TOP HAUSA NOVELS atOptions = { 'key' : '20e08520dad54dbf6d9e963271

Makauniyar soyayyah page 45-46

 [4/20, 20:29] Mrs Mansoor: *MAKAUNIYAR SOYAYYA*💝💖💞



🤦🏽‍♀🤦🏽‍♀🤦🏽‍♀🤦🏽‍♀🤦🏽‍♀🤦🏽‍♀🤦🏽‍♀🤦🏽‍♀🤦🏽‍♀



*STORY & WRITTEN*


                *BY*



*MARYAM AHMAD PAKI*



*🌈KAINUWA WRITERS ASSOCIATION*🤝🏽





*Wannan Shafin na ba ku shi ne kyauta*

*Rabi’atu sk msh* (llileee)

(Marubuciyar Haramtaccen zama)




_Ummerherny Nerserllerh_


(Marubuciyar Da Aurena A Kanki)


_Ina muku fatan alkhairi a duk inda kuke, Allah ya bar zumunci_.




 _BA ABIN DA ZANCE MUKU SAI GODIYA_ 



 *Hak’ik’a ina jin dad’in yadda kuke k’ok’arin ba da amsar kun a question of the day, ba da amsar ko ba daidai ba ne zai sa mutum ya k’aru, saboda shirin tambayoyin musulunci ne, ta hakan nima nake k’aruwa saboda nobody is perfect, ba wanda ya wuce kuskure*


 *Da fatan za a ci gaba da min gyara a cikin shirin, dan har yau nima d’aliba ce.* 


*Xarah Auwal*(Ass Queen)


*Maman Walida*


*Sakina  iliyas* (Maman Khalil)


 *Ku ne ku ka ba da amsar daidai na question of the day, A matan manzon Allah (s.a.w) wacce ta lurar da manzon Allah (s.a.w) game da wata dabara da zai jawo hankalin sahabban sa a ranar hudaibiyyah, kuma dabarar taci nasara sosai itace Ummu Salma, cikakken sunan ta shine Ummu Salma Hindu ‘yar (bn) Umayyata.* 



*TUNATARWA*


 _* Ka/ ki zamo mai hikima, amma ka/ki yi amfani da hikimar ka/ki ba tare da ka/ki ‘batar da wasu ba_.


_*Ka/ki zamo mai adalci, amma kar ka/ki ce sai ka/ki iya wa kowa_


_*Ka/ki zamo mai neman na kai, amma ka da ya kai ka/ki ga neman haram._ 


 


 

45&46


Ko da ya isa Abuja, basket d’in da Ummu ta bashi ya ajiye a falo, bathroom ya shiga ya watsa ruwa ya fito.


Canza shigar shi yayi zuwa k’ananun kaya.


Fridge ya wuce ya d’auki favourite d’in shi wato exotic da glass cup d’in da ke ajiye a saman fridge d’in.


1-sitter ya nemi guri ya zauna ya d’akko dambun naman da Ummu ta zuba mishi ya d’auka ya fara ci, a lokaci d’aya yana kora wa da wannan ruwan exotic din.


Wayar shi da ke gefen shi ya d’auka yayi dialling d’in numban Mus’ab, bugu d’aya, ana biyu Mus’ab ya d’auka.


"Asslamu alaikum Bregadier Faruk na Teemah" abin da Mus’ab ya fara fad’a kenan.


Murmushi yayi don yasan Mus’ab so yake yi ya zolaye shi, amsa wa yayi "Wa’alaikumus salam, kana gida ne?".


"ina gida, ba dai har ka dawo ba?".


"eh na dawo, ina nan zuwa".


"Ok sai kazo".


Remote ya d’akko ya canza channel d’in zuwa tashar Aljazeera yana kallon labarai.


Bayan ya gama abin da yake yi ne ya kasha tv d’in, ya d’auki wannan d’an basket d’in ya nufi block d’in Mus’ab.


Sallama yayi ya nemi d’aya daga cikin kujerun ya zauna, gaba d’ayan su suna kallon wani hausa film mai suna *HAKK’IN RAI* wanda ake haskowa a tashar Arewa Tv.


Maryam ce ta gaishe shi tana tambayar shi mutanen gida.


Amsa mata yayi da duk suna lafiya.


Nana ce cikin zazzak’ar muryar ta gaishe da yaya Faruk.


D’ago kai yayi ya kalle ta wanda sai a lokacin ya lura da ita.


Da fara’a a fuskar shi ya amsa mata yana cewa "ashe ba ki koma school ba?".


"ban koma ba, sai next week".


"Ok" ya amsa a gajarce.


Yamutsa fuska yayi ya maida kallo shi ga Mus’ab yace "wai me kuke fahimta ne a hausa film, ni ban ga abin kallo ba, saboda a tunani na basa film mai ma’ana da wanda za a k’aru, sannan ba yin film akan al’adar su".


Mus’ab ne ya cewa "Ni ma dan ba inda za ni ne, shi yasa na zauna ina kalla, kuma madam na so, dole in biye mata mu kalla".


Maryam ce ta kar’bi zancen da cewa 


"Mu dai ba za mu k’i yaren mu da al’adar mu ba duk lalacewar su, kuma Hausa film d’in da kuke Magana, ai akwai masu ma’ana da kuma wanda suke nuni da al’adar su, kamar wannan film d’in da kuke gani da aka sa a Tv, ya ta’allak’a ne akan ku masu kaki, duk da ba duka aka taru aka zama d’aya ba, amma shi wannan d’an sandan saboda kwad’ayin kud’in da zai samu yasa ya d’auki wanda bai da laifi ya kai aka harbe shi, ya saki wanda yake da laifi saboda ya bashi kud’i, k’arshe kud’in shi bai mai amfani ba saboda rai da yakai aka kashe, kaga kenan *Hakk’in Rai* ba zai bar mutum ya samu kwanciyar hankali ba".


Mus’ab ne ya kalle shi da alamar tsokana yace "mutumin ai ban zaci za ka dawo da wuri ba, ina sha ai Fatima za ta rik’e ka".


Murmushi yayi yace "kaima kasan ba yadda zanyi ne na dawo, amma ni ban k’i in zauna gurin Teemah na ba".


Maryam ce ta sa bakin ta a zancen nasu tace "wai Bregadier, kai nake jin kana maganar budurwa? Kai da kake cewa ‘yan mata ba sa gaban ka, amma ko wacece Fatiman nan, ta burge ni da ta kama zuciyar soja" ta k’arasa zancen tana dariya.


Bai ce mata komai ba illa murmushi da yayi.


Basket d’in da ke d’auke da snacks d’in ya ajiye a gaban Maryam yace


 "Madam in ba damuwa plsss ga Samosa nan da spring roll za ki taimaka ki soya min, Teemah nasa ta min a d’anyen shi, may be ma ya lalalce saboda naji tace yana da saurin lalacewa".


Mus’ab cikin tsokana yace "ai ko ya lalace sai an soya kaci shi, tun daga hanun masoyiyar ka ya fito, ba zai maka komai ba illa k’ara maka son ta da zai yi".


"kan ka ake ji, naga alamar ka maida ni wani kakan ka" yaya Faruk ya fad’a.


Maryam ce ta bud’e food flask d’in taga bai yi komai ba, kallan Nana tayi tace "Nana d’auka kije kitchen ki soya mai, sai ki zubo mishi a plate yaci a nan".


"To Anty Maryam" ta mik’e ta d’auki basket d’in ta nufi kitchen.


Sai a lokacin ya d’aga kai ya k’ara kallon Nana, yana mamakin shirun ta yayi yawa, dan tun da aka fara maganar ba ta sa bakin ta ba, illah wayar ta da take pressing, bin ta yayi da kallo san da ta nufi kitchen, yana yabawa da natsuwar ta.


Ko da ta shiga kitchen d’in, mai ta d’aura akan wuta, sai da yayi zafi sannan ta fara soya wa.


Cikin ‘yan mintuna ta gama soyawa ta zuba a glass plate, ta had’o da ginger drink d’in da ke cikin fridge wanda sai k’anshin citta da lemun tsami da yake tashi.


Tana zuwa ta ajiye a kusa dashi tace "yaya Faruk gashi".


Da murmushi a fuskar shi yace "sannu da aiki khadijah, an sa ki aiki ko?"


Fad’ad’a murmushin ta tayi tace "ba wani aiki yaya Faruk".


D’aukar wayar ta tayi dake kujeran da ta tashi ta fara tafiya, da alama d’aki za ta tafi.


Yaya Faruk ne ya kira sunan ta


 "Khadija".


Juyowa tayi ta kalle shi da oily eyes d’inta ta amsa "Na’am yaya Faruk".


"ya za ki tafi ba ki ci ba".


Rasa me za tace mai tayi, dan haka tace "Samosa da spring roll bai cika damu na ba, na k’oshi ne yaya".


Kallon ta yayi kawai yace "Ok, za ki iya tafiya".


Kamar jira take yi, ta nufi d’aki ba tare da ta k’ara juyowa ba.


Mus’ab ne yace "ko da mu ba a mana tayi ba, bazan yi zuciya ba, ci zan yi in ji ko gimbiyar hannun ta na da zak’i".


Girgiza kai kawai yaya Faruk yayi saboda yasan in ya biye ma Mus’ab sai ya sa shi Magana don ya fi shi Magana.


Yaya Faruk ne ya kalli Maryam yace "bismillah madam, zo ki d’ibi yanda zai ishe ki".


Cikin wasa tace "da ba dan na k’oshi ba, da sai na ci naji, amma dai yanzu a min hak’uri soja, snacks d’in nan ba zai shiga ba".


Shiru ya mata saboda yasan Maryam da tsokana kamar mijin ta, in ya biye musu sai sun sa shi Magana.


Mus’ab ne ya d’auki d’aya yasa a bakin shi, lumshe ido yayi ya bud’e ya kalli Maryam da ta mai da hankalin ta ga tv.


"Maryam! Mus’ab ya kira ta.


Kallon shi tayi tace "ya aka yi ne Nurul k’albi".


Cikin tsokana yace "gaskiya kar ayi ba ke, bud’e bakin ki in sa miki ki ji, snacks sai kace a bakery, kice dole mutumin ya rud’e akan ta".


Dariya tayi tace "tun da naji ka yaba, to lallai Fatima ta ciri tuta".


Bud’e baki tayi, Mus’ab ya d’auki samosa ya sa mata a baki.


Taunawa ta fara yi a hankali tace "wow! Delicious, amma dai Faruk catering Fatima take karanta ko?".


Ta’be baki yayi yace "Santi take karanta".


Gaba d’ayan su suka sa dariya, saboda sun san rama tsokanar da suke mai yayi.


Mik’e wa yayi yace "Ni kin ga tafiya ta, kai da matar ka kun tasa ni a gaba sai tsokana ta kuke yi akan Teemah, bari in na koma Kaduna sai na fad’a mata abin da kuke min".


"Tuba muke yi na Teemah" Mus’ab ya fad’a yana dariya.


Tafiya ya fara yi yana cewa "Maryam sai anjima".


"To sai anjima Faruk".


Mus’ab ne ya mik’e dan ya taka mai.


Nana Khadija tun da ta shiga d’aki, ta fad’a kan gado, ta rasa abin da yake mata dad’i tun da taji an fara zancen Fatima,

Me hakan ke nufi? Me yasa za taji haushi dan yaya Mus’ab da Anty Maryam suna tsokanar yaya Faruk akan Fatima? Mai yasa ba ta ci snacks d’in da ta soya ba, duk kuwa yadda take son Samosa da Spring roll? Hakan na nufin dan ya fito daga hannun Teemah ne kamar yadda ta ji yaya Faruk na kiran ta.


Duk wannan tarin tambayoyin ba ta da amsar su.


 Mai yasa yaya Faruk ke burge ni? ta tambayi kan ta.


Zuciyar ta ce ta ba ta amsa akan saboda yana da irin qualities d’in da kike so a gurin namiji, shi yasa kika ji yana burge ki...


Ganin tunanin da ta fara bai da wani amfani yasa ta d’auki wayarta ta kunna cool music tana saurare, a haka bacci ya d’auke ta.





*KADUNA*


Karatun mu ya ci gaba da tafiya da dad’i da ba dad’i saboda matsalolin high institution da ba za a rasa ba.


Yau sanye nake da cotton material kalar pink, yayin da nake sanye da white hijab & flat shoe, jakar dake hannu na kalar pink rik’e a hannu na.


Magana na fara ma Halima wacce ta maida hankalin ta ga rubutun da take yi na ce "Halima bari in lek’a cikin asibiti, kwana biyu ba na jin dad’in jiki na".


Tsayar da rubutun da take yi ta maida hankalin ta gare ni tace "Ayya Sorry Fatima, ki jira in k’arasa rubutun da nake yi sai in raka ki".


"kar ki damu Halima, ki ci ga ba da rubutun ki, nima ba dad’e wa zanyi ba".


"Sai kin dawo, Allah ya k’ara sauki".


"Amin" na amsa mata kana na fita daga class d’in. 


Ko da na k’arasa asibitin, ba da kati na nayi a record room, ba a d’au wani lokaci ba naji an kira suna na, bayan naje ne ta tura ni room 5.


Ko da na isa gurin, ba wasu mutane, dan haka ba a d’au lokaci ba aka kira suna na.


Yau sanye yake da wani tsadadden yadi kalar ruwan madara sa’banin ran nan da na ganshi da shigar likitoci, yana sanye da d’an k’aramin medicated glass a fuskar shi, sai k’amshi dake tashi a room d’in.


Zama nayi a kujerar da marasa lafiya ke zama, yau ma rubutu yake yi ba tare da ya d’ago ya kalle ni ba.


Ganin bai ce min komai ba yasa nace "Ina wuni Dr".


"lfy lau, me yake damun ki".


Har a wannan lokacin bai d’ago ya kalle ni ba.


"fever nake fama dashi kusan 1 week kenan".


Sai a lokacin ya dakatar da rubutun da yake yi ya kalle ni.


Kin ce kin kai kusan 1 week kenan kina fama da fever, bayan shi ba inda yake miki ciwo?" Ya tambaye ni.


"gaskiya babu" na amsa masa a tak’aice.


Hannun shi yasa a kan wuya na don jin yanayin temperature d’ina.


Wani irin shock na ji san da ya ta’ba ni, ko dan shi ba muharrami na ba ne yasa naji haka? na tambayi kaina.


Wata farar takarda yayi rubutu a jiki ya mik’o min yace "ga wannan takardar sai ki je lab a miki test duk da nafi tsammanin malaria ce ke damun ki, in kin yi test d’in sai ki kawo min result d’in in gani".


"na gode Dr".


"aikin mu ne, kar ki damu".


Sallama na masa na tafi.


Hakan ta kasance, washegari nayi sammakon zuwa aka d’ebi jini na a laboratory suka ce an jima in dawo, na tafi class, muna gama lectures na first period na koma.


Da na amshi result d’in a laboratory na wuce na kai kati na a record room, tambayar su nayi Dr Abubakar nake son gani, sun fad’a min cewa yau sai da rana yake da aiki, dan haka na koma class da niyyar in in mun gama lectures kan in tafi gida sai in zo in ganshi.


Muna gama lectures d’in na je na musu Magana kasantuwar sun d’auko folder na tun da safe, dan haka suka ce in wuce room 4 yau a nan zai ga patient.


Ina zuwa ban samu mutane ba kasancewar rana ne, hakan yasa na wuce d’akin direct.


Sallama nayi na nemi guri na zuna

Amsa min yayi da murmushi a fuskar shi.


"Fatima ko? ya tambaye ni.


Mamaki ne ya kama ni yadda aka yi har ya rik’e suna na.


Folder na ya d’akko ya ajiye a gaban shi, tambaya ta yayi na yi test d’in da ya ba ni?


Mik’a masa takardar nayi nace "eh nayi".


Sai da ya gama nazarin takardar sannan ya fara rubutu yace "Maleria ce ke damun ki, zan rubuta miki magani".


Takadar ya mik’o min yace in amsa maganin a pharmacy.


"Allah ya k’ara sauk’i student"


"Amin Dr".


Sallama na mishi na bar office d’in.


Tun daga wannan lokacin in ban da lafiya ya zamana gurin shi nake zuwa ya duba ni, sai dai in ba ya nan ne nake ganin wani likitan.


Lokaci na ta tafiya in da muka cinye zangon karatun mu na farko muka fara rubuta jarabawar mu ta farko.


Muna chat da yaya Faruk amma ba sosai ba, kasancewar ya ce min in da suke ba network mai kyau.


Duk san da muka had’u a chat yana k’ara jaddada min irin son da yake min.


A can ‘bangaren yaya Faruk sai ya zama sun fara sabawa da Nana Khadijah kasancewar yana lek’a wa gidan su Mus’ab in kad’aici ya dame shi.


Duk da in yaje ba wata hira suke yi ba kasancewar ita ma Magana ba ta dame ta ba amma yana yabawa da natsuwar ta da kamun kan ta. 


A haka har ran tafiyar su tazo suka tafi garin Adamawa.




Post a Comment

0 Comments