'Ka naɗe tabarmar kunya ka je Allah ya yafe ma.'


'Maƙaryaci babu ni babu shi.'

'Tuntuni mun raba hanya da shi.'

'Ko da tsautsayi ya gifta.' 'Ni ba ni so nai gamo da shi.'

        Waɗannan baitukan ba ƙaramin tasiri suka yi wa zuciyata ba, domin sun ƙara tunzura ni na kai maƙura a kan abin da na kitsa wa zuciyata.            

      Wanda na gama amanna da cewa shi ne abin da zai kawo ƙarshen zaman yaƙin da nake yi da Mukhtar. Har aka kai ni ƙofar gidan mai adaidaitan bai canza waƙar ZO MU SASANTA ba tamkar da gayya. 


    Jikina yana rawa na biya shi kuɗin shi na nufi ƙofar gidan, ganin shi a buɗe ya tabbatar mini da su Ummu Salma suna nan. Afujajan na faɗa falon da ƙudurin na aiwatar da nufina, sai ga shi na yi turus babu shiri saboda Ummata na gani zaune a falon cikin yarana.

      Har a raina ban ji daɗin ganin ta ba, ƙarin takaicin kuma ƙofar ɗakin Mukhtar a rufe alamun bai dawo daga aiki ba. Gani na ya sa su Ummu Salma suka yo kaina suna ihun murna tare da faɗin,

 "Oyoyo Mama!" 

Fuskata a haɗe na isa tsakiyar falon na zauna babu yabo babu fallasa na gayar da ita. 

       Ba ta amsa mini ba, sai kallon da na ga tana yi mini ta gefen idona, Domin na kasa haɗa ido da ita. Don ba na so ta katse mini hanzari dangane da abin da na kitsa wa zuciyata, ko da tsiya-tsiys ko ta halin ƙaƙa. 


      Ummu Salma ta kawo mini abinci na ce ta mayar da shi sai na tashi, sannan suka yi tsakiyar gidanmu suna wasa suka bar mu mu zanta. Kasancewar ba a zuwa makarantar islamiya a ranar.

     Ganin hakan ya sa na miƙe zan shige ɗakina da niyyar na yi sallah, saboda ƙarfe biyu da rabi har gota. Umma ta yi hanzarin faɗin "Wurinki na zo Zaituna."

      Cikin dakiya na ce "Sallah zan yi lokaci ya tafi."

      "Je ki dawo ina jiran ki, duk da ban so na daɗe ba." 

     Ban iya sake cewa komai ba na shige ɗakina, a gurguje na yi sallar ba tare da na tsawaita ba. 

     Dawowa na yi na zauna kan  kujerar da muke fuskantar juna ni da Umma, Gyaran murya ta yi sannan ta kira sunana har sau uku. 

"Zaituna!"

"Zaituna!"

"Zaituna!"

      Sai da ta ɗan tsahirta sannan ta ce, "Sau nawa na kira sunanki?"

      Cikin dakiya na ce "Sau uku." 

    

      "Idan har da gaske ni ce na haife ki kuma na isa da ke, to ki daina kula wannan mutumin daga yau har zuwa abada!"

       Shiru na yi ina maimata kashedin da take ƙoƙarin yi mini da MD a zuciyata, wanda nake ji gara ta ɗiga mini ruwan dalma a jiki da ta yi mini iyaka da shi. Zuciyata a soye na goge hawayen da ke kwarara daga idona zuwa dandamalin fuskarta. 

       "Ba zan iya daina kula shi ba, duk da babu komai tsakanina da shi. Amma a matsayin shi na babba a wurin aikinmu, akwai abubuwan da za su haɗa ni magana da shi ko ba na so. Matuƙar dai ina aiki wurin ba sauya mini wani aka yi ba."

     Amsar da na ba ta kenan kafin shiru ya ratsa tsakani, tsawon mintuna ba ta ce da ni komai. Wanda ba na raba ɗaya biyu a kan maganganun da na yi ne take juyawa a ranta.     

     Kuka na shiga yi marar sauti domin a lokacin ba na iya taɓuka komai idan ba shi ba. Cikin muryar kuka na ji sautinta yana fita daga bakinta zuwa kunnena.

      

       "Na san ina tauye ki Zaituna, amma ni Allah ya sani akwai tunanin da nake yi miki daban, dangane da tarbiyyar 'ya'yanki. Domin sun kai lokacin da suka fi buƙatarki, kuma sun kai lokacin da kike cin moriyar abinki. Ba na so ki bar yaranki a gantale domin kin fi kowa sanin ubansu ba zai iya kula da su kamar yadda kike yi ba. Abu na biyu babu inda za ki je da su matuƙar kina buƙatar zama lafiya a wani gidan auren. Sannan ni ba ni da muhallin kaina balle na kwashe su na riƙe a hannuna. Kuma kin san babu kyatawa idan kika tare gidan Alhaji Ali daga ke har su, saboda ɗawainiyar kan shi ma ta ishe shi balle a ƙara masa da wata, bayan ya gama taki tun ƙurciya har girma. Saboda gidan zumu ba kasuwa ba ce balle a shiga duk lokacin da aka ga dama. Ki yi nazari da kyau zawarci a wannan lokacin da muke ciki ba abu ne mai kyau ba. Idan kika saka wa kanki haƙuri a yadda kike yanzu, a gaba za ki tsinci ribar hakan a wurin 'ya'yanki, a lokacin da ƙafafuwansu za su tsayu."


        Ruwan hawayena ya ƙara ɓallewa, domin na san gaskiya ce take faɗa mini. Amma ta kasa gano har yanzu ban mori aure ba, ban san daɗin aure ba balle more wa saduwar aure tsawon shekara goma sha biyu da na yi a gidan Mukhtar. Wanda na canye lokutan ina bautar auren kuma ta sani amma take ta kawar da kai. 

      'Shin idan ban ƙwaci wuyan hannuna na samu 'yanci a yanzu ba, yaushe ne zan taimaki kaina domin na fita daga wannan bahaguwar rayuwar aure, marar fasalin da nake ciki?'

        

     Tambayar da na jefi kaina da ita kenan kafin na yi jarumtar furta mata cewa, "Ba zan iya ci gaba da wannan zaman ba, domin Allah ma bai ce na yi irin shi ba. Asali ma ya ba ni damar na kai kotu a raba mana auren matuƙar na ji ba zan iya jurewa ba."

       "Ana barin halas ko don kunya Zaituna, idan ba ki raga wa Mukhtar saboda yana aurenki ba, za ki raga masa ko don 'ya'yan da ke tsakaninki da shi. Ki yi haƙuri ki bar wa Allah lamarinki, da yardar Ubangiji sai ya kawo miki haske a cikin rayuwarki ta nan gaba. Matuƙar kika saka dauriya kuma kika iyar da ladarki domin ki kai matakin nasararki."

      Ban ce da ita komai ba, domin na sani duk yadda zan nuna mata abin da nake nufi, ba za ta fuskance ni ba, balle ta gamsu da ra'ayina mu daidaita. 

      Nasiha ta shiga yi mini wadda fiye da rabinta a kan na ji tsoron Allah ne, sannan da ƙoƙarin gina mini katangar ƙarfen da take yi a tsakanina da MD.


     Har ta yi ta gama ban sake cewa komai ba, raka ta na yi ƙofar gida ta tafi tana goge ƙwalla tare da saka mini albarka. Dawowa na yi na zauna, zuciyata a cunkushe ina tunanin me zan yi na raba kaina da auren Mukhtar.

     "Ki gudu kawai!"

Amsar da zuciyata ta ba ni kenan, na nutsu sosai ina nazarin hanyoyin da zan bi na gudun ba tare da wani tarnaƙi ba. 

      Ajiyar zuciya na sauke saboda kai wa matsaya ɗaya a kan wannan shawarar da zuciyata ta gama ba ni. Amma hakan ba zai yiwu ba har sai ya dawo na fara ta kan shi, idan ya ƙi bin ra'ayina sai na ɗaukar wa kaina matakin gaggawar da ya fi dacewa da ni.


     Ranar bai dawo ba sai da dare ya yi sosai sawu ya ɗauke. Ƙarfe ɗaya saura na ji yana rufe gida, na miƙe zumbur tamkar wadda aka tsikari da allura. Na buɗe ɗakina na fito a daidai lokacin da ya shigo falon, hanzarin shan gaban shi na yi ban yi jinkirin komai ba na ci kwalar shi. Cikin matsanancin fushi da kai wa ƙololuwar ɓacin rai na fara faɗin,

       "Idan ka haifu cikin uwarka da ubanka ka sake ni yanzun nan!"


     Ƙwace kan shi kawai ya shiga yi yana shegen murmushin shi, wanda a koyaushe yake tura mini haushi da shi idan irin haka ta kama. "Shin ba ka ji maganata ba ne? Ka sake ni na ce! Idan har ka haifu cikin uwarka da ubanka!"

        Fisge kwalar shi kawai ya yi, sannan ya bangaje ni ya shige ɗakin shi, ba tare da ya ce da ni komai ba balle na san matsayata. Kuka na fashe da shi mai sauti tare da fasa ihu cikin ƙaraji na zube ƙasa ina turmuza tamkar ƙaramar yarinya. 


     Ban san ya aka yi ba na ji muryar su Ummu Salma a kaina, suna kuka tare da rungumata suna faɗin don Allah na yi shiru. Tausayinsu ya sa na ƙara sautin kukana maimakon na rage kamar yadda suke da muradi. 

      Mun ɗauki lokaci muna kukan daga ni har su kafin ya fito ya janye su daga jikina, suna tirjiya ya tura su ɗakinsu ya rufe ƙofar ya zare key. Ko kallo na bai yi ba ya koma ɗakin shi ya rufe tare da saka masa key a lokaci ɗaya. 

      Idona a rufe na miƙe tamkar wata zakanya na yi ɗakina, kayana na shiga haɗawa a jaka maidaidaiciya. Wadda ke ɗaukar kala biyar da wasu tarkacen da ba a rasa ba, sannan na saka abubuwan da zan buƙata dole a jakar hannuna.

     Agogon da ke manne jikin bangon ɗakina na kalla, wanda ke bugawa yana nuna ƙarfe ɗaya da minti goma sha shida na dare. Amma ban ji ko ɗar ba wurin janyo jakata na rataya ta hannun a kafaɗata na fito. Cikin ƙunar rai da bushewar zuciya na durfafi ƙofar gidanmu na buɗe, kai-tsaye na fice ina jan jakata ba tare da na ji tsoron duhun daren ba, balle abin da zai same ni.




Wayyo!😨🙆🏻‍♀️ Don Allah ku ce ta dawo🤦🏻‍♀️




D. AUTA CE✍🏼


 

  *ABOKIN AIKINA*



*@HADIZA D. AUTA*



*SADAUKARWA: DAUGHTER ANUP*



*LAMBA SHA HUƊU.*


          Tafe nake ina sharɓen kuka tare da jan jakata har na fita unguwarmu. Babu motsin komai da kowa, garin ya tsit illa karnukan da nake jin kukansu nesa da ni jefi-jefi. 

      Sai da na yi tafiya mai nisa sannan na fara jin wani ƙugi da gurnani a bayana, cikin sauri na juya tare da dakan luguden da zuciyata ke yi. Ido na zare ina ƙoƙarin  tafiya da baya-baya saboda wani Mahaukacin karen da na yi  tozali da shi yana zaro harshe. Jefar da jakar kayana na yi cikin matsanancin tsoro na zunduma da gudu. Shi ma ƙaton baƙin karen ya biyo ni aguje yana ta haushi "Wu! Wu!" Tamkar an ba shi kwangilar cinye ni da raina.

        Gudu nake yi iya ƙarfina yana bi na da ihu tamkar yana ƙoƙarin kama ɓarauniyar da ta yi gagarumar sata. Cikin sa'a na afka wani gida da na hango ƙofar shi a buɗe. Saboda duka gidajen da ke unguwar a rufe suke ruf, kuma ban yi Hausar samun wata kwana ko lungun da zan ɓoye masa ba.

        Sakata na danna wa ƙofar gidan jikina yana rawa, ga numfashina da ke ta hawa da sauka cikin sauri saboda tsabar tashin hankalin da na shiga. Haushin da karen yake yi a bakin gidan yana yagar ƙofar ya sa na ƙara ɗimaucewa. Na bazama da gudu na yi ƙofar da na hango ta miƙe, na zarce cikin gidan a miliyan ina ihun a kawo mini agaji.

       Mutanen da na gani suna fitowa daga ɗakunan gidan babu suturar kirki a jikinsu, hakan ya sa na fara rabon ido ina neman wurin wanda zan nufa da sigar taimako. Domin kuwa a kallo ɗaya na gano ba gidan mutanen kirki ba ne, duba da yadda dukansu suke tamkar tsirara kuma ba su ji nauyin fitowa a yadda suken ba.

       Kuka na fashe da shi ina ja da baya saboda mugun kallon da na ga suna bi na da shi, a ruɗe na fara faɗin, 

        "Don Allah ku yi haƙuri Wallahi kare ne ya biyo ni zai cije ni, ga shi can ma yana ƙoƙarin haurowa ta katanga domin ya illata ni."


     Kallon juna na ga suna yi kafin su fashe da dariya, wani ɗan gajeren cikinsu ya nufo ni yana wasar baki. Na fara ja da baya ina faɗin,

           "Don Allah ku yi haƙuri Wallahi ban san lokacin da na shigo gidan nan ba".


      Daga mazan har matan dariya suka fashe da ita, sannan dukansu suka zagaye ni duk da ƙoƙarin guduwar da nake yi sai da suka yi nasarar hana ni. Wata tsamurmurar yarinya ta nufo ni daga ita sai towel a jikinta, ganin yanayinta ya sa na ƙura mata kallo har ta iso gabana ta tsaya. Hijabin da ke jikina ta fara ɗagawa na yi hanzarin buge mata hannu, ta yi mini wata munafukar dariya tana faɗin, 

        "Fuskarki ta nuna za mu ci abinci da ke. Don haka ki bari mu gama tantance ki kafin mu yarda da ke, don ba na raba ɗaya biyu a kan cewa rashin gaskiya kika fito yi a cikin daren nan, da aka zo kama ki shi ne kika gudo kika zo gidan nan domin mu cece..."


      "Ba rashin gaskiya ta fito da ni daga gida ba, asali ma baƙincikin da nake ciki ne ya sa na kasa haƙuri na fito zan koma gidanmu."

        Ban yi aune ba na ji ta kai hannunta ta taɓo ƙirjina, da azama na sake buge mata hannun. Cike da jarumta na fara nuna ta da hannu cikin ƙololuwar ɓacin rai na ce, "Ban zo gidan nan don ku wulaƙanta mutuncina ba, taimako na zo ku yi mini saboda tsoron karen da ya biyo ni. Don haka ku yi haƙuri yanzu zan tafi ba sai kun nemi tozarta martabata ba."

      Ina ƙare faɗar hakan na juya da nufin raɓa waɗanda ke bayana na wuce. Caraf na ji an janyo hijabina ta baya babu shiri na juya cike da tsoron da ya cika mini zuciya, kallon mamaki da rashin mutumci na hango kwance a kan fuskokinsu, ya san natsure.  Nan take hantar cikina ta kaɗa na fara rawar murya ina faɗin, 

           "Don Allah ku yi haƙuri Wallahi mijina ne ya koro ni cikin daren nan."

       "Mu dama irinki muke nema, waɗanda ake cewa je-ki-kya-gani. Domin da kin fito mu ne za ki taras. Ummita tuɓe mana ita yanzun nan mu albarkaci daren nan da kalacinta."

        Abin da na ji ya faɗa ya sa fitsari kufce mini, jikina ya hau rawa tamkar mazari hakan ya bai wa fitsarin damar tsiyaya daga jikina yana sauka ƙasa. Ja da baya na fara yi saboda ganin wadda aka kira Ummitar tana nufo ni, waɗanda ke bayana kuma suka rirriƙe ni ta fara kiciniyar cire mini hijabi ina ƙoƙarin hana ta.  

       Mahaukacin mari na ji ya sauka kan fuskata har sai da na hango taurari, kafin na dawo cikin hayyacina na ji an fisge hijabin nawa. Abin bai tsaya iya nan ba suka fara ɗaga doguwar rigar dake jikina aka yi sama da ita za a cire mini. Hannuna na fara ƙoƙarin ƙwata da nufin na hana su tuɓe ni.

       Wani saukar wani marin na ji a gefen fuskata har saman idona. Azabar da ta ziyarce ni ta sa na fasa ƙara tare da kukan kura da niyyar ƙwatar kaina. Muka fara kokawa ni da su har suka yi nasarar raba ni da doguwar rigata, suka bar ni daga wata guntuwar vest mai kama da bra, sai dogon wandon legis da ke sanye a jikina.

         Idona a rufe na zille daga riƙon da aka yi mini na duƙe, hakan ya ba su damar rufe ni da duka. A duƙen da nake na yi sa'ar damƙo ƙasa, da hannuna biyu na kwaso na watsa musu a idanuwa. Ban yi jinkirin komai ba na nufi hanyar fita gidan da gudu suka biyo ni, cikin sa'a na zare sakatar na fice ina ta gudu. Biyo ni suka yi suna mini ihun ɓarawo har muka hau babban titi, a daidai lokacin d wata mota ta haske ni da ƙwan fitilarta mai mugun haske, wanda ya sa na ja na tsaya saboda na kasa gaba balle baya. 


    "Innalillahi wa inna ilaihirraji'un!"   Ita ce kalmar da na ji an ambata cikin kunnuwana.  Muryar da na ji ta sa na hau rarraba ido ina neman ta ina zan hango shi, domin ko a cikin mafarki na jiyo sautin ina shaidar muryar MD balle a farke. 

      Abu na ji an ɗora mini a jiki ana ƙoƙarin yi mini lulluɓi, saboda har lokacin hasken yana kan fuskata ina ƙoƙarin karewa da hannuna.  Ja na na ji an fara yi ina tirjiya tare da faɗin don Allah ku yi haƙuri, saboda ban da tabbacin masu bi na ne ko kuma MD da na ji muryar shi da ƙamshin turaren shi. 

       Lallausan hannun da na ji an riƙa ni da shi ya sa na yi ammana da shi ne kai-tsaye na bi shi. Sai da ya saka ni cikin motar ya rufe sannan ya shiga ya tayar aguje ya bar wurin. Tafiya mai nisa ya yi kafin na ji ya sauke ajiyar zuciya mai sauti, a lokacin ganina ya dawo daidai ina sharɓen hawaye tare da shesshekar kuka cikin sauti. 


    "Ina zan kai ki?"


Ita ce tambayar da ya jefo mini wadda ta zamo magana ta farko da ta shiga tsakanina da shi. Ban ce da shi komai ba ina ci gaba shesshekar kukana har sai da ya sake tambayar, sannan na yi ƙarfin halin faɗin,


      "Tasha"


      "Ba zan je tasha a yanzu ba, domin ko na je ba lalle ne a samu abin hawa ba."

         Maganar da ya yi kenan cikin matsanancin fushin da ya kausasa muryar shi. 

     "Ba ni da kowa a garin nan.. Birnin Keb...bi zan..je." Na ƙare maganar da ƙyar saboda kukan da ya ci ƙarfina. Daga haka bai sake cewa da ni komai ba har muka je wata unguwa, a lokacin da ya isa bakin wani ƙofar gida ya fara horn Maigadi ya wangale masa babbar ƙofa.

        Nan take ƙirjina ya buga, cikina ya katsa saboda tunanin da ya ɗarsu raina. A kan zancen da zuciyata take sanar da ni gidan shi ne ya kawo ni, hakan ya saka ni faɗuwar gaba tare da wani sabon tashin hankali. Saboda tuno masifar matar shi da irin kashedin da ta yi mini a kan shi.

      

    "Fito mu je!"


    Zancen da ya yi kenan sannan ya yi gaba, ni kam motsin kirki kasa yi na yi balle na samu kuzarin fita daga motar, na bi shi kamar yadda ya umurta. Tsawon minti biyar ina cikin motar ban motsa ba, cikin tashin hankalin da ya saukar mini da gumin da ya jiƙa mini fuska nan take.


    "Ki fito na ce!" 


    Maganar shi kenan da na sake ji a cikin kunnuwana cikin tsawa tare da saukar abu a jikina, hannu na saka na  ɗauki abin da ya jefo mini a jiki na shiga warware shi. Fahimtar hijabi ne ya jefo mini na saka, ya sa na yi hanzarin sakawa kafin na  fito daga motar. 

      Bayan shi na bi tamkar raƙumi da akala har muka shiga cikin gidan muka haye sama, mun wuce wasu ɗakuna sannan muka isa wani ɗakin ƙarshe ya tura ƙofar muka shiga. 

      Ƙamshin da ya daki hancina da raɓar da ɗakin ya kwasa nan take jikina ya yi sanyi ƙalau. Kujera ya nuna mini na zauna sannan ya fice mintuna goma tsakani ya dawo ɗauke da plate ɗin abinci. 

       Gabana ya ajiye sannan ya nufi firij ya ɗauko gorar ruwa da Hollandia ya sake ajiyewa a gabana. Zama ya yi nesa da ni yana haɗe fuska ya ce, 

"Ki ci abincin."

 Kai na fara girgizawa domin ba zan iya magana ba.


"Ki ci na ce!"


     Tsawar da ya katsa mini ce ta sa na yi hanzarin jawo plate ɗin na buɗe, Indomie  shaƙe a cikin plate ɗin sai dafaffen ƙwai guda biyu har an ɓare.

      Cokali mai yatsun da na gani a ciki na shiga ɗebo abincin ina kai wa bakina hawaye yana zarya a kan fuskata. Sai da na kusa cinyewa sannan na ajiye cokalin na sha ruwa, bai matsa mini a kan na sha madarar Hollandia ba. Illa kafe ni da idon da ya yi fuskarsa a haɗe wanda idon shi yake nuna mini tamkar ya rufe ni da duka.


     "Me ya fito da ke a cikin tsohon daren nan?"

       Tambayar shi kenan zuwa gare ni, ina zuƙar majinar kuka na ce, "Tafiya zan yi." 

"Zuwa ina?" 

"Kebbi."

        Shiru ya ratsa tsakani bayan na sanar da shi inda zan je, duk da ba haka ne gaskiyar abin da ke raina ba. Domin babban burina a lokacin na yi nesa da duk inda aka san ni, balle na je inda za a dawo da ni gidan Mukhtar domin na ci gaba da zaman 'ya'yan da nake yi. 


      "Me ya haɗa ki da mutanen da na ga sun biyo ki?"

         Ya sake jefo mini wata tambayar, kai-tsaye na sanar da shi duk abin da ya faru. Sai dai ban sanar da shi Ummita ta taɓa ƙirjina ba, saboda na tsani duk abin da zai zubar mini da ƙima a rayuwata.


      "Me ya sa ba ki bari da safe ki yi tafiyar ba? Yanzu da ace wani abu ya same ki a hannun waɗannan azzaluman wa gari ya waya? Ga shi kin zubar da jakunkunanki, wataƙila ma akwai abubuwa masu muhimmanci a ciki."

      Maganganun da ya faɗa kenan cikin faɗa tare da ɗaga murya, cikin tsoro na dinga kallon ƙofar ɗakin saboda tunanin yadda zan kare kaina idan matar shi ta iske ni tare da shi a ɗakin.


      "Daidai ina kika jefar da jakunkunan?" 


          Sai da na haɗiye yawun tsoro sannan na yi masa bayani, tare da tsoron kada ya ce zai koma ɗauko su wani abu ya same shi saboda ni. Bayan haka kuma ba na so ya bar ni gidan matar shi ta nemi salwantar mini da rayuwa, don na san muddin ta yi ido biyu da ni sai buzuna. 


     "Me da me ne a cikin jakar?"  

       "Credentials ɗina ne da wasu 'yan kayana, sai wayata da ATM tare da sauran wasu tarkace."

       Na ba shi amsa jikina yana rawa, kai-tsaye ya nufi hanyar fita ɗakin tare da faɗin,

 "Jira ni yanzu zan dawo."

      Zumbur na miƙe tare da rawar jiki da ta murya ina haɗiyar yawun tsoro masu wucewa muƙut a wahalce. Kuka na dawo yi masa ina faɗin, "Don Allah ka bar kayan nan kada ka koma ba sai an ɗauko ba, idan ma za ka je mu je tare dukanmu daga can ka ajiye ni wani wuri na jira asuba." 

            "Babu inda zan je da ke! Ki jira ni a nan yanzu zan dawo." 

         Yana ƙare faɗar hakan ya fice tare da rufe ni ta baya, dole na durƙushe jikin ƙofar ina wani irin kuka mai kama da na mutuwa. Saboda abubuwa sun cakuɗe mini a kwanya na rasa me zan kama na ji sanyi. 

        

       Na daɗe a cikin halin kafin na fara jiyo sautin kukan yaro wanda ya sa hantata kaɗawa, domin hakan ya tabbatar mini da dole ne matar shi ta farka duk nauyin baccin da take yi. Kuma faruwar hakan tamkar fallasa asirin rufin ɗakin da aka yi da ni ne, wanda alamu ya nuna mini kafin ya dawo ta yi watanda da naman a cikin gidan. 


     Safa da marwa na fara yi da a tsakiyar falon, hannuna a ka ina tsiyayar ruwan hawaye mara sauti. Kukan yaron na ji ya yi yawa, da muryar shi gwanin tausayi. Na nufi ƙofar ɗakin na kara kaina jikin ƙofar domin na ji ko akwai wani motsi bayan na shi. 

      Amma har ya ci kukan ya bari don kan shi  ban ji muryar kowa ba balle wani motsi. Ƙarfe biyu da rabi na dare da mininti shidda, na ji alamun takun tafiya yana kusanto ɗakin da nake, gabana ya ƙire ya faɗi dum-dum! A lokacin da na ji ana murɗa ƙofar ɗakin da nake ciki.






Shin wane ne? MD ne ko matar shi?😹





D. AUTA CE✍🏼


*ABOKIN AIKINA*



*@HADIZA D. AUTA*



*SADAUKARWA: DAUGHTER ANUP*



*LAMBA SHA BIYAR.*


            Ƙoƙarin buɗe ɗakin da na ji ana yi, hakan ya ƙara ƙarfin dakan luguden uku-uku da zuciyata ke yi. A ɗari na bazama da gudu na faɗa wata ƙofar da na gani, babu jinkiri na saka key tare da shan jinin jikina na lafe a jikin bango. Addu'a na dinga yi a zuciyata bayan na toshe bakina da nake gudun ya tona mini asiri.

        Takun tafiya na ji ana nufo bakin ƙofar toilet ɗin da na ɓuya, hankalina bai ƙara tashi ba har sai da na ji an sake taɓa handle ɗin ƙofar an murɗa. Babu shiri na darje daga tsayen da nake, saboda sulɓin tyles ɗin da ya ja ni zuwa ƙasa na yi zaman 'yan bori.

        Ƙuguna na dafe ina yarfa hannu saboda sosai na ji zafin faɗuwar. Shiru ban san sake jin motsin komai ba bayan takun tafiyar da na ji kamar an bar bakin ƙofar. Mintuna a tsakani na fara jin kukan yaron a cikin ɗakin.

     

     "Shiii!" Na ji ana faɗa wa yaron da muryar da nake da tabbacin ta MD ce, amma fargaba da tashin hankalin da nake ciki ya sa na ƙaryata hakan a zuciyata. Saboda ina gudun na fito ya zamana matar shi ce take kama da muryar shi, ko kuma a ce suna tare tsautsayi ya sa ta gan ni na janyo masa rigima daga taimako.

         

       Tsawon minti goma ina zaune inda nake ban motsa ba, har zuwa lokacin da na ji an fara ƙwanƙwasa ƙofar toilet ɗin. Sannan na tsinkayo muryar shi yana faɗin,

       "Wannan shirun na lafiya ne kike yi a cikin toilet kuwa?"

         Dafa ƙirjina na yi sannan na sauke ajiyar zuciya tare da haɗiyar yawun da suka tsaya mini a maƙoshi. A daddafe na dafa bangon na miƙe ina jan ƙafafuwana da suka yi mini nauyi. Na buɗe ƙofar cikin sauri na kawar da kaina gefe, saboda kallon da yake aiko mini fuskar shi a haɗe mai kama da tuhuma. 

      Wucewa ya yi na biyo bayan shi caraf idanuwana suka sauka a kan jakar kayana, cikin sauri na nufi jakar ina faɗin, "Yanzu sai da ka je ɗauko..."

       Kuka ya suɓuce mini wanda ya hana ni ƙarasa maganar da na yi niyya. Shiru na minti biyu sannan ya yi gyaran murya ya ce da ni,       

        "Wannan jakar kaɗai na gani, amma ban ga ƙaramar ba. Ko a can gidan da kika shiga kika jefar da ƙaramar jajar ba ki sani ba?"


        "I, a can na zubar da ita, don ko da na shiga gidan tana maƙale a kafaɗata."

       "Za ki iya gane gidan idan mun je unguwar?"


    "Zan gane"

     "Ok! Tom da safe za mu koma ki karɓo jakar."


      "Ba sai mun koma ba na yafe musu." Na yi hanzarin faɗin maganar don ba na son su yi masa rashin mutunci, domin na fahimci tsagerun mutane ne. Kuma 'yan iska ne ajin farko. 

         "Za mu koma! Idan ma sun kawo mana rashin kunya sai na haɗa su da jami'an tsaro."


    Shiru kawai na yi masa don a ɗan zaman da na yi da shi, na gano mutum ne mai magana ɗaya. Kuma duk abin da ya furta ta tabbata babu sauyi ko da bai yi wa mutum daɗi ba. Jikin jakata na rakuɓe tare da yin tagumi har zuwa lokacin da yaron ya sake motsawa yana kuka. 

       Wanda ban lura da shi a kan gado ba har sai da kukan shi ya shiga dodon kunnena. Na yi hanzarin miƙewa na riga MD ɗaukar shi, jijjiga shi na fara yi tare da bubbuga bayan shi har ya sake komawa bacci. 

       MD ya ce na kawo shi ya kai wa mai aikinsu na ce ya bar shi wurina, daga haka ya fice ɗakin bai musa ba. Na lallaɓa na ajiye shi a kan gadon, sannan na zauna ƙasa na ɗora kaina saman katifar gadon. Hannuna riƙe da hannun yaron na shiga nazarin tafiyar da zan yi idan safiya ta waye. A gefe ɗaya kuma zuciyata cike take da fargabar abin da zai faru, idan matar MD ta yi ido biyu da ni a cikin gidanta.

      Ban san lokacin da bacci ya yi awon gaba da ni ba, sai bayan na farka idona ya kai kan agogon da ke manne cikin ɗakin. Wanda nake tantama a kan gaske ne abin da na gani ko kuma daman can ba ya aiki. Domin kuwa ƙarfe bakwai saura na gani. Abin da ya ƙara ba ni mamaki kuma; yaron da nake riƙe da hannun shi ba ya kan gadon, wanda alamu ya nuna an ɗauke shi ba tare da na san an shigo ɗakin ba. 

      Zumbur na miƙe na faɗa toilet na yi wanka agurguje saboda fitsarin da ke jikina har lokacin. Na yi arwala na fito na ƙargame ɗakin da makulli, sannan na yi sallah a gaggauce cike da tsoron kada ina sallah na ji saukar duka. 

       Na shirya cikin doguwar rigar shaddar da ke cikin kayana, sannan na saka mayafi mahaɗin shaddar ba tare da na shafa ko da mai ba. Jakata na ɗauka na fito daga ɗakin babu shiri na ja baya na rakuɓe, saboda ganin wata dattijuwar mata ta nufo ni da tire a hannunta, wanda nake da tabbacin abinci ne za ta kawo mini. 

      Kallon mamaki na bi ta da shi har ta shige ɗakin, saboda ganin ta gaishe ni cikin mutunci da sakin fuska tamkar ta san ni. Yaƙe kawai na yi mata a lokacin da ta ce da ni,     

       "Hajiya ki koma ki karya kafin ki tafi. Yar laɓai ya ce idan kin gama ki same shi waje." 

        Bayan ta wuce na ja jakata ba tare da na bi ta kan abincin ba. Sauka na yi ƙasa da sauri har da sassarfa cike da burin na fita gidan ko da hankalina zai kwanta, domin na huta da fargaban da nake ciki. 


       Cikin motar na same shi yana sauraron ƙira'ar sudes daga cikin ayoyin ƙarshe na suratul Rahman. Ban jira ya ba ni umurni ba na buɗe motar na shige ina zarar ido rungume da jakar kayana. Kai-tsaye ya fice gidan ba tare da ya ce da ni komai ba ya cilla motar a kan titi. Sai da muka yi doguwar tafiya muna gaf da shiga unguwar da na baro jakar, sannan ya ce da ni, 

        "Idan mun kai gidan ki sanar da ni."

        Daga haka ya ja bakin shi ya tsuke ni ma ban ce komai ba sai kai da na ɗaga alamu 'To'. Tun daga nesa na nuna masa gidan ya ci birki a  daidai ƙofar gidan, sannan dukanmu muka fito ya ce na jira shi a nan. Cikin gidan ya ɗan tura kai tare da ɗaga murya ya fara rafka musu sallama, sannan na ga ya dawo ya jingina bayan shi jikin motar shi yana dannar waya.  

       "Ku ƙaraso za ku hango motata."


    Maganar da na ji ya faɗa kenan a cikin wayar sannan ya mayar da ita aljihu, a daidai lokacin da wani ya fito daga cikin gidan yana ƙare mana kallon sama da ƙasa. 

       Yana ƙoƙarin yin magana muka jiyo jiniyar motar 'yansanda, a ruɗe na kai kallona ga fuskar MD, cike da mamakin abin da ya sa shi kiran su tun kafin a yi musu zancen jakar. 

       Ko da na dawo da kallona a kan ƙofar gidan wayam na gani babu mutumin da ya fito gidan balle alamun shi. Yansandan suka ƙaraso wurin suka bai wa juna hannu da MD suk gaisa, sannan wani daga cikinsu ya ce da shi, 

      "Ya kuka yi da su?"


        "A fito mana da su duka idan har sun ƙi bayar da jakar da kayan cikinta a yi musu duk abin da ya dace."

      Abin da MD ya faɗa kenan fuskarsa a haɗe tare da rungume hannun shi a ƙirji yana feso iska a bakin shi. Ɗaya ɗan sandan ya fara yi musu sallama kamar yadda MD ya yi a farko. Mintuna a tsakani sai ga maza da mata suna fitowa daga cikin gidan fuskokinsu ɗauke da tsoro.

       Sai da 'yansandan suka ƙare musu kallo sannan ɗaya ya ce da su, "Ina jakar wannan yarinyar da kuka ƙwace a cikin gidanku?" Kallon juna suka fara yi kamar ba su san komai ba. 

          "A gaskiya ranku ya daɗe ba mu san komai dangane da batun jaka ba."

 Zancen wata koɗaɗɗiya kenan wadda fuskarta ta gama ƙonewa da bilicin. Maganar MD na ji a fusace cikin ɗaga murya ya ce, "A cikinsu wace ce ta zare miki hajabi?"  Idona a kan Ummita na nuna ta da hannu tare da ƙarin bayani kamar haka, 

       "Ita ce ta cire mini hijabi, wurin kiciniyar cire mini riga jakar ta faɗi a wurin, lokacin da zan fito kuma na bar ta a can, saboda gudun tsira na manta shaf ban bi ta kan jakar ba."

       "Minti biyar aka ba ki ki fito da jakar nan yanzun nan." 

          Wani daga cikin 'yan sandan ya yi maganar tare da nuna Ummita da bakin bindigar da ke hannun shi.  Ummita ta fara zarar ido tana nuna kanta cikin wayancewa da ƙoƙarin zare kai ta ce, 

        "Ni ban ɗauki jakarta ba, sai dai idan a cikinsu wani ya ɗauka ban sani..." 

       Bahagon marin da wani ɗan sanda ya kwaɗa mata, babu shi ta fasa ihu tare da komawa cikin gidan da gudu tamkar wata zararriya. Tara-tara 'yansandan suka yi da sauran maza da matan gidan suka jefa su motar shiga-ba-biya, sannan wata 'yar sandar da ke cikinsu ta faɗa gidan a sukwane.


      Minti biyar kacal ta fito riƙe da ƙugun Ummita da ke riƙe da jakata tare da wani matashi hannun shi da ya ɗaga hannun shi sama alamun miƙa wuya. Motar aka watsa su duka sannan aka ba ni jakata bayan na buɗe ta gaban kowa, kuma na tabbatar musu da komai yana ciki yadda na saka. 

       Motar 'yansandan ta fara barin ƙofar gidan tare da mutanen gidan da suka kwasa, kafin ta MD ta bar wurin tare da ni da ke baya na hakimce ina hurar hanci. Amma duk da hakan nan take gumi ya jiƙa mini fuska, zuciyata ta hau bugawa da sauri tamkar za ta fasa ƙirjina ta fito waje. 

       Saboda hango Mukhtar dumu-dumu a cikin 'yan kallon da suka zagaye mu suna rabon idon ganin ƙwam. Wanda shi ma nake da tabbacin ya gan ni a lokacin da zan shiga motar MD, na yi mamaki matuƙa da ganin shi wurin, tare da ko-in-kulan da ya yi wa ganina ba tare ya nuna ya san ni ba, balle ya ɗauki mataki a kaina ko a kan MD.


     Ban dawo natsuwata ba har sai da na ga mun shiga gidajen Sama road, mamaki ya so kashe ni saboda ganin da na yi ya doshi hanyar da za ta kai mu Bafarawa Estate. 

      'Ina zai kai ni?'

Ita ce tambayar da na yi wa kaina a zuciya, sai ga amsa tiryan-tiryan ta bayyana kanta. Domin kuwa ƙofar gidan Kawu Sale ya ci birki, gidan da Ummata take rayuwa tun da jajayen sawu har yanzu da girma ya kamata.

      "Fita ki je! Kuma ki yi mini sallama da Umma!"

      Zancen MD kenan a fusace kuma cikin ɗaga murya. Haka na fito tamkar wadda aka kama ta yi wa Sarki ƙarya. Haka na fito jiki a mace na ja jakar kayana da ta hannuna na yi cikin gidan, ba tare da na waigo ba balle na damu da ce masa na gode. 

        Saboda har raina ban ji daɗin taimakon da ya yi mini ba, tun da har  ya kawo ni gidan a maimakon tashar da nake so ya kai ni. 

       'Tukunna ma wa ya sanar da shi unguwar su Umma da gidan duka?' 

        Tsaki na ja sannan na faɗa gidan ko sallama babu na yi ɗakin Inna Kulu ina haɗe fuska. Ummata da Inna Kulun duk suna tsakar gidan amma babu wanda na yi wa magana. Saboda tsabar mugun haushin da MD ya cusa mini a zuciya, ji nake yi tamkar na kama da wuta na ƙone ƙurmus kowa ma ya huta.

      Ina ji lokacin da wani yaro ya  shigo yana sanar da Ummata ana sallama da ita waje. Ban san ya aka yi ba ni dai na ji ta shigo tana balbala faɗa tamkar ta ci babu. 

     Sai ga ta cikin ɗakin tamkar an jefota, ba ta yi ƙasa a gwiwa ba kawai ta fara kai mini duka da hannu bibbiyu tana kuka. Da ƙyar Inna Kulu ta taɓe ni a hannunta bayan ta gama jibga ta son ranta har da gwabra kaina a bango. 

         Ban haushin abin da ta yi mini ba, domin ba na tantama a kan ta yi hakan ne kawai saboda ta huce haushin da na ba ta a lokacin, wanda ni ko kaɗan ban ji dukan ba, don zafin da zuciyata ke yi ya fi dukan da take yi mini linkin.

            Inna Kulu ta fitar da ita daga ɗakin tana haki, tare da jifa ta da miyagun maganganun da suka tsaya mini a zuciya.  Wanɗanda suka saka ni sabon kuka tare da yi wa Mukhtar Allah ya isa ta fi dubu, saboda shi ne ya shiga tsakanina da ita, kuma sanadin shi ne ta fara kyara ta, tare da jifa ta da miyagun kalamai munana, a duk lokacin da rigima ta haɗa ni da shi. 


      'Ina mafita?'

            Tambayar da na yi wa kaina kenan bayan na gama naɗe maganganun Umma a kwanyata. Domin babu komai a cikinsu sai muguwar fata gare ni, a kan muddin ban koma gidan Mukhtar na ci gaba da zaman 'ya'yana ba.






Hmmmm! Ana dara ga dare ya yi




*ABOKIN AIKINA*



*@HADIZA D. AUTA*



*SADAUKARWA: DAUGHTER ANUP*



*LAMBA SHA SHIDA.*


        Daga nan ɗakin da nake ina jiyo sautinsu ita da Inna Kulu tar-tar a cikin kunnuwana. "Haba Kulu! Shi kenan kullum abu ɗaya za a dinga yi? Har yaushe Zaituna za ta gano abin da nake lurar da ita? To ni kam a wannan karon, wallahi zan fitar da wuyan hannuna a cikin duk abin da ya shafe ta. Ta je ta yi duk abin da take so tun da ta isa da kanta da rayuwarta, amma wallahi ba zan zauna da ita cikin gidan nan ina ganin wulgawar ta ba. Don duk lokacin da na tuna ta kashe aurenta ta bar 'ya'yanta a wulaƙance sai na ji baƙinciki."

         "Ki yi haƙuri Habi, tun da dai hannunka ba ya ruɓewa ka yanke shi ka jefar." Zancen Inna Kulu kenan cikin tausasa murya a ƙoƙarin ta na tausar Ummata, daga mugun fushin da ta shiga tana ta feso hayaƙin maganganu masu nuni da zallar ɓacin ran da ta shiga, sannan kuma masu kama da yi mini baki a fakaice. 

         "To ke Kulu sau nawa mutum ya sa aka cire masa hannun aka jefar? Ai sai dai idan ba ta kama ba. Don haka ta tashi ta koma gidan mijinta yanzu tun muna shaida juna. Idan kuma zaman gidan take so ni zan bar mata gidan ta zauna, amma ba za mu jeru ni da ita ba"


         "Ba za ta zauna gidan nan ba, sai dai ta koma gidan Alhaji Ali tun da daman can shi yake ɗaure mata ƙugu tana iskanci." 

        Maganar Kawu Sale kenan da na tsinkayo muryar shi a sama alamun shi ma ya ɗauki zafi da ni. 

        Hawayena na share sannan na miƙe ina gyara zaman mayafin da ke jikina, na rataya jakar hannuna, na ja ta kayana na fito ɗakin.

      Ƙofar fita gidan na nufa ina sharɓen kuka ba tare da na ce da su ƙanzil ba, "Wallahi muddin kika fita gidan nan a yanzu sai na tsine miki albarka, matuƙar ba gidan Mukhtar za ki koma ki rungumi 'ya'yanki ba."

        Turus na yi babu shiri na ja na tsaya, domin a raina babu zancen komawa gidan Mukhtar har abada. Inna Kulu ta zo har inda nake ta karɓi jakata tare da riƙo hannuna muka koma ɗakinta. 

       Nasiha ta fara yi mini cikin kwantar da murya, tana ƙoƙarin fahimtar da ni muhimmancin yi wa Umma biyayya, da gudun lalacewar tarbiyyar 'ya'yana da take yi. Wanda abu ne a bayyane ko ni na sani Mukhtar ba zai iya ɗora su a kan tarbiyyar da na ba su ba. Domin zai iya dawo da hannun agogo baya kamar yadda na sha yaƙi da shi a kansu, kafin komai ya daidaita ya daina mayar mini da 'ya'ya kishiyoyi. Saboda duk wani aikin da ya dace mata ta yi wa mijinta idan aka cire kwanciyar aure, to shi yake saka su ba tare da ni ya damu da ni balle ya ce na yi masa. A kan haka mun yi faɗa ya fi a ƙirga da ƙyar na samu ya daina, saboda ƙaƙƙarfar iyakar da na yi masa da yarana.        

        Da wannan tunatarwar Inna Kulu ta samu kaina na rage kukan da nake yi, saboda matuƙar na ce zan tsallake na watsar masa da su, to babu makawa sai ya dawo da bara bana. Idan kuma hakan ta faru to babu amfanin nema wa kaina 'yanci bayan na wargaza tarbiyyar yarana.  

       "A ce.. ya kawo.. su idan.. na... tashi mu koma.. tare da su..." 

       Maganar da na faɗa kenan cikin ajiyar zuciya da shesshekar kuka. Domin jikina ya yi sanyi ƙalau musamman da na tuno lokacin da ya rufe su a ɗaki suna kuka, ba tare da ya damu da rarrashin su ba balle ya nuna musu tausayi irin na Uba.

      "Tun da sassafe yau ya kira Ummarki yana sanar da ita ba ki kwana gidan ba, shi ma bai san ba ki nan ba har sai da ya zo yi miki ina kwana sannan ya gano ba ki gidan."

          Murmushin takaici na yi sannan na ce, "Idan har da gaske ya san ban kwana gidan ba, to dole ne a ce yana sane na fita ko kuma a kan idon shi. Idan kuma har bai san ba na gidan ba har sai da ya zo yi mini ina kwana kamar yadda ya ce. To bai da masaniyar lokacin da na fita balle ya san gidan na kwana ko ba gidan ba. Abu na ƙarshe kuma ni rabon ina kwana ta haɗa ni da shi; na yi masa ko shi ya yi mini an fi shekara uku ko huɗu. Domin ko sallar asubu ba ya tayar da mu daga ni har yaran, balle zuwa ya ga tashin mu idan safiya ta waye."


     Ajiyar zuciya Inna Kulu ta sauke sannan ta ce, "Ni wannan zama naku Zaituna, ban taɓa ganin irin shi ba sai gare ku. A ce ko kaɗan babu jituwa tsakanin mace da mijinta; to ya ya za ku fahimci juna balle ku nemo hanyar gyara domin ku gyara zamantakew...?"

         "Ita ma ai tana da matsala, babbar matsalar Zaituna a rayuwa bai wuce kafiya ba. Da tana bin shawarar da muke ba ta da tuni ta zauna lafiya mu ma ta bar mu mun huta. Amma duk abin da kika ce ta yi sai ta nuna miki ta fi iyawa. To zama da Mukhtar ya zama dole ko don 'ya'yanta, tun da tun farko ba ta bayyana mana matsalar shi da wuri ba. Balle a taro tun kafin ta yi tsanani, har sai da komai ya lalace sannan ta faɗa bayan ta fara tara zuri'a da shi."

      Maganar Umma kenan da muka ji a sama ba tare da mun ji shigowar ta ɗakin ba, sai da ta ja numfashi sannan ta sake cewa, 

     "Na sani Mukhtar bai yi mata halacci ba mu ma bai yi mana ba, amma babbar matsalar shi ne yaran da ke tsakaninsu. Mahaifiyar shi ba ta duniya balle a miƙa mata yaran, domin ta san yadda za ta yi da su, shi kuma ba ɗa ba ne balle a ce za a bar masa su hannun shi. Sannan kaf dangin shi babu mai zuciyar riƙa masa 'ya'ya tsakani da Allah balle a kai musu su karɓa, saboda zuri'arsu kaf babu haɗin kan taimakon juna balle a share wa ɗan'uwa kuka. Babbar matsalar ita ce a cikin gidan ma tarbiyyar yaran za ta fara gurɓacewa ba sai an je nesa ba. Domin idan kin manta na tuna miki, sau nawa suna neman 'ya'yanki da lalata Allah yana tsarewa kafin ki baro gidan?"

       Ta ƙare maganar a fusace cikin ɗaga murya, saboda fuskarta ta nuna kai wa ƙoluwar ɓacin rai. Kafin na ba ta amsa ta ƙara da cewa,

        "Lokacin da kika daka yaji kika zo gidan nan, watanki biyu ana faɗi-tashi da yaran, nawa Mukhtar ya kawo mana domin mu ciyar da su ko a yi musu wata lalura? To a haka kike so na kawo ki gidan nan ke da yaranki ya bar mu ciyar da ku da sauran laluro, shi ya rungume hannun shi ya zuba mana ido? To ba za ta saɓu ba bindiga a ruwa. Sawunki a likkafa ki ɗauki jakarki ki koma tun kafin wankin hula ya kai ki dare, baƙincikin ɗa namiji ba a kanki aka fara ba kuma ba za a ƙare kanki ba. Kula da tarbiyyar yaranki ya fi miki alkhairi da neman wani matsugunnin da kike yi. Saboda inda kika sani kin raina shi, shi kuma inda za ki je an raina ki."


      Tana ƙare faɗar hakan ta fice, mintuna a tsakani na ji tana magana a waya. "A kawo yaran nan idan ta tashi ta koma tare da su. To idan sun dawo a kawo mata su."


       Daga ni har Inna Kulu babu wanda ya yi motsin kirki balle mu samu kuzarin cigaba da bitar maganganun. Domin har zuciyata na gamsu da zancenta ɗari bisa ɗari, saboda ta tunanar da ni wasu abubuwan da na manta a baya. Hakan ya sa na yi ammana da Mukhtar ne ƙaddarata a cikin duniya, wanda ban da ikon gyara ƙaddarar ta dawo mini daidai yadda nake so; har sai ranar da Allah ya kawo mini sassauci da mafita a cikin rayuwata da ta 'ya'yana.  

       Inna Kulu ta tashi ta fice, mintina a tsakani ta dawo ɗauke da kofin kunu da ƙosai a ƙaramin faratin silba. Gabana ta ajiye tana faɗin,

       "Ɗauki ki karya sannan ki bar wa Allah lamarinki, in Sha Allah za ki ga haske a gaba muddin kika cusa wa zuciyarki dangana, kuma kika bi abin da Mahaifiyarki take so."

        Ban musa ba na sauko daga kan gadon na fara shan kunun, domin shi kaɗai nake jin zai iya shiga cikina. Ko shi saboda yunwar da nake ji maƙoshina har ya fara bushewa.


      Kasancewar yaran sun je makaranta, bai kawo su ba har sai da aka gama sallar juma'a. Sannan suka shigo da gudu suna ihun murna tare da ƙwala mini kira, tarbon su na yi fuskata ɗauke da mayalwacin murmushi. Jikina suka faɗo dukansu suka rungume ni, ni ma na rungume su ƙam-ƙam. Nan take damuwa ta ziyarce ni har ta bayyana kan fuskata.

        Saboda kukan da Ummu Salma da Iman suke yi. Jan su na yi muka ƙarasa cikin ɗakin ina faɗin, 

     "Ya isa, ku daina kukan haka."


      Haidar riƙe da hannuna ya ce, "Mama wai da gaske kin ce ba za ki sake zama gidan Abbanmu ba?"

      Kallo na ƙura wa fuskar shi kafin na ce, "Wa ya faɗa maka?"

        "Abbanmu ne ya ce dama mun daina kuka don kin ce ba za ki sake zama da mu gidan ba, shi ya sa da dare kika tafiyar ki kika bar mu."

Amsar da Ummu Salma ta yi hanzarin ba da ni kenan tun kafin Haidar ya faɗa.

            Ajiyar zuciya na sauke sannan na ce, "Ko ma dai mene ne ina tare da ku abadan in Sha Allah! Ku je ku gayar da Umma." Har sun fice Iman ta dawo tana goge hawaye ta ce, "Abbanmu yana wurin Umma da Baba Sale suna magana." 

       Zumbur na miƙe saboda na san sharri da ƙage irin na Mukhtar, abu kaɗan zai iya juya shi zuwa babba. Balle ganin da ya yi mini tare da MD komai zai iya faɗa domin ya jaza mini wani sabon tashin hankali na daban.

           "Wallahi Umma da idona na gan ta tare da shi a ƙofar wani gida, kuma a gabana ta shiga motar shi suka tafi tare da 'yansan..."

        "Ban katsi hanzarinka ba Mukhtar! Amma mutumin nan ya faɗa mini duk abin da ya faru a lokacin da ya kawo ta gidan nan. Asali ma ban da shi; da tuni an cutar mana da ita saboda sakacinka. Kada ka ga ina zuba maka ido kana zaluntar mini yarinya ka ɗauka ba na son ta. Wallahi duk girman mutuncin da kake gani ina yi maka albarcin 'ya'yanka kake ci. Domin ni ba ki yi mini halacci ba kuma ba ka yi wa Zaituna adalci ba. Saboda ta nuna maka ƙauna kuma ta yi maka rufin asirin da a tara mata dubu ba za su iya yi maka irin shi ba. Mutumin da kake aibatawa kuma, mahaifiyar shi ya kai asibiti a daidai lokacin da taƙadarun suka biyo ta.  Saboda ciwon asma gare ta wanda tashin shi cikin daren ya yi sanadin ceton Zaituna. Domin ba don ta ya fito ba, kuma ita ma ba wurin shi ta je ba, amma idan har ba ka yarda da zancen ba; kana da damar ɗaukar mataki daidai da laifin da kake ganin ta yi maka."


       Maganganun da na ji kenan a lokacin da na durfafi ɗakin Kawu Sale, saboda a can ne mahaɗarmu a duk lokacin da aka zo sansancin rikicinmu ni da shi.

       Hawayen daɗi na goge a fuskata na sha jinin jikina a bakin ƙofar, saboda ba ƙaramin farinciki zancen Ummata ya saka ni ba.

 'Ashe har yanzu Umma tana so na.' 


        Zancen zucin da na yi kenan kafin na ji ɗaci ya ziyarci kan harshena, a sanadiyyar muryar Baba Sale da na ji yana faɗin, "Ke Habi ba haka ake sulhu ba, yadda ya kawo ƙara ya dace ki tsaya a saurari ta bakin..."

         "Babu abin da zan tsaya sauraro daga gare shi Sale, don magana ta gaskiya kai kanka ka san Zaituna ta sha wahalar auren shi. Kuma ba wai mun rasa inda za ta zauna ba ne ko abincin da za mu ba ta, balle ya zargi neman kai muke yi da ita shi ya sa muke tauye ta zama da shi koyaushe. Don haka idan har ya gaji babu dole ba sai ya yi ta ɗora mata ƙazafi ba, ya sake ta kawai gari da yawa maye ba zai ci kan shi ba wallahi. Amma ba ita ba ni kaina na gaji da matsalolin shi, idan bai gyara ba a wannan karon; to zan bai wa Babanta Ali dama ya raba auren kowa ya huta. Don daman can ni na hana da yanzu duk mai sha ta sha komai ya zama labari. Miji goma ai ba Uba goma ba ne."


       Ajiyar zuciya na sauke mai ƙarfi tamkar an sauke mini ƙaton dutsi a saman kaina, domin yau kaɗai Umma ta tabbatar mini da lalle ita ce ta haife ni. Saɓanin baya da nake tantamar hakan a duk lokacin da ta ɗauki gaskiya ta miƙa wa Mukhtar. Ko idan ta kawar da kai ga duk matsalolin shi idan na rattaba mata, a matsayin kare kaina daga wani laifin da ya ƙaƙaba mini ban ji ban gani ba, ko faɗan da take yi mini a kan boren da nake yi wa auren lokaci bayan lokaci.


     "Wallahi Umma ban san ta fita ba, sai bayan na farka tsakar dare na ga ƙofar gidanmu a buɗe. Kuma na yi ta kiran lambarta ban samu ba, haka ma sai da na biyo sawunta kafin na sake rufe gidan. Ke ce kawai ban yi tunanin kira ba sai da safe gudun na tayar miki da hankalin."

        "Ai da zafi-zafi ake bugun ƙarfe ba sai ya huce ba, domin da ka kira ni a lokacin dole mu fita neman ta mu da muka san zafinta. Saɓanin kai da rashin  ganin ta bai hana ka komawa gidanka ka rufe ba, saboda ba ka da asara ko mutuwa ta yi akwai mata da yawa a gari har waɗanda suka fi ta." 

        Cikin kakkausan sauti na ji Umma ta ba shi amsa mai harshen damo. Babu shiri na maka wa ƙofar harara saboda maganar da na ji yana faɗi daga bakin shi cike da yaudara da daɗin baki,

        "Yanzu dai don Allah Umma ku yi haƙuri, in Sha Allah hakan ba za ta sake faruwa ba. Domin Wallahi gabana har  faɗuwa yake yi a duk lokacin da na ji ana zancen sakin nan. Saboda ko maƙiyina ba na fatar ya saki matar shi balle ni na aikata. Kada Allah ya nuna mini ranar da zan furta wannan mummunar kalmar daga bakina zuwa ga Zaituna."





    To ni ma dai ga tawa harara🙄haɗi da tsaki😼 zuwa ga Muntari😂





D. AUTA CE✍🏼




*ABOKIN AIKINA*



*@HADIZA D. AUTA*



*SADAUKARWA: DAUGHTER ANUP*



*LAMBA SHA BAKWAI.*


         Shiru na ji ya ratsa tsakani bayan maganar Mukhtar, sannan na ji muryar Kawu Sale yana faɗin, "Yanzu ke Habi tun da ya gano laifin shi, yana da kyau a ƙara ba shi wata dama. Idan har ya kiyaye abubuwan da ke janyo musu  rikici shi kenan matsala ta kau, saboda haka ki zubar da komai a daina bitar abin da ya wuce. Kai kuma tsakani da Allah matuƙar ba ka gyara halinka ba, to duk abin da ya ƙara tasowa a gaba kada ka ga laifin kowa kai ka janyo. Abu na ƙarshe kuma ka daina zargi, domin muddin ka tsayu a kan zargin matarka to ba za ka taɓa jin daɗin zama da ita ba. A wani ƙaulin Malamai ma an tabbatar da cewa zargi yana ɓata aure."

         "Ni a wurina komai ya wuce Kawu, amma maganar gaskiya aikin nan da take zuwa, ko kaɗan ban da natsuwa da shi. Saboda mutumin nan babu komai a ran shi face buƙatar kashe mata aure domin ya aure ta."

        Maganar shi nan take ta saka idona  rufewa, ta yadda ban san lokacin da na yi wuf na faɗa ɗakin ba. Cikin ƙunar zuciya na fara nuna shi da hannu ina cewa, 

        "Kai dai baƙin munafuki ne ƙarshen bugun lamba. To wallahi ko za ka mutu ba zan fasa zuwa aik..."

          "Yi mana shiru Zaituna!" Babu shiri na gantsara saboda tsawar Baba Sale da carbin da ya watsa mini a jiki, na durƙushe ƙasa ina sosa wurin tare da aika wa Mukhtar harara ta gefen ido. Kafin Baba Sale ya ci gaba da magana cikin fushi tamkar ya dake ni.

       "Me ya kawo ki nan balle ki saka mana baki? Ko kin ji an kira ki da za ki zo kina yi wa mutane hauka? Wannan rashin mutuncin naki yana daga cikin abin da ke ƙara lalata muku zaman lafi..."


       "Wallahi ko a gaban yara haka take yi mini ba ta shayin komai. Na sha faɗa mata duk abin da za ta yi mini zan jure matuƙar ba gaban wasu ko 'ya'yana ba. Domin yanzu silar hakan har yaran sun fara yi da ni a tsakaninsu. Ko yau da safe ina jin Haidar yana faɗin; shi ya gaji da kukan da nake saka Mamarsu, Idan ban bari ba shi ma zai rama mata a kaina. Ka ga a nan ta yi ƙoƙarin cusa musu ƙiyayyata tun kafin su mallaki hanka...'" 

       "Wannan kuma ba laifinta ba ne kai ka janyo. Don a irin halinka babu abin da 'ya'yanku ba za su yi ba, matuƙar aka biye doron da kake ajiye tsarin gidanka a kan shi. Yana da kyau ka fahimci matsalar taki ce duka ba ta mutum guda ba, yadda kake da laifi ita ma tana da shi. Don haka ku taru ku gyara dukanku ko don tarbiyyar yaranku. Ke kuma ki ji tsoron Allah ki daina cin zarafin mijinki don komai lalacewar shi miji miji ne, kuma yana sama da ke ko babu auratayya balle aure ya haɗa da 'ya'ya a tsakani."


      Zancen Mukhtar da Ummata kenan a  lokacin da ya so goga mini laifi,  ta yi hanzarin toshe komai ta hanyar ankarad da shi domin ya hankalta. 

       Daga ni har shi suka rufe mu da faɗa, a kan mu zauna lafiya mu daina raba wa kanmu abin faɗa. Da nufin a bar wanda aka yi baya a matsayin ya wuce a fuskanci gaba, sannan batun aikina ma ba a hana ni zuwa ba kamar yadda yake da buƙata. Sai dai sun tunantar da ni abubuwan da baƙinciki ya sa nake ƙoƙarin aikatawa, ba don na manta da hukuncin laifi ba a musulunce ko a al'ada ba.

        

         Sannan aka tashi zaman sasancin da zummar da dare zan koma gidan shi, bayan an saka ni dole sai da na ba shi haƙuri ba don na so ba. 

      Ina gunguni na fito ɗakin saboda ko kaɗan hukuncin bai yi wa zuciyata daɗi ba. Domin ni a rayuwata ban da wani buri a lokacin; face  ya tsinke igiyon aurensa da suka yi mini mugun ɗaurin talala a jiki. Saboda ina so na kasance free babu aure ko da zan mori sauran rayuwar da ta rage mini a duniya. Domin na  yi nagartacciyar ibada irin wadda zan samu natsuwar zuciya, saboda ina so na daina aikata alfashar da nake yi a ƙoƙarin kaucewa zinar zahiri.  

       Inna Kulu ta dinga ba ni haƙuri domin na rungumi ƙaddarata har zuwa lokacin da Allah zai kawo mini ƙarshenta. Sauraron ta kawai nake yi, amma ba don babu abin da take faɗa mini zai yi tasiri a zuciya ba, matuƙar ba za ta goya mini bayan rabuwa da auren Mukhtar ba.

     Ƙarfe huɗu da minti goma na rana, bayan na gama sallar Asr ina kan sallaya da carbi a hannuna ina ja. Na jiyo sallamar Amina a tsakar gidan. Tana tambayar inda nake tare da yi wa su Umma bayanin ni ta zo dubawa, har da yi musu ya jikina suka amsa mata tamkar da gaske ciwon nake yi. Inna Kulu ta fara shigowa ɗakin sannan Amina a bayanta har inda nake zaune. 

      Murmushi muka yi wa juna ni da Amina sannan ta zauna tana faɗin, "Kai matar nan, ashe ma ciwon da sauƙi MD ya tsorata mu da cewa ciwon ya sa aka dawo da ke gida. Wataƙila ma lamɓo ne kawai gidan kika yi marmari, shi ya sa kika dawo don ki saka su Umma aiki." 

       Murmushi na yi mata da jajayen idanuwana, waɗanda har lokacin ba su gama washewa ba a kan kukan da na sha. Baki har kunne na ce da ita, "Ciwon kaina ne ya motsa, ban san lokacin da aka kawo ni gidan nan ba. Amma yanzu Alhmdulillah da sauƙi komai ya lafa."

        "Allah ya ƙara lafiya, amma ki daina cin abin da ke tayar miki da ulcer, sannan ki dinga shan magani saboda ki samu ta lafa miki ki huta."

       "In Sha Allah!"


     Dukanmu muka bi ƙofa da kallo saboda shigowar Inna Kulu da kula. Gaban Amina ta ajiye tana faɗin, "Ku ci awara tun kafin ta yi sanyi."

        Bayan fitar Inna Kulu Amina ta miƙe tana faɗin, "Bari na fara yin sallah don ba na son na ci na kasa motsin kirki. Tun da kin tayar mana da hankali a wurin aiki ana ta jimamin ciwonki, MD ma yau bai zauna ba tun da ya zo da safe ya fita har na baro wurin bai dawo ba."

      "Uhumm!" Kawai na ce ta fice na ci gaba da jan carbina, har ta dawo na tashi na ba ta sallayar. Kafin ta gama na zuba mana awarar a plate ɗaya, tare da ruwa a kofuna.

       Bayan ta gama muka fara cin awarar ta sha kayan haɗi da daddaɗan yaji, domin sana'ar Inna Kulun ce kuma sosai take samun rufin asiri da ita. Shiru ya ratsa tsakani, kafin Amina ta kawar da shirun da cewa,

         "Da zumuɗi na tashi yau domin na zo na ji cigaban labarina, abin haushi sai ga shi na tsinci zancen ciwonki a bakin MD. Bayan na yi ta rangadin zuwa offishinki ina ganin shi a kulle, a zuwa na ƙarshe ne da na gan shi zai fita nake tambayar shi ko kin zo; ya ce da ni kin turo masa saƙo ba kya samun damar zuwa ciwonki ya tashi kina gida. Da ƙyar na samu na kammala aikina na nufi gidanki, ganin gidan a rufe ya sa na kira lambarki ba ta shiga. Dole na  na sake neman shi na sanar da shi ba kya gidan,  ya sanar da ni kin ce kina gidanku wurin Umma Bafarawa Estate. Adaidaita na ƙara samu na yi gida, sai da na kammala ƙananun ayukana sannan na ƙara shiri zan fito." 

      Ƙasake ta yi tana lagudar awarar da ke hannunta wanda a take na gano akwai abin da ya faru kafin ta fito gidan. Hakan ya sa na samu kuzarin faɗin, "Ai da kin yi haƙuri gobe ma zan shiga aikin. Kin ga sai mu ɗan samu abin da zai sauwaƙa kafin a tashi."

       "Hmm! Ai ba zan iya haƙurin ba wallahi, in da na samu wayarki da ba zan shiga damuwar da na shiga ba. Saboda ina tunanin a wane hali kike ciki duba da  yanayin da kika baro wurin aikin jiya, kamar akwai wani abu maras daɗi da ya faru da ke. Hakan ya ƙara tayar mini da hankali ga shi matsalar da na samu ban san gidan da zan faɗa a kawo ni ba. Kuma ina da tabbacin MD ma bai san gidan ba shi ya sa ban neme shi ba." 

       "Ya aka yi kika gano gidan yanzu?"

        "Tambaya muka fara yi ni da mai adaidaitan da muka zo unguwar, har na yi katarin ganin Haidar tare da wasu yara a daidai wani shago. Da hanzari na kira shi yana gani na ya nufo ni yana gaishe ni, a nan yake yi mana kwatance na ce ya shigo ya kawo mu kawai."

             

     Ajiyar zuciya na sauke sannan na ce, "Allah Sarki Amina, na gode sosai da ƙoƙarinki. Allah ya bar zumunci."

         "Amin" ta ce sannan ta yi hanzarin fiddo wayarta a jaka saboda kiran da ake yi mata. "Ga ni nan zuwa yanzu." Abin da ta faɗa kenan fuskarta a haɗe bayan ta gama sauraron abin da aka ce cikin wayar. Mere na ga ta yi tare da hurar hanci tana lasar maiƙon da ke hannunta. Ban ce da ita komai don na san tatsuniyar gizo ba ta wuce ta ƙoƙi. 

          "Na rasa me na tare wa Mama da ko kaɗan ba ta ƙaunar farincikina. Yanzu fa ba ta ji kunyar kai ƙara ta wurin shi ba. Kuma shi ya bar ni fitar nan amma ƙiri-ƙiri ta so hana ni fitowa, saboda girkin da zan gama wahala a hana ni kwana da miji."

        Ta ƙare maganar fuskarta a cure, hakan ya tona mini asirin takaicin da take ƙumsa dangane da baƙar dokar Mama. Wadda mijinta ya mayar tamkar faɗar Allah da ta faɗa sai ya aiwatar ko ba ya so, duk da san kuskure ne yake aikata wa matar shi, bayan alaƙar zumuncin da ke tsakaninsu mai ƙarfi. Domin Mama uwar miji ce gare ta kuma Gwaggonta, saboda Yaya take ga Mahaifin Aminar uwa ɗaya uba ɗaya. 


       Amina ta so zama na ɗora mata labarin, amma dole na dinga nuna mata rashin dacewar zaman tun da gobe zan fito aiki. Sannan na ba ta haƙuri sosai tare da nuna mata alfanun juriya a kan cutarwar da Mamar take yi mata da gangan, matuƙar tana son ganin ribar a gaba. Cikin nasara na ci kanta ta miƙe tana saɓa jakarta a kafaɗa tana faɗin,        

          "To ni zan tafi Allah ya ƙara sauƙi. Amma don Allah ki ƙoƙarta ki fito goben."


        Har bakin titi muka raka ta ni da su Ummu Salma, tare da ba ta tabbacin zan fito gobe ta tsumaye ni. Ta tafi muna ɗaga wa juna hannu na juyo ina goge ƙwallar tausayin kanmu ni da ita, duk da na fi ta matsala amma har zuciyata ina jin tausayin ta a raina. Saboda ba ta da ƙarfin zuciyar shanye damuwa, saɓanin ni da na zamo turmin tsakar gida sha luguden mahassada. Domin duk wani sara da sukan da aka yi mini bai hana ni kirkiza ba, balle damuwar hakan ta bayyana a jikina. Dalilin hakan ya sa wasu da yawa suke hawa kan batutuwan Mukhtar su zauna.  Saboda na kasa zama abin tausayi a kan fuskokin mutane, ta yadda za a gano matsalar da nake ciki ta hanyar rama ko lalacewar da ido zai tabbatar da lalle ina shan wahala a gidan shi.


        Da dare misalin ƙarfe tara da rabi na dare, Umma da Inna Kulu suka kai ni gidan Mukhtar. Da motar wani Baban ƙawata kuma maƙocin Kawu Sale kuma abokin shi. Bayan sun gama jan kunnena sosai a kan na yi haƙuri na zauna lafiya da mijina, sai dai ni ko kaɗan ban ɗauki shawarar zama da shi a yadda suke so ba. Don ya gama sire mini kuma mutuncin shi ya daɗe da zubewa a idona. Saboda ba na jin zai iya dawo da martabar shi gare ni ko da zai mallaka mini ƙasar Nigeriya da abin da ke cikinta.  

         Ko da muka je mun tarad da shi, suka ƙara haɗa mu duka suka yi mana nasiha tare da saka mu neman yafiyar juna. Bayan sun tafi na saka yarana suka kwanta na tofe su da addu'o'in bacci sannan na rufo musu ɗaki. 

           Ɗakina na nufa na yi sabon wanka don jin daɗin kaina, sannan na kwanta tare da janyo wayata. Messages na shiga dubawa ta inbox da saƙonnin da ake ta turo mini daga waɗanda nake mutunci da su a wurin aikinmu. inda ake ta yi mini ya jiki tare da fatar samun sauƙi, saboda tun an karɓo mini jakata a hannun su Ummita, ban sake kunna wayar ba sai a lokacin. Shi ya sa ban san da shigowar saƙonnin ba. Amsa na shiga bai wa mutanen har na  zo kan saƙon MD, haka ƙawa na tsinci kaina da yin guntun tsaki ba tare da na shirya ba. Saboda har lokacin ban daina jin haushin abin da ya yi mini ba, wanda nake ji a raina tamkar ya datse ganin walwalar fuskata har abada. Domin na ci alwashin ko kallo don ya zama dole na gan shi, amma da ina da iko da hana kaina ganin shi saboda tsabar takaicin shi da nake ji. 

       Bubbugar da na ji ana yi wa ƙofar ɗakina ya sa na yi kasaƙe ina sauraron muryar Mukhtar da ke ta faɗin, "Ki buɗe magana za mu yi." Tsaki kawai na ja sannan kashe wayar tare da juya kwanciyata, yawan bugun da yake yi wa ƙofar ya sa na miƙe a fusace na buɗe ƙofar tare da tare hanya, ƙugu na riƙe fuskata a cure na ce,

         "Malam lafiya?"

         "Lafiyar ce ta kawo hakan!"

Amsar da ya ba ni kenan ya ratsa ta gefena ya shigo ɗakin. Zama ya yi a kan gadona yana murmushin shi da ke nuna mini alamun wata sabuwar yaudara ta kawo shi ɗakina. Domin ba na kawo ƙarshen zuwan shi ɗakin cikin lalama ba tare da tashin hankali ya ingizo ƙeyar shi ba. 

       "Zo ki zauna." 


       Abin da ya faɗa kenan yana nuna mini kan gadon a kusa da shi, kallon banza na aika masa tare da sakin guntun tsaki na rungume hannuna a ƙirji ina kallon gefe. Tasowa ya yi kai-tsaye na ɗauka fita zai yi kawai na ji ya rufe ɗakin da key yana ƙoƙarin tuɓe kayan shi. 

        Kallon mamaki na bi shi da shi tare yin dariyar takaici saboda na san ƙarshen wasar. Domin fankam-fankam ba shi ne kilishi ba, an sha yin ruwa ƙasa tana shanyewa. Idan ba yaudarar kan shi yake so ya yi ba ya san ba zai iya ba komai ba a nan fagen, amma don ya nuna mini shi ma jan wuya ne ya zo mini da ɗanyen kan da babu inda zai ƙare sai rabuwa baram-baram ni da shi.





Shin wane shiri ne Mukhtar yake yi wa Zaituna? Domin alamu ya nuna shi ma wannan karon zai zo da sabon salo.🤔





D. AUTA CE✍🏼


*ABOKIN AIKINA*



*@HADIZA D. AUTA*



*SADAUKARWA: DAUGHTER ANUP*



*LAMBA SHA TAKWAS.*


         Nufo ni ya yi gadan-gadan yana ƙoƙarin haɗa jikin shi da nawa, cikin zafin nama na tura shi ya yi baya. Sannan na nuna shi da hannu cikin ƙololuwar ɓacin ran da ya ziyarce ni. 

      "Kada ka yi gangancin zo mini da wani sabon sanabe, don sanin kanka ne babu wata alaƙa da ta yi saura tsakanina da kai yanzu. Sawunka a likkafa ka fice mini daga ɗaki tun muna shaida juna, idan kuma ka fi so ka tunzura ni na yi maka aika-aika to ka sake zuwa kusa da ni."

        Kallo na ya tsaya yi na ɗan lokaci, kafin ya sake nufo ni yana dariya kamar bai ji kashedin da na yi masa ba. Janyo ni ya yi da ƙarfi na zille, nan take muka fara kokawa ni da shi, cike da ƙarfin zuciya nake ta hana shi abin da yake ƙoƙarin aikata mini. 

     Ganin da gaske ba zai samu haɗin kaina ba, ya dawo magana cikin haki yana faɗin, "Wallahi duk abin da ya biyo baya kada ki ga laifina. Ba dai kin hana ni haƙƙina ba? To ke kuma ki jira me zai faru cikin kwanan..."

       "Kai har kana da bakin faɗar wani haƙƙinka da ke kaina yanzu? Kenan ka manta tsawon lokacin da ka ɗauka ba tare da ka neme ni ba? Ko an faɗa maka kai kaɗai ne mai haƙƙi ni ko oho? To ka je ka ɗauki matakin kada ka yi sanya, idan kuma ka fasa wallahi ban gode maka ba. Mitsssss! Aikin banza tura agwagwa cikin ruwa."

         Na ƙare maganar a fusace saboda furutan shi sun sa na ji ya kai ni bango Ya jingine. 

     "Za ki gani!"

    Zancen da ya yi kenan ya ja rigar shi ya fice fuu tare da bugo ƙofar ɗakin da ƙarfi. Ƙofar na bi da harara tamkar idona zai faɗo ƙasa, sannan na je na saka makulli na rufe na dawo na zauna ina haki. Mamaki na shiga yi a kan rashin adalci irin na Mukhtar, saboda rabon da ya nemi ni a matsayin matar shi ta sunnah sama da shekara uku. Kuma duk na yi haƙuri na jure amma sai yanzu zai zo mini da guntun rainin hankali. 

         Wanda na sani idan da zan kai shi kotun musulunci take yanke za a raba aurena da shi, saboda iya cutarwar duniya ya yi mini kuma ya tauye ni da baƙar igiyar da yake tinƙaho da ita.  

      Daren ranar ma sai da na gamsar da kaina sannan na samu damar yin bacci cikin nishaɗi, saboda ya tayar mini da tsohuwar jarabar da kullum nake ƙoƙarin kawar da kaina kanta, tare da addu'ar samun sauƙinta a wurin Allah. 

        

      Da safe ma tun da ya fita bai dawo gidan ba, sai dare bayan mun shige bacci sannan na ji yana rufe gida, ban wani damu ba don daman can bai ɗaɗa ni a ƙasa ba. Haka ma ranar Lahadi bai zauna ba, don ko yaran bai bi ta kansu ba a lokacin. Saboda ba wannan ne karon farko da fara yi musu hakan ba, domin ya sha shafa musu laifina a duk lokacin da na samu saɓani da shi, don a baya ma ko abu ya siyo ba zai bai wa kowa ba ko da yaran sun gani. Haka zai cinye abin shi muna kallo ba tare da ya ba mu ba, tun yaran suna jin haushin abin har suka daina zuwa kusa da shi idan sun gan shi da leda. Saboda a can baya ma idan ta yi masa daɗi, miƙa wa ɗiyan 'yan'uwan shi yake yi Ummu Salma tana kallo ya hana ta. A tunanin shi ni yake yi wa baƙinciki don na ji haushi.

       

       Ranar Litinin tun da sassafe na tashi, na haɗa wa yarana abin kari sannan muka shirya tare da su muka fice. Ganin ɗakin shi a rufe ya sa na gano ya yi wurin aiki don ban san fitar shi ba. 

       Bayan na ajiye su makarantarsu, na ba su kuɗin tara da waɗanda  za su hau abin hawa idan aka tashi. Sannan mai adaidaitan ya ajiye ni wurin aiki bayan na nemi alfarmarsa, a kan idan lokacin tashi ya yi daga makaranta ya koma ya ɗauko mini su Ummu Salm. 

        Saboda akwai sanayya tsakanina da shi kuma sosai yake girmama mutuncina a zahiri. Ina tafe zuciyata cike da tunanin  riƙon shi a matsayin wanda zai dinga kai su Ummu Salma makaranta, kuma ya ɗauko su a duk lokacin da aka tashi. Da zummar idan an yi mana albashi na dinga biyan shi kuɗin shi gabaɗaya.

       Zancen zucin da nake yi ya katse a daidai lokacin da mutanen wurin suke ta yi mini ya ƙarfin jikin ina amsawa. Turus na yi saboda babu makullin ofishin a hannuna, domin a ranar Alhamis da na bar wurin tashin hankali bai sa na tsaya rufe offishin ba. Ficewa kawai na yi saboda kwata-kwata na manta kowa da komai, face neman hanyar da zille wa auren Mukhtar a idona. 

      Ofishin MD na nufa raina yana suya, saboda ba na farinciki da ganin shi saboda haushin shi da nake ji. Na yi wa kaina katanga da shi kuma na kwance ƙaƙƙarfar alaƙar son da na fara ginawa a tsakanina da shi. Kaina a ƙasa ina shan ƙamshi na ƙwanƙwasa masa ƙofa, 

     "Yes! Come in"

      Ita ce maganar da na ji ya faɗa na tura ƙofar kaina a tsaye na isa gaban shi. Ban damu da gaishe shi ba cikin haɗe fuska na ce,

 "Key za a ba ni."

      Ya miƙo mini yana ta rubutun shi ba tare da ya kalle ni ba, cike da haushi na fice saboda ganin ko-in-kular da ya yi mini. 

       Zama na yi bayan na zauna, ina nazarin abubuwa da yawa a cikin kwanyata. Sannan na fara duba files ɗin da na gani a saman teburina, na shiga aiki tuƙuru ba tare da na nemi ba'asin komai kansu ba. Saboda ina da masaniyar komai nasu, bayan lissafin da na shiga bugawa da calculator, ina ta rubuta adadin da na samu a wuraren da ya dace a jikin files ɗin.

         Turo ƙofar ofishin da sallamar Amina bai sa na ɗago daga aikin da nake yi ba, na dai amsa mata sallamar saboda ba na so ta katse mini aikin har sai na gama. 

      Tsawon minti goma tana zaune har na kammala aikin na ture files ɗin gefena. Tagumi na yi da hannuna biyu muna kallon juna muna murmushi, sannan na cire farin gilashin da nake sanye da shi ina faɗin, 

        "Sannu cika-aiki. Wannan sammako haka ba kya bari a kira ki?"

          "Gara dai na zo don zuwa da kai ya fi aike." 


      Dariya muka saka a tare sannan na jingina bayana jikin kujera ina ɗan juyawa a hankali. Murmushi ɗauke a kan fuskata na ce da ita, "A ina muka tsaya da labarin? Don na san kin fi ni sanin inda za mu tashi."

       Zama ta gyara sannan ta ce, "Abu mai sauƙi cire wando ta kai, mun tsaya ne a daidai inda cikinki ya kai wata tara haihuwa yau ko gobe. A lokacin da Abban  su Ummu ya yi miki laifin da ya so katse igiyoyin aurenku."

       "Madallah da ke, don ni haddar kaina ta daɗe da gogewa." 

       Shiru na yi ina nazarin abubuwan da suka faru a lokacin, sannan na yi murmushin da iyakacin shi leɓe tare da sauke ajiyar zuciya na ɗora daga inda na tsaya.


      _EDD na yana cika na ce da shi ya bari na koma wurin Ummata, saboda koyaushe zan iya haihuwa amma ya nuna ba zan je ba har sai na haifu. Domin ita kanta Ummar ta so a mayar da ni wurinta na haifu gabanta, amma babu kunya ya nuna ya fi so sai na haifu gidansa. Ba ta ja da tsauri ba ta bar maganar saboda ya fito ƙarara ya nuna ba ya so._

       _Duk da girmama al'ada irin ta Sakkwatawa haka ta haƙura, domin abu ne wanda kowa ya sani haihuwar farko a gida yarinya take yi. Wani lokaci ma da wuri ake komawa a yi ta dakon zuwan haihuwar._

       

      _Ranar da zan haifu, tun cikin dare na fara naƙuda, amma ban da bacci babu abin da yake yi. Sai idan na ji azaba ta yi mini yawa na ƙwala masa kira ya tashi yana jera mini sannu. Da ƙyar na ga asuba, zuwa lokacin na galabaita sosai ta yadda ko magana ba na iya yi. Ko da 'yan gidansu suka zo ban san lokacin da suka kai ni asibiti ba, saboda jinin da ya fara zubar mini ya sa na cire rai da duniya balle ganin abin da zan haifa._

       _A gurguje aka karɓe ni cikin sauri aka yi labor room da ni, a saman gadon ɗaukar marasa lafiya jini yana ta bin jikina. Cikin ikon Allah har an fara zancen yi minti aiki sai ga yarinya ta kunno kai. Nan take na haifo 'yata ba tare da cikina ya sha askar likitoci ba._

        _Bayan na samu kaina na ga an kimtsa ni tare da abin da na haifa. Ummata na fara gani sannan Inna Kulu da sauran 'yan gidansu Mukhtar, har da ƙawata Hafsa waton ɗiyar maƙocin Kawu Sale da muke kai ɗaya a nan Bafarawa Estate. Murmushi na bi kowa da shi cike da jin daɗin ganin kyautar da Allah ya ba ni. Mamaki fal raina tare da bin Mukhtar da kallo saboda ganin wasar bakin da yake yi, wanda alamu ya nuna fili ya yi farincikin da samun Bbyn. A raina na ce 'Ashe dai ana so ake kai wa kasuwa.'_

      _Kwanana ɗaya Asibitin ana ƙara mini jini, saboda jinina ya yi zubar da dole sai an ƙara mini da wani. Da dare aka sallame ni muka yi tsinke sai gidan Kawu Sale, a nan ma mutane suka fara tururuwar zuwa gani na tsakanin 'yan'uwa da abokan arziƙi._

       _Kwana huɗu da haihuwa 'yan gidansu Mukhtar suka kawo mana kayan fitar suna, kayan da suka janyo mana ce-ce-ku-cen mutane. Domin kala uku ce da kayan jarirai biyar sai wasu tarkacen da rashin su ya fi kawo su rana. saboda ba a kawo sauran kayan da Sakkwatawa suka mayar tamkar ibada ba. Domin babu kayan yajin da suka daɗe da camfi kansu, a kan duk maijegon da ba a ba ta su ba, ko lahira sai an biya ta su a gaban Allah. Surutun mutane ya sa Umma ta je kasuwa da kanta ta siyo tare da wasu kayan da ya dace a ce Mukhtar ne ya kawo su._

      _Ana gobe suna mutanen Kebbi suka zo, farinciki fal raina saboda ganin babbar ƙawata Asma'u. Wadda muka yi karatu tare tun daga matakin primary har zuwa Sakandire, ko a Jami'a mun yi makaranta ɗaya sai dai kowa da ɓangaren da ya karanta. Akwai shaƙuwa sosai a tsakanina da ita, irin wadda kowa ya san ta zai san ni, haka ma wanda duk ya san ni ya san ta a baki ko a zahiri, saboda ƙarfin abotarmu._

        _Ranar suna aka raɗa wa yarinya Ummu Salma,  an sha hidima sosai komai a wadace ma Sha Allah, saboda ƙoƙarin Ummata da Baba Sale har ma da Baba Ali. Domin sun yi namijin ƙoƙari wurin fitar da ni kunyar 'yan biki, saboda ɓangaren abinci da abin sha Alhmdulillah har rara aka yi da dare. Domin girka abincin ake yi wani kan wani, sai da sawun mutane ya ɗauke aka dawo jinyar jiki._

       _Da safe aka fara rabon tsokar abin sunan kusufa-kusufa lungu da saƙo. Saboda babu laifi Mukhtar ya yi abin kai gida, domin dabba biyu ya yanka amma sai da Umma ta dawo siyen ƙaramar tunkiya saboda mutanen kunyar da ba su samu ba._

        _Yan Kebbi kuma suna gama sallar zuhur suka fara sallama da mutanen gida. Don daman can sun haɗa kayan tafiya tun da sake aka dakatar da su domin a ba su nasu kaso. Sai da suka soye namansu sannan suka yi haramar tafiya, har raina ban so tafiyar Asma'u ba. Na so a ce ta zauna amma ta nuna mini wannan tafiyar da da ƙyar aka bar ta, saboda Babansu mutum ne mai tsattsauran ra'ayi da masifar faɗa tamkar ya ci babu. Amma ni duk da faɗan shi Allah ya haɗa jinina da shi sosai yake mutunta abotarmu._


       _Sai da suka isa gida sannan hankalina ya kwanta, domin lokaci bayan lokaci ina kiran su na ji sun isa ko suna kan hanya._

       

        _Na ci gaba da zaman jego a gidan Kawu Sale har yi arba'in, sannan na tafi Kebbi cike da jin daɗin ganin Baba Ali da sauran 'yan'uwa da abokan arziƙin da aka yi zaman mutunci. Satina biyu a can na dawo saboda matsin lambar Umma da Kawu Sale suke yi mini, a kan na dawo haka nan na koma gidan mijina. Sai dai su abin ba su sani ba, koyaushe muna waya da shi, amma bai damu da sai na dawon ba. Bayan wata tambayar da ya yi mini wadda ta sa na kasa tantance ina zancen shi ya dosa. Domin a lokacin da muka gama waya da Umma a kan dawowar sai ga kiran shi, na dauka cike da tunanin shi ma zancen da zai yi mini kenan. Sai ga shi na ji sabanin abin da zuciyata ta zata._

        "Telar nan taki da firij. Kina so a sayar miki da su kafin ki dawo?"

       "Kada a sayar domin idan na dawo zan fara koyon ɗinki, kuma zan dinga yin zoɓo da ƙanƙarar zaƙi na san yaran unguwar za su saya."

       "To" _Kawai ya ce sannan ya katse kiran, bayan mintina kaɗan ya sake kira yana yi mini gargaɗi a fakaice._

     "Yawwa! Ki bar zancen nan a tsakaninmu ba sai kin faɗa wa kowa ba."

        _Murmushi kawai na yi masa sannan na ce,_ "Wannan maganar ai ba ta kai na yi yamaɗiɗi da ita ba." 

       _Daga haka muka yi sallama tare da sanar da shi gobe zan koma Sokoto, sai dai ban ji ya yi murna ba balle ya yi zumuɗin dawowar ta yadda zan gane._ 

   

      _Tun da safe na yi sallama da waɗanda ya zama dole, sannan Baba Ali ya sa aka kai ni tasha tare da kayan alherin da na samu niƙi-niƙi. Saboda mutanen Sokoto da Kebbi akwai ƙara kuma akwai girmama baƙunta._ 

        

       _Sai dai abin da su Umma ta tarbe ni da shi ya kaɗar mini da 'yan hanjina, duk da ban bari na fito da firgicin a fili suka gani ba. Amma na shiga rashin natsuwar da ta janyo mini kiran Mukhtar babu shiri, saboda Inna Kulu ta sanar da ni,_

      "Mun yi ta zuwa a gyara miki ɗakinki ba a iske Mukhtar gida. Kuma an sanar da Mahaifiyar shi ta karɓi makulli a hannun shi idan muka zo mu karɓa, nan ma duk muka je haka muke dawowa babu makullin. A ƙarshe ma cewa ta yi da mu ya yi tafiya, kuma bai bar musu makullin ba.  Amma ya ba da haƙuri a kan ki koma gidansa shi ma zai dawo garin a ranar da kika dawo."

       

       _Ajiyar zuciya na sauke sannan na ce ta bari na kira shi na ji yaushe zai dawo. Ni ma hakurin ya ba ni a lokacin da na kira shin, tare da saka mini ranar da zan koma domin shi ma a ranar zai dawo._

        _Kasancewar rana ba ta ƙarya sai dai uwar ɗiya ta ji kunya, hakan ya sa na tattara kayana na koma gidansu Mukhtar. Tare da rakiyar su Inna Kulu da Hafsa, sai wata ƙawar Umma da wasu mata biyu daga cikin dangin su Ummata da ke Dunguza._

        _Sai dai har tara na dare ta wuce goma ta doso Mukhtar bai dawo ba, dole suka tafi ba tare da sun kai ni ɗakina ba. Ni ma a nan ɗakin Mahaifiyar shi bacci ya kwashe ni, kasancewar Ummu Salma tana hannun matar Baban shi._ 

        _Cikin bacci na ji muryar shi na yi firgigit na tashi, ya iso inda nake cike da mayalwacin farinciki a kan fuskar shi. Ni ma sosai na ji daɗin ganin shi har raina, ya saɓa Ummu Salma a kafaɗar shi muka yi ɓangarena. Makulli ya ba ni sannan ya miƙo mini ita ya ce; bari ya je ya kwaso mini kayana da muka baro ɗakin Mahaifiyar shi. Ban kawo komai a raina ba, kawai na buɗe na shiga da guntuwar sallamata, sai dai babu shiri na zaro ido tare da kwarma ihu iya ƙarfina ina faɗin,_

       "Innalillahi wa inna ilaihirraji'uun!" 






Shin me ke faruwa ne😨 na yi nan ni ma🏃🏻‍♀️



Idan ban ga ruwan comments ba zan je hutun sati ɗaya😒




D. AUTA CE✍🏼



*ABOKIN AIKINA*



*@HADIZA D. AUTA*



*SADAUKARWA: DAUGHTER ANUP*



*LAMBA SHA TARA.*


         "Subhanallah! Me ya faru a lokacin? Me kika gani bayan kin shiga ɗakin?" Tamboyoyin da Amina ta jefo mini kenan a ruɗe, tare da firgici kwance a kan fuskarta. Murmushi na yi saboda ganin yadda hankalinta ya tashi, cikin sauri ta ce da ni,

       "Don Allah ki sanar da ni me ya faru a lokacin? Na mats... 

       

      "Me dai yake shirin faruwa a yanzu!"


     Maganar da muka ji kenan daga ni har Amina a bakin ƙofar ofis ɗina, cike da mamaki muka bi mata biyun da ke shigowa da kallon mamaki, waɗanda ke ƙoƙarin isowa inda muke cikin gadara. Kallon sama da ƙasa ɗaya ta fara yi mana sannan ta tsayar da kallonta a kaina, nuna ni ta yi da key ɗin da ke hannunta ta ce, 

       "Da alamu ke ce Munafukar da nake nema!" 

        "Ta ya za ki neme ni bayan ni ban san ki ba!" Maganar da na faɗa mata kenan cike da jin haushin rainin hankalin da take ƙoƙarin yi mini,  har cikin ofishina. Bayan dakan luguden da zuciyata ta hau yi saboda tsabar kaɗuwar da na shiga"

       Kallon uku kwabo ta yi mini sannan ta miƙa hannu ta baya wadda suka zo tare ta saka mata wani wallet a hannunta, sai da ta buɗe shi sannan ta wurgo mini a fusace saman ya daki ƙirjin ya yi ƙasa. Daga shi har kayan da ke cikin shi suka yi ɗaiɗaya, na yi hanzarin kai kallona a kayan da suka zuba daga wallet ɗin, cike da mamakin yadda aka yi ta yi ta same su. Kafin na duƙa na ɗauko Amina ta riga ni haɗa kansu ta ɗago, cike da zallar  mamaki a kan fuskarta ta fara jujjuya kayan cikin wallet ɗin a hannunta tana faɗin, 

      "Wai ku bayin Allah me ya kawo ku ofinshin nan da rana tsaka haka? Sannan ina kuka haɗu da Id card ɗin ta, da passport har da ATM?"

      "Za ki samu duka amsoshin tambayoyinki dalla-dalla, kuma zan yi miki gwari-gwari yanzu ba sai na ja zaren da tsawo ba. Amma kafin nan ke ki yi mata bayanin inda kika je kwatankwaci kika baro wallet ɗinki."

 

      "Kwartanci kuma!?"

        

      Maganar da muka haɗa baki kenan wurin faɗa ni da Amina cikin tashin hankali, babu zato na ji 'Karaf' sauti da dirar marin matar a kan fuskata. Kafin na yi wani yunƙurin ramawa ta ci kwalata a masifance tana faɗin,

       "Sai na illata ki, ta yadda gobe ko da kuɗi aka ce ki sake zuwa gidana kwartanci ba za ki iya taka ƙafarki ki je ba."

       Duka ta fara kai mini Amina tana riƙe hannunta cikin zafin nama, yayin da ni kuma na shiga ƙwatar kaina ta ƙarfi duk da fargaba ya hana ni kataɓus. Ƙawarta ta fara janye Amina tana faɗin, 

      "Ke dalla malama matsa daga gefe ba wurinki muka zo ba. Ci ubanta Fatima gobe ko kallon MD aka ce ta yi ba za ta sake ba, balle ta kai ƙafarta gidanku a matsayin ƙatuwar kwartuwar da ba ta ramin kanta sai na wasu."

         Sunan MD da na ji ƙawarta ta faɗa na ji ƙirjina ya buga dam-dam! Amma a hakan bai hana ni jarumtar ƙwace riƙon da ta yi mini. Amina ta yi hanzarin shiga tsakaninmu tana tura ta baya, ita kuma sai ƙoƙarin kai mini bugu take yi ta gefen Amina. 

     Cikin ƙololuwar ɓacin rai na fara nuna ta da hannu ina huci na ce,

     "Zan nuna miki na fi ki tashanci matuƙar kika sake taɓa ni da sunan du..." 

      Kafin na rufe bakina ta shammaci Amina ta kawo mini wani sabon duka, kukan kura na yi tare da ture Amina gefe. Cikin rufewar ido da na zuciya na yi cikinta da duka iya ƙarfina. Kokawa muka fara yi ni da ita Amina tana ƙoƙarin raba mu, ƙawarta kuma tana ƙara zuga ta da ihun faɗin ta ci ubana kada ta ƙyale ni.

       Ta dake ni na dake ta muke yi a tsakiyar ofishin ba tare da ta yi nasarar kayar da ni ƙasa ba. Cikin sa'a na saka mata ƙafa ta faɗi na hau kanta ina ta jibga, ƙawarta ma tana kai mini duka tare da ƙoƙarin ture ni daga saman ruwan cikinta.

      Ban san ya aka yi ba na tsinkayo muryar MD yana salati, amma hakan bai hana ni ci gaba da jibgar ta ba inda ta yi mini daɗi. Domin ko a shekaru zan iya girmar ta kaɗan ko mu zo tsara, duk da ta fi ni zama duma-duma amma hakan bai sa ta yi nasara kaina ba.

       Amina ta janye ni daga samanta ina huci tare da ƙoƙarin ƙwacewa na koma, da nufin sake kai mata wani dukan domin na cire rainin da ke tsakaninmu. Saboda raina ya yi ƙololuwar ɓaci a kan abin da ta yi mini, haka idona ya rufe ba na ganin komai face na yagalgala ta iya son raina. 

       

     "Yanzu miye fa'idar wannan abin da kuka aikata? Tukunna ma ke me ya kawo ki wurin nan har cikin ofishinta?"

      MD ya yi magana cikin sanyin murya mai ɗauke da tsananin ɓacin rai, na ƙwace daga riƙon da Amina ta yi mini na koma kujerata ina gyara zaman mayafina, wanda ya saɓule a jikina yayin damben ba tare da na sani ba.

    

    "Ai dole ka ga laifina yanzu, bayan ka gama kai ta har gidana a matsayin kwartuwarka kun ci amanata. Shi ne ka matsa mini a kan na je jinyar Ammi don ka ji daɗin sheƙe ayarka son ranka da ita. To Allah ya toni asirinku daga kai har ita, saboda ta bar mini shaidar da zan gane ta zo gidan, domin ta nuna mini ta fi ni matsayi a wurinka. Wallahi sai Allah ya saka mini a kan tozarcin da ka yi mini Aliyu, kuma daga kai har ita ba zan taɓa yafe muku cin amanar da kuka yi wa aurena ba."

       Tana ƙare faɗar maganganun ta juya fuu za ta fice daga ofishin, kamar zautacciya ta ƙara dawowa tana nuna ni da hannu ta ce,

      "Sai na nuna miki na fi ki iya karuwanci wallahi. Don sai kin raina kanki a kan wannan abin da kika aikata mini."

      Tana ƙare faɗar hakan ta fice tana ci gaba da masifa cikin ɗaga murya, ƙawarta ta rufa mata baya sum-sum cikin takun munafukai. Ajiyar zuciya MD ya yi sannan cikin sanyin murya ya ce da ni,

       "Ki yi haƙuri don Allah! Wani lokaci tana yin wasu abubuwa tamkar akwai wani abu saman kanta. Ban san za ta zo ba da ban bari ta fito daga gida ba wallahi, don haka duk da ban san dalilin da ya sa ta yi miki hakan ba, ina ƙara ba ki haƙuri don Allah ki yafe mata."

      Kallo ma bai ishe ni ba balle na tanka masa, Amina ce kawai ta ce da shi, 

     "Muna zaune kawai muka ga sun shigo ita da ƙawarta suna ci mata zarafi. Mamakina ma yadda aka yi ta haɗu da wallet ɗin Zaituna, wanda kusan shi ne musabbin duk wannan jidalin."


       "Ranar Alhamis ta manta shi a nan, Baba masinja ya kawo mini shi na karɓa da zummar na ajiye mata har yau na ba ta. Shi ne fa na manta shi a gida ban fito da shi ba, wataƙila dalilin da ya sa ta zargi wani abu kenan ta zo wurinta da wannan sifar. Ki ƙara ba ta haƙuri in sha Allah hakan ba za ta sake faruwa ba matuƙar da gaske ni ne mijinta."


      Zantukan shi ko kaɗan ba su burge ni ba, duk da ya yi ƙoƙarin binne gaskiyar abin da ya faru, a ƙoƙarin shi na gudun zargin da za a yi mana tare da ɓacin sunanmu daga ni har shi.

      Bayan ya fice Amina ta zauna ci masa albasa, tana ta ba ni baki a kan na yi haƙuri ko don shi. Ƙanzil ban ce mata ba, domin duk maganar da zan yi a lokacin sai na zubar da ruwan hawaye, kuma ba na so ta ga kasawa ta gudun ta yi tunanin matar MD ta yi nasara kaina.

        Jugum-jugum muka yi daga ni har ita babu mai magana, bayan ta gama ba ni haƙuri da maganganu masu daɗin da suka rage mini takaicin MD da matar shi. 

      Da lokacin tashi ya yi muka fito zuwa bakin gate, sai dai mamakin da na yi duk inda muka wulga zancen faɗan ake yi da an hango mu a yi shiru. 

      Muna gaf da ficewa muka jiyo muryar Sara tana ƙwala wa Amina kira, tare muka juya bayan mun tsaya har ta ƙaraso inda muke. Kafaɗar Amina ta dafa tana dariyar shaƙiyanci ta ce, 

       "Ashe abin da ya faru kenan a yau? Gaskiya dai abin bai yi daɗi ba, don babu kyau abin da mutum yake yi a ɓoye a fito da shi fili a yi masa terere kowa ya gani. Ubangiji dai ya ƙara tsare tsautsayi, da ranar tonuwar asirin da ya fi wanda aka yi yau."

      Ta ƙare maganar tare da yi mini wani kallon rainin hankali ta yi gaba, Amina ta yi hanzarin janyo mayafinta a fusace tana faɗin,

        "Duk wanda ya faɗa miki wannan tatsuniyar gizo da ƙoƙin bai san yadda gaskiyar abin yake ba. Domin ita kanta matar MD ta yi ne a rashin sani, amman idan kina tantama ki je wurin shi ki ji gaskiyar komai daga bak..."    

   "Zo mu je Amina, kin san shi mutum mai mummunan zato da jiran ƙiris, komai za ki faɗa masa gaskiya ba zai hankalta ba. Idan ma abin da take tunanin gaskiya ne ita ta je ta yi idan fitsari banza ne."

     Abin da na faɗa kenan bayan na yi gaba na bar su a nan, saboda na sha ganin MD yana kyarar ta ba sau ɗaya ba. A ƙarshe ya yi mata iyaka da ofishin shi komai uzuri, idan ma wani abu ne sai dai ta bai wa wani ya kai masa. 

       "Allah ya raba ni aikata fasadi da aurena. Ke dai da kika ji za ki iya ki je ki yi ta yi akwai ranar ƙin dillanci."

       Maganarta ta sa na juyo a fusace na shaƙo wuyanta, Amina ta shiga ɓanɓare hannuna tare da faɗin a kawo mata ɗauki. Saboda ganin na kai maƙurar ɓacin ran da komai zan iya aikatwa a lokacin, domin zafafan maganganunta sun dakar mini zuciya ba kaɗan ba, wanɗanda nake ji tamkar ta ɗana mini garwashin wuta a cikin zuciyar ta fara cin wuta.

      Taro aka yi mana sosai, bayan an ƙwace ta daga hannuna tana tarin wahala, ana ba ni haƙuri tana sake jifa ta da miyagun maganganu masu zafi bayan ƙazafin da take jifa ta da shi son ranta ni da MD. 

     Babu wanda ya ga zuwan MD sai marin da ya kwaɗa mata a fusace yana nuna ta da hannu ya ce, 

        "Matuƙar kika sake jingina ƙazafinki a kaina, sai na yi ƙarar ki a kulle ki har makulli ya yi rara, domin na ga wanda zai tsaya miki a faɗin garin nan. Me ya sa ku mutane ba ku da adalci ne? To duk iskancinki kada ki bari ganganci ya sa ki saka ni. Idan ban da ke shashasha ce har ni za ki yi ƙoƙarin manna mana sharri?  Kaf faɗin ma'aikatar nan ban da wata alaƙa mai ƙarfi da kowa, idan aka wuce ta aikin da ya haɗa ni da mutum abu ne wanda kowa ya sani. Me ya sa kika manta rawar ƙafar da kike yi a kaina, a kan kawai ki samu na saurare ki na ƙi? To tun da tonon sililin kike so, idan kin manta zan tuna miki yanzu, ko satin da ya wuce sai da na ci zarafinki a kan wannan mugun abin, wanda kike ƙoƙarin manna wa wata a bisa zargi ba tare da kin tabbatar ba."


    Soshe-soshen kai Sara ta fara yi tana mutsu-mutsun rashin gaskiya, tare da roƙon shi a wayance a kan ya yi shiru ya daina bankaɗa mata labulen sirri. 

       Murmushi na ji ya suɓuce mini babu shiri, na yi gaba fuskata a washe saboda fiye da rabin ɓacin raina ya zumame. Ban san ya aka ƙarke ba ni dai na haye adaidaita na yi gida, zuciyata cike da tunanin,

     'Ya aka yi na baro wallet ɗina a gidan MD har matar shi ta gani.'


     Ajiyar zuciya na sauke a lokacin da aka ajiye ni ƙofar gidan. Tunani fal zuciyata na shiga gidan, da sassarfa na faɗa falon saboda kukan Haidar da na ji yana tashi. 

      Ummu Salma da Iman suka yi kaina da gudu suna ihun murnar gani na. Mamakina da na hango Haidar ya ƙara shan jinin jikin shi, sai matsar ƙwalla yake yi tare da goge hawayen da ya jiƙa masa fuska.

      Da sanyin jiki na nufo shi da nufin na ji wa taɓa shi, sai dai kafin na isa wurin shi ya yi hanzarin tashi da gudu ya yi ɗakinsu ya rufe. Baki a sake na bi ƙofar da kallo kafin na dawo da kallona a kan fuskar Ummu Salma, wadda ke wasa da yatsun hannunta tana so ta yi magana tana shayi. 

       "Me aka yi wa Haidar?"

      Tambayar da na jefo mata kenan don na san Iman ba gwanar magana ba ce. 

       "Don Allah Mama kada ki dake shi don Abbanmu ma ya dake shi."

      Gabana ya ƙire ya faɗi cikin sauri bakina yana rawa na ce, "To me ya yi aka sake shi?"

         "Taba ya ɗauko ɗakin Abbanmu ya kunna ya sha, ni da Iman ba mu sani ba sai da muka jiyo ihun shi cikin toilet sannan muka je da gudu. A nan muka ga tabar a hannun shi yana ta tari kamar zai mutu. Na fara zuba masa ruwa a fuska ni da Iman muna ta kuka, na ce da ita ta kira Abbanmu kada ya mutu mu shiga uku. Ko da Abban ya zo na faɗa masa taba ya sha shi ne fa ya yi ta dukan shi, da ƙyar ya ƙyale shi saboda ganin muna ta kuka ni da Iman."

       Zaman na yi babu shiri tare da furta kalmar, "Innalillahi wa inna ilaihirraji'uun!" Saboda ita kaɗai ce kalmar da zan iya furtawa a lokacin.




Ni ma dai jikina ya yi sanyi😰🚶🏻‍♀️





D. AUTA CE✍🏼



*ABOKIN AIKINA*



*@HADIZA D. AUTA*



*SADAUKARWA: DAUGHTER ANUP*



*LAMBA ASHIRIN.*


      Shiru na yi na ɗan lokaci dafe da kaina da ke ta sarawa, sannan na miƙe su Ummu Salma suka fara kuka tare da roƙo na don Allah kada na buge shi.

       Ban bi ta kansu ba balle ta kan Haidar da ke kulle cikin ɗakinsu. Ɗakina na nufa yaraf na zauna bakin gado saboda jirin da ke kwasa ta, mintuna a tsakani na miƙe na ɗoro arwala. Sallah na gabatarwar tare da ɗaga hannuwana sama ina roƙon Allah shiriya zuwa ga 'ya'yana. Ruwan hawaye yana zarya a kan dandamalin fuskata cikin ƙanƙan da kai tare da tawassuli da haƙurin da nake yi a gidan Mukhtar. 

       Ummu Salma ta shigo ɗauke da kula ta ajiye gefena, tana ƙoƙarin ficewa cikin sanyin murya na ce da ita, 

       "Kira mini Haidar ku zo tare."

       "To" Ta faɗa sannan ta fice jim kaɗan ta dawo riƙe da hannun Haidar yana tirjiya tana janyo shi, Iman ta yi hanzarin zuwa inda nake tana matsar hawaye ta ce,

       "Don Allah Mama ki yafe masa Abbanmu ya dake shi sosai."

          Kallo na bi fuskar shi tare da tsuke tawa fuskar na ce,

 "Zo nan!"

      Ya tako yana ɗari-ɗari tare da haɗa hannuwan shi wuri ɗaya yana faɗin,

      "Don Allah! Don Allah Mama wallahi ba zan sake ba." 

        Har ga Allah jikina ya yi sanyi da zancen shi, uwa-uba yanayinsu duka da ya koma kalar tausayi. Wuri na nuna masa da nufin ya zauna, zama ya yi a ɗarare yana tsiyayar hawaye daga idanuwan shi da suka yi jawur saboda kuka. 

   

     "Kana so na mutu?"


        Tambayar da na fara jefa masa kenan ina ƙoƙarin goge hawayen da ke ta ambaliya a cikin idona, kai ya shiga girgizawa tare da faɗin, 

       "Ba na so!"

        "Kana so Allah ya ƙona ka?"

     A nan ma ya girgiza kai, "To idan har kana so na ci gaba da zama tare da ku, to kada ka sake shan taba daga yau har ranar tashin duniya. Domin duk ranar da ka sake shan tabar nan, ina tabbatar maka da cewa a ranar zan mutu, kuma muddin ka sake sha har na mutu kai ma za ka mutu ka je lahira a saka ka wuta. Kana so Allah ya ƙone ka saboda shan taba?"

       Girgiza kai ya shiga yi hawaye yana zarya kan fuskar shi har yana feso mini. Hannuna ya riƙe da hannunsa biyu yana faɗin,

       "Wallahi na yi alƙawari ba zan sake sha ba. Idan kuma na sake ki ce Allah ya kashe ni Mama."

         "Allah ya ba ka ikon dainawa. Kuma ya sa daga wannan shi kenan har abada. Idan kuma ka sake shi kenan da ni da kai duka za mu mutu a rana ɗaya."

      Rungume ni ya yi tare da fashewa da kuka yana faɗin, "Ba na so ki mutu don Allah kada ki mutu."

      Daga haka na cire shi jikina saboda warin tabar da nake ji yana tashi a hannunwansa. Wanka na ce ya je ya yi kuma dukansu su yi shirin zuwa islamiya. Sannan na fito ɗakin ba tare da na bi ta kan abincin da Ummu Salma ta kawo mini ba.

      Ɗakin Mukhtar na nufa, na ga ƙofar a rufe alamun ya fita. Sannan na dawo na yi wanka zuciyata a cunkushe da zallar nadamar auren Mukhtar a raina. Cike da takaicin haihuwar 'ya'yana ga wanda bai cancanta ba. 

      'Ashe ba namiji kaɗai ya dace ya nemar wa yaran shi uwa tagari ba har da mace.' 

        Zancen zucin da na yi kenan a zuciyata cike da tausayin matan da ke zumuɗin yin auren. Saboda da sun san tarin ƙalubalen da ke cikin auren, maimakon murna kuka za su yi. 

      Shigowar su Ummu Salma ya katse mini tunanin da na lula, saboda ko kayan da na fitar daga wardrobe ina riƙe da su ban saka ba. "Allah ya tsare na ce musu, tare da Addu'ar kariyar da nake yi musu koyaushe." 

      Har sun fita Haidar ya dawo ya durƙusa gabana tare da haɗa hannuwansa wuri ɗaya yana faɗin, "Ki yafe mini Mama. Na yi miki alƙawarin ba zan sake ba daga wannan."

        "Na yafe maka Haidar, tashi ka je Allah ya yi muku albarka dukanku."

       Ya fice yana yi mini bye-bye ina yi masa tare da murmushin jin daɗin farincikin Allah ya mallaka mini yarana, ba don iyawata ba kuma ba don na fi kowa ba. 

      "Alhmdulillah!"

    Ita ce kalmar da na faɗa sannan na miƙe na saka kayana, abincin na janyo na cakula kaɗan na ture. Sannan na fito falo mintuna kaɗan na fara jin ƙarnin taba yana tashi.

      Na miƙe na nufi ƙofar ɗakin inda hayaƙin da ke fitowa ta kusufar makullin ɗakin Mukhtar, haksn ya tabbatar mini da yana ciki. Tura ƙofar na yi babu shiri na ja baya ina toshe hanci, saboda gabaɗaya ɗakin ya turnuƙe babu abin da ke fitowa sai hayaƙin tabar. 

      Tari na fara yi ina kaɗe hayaƙin a fuskata har ya lafa, sannan na yi ƙarfin halin faɗin,

 "Idan ka gama ina son magana da kai."

        Da hanzari na koma falon na zauna ina sauke numfashi a wahale, don na kasa sabawa da warin tabar duk tsawon lokacin da muka ɗauka da shi. Bai fito ba tsawon lokaci sannan ya fito yana zuba ƙamshin turare, tare da haɗe fuska ya yi tsaye nesa da ni, fuskata babu yabo babu fallasa na ce da shi,

      "Zama za ka yi, don maganar ba ta tsaye ba ce."

     Ya zauna yana shan ƙamshi tare da faɗin, "Sauri nake yi akwai inda zan je. Idan maganar mai tsayi ce ki bari na dawo kawai."

      "Yanzu ya dace mu yi maganar, don haka yana da kyau ka san illar da ke cikin shan tabar da kake yanzu. Domin idan can baya ka yi babu yara, yanzu da suka fara mallakar hankalin kansu yana da kyau a ce ka daina. Saboda ci gaba da sha zai iya gurɓata mini tarbiyar da nake ƙoƙarin ɗora su a..."

       "Me kike nufi? Kina zaton ni na koya masa shan tabar? Ko kuma ni na ce ya zo ya ɗauka ya sha!?"

      Tambayar da ya jefo mini kenan a fusace, wanda alamu ya tabbatar ba za mu kwashe ta daɗi ni da shi ba. Saboda ba ƙaramar danna nake yi wa zuciyata ba, dalilin da ya sa ban zo da zafi ba saboda ina so ya fahimci abin da nake son nuna masa.

      "Ban ce ka ba shi ba, amma tabbas kai ka koya masa. Saboda kai ya ga kana sha shi ya sa shi ma ya fara gwadawa, domin ƙaramar ƙwaƙwalwarsa ba ta hango masa illar abin, saboda ganin  kana sha tunaninsa zai ba shi babu matsala a ciki. Don da akwai illa a ciki matsayinka na babba ba za ka dinga sha ba."


     "Oh! Kenan dai ni kaɗai suke ganin ina sha shi ya sa ya koya?" 

    

      "Kai ne dai kusa da shi, don haka ka taimaki yaran nan ka daina sha a gidan nan ko da ba za ka fasa sha duka ba. Sannan ka yi ƙoƙarin nisanta tabar a inda ka san za su gan ta su ɗauka. Saboda tarbiyya daga gida take farawa, kuma Iyaye su ne makaranta ta farko da suke bai wa 'ya'yansu karatun da zai fi shiga kansu."

     "Za a yi yadda kika ce!"

       Yana ƙare faɗar hakan ya miƙe ya fice da sauri saboda kiran da ake yi masa a waya, tun a lokacin da muka fara magana yana ƙin ɗauka. Ya bar ni zaune ina bin ƙofar da kallo, tare da sauraron maganar da ya yi a wayar kafin ya fita gidan.


     "Ga ni nan zuwa yanzu ki jira ni."


     Tagumi na yi ina goge hawayen da ban san lokacin da suka gangaro kan fuskata ba.

        'Habi ba ta san matsalar zama da irin wannan mijin naki ba, saboda labari ya zo mini har gida a kan riƙaƙƙen ɗan iska ne kuma ɗan shaye-shaye. Duk zaman da za ki yi da shi ba za ki taɓa samun farinciki ba sai kayan takaici da za ki yi ta kwasa kina jibga wa kanki. Amma tun da ta kafe a kan ba ta yarda a sake ki ba, to ki je ki ci gaba da zaman na zare hannuna a cikin sakin da nake nemar miki wurin shi. Don haka zancen zuwa kotun ma na ajiye ki je ki ci gaba da zaman haƙurin har Allah ya kawo miki ƙarshen shi.' 

   

     Maganar Baba Ali ce ta faɗo mini a rai, ranar da muka yi wani zama a lokacin da rikicinmu da Mukhtar ya yi tsananin da Baba Ali ya ce; na baro gidan Mukhtar na dawo Kebbi shi zai karɓar mini takardata a hannun shi, ko ta arziƙi ko ta tsiya idan ya ƙi bi ta lalama. Saboda ƙazafin da ya jefe ni da shi tun kafin na san MD kuma tun kafin na fara aiki a ma'aikatarsu.

       Daren ranar ma na yi shi ne da ƙunci tare da kai wa Allah kukana a kan ya kawo mini sauyi da mafita ta alheri.

       Da safiyar ranar Talatar, mai adaidaitan har gida ya ɗauke mu kamar yadda muka yi ajanda. 

      Fuskata a sake na shiga ma'aikatar saboda tuno abin da MD ya yi wa Sara, ban damu da kallon da mutane suke yi mini ba saboda na yi amanna da cewa, fiye da rabinsu ba za su yarda da ƙazafin da Sara ta jefo mini ba. Duba da yadda ban da sakewa da kowa daga matan har mazan, idan aka cire Amina da gaisuwar mutuncin da nake yi da kowa.


     Aikina na yi cikin natsuwa har ana gaf da tashi, sannan Amina ta shigo fuskarta ɗauke da murmushi ta zauna. Kallo na bi ta da shi ina 'yar dariya saboda tuno damben da muka sha ni da Fatima matar MD. 

    "Hajiyata! Me ya sa a cikin labaran da za ki ba ni ba ki sanar da ni kin iya faɗa da dambe ba?"

    Baki na rufe ina ƙumshe dariya saboda ba ƙaramar dariya maganar ta ba ni ba. "Ai faɗa zuwa yake yi, kamar yadda dambe yake afkuwa bagatatan ba tare da an shirya masa ba. Wataƙila hakan ce ta hana ni sako su a labarin, sai da suka zo da kansu kika gani domin ki tabbatar da komai zuwa yake yi a lokacin da aka rubuta. Yanzu dai na ga fuskar ki da yalwa, me ke faruwa ne? Ba ni na sha tun kafin ta sarare a iska."

       "Hmmmmm!" Ajiyar zuciyar da ta sauke kenan sannan ta ce, "Yau dai Mama ta amsa gaisuwata. Saboda 'yarta ta zo jiya kuma a gabanta na koma gidan, ko ɗakina ban shiga ba sai da na je wurin Mama domin ta san dawowata. Saboda wani lokaci faɗa masa take yi ta ce ban dawo gidan ba sai gaf da magriba. Dalilin hakan na tsiro zuwa wurinta idan na dawo domin ta san lokacin da na dawo ta daina haɗa ni da shi."


    "Ma sha Allah! In Sha Allah da sannu za ki ga komai ya zama tarihi. Saboda ko Bature ya ce; No condition is permanent. Babu abin da yake tabbace idan ba ƙudura da irada ta Ubangiji ba. Wanda yake kum-fa-kun ne da ya ce a yi komai zai tabbata babu jinkiri."

        "Na yarda da zancenki, kuma in Sha Allah zan ci gaba da haƙuri. Fatana kawai ta gane da wuri saboda ta daina ɗaukar zunubin da take loda wa kanta." Zancen da ta yi kenan bayan ta sauke ajiyar zuciya. Sannan ta ce, 

        "Yanzu nake ji, wai jiya Basiru ya ɗebo wa MD 'yansanda a kan ya mari matar shi. Shi kuma MD an ce ya maka Sara kotu, a kan ƙazafin da ta yi muku."


      "Subhanallah! Abin duka bai yi daɗi ba. Gaskiya da bai biye shirmen su ba. Saboda suna yi ne duka don haushin korar da ya yi wa Basirun. Da ya bar su don ko ba komai shi sama yake da su, kuma ya fi su mutunci a idon mutane, bai dace ya biye su girmansa ya zube a banza ba saboda hakan."

         "Ni ko sai na ga ya kyauta, saboda sun yi ne kawai don su ci zarafin shi. Amma nuna musu da ya yi ya fi su hauka, hakan zai rage wa iskancinsu kaifi. Don na tabbatar da ba su da kuɗin ɗaukar lauyan da zai ƙaryata abin da Sara ta faɗa a idon mutane."

        Sai da na sauke ajiyar zuciya sannan na ce, "Ba za ki gane ba Amina. Wani abin fa kana da ikon ɗaukar mataki kake haƙura, saboda illar da abin zai haifar maka ya fi amfanin shi ya yawa. Domin fallasuwar wannan abin zai taɓa ƙimar MD sosai wallahi, kuma ba zai gano hakan ba har sai an gama shari'ar tsegumi zai fara tashi a tsakanin mutanensa da bai yi tsammani ba. Amma idan ya haƙura ya ƙyale shi kenan komai zai wuce waɗanda suka sani ma za su manta. Saɓanin fallasar da za ta janyo labarin ya fantsama ta yadda goge tarihin zai yi wahala a zukatan mutane."


        "Lalle kin fi ni gaskiya Maman Haidar. Don haka ya dace ki yi wannan gudunmawar domin ki datakar da shi ko za a dace ya haƙura ya janye." 

      Shiru na yi ina nazarin maganar, saboda duk abin da zai haɗa ni magana da shi personally ba na so, amma idan aiki ya haɗa ko ɗar ba zan ji ba saboda babu yadda zan yi.  

      "Ba na son duk wani abu da zai haɗa ni da shi Amina."

        "To ki tura masa saƙo!"

Shiru na yi na ɗan lokaci, sannan na janyo wayata ba don ina so ba na tura masa saƙo kamar haka;

       

         'Ka yi haƙuri ka janye ƙarar da na ji ka saka. Saboda babu alfanu idan sirrin ya fallasu a idon waɗanda ba su san da shi ba. Maimakon kankare laifin, sai ka ƙara ɓanɓaro mana yamaɗiɗin mutane, garin neman gira za a rasa ido. Ba na jin kaina, amma ina jin takaicin ƙimarka ta taɓu ta sanadina.'


         Amina na bai wa ta karanta, sannan ta dawo mini da wayar tana faɗin.

     "Sannu gwanar hikima da azanci. Allah ya ba ki iya tsara magana da hangen nesa. Ina ma kaso mafi rinjaye na mutanen duniya haka suke. Da an samu rangwamen cakwalkwalin cakwakiyar da ya baibaye mutane a wannan lokacin da muke ciki. Ubangiji ya kawo miki mafita a cikin rayuwarki."





Amin Amina. Tare da sauran masu Matsala irin taku da ma wadda ta fi.👏🏻




D. AUTA CE✍🏼



*ABOKIN AIKINA*



*@HADIZA D. AUTA*



*SADAUKARWA: DAUGHTER ANUP*



*ASHIRIN DA ƊAYA.*


        Mun tattauna sosai da Amina, tana sanar da ni matsalar Basiru mijin Sara. Da irin tataɓurzar da aka yi da su a lokacin da suke ganiyar rashin mutuncinsu. Bayan an tashi muka fito bakin ma'aikatar muka tsaya, da niyyar neman adaidaita amma muka buge da hira. 

      Amina ta kalli agogon da ke hannunta ta ce da ni, "Yau dai na yi missing ba a tsakura mini komai daga cikin labarin ba. Ga shi na matsu na ji yadda ta kaya a lokacin da kika shiga ɗakin, domin ina so na ji me ya ba ki tsoro wanda ya sa kika yi salatin da, har yanzu ban daina jin sautinsa cikin kunnuwana ba."

      Baki kawai na riƙe cike da mamakin sharotan da take ƙoƙarin yi, domin kawai ta yi mini daɗin bakin da zai sa na ɗora mata labarin, daga inda na tsaya ban shirya ba. Cike da zolaya na ce da ita,

     "To ko za mu tsaya ki ji sauran kanun labarin ne?" 

      Cikin sauri ta dawo daga bakin titin da ta nufa tana ƙoƙarin tare wani ɗan adaidaitan da zai wuce. "Wallahi in dai za ki ƙarasa mini labarin yanzu, to na yarda mu kai wata safiya a nan ba tare da na ƙosa ba."

       "Rufa mini asiri kada ki sa Mama ta zo har wurin nan ta ci ubanmu."


      Dariya muka fashe da ita dukanmu, kafin na shammace ta na shige adaidaitan. Da hanzari ta matso inda nake tana faɗin, "Ji nake kamar na biyo ki mu je tare wallahi. Domin har ga Allah matse nake da jin labarin nan, kamar na yi tsuntsuwa na dira tsakiyar ɗakin domin na ga komai ba sai na jira an sanar da ni ba."

      "Ai kuwa dole ki jira har lokacin da za a sanar da ke, don haka mu haɗu goben kawai Hajiya ko shi idan da rabon ki. Domin haka kawai ba za ki janyo mini fushin Mama ba. Tsautsayi ya sa a binciko mata inda nake ta ci kwakwata, ni kin ga tafiya ta mu kwana lafiya ki gaishe da my boy."

     Daga haka muka tafi muka bar ta a tsaye tana aika mini harara har da ƙwafa. Hakan ya sa ko da muka yi nisa ban rufe bakina daga dariyar da ta ba ni ba, sosai nake tsintar kaina cikin farincikin a duk lokacin da muna tare, domin tana ɗebe mini kewar 'yar uwa macen da na rasa kuma ƙawa makusanciya.

 

***

     Mamaki fal raina a lokacin da na shiga gidan na yi tozali da kayansu Ummu Salma tsibe , na bi kayan da kallo cike da tunanin me ya kawo jakunkunan su a ƙofar ɗakina. Duk da oyoyon da suke mini bai sa na ɗauke kallona daga kan kayan ba.

     Da sassarfa na isa bakin ƙofar ɗakinsu ina murɗa handle idona ƙur a kansu, tare neman ba'asin dalilin da ya janyo hakan, tambayar da tun kafin na furta ta fito da kanta cikin ƙwayar idona.

       "Mu ma ko da muka dawo mun taras da kayan a wurin. Kuma har yanzu Abbanmu bai dawo ba balle mu ji ko shi ne ya fito mana da su."

     Ajiyar zuciya na sauke mai ƙarfi sannan na ce, "Ku ɗauko kayan mu je ɗakina, idan ya dawo mu ji me yake nufi."

       Da ƙyar na yi maganar saboda hadarin baƙincikin da ya taso ya rufe idona. Guguwar takaici ta sa ban iya ɗaukar komai daga cikin kayan ba. Domin har da katifunsu biyu tasu ita da Iman da ta Haidar.

     Sun shigar da kayan duka a lokacin da na kammala sallah, a kan kayan na ɗora idona saboda tunanin abin da yake nufi da abin da ya aikata. A take zuciyata ta hasko mini zallar manufar shi duk da bai faɗa mini ba, duba da kalaman barazanar da ya yi mini a ranar da ya tuna da haƙƙinsa da ke kaina.

     'Wallahi duk abin da ya biyo baya kada ki ga laifina. Ba dai kin hana ni haƙƙina ba? To ke kuma ki jira me zai faru cikin kwanan..'

      Maganar shi kenan da ta faɗo mini rai, kuma ta shiga kunnena tamkar a lokacin yake furta mini ita.

     "Waton aure zai yi?"

     Tambayar da na jefi kaina da ita kenan a fili, sannan wani murmushi mai sauti ya suɓuce mini ba tare da na shirya ba, saboda tabbacin da zuciyata ta ba ni a kan hasashen da nake yi. Nan take wani sabon kuzari ya ziyarce ni, wanda ya kore rabin damuwar da ya haifar mini a lokacin. 

       Ummu Salma na ƙwala wa kira, ta shigo ido tsakar ka bayan ta amsa kiran, sallayata na shiga naɗewa ina cewa, "Zo mu saita kayan nan. Kafin lokacin makaranta ya yi."

     Da Mamaki ta bi ni da kallo wanda ya nuna tambayar da take son yi mini, ina mata 'yar dariya na ce, "A nan za ku dawo da zama dukanku. Don daman can ina ta so ku dawo nan mu dinga kwana tare. Kafin lokacin da Haidar zai ƙara girman da za a ware masa makwancinsa daban."

     Farinciki mayalwaci ya ziyarci fuskarta, ta fara murna tana ƙwala wa su Haidar kira bakinta har kunne, ko da suka shigo ta fesa musu labari suka hau ihu, domin alamunsu ya bayyana jin daɗinsu a kan sabon tsarin da nake ƙoƙarin zartarwa. 

      

      Tare da su duka muka gyara ɗakin tsaf komai muka tanadar masa a muhallinsa, duk da katifar Haidar ba ta samu wuri ba dole jingine ta muka yi. Saboda an laƙume ɗan filin ɗakin da katifar su Ummu Salma, sannan da jakunkunan kayansu. Don ma na cire wasu na saka a wardrobe domin a rage tarkacen kayan. 

      Saboda suna da sutura sosai domin ba na ɗaukar lokaci ban yi musu ba, musamman Haidar da ko kan hanya na zo wucewa na hango yadin da ya burge ni, sai na saka an yanka masa ko da iya kuɗin jakata kenan. Wani kuma idan ban da kuɗin, cewa nake yi a yanka a ajiye mini. Daga baya na dawo na karɓa tun a lokacin da yake cin yadi ɗaya, har yanzu da yake shekara bakwai ya fara laƙume yadi ɗaya da rabi.

      Su ma atamfa ɗaya nake saya a ɗinka musu su biyu, saboda Ummu Salma shekararta goma sha biyu, Iman ce mai shekara tara. Domin tsakaninta da Haidar babu tazara mai yawa, kuma yana da jikin girma, don ya kusa kamo tsawon Iman.


      Bayan sun tafi makaranta da murna, na shirya na nufi gidan maƙociyata Maman Taufiƙ. Saboda na yi sha'awar ganin ta kwana biyu ba mu haɗu ba, daman can makulli ke sa ina shiga gidan idan yara sun bar mata. Ita ma halin Mukhtar da zargin da yake yi mata, a kan tana zuga ni ya sa ta rage zuwa gidanmu.

     Da fara'a ta tarbe ni muka zauna murmushi a kan fuskata muka gaisa, ta kawo mini molt da ruwa a faranti, sannan da doghnut a gefe. Domin ɗabi'arta ce da wuya a shiga gidanta a fito ba ta karrama mutum da abin da take da shi ba. Su Ummu Salma har ɗokin suke yi na aiko su wurinta, domin ba za su fita hannu rabbana ba sai ta musu alheri ko da babu yawa. 

 Saboda kaf unguwar babu inda nake zuwa sai wurinta, haka su ma babu inda nake bari su je sai gidan. Ko shi iya aiken da ya kai su kawai suke yi su fito, saboda maigidanta kullum yana gidan. Sannan a gaban kowa ba ta shayin nuna masa ƙauna sai dai shi mutumin da ya zo ya ji kunya, saboda yaronta ɗaya Taufiƙ kuma ya yi shekara sha huɗu har yanzu ba ta sake haihuwa ba. 

     Rayuwarsu tana burge ni sosai, saboda ta yi dacen mijin ƙwarai kuma wanda ya san muhimmancin aure. Dalilin da ya sa ba ta gano matsalar Mukhtar a yadda nake sanar da ita, ta fi ɗora mini laifi a kan wasu abubuwa ko da ta gani da idonta. Ganin take yi rashin tattalin miji ne yake janyo mini abubuwan da ke faruwa. Kayan mata babu kalar da ba ta ba ni, amma sai dai na ajiye ko na kyautar don ni babu amfanin da za su yi mini. 


     "Kwana biyu kin ɓuya!"


  Maganar da ta yi mini kenan a lokacin da na gutsura doghnut ina taunawa. "Shirye-shiryen zuwan amarya muke yi. Shi ya sa kika ji ni shiru, ga kuma aiki da yake hana ni zama kullum ina zarya kan titi."

      Kallo mamaki take yi mini sannan ta ce, "Wace Amarya kuma?" 

      "Amaryar Mukhtar!"

Amsar da na ba ta kai tsaye kenan, murmushi a kan fuskata. Baki a sake take kallo na bayan  tagumin da ta rafka, dariya na shiga yi mata alamun ko a jikina illa tsabar farincikin da nake ciki. Wanda ya kasa ɓoyuwa har sai da ya bayyana kan fuskata.


     "Yanzu ke don Allah a kan auren Mukhtar kike wannan murnar?"

      "Sosai ma! To miye cikin ido ban da ruwa? Ai inda akuyar gaba ta sha ruwa, ko ta baya idan ta zo a nan za ta sha."

      "Hmmmmm! Kina wasa da lamarin maza Maman Haidar. Ke a tunaninki abin da ya yi miki shi zai yi wa wata idan ta shigo?"

      "Sosai ma kuwa! Don ƙwaryar sama ce take dukan ta ƙasa. Kuma ni wannan auren ma da ina da dama har sadaki ni zan biya masa. Domin kawai ya gano na fi shi farinciki da ƙulluwar auren."

       "Lalle da sauranki har yanzu Maman Haidar. Ai wallahi ni da na ga ranar da Amini zai yi aure, gwara na ga ranar mutuwata."

       Dariya ta suɓuce mini babu shiri, da abun ya yi mini daɗi ma har da bajewa na yi a kan kujerarta riƙe da ciki. Saboda zancenta ba ƙaramar dariya ya ba ni ba, domin zurfin da ta yi a kan sha'anin maza, ya nuna har yanzu ba ta san zafin duniya ba.

      Natsuwar dole na gayyato, saboda yanayinta da na ga ya juya zuwa kalar tausayi.         

      "Ko ni na samu mijin ƙwarai wanda ya san zafina, wajibi ne kuma dole na yi kishin abuna. Amma kuma ba zan zafafa kishina irin haka ba, saboda ba gare ni aka fara ba kuma ba za a ƙare kaina ba. Sannan shi ɗa namiji, a duk lokacin da kika zafafa kishinki a kansa, matuƙar ba ki yi dace da mai dogon nazari da hangen nesa ba. To zai yi miki kallon wata shashasha wadda ba ta san abin da take yi ba, ƙarshe ma ya ce ba kya son zaman lafiya, ko kin cika fitina da janyo abin da zai kawo muku faɗa. Saboda a lokacin idonsa a rufe yake da son auren, duk abin da za ki yi masa ba zai burge shi ba, matuƙar ba goya masa baya za ki yi a kan auren ba."  

        "Ai kuwa wallahi sai dai kada ya gani, domin ba zan taɓa goya masa baya ya yi mini kishiya ba. Cabɗijam! Allah kada ya nuna mini wannan ranar, don na san tun kafin lokacin auren ya yi zan mutu saboda mugun kishin Amini da nake yi. Shi ma ya sani ba zai taɓa zo mini da irin wannan zancen ba."


      Shiru na yi ina kallon ta, domin idan akwai naƙasunta da na sani duniya bai wuce kishi ba. Kuma ina yi mata uzuri saboda shaƙuwar da ke tsakaninta da Aminin mijinta. Wanda saboda tsabar so da shaƙuwar da ke tsakaninsu yake kiran ta Aminiya ita ma ta kira shi Amini.

      "Ni dai kam! Ko a kwalar rigata Maman Taufiƙ. Idan zai yi huɗu a rana ɗaya wallahi babu abin da zai ɗaga ni sama balle ya buga ni a ƙasa. Tsuntsun da ya ja ruwa shi ruwa kan doka. Kuma wanda duk ya ce zai iya haɗiye gatari ya dace a riƙe masa ɓota."


      "Wallahi Zaituna kina ba ni mamaki, shin wai ba auren soyayya kuka yi da Abban su Haidar ba?"

      "Soyayyar gaske ma, irin ta bugawa ga jarida a yi talla. Amma yanzu, ƙiren sonsa ba na ji a cikin zuciyata, kamar yadda ko wulagawar shi na hango daga nesa, sai na ji haushin sa ya yi mini rumfa."


       "Anya ba namijin dare ne yake aurenki ba?" Tambayar da ta jefo mini kenan na ba ta amsa.


     "Idan ma shi ne ya burge ni, domin ya nuna zallar kishin da yake yi mini wanda ba ya son kowa ya raɓe ni. Domin ina da tabbacin zai ba ni kulawar da za ta gamsar da ni, kuma zai hana ni kukan kaɗaaicin da nake yi yanzu."

        "Hu'ummm! Kin yi nisa Zaituna, amma ni kam har abada ba na fatar Amini ya yi mini kishiya ko da a mafarki. Ke akwai wata da ta so zautar da ni a kan nacin da ta yi masa ya aure ta, don bala'i macen da yaranta har sun je jami'a. Wai a haka ta nace masa dole sai ya aure ta tun da mijinta ya mutu ya bar mata gado. Ai na rantse da Allah ranar da na gano, daga ni har shi ba mu yi bacci ba, asubar farin na bar garin nan na yi Kano. Domin gabaɗaya idona rufewa suka yi ba na hangen komai a lokacin face mutuwata. Abin baƙinciki kuma babu wanda ya goya mini baya a gidanmu, sai laifina da aka dinga gani ana ƙoƙarin nuna ya fi ni gaskiya. Sun kasa gano zafin da nake ji idan na tuno girman matar da manyan 'ya'yanta. Don akwai wata 'yarta da ta ci ta ƙoshi, wadda ko yanzu aka ce ta haifi yara uku ba zan musa ba. Amma wai a hakan take son Amini ya aure ta don baƙar zalama irin ta wasu ƙattin mata."






🤭sannu Maman Taufiƙ😂



D. AUTA CE✍🏼


*ABOKIN AIKINA*


*@HADIZA D. AUTA*


*SADAUKARWA: DAUGHTER ANUP*


*ASHIRIN DA BIYU.*

        Dariya na sha sosai har ta nemi ƙulle mini ciki, saboda maganganun Maman Taufiƙ sun saka ni dariya ba tare da na shirya ba. Fuskarta na kalla bayan na gama dariyar, hadarin da fuskar ta ɗoro tare da ƙwafar da na ga ta yi, alamunta ya nuna mini har lokacin kishin matar bai daina cizon ranta ba.
        "To ke Maman Taufiƙ, ai ita ce ke son shi idan na fahimci labarin da kyau. Da kin bari an yi auren, wataƙila da yanzu har mu maƙotanki mun je hajji. Saboda bauta ce kawai za ta zo yi miki tun da kin fi ta power a wurin Baban Taufiƙ." 
        "Hmmmmm! Ba za ki gane ba!" 
        Zancen da ta yi kenan tana haɗe fuska tamkar ta yi kuka, kafin ta cire tagumin da ta rafka hannu bibbiyu ta sake cewa, 
         "Kin san me? Ko da za ta kwanta ƙasa na dinga taka ta da ƙafafuwana saboda biyayya, ba zan taɓa cire takaicin ta a raina ba. Wai ko ki san yadda nake kishin Amini kuwa? Ke ni fa da dai a ce ya haɗa ni sharing ɗinsa da wata, gara kawai ni na haƙura na bar wa kowace ce shi. Na fi son haka da a ce na zauna baƙinciki ya kashe ni."
      "Ba fa za ki mutu ba! Matuƙar ba ke ce kika ƙwallafa wa kanki hakan ba. Saboda duk abin da kika gani daman can muƙaddari ne daga Allah, don haka ki daina zafafa kishinki gudun ki saka kanki matsala a banza."
     Na yi maganar cike da burin saka mata ƙwarin gwiwa a zuciya, sai dai ko kaɗan zancen bai yi tasiri ba. Domin idonta a rufe ta ce da ni,
      "Ni fa komai za ki faɗa in dai a kan zancen kishiya ne, to ba zan fahimta ba balle na gane.  Don haka mu bar zancen kawai raina suya yake yi sosai wallahi." 
        Shiru ya ratsa tsakani sannan na sauke  ajiyar zuciya, bayan na dawo daga zuzzurfan tunanin da na lula, a kan tashin hankalin da za ta shiga a lokacin da ta ji Baban Taufiƙ yana neman aure, domin da idanuwana na gan shi da wata bazawara a bayan layinmu suna taɗi.   
       Saboda kusa da gidan su bazawarar nake zuwa kitso, da tunani fal raina na shiga gidan a lokacin, bayan zancen zucin da nake yi. Ina ta jefa wa kaina tambayoyin da ba amsa, a kan miye haɗin shi da ita? Duk da yanayinsu ya bayyana mini zahirin abin da ya haɗa sun. Amma ban gasgata ba sai lokacin da bazawarar ta shigo gidan ana tsaka da yi mini kitso, mai kitson tana 'yar dariya ta ce da ita,
     'Har ya tafi?' Ita ko bakinta har kunne ta zauna tana faɗin, 
      'Ya tafi! Ai mutumin ya san kansa, sosai yake da qualitys ɗin da nake so, kuma nake fatar samun su a wurin namijin da nake muradin ya zama mijina. Yanzu haka duk da ba mu jima tare ba, amma ya nuna mini shi ba ya son a ja lokaci. Idan na shirya wata biyu masu zuwa a yi komai a gama.'
     'Caɓji! Lalle wannan da zafinsa ya zo.'
       
      Haka na yi ta tuno hirar bazawarar da mai kitsona, wadda har suka ci suka cinye ban ce da su ƙanzil ba. Saboda ba na so na katse musu zancen, sannan kuma ba zan iya shiga sabgar da ba a kasa ta da ni ba.
      'Yanzu idan ta ji wannan batun ya za ta yi?'
      Tambayar da na jefi kaina da ita kenan, wadda ban samu amsarta a zuciyata ba na fara jiyo sallamar da su Ummu Salma suke ta rafkawa.
       Tare muka amsa musu ni da Maman Taufiƙ, sai da aka ba su umurni sannan suka shigo. Gayar da ita suka fara yi ni ma suka gaishe ni, na miƙa musu makulli  suka fice suna faɗin sai na zo.
       Ajiyar zuciya na sauke sannan na ce da ita, "Wallahi kin sa jikina ya yi sanyi Maman Taufiƙ. Saboda har raina, ba na jin daɗin zafin kishin nan naki, da ina da iko da na rage miki shi ko da kaɗan ne. Domin ina jin tsoron abin da zai faru a lokacin da ƙaddarar aure ta haɗa Baban Taufiƙ da wata."
         "Innalillahi wa inna ilaihirraji'uun! Don girman Allah ki daina ambatar wannan magana, kada tsautsayi ya sa 'yan amin su amsa ki janyo mini masifa. To idan ma wannan ne in Sha Allah babu shi babu aure nan gaba, saboda ni kaɗai na ishe shi rayuwar duniya, kuma ni kaɗai yake da buri zama da ni. Baya hangen kowace mace balle ya yi mata kallon daraja, saboda Allah ya karɓi addu'ar da nake yi masa koyaushe. A kan duk matan duniya, fuskarsu ta koma ta akuyoyi a idonsa, balle ya ga kyawunsu ya ƙyasa ya ɗauko mini jangwam!"
           "Hmmm! Kin fi ƙarfina Maman Taufiƙ! Ni zan tafi don babu amfanin duk wata maganar da zan ƙara yi a kan hakan. Saboda kin fi ƙarfina, amma duk da haka, na yi alƙawarin zan dinga yi miki addu'a a kan wannan kishin balbal, domin ina da burin Allah ya rage miki shi ki samu sukunin zuciya ko don ki ji daɗin fuskantar rayuwa."
         Zancen da na yi mata kenan a lokacin da na miƙe, fuskarta a haɗe ta rako ni tana faɗin, "Ban ji daɗin wannan zuwan ba, domin kin fama mini mikin da na daɗe ina jinyar zuciyata kafin ya warke."
          "Kwantar da hankalinki, in Sha Allah sai kin daɗe ba ki gan ni cikin gidan nan ba. Sai dai kuma hakan ba shi zai hana ni yi miki fatan shiriya daga wannan azababben kishin naki ba."
       Ina gama faɗin hakan na fice gidan, ta raka ni da faɗin, "Kishi halas ne! Ke da ba kya yi kuma ai kin hutar da kanki daga ladar da ake samu."

        Dariya na ƙumshe gudun ta ga damata, sai da na shiga gida sannan na tuntsure da dariyar tamkar wata zautacciya, 'Waton shi ma zazzafan kishin miji ibada ne da ake samun lada a ciki idan an yi?' Tambayar da na yi wa kaina kenan ina dariya. 
        "Wallahi sai dai kada na samu wannan lada, da dai a ce na yi kishin Mukhtar irin haka. Cabɗijam! Da sake!"
      Maganar da na yi kenan a fili lokacin da nake shiga falon, kiran sallar magrib da na ji an fara yi ya sa na ce da yaran,
 "Oya a tashi a yi sallah."
          Sannan na shige ɗakina na faɗa toilet. Har na gama sallah tunanin hira ta da Maman Taufiƙ nake yi, ban tashi daga kan sallayar ba sai da aka yi Isha. Na daɗe ina yi wa Maman Taufiƙ addu'a tamkar damuwarta ce kaɗai abin da yake damu na. 
     wayata na ɗauka na fito falo inda su Ummu Salma, tare muka ci abinci da su ina duba saƙonnin da ya tarar mini. Waɗanda suke buƙatar amsa ta dole, saƙon MD na fara buɗewa raina  a haɗe tamkar yana gabana. 
        'Na gamsu da hangen nesanki. Kuma in sha Allah na janye ƙarar daga yau. Na gode sosai!'
        
     Mere na yi kaɗan sannan na tura masa 'Ana tare!'  
          Daga haka ban sake bi ta kan shi ba duk da yana online a lokacin. Bugun da ƙirjina yake yi, ya sa na bar WhatsApp na koma facebook. Saboda a duk lokacin da na hango sanarwar da ake yi mini a kan yana online, sai na ji gabana ya ƙire ya faɗi dam-dam!
       
      Bacci ya ci idona, ban san lokacin da Mukhtar ya dawo gidan ba, sai da safiya ta waye muna shirin fita. Sannan na hango shi ya nufo ɗakin su Ummu Salma ya buɗe da makulli ya shiga, jim kaɗan sai ga wani garjejen ƙato ya shigo da bokitin fenti biyu a hannunsa ya shige ɗakin. Mintuna kaɗan wani ya ƙara shigowa da wasu bokitan ya shige.
       Raina ya fara turirin baƙinciki, saboda haushin shigowar mutunen ba tare da Mukhtar ya sanar da ni ba, domin a tunanina ko ba gidan aure ba ne, yana da kyau a sanar wa masu gida wasu gardawa za su shigo, domin su kimtsa. A matsayin su na mata ko ba su da aure, tun da ba maza ne danginsu ba balle a ce duk ɗaya ne.
        Zuciyata ta zo wuya, na dinga ji kamar na shiga na shaƙe wuyan Mukhtar a gaban mutanen, kuma na gasa masa baƙaƙen maganganun da ke cizon raina. Da ƙyar na iya furta 'Innalillahi wa inna ilaihirraji'un!' A zuciyata, domin na samu sauƙin da nake ji, dangane da ingizanin da take yi, a kan na yi abin da zai rage mini takaicin da aka ƙumsa mini.
      A gurguje muka shirya muka fice gidan, daga ni har yaran babu wanda ya bi ta kan shi, ko mai adaidaitan a kan hanya ya haɗu da mu ya ɗauke mu, saboda gudun na yi jinkirin jiran shi cikin gidan, na aikata aika-aikar da zan raba halina a gaban gardawan.

        Raina a jagule na kammala aikin da na taras ofishina, ko da Amina ta zo ta daɗe ban ce da ita uffan ba bayan gaisuwar da muka yi. Har sai da ta kasa haƙuri ta ce da ni, 
       "Yau dai kamar an sake taɓa mana ke?"
      Shiru na yi mata tsawon lokaci, sannan na sauke ajiyar zuciya tare da fesar da iska a bakina na ce, "Ina muka tsaya a labarin?" 
         "Inda kika shiga ɗaki"
    Amsar da ta ba ni kenan a taƙaice cikin sanyin murya. Na cire gilashin da ke sanye a idona, sannan na gyara zama na ce da ita,

     _"Baƙin tozalin da na yi ya sa na yi salatin da na yi babu shiri. Saboda falona babu komai a ciki face ledar tsakar ɗaki da agogon da ke manne jikin bango, da sassarfa na yi ƙuryar ɗakin, a nan ma sai da jiri ya so kayar da ni. Bango na yi hanzarin kaiwa na jingina bayana ina sauke numfashi da sauri da sauri. Nauyin da ƙafafuwana suka yi mini, ya janyo na kasa ɗaukar kaina a hankali na sulale na yi ƙasa. Zaman dirsham na yi rungume da Ummu Salma da ke baccinta sharkaf ba tare  da ta san wainar da ubanta ke toya mini ba._
         _Na jima ina karanta wasiƙar jaki kafin Mukhtar ya shigo da guntuwar sallamar shi, ban iya ɗaga kai na kalle shi ba balle na samu kuzarin amsa masa sallamar da ya yi. Zama ya yi kusa da ni ya miƙe ƙafa tare da janyo mu jikin shi, na yi hanzarin sakar masa Ummu Salma sannan na miƙe tamkar wadda aka tsikari. Jikina yana rawa tamkar mazari muryata tana harɗewa na ce da shi,_
          "Ina ka kai mini kayana!? Ka yi gaggawar dabon fito mini da su yanzun nan, kamar yadda suka yi ɓatan dabo a cikin gidanka. Domin na tabbatar da ka san yadda aka yi suka salwanta, shi ya sa kake gwara kan mutane ka dinga zagaye-zagayen ƙarya!" 
         _Na ƙare maganar muryata a sama numfashina yana hawa da sauka saboda tsananin ɓacin ran da na shiga. Kansa ya duƙar ƙasa ba tare da ya ce da ni komai ba, mintuna a tsakani na fara jin sharɓen kukan shi. Mamaki fal raina na bi saman kan shi da kallo, domin idan ba kunnuwana ne suke ƙoƙarin yaudarata ba, to tabbas na ji sautin kukan shi. Lallaɓawa ya yi a hankali ya ajiye Ummu Salma, idona a kan shi har ya durƙusa a gabana gwiwa biyu, tare da haɗa hannuwansa wuri ɗaya yana sharɓar kukan da ya saka jikina yin sanyi. Kafin ya samu kuzarin yin magana cikin muryar kuka ya ce,_

        "Ki yi haƙuri ki yafe mini, saboda na san na yi miki laifin da na cancanci duk wani hukunci daga gare ki. Amma don alfarmar Ubangiji da darajar Manzonmu Annabi Muhammad Sallallahu alaihi Wasallama ki yafe mini. Ta wannan hanya ce kaɗai idan kin yafe mini zan iya ba ki labarin dalilin da ya sa na sayar da kayan nan, wanda ko ke kika ji za ki iya ba ni da kanki ki ce na sayar domin daga ni har ke cigaban namu ne. Don haka don Allah ki yafe mini ba don halina ba, saboda matsin da na shiga wurin nemo mafita ya sa na sayar da kayan nan. Kuma na tabbatar da idan kika ji za ki amince da kanki ki ce na je na sayar domin mu rufa wa kanmu asiri."
        _Jikina ya yi sanyi ƙalau! Saboda maganganun shi sun shiga jikina, kuma ratsa zuciyata sosai. Saboda idan akwai abin da ba na iya kaucewa a duniya, shi ne a haɗa ni da Allah a kan abu. Komai hawan da na yi sai na sauko saboda ba na kauce tayin alfarmar da duk aka haɗa ni da roƙon Allah. Sai dai kuma zama da shi ya fice mini a rai, duk da na ƙudurta yafe masa laifin kamar yadda ya roƙa. Tsayuwata na gyara, sannan na sauke hannuna ƙasa daga rungumar da na yi musu a ƙirji, tare da kawar da kaina gefe bayan na riƙe ƙugu na ce da shi,_
      
        "Zan yafe maka kamar yadda ka roƙa, amma sai ka yi mini alƙawarin za ka yi abin da zan nema daga gare ka. Saboda zuciyata ba za ta taɓa yarda da kai a matsayin miji ba, ka sauwaƙe mini kawai cikin ruwan sanyi ba tare da kowa ya sani ba. Ni kuma na yi maka alƙawarin zan yafe maka duk kayan da ka salwanta mini. Don haka ka ba ni takardata yanzun nan gobe idan Allah ya kai mu lafiya na koma inda na fito. Kuma komai za a yi ba zan fasa wannan ƙwan ba balle wani ya ji warinsa, amma fa idan ka sallame ni cikin mutunci ba tare da wani ya ji ko ya sani ba. Domin Wallahi ba zan iya zama da miji irinka ba."
      "Don Allah! Don girman Allah ki yafe mini Zaituna! Wallahi ba zan iya sakinki ba ko da za a ɗora mini wuƙa a wuya." 
       _Ya ƙare maganar tare da riƙo hannuna yana cisgar kuka tamkar zai shiɗe. Ƙwace hannuna na yi sannan na tura shi ya faɗi ta baya, saboda tsabar takaicin da ya ba ni. Amma hakan bai hana shi furta mini  cewa,_

       "Gara kawai ki yi mini duk abin da kike so a matsayin huce haushin laifin da na yi miki, idan ma dukana za ki yi na shirya karɓar hukuncin kowane irin duka daga gare ki, amma ba zan taɓa yafe wa kaina ba muddin na yi abin da kike so. Na fi so na mutu, ko kuma duniya ta Allah-wadai da ni, a kan abin da na yi miki da a ce na sake ki."
       
       



Uhumm! Maza mutanenmu😊




D. AUTA CE✍🏼

*ABOKIN AIKINA*


*@HADIZA D. AUTA*


*SADAUKARWA: DAUGHTER ANUP*


*ASHIRIN DA UKU.*

       _Kallon takaici nake aika masa ta gefen idona, hawaye yana zarya a kan dandamalin fuskata. Duk da maganganun shi sun saka zuciyata rauni, sannan kukan da yake sha tamkar wani ƙaramin yaro, ya saka ni jin lalle akwai babban dalilin da ya sa shi sayar mini da kaya dole. Tsayuwata na gyara tare da zuƙe majinar kuka na ce,_
       "Me ka yi da kuɗin kayan? Sannan wace lalura ce ta janyo ka salwantar mini da kaya ba tare da sani na ko na Iyayena ba?"
       _Miƙewa ya yi daga durƙushen da ya yi, ya iso inda nake ya riƙo hannuna. Ya zaunar da ni  bakin gefen ƙwalluwar katifar da ta yi saura a cikin ɗakin, shi ma ya zauna tare da rungume ni jikin shi yana share mini hawayen da suka kasa tsayawa a kwarmin idona. Sannan ya goge na shi da gefen hannunsa, tare da kama hannuwana duka biyu ya riƙe gam-gam! Kamar wanda yake gudun na tsere masa._
      
       "Na san ban kyauta ba saboda ban yi shawara da ke ba kafin na zartar da hukunci. Amma ki sani wallahi Allah ya sani ban da wata mafita ne shi ya sa na yi hakan."
        _Ajiyar zuciya ya sauke mai ƙarfi sannan ya sake cewa,_ "Kamar yadda kika sani, wurin da nake aiki ba wani albashin kirki ake ba ni ba. Saboda matsayin ajiya nake yi a wurin har zuwa lokacin da zan ƙara karatu, domin a ba ni gurbi mai kyau da karatun da zan ƙaro idan na gama. Shugaban wurin namu ya uzzura mini a kan ko na ƙaro karatuna, ko kuma su canza ni da wani mai manyan takardu.
      Dalilin da ya sa na shiga neman kuɗin registration kenan ido rufe, lungu da saƙo kusufa-kusufa a cikin faɗin garin nan ban  samu ko dubu biyar ba. Har na gaji da gantalin neman bashi ga shi taimako ya yi ƙaranci ga mutane yanzu. Ga kuma karatun yana buƙatar kuɗi masu ɗan kaurin da zai wadata, kuma ana saura ƙiris a rufe sayar da foam ɗin a lokacin. Wannan dalilin ya sa na shiga damuwa tare da neman ta wace hanya zan samu kuɗin nan, saboda tsoron na rasa aikin kuma na zo mu rasa ya za mu yi ni da ke a cikin gidan nan. Tunanin sayar da firij da telarki ya zo mini, shi ne ya sa har na kira ki a lokacin na yi miki zancen. Duk da kin nuna kada na taɓa dole ta sa na sayar da su, sai dai abin haushin kuɗin ba su kai ko rabin na registration ɗin ba. Tunanin na haɗa da kayan gadonki ya faɗo mini, da nufin duk lokacin da na samu sarari na saya miki wasu idan buƙata ta biya.
       Dalilin da ya sa na saka su kasuwa kenan domin mu samu abin da za mu rufa wa kanmu asiri. Shi ne na sayar da kayan na yi kuɗin registration, amma ki kwantar da hankalinki in sha Allah cikin kwanan nan zan saya miki wasu. Saboda ba zaune nake ba akwai buge-bugen da nake yi, idan Allah ya saka mana hannu komai zai wadata gare mu da yardar Allah."

     _Shiru ya ratsa tsakani bayan dire maganganun shi, na shiga nazarin dalilin da ya janyo kayana suka salwanta. Sai dai ni a nawa hangen da ya yi shawara da ni, da ban ji rabin zafin da na ji yanzu ba. Saboda ni kaina ina buƙatar cigabansa, kuma ina fatar ya samu rufin asirin da zai riƙa ni ni da jinjirar 'yata Ummu Salma. Ajiyar zuciya na sauke mai ƙarfi sannan na ce da shi,_
       "Tabbas! Ranar biyan buƙata rai ba a bakin komai yake ba. Amma da ka yi shawara da ni tun farko ba za a rasa yadda za a yi ba, domin ina da tabbacin zan samo nama kuɗin registration ɗin ba tare da an taɓa kayana ba. Saboda ni yanzu ban san da wane baki zan yi wa su Umma bayanin yadda kayan suka yi b..."
      "Ni ma ba na son ki yi musu bayani, don Allah ki bar zancen nan a tsakanina da ke ba tare da kowa ya sani ba. In da hali ma ki nuna kawai ni da ke ba mu san yadda suka yi ba, idan ta kama ma za mu ce ɓarayi ne suka sace a lokacin da ba na garin. Don Allah ki yi mini alƙawarin ba za ki tona cikin wannan magana ga kowa ba,  har da Umma don Allah kada ki bari ta san gaskiyar maganar nan!."
       
     _Gabaɗaya ya ɗaure ni da jijiyoyin jikina, na shiga tunanin maganganun shi tare da yadda zan fuskanci lamarin a tsanake. Domin na kare shi ba tare da an gano shi ne ya yi sanadin rasa mini kayan ba, amma na san duk abin da zan faɗa ba zan fita daga wannan laifin ba. Matuƙar ba gaskiyar zancen na tona ba domin na wanke kaina. Haƙiƙa zuciyata ta yi amanna da tsayuwa kai-da-fata, domin na yi masa garkuwar da za a kasa hango laifinsa, balle a jefe shi da wata maganar da ransa zai ɓaci."_
       _Da wannan tunanin na kwana cikin raina, shi ko lallaɓa ni kawai yake yi tamkar wata sabon ƙwai har baccin ya ɗauke ni. Tun da safe ya fice gidan ko kayan cefane aiko mini ya yi a lokacin da rana ta take, domin na fahimci ko ido ba ya son mu haɗa kafin ya fita. Hakan ya sa jikina ya yi sanyi na tabbatar da cewa dole ce ta sa shi ya yi mini hakan, duba da yadda yake jin nauyina kuma yake jin kunya ta a kan abin da ya aikata mini._  
      _Ban san ya aka yi ba, mahaifiyar shi ta shigo ɗakin fuskarta a haɗe, tare da yin tagumi tana ƙare wa ɗakin kallo. Kafin ta yi magana cikin sanyin murya tamkar ta yi kuka._

      "Don Allah ki yi haƙuri Zaituna, wallahi ban san wainar da yake shukawa ba sai yanzu da ya shiga yana yi mini bayani. Saboda a lokacin da na ji ana ɗibar kayan ana sakawa mota, sai da na kira shi na tambaye ina za a kai miki kaya. Kai-tsaye ya ce da ni daga gidanku aka aiko ɗauka, za a canza miki sababbi kafin ki dawo. Da wannan maganar ya rufe mini baki kuma ya toshe ƙofar zargin da ya shiga kaina. Don Allah ki yi haƙuri Zaituna, kuma in Sha Allah yau-yau ɗin nan duk inda zai nemo miki wasu kayan sai ya yi ko na tsine masa albar..."
       "Haba-haba! Ai abin duka bai kai can ba Innar Hanafi. Ya yi mini bayanin komai tun jiya kuma na gamsu, don haka kada ki damar da kanki a kan hakan. In sha Allah babu abin da zai faru domin ba zan bari kowa ya san yadda gaskiyar abin yake ba. Kuma ya ce zai san yadda za a yi kafin hankalin mutane ya kawo kan kayan."
     
        _Hawaye ta shiga sharewa da gefen mayafinta sannan ta fice gidan tamkar ta kife saboda sauri, domin fuskarta a haɗe take babu alamun wasa. Hakan ya tona asirin takaicin ta a kan abin da Mukhtar ya aikata mini ba tare da sanin ta ba._
       _Bayan fitar ta da mintuna kaɗan ta aiko na rufo ɗakin na zo tana nema na, na yi wa Ummu Salma wanka na shirya ta tsaf tana zuba ƙamshi muka yi gidan. Haƙuri ta ƙara ba ni sannan ta roƙe ni da Allah kada na bari wani ya san da maganar, a cikin 'yan'uwana ko nasu. Saboda abin kunya ne da gori kawai hakan zai janyowa tare da faruwar abin da ba a yi tsammani ba. Don ta nuna mini muddin gidanmu aka sani rikici zai iya ɓallewa sanadin hakan, a ƙarshe ma abin ya shafi aurenmu._
      _Har raina ba na fatar rabuwa da Mukhtar a lokacin, ko sakin da na nema ƙarfin hali ne kawai na yi domin na rage ƙunar da zuciyata ke yi._
       _Daren ranar a gidansu Mukhtar na wuni, duk wanda ya zo a nan yake iske ni mu gaisa. Domin ko cefanen da ya aiko a nan na yi girkin ƙannen shi da Sajida ɗiyar Yayar shi suka taya ni. Domin Innar Hanafi tun da muka gama magana ta fice gidan, ba ta dawo ba har sai da duhun marece ya fara kawo jiki. Sannan ta zauna tana sauke numfashi, ina lura da fuskarta har da 'yar rama ta yi. Cike da mamakin me ya jigatar da ita take ta sauke numfashi alamun gajiya a tattare da ita._ 
     _Abinci na kawo mata ta ci tana saka mini albarka, bayan ta gama ci ta ja  ni ƙuryar ɗakinta  ta ce na zauna. Cikin sanyin jiki na zauna zuciyata cike da tunanin abin da take ƙoƙarin sanar da ni, wanda ba ta so kowa ya ji daga ni sai ita sai Allah._
       "Zaituna! Ina ƙara ba ki haƙuri a kan laifin da Mukhtar ya aikata miki. Kuma don Allah ki yafe masa don ko kaɗan bai yi miki adalci ba. Sannan abu na biyu da nake son sanar da ke, ki yi haƙuri a kan abin da za ki gani a ɗakinki. Na je na ƙulla da ƙyar na samo miki gado da kujeru, domin ba na farinciki mutane su taras da ke a yadda na gan ki babu komai sai faƙon ɗaki. Kuma don Allah kada ki bari hakan ya janyo muku tashin hankali ko ki ce za ki yi zuciya watarana ki sanar da Ummarki. Saboda muddin ta ji wannan magana ba za ta sake ganin girmansa idonta ba, kuma in Sha Allah sai ya biya ki kuɗin kayanki ko da arziƙi ko da tsiya-tsiya."

       _Har ga Allah tausayinta ya kama ni, duba da yadda ta ɗaga hankalinta sosai a kan lamarin. Kuma kayan da ta faɗa na yi haƙuri da su, hakan ya nuna mini ita ce ta yi fafutukar nemo mini su, domin ta wanke kaso biyar a cikin goman laifin da Mukhtar ya aikata mini._
        _Cike da ladabi na nuna mata babu komai kada ta damu, domin na ƙudurta komai za a yi mini a gida ba zan faɗi abin da zai sa a gano laifin Mukhtar ne ba._
      _Sai da na yi sallar Isha sannan ƙannen shi suka raka ni ɗauke da Ummu Salma Sajida da kular abincin shi a hannu. Wanda na dawo takanas na ɗauki kula sabuwa na zuba masa, don Allah ya tsare bai taɓa mini kayan kitchen ba, sannan kuma na dawo da wasu sababbin da Umma ta saya mini na ƙara da waɗanda nake da su._ 
   
      _Ƙwalla na shiga gogewa bayan ƙannensa sun tafi Sajida ma ta bi su sun fice. Na shiga dudduba kujerun da na gani a falona, sannan na nufi ƙuryar ɗaki na ga sabon gado da wadrobe har da madubi. Duk da ba su kai darajar nawa ba, amma har zuciyata na ji daɗin ganin su kuma na  yi farinciki._
      _Wanka na shiga sharp-sharp na kammala, sannan na feshe jikina da turaruka masu sanyi, na mulke jikina da wata shu'umar humra mai taken 'Yar Sakkwato.  Saboda kayan matan da aka ɗirka mini da kazar ƙarin ni'imar da na ci, sun sa na ji ina kewar Mukhtar tare da zumuɗin ya kasance ni a raina. Kuma na yi alƙawarin zan faranta masa a daren ranar ko don Innar Hanafi, saboda ba ƙaramin daɗi na ji a kan kulawar da ta ba ni ba. Saɓanin baya da ba ta sake mini fuska tun bayan rikicin abincin da suka ce ina ba su kaɗan._

      _Ban san na yi bacci ba sai da na ji ana shafa jikina, firgigit na farka tare da motsawa amma na kasa. Saboda Mukhtar da na ji ni gabaɗaya ya matse ni, sai aikin shinshina ta yake yi tamkar wani ƙaramin bunsuru. Don ko bai faɗa ba na sani turarukan da na saka a jikina ne suka zautar da shi. Idanuwana a rufe ina karɓar saƙon da yake ƙoƙarin aika mini na ce da shi; abincin shi yana falo bai ci ba, cikin wata maƙalalliyar murya ya sanar da ni ya ci tun ɗazu._
       _Ya miƙe jikin shi yana rawa ya yi nesa da Ummu Salma da mu zuwa ƙarshen gadon, sannan ya dawo gefena ya janyo ni jikin shi ya shiga yamutsa ni. Nan take ya saka ni shiga sabon yanayin da ban taɓa jin kaina a ciki ba, cike da zumuɗi na shiga mayar masa raddin abin da yake yi mini a ruɗe, saboda gabaɗaya na ƙagu ya shiga jikina na huta da zut-zut ɗin da nake ji. Cikin sa'a ya yi dabarar jefa alƙalamin shi da ƙyar ya shige, abin mamaki luf ya yi mini a jiki babu wani motsin kirki. Sai sauke ajiyar zuciya da yake yi wata bayan wata, ba tare da ya motsa jijiyar shi cikin jikina ba.  A hankali ya zare jikin shi ya yi gefe yana ta sauke numfashi. Shiru na yi ina jiran ya dawo gare ni saboda a ƙagauce nake da shi a lokacin, babu zato na fara jin minsharin shi yana tashi. A ruɗe na janyo shi jikina ina fara yamutsa shi a haukace saboda yadda nake ji kamar na zauce. Rungume ni kawai ya yi ta ko'ina ya yi mini lulluɓi kafin ka ce me ya sake komawa baccin shi, sai saukar numfashin shi nake ji cikin sauti alamun baccin yana yi masa daɗi._
      _Ture shi na yi tare da juya masa baya ina goge hawayen da ke ta mini ambaliya a cikin ido. Saboda takaicin abin da ya yi mini a lokacin da na fi buƙatar shi, don tun da nake da shi ban taɓa jin ina son ya kasance ni ba sai a wannan lokacin. Shi ya sa ban damuwa da yadda yake tafiyar da ni a shimfiɗa, saboda daman can minti biyar ya yi masa yawan da zai zare alƙalamin shi daga jikina. Amma wannan karon ba na zaton ma ya yi minti uku cikakku na ji alamun gamsuwar shi tana tsiyaya cikin jikina._
       _Bacci na yi rabi da rabi ina matse ƙafafuwa saboda yadda nake jin kaina tamkar na yi ihu. Da tulin haushin shi na kwana a raina, tare da alwashin sai na rama abin da ya yi mini idan ya sake nema na. Da safe Shar ya tashi yana faman murmushi ni kuma na shiga haɗe masa fuska, ya janyo ni jikin shi yana ƙoƙarin yamutsa ni na ƙwace kaina ina aika masa harara. Saboda na ji haushin abin da ya yi mini, don har lokacin ban daina jin tsikar jikina tana tashi ba. Kasancewar a wuya nake da buƙatuwa bai sha wata wahalar shawo kaina ba, nan take na manta da alwashin ramuwar da na ci.  Na koma ba shi wata damar da ya jefa ƙwallon shi cikin raga, ya fara kai-da-komo ina jin farinciki da jin daɗin yanayin sosai, na shiga lumshe ido saboda daɗin da ke ziyartar ƙwaƙwalwata. Sai luf na ji ya sake bajewa a jikina yana kyarma, kafin ya zame a hankali ya koma gefe yana sauke numfashi, tare da jera mini albarka ta fi ƙwara goma ba tare da ya ankara da tashin hankalin da ya ziyarci fuskata ba._  





🤭😂





D. AUTA CE✍🏼


*ABOKIN AIKINA*


*@HADIZA D. AUTA*


*SADAUKARWA: DAUGHTER ANUP*


*ASHIRIN DA HUƊU.*

         _Miƙewa ya yi ya shige toilet, a gurguje ya yi wanka ya shirya. Ina nan inda ya bar ni kwance ko motsin kirki na kasa yi, saboda tsabar takaici da baƙincikin da ya turnuƙe mini zuciya. Wurina ya zo yana faman murmushi ya sauke mini kiss a goshi, sannan ya nufi hanyar fita yana faɗin,_
        "Ni zan tafi Makaranta, zan aiko da cefane." 
          _Murmushin yaƙe na yi masa ya fice yana yi wa Ummu Salma bye-bye, wadda ke ta wutsil-wutsil da ƙafafuwa tana tsotson hannu. Shiru na yi ina tunanin abin a raina, a ƙarshe na miƙe  babu kuzari na tsarkake jikina ina jera tsakin haushin wanka ba tare da na mori komai ba._
      
****
_Haka rayuwa ta ci gaba tafiya kullum abin yana damuna a zuciya, ga shi ina jin kunyar sanar da shi meke damuna balle na yi masa bayanin abin da yake yi mini ba na jin daɗin shi. Saboda kunya da kuma nauyin ta yadda zan fito masa da abin da ke zuciyata, amma a raina kullum muka haɗa shimfiɗa sai na ji kamar na kuwata don haushi da takaici. Saboda ko kaɗan bai damu da nemar mini gamsuwa ba, da ya tsiyayar da ruwansa cikin minti biyu, uku zuwa biyar ya gama. Kuma babu wata wasar kirki da yake yi mini balle na ɗan rage zafin abin da ke damuna, ga shi da yawan buƙatuwa a lokacin kai-da-kai yake nema na kuma da buƙatarsa ta biya shi kenan._ 
       _Haka ma dangane da kayan ɗakina babu wani tarnaƙin da ya fuskanta,  saboda na bi na toshe duk wata ƙofar da za a ganin laifin Mukhtar. Domin da labarin canjin kayana ya je kunnen Umma, ta kira ni tana faɗan me ya sa aka canza mini kayan ɗaki ba tare da na sanar da ita ba. Na ce da ita ta yi haƙuri saboda ba na so ta yi mini faɗa shi ya sa ban sanar da ita ba, maganata ba ƙaramin ɓata wa Umma rai ta yi ba. Saboda faɗan da na ce ina gudu ta yi mini shi ta balbale ni da shi tamkar ta kamo ni cikin wayar ta yi ta jigba. Ban da haƙurin da nake jera mata babu abin da nake yi a lokacin, saboda jikina ya yi sanyi musamman da ta nuna don ba ta isa da ni ba ne shi ya sa ban yi sanar da ita ba._
       _Ranar da ta zo ta ganar wa idanuwanta kayan, da ɓacin rai ta fice gidan tare da yi mini kashedi a kan; Duk lalurar da ta taso mini a gaba kada na neme ta. Saboda na sanar da ita wata lalura ce ta sa na sayar da kayan dole ba don na so b, ta tambaye ni to me na yi da kuɗin. Na fara kame-kame haushi ya sa ta kwaɗa mini mari tare da nuna ni da hannu ta ce,_
      "Daga yau ki zamo uwar kanki da uban kanki, domin na zare hannuna a cikin duk wata buƙatar da za ta taso miki a gaba. Tun da har kina iya sayar da kayanki ina cikin gari ba tare da kin sanar da ni ba. Ke ko ba na garin nan idan kina mini kallon daraja ba za ki rasa ɗaga waya ki kira ni ba. Don haka yanzu na yarda kin ishe kanki, ki je ki yi duk abin da kike so babu hannuna babu ƙafata, balle abin da zai fito daga aljihuna."
       _Na yi kuka sosai ranar, saboda fushin da ta yi da ni, ya fi komai tsaya mini a zuciya. Amma duk da hakan bai sa na ji haushin Mukhtar dangane da abin da ya yi mini ba, saboda na gamsu da abin da ya sanar da ni don a lokacin ma har ya fara zuwa makarantar. Kuma na sa a raina idan ya zamo wani abu ta sanadin karatun ita ma za ta ji daɗi, a lokacin zan sanar da ita yadda kayan suka yi na san za ta ji daɗi, kuma za ta yaba mini a kan rufin asirin da mijina ya samu ta sanadina._

      _Akwai wata matashiyar budurwa mai suna Jamila, wadda ke cikin unguwar kuma muke maƙotaka da gidansu. Tana shigowa sosai gidan saboda ƙaunar Ummu Salma da take yi, kullum tana hannunta na yi ta aikina tana yi mata wasa ko ta goya ta. Wani lokaci kuma har aikin gidan tana taya ni don ba ta da ƙiuya ko kaɗan, hakan ya sa na saki jikina da ita sosai tamkar ƙanwata uwa ɗaya uba ɗaya. Ba na baƙincikin ba ta komai daga na ci har wanda za ta je da shi gida bayan na amfanin rayuwa._
     _Matsalar da na fara fuskanta dangane da zaman da take yi da ni; Yawan damuwa da lamurranta da Mukhtar yake yi, ita ma idan ya zo gidan idanuwanta a kan shi ko ƙyaftawa ba ta yi. Sai ta ga ina haɗe rai sannan za ta shiga taitayinta._
      _Ba na manta watarana yana tsaka da cin shinkafa da wake, ya shiga zuzuta yajin yana faɗin,_
        "A gaskiya wannan yajin ya yi mini daɗi, ke kika daka shi kuwa?"
       "Jamila ce ta daka. Kuma yadda nake dakan yajin kullum haka na sa ta yi mini."

       "To gaskiya ta samo shi da kyau."

       _Ban sake cewa da shi komai ba, duk da ban ji daɗin yabon da ya yi ba. Amma ban kawo komai a raina ba, sai da na nutsa nazari sannan na tuna ai ya shigo ya taras da ita tana dakan yajin, to kuma me ya sa ya tambaye ni bayan ya san ita ce ta daka. Haka kawai na tsinci kaina da ce masa,_

      "Yanzu shi dakan yaji har wani abu ne mai girman da za a yi ta zuzutawa haka?"

       "Allah ya ba ki haƙuri! Daɗin shi da na ji ne shi ya sa na yaba."

       "To ba na son yabon tun da ba a yi maka dole sai ka yi ba, idan kuma ita kake so ka jinjina ma to ka bari idan ta zo gidan ka yi mata godiya. Ko kuma ka same ta gidansu idan abin ya dame ka."

      "Can kika nufa kuma? To ni kin ga fita ta Allah ya huci zuciyarki!" 

     _Ya fice ya bar ni ina aika wa robar yajin harara tamkar shi ne nake kallo. Tun daga lokacin na hana ta taya ni duk wani aikin da ya shafi girki ko abin da za a ci. Sai dai ta kula mini da Ummu Salma ko shara da wanke-wanke, amma na katange ta da yin abin da Mukhtar zai yaba saboda masifar kishin shi da nake yi. Wanda in da ina da iko a lokacin, kallon wata ma ba zai yi ba balle ya hango kyawunta, don ko waya na ji yana yi cikin siririyar murya sai na ji haushi da kishi ya kama ni, kuma sai na zargi da wata yake yi. Wani lokaci ma har kiran waɗanda suka yi wayar yake yi domin na ji gaskiya a bakinsu, musamman idan ya yi ta rantsuwar ba da wata yake ba na ƙi yarda._ 
      _Akwai watarana da na ji yana waya cikin toilet yana kashe murya, na je jikin toilet ɗin na lafe ina sauraron hirar da yake yi da wata. Raina a ɓace na dinga dukan ƙofar ina faɗin sai na kashe ko wace ce yake waya da ita cikin ɗakina. Hankalin shi a tashe ya fito yana ta rantsuwar babu macen da yake waya da ita. Idan kuma ban yarda ba sai ya kira mini wanda suke wayar na ji da kunnena. Ban ce da shi komai ba sai hucin da nake yi riƙe da ƙugu ina aika masa harara, ina sauraron ringing ɗin da wayar take yi saboda ya saka ta hands free domin na ji komai._

"Hello! Don Allah da kai na gama waya yanzu ko ba da kai ba?"

"Da ni, me ya faru ne?"

"Madam ce daga jin ina waya ta fara zargin da wata nake waya."

"To idan ma da wata kake yi ai ba haramun ba ne! Don kai mijin mace huɗu ne kuma kana da ikon ka yi abin da kake s..."

      _Haushin da ya turnuƙe ni ya sa na wafce wayar na buga ta ƙasa, sannan na durƙushe ƙasa ina kuka cikin ɗaga murya. Wayar shi kawai ya tattara ya fice yana surutan faɗin sai zargi ya kashe ni, tun da bai isa ya yi waya ba sai na ce da wata yake yi._
       _A irin wannan lokacin ne aka yi ƙaramar sallah, ni da kaina na ba shi shawarar ya yi wa Jamila ɗinkin sallah. Saboda yadda take ƙoƙarin rainon Ummu Salma ba ƙaramin jin ta nake yi a raina ba. Amma ya fitittike a kan shi bai da kuɗi ba zai yi ba, na ciyo bashin zane biyu na kai aka ɗinka wa Jamila na ba ta tana ta jin daɗi. Godiya ta yi mini sosai tare da addu'o'i iri-iri gare ni, cikinsu kuwa har da zama ni kaɗai a gidan Mukhtar iya rayuwa. Sosai na ji daɗin addu'o'inta ina ta wasar baki saboda ganin ta gama mallaka mini komai a rayuwa, tun da ta yi mini fatan zama da Mukhtar ni kaɗai babu kishiya._
      _Da dare Mahaifiyar Jamila ta zo fuska faram-faram na tarbe ta cikin fara'a muka gaisa. Ta ce da ni yana nan na ce da ita ba ya nan, zama ta gyara tana wasar baki ta ce,_
      "Don Allah idan ya zo ki yi masa godiya, mun ga abin arziƙi mun gode sosai Allah ya ƙara buɗi."
 
      _Sakato na yi ina dariyar yaƙe, saboda mamakin godiyar da take yi masa bayan ni na yi wa Jamila ɗinki ba shi ba. Na kasa shanye mamakina iya ni na ce mata,_

     "Ai ni na yi wa Jamila ɗinki ba shi ba."

      "E, na sani kuma mun gode sosai, amma idan ya zo don Allah ki yi masa godiya ki ce mun gode sosai Allah ya saka da alheri."

     _Murmushin yaƙe kawai na bi ta da shi tare da faɗin "To" Saboda raina bai yi mini daɗi ba ko kaɗan. Musamman da na fahimci akwai abin da take ɓoye mini wanda ba ta so na sani._
       _Da ya dawo na sanar da shi saƙon Mamar Jamila, baki kawai ya washe yana sosa ƙeya. Amma bayan hakan bai ce da ni komai ba balle na gano inda zaurancen su ya sa gaba. Na kasa danne zuciyata har sai da na ce da shi,_
       "Aikin me ka yi musu da har suke gode maka?"

      "Aiki kuma?"

          "E, don na san banza ba ta kai zomo kasuwa. Kuma babu yadda za a yi su yi maka godiya ba tare da ka yi musu wani abu ba."
        "To ki je ki tambaye su ki ji tun da abin ya dame ki."
  
       _Daga haka ya yi kwanciyar shi bai sake cewa da ni komai ba, duk da faɗan da nake yi masa a saman kai tamkar na dake ki. Saboda na rasa me zan yi na ji daɗi a raina, domin zuciyata ta kasa cire mini tunanin abin da ya ba su ban sani ba. Da ƙyar na saita kaina daga haukar kishin da nake yi masa_
       _Tun daga lokacin na fara jan jikina da Jamila, duk da ita ba ta nuna mini komai na baƙin hali idan aka cire kallon ƙurullar da take yi wa Mukhtar.  Ko shi da ta gano take-taken shan ƙamshin da nake yi mata ta rage a gabana, amma idan Mukhtar yana falo ta dinga sintiri kenan tana bi ta ƙofar ɗakin tana dawowa. Musamman a lokacin da Ummu Salma ta fara rigima, haka za ta yi ta yawo da ita tsakiyar gidan tana yi mata kurrrr! A cikin kunnuwa har ta yi shiru._

***
     _Zamanmu da Jamila ya miƙe har zuwa lokacin da Ummu Salma ta iya tafiya. Duk da kafin lokacin wani babban al'amari ya faru da ni, wanda har yanzun nan da nake ba da labari ban daina jin zafin abin cikin raina ba. Saboda Ummu Salma tana da wata bakwai na samu wani ciki, Mukhtar ya fito fili ya nuna mini ba ya son haihuwar cikin. Sannan ya yi ta ɗora ni a kan hanyar da za a salwantar da cikin ina jin tsoro, duk da ni kaina ba na son cikin saboda wahalar da nake sha, ga Ummu Salma ta fara ciwo kullum jikinta zafi rau ga afkin kukan da take hana ni shaƙat da shi. Dalilin hakan ya sa na ji ina son rabuwa da cikin kamar yadda Mukhtar yake ɗora ni a hanyar. Wani ɗan'uwansa ya nemo mai aiki asibiti, ya zo da shi har ɗakina na yi masa bayanin watannin cikin, sannan da halin da nake ciki dangane da wahalar da yake ba mu ni da Ummu Salma. Tare suka fice yana cewa da ni na kwantar da hankalina in Sha Allah za mu samu lafiya._
       _Da dare suka dawo tare da shi ya kawo mini wata ƙwayar magani ya ce na saka a jikina. Tare da yi mini bayanin cikin zai zube kafin safiya saboda ko wata uku bai rufa ba. Sai dai da a ce na san abin da zai biyo baya, da na fi son na haife cikin da azaba, takaici, fargaba da baƙincikin da na ƙumsa tsakiyar daren zuwa safiya._
       _Kamar yadda ya faɗa mini haka na aikata, lafiya lau na kwanta bacci har ina tunanin ko dai cikin ba zai zube ba. Kwatsam tsakiyar dare ina tsaka da bacci na ji kamar an saka wuƙa an yanki marata, babu shiri na farka a firgice dafe da ƙuguna da nake ji tamkar zai rabe gida biyu. Kafin bayana ya karɓa da luguden bala'in zafin da nake ji tamkar a raba ni da ƙugun na huta. Na fara buge-bugen hannuwa ina ƙwala masa kira ya tashi a firgice yana tambayar me ya faru. Na cije leɓe tare da baki saboda azabar da nake ji ba zan iya kwatantawa ba, sannu ya fara jera mini ba tare da na iya amsawa ba. Kwanciyar shi ya koma yana ta kallona bai koma baccin ba, saboda azabar da nake ji ta kai ƙololuwar da na kwashe tsawon lokaci ina fama. Cikin ikon Allah ina zaune tsakiyar ɗakin na ji wani abu ya fito jikina, nan take jini ya ɓalle mini tamkar an buɗe famfo. Ya taso yana yi mini sannu na ce da shi ya riƙa ni na tashi, ya fara ɓata fuska cikin ƙyanƙyami ya riƙa ni a lalace kamar ba ya so. Haushi ya sa na ƙwace hannuna na dafa ƙasa na miƙe da ƙyar abin ya faɗo daga cikin zanina zuwa ƙasa._
       _Babu shiri ya ja baya tare da yin salati saboda ganin abin da ya faɗo tamkar ɗan ƙadangare. Na yi toilet jini yana biya ta duk inda na taka. Jikina na wanke sannan na cire zanin na fito a daddafe saboda jinin da bai daina bin ƙafafuwana ba._
      _Always na linka na saka a tunanina za ta iya tare jinin, sannan na samu kuzarin saka wata riga na kwanta. Mukhtar ya shigo ɗakin yana faɗin, na tashi na gyara ɗakin shi ya jefa abin masai. Har ga Allah ban ji daɗin masan da na ji ya ambata ba, domin sai da ƙwalla ta zubo mini saboda wani tsoron Allah da ya shige ni. Banza na yi masa kamar ban ji me ya faɗa ba, saboda takaicin rashin imanin da ya sa muka aikata wa albarkar da Allah ya azurta mu da ita."_
     _Miƙewa na yi ina layi na koma toilet na wanke inda jinin ya ɓata, sannan na dawo ɗakin na gyara shi tas na fesa turaruka saboda ƙarnin jinin. Na koma na kwanta ina tunanin ƙyamar da Mukhtar ya nuna mini, ban san lokacin da bacci ya kwashe ni ba sai da asubar farin ana kiran assalatu marata ta karta. Nan take jini ya banke always ɗin da ke jikina yana ta ɓulɓulo mini gundali-gundali._






😱Wai Allah!🙆🏻‍♀️🤦🏻‍♀️






D. AUTA CE✍🏼


*ABOKIN AIKINA*


*@HADIZA D. AUTA*


*SADAUKARWA: DAUGHTER ANUP*


*ASHIRIN DA BIYAR.*

        _Hankalina a tashe na miƙe da sassarfa na isa toilet na duƙa. Sai ga jini ya ɓalle mini mai uban kauri. Na jima tsugunne ina kallon ikon Allah, sannan na miƙe na fara wanke jikina na gyara wurin. Jikina babu kuzari na fito ina layi, domin na sare da cewa jinin jikina ne ya tsiyaye kuma mutuwa zan yi. Mukhtar na tayar daga baccin da yake shararawa har da minshari, na nuna masa jinin da ya bi ƙafafuwana zuwa toile cikin sanyin murya na ce da shi,_
         "Mutuwa zan yi."

    "Ban gane ba! Mutuwa kuma me ya faru yanzu?"

       _Sai da na goge hawayen da ke gangaro mini a kan fuska sannan na ce da shi,_
      "Jinina ya gama tsiyayewa, don Allah ka yafe mini ka ce ni ma na yafe wa kowa."
          _Ina ƙare maganar na miƙe na fara ƙoƙarin gyara ɗakin, shiru ya yi yana ta kallona. Sannan ya tashi ya fice daga ɗakin, ko da ya dawo har na gama gyaran har na canza kaya, na koma falo na kwanta kan kujera. Ya shigo falon tare da wanda ya ba mu maganin idanuwansu a kaina._
       _Tambaya ta ya fara yi me nake ji, na yi masa bayanin jinin da na zubar da rashin ƙarfin da nake jin jikina. Tare suka fice ya ce na bari a kawo mini magunguna, da na sha zan ji sauƙi, shiru na yi kawai ina goge hawayena da ke bin gefen fuskata. Saboda na yi da-na-sanin biye musu na zubar da cikina, don da na mutu sanadin hakan ni ce da laifin ba su ba. Kuma ni Allah zai ƙona domin babu ɗa'a ga abokin halitta a wurin saɓa wa mahalacci._

     'Me ma ya sa na amince wai?'

     _Tambayar da na jefi kaina da ita kenan a zuciya, na yi ta saƙe-saƙen illar zubar da ciki da haɗarin da ke cikin shi. Mukhtar ya dawo mini da magunguna na sha tare da maltina da madara, sannan ya ɗauki Ummu Salma ya fice da ita ban san lokacin da bacci ya yi awon gaba da ni ba._
      _Bayan 'yan kwanaki ina shan magungunan da abubuwan da ke ƙara jini, cikin ikon Allah na ji sauƙi garas kamar ban taɓa ciwo ba. Mukhtar ya sanar da ni za a yi mini allurar planning saboda gudun na koma samun wani cikin kafin a yaye Ummu Salma._
         _Ban ja da tsauri ba na amince, saboda ko ni ba na so na samu wani cikin a lokacin. Duba da yadda na sha wuyar cikin da zubar da shi, kuma alƙawarin na yi wa kaina ko sau dubu zan haifu ba zan sake zubar da cikina ba._

****
      _A lokacin da na yaye Ummu Salma ta iya tafiya ko'ina tana zuwa da gudu, sannan da bakinta ta iya faɗin Mama da Baba har ma da wasu sunayen 'yan gidan tana kamawa. Jamila ma ta iya sunanta raɗam kamar yadda ta laƙaba mata kiran "Jayiya."_  
      _Watarana da yammaci na shiga gidan su Mukhtar, na bar Ummu Salma wurin Jamila da ke yi mini shara. Ana tsaka da hira a ɗakin matar Baban Mukhtar, sai ga ƙanen shi ya zo yana sanar da ni ya dawo. Na miƙe zan fito wata ƙanwar shi ta ce da ni,_
     "Da kin yi zamanki tun da Jamila tana can sai ta tarbar miki shi."
        _Murmushi kawai na yi na fito, saboda surutun da duk suke yi a kan aikin da Jamilar take taya ni ya dawo kunnena. Kuma na san gatse ne ta yi mini saboda haushin jan ta jikina da nake yi. Ina ƙoƙarin shiga gidan na haɗu da Ummu Salma za ta fito da Cheezee a hannu tana nuna mini tare da faɗin,_ 
  
    "Abba! Jayiya!"

      _Cikin sauri na faɗa gidan, sai ga shi ya fito daga kitchen ɗina da leda a hannun shi. Murmushin rashin gaskiya ya fara yi mini sannan ya shige ɗaki, Da mamaki fal raina na tsaya bakin ƙofar kitchen ɗin, ina kallon Jamila da ke ta faman gyara wa kuloli zama._
      _Shiru na yi na rasa me zan ce, don jikina ya ba ni akwai wata a ƙasa. Amma ban ga abin da zai sa na tabbatar da abin da nake zargi ba. Na bar wurin ba tare da na ce da ita komai ba, zuciyata tana ƙuna na nufi murhuna da ke a tsakar gidan na fara tuƙa tuwo. Ta gefen ido na hango Jamila ta fice gidan sum-sum! Sai ga shi ya fito daga ɗaki yana shan lemu ya yi tsaye kaina. Ban kalle shi ba balle na tanka shi, da ya gaji da tsayuwar shi ya ce da ni,_
        "Idan zuwan yarinyar nan zai kawo mana matsala, kawai ta daina zuwa gidan nan gaskiya."

     "Matsalarku ce kai da ita, don ni ba ka ji na ce komai ba balle ka zo da wannan zance."

     "Yanayinki ya nuna abin da kike nufi da ganin na fito kitchen ɗin, to wuƙa na ɗauko domin na yanka lemun da na zo da shi. Ashe ma an yanka shi tun daga can ban sani ba sai da na buɗe na gani."

     "Haka kam!" 

       _Amsar da na ba shi kenan, ina tuƙa tuwon da sauri saboda tsabar gaskiyar da ta yi mini yawa. Daren ranar haka muka kwana ba tare da na bi ta kan shi ba, don shi ma a lokacin ya daina ƙulafucin da yake yi mini wurin neman haƙƙinsa._
     _An kwana biyu Jamila ba ta zo gidan ba, na aika aka kira mini ita muka shiga ɗaki, fuskata a haɗe na ce da ita,_

       "Me ya sa kika daina zuwa gidan nan?"

   "Babu komai."

_Abin da ta faɗa kenan tana wasa da gefen hujabinta, na sauke ajiyar zuciya sannan na kira sunanta cikin sanyin murya na ce,_  
       "Jamila ki sanar da ni abin da ke tsakaninki da Abban Ummu Salma. Saboda jikina ya ba ni akwai wani abu da kuke ƙoƙarin ɓoye mini ke da shi. Bayan ni ina yi miki kallon ƙanwata kuma ina zaune da ke tsakani da Allah kuma da zuciya ɗaya, Allah ya sani duk abin da zai same ki wanda ba alheri ba ba na fatar shi. Sannan ina murna da farincikinki kowane iri ne saboda matsayin da nake jin ki a raina tamkar amana kike a wurina, don akwai gidaje da yawa cikin unguwar nan ba ki je ko'ina ba sai gidan nan kuma wurina. Ki faɗa mini idan akwai abin da yake yi miki wanda bai dace ba sai na sani, domin na yi wa abin tufƙar hanci tun kafin ya yi tsaurin da ba za a iya shawo kan matsalar ba."

     _Shiru ta yi mini kafin ta fara rantsuwa a kan babu abin da ke tsakaninsu, kuma ita bai taɓa yi mata komai wanda bai dace ba. Ganin ba za ta faɗa ba ya sa na sallame ta ta yi gida. Amma zuciyata ta kasa natsuwa da su, kuma ko kaɗan ba na so na ci zarafinta a kan abin da ba ni da tabbas a kan shi._
      _Ta dawo da zuwanta gidan amma ba kullum kamar yadda ta saba ba, ni ma ba na wani sake mata fuska sai dai ta yi ta wasa da Ummu Salma, ko kuma ta goya ta har ta yi bacci. A cikin lokacin ne ta fara amaye-amaye, don duk ta zo gidan kafin ta tafi sai ta yi aman da ya kai biyu zuwa uku._
      _Tun ba na bi ta kai har na fara yi mata magana, a kan idan ba ta da lafiya ta je asibiti a duba ta ya fi zama da ciwo kullum. Ban san ya aka yi ba wata safiya ta zo tana sanar da ni za su je Katsina, wurin dangin Mahaifiyarta. Na yi mata fatan a dawo lafiya da ƙyar ta bar gidan Ummu Salma tana kukan sai ta fita da ita._
       _Sun yi wata ɗaya da kwanaki kafin su dawo, lokacin da ta dawo na gan ta fess da ita alamun ziyarar da suka je ta amshe ta. Sai dai tun zuwan da ta yi sau ɗaya ba ta sake zuwa wurina ba, sai da aka kwashi kwanaki sannan ta zo gidan, muna tsaka da gaisawa Kakarta ta shigo da faɗa tun a soron gidan._

     "Ina take baƙar 'yar iska munafuka, wadda ba ta san ciwon kanta ba, wallahi muddin ba ki daina zuwa gidan nan ba,  sai an sabauta miki rayuwa a kan baƙin kwaɗayi irin naku ke da uwarki."

     _Gabaɗaya muka fito tsakar gidan, Kakar ta ci gaba da zagin ta tana ƙoƙarin kai mata duka da wata ƙatuwar sandar da ke hannunta. Zagayen gidan suka fara yi kafin ta yi nasarar kora ta tana ci gaba da bala'i, ta inda take shiga ba tan take fita ba har ta fice ba ta daina masifa ba._
      _Shiru kawai na yi ina tunanin abin da maganganunta suke nufi, saboda iya sanina ko ƙannen Mukhtar maza ba su zuwa gidan su zauna. Balle na ce maza suke zama gidan shi ya sa Kakarta take gudun a lalace ta._
      _Duk da korar da Kakar take yi mata bai hana ta zuwa jefi-jefi muna gaisawa ba, amma ni ma da kaina na zaunar da ita na nuna mata cewa; Ta daina zuwa kamar yadda Kakarta ta gindaya mata doka, ni kuma duk abin da Allah ya hore mini ko ba ta zo ba zan aika mata. Saboda har raina ina jin daɗin yadda take ƙaunar Ummu Salma, amma tun da abin ya zo da haka dole na yi ƙoƙarin ɗora ta a kan abin da Kakarta take so. Da haka ta daina zuwa sai ranar da kakar ba ta nan ta leƙo mu gaisa tsaitsaye, sannan ta miƙa wa Ummu Salma abin da ta zo mata da shi ta fice._

      _Wata safiya bayan Mukhtar ya fita Mamarta ta zo gidan, mun gaisa a mutumce ta ce da ni wurina ta zo. Zama na gyara ina murmushi ta ce da ni,_ 
      "Na ji duk abin da Inna Huse ta yi, kuma Jamila ta sanar da ni yadda kuka yi da ita. Ubangiji ya saka miki da alheri Allah ya bar zumunci."
 
       _Cike da jin daɗi nake ta faɗin amin amin. Sannan ta yi shiru na ɗan lokacin kafin ta sake cewa,_
       "Don Allah akwai wani taimakon da nake so ki yi mana Maman Salma."
      "Kamar wane fa?"
    "Yawwa! Ai kin san Nura mai son Jamila ko? To zancen auren ne ya ƙi fitowa da gaske sai ja baya yake yi. Ga mutane suna son shigowa amma shi ya ƙi gaba ya ƙi yin baya, don haka nake so ki kira mini shi don Allah ki yi masa magana a kan matsalar. Saboda na gaji da ganin ta a gabana, idan bai tashi ba sai a tsayar da wanda ya shirya, tun da abin na shi ya zama rainin hankali da shiririta."

       _Ban yi tunanin komai ba na karɓi lambarsa gare ta na danna masa kira. Babu wani jinkiri ya ɗauka tare da yin sallama. Na amsa masa sannan na sanar da shi wace ce ni, tare da maƙasudin da ya sa na kira shi a fakaice ba tare da na nuna masa Mamar Jamila ce ta saka ni ba. Buɗar bakin shi ya ce da ni,_

      "E kam! Idan ma ban shirya ba ai sai ki yi mata auren gida a matsayinki na uwar ɗakinta. Don haka idan kun matsu ina jiran goron ɗaurin auren domin ya ƙarasa ɓarnar da ya aikata."

     _Sororo na yi da waya a hannu, domin tun da ya gama faɗin maganar cikin ɗaga murya ya katse kiran, da sanyin jiki na sauke wayar daga kunnena. Sannan na yi mata bayanin abin da ya ce ba tare da na gano inda zancen shi ya dosa ba. Jikinta yana rawa ta miƙe tana yi mini godiya ta fice gidan, yanayinta da maganganun Nuran suka ƙara cukurkuɗe mini kwanya._

      'Shin me yake nufi da jefa mini wannan magana? Kuma me ya sa Mamar Jamila ta shiga tashin hankalin da na gani kwance a kan fuskarta.'

     _Tambayoyin da na yi wa kaina kenan, waɗanda ban san amsar su ba sai daga baya, a lokacin da na ji abin da ya hasko mini ma'anarsu da inda suka dosa._





Ni dai kam ban gane komai ba😼 wanda ya sani ya sanar da ni plss🙁





D. AUTA CE✍🏼


*ABOKIN AIKINA*


*@HADIZA D. AUTA*


*SADAUKARWA: DAUGHTER ANUP*


*ASHIRIN DA SHIDA.*

          "Hmmmmm! Tabbas tarihinki shi ne makarantar aure, mai kwasa-kwasai ɗauke da tarin aji-aji, waɗanda ke ƙumshe da darussa iri-iri wani bayan wani. Dole ki kalli matsalata kamar an ɗebi ruwan rijiya da sirinji. Haƙiƙa kin yi gwagwarmayar aure, duk da har yanzu ban gama shanye romon labarin ba. Amma ni kam ko iya haka ma ba zan yi kwatar jarumtarki ba. Saboda zuciyata ba ta da ƙarfin shanye waɗannan tarin matsalolin, masu ƙoƙarin yi wa mutum kisan mummuƙe ba tare da an san mafari ba."
       
      Maganganun Amina kenan a lokacin da na tsayar da labarin, murmushi na yi mai sauti sannan na ce, "Za ki iya! Domin ni kaina a yadda nake da masifar zuciya a baya, ban taɓa tunanin zan iya shanye tarin damuwowin ba. Sai ga shi Allah ya ɗora mini  kuma ya ba ni ikon ɗauke komai a saman kaina, ba tare da sun yi nauyin da za su karya mini wuya ba."
       "Danƙari! Waton dai ƙalubalen rayuwar aure hawa-hawa ne kuma kala-kala. Amma duk da haka taki ta zamo shakundum! Domin ta haɗe ɓangarora da yawa."
       Shiru na yi kawai ina mata dariya, saboda yanayin da take kallo na tana jinjina kai tare da faɗin, 
"Hu'ummm! Lalle! Cabɗijam!" 
        Sai da ta ɗauki mintuna a haka sannan ta cire tagumin da ta yi tare da jefo mini wata tambaya.
      "Yanzu kina nufin duk wannan badaƙalar babu wanda ya sani a cikin familynki a lokacin?"
       Ajiyar zuciya na sauke mai ƙarfi, murmushi a kan fuskata na ce da ita, "Babu wanda ya sani daga dangin Ummata har dangin Babana da ke Birnin Kebbi. Saboda na riƙe sirrin aurena da kyau, kuma na ɗauke shi abu mai muhimmancin da za mu rayu mu kaɗai a cikinsa ba tare da kowa ba. Ba a fara sanin tsakanina da shi ba har sai da ya yi mini wata gagarumar cin amanar da na kasa shanye baƙincikinta a zuciyata, na fara yi masa bore. Kuma ko fashewar ƙwan ma ba daga hannuna ya fito ba, shi da kansa ya yi kururuwa ya luma wa kansa wuƙar da ta yi barazanar ɓurma masa baya."

      Shiru na yi bayan na tsahirta da maganar ina duba agogon da ke tsintsiyar hannuna. Na fara haɗa kayan da ke saman teburina ina faɗin,
      "Babu time, da na sanar da ke abin da ya yi mini a lokacin, wanda ya yi sanadin yanke ƙaƙƙarfar alaƙar da ke tsakanina da ƙawata Hafsa. Domin har yau da nake yi miki wannan magana babu jituwar kirki a tsakaninmu. Saɓanin baya da nake yi mata kallon 'yar'uwa kuma abokiyar haihuwa, duk da maƙotaka ce ta haɗa mu tsakanin gidan Kawu Sale da gidansu. Sannan Mamarta ƙawar Ummata ce, haka ma Babanta abokin Kawu Sale ne na ƙud-da-ƙud."
       "Tabbas! Akwai alaƙa mai ƙarfi a tsakaninku."
       Zancen Amina kenan a lokacin da muke ƙoƙarin fitowa daga offis ɗin. 
      "A hakan kuma ta rufe idon sani ita da Mukhtar, suka so jefa ni rami su binne da rai ba tare da sun jira na mutu ba."
        
      A tsaye na bar ta na nufi offis ɗin MD, na tura ƙofar da sallama kai-tsaye na nufi gabansa. Takardun da ke hannuna na ajiye masa na juyo, sai dai bai fasa faɗar maganganun da yake yi a cikin wayar da na taras yana yi ba.
       "Ko da Ammin ta ce ki je, to ni na ce ba za ki je ba! Kuma kada ki bari na dawo na taras da ba kya nan, Domin wallahi ba zan lamunci wannan rashin mutuncin da kike ƙoƙarin yi mini ba. Ok tom ki yi yadda kike so kawai tun da d..."

     Iya abin da kunnuwana suka jiyo mini kenan tsakanin shiga ta offis ɗin zuwa fitowa ta, hakan ya sa bai bi ta kaina balle ya tanka ni. Bakin gate muka nufa zuciyata cike da tunanin halin matar MD, domin a lafuzzan da yake furzarwa na fahimci mace ce mai yawo, sannan ga kafiyar bala'i ta fito a cikin zancen shi ɓaro-ɓaro. 

       "Allah ya kyauta!" 

     Abin da na faɗa kenan bayan na gama nazarin kalaman shi a raina, da kashedin da ta yi mini a wayarsa lokacin da na kira shi. Har mai adaidaita ya ajiye ni ƙofar gida ban daina tunanin MD da matarsa ba, musamman sauyin yanayinsa tamkar ya kai duka a lokacin da yake wayar.

      'Abincin wani gubar wani.'

      Zancen zucin da na yi kenan ina tura ƙofar gidan, saboda yanayin MD ya nuna ba ƙaramin haƙuri yake yi da halin matarsa ba, kamar yadda nake haƙuri da Mukhtar duhun dare, da hasken safiya zuwa yamma.
     Hannuna na bi da kallo saboda fentin da na dangwalo ban sani ba, domin kwata-kwata ban lura da sabon fentin ba har sai da na gan shi a hannuna.
       Baki a buɗe nake kallon su Ummu Salma da ke tsakar gidan suna shirin makaranta. Jakunkunansu da komai a wurin suna ƙoƙarin shjryawa, ƙofar falon na bi da kallo saboda ganin ita ma ta sha fenti cement color kalar na ƙyauren ƙofar gidan.

     Da gudu suka taso suna ihun murnar gani na, idona a kansu na ce da su, 
      "A nan kuke shirin yau kuma?" 
        Haidar ya yi saurin faɗin, "Abbanmu ya ce mu ɗauko duk abin da muke so mu tsaya nan, kada mu ɓata masa fenti."
       "Ah! Tabbas ya kyauta, ko ba komai kayanku za su huta da kwasar fentin da za a sha wuyar fitar da shi idan an zo wanki."
       Ummu Salma ta ɓata fuska tana faɗin, "Har fa dukan Haidar ya yi, don ya taɓa fentin bai sani ba ya goge wurin."
      "Da bai taɓa ba ai ba zai dake shi ba! Ni dai ku yi sauri ku shirya ku tafi makarantar. Kun ci abinci dai ko?"
       "Bai bari Aunty Ummu ta dafa mana ba, wai kada a ɓata masa fenti a bari sai gobe idan ya ƙame."
        "To me kuka ci?"
Tambayar da na jefo wa Iman kenan saboda ita ce ta ba ni amsar. 
        "Gari da suga ya siyo mana muka sha. Kuma wallahi ni ban ma ƙoshi ba." Haidar ya faɗa yana turo baki a ƙoƙarin shi na nuna mini haushin da ya ji a kan hakan. 
     "Oya ku gama shirin kafin na dafa muku Indomie yanzu shaf-shaf!"
      Ban jira cewarsu ba na yi ciki da sauri don raina ya yi ƙololuwar ɓaci. Kallo na bi falon da shi saboda ganin yadda aka mayar da kayan cikinsa duka gefe, an shafe falon tas da fenti mai kala biyu sai ƙyalƙyali yake yi. Sannan ƙofofin ɗakunan duka sun sha fenti har maiƙo suke yi.
      Ƙofar ɗakina na tura na shiga, shi kam yana nan yadda yake ba a taɓa mini komai ba. Jakata na ajiye tare da cire hijabin da ke jikina na fice zuwa kitchen. A nan ma ya Sha fentin ko'ina fes-fes duk da an hargitsa mini kayan cikinsa. 
        Cikin mintuna ƙalilan na gama dafa Indomien, na wanko tire na juye duka sannan na fito tsakar gidan. A kan tabarmar da suke kai muka baje, sai da suka ci suka ƙoshi har suka bar mini saura. Sannan na yi musu addu'a kamar yadda na saba suka fice suna faɗin "Mama sai mun dawo."
      Da sauri na miƙe saboda alamun zuwan period da na ji a jikina. Wanka na faɗa a gurguje na fito, a nan na ga toilet ɗin ma ya sha fenti har da ƙyauren ƙofar.
      Murmushi na yi a raina na ce, 'An zo wurin' Domin har cikin zuciyata ina farincikin auren duk da bai fito ya sanar da ni ba. 
      Bayan na kimtsa na dawo kitchen na ɗora mana girki dare, saboda time ya tafi biyar har ta wuce. Kasancewar ina da sauran garin semo tuwon shi na yi mana shaf-shaf da miya yauɗi. Na jefa mata ƙwarorin busasshen kifin da ya rage mana nan take ƙamshi ya karaɗe gidan. 
       Ina tsaka da kaɗa miyar Mukhtar ya shigo kitchen ɗin, hannuwansa a aljihu ya tsaya bayana bai ce da ni komai ba. Tun kallon farkon da na yi masa ban sake bi ta kan shi ba har sai da ya yi gyaran murya ya ce,
       "Girki kike yi?"
     "Idonka ya ganar maka ai!"
Amsar da na ba shi kenan, ba tare da na daina abin da nake yi ba.
      "Ban so aka yi girki a gidan nan yau ba, saboda fentin nan ba na so a lalace shi tun kafin ya gama ƙamewa."

      "Idan kai ka iya hora Yaranka saboda fenti, ni kam ba zan iya barin su da yunwa ba a kan ka yi sabon fentin."
        "To shi kenan a bar zancen kawai, daman ina so na sanar da ke auren da zan yi a cikin satin nan mai zuwa. Saboda ba na so ki ji a wani wuri gara ki ji komai a bakina."

     Dariya na yi mai sauti sannan na saukar da miyar ina goge wurin da na ɓata na ce, "Wannan ai abin farinciki ne ba kaɗan ba. Da ka faɗa mini da wuri ma ɗakina zan bar wa amaryar na koma ɗakin su Ummu Salma. Saboda sai ta fi jin daɗinsa fiye da ɗakinsu don ya fi shi girma. Amma tun da a can ka fi so ta zauna shi kenan babu damuwa, ina taya ka murna Allah ya kawo ta lafiya, kuma ya ba da zuri'a ɗayyiba a tsakaninku."
      Shiru ya yi kawai yana kallo na, ni kam abincina kawai na zuba a plate na raɓa gefen shi na fice. Jikina ya ba ni kallon mamaki ya ni da shi a lokacin da zan bar kitchen ɗin, shigowar su Ummu Salma ya sa na fice tsakar gidan ina cewa da su su je ɗakinmj su cire kayan makarantarsu, su yi shirin sallah. 
         Kujerar roba na janyo na zauna a tsakar gidan ina ta cin abincin ina 'yan waƙe-waƙena. Tsayuwar shi kawai na ji a gabana yana huci ya ce, 
     "Ko ba ki yi hakan ba, na san yanzu ba kya so na, to ki sha kuruminki in dai ni ne sai na nuna miki na fi ki rashin mutunci. Kuma ki sani ban ji zafin kin daina kishina ba, tun da zan auro mai sona tsakani da Allah kuma wadda ta san zafina. Ki je ki ci gaba da ƙuncinki ni ko a jikina wallahi, don ba ke kaɗai Allah ya ba ni damar aure ba balle ki nemi wulaƙanta ni a banza."

 "Bazar kowa bazar kowa."
"Da bazarka ce nake taka rawa."
 "Haƙiƙa ya habibina"
"Ƙaunarka ce ta sa ni zumuɗi."
"Yau sai ka zo mu ɗan taka rawa. Yau sai ka zo mu ɗan taka rawaaaa!"

     Waƙar da na fara rerawa kenan, da abin ya yi mini daɗi na ajiye plate ɗin tuwona na fara tiƙar rawa, gaban shi na zo ina laƙamo wuyansa tare da goga fuskata jikin tashi musamman da na zo ƙarshen baitin ina faɗin "Taka rawaaaa!" 
       Cire hannuna ya yi daga wuyan shi ya wurgar cikin fushi, tare da nuna ni da hannu yana faɗin,
       "Sai kin san ni kika wulaƙanta!"

 Yana ƙare faɗar haka ya juya zai fice gidan, na bi shi da waƙar,
"Ku yi ta kanku"
 "Mu ma mu yi ta kanmu"
"Dariyaa ba fa so ba"
"Ya raye daɗin dariyalle"
"Mai hali bai bari ba"

       Har ya fita ya dawo buguzum ya shiga ciki kamar ya kifa, na koma na zauna tare da ɗaukar plate ɗin tuwona ina ci. Lokacin da na ji zai fito na sake ɗauko wani sabon baiti na ɗora.
 "Bana an gama komai"
"Bori ya kashe boka"
"In dai taro ne in babu ai suna ne"
"Allah ya yi sarkin daka shi ne turmi ahayye"
"Takun ya yi wasu sun saki reshe sun kama ganye."
       Babu zato na ji ya shaƙo wuyana, cikin azama saki plate ɗin na rarumi jarumar shi na matse iya ƙarfina. Ya yi hanzarin saki na ya dafe gaban shi hannu biyu yana faɗin,
        "Wallahi sai kin gane kuskuren tozarcin da kike ƙoƙarin yi mini a gidan nan."
      Daga haka ya fice gidan dafe da gaban shi yana nuna ni da hannu yana ƙwafa.

     Na bi ƙofar da harara kafin murmushin mugunta ya suɓuce mini ba tare da na shirya ba. Haka kawai na tsinci kaina cikin nishaɗi, ko babu komai ban bari ya gano dakan luguden da zancen auren shi ya yi mini a zuciya ba. 
      Saboda ban yi zaton zan ji kishin shi a raina ba, kamar yadda na ji zafin zancen auren da ya yi mini ba a zuciya. 
      Daren ranar kwana na yi cikin yarana cike da jin daɗi da farinciki, duk da wani gefen zuciyata yana hasko mini kalar matar da Mukhtar zai aura. Tsaki na yi ya fi a ƙirga saboda tunanin kowace ce wataƙila ta fi ni komai, shi ya sa ta yi nasarar kama masa wuya har ya amince zai aure ta.
     
     'To ina ruwanki idan ma ta fi ki? Ke da ba ki son shi kishin me za ki yi na shi?' 

       Tambayar da zuciyata ta kitsa mini kenan, wadda na kasa bai wa kaina amsa. Saboda ni na sani ba Mukhtar ne ba na so ba, halinsa ne ya janyo ya sire mini na juya wa son shi baya. Kuma ba na ji zai iya yi mini abin da zai ya goge tabon baƙincikin da ya bar wa zuciyata iya rayuwa.



Warr💃🏻

Na yi nan kada Mukhtar ya ci ufana🤣🏃🏻‍♀️🏃🏻‍♀️






D.AUTA CE✍🏼


*ABOKIN AIKINA*


*@HADIZA D. AUTA*


*SADAUKARWA: DAUGHTER ANUP*


*ASHIRIN DA BAKWAI.*

         Da safe ban fita aiki ba har sai da na gyara zaman kujeruna, kasancewar falon babba ne na yi gefen ɗakina da su duka. Sannan na sa aka kafa mini plasma TV ta a bango, daidai tsakiyar kujeruna. Saboda ba na son a zo yi wa amarya jere a nemi kawo mini rainin hankali, ko kuma shi ya faɗa mini abin da ba zan ji daɗi ba a samu matsala.
       Ranar sai ƙarfe sha ɗaya na je ma'aikatarmu, na duƙufa aiki sosai ba tare da na biye surutun Amina ba. Lokacin da aka tashi ma ban yi jinkirin komai ba na nufo gida, saboda tunanin yaran da ke raina. Domin fargabar da nake ciki a kan kada ya hana su yin girki kamar yadda ya yi jiya, cikin sa'a na taradda Ummu Salma kitchen tana aikin abincin. 
     Sannu da zuwan da suke yi mini kawai na amsa, sannan na yi wanka a gurguje na fito. Iman na ce ta zo ta raka ni mu je gidan Maman Taufiƙ. Haidar ya fara rigimar sai ya bi ni na ce da su kowa ya yi zamansa na fasa ba zan je ba.
       Abincin Ummu Salma ta kawo mana muka baje a tsakiyar kujerun muka fara ci muna hira. Mukhtar ya shigo da manyan ledodi a hannunsa ya yi ɗakin shi yana muƙu-muƙu, sai da ya fito sannan ya fara faɗin ina abincin shi. 
      Kallo ma bai ishe ni ba balle na tanka masa, Ummu Salma ce ta miƙe ta ɗauko masa kular abincin ta miƙa masa. Karɓa kawai ya yi ya nufi ɗakinsa, na bi bayansa da harara saboda haushin auren da ya jajiibo wa kansa nake ji. 

***
      Abu kamar wasa, cikin kwana biyu Mukhtar ya shiga fafutukar auren shi gadan-gadan. Domin kuwa na ji labarin ya kai wa amaryarsa lefe daidai gwargwadon ƙarfinsa. Mafarin na sani ma, yara ya shigo wa da lemuna ya bai wa kowa gora ɗaya, sannan ya ba su biskuit guda huɗu ya ce a kawo mini. 
       Muna falo ni da su muna kallo Sajida ta kira ni a waya, cikin muryar damuwa ta ce da ni, "Aunty ke ya ba ki kayan?" 
       "Waɗanni irin kaya Sajida?"
      Tambayar da na mayar mata kenan don ban gane inda zancenta ya dosa ba, "Kayan faɗar kishiya mana, saboda na ga ya yi wa amaryar lefe ma sha Allah tamkar wata budurwa." 
      Ƙirjina na ji ya buga dam-dam!  Sai da na dafe saitin zuciyata saboda luguden da take yi mini, sannan na yi murmushin ƙarfin hali na ce da ita, 
"Ma sha Allah! Ki ce da ke aka kai lefen? To Allah ya tabbatar da alherin da ke ciki."
      "Amin Aunty!  E, da ni aka je. Amma ke kala nawa ya ba ki? Don na ga ita kala goma sha biyu ne bayan tarkacen da ke ciki." 
        "Allah ya sa ta kashe lafiya. Sai dai ni bai ba ni komai ba Sajida, amma kuma hakan ba zai hana ni saka sabuwar sutura a ranar bikin ba."
      Ajiyar zuciya ta fara saukewa sannan ta ce, "Allah dai ya kyauta Aunty. Wallahi idan kika ga matar sai haushi ya nemi kashe ki. Ni na rasa me ya gani a jikinta yake wannan rawar jikin auren. Ki yi haƙuri Aunty in Sha Allah babu inda auren nan zai je, don kina zaune za ki ga haƙƙinki ya fita a kan duk wanda ya zalunce ki."
        "Kada ki damu Sajida, Allah yana tare da ni koyaushe. Na gode sosai da ƙaunar da kike nuna mini a kowane lokaci."

      Daga haka muka yi sallama ta kashe wayar, shiru na yi ina nazarin maganganunta.
      'Waton dai tukuicin kai lefen ne ya ba mu muka laƙume ba tare da na sani ba.'
      Haka kawai na tsinci kaina cikin damuwar da ta janyo mini zubar ruwan hawaye, waɗanda ban shirya wa zuwan su ba. 

'Ashe ma Bazawara ce!'

      Zancen da na yi kenan a zuciyata ina kuma maimatawa a cikin raina.
      Murmushin takaici na yi tare da jin haushin Ummata, wadda ta janyo mini ganin irin wannan ranar baƙincikin a gidan Mukhtar. Don da a ce ta bar ni na yi abin da nake so, da tuni ba wannan zancen ake yi ba. Da rayuwata ta yi farin da zan hango haskenta gaba da bayana.

     "Babu komai akwai Allah!" 

      Maganar da na yi kenan a zuci ba tare da na san ta fito fili ba. Gaba su Ummu Salma suka saka ni da tambayoyi.
"Me ya faru Mama?"
"Me Sajidar ta faɗa ne?"
      "Babu komai ku jira na je gidan Maman Taufiƙ na dawo yanzun nan!"
       Daga haka na koma ɗaki na janyo hijabina, waya a kunnena na fice muna magana da Firdausi.

 "E da gaske ne mana! Satin nan ma za a kawo amaryar." 
       Amsar tambayar da ta yi mini kenan daga bakina, kafin ta gama jimami ta samu sukunin cewa, 
       "Anya Mukhtar kansa ɗaya kuwa?" 

  Murmushi na yi mai sauti sannan na ce da ita,
  "Me kika gani?"
         "Yo idan ba don Allah yana son tona masa asiri ba, me zai sa ya rikito aure yanzu? Bayan ke ɗin ma bai iya sauke haƙƙinki ba amma yake neman ɗebo wa kansa masifa."
      "Ya ji ya gani ne! Kuma kika sani ko ya samu lafiya ni ce bai bari na gane ba?"
       "Shi dai ya sani, namu kallo ne kawai! Amma don Allah kada ki nuna masa komai a kan auren nan. Ki bar shi da kan shi zai yi regretting ɗin me ya sa ya aikata."
        "Na bar shi ai! Tuni na zamo 'yar kallo."

    Daga haka muka yi sallama na shige gidan Maman Taufiƙ zuciyata babu daɗi, don daman can ƙofar gidan na tsaya saboda ba na so na shiga gidan ba mu gama maganar ba.
          Zama na yi a kan ɗaya daga cikin kujerun falonta, bayan ta amsa mini sallama ta yi mini jagora har cikin falon, sannan ta fice. Lemun Coca-Cola a ɗan ƙaramin tire ta ajiye gabana, sannan ta zauna tana faɗin,
         "Oyoyo Maman Haidar! Yau na so shiga gidanki Amini ya kawo mini aikin kajin da ya hana ni fitar."
          "Ni ma yanzu wani uzuri ya shigo da ni, wurin mai hajarki nake so ki kai ni na zaɓo kaya. Sannan ki yi mini jagora wurin mai ɗinkinki ya rantsama mini ɗinki mai kyau, irin na gani na faɗa da tsokanar magana."
        Da dariya na ƙare maganar saboda ƙoƙarin kore damuwar da nake ciki a kan fuskata. 
"Wai don Allah da gaske auren nan zai yi?"
          Tambayar da ta yi mini kenan bayan ta shiga natsuwarta.
 "Tun ranar ai na faɗa miki, yanzu haka a cikin satin nan za a yi auren idan Allah ya ara mana numfashi."

         "Hmmmmm! Ikon Allah!"

Abin da ta faɗa kenan sannan ta janyo wayarta ta yi kira, mintuna a tsakani bayan an ɗauki wayar ta ce, 
            "Hajiya Ruƙayya Wada, kaya nake so ki turo mini yanzu na zaɓa. Ki haɗo da sarƙoƙi da takalma half shoe's masu kyau kalar ya yi." 
      Tana ƙare maganar ta ajiye wayar tare da rungume hannu ta ce,
      "Jarumtarki tana burge ni Maman Haidar. Ina ma zan iya kwatanta ko da rabinta idan Amini ya tashi aure? Amma har ga Allah na san ba zan iya ba."

          "Za ki iya! Matuƙar kika saka kanki."

    Ajiyar zuciya ta sauke mai ƙarfi sannan ta ce, "Mu bar maganar! Wane shiri kika yi wa kanki a matsayinki na Uwargida?"

      "Shiri kuma?" 
      "E"  Ta ba ni amsa, cikin rashin sanin inda zancenta ya dosa na ce, 
     "Wane iri fa?"
             "Gyaran babbar hedkwatar mana! Don ke ma kin san ba zai yiyu amarya ta zo ta same ki a haka babu wani canji ba. Saboda ita kanta sai ta yi gyara sosai kafin ta shigo, to ke ma me zai hana ki yi gyaran da za ki mayar da tsohuwar shimfiɗarki sabuwa dal?"

        "Zan yi! Yanzu haka ma ina kan yi."
Amsar da na ba ta kenan, don ba na so ta fara nuna mini ban iya komai ba a kan tattalin miji kamar yadda ta saba. 
       "Kin yi farar dabara, bari na ƙaro miki wasu zafafan da aka kawo mini daga Maiduguri jiya. Don mazan nan idan babu sabon service kullum idanuwansu suna kan leƙe-leƙen wasu matan. Amma idan kina gyara jikinki komai cif-cif, da wuya su yi miki kallon raini balle su nemi ɗauko miki wata masifar a waje."

       Ta miƙe ta kawo mini kayan mata kala-kala, tun daga kan shu'umar humra har wani ɗan matsin da ta tabbatar mini yana mayar da tsohuwa yarinya. Sannan turaren tsugunno da na jiki, bayan tsimin da ƙamshinsa kaɗai zai sa mutum ya ji sha'awar shan sa. 
        Leda na zuba su duka, na ce da ita sai na je gida zan sha, ta matsa mini na sha tsimin a nan saboda ya yi saurin kama jikina. Domin akwai buƙatar na sha shi kamar sau uku kafin bikin, domin ya haɗe mini jiki ta yadda idan na karɓi girki zai rasa bambance wace ce amarya a tsakaninmu. 
         Kasa musa mata na yi, saboda ba na so ta gano ba na so, kaɗan na kurɓa na rufe gorar swan ɗin da ta cika mini ita taf! Hira muka ci gaba da yi a kan amfanin kayan mayen, tare da yi mini bayanin yadda suke yi mata aiki sosai har aka kawo kayan.
         Kala biyu na zaɓa masu kyau shadda da lesi, sannan na zaɓar wa su Ummu Salma atamfa ɗaya da shadda gizna, wadda ba ta kai kuɗin tawa ba yadi bakwai su uku. Saboda na san estimate ɗin abin da suke ci don na fara koyon ɗinki tun kafin na yi aure. Yanzu ma ina da experience sosai a kan abin da ya shafi ɗinkin duk da ba na yin sa.
          Gyale, takalmi da jaka na samu mahaɗin shaddar da lesin. Sannan na zaɓar mana sarƙoƙi nawa set biyu su Ummu Salma ɗaiɗaya. Na ɗaukar wa Haidar 'yan kanti ɗaya shi ma ya yi kala biyu kamar yadda su Ummu Salma za su yi. Maman Taufiƙ ta kira mai kayan aka haɗa lissafin kuɗin dubu saba'in da uku cif. Shiru na yi ina nazarin kuɗin a raina, saboda ba na so na yi abin da zai ƙure  mini maneji. 
        Kamar Maman Taufiƙ ta fahimce ni ta ce, "Kayanta akwai tsada, amma kuma quality ne za ki ji daɗinsu sosai."

       "A ido ma kayan kowa ya gani zai san sun ci kuɗinsu. Amma akwai uzurorin da ke gabana, zan rage kala ɗaiɗaya mu ji nawa kudiyn za su kama."
          "Kada ki rage ki bar su kawai, ba ta da matsala duk lokacin da kika samu dama da ƙire-ƙire ma za ki biya ta ba sai duka ba."
          "Gaskiya na ji daɗi Maman Taufiƙ! Saboda a yanzu samun masu haƙurin bashi 'yan kaɗan ne a wannan lokacin da muke ciki."
          Ta yi murmushi mai sauti sannan ta ce, "Ai Maman Marwan ba ta da matsala ko kaɗan, kuma ta iya hulɗa da mutane sosai. Duk masu sayen kayanta sun san da hakan, shi ya sa ba na iya sayen kaya a wurin kowa sai wurinta. Ga quality, ga sauƙin kai, kuma babu matsi balle a dame ka da aiken kawo kuɗi wata ya ƙare. Tana ɗaga ƙafa musamman idan ta san kana cikin masu biya babu taurin bashi."
         "Ai kuwa in Sha Allah za ta same ni mai cika alƙawari, don ni ma ba na son bashi sai ta kama dole. Ki ce ta turo account yanzu na tura mata 20k ɗin da nake da ita ƙasa, idan aka yi biya zan ƙara mata wani abu in Sha Allah!"

       A haka muka kai ƙarshe ta turo da account na yi mata transfer, sannan Maman Taufiƙ ta kira mini mai ɗinkinta ya zo muka ba shi kayan, Bayan mun zaɓi wanda zai yi mana a wayarsa. Shi ma na ba shi 10k deposit ta account ɗinsa, ya tafi bayan ya yi mana alƙawarin zai haɗa ɗinkin a cikin kwana uku.
       Sauran kayan na saka a leda na yi gida, zuciyata cike da nishaɗin. Ko babu komai zan yi wa Mukhtar barazana tare da gayyar danginsa da zugar mutanen amarya.
       Yaran ma da na sanar da su suka shiga tsalle suna murnar sun yi sababbin kaya. Ummu Salma kaɗai ce na hango damuwa a kan fuskarta, hakan ya sa na tattara kayan na mayar a leda na bai wa Iman ta kai ɗakinmu. Sannan na zaunar da ita na gyara zamana na ce, 
        "Damuwar me ce na gani a kan fuskarki?"
        Hawaye ta goge sannan ta ce, "Wai da gaske Abbanmu aure zai yi?"

        "E gaske ne! Me ya faru?"

    Amsar da na ba ta kenan ina haɗe fuska, domin ba na so ta ɗora wa kanta takaicin auren. Ta hana kanta sukuni a banza a kan abin da ko ni ban da ikon hanawa balle ita. 

        "Wace ce zai aura?"

      "Ko ma wace ce, idan ta zo ai za mu gan ta. Don haka idan ma damuwa kike yi a kan auren nan da Abbanku zai yi ki daina tun wuri, saboda babu wanda ya isa ya sauya abin da Allah ya ƙaddara. Shi ya ke sa a yi, kuma shi yake hanawa, idan ya nufa babu wata damuwar da zai sauya abin da aka rubuta. Idan kuma bai ƙaddara ba, duk yadda aka kai ƙololuwar son abin sai an bar shi dole."

       "To Allah ya sa tana da kirki."

        "Ko tsiya take yawo a jikinta babu abin da ya shalle mu, don ba a kanmu za ta zauna ba."
            Amsar da na ba ta kenan raina a ɓace, saboda maganganunta sun dawo mini da jin zafin auren sabo. Cikin tsananin ɓacin rai na fara nuna su da hannu na ce, 
        "Duk wanda ya yi gangancin shiga shirgin amaryar nan, sai na saɓa masa. Ku tsaya inda Allah ya ajiye ku, hakan sai ya fi mini alheri da ku shiga hurumin da ba naku ba. Sannan ku yi nesa da duk abin da zai sa a ga laifinku, don ta wannan hanyar ne kawai za mu tattara komatsan matsalar duka mu wurgar gefe, domin a zauna lafiya mu huta da hayaniya."
        Yanayin fuskokinsu ya tabbatar mini da maganganuna da kashedin da na yi musu, sun shiga kansu da kyau sun zauna. Na miƙe da ledar kayan da Maman Taufiƙ ta ba ni na yi ɗaki, zuciyata sai zafi take yi mini a kan tsananin kishin auren da nake ji a raina.
        Ina ɗakin na jiyo sallamar Taufiƙ yana faɗin,
     "Ku bai wa Mamarku in ji Mamata."

        Haidar ya shigo da leda baƙa ya miƙo mini, tun kafin na karɓa na ji ƙamshin naman kaji. Na karɓa na ce ya yi masa godiya, ya ce da ni ai ya wuce, na buɗe ledar na ɗauki yanka ɗaya na miƙa masa sauran na ce su je su raba.
        Duk ƙaunata da naman kaji, haka na ajiye shi a kan bed side na kwanta ina ta ƙuncin rai. Saboda tunanin lefen da ya yi bai faɗa mini ba balle ya nuna mini na gani, sannan ni bai ba ni ko falle ɗaya ba balle na rage takaicin da yake ƙoƙarin cusa mini. 
           Wayata da ke ruri ta katse mini tunanin da nake yi, da hanzari na ɗauka ina sauraron abin da Ummata take cewa, 
         "Yanzu Zaituna Mukhtar zai yi aure amma ba ki sanar da mu ba?"

       "Ki yi haƙuri!"

    Abin da na iya cewa kenan bayan na sauke ajiyar zuciya mai fito da feshin iska 'Huuuuuu!'
           "Shi kenan! Allah ya ba ku zaman lafiya. Zuwa gobe zan aiko miki da sababbin kujeru, idan an zo za a ɗauki naki a kawo mini."

         "Na gode sosai Allah ya ƙara buɗi."

Iya maganar da na yi kenan ta kashe wayar, hawaye ya dinga fareti daga kwarmin idona zuwa gefe da gefen fuskata. Motsin shigowar yaran ya sa na yi jarumtar gogewa tare da gyara kwanciyata, don ba na so su gano damuwar da nake ciki balle hakan ya saka su rashin walwala.




Kishiya akwai zafi. Amma idan an saka haƙuri da juriya komai zai zamo kamar ba komai ba.🥲




   
  D.AUTA CE✍🏼


*ABOKIN AIKINA*


*@HADIZA D. AUTA*


*SADAUKARWA: DAUGHTER ANUP*


*ASHIRIN DA TAKWAS.*

         Da sanyin jiki na wayi safiya, domin kuwa ban yi wani baccin kirki ba a daren ranar. Hakan ya janyo mini ciwon jiki da ciwon kan da na ji ba na ra'ayin fita ranar. Kai-tsaye na tura wa MD saƙon ba na samun damar zuwa offis.
        Bayan mun karya ni da yaran muka fara ƙoƙarin fitar da kujeru a tsakar gida, kafin mai adaidaita ya zo ɗaukar su.
       Muna tsaka da fito da su Mukhtar ya fito daga ɗakinsa yana waya.

       "Ki kwantar da hankalinki, ba ni na ce zan ba ki ba? Zan ba ki... Yawwa! Ko ke fa! Ki jira ni anjima kaɗan zan aiko mi..."

      Wani tuƙuƙin baƙinciki ya taso mini, nan take hawaye mai zafi ya cika mini ido. Na fakaici idon yaran na goge, sannan na bar tsakar gidan na koma ɗakina. Kwanciya ta kenan yaran suka shigo da gudu, suna sanar da ni ga Najib mai adaidaita ya zo ɗaukar mu, na ce su tafi kawai Allah ya tsare hanya. 
      Bayan fitar su na ji kuka mai ƙarfi ya suɓuce mini ba tare da na shirya wa zuwansa ba. Na jima ina kukan kafin na ji sassaucin nauyin da nake ji a cikin zuciyata. Na shiga tunane-tunanen  matsayin aurena da kalar zaman da nake yi a gidan Mukhtar. 
      Ban san lokacin da bacci ya kwashe ni ba sai da na ji yana rafka mini sallama a saman kai. Firgigit na farka tare da zabura saboda ganin shi a saman kaina, da hanzari ya juya zai fice ɗakin yana cewa,

       "Umma ce ta aiko da kaya, ki tashi ki je ke yaran suke jira tun ɗazu."
        
       Na miƙe ƙasusuwan jikina suna ƙara na fito ɗakin jikina liƙis, taku nake yi babu kuzari na yi tsakar gidan. Inda na ga yaran tsaye cirko-cirko da sababbin kujerun da suka kawo a gabansu, waɗanda muka ajiye kuma har sun fitar da su waje ban sani ba.
        Umurni na ba su a kan su shigo da kujerun, na nuna musu inda za su ajiye da yadda za su jera mini su. Yadda na faɗa haka suka yi, nan take wurin ya fito fes ma sha Allah gwanin burgewa. Musamman da suka maƙala mini sababbin labulan da suka zo da su masu matching da kalar kujerun. 
       Farinciki ya ziyarci zuciyata, a lokacin da suka tafi na zauna saman kujerun ina goge ruwan hawayena. 
     'Umma ta kasa fahimtar gundurar da na yi da rayuwar auren Mukhtar. Ta kasa gano inda matsalata ta fuskanta ba zama da shi ne damuwata ba. Yaushe zan fita daga ƙangin wannan aure na kama-karyar da nake yi?' 
         Shiru na yi daga zancen zucin saboda amsar da zuciyata ta ƙara kitsa mini wadda ta sa ƙirjina bugawa dam-dam! 

     'Sai kin tsufa yaranki za su yi miki amfani idan ciwon hawan jini ya kama ki, a lokacin za su dinga zaryar kai ki asibiti ana rubuto miki magunguna wani bayan wani.' 

    "Innalillahi wa inna ilaihirraji'un!" 

      Ita ce kalmar da ta fito daga bakina ban shirya ba,
     'Idan kuwa har haka ƙarshen haƙurin da na yi zai kai ni. To rayuwar da nake yi a yanzu ba ta da wani amfani ko kaɗan, matuƙar ƙarshe na ya zo a ɗawainiyar kai ni asibiti. Domin a yi ta jera mini takardun maganin hawan jini, yarana su sha wahalar kai-da-komo da ni a tsakanin gida da asibiti.'

      Amsar da na bai wa kaina kenan a zuciya kamar yadda zuciyar ce ta kitsa mini komai.
       ''Ya zama dole na yi wata hoɓɓasa, tun kafin wankin hula ya kai ni dare"
         "Komai za ka yi yanzu, aikin gama ya  gama sai haƙuri. Kuma zama da ni yanzu kika fara, don wallahi babu wata kotu ko alaƙalin da zai sakin ki ba tare da amincewa ta ba. Yadda muka fara rayuwa tare haka za mu ƙare ta, saboda babu ɗan iskan ƙaton da zan bari ya aure ki bayan ya gama bibiyarki da aurena, ba tare da ya yi duba da illar ɗaukar wa kansa kaya a dalilin auren da ke saman kanki ba."
      Maganar Mukhtar kenan a kaina yana huci tamkar ya dake ni, da kallon mamaki na bi shi baki a sake. Saboda ƙoƙarin datse mini farincikin rayuwa da yake yi koyaushe. A bahagon tunaninsa wannan barazanar da yake yi ce take hana ni ɗaukar wa kaina matakin gaggawa. 
       Ajiyar zuciya na sauke sannan na yi dariya a matsayin tura masa haushi na ce,        
        "Maimakon tsoro ko fargaban da kake ƙoƙarin cusa mini a zuciya, sai maganganunka suka dawo ba ni dariya haiƙan. Wai kai a tunanin da kanka yake ba ka burgarka ce take riƙe da ni a gidanka? To ka yi kuskure kuma ka saɓa lamba. Kamar yadda na sha faɗa yanzu ma zan maimaita; neman gamawa lafiya da rabuwa da mahaifiyata cikin aminci; ya sa ba na zartar da hukuncin da nake yanke wa kuturun aurenka, a kowace daƙiƙa da bugun numfashina. Ka gode wa Allah ko lahira wani yana cin albarkacin wani; kamar yadda kake cin na 'ya'yanka a wurin Ummata yanzu, duk da kai ko kaɗan ba ka san zafinsu ba. Amma idan tani ake bi abin da ka sani ne zan maimata yanzu ka ji, idan ana saki dubu duka sai na katse igiyoyin har ma nemi ƙarin wasu na daddatsa."

     A fusace ya yi kaina zai kai mini duka, na yi hanzarin ja baya tare da nuna shi da hannu ina cewa, 
       "Kul! Kada ka yi gangancin taɓa ni ka janyo na yi maka aika-aika yanzun nan. Na fi so na je gidan kaso da na bari ka dake ni ka hana ni kokawa, domin mari da tsinka jakar da kake yi mini kullum ba don ba na iya ramawa ba ne nake ƙyalewa. Idan ka kai ni bango kuma zan nuna maka na fi ka zama 'yar tarawi."

      "Idan ma kin ce za ki rama ai ke ce a wahale, domin aurena ne ba kya so kuma ba zan taɓa sakinki ba."

      Yana ƙare faɗar hakan a fusace ya bar wurin zai fice falon, na biyo shi a zafafe ina faɗin, "In dai wannan baƙin auren kake taƙama da shi ka faɗo. Don tuni ya lalace babu komai a cikinsa face kwasar zunubai."

      "A hakan kuma za ki zauna ko kina so ko ba kya so!"
        Abin da ya faɗa kenan ya fice gidan, tare da bugo ƙofar da ƙarfi har sai da ƙirjina ya buga sanadin sautin ƙarar ƙofar,

  'Garam!!!'

      Dawowa na yi na zauna, zuciyata sai hawa da sauka take yi ina fisgar numfashina da ƙarfi. Na ɗauki lokaci a haka sannan na fara jin sallamar wasu mata a bakin ƙofar falon.
     Na fito ina amsa sallamar idona a kansu, tunanin inda na san su a raina na yi amma na kasa. 

"Dangin amarya ne, mun zo duba ɗaki." 

        "Allah Sarki to ku shigo mana!"

       Na ƙare maganar cikin sakin fuska da murmushin yaƙe na yi gaba, suka bi ni a baya na ja na tsaya a bakin ƙofar ɗakin. Da fara'ata a kan fuska na ce da su,
      "Ku jira na karɓo muku makullin ɗakin a wurinsa."
         "Ai shi ya ce mu shigo, ga makullin a nan ya ba mu."
       "Faɗuwa ta zo daidai da zama, yanzu yake sanar da ni zai ba ni na ajiye muku kafin ya fita."
     Maganar da na yi kenan ina 'yar dariya, a ƙoƙarin kore damuwar da ke kan fuskata.
      "An hutar da ke ai tun da ya ba mu!"

       Wata matashiya daga cikinsu ta faɗa cikin haɗe rai tana ƙoƙarin buɗe ɗakin, ɗakina na nufa zuciyata tana tafasa saboda duka biyun da yake ƙoƙarin hawa kaina. Tsakanin rashin mutuncin da Mukhtar ya yi mini da rainin hankalin da dangin amaryarsa suke ƙoƙarin kawo mini.
       Wanka na faɗa shaf-shaf na dirje jikina, cike da jin haushin bai sanar da ni zuwansu ba. Da ban bari suka same ni a yadda nake ban cancanɗa kwalliya ba. 
      Ƙwafa na yi kawai tare da cije leɓen ƙasa a lokacin da na gama shafa hoda sama-sama.  Wata doguwar rigar atamfata na saka fited gawn, kuma mai fitting ɗina sosai a duk lokacin da na saka. Turaruka nake fesawa ina jiyo sautin muryoyinsu suna yaba tsarin falon.
      A daidai lokacin da suka shiga kitchen na fito na kunna tv sannan na zauna kan kujera ina kallo. Duk da ba na gane komai amma ban ɗauke idona daga kan tv'n ba jefi-jefi na latsa wayata.
     Sun ɗauki minti sha biyar a kitchen ɗin, suna ta maganganun da ba na tantance abin da suke faɗa. Sannan suka fito daga Kitchen ɗin suna faɗin,
      "Ma sha Allah wuri ya yi kyau! Sai fatan Allah ya ba da zaman lafiya da ƙazantar ɗaki."

     Kaina na ɗago daga latsar wayar da nake yi na ce da su, "Amin, har kun gama?"
      Wasu biyu suka wuce suna faɗin
 "E, mu za mu tafi."
        Yayin da wasu masu hankalin cikinsu uku suka ce, "Mun kammala, gobe idan Allah ya kai mu za mu zo a yi jere. Allah ya ba ku zaman lafiya da haƙuri da juna."

     Da murmushi a kan fuskata na ce da su, "Amin-amin." Suka nufi hanyar fita na rako su ina yi musu godiya da Allah ya tsare. 
      Sai da suka fice gidan sannan na rufo ƙofar na juyo zuciyata a cunkushe da takaicin Mukhtar. Don da ya faɗa mini za su zo, dole ne a tanadar musu wani abu, saboda babu daɗi su tafi hannu rabbana ba a ba su komai ba.
     Ko zama ban yi ba Maman Taufiƙ ta shigo na tarbe ta da fara'a muka zauna. Kallon tsarin falon ta shiga yi da kujeruna da muke kai, fuskarta a sake ta ce da ni, 
     "Kujerun nan sun yi mini kyau Maman Haidar!"
         "Na gode" Na faɗa cike da murmushin da ya kasa barin fuskata. Zamanta ta gyara tana faɗin,
      "Wasu mata na gani sun fito daga gidan nan suna ta yabonki. Kuma jikina ya ba ni kamar dangin amaryarsu ne?"
      "E, su ne. Sun zo duba ɗakin amarya da tsarin gidan."
       "Cabɗijam! Lalle kin fara aika musu makaman nuclear. Domin kuwa da kunnena na ji wata yarinya daga cikinsu tana faɗin"
       'Ni fa haushi ya hana ni tsayawa na fito gidan. Don wannan haɗaɗɗiyar mata ko ni aka haɗa kishi da ita an cuce ni balle Barira. Cabɗi! Na tausaya wa mata gaskiya, don ta kawo kanta inda za a ga kasawarta'
       'Idan ban da ma hali irin na maza da ba a iya musu; mai irin wannan  zankaɗeɗiyar macen ne zai auri Barira?'
        'Shi aure ai nufi ne na Allah! Ita ce matarsa shi ya sa ya nemo ta. Don haka ku zo mu je mu bi su da addu'ar zaman lafiya, saboda alamu ya nuna a fili ta yi sa'ar kishiyar da babu ruwanta'

      Sanyin daɗi na ji ya tsirga mini, domin labarin da Maman Taufiƙ ta faɗa mini ba ƙaramin faranta zuciyata ya yi ba. Shiru kawai na yi ina ta murmushi, sai da ta yi 'yar kuwwar jin daɗi sannan ta sake cewa,
        "A gaskiya Maman Haidar ke ƙwaro ce! A tashi guda kin hargitsa musu lissafi sun fita da ke a bakinsu."

     Murmushi na yi mai sauti sannan na ce, "Ai shi yaƙi ɗan zamba ne, idan ba ka iya shi ba za ka sha wahalar kashe abokan gaba, kuma za a yi saurin gano maɓoyarka domin a kawo maka farmaki. Don haka ta wannan hanyar kaɗai zan iya rama abin da ake ƙoƙarin yi mini a fakaice. Saboda faɗa da tashin hankali ba zai kawo gyara ba, kuma ba zai sa a fasa abin da aka yi niyya ba. A ƙarshe ma biyu babu ake yi a rasa mutunci kuma a ɓarar da ƙima."
       "Kai jama'a! Maman Haidar ke ta daban ce a cikin dubban mutane. Ban taɓa cin karo da macen da za a yi wa kishiya ta yi juriya irin taki ba. Wai don Allah da gaske ba kya jin komai a cikin ranki? Ni fa na kasa gasgata wannan lamari naki mai kama da almara."
       Tambayar da ta yi mini ba ƙaramar dariya ta saka ni ba, saboda yanayin da ta yi maganar tamkar wata zautacciya. Sai da na gama dariyar sannan na ce da ita, 

       "Kowace mace tana da kalar nata kishin Maman Taufiƙ! Amma da a ce za a yi koyi da kalar kishin da magabata suka yi; Da mata da yawa ba su ɓarar da damar da Allah ya mallaka musu ba. Don sau da yawa namiji ba don ba ya son matarsa yake ƙara aure ba, ke wani lokaci ma ba ya ƙara ƙaunarki; har sai ya jera ki da wata ya gano akwai tazara a tsakaninki da sauran mata. Saboda haka da a ce za mu gane mu daina zafafa kishin maza idan za su ƙaro aure, da mun taimaki kanmu mun rage nauyin wahalar da muke ɗaukar wa kanmu a kan ɗa namiji. Ni kin ga ma a ranar da ya zo mini da zancen auren..."
      Na kwashe duk yadda muka yi da Mukhtar na faɗa mata, dariya ta shiga sheƙawa har da riƙe ciki. Sai da ta gaji don kanta tana goge ƙwallar dariyar ta ce da ni, 
     "Wallahi ba ki da kirki Maman Haidar! Wannan tura haushin har ina saboda Allah?"

     "Da a ce ban yi masa hakan ba, hauka zai siyo kasuwa ya manna mini ban ji ban gani ba. Saboda duk wani tashin hankalin da zan yi a lokacin; kai-tsaye zai ɗora shi a mizanin taɓin hankali. A ƙarshen ma zagina mutane za su dinga yi ba tare da sun yi duba da ƙunar da zuciyata ke yi, su tausaya mini ba."

     "Wallahi zancenki gaskiya ne Maman Haidar! Amma kin san me? Ni ba zan iya wannan dauriyar ba. Allah kada ka jarrabe ni da irin wannan musibar mai wuyar shanyewa, don na san duk ranar da Amini ya sanar da ni zai yi aure; ba zan ɗaga daga inda nake ba zan mutu."




😱cab!🤭 Na yi nan🏃🏻‍♀️




D.AUTA CE✍🏼

*ABOKIN AIKINA*


*@HADIZA D. AUTA*


*SADAUKARWA: DAUGHTER ANUP*


*ASHIRIN DA TARA.*

         "Ba za ki mutu ba!" 
 Zancen da na faɗa mata kenan cike da karsashin da ke cikin raina. Wani kallo take yi mini ko ƙyaftawa babu, kafin ta muskuta kaɗan tare da sauke ajiyar zuciya ta ce,
       "Ni kaɗai na san yadda nake jin zafin abin a cikin raina. Yanzu haka ke za a yi wa kishiyar nan, amma wallahi har zuciyata nake jin ƙunar kishin a haɗa ki da wata, a matsayin abokiyar zama a cikin gidan nan."
       "To ki ma daina, don ni babu wani abu da zan gani yanzu a gidan nan, wanda zai ɗaga ni sama balle ya buga ni a ƙasa na ji zafinsa. Ke ma da za ki sauke tulin nauyin da kike ƙoƙarin lodawa, da kin taimaki kanki kin huta da tashin hankalin da zai iya bijiro miki a gaba."
     Na faɗa mata maganar ne daga zuciyata, don na fara ƙosawa da ɗora ta a kan hanya tana zamewa. Shiru ya ratsa tsakani ba tare da mun sake cewa komai ba. 
      Girgizar ƙafar da take yi, tare da haɗe fuska da cizon leɓe; ya tabbatar mini da ba ta ji daɗin maganar da na yi ba. Hakan ya sa na yi hanzarin faɗin,
      "Ki yi haƙuri da ni Maman Taufiƙ! Amma Allah ya gani ba na son wannan zaƙewar da kike yi wa kishi, maimakon ki yi masa rigakafi tun kafin ya riske ki; amma ke kullum sai ƙara taryar gabansa kike yi domin ku yi arangama." 
       Na tsahirta da maganar ina karantar yanayinta, sannan na ɗora da cewa,
       "Ina faɗa miki wannan maganar ne a matsayinki na wadda na yarda da ita, kuma nake yi mata kallon ƙawa, aminiya, kuma abokiyar shawara. Don haka ki yi haƙuri da gaskiyar da nake faɗa miki tsakani da Allah babu rufa-rufa."

      "Na san gaskiya kike faɗa mini, amma zancenki na ƙarshe ya yi matuƙar taɓa mini zuciya. Domin ina ji a raina tamkar kina mini bushara da zuwan tawa kishiya bayan taki."
       "Maganar da na faɗa ko kaɗan ba ta danganci hakan ba, don ba na fatar a yi miki kishiya ko don wannan zazzafan kishin naki. Amma ina miki hannuka mai sanda ne saboda ki karɓi abin da ya shiga gabanki; ko don kare kanki daga matsalar da ke biye da ke, ba tare da kin shirya wa zuwan ta ba."
      Miƙewa ta yi tana dakan ƙasa da ƙafafuwanta tamkar wata yarinya, fuskar tausayi ta yi tare da langaɓe kai ta ce,
      "Oh my God! Kin sake kwatawa Maman Haidar. Ni wallahi shi ya sa ban cika son muna zancen kishiya da ke ba. Saboda kina bar mini zantukanki koyaushe suna mini zillo a zuciya."
       "To na daina mu zubar da zancen duka! Gobe idan Allah ya kai mu za a yi wa amarya jere. Me kike ganin ya dace a yi musu a matsayin abincin da za su ci idan sun zo."
      Zama ta yi tana haɗe rai tare da aiko mini harara ta ce, 
       "Wannan nauyin ai ba naki ba ne Hajiya! Ki jira idan angon ya zo ku yi shawarar abin da za a yi musu. Don haƙƙinsa ne, kuma shi zai bayar da duk abin da za a dafa daidai ƙarfinsa."
       
     Murmushi na yi mai sauti sannan na ce, "Yo to ni ina na san yadda abin yake? Na ɗauka kamar yadda muke dafa abincin gida haka za a ba su su kora da ruwa. Ashe abin babba ne ba yadda na zata ba?"
       "Idan ya zo kuka gama shawara, sai ki kira ni a waya ki sanar da ni. Saboda goben a yi komai da wuri ba sai sun zauna jira ba."
       Natsuwata na shiga sosai ina ɗaga mata kai tamkar wata doluwa, saboda tunanin da zuciyata ta faɗa. A kan yadda za mu kwashe da shi hanyar 'yan barkono idan na yi masa zancen. Na so ko bai sani ba na yi musu girkin na fita kunyar idonsu, saboda ba za su yi zaton shi ne da laifin ba idan an hana su abincin. A kaina komai zai juye su je su yi ta zagi na a banza ban ji ban gani ba.
     Daga haka muka kitse zancen na rako ta har bakin ƙofar gidan, muna ci gaba da tattaunawa su Ummu Salma suka dawo makaranta. 
      Cikin sa'a shi ma mai mashin ya dire shi a ƙofar gidan yana shan ƙamshi, Maman Taufiƙ ta yi hanzarin shigewa gidanta ni ma na koma cikin gida. Tsakar gidan na ja na tsaya bayan yaran sun shige ciki.
      Ya shigo gidan ko sallama bai yi ba zai wuce buguzum! Na yi hanzarin bin sa a baya ina faɗin, 

"Magana za mu yi ranka ya daɗe!"

      Ya tsaya ba tare da ya waigo ba, na je ta gabansa kamar ban taɓa jin haushin sa duniya ba. 
       "Gobe za a yi wa amarya jere. Me za a tanadar musu a matsayin abincin da za su ci, da wanda za su riƙa idan sun je gida su raba?."
      Kallon mamaki ya fara bin fuskata da shi kafin ya ce, "Me ya haɗa ki da tambayar abin da ya shafi aure na?"

       "Saboda ina cikin gidanka ina amsa sunan matarka a zahiri."
        
    Na ba shi amsa cikin gadara don na fahimci take-takensa ba zai bari mu ƙare maganar cikin daɗin rai ba.
        "To wannan ba abin da ya shafe ki ba ne! Ki fitar da kanki cikin abin da babu ruwanki."
       Yana ƙare maganar ya wuce fuu zai shige falo, na bi shi ina faɗin, "Da ruwana fa! Don ba na so a ce ban tarbe su da komai ba, a matsayina na uwargidan amarya mai ƙashin arziƙi."

    Ƙanzil bai ce da ni ba ya shige ɗakinsa, dariyata na ƙumshe ina faɗin, 
     "Ka kira mana Barirar mu ji su nawa za su zo? Domin a yi musu komai a wadace babu harkar ƙaranta."
     Bai kula ni ba har ya gama abin da yake yi a ɗakinsa ya fito ya nufi hanyar fita yana haɗe rai,
     "Na ce ka kira mana Barirar mu..."
      
       "Yanzu don biyar diddigi har da sunanta sai da kika binciko? Ai da kin yi haƙuri idan ta zo komai za ki gani da idonki."
       "Yo ita Barirar da ta gama gantalin talllar awara zan bi diddigi don na binciko wace ce ita?"
      Dariya na tuntsure da ita ina riƙe ciki saboda ganin yadda ya yi shock tare da ƙura mini ido baki a sake. Hakan ya ƙara mini kuzarin faɗin, 
     "Kai ma dai da neman zance kake wallahi. Allah dai ya ƙara danƙon ƙauna mijin Barira mai awara."

    "Ko kashi take kasawa a kasuwa ai sana'a ce balle awara. Don haka ni ita na hango ba awarar da take sayarwa ba, ki je ki ci gaba da tsegumin ki tun da ba sata take yi ba Alhmdulillah!"
      Na bar wurin ina ta  dariyar ƙeta, saboda safci faɗi ne kawai ya sa na laƙaba mata tallar awarar. Ashe da gaske na yi sara a kana gaɓa, tun da ya kasa shanye damuwar ya tona wa kansu asiri a ƙoƙarinsa na wanke ta.
       
      Har ga Allah na ji na ƙara raina auren a raina, na ji haushin kashe kuɗina domin na yi musu barazana. Ashe ma a hakan da nake na fi ta kyaun gani ko da ban yi wanka ba, saboda duk macen da ta san kanta ba za ta iya talla ba. 
      
   ***
Tun da safe wayar Maman Taufiƙ ce ta katse mini baccin da na koma bayan sallar asuba. Tambayar da ta yi mini a kan girkin ya sa na wartsake daga baccin ina faɗin,
     "Ki bar shi kawai, ashe ma ya ba da komai a gidansu za a dafa a kawo musu."
      Daga haka muka gama wayar na sauko daga kan gadon, saboda ganin su Ummu Salma har sun gyara katifar da suka kwana an ɗauke ta Haidar. 

       Ƙamshin wainar ƙwan da na ji yana tashi ya tabbatar mini da Ummu Salma tana kitchen. Faɗawa na yi idona a kan plate ɗin da nake da tabbacin kalacina ne ta zuba.
      Gaishe ni ta fara yi sannan ta ce, "Yanzu nake zancen na tayar da ke kada Indomien ta yi sanyi."
       Ƙwan da take soyawa na karɓa ina faɗin, "Je ku shirya kada ku yi latti lokaci ya tafi." 
      Na gama soya wainar ƙwan da ta rage na saka wa kaina, sannan na buɗe kulolin su Haidar na jefa musu tasu wainar. Ita ma na saka mata a wani plate ɗin silbar da take cin abinci da shi idan ta yi ra'ayi. 
     Sanin ba ta son zuwa da abinci Makaranta, ya sa na ɗauki plate ɗina da nata na fito ina ƙwala wa su Iman kira su zo su ɗauki kulolinsu.

        Na taras ta saka unuiform na ajiye mata plate ɗin a kan mirror ina faɗin, 
"Ki yi sauri fa! Don yau kun makara."
        Tura Indomien take yi cikin sauri sai ga su Haidar da gudu suna faɗin ta fito Najib ya zo. A gurguje ta lamushe ta fice da plate ɗin tana faɗin,

      "Mun tafi Mama!"

A dawo lafiya na yi musu har sun fice na ji dawowar Haidar da gudu yana faɗin, 
"Ba a ba mu kuɗin tara ba!"
      Jakata na janyo na zazzage kayan cikinta, na lalubo nera ɗari na miƙa masa ya fice da gudu. Addu'o'ar tsari na dinga yi musu ina jefawa a bakin ƙofar kamar suna wurin, sannan na je na yi brush na fito na karya.

      Ina gamawa na share gidan fes sannan na wanke kayan da aka ɓata, na ɓoye wasu kayana. Wanka na faɗa na shirya cikin shigar da ni kaina na san na yi kyau. Sallamar su Sajida da na jiyo na fito daga ɗakin ina zuba ƙamshi da murmushi a kan fuskata. Sajida da Mamarta na hango, sai wasu yayun Mukhtar na 'yan'uwa tare da yaransu. 
       Gaisawa muka fara yi da su babu yabo babu fallasa sannan na zauna. Sajida ta fara koɗa ni bakinta a sake take ta yabon kwalliyata, ina hankalce da Mamarta tana aika mata harara ta gefen ido. 
     Ganin ba za ta daina rawar ƙafar da take yi da ni ba ta miƙe tana faɗin,
      "Abincin masu jere za mu dafa. A fito mana da tukanen girkin mu je mu yi abin da ya kawo mu."
      Na miƙe tare da kiran Sajida da wasu yaran da suka zo da su muka nufi kitchen. A nan muka fito da manyan tukanena da murhu biyu, tare da wasu kayan da za a buƙata duka muka fitar da su a tsakar gidan.
      Ina ƙoƙarin shige falo na ji ihun yara suna faɗin ga motar kayan amarya nan ta iso. Dam-dam! Na ji dakan lugude a tsakiyar zuciyata, da murmushin yaƙe na zauna falo ina kiran lambar Firdausi. 
       Bayan ta ɗauka nake sanar da ita Mukhtar zai yi aure yau ake gyaran ɗaki,

      "Ai na ɗauka ba za ki faɗa mini ba har sai an kawo amaryar mu zo ganin ta."

        "Kwantas Hajiya! Ni ma daga sama na tsinci zancen auren. Don haka gobe ki fito ku danne mini ƙirjina."

       Na ƙare maganar a daidai lokacin da ake shigo da kayan gadon amarya ana shigar da su ɗakinta. Miƙewa na yi na koma ɗakina, mayafi na ɗauko mahaɗin kayan na saka, sannan na rufe ɗakin da key na yi wa matan da ke shigowa sannu da zuwa.
       Na fice tsakar gidan bayan jikina ya ba ni shaidar kallon da dangin amaryar suke yi mini. Maman Taufiƙ na kira a waya na ce ta fito ga aikin an kawo mana har gida. 
      Hannu na saka ina taya su aikin ba tare da na damu da kallon mamakin da Yayunsa suke yi mini ba. Na dinga jan Sajida da hira muna dariyar da iyakacinta kan fuskata, saboda ina so na nuna wa kowa ba na baƙinciki da auren a zahiri. 

    Ko da Maman Taufiƙ ta shigo har mun fara cin ƙarfin aikin, tare da ita aka dafa jallop ɗin shinkafa. Sannan aka yi musu tuwon da za su je da shi gida bayan jinjer drink. 
       Najib mai adaidatana na kira a waya ya siyo mana ƙanƙara da nufin idan ya zo na ba shi kuɗin. Babu ɓata lokaci ya siyo mini ya kawo na biya shi, aka baza ta cikin jinjar da aka shaƙe kula biyu da ƙullinta.
       Muna tsaka da haɗa kayan Mukhtar ya shigo gidan ya kira Mamar Sajida, wasu manyan ledodi biyu ya miƙa mata yana faɗin,
      "Don Allah a saka musu yadda na bayar kada a bari a taɓa musu komai."
     Ban bari na sake kallon inda yake ba ma balle abin da yake faɗin kada a taɓa. Sajida kawai ta kira tana faɗin ta samo wata kula a kitchen a saka musu naman kajin a ciki.
      Shock na yi da jin maganar kajin, nan take raina ya ɓaci ta yadda har na kasa ɓoye damuwa a kan fuskata. Miƙewa na yi ina faɗin,

     "Bari na kawo miki don kulolin suna ɗakina kuma na rufe."
       
       Ba ƙaramar jarumta na yi wurin haɗa kalmomin ba, saboda muryar kuka da ke ƙoƙarin tona asirin zuciyata. Toilet na shige na yi kukan rabin lokaci, sannan na wanke fuskata na fito na ƙara goga mai na bi da 'yar hoda sama. 
       Kulolin na ɗauko a cikin durowar Kitchen ɗina da na kulle da makulli. Sannan na rufe ina ƙoƙarin ɗagowa na ga Sajida a saman kaina, murmushi ta yi mini tana ƙoƙarin goge hawayen fuskarta ta ce,
       "Ki yi haƙuri Aunty! Duk da na san ba a kyauta miki. Amma kuma hakan ba zai hana na ba ki haƙurin ba, don na fahimci ba ki ji daɗin abin da Baba Mukhtar ya ce ba."
       "Kada ki damu! Na saba da halinsa ko kaɗan ban ji komai a kan zancensa ba. Kuma ai yana da gaskiya, idan ba mu ƙara ba ba zai yiyu mu rage musu ba."
     Ina ƙare faɗar hakan muka fito kitchen ɗin muka koma tsakar gidan.  A nan na ji Mamar Sajidar sun haɗa kai da wata 'yar'uwarsu, suna ta gulmar kayan ɗakin amarya.

      "Ni fa ina ganin kamar ba sababbi ba ne fenti ne."
       "Da gaskiyarki Maimuna! Don ko kujerun gyaransu aka yi ba sabon katako ba ne."

    Murmushi na yi mai sauti sannan na matso kusa da su na ce, 
     "Kaya ba su ne aure ba Yaya Maimuna, ku yi musu fatan zaman lafiya sai ya fi yi da sun da kuke yi."
       Kallon juna suka fara yi a muzance, kafin Yaya Maimunar ta ja kular da Sajida ta ajiye gefenta tana faɗin, 

       "Iyayi ne fa saka suruka makarantar boko. Tun da ya samu mai son sa tsakani da Allah ko yau ya mutu ya bar tarihi. Don ya ƙwaci wuyan hannunsa daga muguwar damƙar da aka yi masa." 

      Murmushi kawai na yi mata na bar wurin, saboda idon Sajida da ke kanmu. Kuma na tabbatar da duk abin da zan faɗa a wannan lokacin ba mai daɗi ba ne, kuma dole sai ta ji zafi domin ba zan yi ƙasa a gwiwa wurin rama daidai abin da ta faɗa mini ba, wataƙila ma na zarce awa wurin ƙoƙarin mayar da raddin na ci zarafinta a banza wofi."
  
      



     Hmmmmm! Shiru ma ai magana ce Zaituna.😢







D.AUTA CE✍🏼


*ABOKIN AIKINA*


*@HADIZA D. AUTA*


*SADAUKARWA: DAUGHTER ANUP*


*LAMBA TALATIN.*
    
       Abincin Sajida ta zuba mana a ƙaton tire, ni da ita da Maman Taufik muka yi ɗakina. Yayin da muka bar Yaya Maimuna da sauran dangin Mukhtar a nan suna cin nasu.
      Muna ɗakina muna ta hira bayan mun gama cin abincin. Ban san ya aka  ƙare da 'yan jeren ba, har sai da suka zo ƙofar ɗakina suna yi mini godiya, tare da sallama a kan sun ƙare za su tafi.
     Sauka lafiya na yi musu a bakin ƙofar ɗakin ban fita ba, a gabana suka fice ɗauke da kulolin abincin da aka ba su. Na dawo ɗakin inda su Maman Taufiƙ da Sajida suke ta hirar amaryar da kayan ɗakinta.
       Zama na yi ina 'yar dariyar yaƙe na ce da su,
 "Idan ba ku daina gulmar matar mutane ba, zan faɗa wa mijinta ya ɗauki mataki kanku." 
       Maman Taufiƙ ta maka mini jar harara tana faɗin, "Gaskiya ce muke faɗa kuma ke ma kin sani, don duk wanda ya gan ki ya san zaman boranci kawai amaryar ta zo yi a gidan Abban su Haidar."
       "Kin taɓa ganin inda namiji zai zuba kuɗinsa ya yi auren so don huce haushi; sannan a kira amaryar da boranci a gidansa?"
       Na ƙare maganar tare da kafe ta da ido ina murmushi, Sajida ce ta yi hanzarin ba ni amsa da cewa,
      "To ita dai wannan amarya Aunty; babu abin da zai tsinta a jikinta face kayan haushi da takaici. Ba ki gan ta ba fa! Yar firit da ita babu kumarin jiki balle gaba ko baya. Ta tafi 1 tamkar taɓaryar da ta shekara jingine cikin rana, ta bi duk ta ƙarmashe sai ɗan banzan son kuɗi ga surutun masifa." 
      
    Baki na rufe ina dariya saboda yadda Sajida take maganar tana yatsinar fuskar, tamkar ta hango wani abin ƙyama. Maman Taufiƙ kuma dariyar mugunta kawai take yi saboda an mata abin da take so.
       Ina ƙoƙarin yin magana kiran Amina ya shigo wayata, da hanzari na ɗauka saboda tuno ban sanar da ita labarin auren ba. Ƙorafi ta fara yi mini a kan rashin zuwana ofis, sannan ta ƙare da tambayar lafiya ko jikina ne ya motsa. Ina murmushi kamar a gabanta na ce,

      "Hidimar amaryar Mukhtar muke yi. Gobe za a yi walima jibi a kawo amarya, idan da hali ki zo mana bikin ko na rana ɗaya ne."

      'Aure!!!?'

  Tambayar da ta yi kenan cikin ɗaga murya, domin sautin da ta yi maganar da shi ya tabbatar mini; da mamakin auren da ta ji na ambata.  Gaskiyar hasashena ya fito a cikin amsar da ta ba ni kai-tsaye muryarta tana rawa.
      'Cabɗijam! Daman can kin san da batun auren ne? Ko kuwa yadda kika sanar da ni a sama haka ke ma kika ji shi?'
        "Na san da batun auren tuni, kawai dai ke ce Allah ya mantar da ni ban faɗa miki ba." 
     Ajiyar zuciya ta sauke mai ƙarfi sannan ta ce, "Ba zan samu zuwa gobe ba sai ranar bikin. Allah ya ƙara miki haƙuri da juriya. Mutanen wurinmu suna ta tambayar lafiya ba ki fito aiki ba jiya da yau. Na faɗa musu abin da MD yake sanar musu cewar ba kya jin daɗin jikinki."
      "Yawwa! Mutuniyata! Kin kyauta da yawa, ki gaishe da kowa don gobe ma da wuya na fito."
      Na ƙare maganar ina rufe baki don na san sai ta yi wani ƙorafin bayan wanda ta yi. 
"Gaskiya dai ki daure ki zo ko ba ki daɗe ba ki koma, saboda aikinki ya yi wa MD yawa ko yau sai da na rage masa wani a madadinki."
      
      "Hmmm! A dai ba shi haƙuri iya gobe da jibi ne kawai hutun, ranar monday tun da sassafe zan shigo har sai na riga ki zuwa."
      "To shi kenan! Amma dai..."
       "Ke dai me? Plss! Ki ba shi haƙuri idan kin ga da matsala kuma ki sanar da shi bikin kishiyata na tsaya yi."
     Ina ƙare maganar na datse kiran, don na san halinta da jan zance ya yi tsawon da sai ta sa na je aikin dole ko ba na so. 

      Sajida ba ta bar gidan ba har sai da aka yi magriba, tana tare da Maman Taufiƙ suna aikin gyaran gidan. Bayan gulmar auren Mukhtar da amaryarsa da suka saka wa gaba. 
Amma Mamarta da sauran waɗanda suka zo tuni suka yi gida. Ita ma don ta ƙi bin su ne ya sa suka tafi suka bar ta, bayan sun gama jefa mini magana a fakaice sanadin kujerun amarya. Da suka hau suna bitar zancen ba sabon katako ba ne. Ni kuma da bakin ƙaiƙayi na sake faɗar; a haka angon yake son kayan amayarsa mai son shi tsakani da Allah. 

   ***
Da safe ma tun wuri Sajida ta zo da jakar kayanta na walima, saboda an ce da ƙarfe huɗu za a yi walimar. Tare da ita muka sake gyare gidan fes muka feshe shi da turaren wuta mai ƙamshi. Ƙamshin sabon fenti da na turaren ya haɗe wuri ɗaya komai tsaf-tsaf.
       Sannan mai lalle ta zo aka tsantsara mana ni da ita, su Ummu Salma suka dawo su ma aka yi musu. Muna tsaka da hira Maman Taufiƙ ta shigo  da ƙatuwar leda a hannunta, Sajida ta riƙo mata suka yi ɗakina. Ganin haka na yunƙura zan bi su da busasshen lallena ban wanke ba.
       Sai ga sallamar wasu mata daga dangin amarya, gaisawa muka yi da su suna ƙoƙarin buɗe ɗakin na shige ɗakina na rufe. Toilet na shige kai-tsaye na wanke jam lallena da ya fito raɗau ma sha Allah!

      Kayan ɗinkinmu da na hango barbaje kan gado wani sanyin daɗi ya ratsa zuciyata. Saboda tun a kallo ɗaya na hango tsaruwar da ɗinkin ya yi. Musamman na shaddodin da suka sha aiki da zare mai kyau sai ƙyallin shuwari stones suke yi.
      Tawa shaddar baƙa ce aka yi wa aiki da jan zare da golden color. Sai ta su Ummu Salma mai golden ta sha aikin da ya ƙara fito da ita ma sha Allah.  Ɗinkin less ɗina kuma half bubu fensil ne, wanda aka yi adon bakin lesin ta gaba da bayan rigar. Kuma aka yi wa tsaguwar tsakiyar bayan rigar adon tattara ta kwanta luf-luf saboda gugar da lesin ya sha. 
     Su Ummu Salma ma ɗinkin atamfarsu A.shape ne ya sha adon stone sai ƙyalli yake yi. Haidar ma aikin da aka yi masa irin zaren su Ummu Salma ne ya yi kyau sosai.
     Zama na yi gefen gadon bakina har kunne muna ta aikin yaba ɗinkin da mai ɗinkin, saboda alƙwarin da ya cika bai saɓa mana ba. 
      Yaran ma da suka ga ɗinkin tsallen murnar suka dinga yi. Da ƙyar aka karɓi kayan hannun Haidar saboda ƙoƙarin sakawa da yake yi tun ba a yi masa wanka ba.

      Ko da ƙarfe uku da rabi ta yi duka mun shirya cikin shiga ta isa ni da yarana. Mun sha ƙamshin turaruka duk inda muka motsa sai ya tashi, saboda Allah ya ƙawata mini ƙamshi a zuciyata ba na sake da turare koyaushe a jikina.
     Hakan ya sa nake lalace rabin kuɗina a wurin masu turaruka, duk da faɗan da Umma take yi mini a kan na yi tanadi ko don yarana mata.

     Gidanmu ya cika da 'yan'uwa da abokan arziƙina, irin su Maman Taufiƙ, Firdausi, Amina da wata maƙociyata da muke ɗan gaisawa. Saboda masu kuɗin gaske ne a cikin unguwar ba kowa take kulawa ba. 
      Da motarta aka yi ta ɗaukar mutane zuwa inda ake yin walimar, sai da aka kai kowa sannan ni da su Maman Taufiƙ da su Firdausi suka take mini baya.
      Tun da muka fito daga motar kallo ya dawo kanmu, fuskata a sake nake kallon mutane tare da gaisawa da waɗanda ke ra'ayin gaisuwar.
     Kujeru na musamman aka tanadar mana muka zauna, ina ta shan ƙamshi da jin kaina wata sarauniya a cikin bayi. Saboda kallo ɗaya da na yi wa matan wurin na raina su. Tsakanin Yayun Mukhtar mata da matan ƙannensa, tare da 'yanmatan gidansu da zawarawan duka. Sannan dangin amaryar da na gama karance muzantar da ke kan fuskokinsu.
       
     Kasancewar ko da muka je an fara gabatar da walimar, ban samu ganin fuskar amarya ba saboda ta duƙe fuskarta cikin gyalen da ya yi wa kanta lulluɓi.
      A kan ƙafarta idanuwana suka sauka babu shiri na ɗauke kaina ina basarwa. Saboda ganin baƙar ƙafar da wani mahaukacin lallen da na hango kamar an zana tsutsotsi.
     Na shiga latsar wayata zuciyata cike da son ƙara kallon ƙafar amaryar Mukhtar, domin na tabbatar da abin da idanuwana suka hango mini tun a kallo ɗayan da na yi. 
     Bayan an gama walimar aka fara rabon ledodin takeaway. Har gabana Sajida ta ajiye mana buhu bayan ta gama raba wa danginsu nasu. Tare da sanar da ni kayanmu ne ni da mutanena. 
     Godiya na yi na miƙe tare da mayar da wayar a jakata ina gaisawa da mutane. Saboda nuno ni da mutane suke yi ana faɗin,

     "Ga Kishiyar Barira."

     Babu shiri dariya ta so suɓuce mini, saboda ganin Sajida riƙe da kafaɗar amarya tana ƙoƙarin isowa da ita inda nake. 
      "Aunty ga Amaryarki na kawo miki ita ku gaisa!"
      Ta ƙare maganar tare da saka mini hannunta a cikin hannuna. Ido na ɗan zaro saboda ƙarfin da na ji a hannun amarya mai kama da  kantar daka.
 
      "Buɗe fuskarki amarya ku gaisa da Auntynki!"

    Maman Taufiƙ ta yi maganar tare da sauke gyalen amarya domin mu ga fuskarta. Rungumo ta na yi a jikina cikin sigar duniyanci na ce,

     "Ku daina kalle wa Abban su Haidar amarya...Rufe fuskarki duk mai son ya gan ki sai ya biya mu kuɗi."
       
         Dariya aka yi duka wurin tare da ihu saboda mamakin da na bar su da shi a zuciya har muka bar wurin. Domin kuwa wasu daga cikin danginta sai da suka biyo mu har bakin mota; suna yi mini addua'r gamawa lafiya tare da zaman lafiya ni da ita da angon duka.
     A cikin mota ma zancen kawai su Amina ke yi Maman Taufiƙ tana ta jinjina abin da na yi. 
      
     "Gaskiya samun irin Maman Haidar a wannan lokaci sai an tona. Cabɗijam! Ni yaushe zan iya yin irin wannan ƙarfin halin ga Kishiya?."

     Firdausi tana dariya ta ce, "Ki bar ta nan da kika gan ta, ita ma ta ciki tana ciki ne fa! Amma da mun watse mun bar ta sai ta sha kukan kishin mijinta."

     "Ai kuma ƙawata ba dai jarumta ba! Don ko haka da ta yi ta ci galabar yaƙin a idon amarya da danginta. Domin ni kaina nan duk da nake da kishiyar a yanzu; Allah ya gani ba zan iya yin hakan ba idan za a ƙaro mana wata." Zancen da Amina ta yi kenan tana 'yar dariyar da ta ba ni dariya ni ma.

****
      A ƙofar gidanmu maƙociyar tawa ta sauke Firdausi da Amina tare da Maman Taufiƙ da Sajida. Saboda su Ummu Salma tun kafin mu baro wurin na kira Najib ya ɗauko su.
     Godiya muka yi mata sosai, sannan ta shige gidanta da motarta bayan an ba ta ledar walimar. A nan Sajida ta bai wa kowa ledarsa Maman Taufiƙ ta yi mana sallama ta shige.
       Firdausi da Amina saboda mazajensu  za su zo ɗaukar su, tare muka yi gidan suna ta tsokana ta.
      A nan ma bayan mun yi sallah wata sabuwar hira aka dasa. Sajida ta tuntsure da wata mahaukaciyar dariya tana cewa,

      "Wai Aunty kin ji ƙaimon da hannunta yake yi, tamkar busassar takarda?"




Kai jama'a😂
Ni dai babu luwana🏃🏻‍♀️🏃🏻‍♀️




D.AUTA CE✍🏼


*ABOKIN AIKINA*


*@HADIZA D. AUTA*


*SADAUKARWA: DAUGHTER ANUP*


*TALATIN DA ƊAYA.*

       "Innalillahi Sajida! Lamarinki da girma fa! Shi kenan kin saka wa yarinya ido komai nata kin kushe."
       Zancen da na yi kenan ina ƙoƙarin danne dariyata, saboda iskancin Sajida a kan amaryar Mukhtar ya shalle tunanina. 
        "Tsakani da Allah ni ma dai na raina ganin ta! Sai ka ce wanda ya hango ta idonsa rufe?" Amina ta ƙare maganar tare da tagumi, bayan jimamin da ya bayyana kan fuskarta a zahiri.
      "Hmmmmm! Ni gaskiyar ma ta yi mini yawa walla..." 
      Kiran da ya shigo wayar Firdausi ya datse sauran maganar da ke ƙoƙarin fitowa daga bakinta.

 "Yawwa! Bari na fito!"

     Abin da ta faɗa kenan ta miƙe tare da saɓa jakarta a kafaɗa ta ce da mu, "To ni zan wuce, sai gobe kuma idan mun dawo tarbar amarya." Sallama su Amina suka yi mata ta fice, na raka ta har bakin ƙofa. Zuciyata a cunkushe na ce da ita,
      "Wai kin san Mukhtar bai ba ni komai na faɗar kishiya ba?"
       "Cabɗijam! Hmm! Ki zura masa ido kawai, don babu inda cin amana take zuwa wallahi! Ko an yi gaba sai haƙƙi ya dawo da mutum baya. Idan ban da ya rasa mafaɗi; wannan ƙazamar yarinya me zai yi da ita?"
      Shiru kawai na yi saboda hawaye masu zafin da suke malala a kan fuskata. "Ki daina damar da kanki a kan Mukhtar! Na sha faɗa miki tun ba yau ba, saboda kuka bai da amfani a wurin da ba za a share maka hawaye ba. Da yardar Allah sai haƙƙinki ya fita a kan wannan auren takaicin da ya ɗebo wa kansa. Dauriyar da kike yi ki ƙara ƙaimi, domin salon takun kisa da mummuƙe ne daga kan shi har amaryar da danginsa duka. Marsiyatan banza azzalumai, marasa tsoron Allah..."
      Odar da maigidanta yake yi ya sa ta fice da sauri fuskarta a haɗe cikin ƙololuwar ɓacin rai. Domin tana matuƙar jin haushin halayen Mukhtar da matsin lambar da Umma take yi mini a kansa. 
     Abin da na sani ne, da ace tana da iko; da tuni ta raba aurena da Mukhtar. Saboda ƙawata ce da ba na ɓoye mata komai nawa, wani lokaci ma idan ta zo gidan tana gani da idonta. A wasu lokutan baya da suka shuɗe ma; ita ce ƙashin bayan ɗauke kwatar lalurorin da Mukhtar ya bar ni da su a cikin gidansa.

      Sai da motarsu ta tashi sannan na koma cikin gidan bayan na daidaita natsuwata. Shiga ta ɗakin ke da wuya Amina ta miƙe tana faɗin, "Ni ma zan tafi, ga shi can a ƙofar gida ya zo!"
      Ita ma na raka ta tare da yi mata godiyar karamcin da ta yi mini. Na dawo muka dasa wata sabuwar hira da Sajida, inda take nuna zallar takaicinta a kan auren Mukhtar. Na dinga nuna mata komai nufi ne na Allah kuma babu wanda ya isa ya kauce wa ƙaddarar shi.

    Bayan kowa ya yi bacci tsakanin Sajida da su Haidar, na yi shiru ina nazarin makomata ta gaba idan rayuwa ta ci gaba da shura mini a haka. Ƙarar shigowar saƙo ya sa na janyo wayata na duba, alert na yi tozali da shi wanda ya sa babu shiri na tashi zaune. 
       Dubu talatin na gani ɗauke da sunan MD na asali ALIYU S. NOMA, a matsayin wanda ya turo mini da kuɗin. Shiru na yi ina nazarin waɗanni irin kuɗi ne ya turo mini, saboda ban san wata ajandar da muka yi da shi ba, wadda kuɗin za su zo mini da yawa haka.
       Ga shi dare ya yi ƙarfe ɗaya saura balle na nemo shi na ji kuɗin na mene ne. Shigowar wani saƙon ya sa na rarumi wayar da sauri na duba, babu shiri jikina ya yi sanyi ƙalau, saboda wani sanyin daɗi ya ratsa zuciyata.

     'Ga tawa gudunmawa nan, Allah ya ba ku zaman lafiya'
   
     Abin da na yi ta maimaitawa a zuciyata kenan, kuma na kasa ɗauke idanuwana a kan saƙon. Juya kwanciyata kawai na yi saboda ban san da wace kalma zan yi masa godiya ba.
     Duk da har lokacin ban daina jin haushinsa a raina ba. Haka na yi kwanan daɗi da tunanin abin da zan yi da kuɗin idan safiya ta waye.

****
    Da safe danginsa suka cika gidan ana ta hada-hadar dafa abincin bikin. Duk da na ji zafin rashin saka ni cikin hidimarsa, amma haka na danne zuciyata saboda ba na so a ga kasawa ta.
       Sai dai ko kaɗan ban saka hannuna a cikin aikin ba. Abinci ma nawa na sa aka girka mini a gidan Maman Taufiƙ, da kuɗin da MD ya ba ni na yi komai a wadace.
      Na shiga tarbon mutanena da ke zuwa daga dangin Ummata da waɗanda muke gaisuwar mutunci. Duk da ban yi gayya ba an yi mini kara sosai.
      Wanka kala biyu na ɗauka na safe daban na marece daban, musamman shiga ta biyu da na saka baƙar shaddata kuma ɗinkin ya zauna jikina daram. Sannan na ƙawata kwalliyar da ɗan kunne da sarƙata mai kama da zinari. Don waɗanda ba su san zinarin a ido ba; kai-tsaye za su gasgata ita ce a kunne da wuyana.
       Na saka gyalena ja da takalmina half shoes jajaye da wata ƙaramar jaka mahaɗinsu, bayan agogon fata baƙi da ke tsintsiyar hannuna. 
      Na fito sharr ina ta haske idon maƙiya tamkar sabon wata ɗan daren goma sha biyu, saboda duk inda na doso sai an lalace wurin kallona da sakakken baki. Haka ma idan na juya baya hararar 'yan hassada ta raka ni tare da cizon yatsan ba haka aka so ba; wai ƙanen miji ya fi miji kyau.
      Tsakar gida muka fito ana ta ɗaukar hotuna, saboda mai hoton ma Sajida ta nace a kan sai ta nemo shi. Domin kwalliyar da muka yi kada ta tafi a iska ba tare da an bar wa bikin tarihi ba. 
     Muna tsaka da hotunan ni da su Ummu Salma sun saka ni tsakiya an saka mana rumfar hoton. Sai ga Mukhtar ya shigo yana baza babbar rigar shadda fara da ke sanye jikinsa. Ihu aka saka ana faɗin ga ango nan, saboda ya yi kyau gwanin burgewa don daman can bai da makusa a halittarsa.

      Sajida ta isa wurin shi tana faɗin, "Don Allah Abban Haidar ka zo a yi hoton nan da kai."
       Har ya yi gaba yana 'yar dariya mutane suka fara roƙonsa a kan ya zo a yi da shi, fuskarsa a washe ya zo wurinmu ya tsaya gefen Iman. Mai hoton ya ce ya dawo kusa da ni Ummu Salma a gefensa, Iman gefena Haidar ya tsaya ta gabansa. 
      Ma sha Allah kawai mutane suke ta faɗa saboda babu ƙarya mun ɗauki na kuti. Bayan an gama mana hoton in group aka ce ya tsaya a yi muna ni da shi, yana shan ƙamshi aka yi mana hoton yayin da na ƙawata fuskata da mayalwacin murmushi.
      Ana gama ɗaukar hoton ya yi ciki ya bar mu muna ci gaba da hotunan, ba tare da ya yi mini kallon tsanaki ba balle mu haɗa ido ya ga kwalliyata. Mintuna a tsakani ya fito ya fice gidan, jim kaɗan da fitar shi wata Yayarsa ta zo kira na. 

      "Mukhtar ne a ƙofar gida yake so ku gaisa da abokansa."
        
      Mayafina na ɗora a saman kai duk da ɗaurin da aka yi mini mai tozo sama. Ina gaf da fita sabon tunani ya shiga kaina, saboda burin da nake da shi a kan na ɓata masa kamar yadda yake ƙoƙarin yi mini a bikin.
      Mayafin na sauke a kafaɗa, na fara taku irin na isa na doshi inda abokan nasa suka yi dandazo. Fuskata a sake na fara gayar da su, waɗanda suka san ni suna tsokana ta da sunan uwargida sarautar mata. 

     "Gaskiya Mukhtar ka yi sa'ar mata, domin kuwa na kasa tantance ita ce uwargidan taka ko kuma amaryar ce?"
     
     Murmushin yaƙe kawai yake yi yana kallona, fari da ido na yi wa mai maganar, duk da ban waye shi ba na ce, 
       "Ai duk macen da ta yi saurin zama jagwaf daga ita ne. Domin babu inda aka ce shi kaɗai ne da haƙƙin gyara ta koyaushe. Yana da kyau ita ma ta taimaki kanta da 'ya'yanta domin ta rufa wa kanta asiri da mijinta."
      Kallona kawai Mukhtar yake yi, domin ya kasa ɗauke idonsa daga kaina. ni ma idona cikin nasa nake jefa masa murmushin,

 'Ya ka ji kafcen?'

     "Gaskiya abokina ka yi sa'ar aure, domin kuwa ka auri macen da ta dace kuma wadda ta san kanta. Congratulations bros"
     Abin da wani ya faɗa kenan yana bubbuga kafaɗarsa, bai ce ƙanzil ba ya bar wurin, yana ƙoƙarin tare wani mai mashin da zai wuce ta gabanmu. 
      Karantar yanayinsa da halin da ya shiga ya sa na yi musu sallama na juya, zuciyata cike taf da farincikin abin da na yi. Don na san shi ya gano inda zantukana suka nufa, waɗanda ba lalle ba ne su abokansa su fahimci inda na dosa, balle su hankalta da bugun gorar da na yi masa a fakaice cikin siyasa.  

      Har aka watse taron bikin ban daina jin farinciki a zuciyata ba, bayan magriba wasu daga cikin danginsa suka je ɗauko amarya. 
       A lokacin da na ji dirar motocin 'yan kawo amarya, ƙirjina ya buga daram-dam-dum! Kafin zuciyata ta karɓa tana ta harbawa ɓal-ɓal sauri-sauri gudu-gudu. Ga uwar guɗar da ake jerawa wata bayan wata a lokacin da aka shigo gidan

 "Ayyururui!!!!"

   Na daburce na ji ina ma na samu ƙafar tserewa na ɓoye, domin kada na yi kukan da zan fallasa kaina a gaban mutane.  Firdausi ta taso daga mazauninta ta zauna tare da yi mini raɗa a kunne.

      "Ki natsu da kyau kada ki bari a gano ki plsss!" 

     Babu shiri wa'azinta ya shiga kaina na mazge, tare da miƙewa na tarbo amaryar. Jikina na saka ta na rungume tare da riƙo hannunta na zaunar da ita a kan kujera.
     Zama na yi kusa da ita ina faɗin,
 "Yau dai ga amarya a cikin gidanta. Allah ya ba ku zaman lafiya ke da angonki."

     "Amin-amin!" 

Gabaɗaya mutanen da ke falon suka amsa cikin ɗaga sauti. Wata daga cikin danginta ta matso kusa da mu tana faɗin,
      "Ga Barira nan mun kawo muku, sannan mun damƙa ta hannunki amanar Allah!"
      Murmushi na yi mai sauti sannan na ce, "Daga ni har ita amanar junanmu muke, saboda zama ya haɗa mu dole ne mu yi haƙuri da juna. Don haka ni a wurina babu wata damuwa, ina mata fatan alheri, zaman lafiyar aurenta da zuri'a ɗayyiba."

     "Allahu Akbar! Sannu 'yar aljanna!"

     Maganar da na ji wata ta faɗa kenan a cikin matan da suka zagaye mu, ba tare da na ga fuskarta ba balle na gano wace ce. Cike da ƙwarin gwiwa na karɓi kuɗi a hannun Firdausi na ɗora a saman cinyar Barira. 
      "Ga nawa kuɗin sayen bakin, tun kafin ango ya riga ni jin muryar amarya." 

      "Na gode Aunty!"

Ita ce maganar da ta fito bakin Barira bayan ta damƙe kuɗinta a hannu, tamkar wadda aka ce za a yi wa ƙwace. Dariya aka shiga yi da ihun murna, Na riƙa ta har zuwa ɗakinta, bayan na saka ta yin basmala da shiga ɗakin da ƙafar dama.
      Sai da na zaunar da ita kan gadonta, sannan na baro ɗakin da ban gama tantance tsarinsa ba. Saboda ko da wasa ban ji ina sha'awar shiga ba bayan an gama jeren, haka ma duk zaryar da danginta suke yi kawo kaya da gyare-gyare ban bi ta kan ɗakin ba, balle na ga kalar kayan gadonta da su Yaya Maimuna suke gulma.

      Su Firdausi suka ja ni ɗakina, haƙuri suka shiga ba ni sosai irin wanda ya sa na ji kuka ya zo mini babu shiri. Sannan suka tafi kowa ya watse aka bar ni daga ni sai yarana da amarya Barira a cikin ɗakinta.
      Ƙarfe goma da mintuna na ji Mukhtar yana rufe gida, sannan ya turo ƙofar ɗakina ya shigo kamar an jefo shi. Ledar da ke hannunsa ya ajiye a kan bed side, sannan ya zo daidai kaina yana faɗin,
     "Yanzu ke abin da kika yi mini a gaban abokaina kin kyauta kike gani? To wallahi duk abin da kike taƙama da shi na fi ki."

     "Ni ce shaida! Domin kuwa ko rashin adalcin da ka fara da shi; ya nuna mini zahirin wane ne kai a yanzu ko da ban san ka a baya ba."

     Amsar da na ba shi kenan ina ƙoƙarin tashi daga kwanciyar da nake. Duk da a raina ba na so mu yi abin da zai raba mana hali, gudun amarya ta jiyo mu.
      "Idan ma don ban ba ki kayan da aka ce ana bayarwa ba ne kike son tozarta ni; to ki yi duk abin da za ki iya. Amma wallahi ba zan ƙara wa mai ƙarfi ƙarfi ba, don kina da kuɗin albashinki, wanda kaɗan ne za a ƙara a kan wanda nake karɓa. Kuma ina da hidimar da ta fi zama dole fiye da saya miki kayan dannar ƙirjin."

   A harzuƙe na ce da shi,  "To da ba ka saya ba sai me!? Ai dai ba ka gan ni a wulaƙance ba ko?"
      "Kanki ake ji! Ga kazar amarya nan ki sa albarka. Ni na shige! Kuma idan an ga ban fito da wuri ba kada a neme ni, don ba ɓata zan yi a cikin gidan ba."

   Sai da na fashe da dariya sannan na ce,  "Allah na tuba ka yafe ni! Wane dare ne jemage bai gani ba?"

       "Na ranar mutuwarsa!"

     "Idan haka ne kuwa babu abin da zai sa na damu da barazanar da iyakacinta a baki. Da ma a ce kai namijin gaske ne mai iya gamsar da mace ya cire mata kwaɗayin wasu mazan; da zan ji zafin aurenka da wannan daren da kake tinƙaho yanzu. Amma abu kamar lagwani ranar me za ta yi mini balle na ji haushin masu zuwa aro?"

     




     Laaaa!😱🤭🏃🏻‍♀️







D. AUTA CE✍🏼


*ABOKIN AIKINA*


*@HADIZA D. AUTA*


*SADAUKARWA: DAUGHTER ANUP*


*TALATIN DA BIYU.*

        "Iyyeeeee! Ke Ni kike faɗa wa magana irin haka mai kama da cin zarafi?"
       "Ina da tabbacin babu ƙarya a cikin maganganun da na faɗa. Kai ma idan za ka yi wa kanka adalci; ka san ƙarin aure na masu cikakkiyar lafiya ne ba irinka ba. Don na sha faɗa maka mace ɗaya ma ta yi maka yawa, amma ka kasa ganewa. To ka yi auren ga ka ga amaryar, muna daga gefe mu ga kalar wainar da za a toya, don duk wanda bai ji bari ba ai ya ji hoho!"
       Takowa ya yi a fusace ya tsaya gabana, nuna ni yske yi da hannu tamkar zai kai mini duka, ƙwafa ya yi ya nufi hanyar fita ɗakin yana faɗin,       
      "Idan ma burinki ɓata mini daren amarci ne; to haƙar ki ba za ta cim ma ruwan ba."

     Ya fice tare da bugo mini ƙofa da ƙarfi. Harara na aika wa ƙofar sannan na miƙe da nufin rufewa da makulli. Sautin maganganun da na ji ya sa na yi riƙe hannun ƙofar ba tare da na bar wurin ba.
       "Don Allah ki yi haƙuri, wallahi ba hirar arziƙi ce muka yi ni da ita ba."
      "Ka je kawai ka kwanta ni ina nan, don wallahi ba zan bari ka taɓa jikina ba bayan ka gama holewa da uwargidanka."

     Dariya ta suɓuce mini duk da mugun haushin maganganun amarya da na ji. barin ƙofar kawai na yi na kwanta, zuciyata cike da tunani tare da tausayin Barira a raina. 
      Saboda ko maƙiyiyata ba na mata fatar auren Mukhtar, balle irinta da tashi ɗaya na fahimci rawar kan da take yi a kansa. 
 Ban san ya suka ƙarge ba saboda addu'o'in baccin da na karanta, sun yi tasiri wurin mantar da ni komai a dalilin nannauyan barcin da ya ɗebe ni.

        Da safe na tashi da wuri na shirya mana breakfast, saboda na taras da doya da kiret ɗin ƙwai har biyu a kitchen. Hakan ya sa na fahimci abin da yake so a yi kenan, Ummu Salma ta taya ni muka kammala.
      Namu muka ci sannan suka tafi islamiyya, na koma ɗakina na kwanta ina huce gajiya. Ba tare da na kalli ƙofar ɗakin amarya ba balle na nemi inda take, saboda maganganun jiya da kunnuwana suka jiyo sun sa na ji ta sire mini. Sannan gargaɗin da Mukhtar ya yi mini ya ƙara tunzura ni na tsaya inda Allah ya ajiye ni.
      Misalin ƙarfe goma saura na ji an fara ƙwanƙwasa mini ƙofar ɗaki. Sanin cewa ba su Haidar ba ne; na miƙe jikina babu ƙarfi saboda baccin da ya kwashe ni, a kasalance na buɗe ƙofar. 

      "Ina kwana Aunty?" 
"Lafiya lau!"
        Na amsa mata a gajarce, tana wasa da yatsun hannunta ta sake cewa, 
"Abin karinmu ya ce na karɓo"
       "Ki je Kitchen za ki ga komai a kan table. Na zaci bacci kuke yi shi ya sa ban yi karambanin tayar da ku ba."
     
     Na ƙare maganar ina murmushin yaƙe, "Hmm! Aunty ai tun ɗazu idonmu biyu."
      "Ok tom! Ki je ki ɗauka."
Ta juya na bi shamulallen ƙugunta da kallo ina ƙumshe dariya, saboda yadda take ƙoƙarin karkaɗa shi ta ƙarfi amma ko motsi babu balle su taka rawar disko.

      Wanka na faɗa sharp-sharp na shirya  cikin riga da wandon atamfa, wadda ta zamo half gown da falalin wandonta ya baje a ƙasa. Na kafa ɗaurin ture ka ga tsiya na koma kitchen da zummar ɗora girkin rana. Shigowar su Ummu Salma suna ihun Mama mun dawo, ya sa na yi saurim ƙwala wa Haidar kira. Saboda shi ne mara jin cikinsu kuma ba na so ya ce zai je ɗakin amarya, gudun ya gano abin da ya fi ƙarfin idonsa.
      
     Ya gida suka fara yi mini, sannan na ce da su kada wanda ya shiga ɗakin amarya. Su jira idan ta fito su gaishe ta, ficewa suka yi bayan sun tabbatar mini da ba za su je ba.
      Hankalina a kwance na kammala girkin cikin ɗan lokaci, zuba wa tsuntsayen soyayya na yi a kula na ajiye gefe. Sannan na zuba namu a tire ɗaya muka baje tsakiyar kujeruna. 
     Muna tsaka da cin abincin, na ji sallamar wani a bakin ƙofar falonmu. Haidar ya amsa ya miƙe ya isa inda mai sallamar da gudu, domin ya ji mana abin da ya kawo shi. 

      "Ka faɗa wa babanka ga ni na zo!"

     "Mama Nura mai Chemist ne yake neman Abbanmu!"
      
    "Nura kuma? To waye bai da lafiya a gidan nan?"
    
     Tambayar da na yi kenan a zuciyata ashe ta fito fili. Tsintar muryar Barira na yi bayan ta buɗe ɗakinta tana faɗin, 
      "Romiyo ne yake zazzaɓi! Shi ne ya kira likita domin a zo a yi masa allura."

     'Romiyo?'

Na jefi kaina da faɗar sunan a zuciyata, a take na faɗaɗa fuskata da murmushi na ce. 
"Allah Sarki! Haidar je ka ce da Nuran ya shigo"

      Bayan na gama ba shi umurnin na ci gaba da cin abincina. Haidar a gaba Nuran yana bayansa suka doshi ɗakin Barira, na yi hanzarin cewa da shi,
      "To kai Alhaji zo mu kammala cin abincin kai muke jira." Saboda ba na so ya shiga ɗakin.
        Ya dawo ya zauna muka ci gaba da cin abincinmu, Barira ta juya ta koma ɗakinta ta bar ni da mamakin ciwon Mukhtar a farkon daren amaryarsa. Saboda sanin da na yi masa shekara yake yi bai kwanta ciwo ba, domin Allah ya wadata masa lafiya ba kamar ni mai yawan laulayin ciwo kala-kala ba.

       Mintuna a tsakani Nuran ya fito Barira a bayansa yana faɗin,
      "Don Allah kada a dame shi a bar shi ya huta sosai."
       Muƙus na ga ta yi ba tare da ta tanka masa ba, alamunta ya nuna a zahiri ba ta ji daɗin maganarsa ba. 
      Kitchen na ga ta wuce, ɗan lokaci a tsakani ta fito da kulolin da na saka musu abinci, ta yi ɗakinta tare da rufo ƙofa. tun daga lokacin ban sake jin motsinsu ba daga ita har shi.
        Baƙinta ma da ke zuwa haƙura suke yi su tafi idan sun gaji da zama, saboda ta ƙi buɗe ɗaƙin balle ta fito ta bi kan 'yan taya ta murnar auren. A taƙaice dai ranar Mukhtar bai fito ba har sai da aka yi sallar Asr. Sannan ya fito dafe da ƙugu yana tafiya tamkar mai tata, sai nishi yake yi yana faɗin,
      
     "Wash! Allah! Wayyo-wayyo!"

      Barira tana riƙe da hannunsa suka yi ɗakinsa tana jera masa sannu. Haka kawai na nemi annurin zuciyata na rasa, sanadin abin da na gani da idona; ya tabbatar mini da sun kwana suna shan ganimar aure. Tuƙuƙin baƙinciki ya taso mini nan take ya rufe mini zuciya. 
     Volume na ƙara wa tv'n da nake kallo, dumar waƙar SAI DA KE ta karaɗe falon gabaɗaya. 

       Abin da ya so ba ni dariya, lokacin da suka je bakin ƙofar ɗakinsa ya dakatar da ita a nan. Ban ji me ya faɗa mata ba, na hango ta tsaye rungume da hannu a ƙirji. Na ƙara ɗora idanuwana a kansu ba don na so ba, ya shige ɗakin shi kaɗai yana jinjina mata hannu sama alamun ta yi haƙuri, kawai ya kulle ƙofarsa dafe da ƙugunsa. Ya bar ta a nan bayan ya gama yi mata dariyar yaƙen kamar an yi masa dole.
Wani juyi ta yi tamkar ta kifa tana fisgar jiki ta faɗa ɗakinta ta rufe ƙofa da ƙarfi. Ajiyar zuciya na sauke tare da kashe tv'n na miƙe kamar wadda aka tsikara, na fito tsakar gidanmu domin na shaƙi iska mai sanyi.
      Safa da marya na shiga yi a tsakar gidan saboda na rasa me ke mini daɗi a lokacin. Sallamar wasu mata biyu ya sa na shiga natsuwata tare da amsa musu sallama. Wani kallo suka bi ni da shi a lalace suka gaishe ni kamar ba su so suka shige ciki. 
       Sosai na ji zafin abin da suka yi mini, amma dole na danne don ba zan bari na fara takun-saƙa da ita tun yanzu ba, balle masu zuwa wurinta su tafi. Zama na yi a kan kujerar robar da ke wurin ina nazarin abin a raina.
     Har su Ummu Salma suka dawo ban tashi daga zaman da nake yi ba, umurnin cire kayan makaranta na yi musu suka yi ciki da gudu. Mintuna a tsakani na miƙe na bi bayansu zuciyata a cunkushe raina babu daɗi.

      "Ke Ruky ina ganin jalala! Ke ko dare ɗaya tak! Amma Romiyo ya susuce tamkar ba namijin kirki ba?"
       "Ga shi kuma ke a nan ɓangaren ba ki da mutunci! To ki dai yi a hankali, kuma ki tuna kina da kishiya ba ke kaɗai ba ce a gidan."
        "Babu ruwana da kowa wallahi kaina na sani, idan ban ga haske ba kuma na tayar da tubana don ba na iya juriya gaskiya."
       "Ba ki da mutunci Barira!"
         
     "E ɗin, a bar ni a hakan! Wa ya ƙi daɗi?" Dariya suka fashe da ita dukansu har da shewa, na tura ƙofar ɗakina na shige ina juya maganganunsu a zuciyata. 

'Waton ita ma jar wuya ce!'

     Zancen da na yi kenan a raina, saboda hirar su ta bayyana wace ce ita, bayan abin da na gani zahirin da idona. Babu shiri murmushi mai sauti ya suɓuce mini saboda farincikin kafcen zai fi daɗi a hakan.
        Wayata na cire daga caji na tura wa MD saƙon godiya, saboda rashin kyautawata ban yi godiya tun da zafi ba. Abin yana ta cizon raina, sai da na tura masa saƙon sannan na ji tamkar an sauke mini ƙaton dutsi a saman kaina.
       
     'Na ga saƙo na gode sosai! Ubangiji ya ƙara buɗi da rufin asiri'

      Mintuna a tsakani ya dawo mini da 'Amin' kawai ba tare da ya ƙara komai a kai ba. Haushi na ji na goge saƙon duka, sannan na mayar da wayar a caji.
      Ban san ya aka ƙarge ba tsakanin amarya da angonta ba, balle marasa kunyar ƙawayenta. A cikin bacci na jiyo sautin muryar Barira tare da bugun ƙofar ɗaki, na so kada na bi ta kai don ban san kalar rainin wayon da suka shirya ba. 
       Amma haƙƙin zamantakewa ya sa na miƙe na buɗe ɗakina na fito, hango ta na yi a bakin ɗakin Mukhtar tana ta dukan ƙofar tare da kiran sunansa. 
       Da sauri na juya da nufin komawa na ji muryarta ɗauke da damuwa tana cewa,
      "Aunty don Allah ki ce ya zo ya buɗe ƙofa, tun yamma da ya shige bai sake fitowa ba. Ga shi ba ya jin daɗin jikinsa kuma ya dace mu san a wane hali yake ciki."  
       Murmushi kawai na yi, sannan na ƙaraso bakin ɗakin na fara kiran sunansa. Kamar jira yake yi ya buɗe ƙofar a fusace yana faɗin,
       "Kun fa dami mutane cikin dare, ko ku ba ku san dare mahutar bawa ba ne?"
       Dariyata na ƙumshe sannan na ce da shi, "Amarya ce ke neman sanin halin da kake ciki. Shi ya sa na ga ya dace na taya ta neman ka saboda haƙƙin zamantakewa."

      "To lafiyata ƙalau ku je ku kwanta! Don ba na jin ƙarfin jikina ne shi ya sa ban fito ba. Tun da kun gan ni ku je ku kwanta kawai sai da safe!."

      Na juya ina 'yar dariya na ce da su, "Mu tashi lafiya."
        "Me za ki yi a nan ke kuma? Wuce ɗakinki ki kwanta ko'ina jikina ciwo yake yi wallahi."
      Maganarsa kenan da na jiyo kafin na isa ɗakina, 'Garam!' Na ji ya rufe ɗakinsa da ƙarfi. Sai da na shiga zan rufe ƙofata na hango Barira a bakin ɗakin tamkar an dasa ta.
       Dariya ta suɓuce mini na yi hanzarin rufe ɗakin, raina fes na koma kan gadona na kwanta ina jin kaina cikin nishaɗi.
       Bacci mai daɗi na yi tare da mafarkin MD a cikin wani kyakkyawan yanayi. Rungume nake a jikinsa, hannunsa cikin nawa yana yi mini raɗa a kunne ina ta faman murmushi. Fuskarsa ɗauke da annuri yana fesa mini siririyar dariyar da ta ƙara wa fuskarsa annuri.

       'Ina sonki da yawa matata!'
      
     Rufe fuskata na yi tare da lakuce masa karen hanci, kiss ya yi mini a goshi cikin shauƙin ƙauna yana aika mini kallon da da ya haifar mini da kasala. Ya rungume ni gabaɗaya a jikinsa, sannan ya sauke ƙaƙƙarfar ajiyar zuciya mai sauti 'Hummmmmm!' Luf na yi cikin jikinsa numfashina yana fita a hankali cikin wani yanayi mai daɗi.

      Kiran sallar asuba ya katse mini daddaɗan mafarkin da na yi, wanda na so na ɗore da shi a hakan ba tare da na farka ba. Jikina ko kaɗan babu kuzari, a haka na yi sallah na tayar da yaran sannan na fito ɗaki da nufin zuwa kitchen.
      Turus na yi saboda hango Barira a yashe ƙofar ɗakin Mukhtar, rigar barcin da ke jikinta gabaɗaya ta kware cinyoyinta a buɗe. 

   "Ita kuma wannan me ya same ta?"






To fa😱 amaryar Romiyo ya take ne?😂






D. AUTA CE✍🏼


*ABOKIN AIKINA*


*@HADIZA D. AUTA*


*SADAUKARWA: DAUGHTER ANUP*


*Ina ƙara tunatarwa!Ban yarda ba! Ban amince ba! Kada a ɗora mini littafi YouTube ba tare da izina na ba! Masu nema daga farko ku yi haƙuri har a kammala🙏*


*TALATIN DA UKU.*

        Tambayar da na yi wa kaina kenan a zuciya, sannan na yi tattaki a hankali har na isa inda take. Sunanta na fara kira domin alamu ya nuna mini ƙarara bacci take yi sharkaf!
       Ba ta motsa ba har sai da na duƙa na bugi hannunta tare faɗin, "Barira!" 
      Ta miƙe firgigit tana waige-waige tare da faɗin, "Don Allah Romiyo ka buɗe mini ƙofar"

       "Lafiya kike kuwa?"

       Na faɗi maganar cike da jin haushin banzancin da take ƙoƙarin yi wa kanta. Kallo ta bi ni da shi sannan ta yi hanzarin miƙewa tana gyara zaman rigar barcin da ke jikinta. Soshe-soshen kai ta fara yi tana mayar da hularta bisa kai, ta nufi hanyar ɗakinta ranta a haɗe cikin maƙoshi ta ce da ni,
 
     "Lafiya lau!"

     Bayanta na bi da kallo har ta shige ɗakinta ta rufe, murmushi na yi tare da girgiza kaina ina maimata sunan Romiyon a raina, wanda ta raɗa wa Mukhtar ba tare da ta san bai cancanta da sunan ba. Domin bai san komai a kan soyayya ba balle abin da ta ƙumsa, saboda iya sanin da na yi a rayuwar zamana da shi; ko kiss irin na haɗuwar leɓe da leɓe bai taɓa haɗa ni da shi ba. 
      Kitchen na koma ina ta hada-hadar ɗora mana abin kari. Zuciyata cike da tunanin rashin kawaici irin na Barira, da rashin sanin darajar Mukhtar balle ya sauke haƙƙoƙan da ke kansa.
      Kasancewar muna da sauran kayan tea na soya mana Irish da ƙwai. Ina ƙoƙarin fitowa daga Kitchen ɗin hannuna ɗauke da cups da flack's, na ji sautin muryar Barira a sama tana masifa.
        "Na rantse da Allah sai ka san ni ka wulaƙanta. Babu wata magana da za ka faɗa mini yanzu na yarda, saboda ni ma ba ka ji kalolin kiran da na yi maka ba amma ka ƙi buɗe mini ƙofa."
       Abin da na ji kenan bayan na fito daga Kitchen ɗin, saman carpet ɗin tsakiyar kujeruna na ajiye kayan sannan na ƙwala wa su Ummu Salma kira. Duk da ina jin sautin Mukhtar ƙasa-ƙasa yana magana amma ban ji me yake cewa ba.
        Fitowar su Ummu Salma ta yi daidai da fitowar Barira a fusace ta nufi kitchen. Mukhtar ya bi ta yana kiran sunanta cikin ƙaramar murya kafin ya rufe ƙofar.

      Baki a sake yaran suke bin ƙofar kitchen da kallo, karantar da na yi wa fuskokinsu na gano mamakin da suke yi. Murmushi na yi mai sauti na miƙe daga durƙushen da nake ina faɗin,

      "Ku bari na kawo muku madarar" 

      Kitchen ɗin na nufa na tura ƙofar, cikin sa'a bai rufe da makulli ba. Kai-tsaye na nufi kular da na saka soyayyen Irish ɗin, duk da na tarar da kular a buɗe Barira tsaye tana ci a cikin plate ɗin da ta shaƙe  taf! Ba tare da ta jira na ba ta ba, ko kuma ta tuna da cewa akwai wasu masu haƙƙi da shi a cikin gidan bayan ita. 
     Sai girgiza ƙafafuwa take yi tana cin abinta shi kuma yana faman yi mata magiya. Na so na yi magana, sai na ga duk abin da zan faɗa a lokacin zai janyo wani sabon tashin hankali a tsakanina da ita.
     Kular kawai na ɗauke sannan na ja biredi, wanda shi ma ta fasa ledar ta bar shi a buɗe, na fice ba tare da na ce da su komai. Raina a ɓace na dire kular na koma na ɗauko tire na kasa musu kowa ya ɗauki na shi. 
      Zuciyata a ƙuntace saboda mummunan ganin da na yi musu a kitchen ɗin. Sai da yaran suka cinye sannan na ce da su, 
       "Oya ku tashi ku je islamiyya kada ku yi latti"
      Suka ɗauko jakunkunansu suka wuce, na bi su da addu'ar a dowa lafiya sannan na karya. Na kasa tashi daga wurin na baje saman 3seater tare da rufe idona kamar mai barci, sai hotonsu nake gani a lokacin da suke shagalinsu.

       "Ina nawa breakfast?" 

     Zancen Mukhtar da na ji kenan cikin tsakiyar kwanyata, ban motsa ba kamar yadda ban yi niyyar amsa masa ba.

       "Da ke fa nake magana!"

     Ya sake maimaitawa a fusace cikin ɗaga murya, gyara kwanciyata na yi ba tare da na ce ƙanzil ba.
      "Ni za ki wulaƙanta ina yi miki magana kina sharewa?" 

      "Wane breakfast zan ba ka bayan wanda ka yi a kitchen?"

       "Haƙƙina ne aka ba ni a can, wannan kuma shi kike da haƙƙin bayarwa" 

      Wani ɓacin rai ya taso mini, nan take ya yi mini lulluɓin da ya rufe mini idon gani, domin ban san lokacin da na diro daga kan kujerar ba ina faɗin,
        "An canye haƙƙin ko kana da abin da za ka yi ne idan an hana ka!?"
      "Kwantas Hajiya! Ai kuma yanzu babu kare bin damo! Ki yi yadda kike so ni ma na yi nawa."
     Yana ƙare faɗar hakan Barira ta fito daga kitchen ɗin sum-sum tamkar munafuka ta shige ɗakinta. Harara na wurga masa saboda kallon da ya bi ta da shi yana 'yar dariya. Na danna masa wani kafurin tsaki har sai da na dantse naman ƙasan leɓena. Sannan na bar wurin ina ƙoƙarin shigewa ɗakina ya ce,

     "Sai haƙuri kuma, ni kam na samu inda aka san muhimmancina."

     Baya na dawo saboda ganin idan na yi masa banza bai san kawaici ba,
      "Bari na faɗa maka zancen da ba ya tashi! Wallahi daga wannan karin safiyar; ba zan sake yi mata girki ba. Tun da ta san muhimmancinka ta girka ta ba ka ka ci kai da yaranka."
 
       "Hahahahahh!"

    Sautin dariyar da ya yi kenan har da buga ƙafa ƙasa, sannan ya yage baki yana ƙwala mata kira cikin ɗaga murya.

      "Barcy!!!"

     "Na'am Romiyo!"

Barira ta fito daga ɗakinta cikin sauri ta iso wurinsa da gudu, towel ɗaure a faƙon ƙirjinta da babu tudun komai face na fatar da ke jikinta. 
      
     "Ki shirya yi mana girkin rana ni da yarana. Zan aiko miki da kayan cefane idan an dafa a zuba wa Uwargida nata."

     Tana fari da ido ta ce, "Haba Aunty! Me ya yi zafi ne haka tsakaninki da Romiyo?"

    Baki a sake na dinga kallonsu ɗaya bayan ɗaya, maimakon na ji raina ya ci gaba da suya; sai na ji wata dariya ta suɓuce mini ban shirya ba. Sannan na gyara tsayuwata na ce da ita,

     "To ke Barcy ina ke ina sanin sirrin mata da mijinta? Yana da kyau ki tsaya inda kike da iko da inda ya ajiye ki, ki daina ƙoƙarin shiga hurumin da ba naki ba har sai an kasa da ke. Girki dai ne ya ce ki shirya yi mana saboda yana so na huta da aikin da na sha haka nan, domin tun da aka fara shagalin bikin aurenku ban zauna ba, kullum ina tsaye tamkar haƙori. Don haka idan kin gama ki zuba mana namu a kula ni da yaransa, kamar yadda ya faɗa miki."

     Ina ƙare maganar na juya ba tare da na damu da kallon tuhumar da take aika masa ba. Na je ƙofar ɗakina na ja na tsaya rungume da hannuwa a ƙirji ina musmushin mugunta.

       "Wallahi ba haka muka yi da ita ba Allah ma ya sani."
 
     Maganar da ya yi kenan  yana ɗaga manunansa duka biyu a ƙoƙarin son ta yarda da zancen shi.
       "Daina rantsuwa zan yi girkin kamar yadda ka saka ni, amma wallahi sai ka biya duk wata wahalar da na sha yau." 

    Ɗakinta ta nufa karaf ta dantse ƙofar, ya fara aiko mini da harara yana nuna ni da hannu yana cewa, 
      "Ko shaiɗan sai ya shafa miki lafiya a wurin ibilisanci. Don haka ki je kawai akwai Allah!"

    Dariya na fashe da ita sannan na yi masa gwalo, ƙwafa kawai ya yi sannan ya tsaya bakin ƙofarta yana faɗin,

      "Ki yarda da ni Barcy! Wallahi ba haka muka yi da ita ba."

     ****
  Tun da na shige ɗaki ban sake fitowa ba, sai da su Ummu Salma suka dawo na ce su je su yi wanke-wanke. Bayan na yi wanka na haye gado ina ta faman chatting da na gaji na koma kallo har bacci mai ƙarfi ya yi awon gaba da ni.
     Ƙarfe uku lis na fito ɗakin, saboda hayaniyar faɗan da yaran suke yi. Kokawa sosai suke suna dambacewa tsakanin Haidar da Iman, Ummu Salma tana raba su Haidar bai bari. Ganin Barira a kan kujerarta zaune tana latsar waya ko a jikinta; hakan ya sa na ji raina ya ɓace.

     Fakar Haidar na yi cikin fushi na fara yi masa faɗa sannan na dawo kan Iman. Ummu Salma ce ta fara yi mini bayanin abin da ya haɗa su faɗan.
      "Wai don ba a ba mu abinci muka ci ba, shi ne ya ce dole sai ya je ya ɗauko. Kuma amarya ba ta ce mu ɗauko ba, ta ce mu jira har Abbanmu ya dawo shi ya ce zai ba mu."
      "Ban gane ba! An gama abincin shi ne ba za a ba ku ba sai ya dawo ya ba ku?"

   Ummu Salma ta ɗaga kai alamun tabbatarwa, 
       "To ai shi ne zan je na ɗauko mana mu ci Iman tana riƙe ni. Ni Ko da na gaji haushi na dinga kai mata duka, daga nan muka fara kokawa."
      Kitchen kawai na nufa ba tare da na ce da su komai ba balle Barirar, kulolin da na gani ajiye na fara buɗewa. Shinkafa da miya na gani a cikin kuloli biyu, ban tsaya neman bayani a kansu ba na ɗauki wadda ta fi girma na fice.
     Ina tsaka da zuba musu abincin na ji muryar ta a saman kaina tana faɗin,

      "Kan ubancan! Abincin Romiyo kike zuba musu?" 

       Ban fasa juye musu abincin a tire ba, na bi abincin da miya tare da zuƙa-zuƙan namun da na gani duk na juye musu. Ina ƙoƙarin tura musu gabansu ta fara faɗin,
      "Gaskiya Aunty wallahi ba ki kyauta mini ba! Saboda Allah yaushe zan yi wa mijina girki ki zube wa yara su cinye?"

     "Abincin daga gidanku kika zo da shi ne? Ina ga ai har yanzu ba a kawo miki kayan garar da ake kai wa kowace amarya ba. Ki jira idan aka kawo ki yi iko da abin ki, amma wannan ba ki da halin hana wa yara abincinsu. Domin ubansu ya sayi shinkafar kuma shi ya yi cefanen da aka yi gurkin." 
          "Haka ma za ki ce?"

"E, haka na ce!" 

     Kuka ta fashe da shi wiwi tamkar wadda aka daka, saboda sallamar da Mukhtar ya yi tun kafin ya shigo falon. Wurinsa ta yi da gudu ta faɗa jikinsa tana rera sani sabon kukan, a ruɗe ya fara tambayar,

      "Lafiya? Me aka yi mata?" 
     
    Kallo ma bai ishe ni ba, na zauna ina faɗin su yi sauri su gama su tafi. Isowa ya yi wurinmu tare da ita a jikinsa yana faɗin,

    "Wai me yake faruwa ne!?"

      Mere na yi musu daga shi har ita, sannan na ci gaba da bai wa su Ummu Salma umurnin su yi sauri su gama su tafi.
      "Wai fa abincinka ne ta ɗauko ta zube wa yaran, bayan kuma sun ci abincin tun lokacin da na gama girkin."

     Kallo na kawai ya dinga yi fuskarsa a haɗe sannan ya ce, 
     "Wai ke don Allah har abada ba za ki bari a zauna lafiya ba? Yanzu wannan abin da kika yi miye ribar shi?"

     "Daga kai har ita ban da lokacinku! Don haka idan ta gama shirya maka zance ka haye, to ka zuba mini fetur ka ƙone mu duka mu kama da wuta daga ni har yaran."

      Wata zabura ya yi tare ƙoƙarin kai mini duka, ta yi hanzarin riƙe shi tana faɗin,
      "Don Allah Romiyo ka ƙyale ta a bar ta da halinta. Idan ma sun ci ai 'ya'yanka ne ba na kowa ba. Mu je na ba ka wanda ta bar mana ai gobe ma rana ce!" 

     "Da ba ki hana shi ba! Tun da ba ki ji kunyar yin ƙaryar da za ki haɗa ni da shi ba. Na rantse da Allah duk ranar da ka yi gangancin taɓa jikina da sunan duka sai na illata ka. Ke kuma baƙar Munafuka annamimiya sai kin gwammace ba ki san shi ba a faɗin duniya, don sai kin yi kukan da ko uwarki ta mutu iyaka kenan. A dai juri zuwa rafi watarana tulun zai fashe."

     Ba su ce da ni komai ba, ta ja shi suka shige kitchen na ce da su Ummu su tashi su je tun da sun ƙare.
      Na zauna ina ta huci tare da girgizar ƙafafuwa, saboda na zo wuya komai zan iya aikatawa a lokacin. Su Ummu Salma suka fice gidan tamkar ƙwai ya fashe musu a ciki, su kuma tsuntsayen soyayya suka fito aka baje tsakiyar kujerunta. Shwagaɓa ta dingà yi masa tana ba shi abinci a baki suna hira ƙasa-ƙasa, idan abin ya yi musu daɗi su fashe da dariya.
    Komawa ɗaki na yi na ɗauko wayata na kwanta, na fara waya tamkar gaske cikin kashe murya ina faɗin,
      "Haba dai ai kai ma ka san bayan kai babu wani a faɗin duniya. Daina zancen wannan lusarin, wanda bai ajiye komai ba face masifa da hargowa tamkar zai cinye mutum da ransa."

    Shiru na yi kamar yadda su ma suka yi tsit tamkar ba su cikin falon, dariya na yi mai sauti sannan na ce,
     "Cabɗijam! Ai ka yi shiru kawai abin ba a cewa komai. Fankam-fankam ai ba ya kilishi, ita ma kwana biyu za a jone mu bi sahu. Ai na rantse da Allah da ta san kowane ne ba za ta yi gangancin raɓarsa ba. Saboda muddin ya ƙyalla ido ya hango wata ƙawarta sai ta sha mamakin abin da zai aikata mata. Yo nawa aka yi wai an yi wa ɓarawo kashedin sata?" 

       Wayar na ji an fisge ba tare da na ji lokacin da aka zo a kusa da ni ba. Da sauri na miƙe fuskata a haɗe na ce da shi,

     "Ban wayata!"

     "Sai kin faɗa mini da uban wa kike waya? Kuma wane ɗan iska ne ya kira ki?"

     Raina fes ba tare da shayin komai ba na ce da shi,    
       "Da uban da ke so na yana dakon aure na! Sannan da ɗan iskan da ka ajiye mini ina lalata da shi a waje."

Kallona ya dinga yi bakinsa yana rawa, na yi 'yar dariya sannan na ce,
      To ba ni wayar tun da na amsa tambayar ranka shi daɗe! Romiyo mijin Barcy!"






Kai jama'a🤭Ni dai babu luwana yasin🏃🏻‍♀️



D.AUTA CE✍🏼


*ABOKIN AIKINA*


*@HADIZA D. AUTA*


*SADAUKARWA: DAUGHTER ANUP*


*TALATIN DA HUƊU.*

        Ƙwafa kawai ya yi sannan ya juya yana ƙoƙarin barin wurin, na bi bayansa da hanzari ina faɗin,
      "Ka ba ni wayata!"

   "Ba zan bayar ba! Idan akwai wanda zai ƙwatar miki ki kira shi ya zo yanzu!"
          "Babu mai ƙwatar mini don ba yau ka saba cin haramun ba, don haka ka ba ni wayata tun muna shaida juna!"
      Banza ya yi da ni ya nufi ɗakinsa Barira ta bi shi tana faɗin,
       "Don Allah Romiyo ka ba ta wayarta mu je ka ƙarasa cin abincinka."

     Juyowa ya yi yana huci tare da nuna wayar a sama yana cewa, "In dai wannan wayar ce! To ba zan bayar da ita ba, gobe ma idan na sake ganin tana waya da wani ɗan iskan; sai na sake ƙwace wata."
      Wurinsa isa a fusace na yi tsalle zan cafke wayar, ya yi hanzarin saukar da hannun tare da tura wayar aljihunsa. Raina a ɓace na ce,
      "Ba ni wayata wallahi ko yanzu na yi abin da bai dace ba!"

        "Ba zan bayar ba ki yi abin da za ki iya."

     Cikinsa na yi na mamaye shi na cafko jarumarsa na murɗe iya ƙarfina, ihu ya saki tare da faɗin,

      "Wayyo! Za ta kashe ni!"

     Jikinsa yana rawa ya fiddo wayar daga aljihu ya miƙo mini sannan na sake shi, barin wurin na yi a fusace ina faɗin,
      "Ai da kada ka bayar! Da na tsinke ta na dafa maka a tukunya ka cinye ƙazantarka."
       "Ta Allah ba taki ba wallahi! Idan burin ki nakasa ni ki yi wa Barcy asara, to gani nan bari nan! A gabanki za mu shimfiɗa rayuwa mai daɗi sai dai baƙinciki ya kashe ki."
      "Soloɓiyo mai aiki irin na matan ne zai iya rayuwa mai daɗi da mace? Ka bari sai ka samu cikakkiyar lafiya sannan ka yi alfakhari da burgar da iyakarta cikin baki."

     "Gaskiya Aunty wallahi abin da kike yi kwata-kwata ba kya kyautawa. Ai Romiyo ko ba mijinki ba ne ya dace ki girmama shi balle yana matsayin uban 'ya'yanki."
      Barira ta yi maganar tare da isa wurinsa ta lafe jikinsa tana faɗin, 
      "Ka yi haƙuri Romiyo, wasu matan haka suke yi wa mazajensu komai a tsaitsaye, tamkar tsararrrakinsu."

    Kallon ta kawai nake yi saboda gaskiya ta yi mini yawan da ban san me zan faɗa mata na huce ba, dawowa na yi gabansu ina nuna ta da hannu na ce,
     "Kada ki sake shiga sabgata idan kika ga ina yi da shi! Idan kuma kika sake zan bambance miki tsakanin aya da tsakuwa."
     Shiru kawai ta yi tana turo baki bayan muimui ɗin da take yi ban san me take faɗa ba. Sannan ta ɗage kanta sama ta ja hannunsa suka yi ɗakinsa.
Bayansu na bi da kallo ina wassafa irin bugun wahalar da zan yi mata idan ta kai ni bango. Ban san ya suka yi ba, ina zaune kan kujerar na ga ta fito ɗakin a fusace ta yi ɗakinta.
      
     Sallamar Sajida da su Ummu Salma ta katse mini tunanin da na shiga tsawon lokaci, sannan ganin su ya kore mini rabin damuwar da Mukhtar da Barcynsa suka cusa mini a zuciya.
     Riƙe da hannun Haidar ta iso tana gaishe ni a ladafce, sannan ta zauna tana faɗin,
       "Tun ɗazu na so zuwa bazawarina ne ya zo!"

     "Sannu Sajiji! Gaskiya ki fito da miji haka nan mu aurad da ke." 

     Shiru ta yi sannan ta sauke ajiyar zuciya ta ce, "Wallahi Aunty har yanzu ban daina jin mutuwar Abbakar cikin raina ba. Shi ya sa duk wanda ya zo nake jin kamar ba zan iya rayuwa da shi ba."

     "Haƙuri za ki yi, don Allah ba ya barin mutum don wani ya ji daɗi. Lokacinsa ne ya yi, kuma Allah ya tsara ba za ku yi rayuwa mai tsawo da shi ba. Allah dai ya ƙara haske cikin ƙabarinsa"
      "Hmmmmm! Haka ne gaskiya, amin Ya Allah. Wai kin san wani abu Aunty?"

      "A'a sai kin faɗa"

Na ba ta amsa cike da ƙaguwar na ji me za ta faɗa mini. Tagumi ta yi sannan ta ce da ni,
      "Mijin maƙociyar nan taki ne yake ta damuna da zancen aure. Ni kuma wallahi kirkin da na ga kuna yi da ita, ya sa ba na son na rufta. Amma ke ya kike ganin lamarin? Don na ga matarsa da shegen kishin tsiya."

     "Wace maƙociyar daga ciki?"

      "Wannan Maman Taufiƙ ɗin."

    Daram-dam! Shi ne sautin bugun da ƙirjina ya yi zuciyata ta hau bugawa.

 "Ina ya gan ki?"
  
     Na jefo mata tambayar a ruɗe bakina yana rawa. "Bari kawai Aunty! Tun ranar bikin da muka je gidanta dafa abincin baƙinki. Ina hankalce da shi yana satar kallo na, hakan ya sa na mayar da hijabina da na cire saboda aiki. Ban san ya aka yi ya samu lambata ba, kawai da dare bayan na koma gida sai ga kiransa a wayata. Bai ɓoye mini komai ba ya sanar da ni so na yake yi da aure, saboda wadda zai aura tsohon mijinta ya dawo Iyayenta sun matsa mata sai ta koma gidansa, ko don yaran da ke tsakaninsu. To ni kuma wallahi ina tsoron kishin matarsa, ga shi mun yi mutunci da ita sosai a lokacin hidimar bikin nan. Har ga Allah ina jin kunyar na auri mijinta, ga  shi kuma ya nace mini da kira dole sai na faɗa masa ra'ayina. Shi ya sa na ce zan yi shawara da ke duk yadda kika ce shi kenan."
      "Cabɗijam! Akwai matsala Sajida! Don wallahi matar nan ta shi ba dai kishi ba. Hmmm! Kin san me? Kawai ki ce da shi ya yi haƙuri kina da wanda za ki aura."

     "Haka za a yi Aunty! Don ni ma dai ina jin nauyi wallahi. Sannan ɗan banzan kishin nan na matarsa ma ba zai bari mutum ya ji daɗin auren ba."
      "Kin gane karatun! Allah ya ba ki wani nagari ki yi auren ki ki huta."

    "Amin wallahi!" 

    Shiru muka yi dukanmu kafin muryar Barira ta katse mana tunanin zucin da muke yi, saboda waƙar da take yi cikin ɗaga murya tana faɗin,
       "Allah ya aika munafukinmu ƙarshen nesa."
 "Tafiyar ƙasa ko da lafiya ko babu."
   "Na sha tabara na sha yasin."
        
     Ƙaƙƙarfan tsaki Sajida ta buga mata sannan ta ce da ni, 
       "Aunty kawo wayarki na saka miki hotunan biki da aka yi mana. Na so tura miki ta WhatsApp, ganin zan zo gidan ya sa na fasa"

     Na miƙa mata wayar ta loda mini su duka. Ta miƙo mini wayar tana faɗin, 
     "Hotunan sun yi kyau duba ki gani. Na ma saka miki wasu status ɗinki."
      
    Ras na ji gabana ya faɗi, saboda ban so ta ɗora wanda muke da Mukhtar ba. Na goge inda nake da shi duk da na san masu GB dole sai sun gan shi. 
      Hira muka ci gaba da yi, da ta tashi tafiya muka yi sallama na raka ta har bakin ƙofar gida. Daidai lokacin da Baban Taufiƙ ya danno kan motarsa ya durfafi ƙofar gidansa.
     Juyawa kawai na yi don ba na so ma na ga abin da zai biyo baya. Saboda har ga Allah ba na fatar Sajida ta aure shi ko don Maman Taufiƙ da halinta.
        
     ***
      Daren ranar ban yi bacci mai daɗi ba, hakan ya sa safiyar Litinin ta waye mini babu kuzari, na ji kamar kada na fita wurin aiki. Ƙarfafa kaina na yi dole na shirya tare da su Ummu Salma, da ke nasu shirin zuwa makaranta.
     Sai dai inda gizon ke saƙar babu komai na kalacin safiya a kitchen, domin alamu ya nuna Barira ba ta fito ba ma balle ta girka mana. Haushi ya sa na yi mana boiling ruwa na jefa Indomie ta jiƙa, a gurguje na saka mana mai da yaji.
     Nan take muka lamushe saboda mun daɗe ba mu ci ta a hakan ba ta yi mana daɗi sosai. Kiran da Najib ya mini a waya ya sa muka fito tare da su duka za mu fice.
      "Ai wallahi ba zan girka komai ba a gidan nan don ba boyar kowa nake ba."

     Maganar da Barira ta yi kenan tana ƙoƙarin fitowa daga ɗakinta Mukhtar yana bayanta. Turus ta yi a lokacin da ta gan mu ni da yaran za mu fice,
     "Aunty ina za ku je ba ku karya ba?"

    Kallo ma ba ta ishe ni ba daga ni har yaran muka fice ba tare da mun tanka su ba dukansu. Muna ƙoƙarin shiga adaidaitar Mukhtar ya iso wurin yana faɗin,
      "Yanzu abin naki har ya kai ki hana yarana su gaishe ni?"

     "Ina kwana?"

Ita ce gaisuwar da Najib mai adaidaita ya yi wa Mukhtar yana sosa ƙeya, ni kam kallo ma bai ishe ni ba illa umurnin da na bai wa Najib,
 
     "Mu tafi ka ji!?"

Ya buga adaidaitarsa ya tafi muka bar Mukhtar a nan tsaye yana kallon mu.

      'Dole na canza tsari'

    Zancen zucin da na yi kenan saboda ganin tsarin da na ɗauka a kan girki, ba zai haifa mini ɗa mai ido ba. Domin ni da 'ya'yana ne za mu tagayyara, ita da shi ko a jikinsu mu ne a wahala. Na tsayu a kan ci gaba da girkina daga ni sai yarana, tun da ba wani amfani yake yi mini ba ba zan jira ta yi girkin kwanakinta na yi nawa ba. 

     'Zan fita sabgarsu duka, kuma zan dinga abincina daga ni sai 'ya'yana.'

     Tunanin da na yi kenan a cikin zancen zuci, na sauke ajiyar zuciya sannan na ce da Ummu Salma. Idan suka dawo ta yi mana abinci kamar yadda take yi kafin zuwan Barira, kuma kada su yi abin da zai janyo rikici a dake su a banza.
     
     Bayan an ajiye ni na fara taku a hankali zuciyata cike da tunanin abin da zai faru, idan sun dawo ba na gidan. Gaisawa na yi da mutane suna yi mini ya jiki ina amswa har na isa offis ɗina. 
     Key na saka na buɗe sannan na shiga da sallama a maƙoshina. Kujerun na kakkaɓe sannan na share Ofishin tas na goge, saboda ƙurar da ya yi tsawon kwanakin da ban zo ba. Ga shi makullin yana hannuna na mance ban bai wa Amina ba a lokacin bikin.
     Zama na yi ina sauke numfashi sai ga ɗaya daga cikin masu shararmu ta ƙwanƙwasa mini ƙofa. Umurni kawai na bayar a kan a shigo ta fara gaishe ni na amsa mata a mutunce.

     "Hajiya shara za a yi!"

    "Ki je kawai Inna har na share!"
       "Allah ya saka miki da alheri ya ƙara duba gabanki da bayanki."

    "Amin." Na faɗa zuciyata a sake saboda na ji daɗin addu'ar sosai. Fitar ta ke da wuya wani masinja ya zo yana faɗin,
     "Ranki shi daɗe Oga yana kiran ki."

     "Ok!" Ita ce iya maganar da na yi ya fice na miƙe ina kakkaɓe ƙurar da ta ƙi sakin jikina, sannan na nufi ofishin fuskata a haɗe ƙirjina yana bugawa.

     Sallama na yi cikin siririyar murya ya amsa mini a gadarance tamkar ba ya so. Takardu na gani a gansa tsibi guda da hannu ya yi mini nuni da su a kan na ɗauka. Harara na wurga wa kwantaccen gashin kansa da ya sha gyara, saboda haushin izzar da yake ji da ita a lokacin.

     Ɗauka na yi kawai ba tare da na ce da shi komai ba na nufi hanyar fita. 
      "Ya hidimar bikin? Fatan Allah ya ba da zaman lafiya." 

     "Amin" Kawai na faɗa na fice, tunanin ƙara yi masa godiya ya faɗo mini a rai na koma. Bakin ƙofar na tsaya ina faɗin,
      "Na gode sosai a kan kyautar da ka yi mini. Allah ya ƙara rufa asiri."

    Bai ce da ni komai ba, har sai da na juya na ji ya ce, "Amin" can cikin maƙoshinsa. Raina a haɗe na fito ina gungunin da ban san me nake ta faɗa ba.
     Saboda sauyin da ya yi mini sosai yake taɓa mini zuciya, saɓanin baya da yake faram-faram da ni, duk da ba ya sakewa sosai ina yabon kirkinsa da Amina. Amma tun daga kan abin da Mukhtar ya yi masa ya daina sake mini fuska, musamman lokacin rikici na da su Ummita har tsawa yake daka mini tamkar ya dake ni.

    Ban ɓata lokaci ba na fara aikina gadan-gadan, Amina ta shigo muna hira ina aikin har lokacin tashi ya yi. Tare muka miƙa wa MD takardun muka fito tana cewa,
     "Wai ina amarya? Na manta ban tambaye ki ba."
     "Amarya tana gidan mijinta. Sauri nake yi ma na koma saboda ba na so yaran su yi mata ba daidai ba. Don na fahimci ita ma rawar kanta ya fi ta yawa."

    Dariya Amina ta yi sannan ta ce, "Ganin take yi karanta ya kai tsaiko. Tun da ta haɗa kishi da mace mai halin kirki da nagarta irin taki. Don wallahi ba don ke ta samu ba; da sai ta gane barno gabas take a yadda na gan ta wata jagwal tamkar sandar makafi."
      Ajiyar zuciya na yi ina tare wata adaidaita na ce, "Ki bari kawai! Nan da kike ganin ta ba ba ƙaramar 'yar hannu ba ce." 
     "A hakan?"

  "Tabbas! Ke dai kin ga mutum!"

     Da haka na tafi muna ɗaga wa juna hannu. Zuciyata cike da tunanin su Ummu Salma har aka ajiye ni ƙofar gidan. Tun da na jefa ƙafafuwana cikin gidan na fara jin sautin kukan Ummu Salma. Da sassarfa na shiga falon idona a kan Ummu Salmar da ke rakuɓe jikin gini tana cisgar kuka har da shessheka.

     'Me nake shirin gani?'





   Wata sabuwa🤔 wa ya taɓa mana Ummu Salma ne haka?😢





D. AUTA CE✍🏼


*ABOKIN AIKINA*


*@HADIZA D. AUTA*


*SADAUKARWA: DAUGHTER ANUP*


*TALATIN DA BIYAR .*

        "Lafiya!? Me ya same ki!?" 
      Abin da na fara faɗa kenan a hargitse tun kafin na isa inda take. Tana gani na da ta tarye ni da gudu ta faɗa jikina, tare da rushewa da wani sabon kukan ya sa jikina kyarma.
      Domin ko ni rabon da na saka hannu na dake ta har na manta, saboda tana ƙoƙarin barin abin da duk ta san ba na so,  balle ta yin abin da zan dake ta a kansa. Haidar ne kawai yake shan duka a wurina, don ko Iman miskilancinta kawai yake sa na dake ta idan na saka ta aiki tana jan jiki.
      Jikina na ɓanɓare ta ina faɗin, "Faɗa mini me ya faru?" Cikin shesshekar kuka ta ce, "Abbanmu ya dake ni"

     "Me kika yi masa?" 

 Ƙirjina yana bugawa na yi maganar saboda sabon ɓacin ran da ya ziyarci zuciyata. 
      "Girki na zo zan ɗora amarya ta ce ba zan ɗora shi ba, ni kuma ganin kin ce na yi kafin ki dawo ya sa na ci gaba da yi. Ban san ya aka yi ba ina tsaka da kwasar abincin na ji muryar Abbanmu yana ta zagi na. Shi ne ya same ni a kitchen ɗin yana ta dukana, kuma ya ɗauke abincin duka ya ce ba za mu ci ba tun da amarya ta yi girki shi kowa zai ci."
 
     "To fa! Abin har ya kai can?" 
       "Har ya wuce ma! Kuma wallahi matuƙar kika sa ta raina Barcy sai na ci uwarta a cikin gidan nan."
      Zancen Mukhtar kenan a sama yana ba ni amsar tambayar da na yi wa kaina cike da mamaki. Na saki hannun Ummu Salma na tarye shi gaba da gaba na ce,
      "Sai dai ka ci ubansu waton kai kenan! Don wallahi daga kai har wannan ƙanjamammar amaryar holoƙon da kake tinƙaho da ita; kun yi kaɗan ku ci zarafin yarana ba bisa haƙƙinsu ba. Abinci da ta dafa kuma ni na ba ta umurnin dafawa, saboda ba zan sake zama wata ballagaza tana hora mu da yunwa ba."
      "Ke kika ba ta umurni Barcy kuma ta hana ta, saboda tun kafin su dawo gidan ta yi girki. Kuma shi za a ci dole don tuni na kyautar da wanda ta dafa."
     Baki a sake nake bin fuskarsa da kallo saboda mamakin zancensa na 'ke kika saka ta Barcy ta hana'.
      "Waton ita Barcyn ce za ta dinga ba mu umurnin abin da za mu yi a gidan da wanda za mu bari?"
      "E! Saboda ni ce amarya kuma har yanzu ina cikin kwanakin girkina. Ki bari idan girkin ya dawo hannunki ki yi duk abin da kike so babu ruwana. Amma yanzu kam babu wanda zai ɗora girki a cikin gidan nan bayan wanda na dafa."
      Martanin Barira kenan tana girgizar jiki tare da riƙe ƙugu. Ta so ba ni dariya amma na fuske na ce,
     "Sannu shafaffiya da mai jikar sarauniyar Ingila 'yar gidan Sarki Macciɗo. To na rantse da Allah zan yi bikin watan cin ubanki a cikin gidan nan. Ko ki fita sabga ta da yarana; ko na nuna miki na fi ki sanin makamar iskanci da rashin mutunci. Abincinki kuma wallahi daga ni har yaran ba za mu sake jiransa ba, ke da cin abinci ya kawo gidan ki buɗe ciki ki yi ta zubawa, nawa kaso da na yarana duka mun bar miki. idan kin ƙoshi ki miƙa saura gidanku don na san suna da buƙata."

   Baki a sake take kallona tare da cizon yatsa tana faɗin,
 "Kai kai kai!"
     Kansa na juya ina faɗin,
 "Kai kuma mijin ta ce! Namijin ho-ti-ho! Ɗankwali ya ja hula! To ka sanar da ita babu kwanakin girkin kowa a kaina. Idan ma akwai duka na bar mata don haka ku sake wa 'ya'yana mara su ji daɗin fitsari. Kuma daga yau abincinmu daban za mu dinga girkawa, idan ka ji tsoron Allah ka ba mu namu haƙƙin. Domin ka rage wa kanka guzurin mugun bugun da Mala'iku za su yi maka a ranar lahira. Idan kuma ka bijire kamar yadda ka yi a baya, ina maka albishir za ka girbi duk abin da ka shuka khairan ko sharran. Na zare hannuna a cikin sha'anin girkin matarka, ni ma daga yau babu ruwanta da duk abin da za mu ci ko mu sha, a cikin gidan nan ni da yarana. Saboda ba za mu zauna tana gasa mana aya a hannu ba saboda abinci."
    " Ina ƙare faɗar hakan na yi gaba zan shige ɗakina, sannan na yi saurin juyowa ina faɗin, 
       "Gass nawa ne, ni na saya da kuɗina, repelling ma ni nake yi ba wani yake yi mini ba. Daga yau kada a sake taɓa mini kaya ko da ɗora ruwan zafi ne!"

     "Wallahi ni kuma ba zan yi girki da itace ba!"

     Abin da Barira ta yi hanzarin faɗi kenan tana murguɗa baki. Saboda Ummu Salma ta faɗa mini ita ce ta nuna mata yadda ake amfani da shi. Lokacin da take girkin tana 'yan waƙe-waƙen farinciki, lokacin da wata ta kira ta a waya baki a sake take faɗin,
     'Ke yarinya na wuce nan! Sabod Allah ya kawo ni gidan arziƙi, inda ba zan sha wahalar hura wutar ice ba. Gass cooker Hajiya shi nake girki da shi yanzu haka har na kusa gamawa... Ja can yarinya! Allah dai ya ba ku irin tawa kawai, don ni na tako arziƙi na wuce da sanin ku ƙananun ƙwari.'

    Tuno labarin na yi murmushi mai sauti sannan na ce da ita, "Wannan kuma mijinki za ki faɗawa ba ni ba!"

      "To ni ko idan dai da ice zan dinga girki, sai dai kada kowa ya ci abinci a gidan nan, daga ni har shi wallahi."

     "Kanku ake ji!"

Kafaɗa na ɗaga, sannan na juya na shige ɗaki yarana suka biyo bayana, Haidar na kalla raina a ɓace saboda yadda ya zama kalar tausayi. kuma na sani ba komai ba ne face yunwa don ko kaɗan bai da haƙurin ci.
     Jakata na ajiye da sauri na nufi kitchen ɗin, dole na yi tsaye ina wassafa abin da zan yi a lokacin. Saboda komai na kayan abinci an kwashe babu komai na sarrafawa, kuma na san ina da sauran Indomie da kayan tea waɗanda ni na saya da kuɗina, ba waɗanda Mukhtar ya kawo ba a daren da aka kawo Barira. 
     Amma duka an haɗa an kwashe domin a nuna mini iyakata. Na fito kitchen ɗin cikin ƙoluwar ɓacin rai na ƙwala wa Haidar kira, umurni na ba shi ya je gidan Maman Taufiƙ ya ce, na ce ta zuba musu abinci su ci shi da Iman.
     Sannan na koma ɗaki na ɗauki kuɗi na fice tamkar wata zararriya, saboda tsananin ɓacin ran da nake ciki. Adaidaitasahu na hau kai-tsaye ta ajiye ni shagon da nake siyayya, na ɗauki duk abin da muke da buƙata tsakanin abin kari da na girki har da rabin buhun shinkafa.
      ATM ɗina na bayar ya zuƙe kuɗin da ke ciki tas, sannan sauran da ya biyo ni na ce da shi mu tara ƙarshen wata. Don a lokacin kwanaki ne kawai suka rage a yi albashi. 
       Cikin Napep aka loda mini kayan na nufi gida. Inda na taras da Mukhtar yana ta bala'i har da kumfan baki, a kan na je roƙon abinci a wani gida bayan ga wanda Barira ta dafa.
     Ƙanzil ban ce da shi ba, illa yaran da na tambaya sun ci abincin suka ce da ni sun ci har sun ƙoshi. Sanyin daɗi na ji ya tsirga mini sosai a raina, saboda ganin kular da ta zubo musu abincin na tabbatar da zai wadace su.
      Tuwon garin masara na fara yi sannan na kaɗa miyar kuka, saboda ban da kuɗin nemo cefanen wata miyar bayan kukar da nake da ita.
      Duk da babu ƙiren nama ko kifi ta yi daɗi sosai, don ta sha daddawa da waken da na kwankwatsa cikin kayan yaji, wanda nake amfani da shi a wasu lokutan, a watsa a matsayin naman miya. 
Ban samu damar yin sallar Zuhur ba sai da aka yi kiran Asr, saboda ina gudun na bar girkin Mukhtar ko Barcynsa su yi mini ganganci.
     Abincin na kwashe duka a kula na kawo ɗakina har miyar, na ce da yaran su ƙara abincin kafin su tafi makaranta. Ummu Salma da Iman suka ce da ni sun ƙoshi, suka fara shirin makaranta Haidar kawai ya ce bai ƙoshi ba, na zuba masa sannan na yi arwala na yi sallah. 
      Ruwa na fara watsawa sannan na fito cikin sauri, saboda surutun da Ummu Salma take yi wa Haidar a kan ya ja sun yi latti. Don huɗu da rabi har ta gota saɓanin dokar makarantar da ake zuwa ƙarshe uku da rabi.
       Gani na ya sa suka fice shi ma ya bi su da gudu yana faɗin su tsaya masa. Ina tsaka da shafa mai a jikina Mukhtar ya faɗo ɗakin kamar an jefo shi yana faɗin,

       "Wai ke wace irin mace ce da ba ki ƙulla alheri sai sharri!?"

       "Koya na yi a wurinka!"

Na faɗa kaina tsaye ina ci gaba da shafa mai, ba tare da na kai idanuwana inda yake ba. 
       "Ni duk abuna, ban taɓa hana sunnar ma'aiki ba! Ke kuma ƙiri-ƙiri kina ƙoƙarin hana abin da Allah ya halasta. Don kin ga yarinya tana jin maganarki shi ne kika hure mata kunne a kan abin da take so. To ta Allah ba taki ba wallahi! Don aure ne ko kin ƙi idan Allah ya nufa za ki ji kunya."
       "Shi kuma wannan soki-burutsun daga ina ya fito? Da kake tayar da jijiyoyin wuya kamar wani zautacce!"
      
     "Da komai ma za ki iya siffanta ni da shi don ba yau kika fara ba, amma auren Sajida da Malam Aminu kamar an yi an gama ne! Ki so ko kada ki so duk ɗaya don babu haɗin dangin iya ke da ita balle na Baba. Saboda tun kafin ya je wurinta sai da ya fara yi mini zancen, kuma Ni na ba shi lambarta da hannuna saboda na gamsu da haɗinsu. Don haka kin yi kaɗan ki hana sunnar ma'aiki a kan wani guntun dalilinki na banza."
      "Wannan kuma ku ta shafa babu ni a ciki. Amma duk wanda ya ƙi ji ba zai ƙi gani ba."

   Zancen da na gama faɗa kenan ina saka kayana, saboda mamakin yadda aka yi maganar ta fito. Da kuma wanda ya faɗa masa ni ce na hana Sajida kula Baban Taufiƙ.

     "Don girman Allah ki ce da ita idan aka kai Sajida kada ta bar ta da rai ta kashe ta tun a daren farko!"
      Maganar da ya faɗa kenan a fusace yana nuna ni da hannu tamkar ya tsokale mini ido. 
      "Ohon muku! Ko a jikina, don babu ni a cikin kashin balle na kwasa." Na yi maganar tare da ɗora haƙarƙarina a kan gado. Saboda jikina ko'ina ciwo yake yi mini duk da wankan da na yi.

     "Na dai faɗa miki daga yau ki zare hannunki a cikin auren nan!"
       "Ummhh! Kanka ake ji!" 
 Data ta na kunna ina duba saƙonni har ya gama bambamin da yake yi ya fice. Zuciyata cike da tunanin abin da ya janyo maganar har aka saka ni ciki. Don na san Sajida ba za ta faɗi yadda muka yi da ita  ba.
     Kasa haƙura na yi har sai da na kira ta a waya, raina babu daɗi na ce da ita,
      "Ya kuka yi da Baban Taufiƙ?"
 'Wallahi Aunty na faɗa masa gaskiya. Kuma ya aminta da zancen har mun yi sallama da shi a kan ya janye. Me ya faru halan?'

      "Mukhtar ne ya zo yana wasu surutan da ban san ina ya jiyo su ba, wai na hure miki kunne komai na ƙi idan Allah ya nufa zan ji kunya."

     'Gaske na ji suna waya da Mama tana ta faɗa. Ashe zancen ne yake faɗa mata. To wallahi wannan munafukar matar tasa ce ta faɗa masa yadda muka yi ni da ke. Saboda lokacin da muke yin maganar tana falon har ta yi waƙa.'

      "Eeeee! Tabbas ita ce! Domin kuwa biri ya yi kama da mutum!"

     'Ki bar ta kawai Aunty! Zan zo har gidan na ci uban shegiya. Ba ta san daman can haushin ta nake ji ba.'

     "Ki ƙyale ta kawai da ni take zancen! Da sannu sai na koya mata hankali a cikin gidan nan."

        'Ke da wa kike waya? Idan mai hure miki kunnen ce ki faɗa mata na ce; ta Allah ba tata ba wallahi...Ni dai Mama don Allah ki san me kike faɗa haka kawa....'

     Tsinke kiran kawai na yi tare da sauke ajiyar zuciya, saboda zancen Yaya Maimuna ba ƙaramin ƙona mini rai ya yi ba. Duk da daman can na san tana adawa da ni tun lokacin da na tuɓure, a kan ba na son zama da Mukhtar sai ya sake ni. Tun daga lokacin ko gaishe ta na yi sai ta nuna mini zallar ƙiyayyar da take yi mini. Bayan zagi da cin zarafin da take yi mini a bayan idona suna dawo mini. 

      Kwance nake kan gadon ina ta juya abin cikin raina, tare da rikicin da za a yi muddin Maman Taufiƙ ta san da labarin. Har su Ummu Salma suka dawo ban tashi daga kwanciyar ba, ba su jima da shigowa ba aka yi kiran sallar magrib. 
     Saboda punishment ɗin da aka ba su makaranta a kan lattin da suka yi. Iman sai ajiyar zuciya take yi saboda tambon bulolin da suka sha sun fito raɗau a tsintsiyar hannunta.
      Da ƙyar na shawo kanta ta daina kukan, don daman can ita raguwa ce. Ko kaɗan aka taɓa lafiyar jikinta sai ta yi raki balle an saka bulala an dake ta.

     Sai da muka yi sallah dukanmu, sannan muka zauna zaman cin abinci ni da su a cikin ɗakin. Bayan sallar Isha muka koma falo muna kallo, Barira ma tana ta wayoyinta da mutane tana shewa. Bayan zagin da take kamfatowa iri-iri tana sauke wa ƙawayenta.

     "Ke shegiya! Gobe ki zo akwai sabuwar chepter...Sosai ma ke dai ki zo kawai akwai labarai...Yawwa 'yar gari ki zo da kayan duka mu ɗan kora an kwana biyu ba a haɗu ba."

     Maganganunta sun saka jikina sanyi, saboda tunanin yarana da za su dawo ba na gidan. Kai-tsaye wata sabuwar idea ta zo mini, na yanke hukuncin tura su wurin Ummata goben. Gudun na taras da tashin hankalin da ya fi na yau, kuma ba zan juri rainin hankalin kowa ba a kan yarana.
      Matsayar da na kai kenan wadda kuma na kwana da ita a cikin raina. Da kayansu na fita na miƙa wa Najib tare da yi masa kwatancen gidan Kawu Sale, sannan muka rabu da zummar idan aka tashi ya kai su gidan. Zuciyata wasai saboda ganin na kashe gobarar da take ƙoƙarin tashi ta ƙone zuciyata da ta yarana. 





   Hmmmmm! Akwai badaƙala fa!🥲





D. AUTA CE✍🏼


*ABOKIN AIKINA*


*@HADIZA D. AUTA*


*SADAUKARWA: DAUGHTER ANUP*


*TALATIN DA SHIDA.*

        Zuciyata ɗauke da tunanin wace irin waina ce Barira take ƙoƙarin toyawa ita da ƙawayenta.  Har na kammala aikina na miƙe na fito offis ɗin, saboda Amina ba ta zo ofishina kamar yadda ta saba ba. 
       Ɓangaren su na nufa cike da burin na gan ta domin na sanar da ita rikicin da ke ƙoƙarin ruftawa da ni. Wanda nake ji a raina muddin Baban Taufiƙ ya nace da son auren Sajida; tamkar ya saka takobi mai kaifi ya datse alaƙar da ke tsakanina da matarsa.
     Saboda duk abin da zan faɗa mata ba zai goge kallon da za ta yi mini ba. Samun ta na yi cikin 'yan ofishin su suna ta hira, gani na ya sa ta miƙe tana faɗin,

       "Yanzu nake son na je hirar Sara ya riƙe ni."

      Gaisawa muka fara yi da mutanen sannan na fito Amina ta biyo ni, wuri muka samu muka zauna Amina ta fara faɗin,
      "Duk abin da mutum yake yi a ɓoye, watarana sai Allah ya tona masa asiri. Ka yi alheri ma ya ka ƙare balle ka ce ɗan akuya za ka mayar da kanka?"

      "Me ya faru da Sarar ne?"

        Tambayar da na cillo mata kenan, saboda ina so na ji domin mu tattauna abin da ya kawo ni.
     "Sara dai halinta na tumasanci ta aikata, har ta janyo Basiru ya darza mata ɗan banzan kashi. Sannan ya yi mata saki uku ringis, saboda ya kama ta da almajirin gidansu turmi da taɓarya a cikin ɗakinta."

     Babu shiri na furta, "Innalillahi wa inna ilaihirraji'uun! Ke duniya ina za ki da mu?"

      "Bari kawai! Ta gama aibata ki cikin mutane ta manna miki sharri. Sai ga shi ita kuma abin ya zo kanta, bayan tayar da jijiyoyin wuyan da Basiru ya gama yi a dalilinta. Duk da kuma shi da ita duka kanwar ja ce! Amma dai nata ya fi muni a matsayinta na 'ya mace."

     Ajiyar zuciya na sauke sannan na ce, "Kada ki shiga cikin masu zancen duk abin da namiji ya yi ado ne. Saboda shi kansa rami ne yake haƙa wa kansa da kansa, wanda idan ba Allah ya tsare ba; shi zai rufta cikinsa tare da Iyalansa duka. Saboda shi ya sayi komai da hannunsa kuma zai girbi abin da ya aikata ko da bayan ya manta. Duk da ban san wane ne Basiru ba sai a bakinku, amma ina da cikakken tabbaci a ksn haƙƙin abin da ya yi ne yake bin sa sanadin Sara."

      "Ban gane ba! Ita ma fa haka halinta yake kuma ya sani tun kafin su yi auren sun yi rayuwa." 

     "To kin ji inda tushen matsalar ya samo asali! Daman an ce wanzam ba ya son aska a jikinsa. Ba wai ina goyon bayan abin da Sara ta aikata ba, amma wallahi Basiru shi ne silar komai. Wataƙila akwai haƙƙin wasu da yake bin sa, wanda Allah ya jarrabe shi ta wannan hanyar domin a rama abin da ya aikata. Saboda sau da yawa mutane su suke janyo wa kansu bala'i da hannunsu, don ba zai taɓa yiyuwa ka yi wa 'yar wani kai ma abin ya ƙi zuwa kanka ba. Idan ba ka da 'ya'ya akwai na dangi ko kuma a juye komai a kan matarka. Allah dai ya ƙara kare mu ya kare zuri'armu, amma wallahi maza da yawa suna aikata abin da suke kira ado, daga baya haƙƙi ya bibiye su har ya samu hawa kansu ya zauna daram!"
       Murya a sanyaye Amina ta ce, "Na yarda da zancenki Maman Haidar. Don ko shi an ce ta sha kama shi da mata, wai da ta zo aiki sai ya kwashi mata ya kai gidan. Watarana ta mamaye shi ta koma gidan ba lokacin tashi ba,  ta kama shi hannu dumu-dumu da macen banza suna lalata."
      Murmushi na yi mai sauti sannan na ce, "A tunaninki idan da a ce shi ne ya sha kama ta aurensu zai yi ƙarkon da zai kawo yanzu?"
      "Gaskiya ba zai yi ba! Don a tashi guda zai hankaɗa ta gida, tare da takardar sakinta kamar yadda ya yi mata yanzu."

      "Kenan shi ne kawai mutum ita daga sama ta faɗo? Wallahi sha'anin maza yana ba ni mamaki. Laifi goma suke yi wa mace ta danne ta yi haƙuri, har ma ta yi ƙoƙarin ɓoyewa gudun wani ya ji a yi masa ɗan kallo. Amma shi guda kacal za ta aikata masa ya tona mata asiri ya rabu da ita."
       "Wallahi haka ne tabbas! Allah dai ya kyauta kawai, amma maza ba za su iya yin kwatar haƙurin da muke yi da su ba. Miye labari? Don tun da na gan ki na san ruwa ba ya tsami banza."

     'Yar dariya na yi sannan na ce, "Kenan dai idan babu dalili ba zan zo ba?"
      "Sosai ma! Yan ofishimu har gori suke yi mini a kan zuwan da nake yi wurinki kullum ke ba ki zuwa. Don na san yau sai na sha surutunsu, duk da zuwan naki zai yi amfani, ko ba komai kin wanke mini gorin da suke yi mini koyaushe."
       "Su dai mutane ba su raina abin magana." Abin da na faɗa kenan ina murmushi tare da gyara zamana na labarta mata komai.
       Shiru muka yi dukanmu kafin Amina ta sauke ajiyar zuciya tare da faɗin, "Danƙari!" Dariya muka yi a tare sannan ta ce, 
"Gaskiya dole ki shiga tashin hankali a kan wannan lamari. Kuma ba abu ne mai sauƙi ba balle ki faɗa wa Maman Taufiƙ ta sani tun wuri, kafin labari ya dawo kunnenta ta zargi da sa hannunki a ciki."
     "Kuma ba zan iya tunkarar ta da wannan batun ba. Domin ba zan taɓa zama sanadin rura wutar bala'i tsakaninta da mijinta ba."

      "To ya za ki yi yanzu?"

Tambayar da Amina ta jefo mini kenan tana kallo na, "Sajida ce kawai makamin da zan riƙa domin na hana ta karɓar abin. Sai dai kuma idan Allah ya ƙaddara babu yadda zan yi da ikon Allah!"
"Ni dai da kin bi shawara kin faɗa mata komai ki fitar da wuyan hannunki."
       
      Shiru na yi ina tunanin maganganun da muka taɓa yi har tana zancen ina mata fatar kishiya. Ina 'yar dariya na ce, "Ba za a ji mutuwar Sarki a bakina. Zan dai yi iya bakin ƙoƙarina wurin hana Sajida shi."

"To Allah ya kawar da fitinar da ke ciki."

      "Amin"

Daga haka muka rabu saboda lokacin tashi ya yi. Har muka je inda muke tsayuwa neman abin hawa ba mu daina zancen ba. 

****
      Zuciyata cike da damuwa na shiga gida bayan mai adaidaitasahu ya ajiye ni. Na kwashe sauran canjin da suka rage mini na miƙa masa, jakata empty take saboda na yi ƙaf daga gida har daji.
       Da guntuwar sallama na shiga falon, saboda sanin yarana ba su gidan. Ban ji motsin komai ba don ɗakin Mukhtar ma a rufe yake ruf alamun ba ya gidan. Har na gota ɗakin Barira na dawo babu shiri na tsaya jikin ƙofar, domin na ji tabbacin abin da kunnena ya jiyo mini.

     Sambatu na ji wanda cikin muryoyi biyu masu ɗauke da tsantsar shauƙi. Sai ihu suke yi suna shan yaji tamkar duniyar don su kaɗai aka yi ta.
     Cikin tashin hankali na nufi ɗakina saboda zuciyata da ke zargin Mukhtar ne tare da Barira a ɗakin. Amma har na zauna kan gadona ban daina jin sautinsu ƙasa-ƙasa ba, wanda kuma alamu ya tabbatar mini ba Mukhtar ba ne take tare da shi. 
      Don tun da aka kawo ta gidan ko daren farkonsu ban ji irin wannan ihu da sambatun ba. Haka kawai zuciyata ta kasa natsuwa da hakan, duk da na yi ƙoƙarin ture abin gefe na yi sallah. 
      Na fito zuwa kitchen sai dai ban ji surutan ba a lokacin, sharp-sharp na girka taliya ƙwaya ɗaya na zabga mata kayan haɗi. Nan take ƙamshi ya karaɗe gidan saboda ni kaina na san za ta yi daɗi ko a ido.
       Falo na dawo na zauna, ina cin taliyar na ji ƙarar buɗe ɗakin Barira. Ban damu da kallon wurin ba balle na ga masu fitowa.
     Shirun da na ji ya sa na ɗaga kaina na kalli bakin ɗakin, Barira na gani tare da wata ƙawarta sun sha jinin jikinsu. Wataƙila ganin da suka yi mini ya sa suka razana.

      "Daman kin dawo Aunty?"

       "E!"

"Yaushe kika shigo ban sani ba?"

     "Tun lokacin da kuka fara ihu ke da ƙawarki."

     Na ba ta amsa ina ci gaba da cin abincina alamun ko a jikina. Barira ta fara rawar murya tana faɗin, 
       "Aljanun..ta ne..suka ta..shi..shi ne fa..na yi mata addu'a..da ƙyar suka kwanta."
       "Allah Sarki! Gara da suka kwanta da wuri, don har na kira Mukhtar na faɗa masa; ya yi gaggawar zuwa Barcynsa da ƙawarta suna ɗaki suna ta sambatu. Domin ya ji daɗin cin uban aljanun da kyau har sai sun daina ihun daɗi"

     "Wallahi Aunty da gaske nake yi ko gidansu an san suna tashi lokaci bayan lokaci." Abin da Barira ta faɗa kenan tare da isowa inda nake jikinta yana ɓari.

      "Daman ai ban ce kina ƙarya ba."

      "Zo Aunty Suby ki yi mata bayani ko za ta gane" Ta ƙare maganar tana zarar ido alamun rashin gaskiya ɓaro-ɓaro a kan fuskarta.
Murmushi na yi mai sauti, sannan na ajiye plate ɗin na ɗora ƙafa ɗaya kan ɗaya a kan teburin na ce,
        "Kun fi ni tashanci, ni kuma na fi ku wayo saboda dukanku na girme ku. Don haka na ji duk abin da kuke faɗa a cikin sambatunku. Kuma na san me kuka aikata, saboda haka zaɓi ɗaya na ba ki. Ko ki daina wannan shashancin daga yau. Ko na faɗa wa Mukhtar gaskiya ya ɗauki mummunan mataki a kanku daga ke har ita."
      "Wallahi Aunty na daina, daman can magani ne muka sha muka yi bacci. Ba mu san duk abin da ya faru ba har sai da muka farka."

     "Wane irin magani ne haka?"

       "Ke kam Barira kin sha haushi! Ita kishiyar kike yi wa wannan rawar muryar? To ki zauna tana yi miki titsiye tun da uwarki ce! Mitsssss! Aikin banza kawai, ni kin ga tafiya kya ji da kayan takaicin ki ke kaɗai."
       Zancen ƙawar Barira kenan wadda na ji ta kira da sunan Suby. Na yi hanzarin miƙewa na biyo ta, gani na ya sa ta ja ta tsaya tana hurar hanci ta ce,

     "Wallahi daidai nake da ke, don ba tsoron ki nake ji ba"

        Gidan na rufe da kwaɗo ta ciki, sannan na koma ɗakina na ɗauko waya na kira Mukhtar. Kira ɗaya biyu ya ɗaga yana faɗin,

     'Lafiya?'

"Ba lafiya ba! Ka zo gida yanzun nan ga wata ƙatuwa nan ta zo har gida tana lalata da Barira."
     'Ban gane ba!'

"Ka zo gidan za ka gane"

    Ina ƙare faɗar hakan na nuna ta da hannu na ce, sai kin san ƙaryar bariki kike yi yau. Don sai kin raina kanki tun da ke kwartanci ba komai ba ne a wurinki.

         "Idan ya zo ki ce ya kashe ni!"

"Ba zai kashe ki ba, amma za ki raina kanki."

     "Don Allah Aunty kada ki biye ta, wallahi ba na so Romiyo ya ji maganar nan. In Sha Allah daga yau ko gidan nan ba za ta sake zuwa ba."
       "Ke kam kina da abin takaici Barira! Har yaushe za ki dinga kwantar da kai ga kishiya irin haka tamkar za ki yi mata sujada. Abin da take tunanin an yi kuma shi aka aikata, idan akwai wani abu da za ta yi kafin soloɓiyon mijin ya zo ta fara yi kafin shi. Ni wallahi da na auri irin wannan ragon mazan ƙara na lalace a kan titi."

      Dariya ta so ba ni, amma kuma na mazge na ce,
 "Oh ita Barirar ce ta faɗa miki soloɓiyo ne?"
      "Ko ma dai mene ne hakan yake."

 Bubbugar ƙofar da ake yi ya sa na je na buɗe kwaɗon na ja gefe, saboda ganin Yaya Maimuna fuskarta a haɗe. Tana ƙoƙarin yin magana Barira ta iso wurinta da gudu tana kuka tare da kai mata ƙara ta. 
       "Kin ga Aunty nan ta saka Aunty Suby gaba tana ƙoƙarin manna mata sharri. Don Allah ki ce ta bar ta ta tafi tun da ba gaskiya ba ne abin da take zargi."
     
     "Yi shiru! Faɗa mini me ya faru?"

Zancen Yaya Maimuna kenan tana ƙoƙarin rarrashin Barira, ta hanyar bubbuga bayanta tana share mata hawaye. 
      Suby ta fara magana tana cewa, 
"Wai daga ta dawo ta gan ni cikin gidan, shi kenan take neman haɗa ni da sharri. To wallahi ni daidai nake da zamaninta don na ci dubu sai ce..." 
       Marin da na kai mata a haukace ya sa ta haɗiye sauran maganar da ke bakinta. Ban jira komai ba, na yi cikinta da duka cikin sa'a na jefar da ita ƙasa na haye. Yaya Maimuna da Barira suna ƙoƙarin ture ni kanta na yi wata zabura na watsar da su ƙasa warwas suka faɗi.
      Sannan na ci gaba da kai wa Suby naushi a baki su ma suka rufe ni da duka. Hargowar Mukhtar ta sa dukanmu muka shiga hankalin kanmu. Gefen bakin Suby ya kumbure tamkar zunɓutun kaza, amma a hakan ta dinga aika mini zagi ta uwa ta uba. 
     Mukhtar ya dakatar da ita, sannan ya tambayi dalilin faɗan. Na yi masa bayanin komai Barira ta fashe da kuka tana faɗin ƙarya nake yi mata. Suby ma ta tuɓure a kan sharri ne na yi musu ba gaskiya ba ne.
     Yaya Maimuna ta dinga jifa ta da miyagun maganganun da suke nuni; da fatar abin da nake yi wa Barira ƙazafi da shi ya hau kaina ko 'ya'yana. 
       Raina a ɓace na ce, "Bakinki ya sari ƙaton dutse, don har abada ni ko yarana ba za mu yi irin wannan halin tumakai ba."
      Mukhtar ya taso mini da masifa kamar ya dake ni, wai na yi wa Barira da Subyn ƙazafi kuma idan na sake duk abin da na janyo wa kaina babu ruwan shi. Haushi ya sa na dinga mayar masa da raddi bakina yana kumfa tamkar na kai masa duka.
     Sanin halina ya sa bai taɓa ni ba, ya dawo kan Suby yana ba ta haƙuri tare da lallaɓa ta har ta fice gidan. Yaya Maimuna kuma ta dawo da faɗan sabo don daman can shi ya kawo ta. 

      "Daman wurinki na zo! Zugar da kike yi wa Sajida ta yi aiki. Amma ki sani wallahi muddin kika ga ba a yi auren nan ba; to sai idan ba na numfashi a cikin duniya. Amma wajibi ne sai Sajida ta auri Aminu ko kina so ko ba kya so."

      "Wane Aminun!!?"

Zancen Maman Taufiƙ kenan cikin muryar tashin hankali, a lokacin da take shigowa gidan idonta a kan Yaya Maimuna. 

       "Aminu na ji kina faɗa!"

         "Ko ma dai wane ne ba ku isa ku hana abin da Allah ya ƙaddara ba"

      Tambaya Maman Taufiƙ kenan da amsar Yaya Maimuna a lokaci ɗaya. Jikina yana rawa na ja Maman Taufiƙ muka shige ciki ina faɗin,
   "Ba da ke suke ba ni aka zo yi wa takakkiya. Ni kuma a yanzu daidai nake da kowa tun da abin nasu babu mutunci balle kawaici."
       "Wai har na ji sanyi wallahi. Ba ki ji yadda ƙirjina ya buga ba a lokacin da na ji ta kira sunan Amini.."
      Zama muka yi a kan kujera tana faɗin, "Ita Sajida aure za ta yi ne?"
      
     "E, kuma ba ta son mutumin."

     "Kuma shi ne za a zo wurinki takakkiya miye naki a ciki?"

      "Su dai suka sani."

  "Hayaniya na ji shi ya sa na zo na gani lafiya? Ashe Mamarta ce take abin da ta saba. Ni na rasa laifin me kika yi wa wannan matar da ta saka ki gaba irin haka."

    "Mijinki ake so a manna wa Sajida ba ki da labari."
      Maganar Barira kenan da muka jiyo daga ni har Maman Taufiƙa saman kanmu.
     
 "Mijina kuma?"

      "E, shi! Kuma babu mai son ta ga auren nan ya ƙullu face wadda kuke zaune da ita yanzu. Don a gabana take saka Sajida ta manne wa mijinki, domin kawai ta ga ƙarshen kishinki."

     "Innalillahi wa inna ilaihirraji'uun!" 

    Ita ce kalmar da muka haɗa baki wurin faɗa ni da Maman Taufiƙ, tare da miƙewa tsaye dukanmu muna kallon Barira.

     "To wasa ce nake yi! Ku yi haƙuri don Allah kada ku cinye ni da raina."

    



     Barcy lamarinki sai ke 🤔😂






D. AUTA CE✍🏼


*ABOKIN AIKINA*


*@HADIZA D. AUTA*


*SADAUKARWA: DAUGHTER ANUP*


*TALATIN DA BAKWAI.*

         Ban san ya aka yi ba, sai hango Maman Taufiƙ na yi maƙare da wuyan Barira tana kakarin mutuwa. Cikin wani sabon tashin hankali na yi kansu ina ƙoƙarin ɓanɓare hannun Maman Taufiƙ, daga muguwar shaƙar da ta yi wa Barira. Wadda azaba ta sa ta gwalalo ido waje gulu-gulu tamkar idanun mota.
       Ganin ba zan iya ni kaɗai ba na fasa ihu saboda gabaɗaya sun fita hayyacinsu, tamkar wasu sababbin halitta. Mukhtar ya iso wurin a ɗari yana faɗin,

      "Innalillahi wa inna ilaihirraji'un!"

      Ya ja Barira na samu na ƙwace hannun Mama Taufiƙ, sai dai hakan bai yi mata ba ta koma ta cafko ta iya ƙarfinta. Mukhtar ya yi hanzarin ture ta gefe ta faɗi sannan ya rungume Barira yana ƙwala mata kira a haukace, saboda alamunsa ya nuna tsantsar kiɗima da ruɗewar da ya shiga. Ganin halin da Barira take ciki riƙe da wuyanta tana juye-juye tare da kakari a lokaci ɗaya.
     Domin a kallo ɗaya za a kira shi da kakarin mutuwa saboda shure-shuren da take yi. Maman Taufiƙ kuma ta baje ƙasa tana gumza tamkar wata raƙuma. Bayan furzar da yawun da take yi  yana baltsi a kan fuskarta.
       Ruwa na ɗebo da gudu na dawo a firgice saboda na gama kai wa ƙololuwar ruɗewa. Sai dai tun  kafin na iso na hango ta zabura tamkar wata zakanya ta yi kan Mukhtar da ke rungume da Barira. 
     Cakumo shi ta yi ta wurgar gefe tamkar a cikin shirin horror, sannan ta fisgo tsorayen Barira sai ga ta da su a hannu ta jefar ƙasa.
      Kukan kura na yi tamkar wata ifirituwa na kai wa Maman Taufiƙ raruma ta baya. Saboda ƙoƙarin fisgo wasu tsorayen da take yi ta sauke su ƙasa kamar yadda ta yi wa na farkon. Kokawa muka shiga da ita tsakiyar falon tana so na sake ta ina damƙe ta iya ƙarfina. Tun muna faɗawa kujeru har muka faɗi ƙasa a tare muna mulmula tamkar wasu macizai. 
       Addu'a na dinga karanta mata a bakina cikin sauti tun tana fisge-fisgen har ta yi luf! Na ci gaba da karanta mata surorin tsari da kore shaiɗanun aljanu. Saboda na gamsu da cewa ba ta cikin hayyacinta balle hankalin kanta, shi ya sa take ƙoƙarin aikata aika-aikar da dukanmu sai mun yi da-na-sani. 

       Ganin ta lafa na hango Mukhtar ya nufi inda Barira da jini ya gama wanke mata jiki kaca-kaca. Ihu ya yi tare da kinkimarta tamkar 'yar tsana ya fice da gudu yana faman kiran sunanta.
     Fitar su da ɗan lokaci na saki Maman Taufiƙ na miƙe ina kiran sunanta tare bubbuga jikinta. Firgigit ta miƙe idonta a zare sun yi jawur tana ƙare wa falon kallo, tamkar wadda aka bai wa aikin ƙididdige abin da ke cikin falon duka.
      
      Hannunta na riƙa ta miƙe tana kakkaɓe kayan jikinta ta ce, 
       "Me ya kawo ni gidan nan?"
      Fuskata ɗauke da mamaki na ce, "Kina nufin ba ki ma san kin zo gidan ba?" Na ƙare maganar tare da zuba mata idanuwa domin na tantance ita ce ko sarakan aljanunta masu neman ɗaukar rai.
       "Wallahi Maman Haidar ban san na zo gidan nan ba! Iya abin da kawai zan ƙaras tuƙin tuwon da nake yi a kitchen.

      "Cabɗijam! To mu je na raka ki gida kada ya ƙone a yi biyu babu"

      Hijabinta na mayar mata sannan takalminta na ja nawa hijabin muka nufi gidanta. Abin mamaki tun a ƙofar gidan na fara jiyo ƙaurin ƙonewar shinkafa. Da sauri na sake ta na yi kitchen ɗinta da gudu na saukar da tukunyar tuwon. Wadda ta turnuƙe Kitchen ɗin da hayaƙi ko gabana da ƙyar na gani, har na samu sararin sauke tukunyar a kan gawayin da take girkin da shi.
     Na fito ina tari tamkar na shiɗe, saboda ulcer ta ko kaɗan ba ta buƙatar hayaƙi. Dalilin da ya sa na daina aiki da komai sai gass, duk da a lokacin da na saye shi ba ƙaramar rigima muka yi da Mukhtar ba. Saboda ya buga kansa a ƙasa shi ba zai iya wahalar shi ba, na ce masa na ji na ɗauka ni zan ɗauki nauyin komai ko don lafiyata.

      Gida na koma na rufe, sannan na dawo na kankare tuwon da fiye da rabinsa ya gama ƙonewa. A gurguje na canza tukunya na ɗora mata wani sabon tuwon, ganin garin semo a buhu ya sa na fara talga tuwon na rufe. Sannan na fito na nufi ƙofar gidan saboda sallamar da na ji Mukhtar yana bugawa.
      Hankalina a tashe na isa ina tambayar shi Barira da halin da take ciki, harara ya kwaɗa mini tamkar idonsa su faɗo ya ce, 
      "Ba ni makulli!"

Na ciro daga aljihun riga ta na miƙa masa ya wuce fuu, duk da alhinin da nake ciki sai da na tuno lokacin da aka jefar da shi ƙasa ya yi zaman 'yan bori. Bayan ya fasa ƙara tare da faɗin,
     
     "Wayyo Allahna uwata!!!!"

     Komawa ciki na yi ina 'yar dariya har tuwon ya yi na kwashe mata, a ledodin da na gani an gama buɗewa. Sannan na kashe gawayin na tafi falonta ina kiran sunanta, hango ta da na yi a kan kujera 3seater tana bacci sharkaf. Hakan ya sa na ji wani sanyin daɗi ya ratsa zuciyata.

     Ficewa na yi gidan ina ƙoƙarin shigewa gida na hango motar Baban Taufiƙ ya doso. Na dawo baya jikina yana tsuma na isa inda ya yi parking motarsa yana ƙoƙarin fitowa.

     "Don Allah! Wata alfarma na zo wurinka a kanta. Na san kana son Sajida, amma ka taimaki rayuwaka da yawa ka janye wannan maganar!"

     Tsayuwarsa ya gyara sannan cikin murmushi ya ce da ni, "Allah fa bai haramta mini ba, don haka ban ga abin tashin hankali a cikin lamarin ba. Idan ma matsalar Aminiya ne ku bar komai a hannuna na san yadda zan tafiyar da ita har ta amince."
       
      "Ba za ta amince ba! Don yanzu haka da ƙyar amaryar Mukhtar ta sha a hannunta. Saboda ta yi gangancin sanar da ita shi ne ta shaƙe ta har da cire mata tsoro uku."

     "Innalillahi wa inna ilaihirraji'uun! Me ya sa ba ku nemo ni tun wuri ba?"

       "Share da ita kawai duk ita ce ta ƙulla komai! Kuma ko za ta mutu wallahi ban ce ka janye ƙudurinka ba! Ita kuma Barira; ki sani duk abin da aka yi mata danginta suna tafe gun ki, domin su ɗaukar mata fansa a kan abin da kika sa aka yi mata."

      Hannuna na rungume a ƙirji bakina yana rawa na ce, "Idan har sun fasa zuwa Allah ya tsine musu albarka. Idan sun zo ka ce kada su bar ni da raina tun da kai ba ka taɓa sanin mene ne adalci ba!"
    
     "Haka kika ce!?"

"Haka na ce!"

     Ina ƙare maganar na kai kallona a kan Baban Taufiƙ cikin matsancin fushi na ce, 
       "Ko ka janye zancen auren nan! Ko ka yi sanadin salwantar rayuwaka da yawa, ciki kuma har da kai idan ka nace wa abin tun da ku maza ba za ku damu da damuwar mace ba; muddin kuna son faranta wa zukatanku babu ruwanku."

      Ina gama faɗar hakan na yi cikin gida da sauri tamkar zan tashi sama saboda tsananin ɓacin ran da nake ciki.

      Ummata na kira a waya bayan na saita kaina na ce, "Su Ummu Salma su kwana a can, saboda gidan babu kwanciyar hankali."

     "Me ya faru!?"

Ta jefo mini tambayar cikin sauri tare da ɗaga murya. 
       "Mijin Maman Taufiƙ ne yake son auren Sajida, shi ne Mukhtar da Yaya Maimuna da amaryarsa suke ƙoƙarin haɗa mini tuggu a wurinta. Garin tsegumtawa Maman Taufiƙ da Amaryar tasa ta yi ƙoƙarin yi. Ta shaƙe ta har da cire mata tsoro uku, kuma Mukhtar ya ƙi tsayawa na yi masa bayanin yadda abin yake. Sai sanar da ni yake yi dangin amaryar za su zo su ɗauki fansa kaina."

     "Innalillahi wa inna ilaihirraji'un! To ki dawo gida kawai tun kafin hakan ta kasance. Don wallahi duk uban da ya taɓa ki a faɗin garin nan sai na nuna masa kina da gatanki. Shi kuma Mukhtar ki bar ni da shi zan ci uban shi a wannan gaɓar."
       "Kwantar da hankalinki Umma, wallahi babu inda zan je! Don za su zargi tsoro ne ya sa ni guduwa."

      "To ki jira ni gani nan zuwa yanzu!"

     Tana ƙare maganar ra kashe wayar, wanka na sake yi saboda gabaɗaya jikina ciwo yake yi. Domin ba ƙaramin gumurzu na yi da aljanun Maman Taufiƙ ba, don ni kaina ban san ina da irin wannan ƙarfin halin ba sai a lokacin.

     Ina ƙare sallar magrib ko tashi ban yi daga kan sallaya ba, na fara jiyo sautin mata da maza suna aiko mini zagi tare da faɗin ina nake na fito.
      Tsam na miƙe na fito cikin jarumta kamar yadda suke umurta ta, sai da na rufe ɗakina da makulli sannan na fara faɗin,

     "Ga ni ta nan! Idan akwai abin da za ku yi mini; don Allah kada ku bar ni da raina!"

      Wani matashin saurayin da a kallo ɗaya na gano ɗan daba ne, ya fara buga zabgegiyar bulalar da ke hannunsa ƙasa yana faɗin,

     "Jarkutumar babakeren alllin karmatakon..."
 
      Ya ƙare da lailayo wata uwar ashariya ya sauke mini, tare da yin ihu yana ƙoƙarin kai mini duka aka rirriƙe shi. Ya fara yunƙurin kufce taron dangin riƙon da suka yi masa, yana ta zillo domin ya dake ni. 
      Sai ga jiniyar 'yansanda wiwi tamkar unguwar za ta tashi, saboda dirin motocin da na ji har cikin gidan. Mintuna a tsakani sai harbi muka jiyo.

 'Ɗwa-ɗwa!!' 

     Babu shiri dukansu suka fara ihu tare da gude-guden neman maɓoya. Rungume hannuwa na yi a ƙirji ina yar dariyar mugunta tare da komawa cikin kujeruna na hakimce.
      Sai ga ɗan wiwin ya zo kusa da ni yana dafa tafin ƙafata, tare da duƙar da ƙansa ƙasa yana faɗin,

     "Don Allah ki yi mini rai! Wallahi ko sati ban yi ba da dawowa kurkuku. Idan na koma ban san loakacin da zan fito ba!"

     Ƙafa na saka na kai masa harbi a muƙamuƙi, ya yi saurin dafe gefen bakinsa yana muzurai. Fuskata a haɗe na ce da shi,
       "Gara ka koma can ka ci gaba da rayuwa don har yanzu ba ka san Annabi ya faku ba!"


      Ummata na ga ta shigo gaba 'yansandan a bayanta fuskarta a cure cikin takun taƙama. Sannan ta ja ta tsaya inda nake tana dudduba kujerun jikina, wanda kai-tsaye na gano raunin da take zaton sun yi mini take dubawa.
     Ganin ina murmushin ƙarfin hali har da gaishe ta, hakan ya sa ta ce,
 "Alhmdulillah!"

    Sannan ta juya wurin 'yansandan tana faɗin, "Ofisa! A tafi da su dukansu har matan babu wanda za ku bari!"

      Haka aka dinga tasa ƙeyarsu ana dukan ɗuwawunsu da kan bindiga har aka fice da su dukansu. Sannan Umma ta sauke ajiyar zuciya ta ce da ni,

      "Tashi mu je gida!"

Kallonta na dinga yi kamar ba ita ba, saboda umurnin da take ba ni a kan mu je gida tamkar almara.
     Domin wannan ne karo na biyu da ta ba ni umurnin zuwa gida da kanta ba tare da na nema ba. Na farko lokacin da Mukhtar ya faɗa wa danginsa da mutanen unguwar na ce sai na kashe shi, ko na kashe kaina idan bai sake ni ba. 

      Tana gaba ina bayanta muka fice gidan, adaidaitar da ta zo da ita muka shiga. Bayan Yansandan sun tafi da dangin Barira. Sai dai har muka je gidan Kawu Sale ba ta sake cewa da ni komai ba.
      Domin na fahimci fushinta ya gama kai wa maƙurar, tun daga fuskarta da yanayin iskan da take furzarwa. Bayan ajiyar zuciyar da take saukewa lokaci bayan lokaci.








Manage plss😢 ni da yarona duka babu lafiya.





D. AUTA CE✍🏼


*ABOKIN AIKINA*


*@HADIZA D. AUTA*


*SADAUKARWA: DAUGHTER ANUP*


*Alhamdullah! Jiki da sauƙi. Na gode sosai da addu'o'inku. Allah ya saka da alheri. Luv u all😘*


*TALATIN DA TAKWAS.*

         Shiga muka yi gidan tare da Umma tana gaba ina bayanta, yaran suka zo da gudu suna murnar gani na. Rungume ni suka yi dukansu tare da faɗin,
     "Oyoyo Mama!" 
Babu shiri na yi hanzarin shanye ƙwallar tausayin su da ta cika mini ido. Saboda har kullum ina tausaya musu a raina, a kan zaɓen tumun daren da na yi musu, wurin nemar musu kamilin uba kuma majinginarsu. Inna Kulu ta fara tsokanar su da cewa, 
     "Lalle ɗan aro ba ɗa ne ba, waton saboda ganin uwarku har kuna ƙoƙarin ture Kakarku. To ke Habi ki san zaman da kike yi da su, duk wani daɗin bakin da suke yi miki na rashin ganin ta ne a kusa da su.
     "Kai Inna Kulu! Kada ki haɗa mu da Umma, ki sa gobe ta ce ba za ta yi mana ɗan malele ba."

    Abin da Ummu Salma ta faɗa kenan tana dariya tare da tsalle tana son rufe wa Inna Kulu baki, a kan ta yi shiru. 
       "Daina rufe mini baki sai na faɗi gaskiya." 

     "To ai muna son Umma ita ma ta sani."

    Haidar ya faɗa yana wata tafiyar gayu hannuwansa duka a aljihu. Daga ni har Inna Kulu dariya muka yi, saboda har da doro yake haɗawa yayin tafiyar yana jefa ƙafa tamkar wani sabon gurgu.
      Duk abin da muke yi Umma tana cikin ɗakinta ba tare da ta ce da mu komai ba.
      Inna Kulu ta shimfiɗa mini tabarma a tsakar gidan na zauna, sannan ta kawo mini tuwon dawa da miyar kuka ta sha nama. Na zauna ina ci tare da Haidar tana tsokanar shi da sunan acici ba ya ƙoshi.

      Daga nan inda muke na jiyo sautin Umma cikin fushi tana faɗin, "Babu wata gaisuwar ka da nake buƙata. Ka yi gaggawar kawo mata takardar sakinta cikin mutunci, ko kuma kotu ta raba mu da kai cikin tsiya."
       Ban san me aka ce da ita cikin wayar ba, amma tabbas wani sanyin daɗi ya ziyarci zuciyata. Domin na tabbatar Mukhtar ne take waya da shi, kuma matakin da ta ɗauka a kan aurenmu ya yi mini daɗi sosai.

     "Babu wani daɗin bakinka da zai yi tasiri gare ni a wannan karon. Abin da nake so da kai kenan, ko da arziƙi ko da tsiya-tsiya."

       Shiru muka yi dukanmu, ina ta juya maganganun Umma cikin raina. Inna Kulu ta miƙe ta yi ɗakin, Mintuna a tsakani na ji ta fara faɗin,
      "Kada ki yanke hukunci cikin fushi Habi. Ki bari a bi komai a hanka..."

        "Babu wani hankali da zan bi Mukhtar da shi yanzu! Allah ya tsine wa damarmakin da aka ba shi a baya yana fatali da su cikin izgilanci. Ko ya ɗauka neman kai nake yi da ita ne? Shi ya sa yake abin da ya ga dama ana ƙyale shi don albarkacin 'ya'yan shi. To wannan karon; ko ɗa dubu ne a tsakaninsu sai ya ba ta takardarta. Idan kuma ya ƙi bi ta lallami; zan nuna masa na fi shi zafin kai. Har yaushe zai dinga dawo mana da hannun agogo baya? Sai an yi gaba a dawo baya! Kullum da sabuwar matsala yake zuwa. To idan na danne ta cikin gidansa yana cusguna mata; wallahi a wannan karon ba zan zaunar da ita ta ƙara fuskantar baƙincikin kishiya ba."

     Daga nan inda nake zaune, ban san lokacin da na juya gabas na yi Sujudu shukur ba. Saboda tsabar farincikin da ya lulluɓe zuciya, bayan wani sabon kuzarin da na ji ya shiga jikina.
     Tuwon da ke gabana na ture gefe, sannan na miƙe na nufi ɗakin Umma cike da karsashi na zauna. Inna Kulu tana ci gaba da tausar ta amma ƙanzil ba ta ce da ita ba. Hakan ya sa na yi gyaran murya na ce,
      "Umma ki daina ɓata ranki a kan banza. Ki bar ni da su daga shi har matarsa na fi ƙarfinsu wallahi. Don da kin ga amaryar tasa ma ba za ki ji haushin komai ba, saboda ko matsayin 'yar aiki ba zan ɗauke ta ba balle matsayin kishiya."

     "Kishiya ko ta 'yar tsana ce sunanta kishiya! Ke ba ki san ire-iren waɗannan matan sun fi komai iya kissa da kisisina ba? To ki bar raina allura ƙarfe ce! Don tuggun da za ta haɗa ke ba za ki iya yin sa ba."
     Abin da Umma ta faɗa kenan idonta a kaina. "Hmmmm!" Ajiyar zuciyar da na sauke kenan ba tare da na sake furta komai ba. Tagumi Inna Kulu ta cire tana faɗin, 
     "Ko dai ya abin yake don Allah kada a yanke hukunci cikin fushi. A bi abin a hankali ko don yaran nan da suka fito daga jikinsa."

    "Yanzu da a ce gayyar marasa albarkar nan sun illata ta ko sun taɓa lafiyarta; me zai ce? Ai ya san da zuwan su amma bai hana ba! Kenan duk abin da za su yi mata su yi kawai ya ba da ƙofa! To wallahi ko ɗiyar riƙo ce na san zafinta, balle ni na durƙusa ƙasa na haifo ta wata tara da kwana tara. Idan ma ya gaji ai babu dole! Ya sauwaƙe mata kawai tun da ba shi ne autan maza ba."

     "Ke kuma ke da wa kike ta masifa har ƙofar gida ana jin sautinki?"

      Zancen Kawu Sale kenan da carbi a hannunsa yana ja, alamun daga masallaci ya fito.
       "Ni da mara mutuncin can Mukhtar mana! Don haka ka sani ka ƙara sani; wannan karon babu mai raba ni da shi sai Allah! Sai na nuna masa na fi shi ɗibar albarka da duk abin da yake taƙama da shi!"

    Umma ta ƙare maganar a zafafe tare da ɗaga murya. "To ki fara shawo kan matsalar yaransa da ke nan ƙofar ɗakinki suna kuka. Tun da ke kullum ba ki bari a bi komai a hankali sai kin yi faɗa da tashin hankali!" 
     Yana ƙare faɗar hakan ya bar jikin ƙofar yana ci gaba da surutai. Umma ta yi wani mere sannan ta ce,
     "Komai za ka faɗa ka faɗa kawai! Amma wannan karon ba zan ɗaga wa Mukhtar ƙafa ba! Idan kuma ka matsa sai na tattara kayana na bar maka gidanka. Na fi so na kama haya na zauna tare da ita da yaranta duka. Amma ba zan taɓa barin ta cikin baƙincikinsa ya kashe ta ba wallahi!"

     "Wannan kuma naki ra'ayi ne! Don ba ki ji na ce komai a kan zamanta gidan nan ba. Idan ma zatonki don ba na so ta zauna mini ne nake so ta zauna gidan mijinta; to ki yi haƙuri na daina daga yau. Ga gida nan ta zauna daga yanzu har mahadi ya bayyana babu mai korar ta."

     Ya ƙare maganar hannunsa riƙe da ƙofar ɗakinta, don har ya tafi ya dawo domin ya mayar mata da raddi. Inda da sabo mun saba ganin rikicinsu, wanda sai sun hau sama ita da shi su faɗo ƙasa su shirya kamar ba su ba. 
     Shi ya sa Inna Kulu da 'ya'yanta suke burge ni, saboda babu ruwansu da shiga faɗansu. Ni ma a baya idan na ga suna yi kuka nake yi, na yi ta bin su ina ba su haƙuri, amma Inna ta fahimtar da ni ba a shiga tsakaninsu kunya ake ji. 
     Na gasgata hakan don sai sun gama faɗan suna cikin fushi Umma ta ce da ni,

       'Ke ni ma fa faɗan ƙarfin hali ne kawai nake yi da Salenmu. Don duniya kaf ban da kamar shi shi ma bai da kama ta.'

     Murmushi na yi kawai saboda tuno zancen Ummar. Fuskata a sake na ce,
     "Yanzu dai Umma don Allah ku bar maganar nan. Saboda Mukhtar bai kai darajar da zai dinga haɗa ki faɗa da ɗan'uwanki ba. Idan ta ni ce ma ko yanzu na koma gidan na ci gaba da haƙurin da nake yi. Don na san komai daren daɗewa gaskiya za ta yi halinta."
     
      "Ba za ki koma gidansa ba! Idan kuma so kike yi a raunata ki ki je ki jira dawowar masu farautar rayuwarki!"

     "Yi haƙuri Umm..."

Sallamar da muka jiyo ana rafkawa a ƙofar gida, hakan ya sa Kawu Sale ya amsa sannan ya fice. Mintuna a tsakani muka yi zaman jugum-jugum har ya dawo yana faɗin,

      "Ke aka zo nema!"

Ummar da yake kallo ya sa muka gano da ita yake, miƙewa ta yi tare da mayar da hijabinta ta fice. Inna Kulu ta sauke ajiyar zuciya sannan ta ce,
     "Tun da tana jin maganarki Zaituna! Don Allah ki fahimtar da ita. Ta bari a yi komai a hankali ko don yaran nan."
     Kawu Sale ya shigo ɗakin yana faɗin, 
      "Na san mijinki bai da mutunci, amma muddin aka biye ta Habi; ba za a haifi ɗa mai ido ba. Idan ma rabuwar ce a yi ta mutunci ba irin wadda girma zai zube ba."

 Murmushi na yi sannan na ce,  "Ka yi haƙuri Kawu! In sha Allah komai zai tafi yadda ya dac..."

    "Wallahi! Ko kai ne autan maza Zaituna ta gama zama gidanka! Ba kuka da ruwan hawaye ba, ko na jini za ka yi ka daɗe ba ka yi ba. Munafukin banza mutumin kawai!"

    Zantukan Umma kenan cikin ɗaga murya, da sauri muka fito ɗakin saboda ba na so tana tayar da jijiyoyinta a kan Mukhtar. 
      Kawu Sale ya shige ɗakinsa ni da Inna Kulu muka nufi ƙofar gidan. 
'Kayan haushi!' 
Zancen da yi kenan a zuciyata tare da guntun tsaki. Saboda ganin Mukhtar durƙushe ƙasa gaban Umma yana kuka har da majina. 
      Hannuwansa ya haɗa yana faman magiya tare da roƙon ta a kan ta janye furucin da ta yi, wanda ta shata mini layin komawa gidansa har abada.
     Baban Taufiƙ da ke tsaye rungume da hannuwansa a ƙirji, shiru kawai ya yi kansa a duƙe ban ji ya ce komai ba. Har sai da ya ɗago kai ya gan ni sannan ya ce da ni,
     "Don Allah ki bai wa Umma haƙuri. In sha Allah ba za a sake samun matsala ba."
     
    Kallon banza na yi masa sannan na ce da Umma, 
      "Koma gida abin ki ki bar ni da su."
    
     A fusace ta ce, "Ba zan bar ki da su ba! Wuce mu je ciki! Kuma daga yau kada na sake ganin ƙafarka a ƙofar gidan nan, matuƙar ba takardar sakinta za ka kawo mini ba!"
     Tana ƙare faɗar hakan Inna Kulu ta ja ta suka yi ciki tana faɗin,

 "Ke ma ki shigo ciki!" 

Ko kallon su ban sake yi ba, muka shige muka bar su a ƙofar gidan tamkar ruwa ya ci su. A cikin gidan ma Inna Kulu ta daɗe tana tausar Umma sannan ta daina faɗan da take yi. Ta janyo Umma Salma da Iman da ke ta kuka ta fara rarrashin su. Haidar kam tagumi kawai ya yi hannu bibbiyu, ba tare da ya yi kuka ko ya tashi daga inda na bar shi ba.






Ni dai Umma ki yi haƙuri 😒




Manage plss!





D. AUTA CE✍🏼


*ABOKIN AIKINA*


*@HADIZA D. AUTA*


*SADAUKARWA: DAUGHTER ANUP*


*TALATIN DA TARA.*

          Daren ranar haka muka kwana cikin tunanin makomar aurena da Mukhtar. Tun da safe Umma ta ce za ta je gidan ta ɗauko mana kayanmu. Na ce ta bari na nemo Sajida ta ɗauko mana duk abin da muke so.
     Ba don ta so ba, na kira Sajida tare da yi mata bayanin abin da nake so ta yi mini.

 "Aunty ke kina ina?"

      Tambayar da ta yi mini kenan cikin sanyin murya. Ina 'yar dariya na yi mata bayanin duk abin da ya faru. "Innalillahi wa inna ilaihirraji'un! Lalle wannan lamari ya wuce tunanina. Ni kam wallahi ba da ni ba gaɗa a hurumi, don ba zan iya dambe da aljanu ba." 
 
     "Kwantar da hankalinki, babu abin da zai faru sai alheri."

      "Haka ne Aunty! Amma maganin a yi kada a fara, tun yanzu ake shawara ba sai abu ya lalace ba a dawo faɗin da an sani."

     "Yanzu dai ki je gidan, zan bai wa Najib makullan gidan da na ɗakina ya kai miki."

     "To Aunty bari na je!"

Daga haka na kashe wayar ina kallon Haidar da ke faɗin, "Ni dai Mama da ma mun bar zuwa makarantar yau! Ni wallahi na ma gaji da zuwan ta"

     "Ai kuwa ba ni auren da kai tun da ba ka son zuwa makaranta." Inna Kulu ta faɗa a lokacin da take shigowa ɗakin Ummar. Kwanon ɗimamen tuwon jiya ta ajiye mini nawa daban na su Ummu Salma daban.

     "To ai kullum sai na je! Ki tambayi Mama. Yanzu kuma na gaji gaskiya! Koyaushe makaranta-makaranta dai. Jiya na je, gobe na je, jibi ma na je, don Allah Mama yau ki ce ban zuwa."

 Godiya na yi wa Inna Kulu ina dariyar Haidar, saboda yadda yake lissafin! jiya ya je gobe ya je, yana lanƙwasa yatsun shi kamar mai lissafin wasu manyan kuɗi.

"To ai ba a gajiya da karatu!" Cewar Inna Kulu tana ƙoƙarin ficewa daga ɗakin. Ya ba ta amsa da cewa,

      "Ni dai na gaji gaskiya!"

     Wayata na cire daga caji na kira Najib, na ce ya zo ya karɓi key ya kai wa Sajida can gidan. Sannan na ajiye wayar na ja tuwona ina ci tare da Haidar. Su Ummu Salma suna cin nasu muna bitar azkar ɗin safiya da ake yi a tashar Tauraruwa. Umma ta shigo ɗauke da taliyar da ta dafa muna a tire.
      Sannu da ƙoƙari na yi mata sannan na ce, "Dama ba ki wahalar da kanki dafuwar ba. Saboda tuwon nan ma zai ishe mu ni da su."
      "Wahala rashi! Ni kuma ban gan ta a nan ba! Ku dai ci ku ƙoshi kawai!"
        Sai da ta zauna tana rage volume ɗin tv'n sannan ta ce, "Yaran nan kamar ba za su je makaranta yau ba. Har yaushe aka ɗauko kayan? Yaushe suka shirya suka tafi?"

     "Sai a tara gobe, duk da ba haka aka so ba."

     Zancen da na yi kenan wanda ya sa Haidar ihun jin daɗi, har da 'yar rawarsa yana yi wa su Ummu Salma gwalo. Saboda yadda ya ga sun haɗe fuska alamun ba haka suka so ba. Najib ya kira ni ga shi ya zo, na miƙa wa Haidar makullan ya kai masa. Bayan tafiyar shi na ƙara kiran Sajida ta ce da ni ta kusa kai gidan. Saboda ita tana Gwiwa Low-cost, mu kuma muna Runjin Sambo.
      Bayan mun gama cin abincin na yi wa Iman da Haidar wanka, ni ma na yi wankan sannan Umma Salma ta shiga. Ina tsaka da shafa mai Sajida ta kira ni, tana sanar da ni Mukhtar ya hana ta ɗauko kayan. Raina a ɓace na ce da ita ta jira ni zan zo da kaina tun da abin nashi babu arziƙi. 
      Umma ta ce "Lafiya?" Na sanar da ita abin da Sajida ta faɗa mini. Fuskarta a haɗe ta ce da ni na yi zamana ita za ta je da kanta.
 "Jiyan ma mantawa na yi da ɗaukar komai shi ya sa muka fito ba ki ɗauko kayanku ba." 
      Tana ƙare maganar ta ja hijabinta ta fice, Allah ya tsare na ce da ita sannan na sauke ajiyar zuciya cike da jin haushin Mukhtar da tsanarsa a cikin raina.

 Ban san ya aka yi ba misalin ƙarfe goma sai ga Umma da Sajida ɗauke da kayanmu niƙi-niƙi. Da fara'a na tarbe su na karɓi kayan ina yi musu sannu muka shige ɗakin Umma. 
      Sajida ta zauna tana faɗin, "Wash! Allah!" Yar dariya na yi mata ina buɗe jakunkunan kayanmu na ce, 
"Sannu da ƙoƙari, ai kun sha aiki."
      "In da ma a ce aikin ne da sauƙi. Don ba ki ga irin tataɓurzar da aka sha tsakanin Umma da Baba Mukhtar ba. Shegiyar matarsa sai leƙe take yi kai ya sha bandeji tana gulma. Ai ni yau na san na kaɗe har hanjina, saboda Baba Mukhtar har dukana ya so yi mijin maƙociyarki ne ya hana shi."

      "Duka kuma!?"
 
Tambayar da na yi mata kenan tare da samun wurin zama na zauna, saboda labarin da take ba ni mai cike da kayan haushi da takaici. 

    "Duka tabbas! Ba ki ga yadda muka zagaye gidan da shi ba yana ƙoƙarin kamo ni ina gudu har ya faɗi. Lokacin da ya tashi ne na fice gidan don na san zai iya halaka ni. Babu zato na ji na faɗa jikin mutum ya yi hanzarin riƙe ni Allah ya tsare ban faɗi ba. Sai ga Baba Mukhtar ɗin da gudu, ice a hannunsa yana neman kwaɗa mini na laɓe a bayan mutumin."

      "Cabɗijam! Ki ce artabu kawai kuka sha ke da shi."
       
     Dariya ta fashe da ita sannan ta ce, 
         "Ai ba ni kaɗai ba har da Umma, don ita ma ba ki ga abin da ta yi masa ba. Sai da mutanen unguwar suka taru ana ba ta haƙuri. Sannan na ja ta muka shiga gidan muka kwaso kayan, munafukar matarsa sai kallon mu take yi, tana harare-harare. Na so ta tanka na rage haushinta da nake ji, don wallahi sai na darji bakinta babu ruwana da ciwon da ke kanta baƙar makira."
      "Gara dai da ba ki taɓa ta ba, ko yanzu ba ki san wane irin mataki zai ɗauka a kanki ba balle kin taɓa masa amarya."

     Mere ta yi sannan ta ce, "Hu'ummm! Ai wallahi komai zai yi sai dai ya yi, don ba na tsoron komai tun da gaskiya nake goyon baya ba ƙarya ba. Shi ma watarana zai yi da-na-sanin abin da ya aikata musamman idan figaggiyar matarsa ta koya masa hankali."

     "Ki dai bi a sannu! Shi kawunki ne Uwa ɗaya uba ɗaya da Mahaifiyarki. Za ki rabu da ni amma shi ba za ki iya sauya shi da wani ba."
     Umma ta shigo tana 'yar dariya ta ce, "Ke ni fa na fara zargin Mukhtar bai da lafiyar ƙwaƙwalwa. Saboda yadda ya tuɓure yau a kan cewa zai sake ki amma sai an dawo masa da yaransa. Saɓanin jiya da yake kuka a kan a yi haƙuri ki koma ba zai iya rayuwa babu ke a gidan ba."
     Ƙirjina ne ya buga dam-dam! Saboda zancen a ba shi yaransa da na ji ya dake ni babu shiri. Gabana yana cigaba da faɗuwa na fara faɗin,
      "Ai wallahi ba zan iya ba shi yarana ba, ko babu Barira a gidan balle tana ciki. Saboda jiya kafin a yi rikicin da Maman Taufiƙ ta cire mata kitso, na kama ta da ƙawarta suna aikata harkar banza. Don haka wallahi komai zai faru sai dai ya faru amma ba zan ba shi yarana ba. Daman ba komai ba ne ya sa ya biyo ta wannan hanyar ba; don kawai ya san ba zan iya rabuwa da su ba. To kada Allah ya sa ya sake ni ɗin ya yi ta riƙon takardar sakin har duniya ta jingine." 
        Na ƙare maganar jikina yana rawa saboda yadda maganar ta shige ni ba kaɗan ba, kuma ta ƙona mini zuciya. 

    "Ki bar ni da shi! A wannan karon zai gano kowane gauta ja ne." 

    Zancen Umma kenan tana ficewa ɗakin, Sajida ta sauke ajiyar zuciya ta ce,
     "Na ji matuƙar haushin da na gano mijin Maman Taufiƙ ne muka yi karo da shi, ya ɓoye ni bayansa ya hana Baba Mukhtar ya sauke mini ƙaton icen da ke hannunsa. Allah ya tsare matarsa ba ta fito ba da na san ko kashe ni za ta iya yi a lokacin."

     "Ki cire wa zuciyarki tsoronta, kawai dai ki yi iya bakin ƙoƙarin ki wurin hana wa kanki shi ko don zaman lafiya."
    Abin da na faɗa mata kenan zuciyata ɗauke da damuwa, saboda gabaɗaya na rasa farincikina. Balle walwalar zuciya a kan zancen Mukhtar da na ji na karɓar yara. Don na san zai yi hakan ne kawai domin ya ƙona mini rai, ba don ya damu da su ba. Ni kuma ba zan taɓa bari tarbiyar yarana ta lalace a kan banzan shirmensa da tunanin kansa maras inganci ba.

     Haka muka yi ta bitar abin a tsakaninmu, ni, Umma, Sajida da kuma Inna Kulu. Ban samu zuwa aiki ba, haka ma yaran ba su je makaranta, saboda lokaci ya ƙure sun yi latti sosai.  Sajida tana gidan har aka yi sallar Zuhur muna tsaka da cin abinci aka kira ta a waya. Fuskarta a haɗe ta ɗaga kiran ba tare da ta yi magana ba. Babu shiri ta miƙe tsaye dafe da ƙirji  tana zaro ido waje ta ce, 

    "Aure!!!?"

Ban san me aka ce mata a cikin wayar ba ta jefar da wayar ta dunƙule tana kuka. Cikin tashin hankali na miƙe na yi kanta a ruɗe ina tambayar lafiya. Su Umma ma suka shigo ɗakin muka rufu kanta da tambayoyi, amma ba ta fasa kukan da take yi ba har da majina.
     Da ƙyar muka samu ta sassauta kukan sannan ta ce, 
      "Rayuwata ta zo ƙarshe! Tun da aka ɗaura mini aure da Aminu mijin Maman Taufiƙ! Wallahi na fi so na mutu da dai na yi wannan aure."

     "Innalillahi wa inna ilaihirraji'uun! Ita ce kalmar da na faɗa a bakina hannuna a kai ina zarya tsakiyar ɗakin."

     Umma ta fara faɗin, "Haƙuri za ku yi dukanku, saboda ba ku isa ku hana Allah aiwatar da abin da ya tsara ba. Daman can an ƙaddara akwai aure a tsakaninsu shi ya sa hakan ta kasance. Don haka ku daina jayayya da ikon Allah! Ku rungumi haƙuri dukanku ba ku san abin da Ubangiji ya kulluɓe a cikin auren ba."

     "Wallahi Umma sai dai na bi duniya ba zan zauna gidan mutumin nan ba!"

      "Subhanallah! Ki daina faɗar ire-iren waɗannan maganganun ba su da daɗin sauraro. Ki rungumi ƙaddararki wataƙila hakan alheri ne ba ki sani ba."
       Inna Kulu ta faɗa tana ƙoƙarin rarrashin ta da hannu. 
     "Babu wani alheri a cikin irin wannan auren! Tun da ban son shi, kuma ba da amincewata aka yi ba. Don haka wall..."

     Kiran wayarta da aka sake yi dukanmu muka mayar da hankalinmu a kanta. Amma ko kallon wayar ba ta yi balle ta ɗauka tana ta kuka har kiran ya tsinke. Sai da aka ƙara wani kiran sannan na yi jarumtar nufar inda wayar take na ɗauka. Ganin sunan mai kiran ya sa na gano Yaya Maimuna ce take kiran ta. 
     Cike da tsabar jin haushinta na ɗaga kiran ba tare da na ce da ita komai ba.
     "Wallahi duk inda kike ki dawo gida yanzun nan ko na tsine miki albarka. Aure kuma ko kina so ba ki so an ɗaura ke kawai ake jira ki dawo a kai ki gidan mijinki. Sai ki je ki yi auren ke ma ki daina shiga rikicin auren wasu, kina ƙoƙarin ci wa ƙanena zarafi a kan Shegiyar matarsa marar tsoron Allah! To wallahi ko ki dawo gida yanzun nan kamar yadda na faɗa ko na tsine miki albarka, sai ki bi duniya ki lalace gabaɗaya kowa ma ya huta da shegen halinki." 

     Kashe wayar kawai na yi ina Safa da Marwa a cikin ɗakin rungume da hannuna a ƙirji. Wayar na fara bubbugawa a bakina sannan na ce da Ummata, 
      "Don Allah Umma ki kai Sajida gidansu ki damƙa wa Mamarta ita hannu da hannu, gudun ta ƙi komawa gidan a ce mu ne muka ba ta ƙofar guduwa."

       "Me ya faru?"

Tambayar da Inna Kulu ta yi mini kenan a ruɗe, zama na yi a bakin gadon Umma sannan na ce da su. 
      "Yaya Maimuna tana yunƙurin tsine wa Sajida muddin ba ta koma gida yanzu ba. Don haka yana da kyau a mayar da ita gudun ta tsine mata a kan banza."
      
      "Lalle kin yi magana mai ma'ana. To bari na watsa ruwa sai mu tafi. Amma ba zan iya shiga gidan ba gudun wata matsala ta biyo bayan hakan."
      "Inna Kulu ku tafi tare don Allah! Ke ki shiga da ita har gidan ki miƙa wa Mamarta ita ki fito ko ba ki ce komai ba."

      Zancen da na yi kenan cikin sanyin jiki saboda na kai maƙurar ɓacin rai da damuwa. Ban iya cewa Sajida komai ba har Umma ta shirya. Inna Kulu ta shigo ta riƙa hannunta suka fita ɗakin, Umma ma ta fita jiki babu kuzari na bi su baya har ƙofar gida. I ta faman share hawayen da ke ta fareti a kan dandamalin fuskata.

    Babu zato sai ga wata adaidaitasahu ta tsaya a ƙofar gidan, Maman Taufiƙ na ga ta fito tana biyan mai adaidaitasahun kuɗinsa. Sajida ta ƙwace daga riƙon da Inna Kulu ta yi mata ta zunduma ihu iya ƙarfinta. 
     Ni ma ganin ta a lokacin da ban yi tsammani ba; sai da na ji cikina ya murɗa hanjina sun dunƙule wuri ɗaya. Da gudu na koma gidan na faɗa bayi, zawo na dinga kwararawa tamkar zallar ruwa ne kawai nake fesowa shaaaa!






     Wayyo🥲








D. AUTA CE✍🏼


*ABOKIN AIKINA*


*@HADIZA D. AUTA*


*SADAUKARWA: DAUGHTER ANUP*


*Commenters, masu share, 'yan Allah ya ƙara basira, da masu danno mini sticker's da emoji idan na yi posting, har ma da wanda karatu ne kawai na shi ba ya motsi. Dukanku Allah ya saka muku da mafificin alherinsa. Ina son ku gabaɗaya, kuma ina yi maku fatar rayuwa mai kyau tare da gamawa duniya lafiya.👏🏻*


*LAMBA ARBA'IN.*

        Jiki babu kuzari na fito daga bayin, ƙirjina yana dakan luguden uku-uku. Takalman Maman Taufiƙ na hango a ƙofar ɗakin Umma, hakan ya tabbatar mini da har ta shigo gidan, su sun tafi.
        Haka kawai na tsinci zuciyata wasai, fargabar da nake ciki fiye da rabinta ya zumame. Daidaita natsuwata na yi sannan na shiga ɗakin, fuskata ɗauke da murmushin yaƙe na fara faɗin,
     "Sannu matar mijinta, shi ne za a zo mini babu sanarwa?" Na ƙare maganar tare da zama kusa da ita  ina ƙoƙarin karantar yanayinta.
     "Ke ce da sannu Maman Haidar! Saboda ke kika yi abin da dole sai na zo ba tare da kin sani ba. Kin ci sa'a ma da ban yi tsuntsuwa na dire saman kanki ba, domin na yi ta tsige miki gashin kai har sai kin gama tattara komatsanki mun juya tare."
    Ajiyar zuciya na sauke mai ƙarfi, tamkar an sauke mini ƙaton dutsen da ya danne mini zuciya. Saboda lafuzzanta sun tabbatar mini har yanzu ba ta san wainar da ake toyawa ba. 
     
     "Idan ma kin tsige gashin, ke za ki tsinto shi ki dawo ki mayar da shi inda kika gan shi." 

    Na ƙare maganar ina 'yar dariya, Maman Taufiƙ ta gyara zamanta sannan ta ce da ni,
      "Wallahi ko kaɗan ban ji daɗin abin da ya faru ba, abin haushin ma ban san da rikicin ba kwata-kwata sai yau. Saboda kwana biyun nan duka wani masifaffen bacci nake yi tamkar wata 'yar maye. Sai yau da safe Amini yake sanar da ni wai ba kya gidan, ashe shi ma sun zo biko gidan nan Umma ta hana su ke? To ni dai don Allah kada ki ba ni kunya. Don na gama cika baki a kan zan shawo kanki, na rarrashi Umma ta yi haƙuri ki dawo gidanki ko don yaranki."

     "To ki furzar da abin da kika cika bakin da shi Hajiyata! Don ni kam sai dai idan gawata za a sake kaiwa gidan Mukhtar. Daman can zaman Umma nake yi a gidan ba don ina so ba, yanzu kuma tun da ita ma ta gaji ni me zai sa na koma?"
    Na ƙare maganar idona a kanta, tagumi ta cire sannan ta yi shiru na ɗan lokaci. Mintuna a tsakani ta ce,
     "Yanzu ke za ki iya barin yaranki a hannun waccan ballagazar yarinyar, wadda ko ita yana da kyau a ce har yanzu ba a gama ba ta tarbiyar ba. Yanzu haka da zan fito na gan ta ƙofar gidan tana siyen kifin Malami Sabo, ga wani garjejen ƙato sai hira suke yi tana cin kifin a gabansa tamkar wani ɗan gidansu."

      "Tsuntsun da ya ja ruwa, shi ruwa kan doka! Saboda ban ci nanin ba, nanin ba za ta faɗo mini ba. Shi ya ji zai iya da ita ne shi ya sa ya nemi a kassara ni saboda ita. Wai har ni za a turowa 'yan daba da wasu karuwai har gida su dake ni, sannan shi don bai san darajar kansa da ta wanda yake tare da shi ba; ya ba da ƙofar su halaka ni don bai da asara. To na bar masa gidan kenan har abada, daman can kamar a saman ƙaya nake zaune ba don ina so ba."
      "Ban gane ba! Kina nufin wasu suka zo har gidan za su dake ki? To me kika yi musu?" Murmushi kawai na yi mai sauti ina kallon ƙwayar idonta, sannan na miƙe na fice ɗakin tare da faɗin,
     "Ni dai jira ni na kawo miki ruwa ki sha, tun da kin saka mu zuba daga zuwan ki tamkar 'ya'yan kanya."
       "Dole ne ai! Don haka ki je ki dawo a yi ta ƙare, haƙuri za ki yi ki koma tun da kin saba da halinsa."
     Ruwa na dire mata da kunun ayar da Umma take sayarwa, sannan na zauna ƙasa ina faɗin,
      "Allah dai ya ƙara shiga tsakanin nagari da mugu. Amma ni kam na kammala rayuwa gidan Mukhtar daga wannan karon."
     Sakato ta yi tana kallon na ba tare da ta ce komai ba, sannan ta miƙe tana gyara zaman jakarta ta ce,
      "To ni zan tafi! Tun da zuwan nawa bai da wani amfani. Idan Umma ta zo ki ce zan dawo ganin ta wani lokaci, amma ke ko a hanya na gan ki ba zan nuna na san ki ba."

     Na miƙe ina faɗin, "Ya za ki tafi ba ki sha ruwan ba?"
     "Ba zan sha ba!"
Tana ƙare faɗar hakan ta fice tana saka takalminta. Har ta yi gaba ta juyo tana faɗin, "Ke! Ji na manta ban tambaye ki ba! Na ga 'yar gidanki a hargitse da na zo, me ya same ta?"

     "Aljanunta ne suka tashi. Shi ya sa su Umma za su kai ta gida." Na ƙare maganar ina murmushi.

     "Allah Sarki! Ki ce ita ma tana ciwo irin nawa? Kai! Allah ya yaye wa mutane wannan lalura."
      Cikin sanyin murya ta yi magana, na amsa da "Amin" cikin sanyin jiki da na muryar duka. Saboda jikina ya ba ni ba ta san komai da ke faruwa ba, tun daga tsige kitson Barira har wannan badaƙalar auren da Amininta ya rikito. Haka kawai na ji tausayinta ya kama ni, saboda sanin duk ranar da ta ji wannan labarin; zuciyarta ma za ta iya bugawa ta mutu faraɗ ɗaya, balle tashin hankali ko damuwar da za ta shiga sai ta fi gaban kwatance.

    Ganin damuwa a kan fuskata ya sa ta yi gaba tana faɗin, "Ke ai yanzu na samu lafiya sosai saɓanin baya da nake ɓacewa ba a san inda nake ba tsawon kwanaki. Ni ma ba na sanin ina nake sai dai na tsinci kaina a tsakiyar daji babu komai da kowa sai kukan tsuntsaye. Amma tun da muka bar gidan da muka fara zama farkon aurenmu, shi kenan matsalar ta kau sai dai lokaci bayan lokaci hargitsattssun kayan suna motsawa."

     "To Allah Ubangiji ya yaye muku gabaɗaya, ya kawo sauƙi da salama a cikin lamarin da rayuwarku gabaɗaya."

     "Amin Ya Allah! Ke ma ya sa ki dawo mana, don ba za mu yarda ki suɓuce ba!"

     Ta ƙare maganar da yar dariya bayan ta juyo muna kallon juna, saɓanin tafiyar da take yi tana gaba ina bayanta har ƙofar gida. Taka mata na yi har muka je bakin titi, sai ga su Umma cikin adaidaitasahu har sun yi gaba na ga mai adaidaitar ya ja ya tsaya. Su Umma suka fito Inna Kulu tana cewa da ni, 

"Ta zo ya kai ta mu sai mu ƙarasa kawai!"

     Tare muka nufi wurin tana faɗin, "Sai wani murna kike yi kin zo gida kina 'yanmatanci. Ni na manta ma ban ga su Ummu Salma a gidan ba, ina suka je?"

    "Suna gidan ƙanwata ɗiyar Kawuna."

    "Allah Sarki ki gaishe mini da su, yawwa ma har na tuna.."

   Ta fito da wata leda a jakarta ta miƙa mini tana faɗin, "Ki ba su don Allah! Kwanan nan gabaɗaya a hargitse nake ji na wallahi."
     Karɓa na yi su Umma suka taya ni godiya ta shige tana cewa Umma, "Zan miki tafiyarki ke kaɗai Umma. Amma don Allah a sassauta kada abin ya yi tsauri ta dawo mana haka nan, don har mun fara kewar ta."

Murmushi Umma ta yi tana faɗin, 
"Allah ya zaɓa abin da ya fi alheri."
    Daga haka suka tafi muna ɗaga mata hannu har suka yi mana nisa, sannan muka juya tare da su muna hira.

 "Gaskiyar magana mijin yarinyar can bai yi mata adalci ba! Don alamunta ya nuna ba ta san komai ba. Saboda yadda ta nuna alhininta a fili a lokacin da ta zo, dangane da yadda ta ga Sajida ta ruɗe sosai tana zunduma ihu. Haƙuri ta dinga ba ta bayan ta gama tambayar mu me aka yi mata. Har muka bar ƙofar gidan tana ta jera mata sannu da Allah ya ba ta lafiya." 

   Zancen Inna Kulu kenan a lokacin da muke ƙoƙarin shigewa gida,  
"Ai duk mutumin da kika gani tare da Mukhtar, ba mutumin arziƙi ba ne. Shi ya sa idonsa ba su yi mini girma ba, balle na fasa sauke musu duk abin da ya fito bakina. Ai dai duniya ce, su yi duk abin da suke so Allah yana jiran su a madakata, domin su karɓi sakamakon abin da duk suka shuka."

    Ummu ta ƙare maganar tare da cire hijabinta ta ja buta zuwa bayi. Na ja kujera 'yar tsugunno na zauna, sannan na sauke ajiyar zuciya na ce,
     "Ni na rasa da me zan fassara wannan lamari. Duk da idan ɓera da sata daddawa ma da warinta. Maman Taufiƙ tana da zafin kishi sosai har na fitar hankali. Shi kuma mijinta yana da idon kallon mata ya ji sun burge shi. Idan ya yi laifi a kan ɓoye matan da ya yi, to laifinsa kaɗan ne nata ya fi yawa. Saboda ya fi kowa sanin zafin kishinta, yana gudun ya faɗa mata hakan ya janyo masa tashin hankali. Amma kuma da ya faɗa mata gaskiya sai ta fi jin sauƙin abin, da a ce ta ji labari kwatsam! Bayan aikin gama ya gama."

      "Maza! Maza!"

Zancen Inna Kulu kenan tare da jinjina kai, kafin maganar Kawu Sale ta shigo dodon kunnuwanmu tun kafin mu gan shi. 

 "Me mazan suka yi?"

Murmushi na yi mai sauti ban ce komai ba, Inna Kulu ce ta yi ƙarfin halin faɗin,
     "Tsohuwar bazawararka aka ce yaushe za ta kawo sadaki a ɗaura muku aure?"
      "Ki rantse da Allah gaske kike yin maganar nan, ni kuma cikin satin nan a ɗaura na dinga zuwa gidanta dangana sanda."
      "Idan da rabon sandar ta jingine ka gidan da ƙarar kwana ai sai ka je ga fili ga mai doki."

   Zancen Inna Kulu kenan da Kawu Sale, tsam na miƙe ina dariya na yi ɗakin Umma. Kwance na yi, bayan na mayar da ruwa da kunun ayar da Maman Taufiƙ ta ƙi sha a furji. Ina ta juya abubuwan da suka faru a kwanyata bi-da-bi, har tunanin Sajida ya faɗo mini a rai zumbur na miƙe na fito waje. Inna Kulu na iske ɗakinta ina faɗin,
    
     "Wai Inna ya aka yi da kuka kai Sajida gidansu?"

Inna Kulu fuskata babu yabo babu fallasa ta ce da ni,
     "Lafiya lau na fito gidan, duk da Uwarta ta yi ta jifa ta da maganganu marasa daɗi. Bayan na ce ga 'yarta nan mun kawo mata kada ta tsine mata. Tun kafin na gama fitowa na ji tana faɗin, yau gidan mijinta za ta kwana ta gama kwana gidan har abada."

    "Allah Sarki Sajida!"

Haka kawai na tsinci hawaye suna kwaranya a kan fuskata, saboda duk abin da aka yi mata sanadina ne. Domin a huce haushi na da ake ji a kanta, saboda ta nuna tana ƙaunata a fili fiye da kawunta.

   "Akwai Allah! Kuma in Sha Allah sai abin ya zame mata alheri."

    Zancen Umma kenan, wadda ke riƙe da labulen ƙofar ɗakin Inna Kulu. Kafin ta ɗora da faɗin, "Ke kuma Kulu idan ba ki daina zancen Bazawarar Sale ba, sai 'yan Amin su amsa ya tare can tun da ba za ki bar shi ya huta da magana ɗaya ba."

     "Ai da yana iyawa da ya yi tun lokacin da take rawar ƙafa kansa. Idan kuma kun isa a yi auren cikin satin nan kamar yadda ya ce."
     "To ba mu so, kuma Allah ya raba mu. Ke ma da kike zancen saboda kishi Allah ya ba ki ikon dainawa. Mace saboda jin daɗin aure da tsufanki ma sai kin yi kishin Salenmu! Amma duk kika motsa sai kin cika baki kamar gaske."

     "Kyale ta Habi! So take yi na ɓanɓaro sabuwar budurwa ɗanya shataf!"

    Zancen Kawu Sale ya sa na yi murmushi ban shirya ba, haka suka dinga wasar su kamar yadda suka saba na baro ɗakin. Zuciyata cike da tunanin. 'Kenan dai mace komai tsufanta idan ta ji daɗin aure tana kishin mijinta. Balle masu rangwamen shekaru waɗanda suke tsaka da cin ganiyar lokacinsu.'

****

     Daren ranar bacci rabi da rabi na yi, saboda na yi ta kiran wayar Sajida domin na ji halin da take ciki. Amma duk kiran da na yi babu wanda na samu wayar kashe ake cewa.
      Jiki babu kuzari muka shirya ni da yara kamar koyaushe, Najib ya kwashe mu ya ajiye su ni ma ya kai ni wurin aiki. 
      Ban yi wani aikin kirki ba ranar saboda ban da natsuwar zuciya, a ƙarshe ma tattara komai na yi na tura drowar teburina. Saboda ƙwaƙwalwata ta toshe ba na gane komai face tunanin Sajida da Maman Taufiƙ. Sai tashin hankalin da zai biyo baya ita da Amininta idan ta ji labarin yankan bayan da ya yi mata.
 
     Misalin ƙarfe ɗaya da rabi kiran Najib ya shigo wayata, duk da ban san me zai faɗa mini ba; sai da gabana ya buga da ƙarfi kafin na ɗaga wayar numfashina yana sama da ƙasa.
       "Maman Haidar, na je makaranta tun ƙarfe ɗaya ban ga su Ummu Salma ba, gabana aka watse makarantar amma ban ga sun fito ba. Har maigadin na tambaya ya ce da ni wani ya zo ya ɗauke su da mashin. Na je Bafarawa Estate a can ma an ce ba su koma gidan ba."
       Dam-dam-dum! Shi ne sautin luguden da zuciyata ke yi tamkar ta fasa ƙirjina ta fito. Ban san lokacin da na zabura na miƙe tsaye ina ta maimaita faɗin, "Innalillahi wa inna ilaihirraji'un!" A bakina ba.
     
     Waya a kunnena na fito da gudu na yi bakin gate, ban ma san ya katse kiran ba har sai da wani kiran ya sake shigowa. 
       "Innalillahi wa inna ilaihirraji'un! Wayyo Aunty wuta! Ki zo ki cece ni wuta! La'i'laha illallah Muhammadur Rasulullah! Shi kenan!!!! Ɗakin duka ya kama da wu..."

     Muryar Sajida kenan da na ji a cikin waya, da wata sabuwar lambar da ban san ta ba, kafin kiran ya katse. A gigice, na durfafi saman titi idona a rufe ba na gane komai da kowa a lokacin, balle na hango abin da ke gabana. Odar mota na ji 'Ɗiiiiiiiiiiiiiii!' A cikin kunnuwana tamkar za a fasa mini dodon kunne. Cak! Na tsaya sai jin na yi an ture ni na faɗi gefen titin, daga ni har wayar mun ɗaiɗaya. Yunƙurin miƙewa na fara yi na ji an riƙa ni da hannu biyu na tashi, sai sannu ake jera mini ba tare da na shaida muryoyin mutanen ba sai ta mutum ɗaya waton MD.
     Ruɗu da firgici ya sa na zama tamkar wata zararriya ina faɗin, "Yarana sun ɓata! Wuta ta canye Sajida! Don Allah ku taimaka mini zan mutu idan na rasa yarana da Sajida. Zan mutu idan na rasa yarana su ne rayuwata."

     Hannuna na ji an ja ban tirje ba na bi, aka saka ni cikin mota sannan aka rufe. Fisgar motar aka yi da ƙarfi idona a rufe ina ta zunduma ihu, tare da kiran sunan Sajida da yarana tamkar wata mahaukaciya sabon kamu.






Hmmmmm! Laifin daɗi ƙarewa. A nan muka kawo ƙarshen ABOKIN AIKINA littafi na ɗaya. Idan Allah ya ara mana lokaci an yi sallah lafiya za mu ɗora da wani sabon salon kafcen. A cikin littafi na biyu mai tsayawa a zuciya. Ubangiji ya albarkace mu da ganin wannan wata mai tarin falala waton Ramadan.



    Fatan alheri gare ku gabaɗaya luv u all😘 




     D. AUTA CE✍🏼


Post a Comment

0 Comments