TOP HAUSA NOVELS atOptions = { 'key' : '20e08520dad54dbf6d9e963271

Babu so page 83

       *_❤‍🔥BABU SO....!!❤‍🔥_*

                 _(Miya kawo kishi?)_




              *_Bilyn Abdull ce🤙🏻_*


*_BABU SO👉🏻AREWABOOKS_*


*_83 End_*





.........Matsalar ba'a raye-raye bane kawai ko abinda bai dace ba ko mara amfani. Akwai canja abokai, dan dole ne yay abokai a wannan yanar gizon, tun ana ƴar nesa da juna har a kai ga haɗuwa, bai san tarbiyyar waɗan can ba ko inda suka fito, sai kiga an koya masa sabuwar ɗabi'ar da baki san yaronki ko yarinya da shi ba. Shaye-shaye ne, maɗigo ne, luwaɗi ne, fashi ne, sata ne, yahoo ne, kai da ire-irensu daban-daban. Wlhy ko a film naga yarinya na shan shisha inajin zafi a zuciyata, dan wata daga wannan abinda ake ɗauka faɗakarwar zataji daɗi ta cigaba, saboda mu a namu wautan ɗaukar shisha muke ba shaye-shaye ba ma. Daga faɗakarwa an koma feɗe tarbiya, an gyara goma biyar bata gyaru ba. Kullum ƴarki abokai da ƙawaye na janta/jansa bin joint-joint, inda anan zata haɗu da wasu masu buɗaɗɗen idon da yafi nata kuma ko yafi nasa. Ya ALLAH, iyaye dan ALLAH mu dake da addu'a. Sannan muma a karan kammu mu gyara halayen da muka san munayi marasa ƙyau. Dan ba media bace bala'i kawai muma a karan kammu bala'in kammu da kammu ne. ALLAH yasa mu dace.


       Ba Fadwa ba kowa ma a falon jikinsa yay sanyi matuƙa, hankalin iyaye da yawa da ba ɗaukar komai suke matsayin komaiba ya tashi matuƙa, dan kamar an farkar da su ne abinda suka kasa hangowa a tsayin hangensu. Fadwa kuka take matuƙa tana mai dana sani da nadama mara misali. Dan kuwa yanar gizo bata bata komai bai sai komawa baya da sakata a gurbin nadama saboda batabi hanyar da zata amfana da ita ba. Inama sauran wanda suke hali irin nata suma zasu farga da wuri kafin su rasa abinda ta rasa koma fiye da ita. Inama zata iya goge abinda ya wuce a zuciya da idanun mutane?. Sai dai kaico, duk da ta daina a yanzu ko waya bata riƙewa haka bai hana videos nata cigaba da yawo ba a media, saboda wasu sun adana a wayoyinsu, kuma suna cigaba da zama illa a garesu tunda suna koyi da su matsayin abin birgewa. Duk wanda ya koya daga gareta kuma ya lalace tanada kamasho na zunibi itama. Kenan ita baɗala koda kayita ka daina sharrinta na biye dakai har bayan ranka, wani lokacin ma har jikokin jikoki? Ya ALLAH ka ganar damu gaskiya tun kafin ta ƙuɓuce mana. Ka shiryar damu tun kafin guri ya ƙure mana, ka ƙuɓutar damu tun kafin ajali ya riskemu. Ka goge laifukamnu tun kafin ƴayanmu da jikoki su riskesu😭🙏🏻.


         Abie ne ya katse tunanin kowa cikin gyaran murya. Hakan yasa kowa maida hankali a garesa. “Babban abinda ya taramu anan shine sake bada haƙuri da roƙo ga iyayenmu, yayunmu, ƴaƴanmu, kuma ƴan uwanmu. Yaya Muhammad, Alhaji Sadiq, Babana Shareff. Musamman abinda ya faru ya rigada ya faru, kuma hukuncinku dai-dai ne dan duk ɗan halak idan an zunguresa ya dace ya nuna yaji zafi kuma ya ɗau mataki.  Sannan wanda yay laifi idan anga nadama a cikin idanunsa da ayyukansa ya kamata ai masa afuwa koda kuwa bazai samu girman daraja irin ta baya ba. Kamar yanda na roƙa a tun sanda kukai sakin nan kuka maidasu bada sanin kowa ba har su a karan kansu dan mu barsu su horu muga kuma idan zasu gane gaskiya, to Alhmdllh sun gane, a tsahon kusan shekara guda. Ina roƙon alfarmar ku maidasu ɗakunansu, ya rage nasu su riƙe igiya ɗaya data rage musu kosu barta itama ta katse a yanzu. Fatanmu zuminci ya cigaba da gyaruwa ba ɓaci ba, sannan dama shi mai laifi ana masa gargaɗi idan yaji to falillahil hamdu, idan ya nuna kunen ƙashi sai a barsa da halinsa ALLAH ya hukuntashi da ikonsa. Halima da Nafisa kunada sauran igiya ɗaya na aure kuma mun roƙa alfarma an maidaku tun kan ku kammala idda, amma bawai hakan na nufin ku cigaba da abinda ranku ke so ba a wannan family, dan a wannan gaɓar mun shirya ɗaukar mataki akan kowacce dazata zame mana iblis wlhy, babu kuma wani cikinmu dazai sake mata alfarma.”

     Sosai Mommy da Gwaggo Halima ke hawayen daɗi, har basu san sun fara zuba godiya da addu'a akan Abie ba. Yay murmushi kawai dan kuwa bai taɓa tunanin ganin irin wannan ranar ba. Hankalinsa ya maida ga Shareff dayay kicin-kicin da rai, sai dai wani sashe na ransa ya masa daɗin maida Mommy, ya kuma sake jin kima da mutuncin Abie a cikin idanunsa da ransa.....

    “Babana”.

Abie ya katse masa tunani.

Ɗagowa yay ya dubesa, sai dai baice komai ba. Abie ya murmusa ganin yanda ya tsuke fuska. “Nasan a gareka abune mai matuƙar wahala iya manta komai, shiyyasa ko a wancan karon ban tunkareka ka maida Fadwa ba, na barka ka huce sosai da sosai kafin muzo a wannan gaɓar. Babu mai tilasta maka a cikinmu, amma zamu roƙeka alfarma. Dan ALLAH ka maida matarka tunda tayi nadama.....”

     Kansa ya shiga girgizawa a hankali. “Abie batai nadama ba, tana muku lumbu-lumbu ne kawai. Koda zan iya maidata domin darajarku bazan taɓa sake sonta ba, bazan taɓa ganinta da mutunci ba, bazan taɓa iya sauke dukkan hakkinta ba. Har yanzu ina ganinta a idona mai ɓakar zuciya, mai mummunan hali, mai karancin tarbiyya, ballagaza da bata san kima da mutuncin kanta ba, Abie mazafa kallonta sukeyi sunaji wani abu a ransu, shin yara matasa nawane da magidanta sukaji hakan? Mutane nawane suka kalleta a hakan? Ta daina amma har yanzu abinda ta shuka na yawo a wayoyin mutane? Bazan iyaba Abie, wlhy ko tunata bana sonyi, bana son ganinta sam......”

     “Karka tsaurara da ƙarfi babana. Nasan akwai ciwo, akwai ɗaci, akwai raɗaɗi. Sai dai muɗin ba masu shiryarwa bane ba. Sannan samun miji na gari na ƙwarai a gareta a yanzu abune mai wahala, duk da nasan wasu zasu iya amfani da nasibin da ALLAH ya bama mahaifinta na suna da dukiya suce zasu aureta, tunda wasu a gurunsu abinda ta aikata ba komai bane a wautarsu, sai dai bai zama lallai su zama na ƙwarai ba......”

     Fadwa dake kuka ta ƙatse Abie ta hanyar rarrafowa gabansa. “Wlhy Abie bazan iya zama da wani namijiba inba shiba. Ina sonsa, kuma ni kaina ina kaico wa rayuwata ta baya. Na ɗauka abinda nake ba komaiba sai nishaɗi kawai, na ɗaukesa matsayin zamanine kawai, na ɗaukesa matsayin lokacina ne kawai. Wasu tsurarun mutane da bazasu amfaneni da komai a duniya da lahiraba kwarzantawarsu a gareni na ingizani inajin babu yani. A tunani na abinda nake ba komai bane tunda ba'a zahiri baneba. Ashe mummunar rayuwace mai wargaza ƙyawawan ayyuka. Ashe ƙofofin matakin zuwa ga zina ce, ashe raguwar darajace a gareni matsayin ɗiya mace, ashe tanadin abin faɗa ne ga ƴaƴana ga ƴan uwana. Ashe makullun rusa dukkan farin cikina ne da rayuwar aurena. Ashe ƙanƙantar da kaina nake tamkar dabbar da bata san inane rufe ko buɗe ba. Kaico na da wannan rayuwa, kaicon duk wata mace mara kamun kai da fahimtar rashin daidai matsayin nishaɗi ko birgewa. Kaicon mace irina dake nuna rashin ingancin tarbiyya da mutuncin iyayenta wa duniya. Nima bazan matsa maka ka maidaniba, amma bazan daina son ka ba, zan mutune da sonka Soulmate, zan amshi wannan hukuncin domin nasan UBANGIJI ne yake horani ta hanyar aza sonka a raina fiye da komai. Na godema ALLAH daya saka maka da mace tagari tun kan kasan niɗin wacece. Na gode ALLAH daya fargar dani illar abinda nakeyi tunkan tsufa da mutuwa su riskeni......”

    Kuka ya sarƙeta, tausayinta ya saka Anaam fara kuka itama. Amma ga Shareff sai ma faman taɓe baki yakeyi alamar ko'a jikinsa. Dan shikam dai har cikin ransa baya fatan sake zama da Fadwan. Sai dai yana mata fatan shiriyar da tace tayi dan shima yana fatan ALLAH ya shirya masa nasa ƴaƴan daya fara haifa da ƙanensa dama duk ƴaƴan musulmi.


     Duk fa yanda aka buga Shareff bai yarda da maida Fadwa ba. Dole aka ƙyalesa dan har yanzu yana akan dokin fushi. Haka taro ya tashi su Mommy dai zasu koma ɗakunansu.


..................


     Rayuwa ta cigaba da shuɗawa har ALLAH ya sake bama Anaam ciki, a kuma lokacin su Abie suka dawo Nigeria, dan haka Muhseenah ta koma hanunsu, wani lokacin kuma tana wajen Mommy data dawo tuni, hakama Gwaggo Halima ta koma, sai dai kuma duk da mijinta ya ɗare karagar mulki ta koma ƴar kallo, komai amaryace ke zartarwa itama ake kira first lady. Haka Gwaggo Halima keshan kukanta, ta kuma ɗauka ɗammarar haƙurin zaman ƴaƴanta. Anaam aka cigaba da rainon ciki har ALLAH ya sauketa lafiya. Alhmdllhi wannan karon dai da kanta ta haihu ɗan ta namiji mai kama da Shareff, anyi farin ciki matuƙa an kuma sha shagali. Yaro yaci sunan Daddy. Wato Muhammad Ameen. Za'ake kiransa Muhammad ɗinsa. Anaam da Shareff suka cigaba da rainon ɗansu, wani lokaci Muhseenah takanzo tai musu har sati suma duk da dai kullum sai sun ganta idan sunje kai Muhammad gida idan zasu aiki ko sun taso. A haka shima ya girma yakai yaye. A kuma lokacinne ALLAH yayma Gwaggo data koma abin kwatance rasuwa, tanata kururuwa da ihun a kira mata su Daddy, sai dai kafimma suje rai yayi halinsa. Dolene kaga gawar Gwaggo ta baka tsoro, ta mugun komawa ƴar tsurut kamar ba gawar mutum ba. Ƙarshen Gwaggo ya sake sanyaya zukatan su Mommy matuƙa. 


      Muhammad nada shekara uku a duniya rabuwar Fadwa da Shareff kuma shekara shida Abie ya sake roƙon Shareff maidata ɗakinta, dan har yanzu ta kasa aure, mazanma da ake tunanin zasuzo kodan alfarmar mahaifinta tamkar ALLAH ya dakatar dasu duk wanda yazo gareta sai da wata manufa amma ba aure ba. Takanci kuka matuƙa idan suna mata izgilanci da abinda ta aikata baya. A wannan karon dai da ƙyar ya amince, sai dai ya sake tabbatar mata bazai taɓa ƙara sonta ba, ba kuma zata samu wani farin ciki daga garesa ba.

     Tana sonsa dan haka ta yarda da hakan da tunanin zata iya haƙuri aka sake ɗaura aure. Sai dai kuma a tarewarta gidan ta tabbatar da abinda ya faɗa ɗin, dan ta kasa gane komai na Shareff, yana sauke mata dukan hakkin da ALLAH ya daura masa na ci da sha da sauran buƙatun rayuwa, amma ko fara'arsa bata gani balle samunsa a gado, kwata-kwata yaƙi kusantarta, babu wata soyayya a tsakaninsu yanzu, komai yana mata alamar tilasne zama da ita ya zame masa dan iyaye. Takanci kuka ta gode ALLAH musamman idan taga yanda suke soyewa da Anaam a gidan kamar suna mantawa da zamanta. Dan ma Anaam ɗin kan noke wani lokacin a gaban idonta. Ga wata irin soyayya da take gani yanama ƴayansa tamkar ya cinyesu. Dan cikin da Anaam ta samu na uku a gidan sai da taji tamkar ta haƙura da auren ma. Gaba ɗaya ya gama lalacewa a kan cikin, koda yaushe yana manne da Anaam ɗinsa da ƴan ƴaƴansa. Ita tsakaninta dashi kawai abinda yake wajibi. Ya hanata riƙe waya kuma sai rakani kashi, itama ya tabbatar mata zai barta da itane domin adalcin kiran iyayenta. Amma kuma kullum cikin bin ƙwafɗin wayar yake. Hakan na damunta, dan a yanzu sam babu wata yarda a tsakaninsu koda ta magana ce. Ko abu ta faɗa masa sai yace sai ya bincika. Tasan alfarmar Abie kawai takeci na zaman gidan. Amma ta rasa Shareff har abada. Ga haihuwa shiru kaleji babu labari har yanzu, koda yake ba'a kusanceka ba ina zaka haihu. Hakan ma na sake tada mata hankali dayin nadama mara misali.

      A yanzu ma kuka take tana kallon Shareff ɗin da su Muhseenah da tazo musu weekend ta window. A tsakar gida suke suna buga ball harda Anaam dake fama da tsohon ciki. A bisa tsautsayi Anaam ɗin ta gurɗe. Gaba ɗaya Shareff ya ruɗe shida yaran duk sukai kanta, jikinsa ya jawota cikin tsananin tashin hankali, itako tana faman riƙe ƙugu da kiran sunansa.

      “Bayana Yaya, cikina, ƙafata ta riƙe, Yaya muje asibiti wayyo Mamie na”.

    Ai babu shiri yay sama da ita yakai mota, dole Fadwan ta fita itama domin taimaka musu. Amma sai yay kamar bai ganta ba har saida Muhseenah tai magana tana kamo hanunta. “Mamah kizo kima Miminmu addu'a Please kinga tana kuka”.

      Cikin ƙarfin hali ta saci kallon Shareff dake ƙoƙarin saka Muhammad a mota. Amma yay kicin-kicin da rai. Muhseenah ta nufesa tana faɗin, “Abbu Please aje da Mama mana ta riƙeta tunda kai zakai tuƙi”.

     Har yayi niyyar ballama yarinyar harara sai kuma ya dake, ya ɗaga mata kai kawai dan yasan fitinar Muhseena ba barinsa zatai ba. Balle gata da shegen wayo, ba kuma ya son ko kaɗan tasan wani abu mara daɗi tsakaninsa da Fadwan. Dan ko Anaam bayayi a gabanta tsakanin shi da itane kawai yake horata. A dalilin Muhseenah suka tafi asibitin tare, suna zuwa babu jimawa ALLAH ya sauki Anaam ɗin lafiya namiji. 

    Cikin ƙanlanin lokaci zance ya zagaye dangi. Kowa sai murna da fatan alkairi, dandanna asibiti ya cika da dangi. Sai da aka sallamesu ƙura ta koma can gidan aka cigaba da shagali. Shima dai yaro yaci sunan Abbah ranar suna. Wato Abubakar Sadiq, zasu kirashi da Saddiq ɗin. A wannan sunanma dai Anaam da jariri sunga gata, itako da iyayenta babu abinda zasuce ma ALLAH sai godiya. Dan yanzu dai family ya zama tsintsiya madaurinki ɗaya kowa na hakuri da ƙoƙarin kai zuciya nesa koda rai ya ɓaci.

      Bayan suna da wasu kwanaki Fadwa ta zaɓi neman saki ga Shareff bayan tayi shawara da Gwaggo Halima, itama dai jikintane yay sanyi dan tasan dama an takurawa Shareff bisa komawar Fadwa gidansa, yana jin kunyar su Abie ne kawai shiyyasa ya amince. Amma a yanzu tunda ita Fadwan da kanta ta zaɓi haƙura da zaman ALLAH yasa haka shine yafi alkairi a garesu, dan insha ALLAH a yanzu itakam bazata sake bari wani abu ya shiga tsakaninta da ƴan uwanta ba, saboda komai Fadwa ta zama a baya itama ta bada nata gudunmawar wajen karancin bibiyar al'amarinta da tsawatar mata. A yanzu itama ta fahimci zamansu tamkar cutar da juna ne kawai, shi zuciyarsa a ƙuntace da ganinta, ita kuma zuciyarta a ƙuntace da buƙatarsa ta kuma kasa samu. Bai waniyi jayayyaba suka je gaban su Abie da kanta tai musu bayani, duk da sun fahimci hakan shine sauƙi da farin ciki a garesu basuji daɗi ba. Amma sun musu fatan alkairi, Shareff ya rubuta mata sakinta. Tana hawaye ta amsa dan harga ALLAH tana matuƙar sonsa, bakuma zata daina son sa ba har ƙarshen numfashinta. Ta zaɓi yin nesa da shine domin yazama cikin farin ciki, dan ta yarda da gaske baya son ganinta, ya tsaneta a yanzu. Shi kansa dai yaji tausayinta a wannan gaɓar, amma dai haka shine mafi sauƙi a garesu, dan yayi ƙoƙarin manta komai ya amsheta hakan ya gagara, bayajin zai taɓa iya ƙara kusantar Fadwa, badan komai ba sai dan daya tuna maganar samarin nan sai yaji tsananin tsanarta da zafinta, yanada kishi matuƙa akan duk abinda yake nasa, dan haka koya cigaba da zama da ita sai dai yayta cutarta dan yayi alƙawarin bazai sake kusantarta ba. Yana mata fatan alkairi, idan tuba tayi na gaskiya ALLAH ya saka mata da abinda zai zame mata alkairi anan gaba.✍



*_To nima dai bari nace Alhmdllhi, ALLAH ka ƙaramana haƙuri da juriya a duk yanda wasu zasu so ganin fushinmu ko ɓacin rai ko damuwarmu ALLAH ya hana. Ya ƙara mana haƙuri da juriyar ɗaukar komai da zaizo a ƙaddarorinmu, ka hanamu yin kuka da dana sani mara yankewa a rayuwa._*


*_ALHAMDULILLAHI_*

     *_ALHAMDULILLAHI_*.

            *_ALHAMDULILLAHI_*


Godiya ta tabbata ga UBANGIJIN talikai daya bani aron rai da lafiyar rubuta wannan ɗan gajeren labari. Abinda na rubuta dai-dai ALLAH ka amfanar damu a ladar. Kuskuren ciki ALLAH ka yafemin.


     Wanda duk naima ba daidaiba a yayin rubutunsa ya yafemin, abinda yazo ba'a haka kuka so ba kuyi haƙuri a haka labarin yazo. Ina fatan kuyi amfani da amfanin ciki ku watsar da marasa amfani, dan wani abun ana sakashine dan kawai nishaɗi. Yaranmu masu tasowa ba komai najin daɗin rayuwa dake zuwa a novels ake samunsa a zahirin rayuwa ba. Kowanne bawa da ƙadarar da ALLAH ya tsaro a tasa rayuwarsa. Idan kinga saɓanin rayuwarki dana littafi ki ɗauka wancan labarine dan fadakarwa da nishaɗi bawai dan sai kin tabbata ko kin samu irin rayuwar ba.


ALLAHU ka gafarta mana ka gafartama iyayenmu. ALLAH ka yafe mana.😭🙏🏻


Kamar yanda na fada a tiktok akwai mutanen kirki, masu yada alkairi DA yawa, hakama akwai na banza, mun tabo irinsu fadwa ne Dan su san illa na abinda suke aikatawa, muna musu kuma fatan shiriya da gane gaskiya kafin komai ya kure musu fiye DA Fadwa. Kazama mutumin kirki sai addininka DA al'adarka suyi alfahari DA kai. Ka kuma zama cikakke a cikin al'ummar MANZON ALLAH (S.A.W) ba komai bane nishadi kamar handa muke kallo a rayuwar wasu yan tiktok, wani abun zubda mutunci DA darajane matsayinki na diya mace musulma.



Masoya muna godiya dan bazamu gaji da godiya a gareku ba akoda yaushe. Muna godiya matuƙa da kasancewar ku da zafafa biyar cikin tafiya mai nisan zango. ALLAH yabar zuminci ya kara mana zama lafiya da kaunar kauna. ALLAH ka bamu shugabanni na gari. Wannan zabe dake tunkaromu ALLAH kasa ayi lafiya a gama lafiya. ALLAH ya zaunar damu a gidajenmu lafiya bisa soyayya da kaunar juna tsakaninmu da mazajenmu. ALLAH ka shirya mana yaranmu damu baki ɗaya. Waɗanan fitintunu da wayoyi suka kawo mana da yanar gizo ALLAH ka bamu ikon tsallakesu. Wanda suka afka ciki ALLAHU ka shiryesu ka ganar dasu gaskiya kafin lokaci ya kure musu. 🙏🏻


Fatan alkairi ga kowa da kowa a duk duniyar dankuke. Kaunar kauna irin 

trillions ɗin nan masoya😍😍😍😍


Taku


Bilyn abdull ce😍🤗👌🏼.




Post a Comment

0 Comments