TOP HAUSA NOVELS atOptions = { 'key' : '20e08520dad54dbf6d9e963271

Saran Boye page 73

 πŸ’ƒπŸ»πŸ’ƒπŸ»πŸ’ƒπŸ»πŸ’ƒπŸ»πŸ’ƒπŸ»

TEAM----ZAFAFA BIYARπŸ”₯😘πŸ₯°πŸ˜


ALLAH ka gafartama iyayenmuπŸ˜­πŸ™πŸ».

[7/6, 9:38 AM] *_LITTAFIN nan na kuΙ—i ne. Dan girman ALLAH ki daure ki biya kafin ki karanta, idan kuma bazaki iya biya ba ki haΖ™ura domin ALLAH karki karanta. Idan kuma kin saya dan girman ALLAH karki yaΙ—a manaπŸ™πŸ»_*.



No. 73


.............A yau kam su Nu'aymah da duk wanda yasan da wannan shirin sun tashi a shirye tsaf bisa yaΖ™inin tarkon da suka Ι—ana ya Ι—anu. Kasancewar sanyi da akeyi duk sauran jama'ar gidan da Ζ΄an biki suna can a sassan gidan a maΖ™ale, duk da madai Ζ΄an bikin da suka rage duk na jikine babu bare. Babu kowa a tsakar gidan sai yaran Jay dake Ι“oΙ“Ι“oye. 

         Yau kam Jay ya shiga har falon baba malam tare da lauyan malam mahaifin su baba malam a zuwan zasu tattauna akan kaddaririn baba malam Ι—in. Acan kuma ta waje little bee ce da wasu jami'a a harabar gidan a mabanbanta wajaje duk da Jay yasan akwai camaras Ι—in da Afrah ta saka masa a wancan zaman. Yafi buΖ™atar gani ga ido ga kowa kafin ya bankaΙ—a sirrikan dake a cctv Ι—in. An kira Aymah da Yoohan falon, sai su Abban Abdallah da hajjo data san komai itama. Sai Omar da yazo matsayin lauyan Nu'aymah shima.

       Bayan buΙ—e taro da addu'a baba malam ya fara da nasiha a garesu duk dai a cikin salon tarkonsu, dan a zahiri fa babu wani maganar mallakama Nu'aymah kaddarorinsa da yakeyi. Shirine kawai irin nasu Jay. 

      A gefe kuwa idanun su Yoohan gaba Ι—aya na'a Windows Ι—in falon a kaikaice. Baba malam kuwa na cikin nasiha sai ga abinda suke jira ya bayyana. Kallon juna sukai shi da Jay dasu Yoohan sukayi murmushi. Daga haka ya cigaba da bayaninsa hankali kwance.


        Acan waje kuwa su Little bee na mammaΖ™ale a maΙ“oyarsu sai ga mutum sanye cikin dogon hijjab har Ζ™asa da niΖ™ab ya fito daga tacan bayan gidan yanda babu mai iya fahimtar daga ainahin sashen da aka fito. Basu da tabbacin mace ce ko namiji, dan komai an rufe ba'a gani. 

      A yanda mai laΙ“e ke tafiya da dabaru zaka san cewar lallai an Ζ™ware, sannan aikine da akeyi tunba yanzuba. Cikin salon iya aiki Little bee taima abokan aikinta wani salo da yatsun hannunsa suka bada Ι—ass!! Sau Ι—aya. A take duk suka Ζ™ara shiryawa dan suma dai suna biye da mai laΙ“e akan idanunsu.

       Sai da suka tabbatar mai laΙ“e ya isa dai-dai sashen Malam marigayi alamar dai Ι—an gidanne, tunda har ansan a ina su baba malam zasuyu taron nasu aiko sai wanda yasan gidan. Kamar yanda mai laΙ“e ya saba a koda yaushe ya isa jikin Window. Wani siririn abu ya saΖ™a a tsakanin glasess Ι—in Window Ι—in da alama na Ι—aukar magana ne. Dan yana gama turashi ya kai hannu ya taΙ“a kunnensa alamar tabbatar da daidaitar komai. Ƙaramin tsaki akaja jin Nasihar da baba malam ya fara dan ba ita ake buΖ™ataba a yanzu. Jin baba malam zai fara jawabinsa mai laΙ“e ya Ζ™ara nutsuwa da maida hankalinsa ga window Ι—in domin saurare.. 

         Da wannan damar su Little bee sukasamu isowa wajen cike da Ζ™warewar aiki suka toshe gaba da baya na Ι—an siririn lungun bayan Ι—akin malam marigayi. Ƙarar saΖ™on daya shigo wayar Little bee daga Jay ne ya fargar da mai laΙ“e ya juyo da sauri. Sai kawai ganinsa yayi zagaye da mutanen da baisan ta ina suka Ι“ullo ba.

      Tashin hankali ba'a saka maka rana. Wannan shine Ι“oyayyar kalma a zuciya da bakin mai laΙ“e duk da bai fito ya furta manaba a zahiri. Dan kuwa dai gabas da yamma kudu da arewa babu wajen guduwa. Katanga a bangon gabas. Ginin sashen malam a bangon yamma. Little bee da jami'ai uku a bangon kudu duk sun nunasa/ta da bindiga. Dawood da jami'ai uku shima a bangon arewa duk sun nunata/sa da bindiga nanma.

     Wannan itace kwana casa'in da tara ta barawo Ι—aya tak ta mai kaya. Little bee ta ciwo wayarta da hannu Ι—aya a aljihu Ι—ayan kuma riΖ™e da bindigar data nuna mai laΙ“e. Kiran Jay tayi a waya. Yana Ι—agawa tace, “Sir! Aikinmu ya kammala zaku iya fitowa”.

       “Woow!” Jay ya faΙ—a yana miΖ™ewa idonsa akan su baba Malam. Takawa yay jikin windown da yake hango inuwoyinsu ya zuge gilas Ι—in tare da net. Abinda mai laΙ“e ya saΖ™ala ya faΙ—o. duΖ™awa yay ya Ι—auka yana jujjuya shi a hannunsa kafin ya kalli su baba malam da suma duk shi suke kallo. 

           “Malam zama ya Ζ™are ai, suspect Ι—inmu yazo hannu zamu iya zagayawa”.

    Harga ALLAH sai da gaban baba malam da Umm ya faΙ—i. Hakama Aymah duk sai taji tsoro kuma. Su Abba Musbahu da basusan mi akeyiba suka shiga kallonsu da tuhuma. Ko a jikin Yoohan da Umar. Dan sunema farkon ficewa a falon.

    Baba malam dake kallon su Abban Abdallah yace, “Kuyi haΖ™uri wannan itace kawai mafita a garemu gudun kar wataran a kai ga rasa rai bisa makircin da bamusan wake Ζ™ullasa ba”. Daga haka yay gaba ya barsu da kallon kallo ma juna sai dai ganin kowa ya fice suma sukabi bayansu jiki a sabule.

      Ganin duk sun iso Little bee ta dakama mai laΙ“e tsawa da faΙ—in, “Cire NiΖ™af”. Ko motsi ba'ayiba. Sai dai yanayin tsayuwar ya tabbatar da koma wanene a tsorace yake kuma cikin Ζ™ololuwar tashin hankali da firgici. 

       “Inada cikaken dama nayin harbi, hakan na nufin bullet Ι—in zasu iya fita a cikin bindigarnan zuwa jikinki/jikinka a koda yaushe. Zan irga iku kawai bisa lasisin dama a gareki ko a gareka. *_Ɗaya! Biyu! Uku!!”_* ta fita daga bakin Little bee tare da bullet Ι—inta zuwa Ζ™afar mai laΙ“e da ko motsi baiyiba balle ya nuna kota nuna zata cire nikab din da aka bada umarni.

     A take Ζ™arar muryar mace ta karaΙ—e gidan saboda azaba shigar bullet. Ƙasa ta durΖ™ushe jiki na rawa. Da wannan damar Little bee ta Ζ™arasa gareta tasa hannu ta fisge niΖ™ab Ι—in ta jefar gefe. Baba malam da Umm da sauri suka kauda kawunansu gefe da tsananin fargabar tsoron ganin koma wanene. Sai da Nu'aymah ta furta,

       “Illalillahi wa'inna ilaihirraji'un Addah!! Kece dama?!!!”.

     Sannan su Umm suka juyo a firgice. A take wajen gaba Ι—aya ya Ι—auki salati. Dan duk jama'ar gidan kururuwar ihun Addah da Little bee ta harba dama duk ya fito dasu a hautsine.

     Cikin girgiza kai hawaye na sakkoma Umm a guje tace, “Inaa bazai yuwuba. Addah ki sanar musu ba abinda suke zargi bane ya kawoki nan. Dan ALLAH ki tabbatar musu domin bamu kariya kema kika zo nan. Ki tabbatar musu bake bace kike laΙ“en nan dama can dan ALLAH, kicemin yau kika farayi......”

      “Bata da bakin baki waΙ—an nan amsoshin domin wanke kanta Umm-Muhammad. Domin kuwa duk saΙ“aninsu da baki eson ji daga bakinta sune gaskiyar amsoshin naki da ma kowa dake anan wajen”.   

     Bily dake kusa da Jay tsaye ta bama Umm amsa kanta tsaye.

        “Karkice dani haka Maman Awwab. Dan ALLAH karkice haka. Wannanfa Fauza ce, wadda muka tashi tare tun Ζ™uruciya tamkar uwa Ι—aya uba Ι—aya ta haifomu. Ban taΙ“a Ι“oye mata sirrinaba, itama bata taΙ“a Ι“oyemin nata ba. Tare muke raba farin ciki, sannan mu raba kuka tare idan ya samemu.....”

         Murmushi Bily tayi da takawa a hankali zuwa gaban Addah daketa faman magowar azabar Ζ™afarta dake zubda jini. Ta nunata tana mai kallon Umm Ι—in, “Tabbas a zahiri haka take a gareki Umm-Muhammad. Amma a baΙ—ini itace babbar maΖ™iyyarku. Idan kuna buΖ™atar tabbatarwa mu a shirye muke wajen nuna shaidar gani da ido a gareku dan duk mun tanajesu dama”. Ta Ζ™are maganar tana duban su baba malam da alamu ya nuna tamkar duk sunyi sumar tsaye ne har yaran Addah da duk suma suna a wajen.

      Daga haka Jay ya bama Yoohan da Omar damar cire bullet Ι—in jikin Addah. Cike da Ι—acin murya Yoohan ya dubi Jay Ι—in idanunsa jazur. “Uncle ka gafarceni, hannuna bazai taΙ“a iya aikata jinΖ™ai ga maci amana ba”. Daga haka ya kama hannun Nu'aymah da jikinta ke karkarwa suka bar wajen.

      Murmushi kawai Jay yayi. Baba malam zaiyi magana Jay yace, “Karka takura masa Malam. Umar Please ka cire mata sai mu wuce da ita. Malam sai ku samemu a statlon Ι—inmu nan kano mu Ζ™arasa maganar”.

       Da sauri baba malam yace, “A'a Jawaad ina neman alfarma komi zai faru muyisa anan cikin gidan domin rufin asirinmu, wannan itace alfarmar da zan nema a gareku”.

     ΖŠan jimm Jay yayi, sai kuma ya kaΙ—a kansa alamar karΙ“awar alfarmar baba malam Ι—in.

     Badan Umar yaso ba ya amince zai cire. Dan haka aka Ι—akko Adda daga lungun zuwa sashen Malam. Gaba Ι—aya yaran sa'an su Muhammad zuwa kansu Adawiya ba'a barsu sun shigaba. Duk da kuka da Adawiya keyi iyakar Ζ™arfinta wanda babu wanda yasan dalilinsa. Su Hajarah da sauran yayunta na ma'auri duk suna gidajensu basusan abinda akeyiba. Sai malam Ζ™arami kawai da sauran Ζ™annensu. Shiko gaba Ι—aya da alama ma jinsa da ganinsa sun gushe dan bai iya motsawa a lungunba har kowa ya fice. Hakama Abba Mustapha saida Hajjo ta kama hannunsa da kanta saboda tsabar firgici.


★★★


        Bayan azabar cire bullet da Addah ta gama sha Omar yay mata allurar rage raΙ—aΙ—i. Umm dake kuka har yanzu ta sake duban Addah. “Fauza dan ALLAH ina roΖ™onki a karo na Ζ™arshe ki Ζ™aryata tuhumar da ake miki. Ki tabbatar musu da kawai yau Ζ™addara ta kawoki amma ba ke bace. Har abada bana fatan kunnuwana da zuciyata suji saΙ“anin tunaninsu a kanki Fauza.......”

        Shiru Addah batai ko motsiba, kanta a Ζ™asa kuma taΖ™i kallon kowa. Gyaran murya Jawaad yayi da gyara zama. “Hajiya karki wahal damu anan, dan alfarma ki ke ci, badan darajar malam ba da zamu wuce dake station ne ki mana bayani ta duk hanyar da mukaso bi da ke. Kar kiyi tunanin Ι“oye mana komai dan a tafin hanunmu kike, duk wanda ke cikin labarinki sai da na gurfanar da shi a gabana kafin ki ganni anan, na zaΙ“i bin komai mataki-mataki ne saboda sauΖ™aΖ™a firgici a zuciyar waΙ—anda kikema cin dunduniya. Nasan kinsan Hamisu ai gashi a gabanki tsaye”.

    Da sauri Addah ta Ι—ago ta kalli inda Jay ke nuna mata. Kallon ido cikin ido sukaima juna kuwa ita da Hamisu. ya ko zuba mata mummunan kallo. Da sauri maida kallonta ga Jay. Kai shima ya jinjina mata fuska a Ι—aure. “Bayan Hamisu akwai Ζ΄arki Kubrah ko, sannan akwai......”

      Da sauri ta Ι—aga masa hannu, sai kuma ta fara tari, gefen Ι—an kwalinta tasa ta tare bakinta sai ga jini na zuba. Babu wanda bai mata kallon tsoro da firgici ba a falon. Ta goge mabinta saboda tsagaitawar tarin sannan ta kalli kowa dake falon tana Murmushi mai ciwo a karon farko. Ta kalli Ζ™afarta dake naΙ—e da bandage hawaye na ziraro mata. Dan har yanzu tanajin raΙ—aΙ—in azabar shigar bullet a karon farko na rayuwarta. Kallon baba malam tayi ta sake sakin murmushi sannan ta maida akan Umm dake a gabanta zaune.

      “Ko babu Ζ™arfin iko hukuma dama lokaci yayi da Firdausi! Zata san wacece Fauza a gareta. Dan tun bayan auren Nu'aymah wannan ranar dama nakewa zaman jiran tazo a gareni, dan nasan tana cikin ranakun da ko naso koban soba sai sun riskeni a duniya ko a lahira, musamman daya kasance gajerun kwanaki suka ragemin a duniya. Wannan Fauzar dake gabanku ba Fauza bace ta shekarun baya mai lafiya, hatsabibiya, mai aiki da zuciya kawai bada tunaniba, mai son kanta, mai aiki da huΙ—ubar shaiΙ—an. Wannan Fauzar maΖ™asΖ™anciyace a gabanku yanzu, mai rauni, mai Ι—auke da ciwon zuciya da ciwon kansar jini (blood cancer), wadda likita ya tabbatarma watanni kaΙ—anne suka rage mata a duniya. Wannan Fauzar mai dana sani ce da nadama da yin kaico akan ayyukan data tafka batare daku kun saniba saboda iya SARAN ƁOYE”.

     Tarine ya kuma sarΖ™eta da kuka. Nanma tanayi jini na fita, saida ta tsagaita sannan ta sake dubansu. “Da wahala shara'ar alΖ™alin duniya ta iya dacewa da laifukan Fauza, shara'ar UBANGIJI datafi cancanta dani ta fara bayyana a gareni tun daga randa likitanci suka sanarmin sakamakon abinda nakeji a jikina. Amma lallai halina dolene yaje kunnunwan mai saurare ko zai zama izina ga masu irin halin suji tsoron ALLAH su canja kafin lokaci ya Ζ™ure musu”. 

         “Firdausi! Da gaske ni Addah na soki so na gaskiya a zamanin Ζ™uruciyarmu. Duk da ko a wancan lokacin duk randa kika samu abinda ni nafi cancanta da samunsa inajin zafinki a raina. Musamman idan nai la'akari dana fiki komai a rayuwa. Ni Ζ΄ar gatace ko a gidanmu, duk wani jin daΙ—i da yaro kan tashi ya samu daga iyaye na samesa. Mahaifina yafi naki komai a rayuwa. Hakama mahaifiyata tafi taki. Hasalima da yawan lokuta Ζ΄an gidanku kunaci ne daga alfarmar iyayena. Sai dai kash duk da wannan gatan namu da tarin alfarma kin fini basirar karatu, bama ke kaΙ—aiba duk Ζ΄an gidanku ALLAH ya basu wannan baiwar, gashi duk kun fimu Ζ™yau, sannan da wahala ku zauna da mutane basu soku ba. Dan yayyenki ma sunsha ciwo nasarorin dake sa yayuna jin zafinsu, sai dai mahaifiyarmu kan Ζ™waΙ“emu akan hakan. Nasararki a kaina bata taΙ“a kaini ga Ζ™ololuwar jin zafinkiba sai a randa Sheikh Soorajidden yazo har gidanmu akan neman aurenki”. 

       Ta share hawaye masu zafi dake gangaro mata har yanzu sannan ta cigaba da faΙ—in,

       “Hakan ta faru dalilin soyayyarsa da taimin shigar sauri cikin zuciya tun a ranar kammala karatunmu. Idan baki mantaba tun a wajen bakina bai hutaba da zance a kansa har kika nuna Ζ™osawarki akan hakan. Mun dawo gida zuciyata na Ι—unbin begensa, sai dai a randa na buΙ—i ido na gansa a gidanmu sai labari ya canja salo. Ke! ke! ke!! Firdausi! kin sake yanke igiyar nasarata kamar yanda kika saba a koda yaushe”.

       Tai maganar da matsanancin kukan da har ya hanata kasa cigaba da magana sai da tai tari mai tsaho. Falon kansa yayi tsit ko motsi kowa ya kasa saboda shock. Da Ζ™yar ta tsagaita kukanta da tarin sannan ta cigaba.

         “Naji zafinki a wannan ranar zafin da idan aka bani makami zan iya halakaki. Nayi kuka harna rasa hawayen zubarwa. Amma daga Ζ™arshe sai nayi haΖ™uri bisa ga shawara da nasihar da babbar yayarmu ta min, a lokacin sai naji na haΖ™ura na barmiki, duk da dai son nasa na nan maΖ™ale a raina. A haka aka kammala komai na maganar aurenku ni bani da wani tsayayyen saryima. Har lokacin biki yayi mukasha bikinku. ALLAH ya sani ban taΙ“a cin karo da rana mai ciwo da raΙ—aΙ—i ba irin ranar aurenku. Dan aranar na gama yanke hukuncin dolene na shigo gidanki matsayin kishiyarki. Amma sai kash. Ƙaddara ta riga fata, dan kuwa haΙ—uwata da Mustapha sai ta kasance almakashin daya datse wannan zaren a karo na biyu. Ya nuna yana sona, amma ban amsa masaba a ranar, shi kuma ya zata kunyace ta sani Ζ™in amsawar, dan haka yay amfani da wannan damar yayma rayuwata kutse ta bayan gidan adalilin neman aurena da Sooraj yaje yayima Ζ™aninsa a gidanmu tamkar yanda yayima kainsa. Babana kuma babu wani tsayawa ja'in-ja ya bashi. Na sake shiga ruΙ—ani a karo na biyu, amma sai yayata dai ta sake Ι—orani akan mizanin hankali da nasiha kamar wancan karon. Ta kuma tabbatarmin Mustapha shine mijina dama ba Sooraj ba, tanada yaΖ™inin kuma shine zai zama mafi alkairi a gareni insha ALLAHU. A wannan karonma taci nasara. Dan duk da babu son Mustapha a raina na aminta zan auresa kodan darajar jini da suka haΙ—a da Sooraj, sannan a fuska ma suna kammani da juna”.

     Ta share hawayenta tana murmushi da kallon Umm.

        “Firdausi! Shigowata gidan nan shine ya sake canzama zuciyata salo a kanki. Dan tun a yanayin taron aurena da Mustapha na fahimci a wannan gaΙ“arma kin sake min tsere. Ban sake tabbatarwa ba sai da na tabbata Ι—aya daga cin wannan ahalin. Zamantakewar ki da Sooraj tana Ι—aya daga abinda ya dagula min tunani. A zahiri mutane Ι—auka suke tsoron Sooraj kikeyi, amma wanda zai ganku a sashenku kaΙ—aine zai goge wannan tunanin a ransa saboda soyayya da tattalin da kike samu daga garesa. Sannan kasancewarsa babban Ι—a a gidannan duk wata daraja ta matar gida kin kwashe a sama da tamu. Wannan yasa ita kanta Momyn Abdallah kejin zafinki ganin anan kikazo kika sameta. Abinda ya Ι—an sakamin sassauci a kanki lokacin haihuwa dana rigaki yi kuma namiji, har takai sai da na jera huΙ—u sannan kika samu ciki. Maganar gaskiya bazan Ι“oye mikiba naji matuΖ™ar jin kishi akan samun cikinki duk da kuwa inada Ζ΄aΖ΄a har huΙ—u a lokacin. Dan idan ina Ζ™aunar mutuwata to ina Ζ™aunar buΙ—ar ido naganki da wani cigaba daya Ι—ara nawa a rayuwa, dan na tsani cikin nan naki tun yana Ι—an tayinsa. Duk da ban taΙ“a tunanin cutar dake ba adalilin cikin nan zuciyata ta fara rayamin hakan, dan kullum huΙ—uba takemin na Ι“arar da cikin kawai kowa ya huta. Sai dai ina shirin aikata hakan a gareki Sooraj ya Ι—aukeki kuka wuce saudia, nayi baΖ™in ciki nayi takaici irin wanda bazai misaltuba. Gashi baku dawoba sai gab da zaki haihu. Koda kuka dawo ban fasa aiwatar da Ζ™udirina akan cikinki ba, sai dai babu wata makamar yin hakan dana samu har ALLAH ya saukeki lafiya a wani dare. Hankalina ya tashi ganin kema da namiji kika fara, zuciyata ta sake bushewa da kangarewa akan na kashesa kawai tun yana jaririn.........”

      Cikin Ι—acin murya Baba malam ya katse Addah da cewar, “Fauza kenan kece kika kashe mana yaro?”.

         Kuka Addah ta sake fashewa da shi kanta a Ζ™asa ta kasa kallonsu. Ga tari ya kuma sarΖ™eta har jini na fita guda-guda yanzun. 

   Ko batace komaiba sun fahimci shirunta na nufin haka Ι—inne. A take gaba Ι—aya falon suka Ι—auki salati. Umm kam ido kawai ta tsurama Addah hawayenma sun tsaya cak. Hakama baba malam kallon Ζ™asa kawai yake ya gaza koda motsi. Abba Mustapha zai miΖ™e Hajjo ta hanashi, dan har yanzu ai ba'azo inda take buΖ™atar ba.

       Jay ne ya katse shirun nata da faΙ—in, “Ke muke saurare”. Yay maganar yana kallon agogon hannunsa.

        Da Ζ™yar Addah ta tsagaita kukanta ta cigaba da faΙ—in, “Na shaΖ™a masa maganine, irin wanda naso shaΖ™ama Nu'aymah aka samu akasi Rabi mai aikinki ta kusa rutsani, dan a lokacin kin tafi wanka Nu'aymah kin barta ta dinga leΖ™ata a Ι—aki, ni kuma saina aiketa domin aiwatar da Ζ™udirina, sai akai rashin sa'a kafin na shaΖ™ama yarinyar maganin Rabi ta shigo, motsin nufowarta bedroom. Wannan shine dalilin tsoratata na saketa a Ζ™asa kanta ya bugu. A take ta suma, ni kuma nai saurin Ι“oyewa dan kar rabi ta ganni gakuma kema naji yanda kika rikice a toilet kina Ζ™oΖ™arin fitowa. Sai da ta fita da gudu tana ihun kiranki saboda rikicewar da tayi ni kuma na samu na fita a sashen, daga baya na shigo cikin matan gidan muka shiga jajen yaya akai a tare. Kowa yama zata Nu'aymah ta rasu, sai dai hajjo ta matsa a kira likita. Zuwansane ya tabbatar mana da suma tayi, ba haka nasoba, amma lokacin da aka dawo da ita daga asibiti da tabbacin sanadin faΙ—uwar tata ta samu ciwo a Ζ™waΖ™walwa sai naji daΙ—i a raina saboda bushewar zuciya da huΙ—ubar sheΙ—an”. 

        “Likita ya fara Ι“usa zargin yaddota akai daga gado, kema kuma Firdausi kin tabbatarma kowa kina toilet kinji motsin shigowar mutum bedroom Ι—inki, sai dai kin zata Rabi ce, sannan kuma kinji sanda yarinyar ta faΙ—i Ζ™asa ta bugu. hakan yasa aka tuhumi Rabi, amma kuma saita rantse da iya gaskiyarta ba ita bace dan nama aiketane ta dawo,, tana shigowa taji Ζ™arar Nu'aymah datai sau Ι—aya kafin ta suma. Maigadi ne ya sake wanke Rabi a wajen kowa. Haka kawai na tsargi kaina akan karfa asirina ya tonu, dalilin da yasani saurin Ι—aukar mataki kenan na saka malamin da ya bani abinda zan shaΖ™ama yarinyar rufemin bakin kowa a gidan nan akama bar wani hasashe-hasashen son sanin yaya akai Nu'aymah ta faΙ—o a gadon?. Ban sake yunΖ™urin cutar da yarinyarba, dan a ganina ciwon data kamu da shi ya isa kai rayuwarta Ζ™arshe. Sai dai na saka an daΙ—e bakin mahaifarki yanda bazaki sake haihuwa ba. ALLAH kuwa ya amincemin baki sake samun ciki ba sai bayan haihuwar Nu'aymah da kusan shekaru biyar, hankalina ya sake tashi na nufi malamina. Saina iske ALLAH ya masa rasuwa. Lallai nayi gamo da tashin hankali na haΖ™iΖ™a a wannan lokacin, dan zan iya cemuku daga wannan lokacin ban sake samun malamin da yaymin aikin da yaci a kanku ba.......”

       “Mtsoww!! Malami ko boka dai”. Abban Abdallah ya faΙ—a a fusasce.

       Wani irin kallo Addah tai masa, sai kuma ta kwashe da dariya ta Ι—auke kanta kawai. Hakan da tayi kuwa yaba kowa mamaki. Amma sai babu wanda yayi magana. Har shima Abban Abdallah Ι—in bai sake cewa komaiba.

      Addah ta cigaba da faΙ—in, “Tunda na fahimci aikin malami ya daina tasiri sai na koma laΙ“e da son zubar da cikinki, to ALLAH ya tabbatar Muhammad sai ya shaΖ™i iskar duniya sai gashi kin haihu lafiya duk da ba haka nasoba. ta wannan hanyar laΙ“e ne nakejin duk wani abinda ya shafeku, dan duk da amintarmu firdausi ke mutumce mai zurfin ciki. Nakan faΙ—a miki sirrikana kai tsaye ko kema zaki warwaremin naki babu shamaki. Amma sai da na fara muku laΙ“e na fahimci kina bala'i-bala'in rainan hankali. Dan babu wani sirrinki mai muhimmanci da kike sanarmin sai Ζ™ananu kawai. Hakan yasa nima na Ι—auki Ι—ammarar bi dake ta yanda kikazo min”.

      Ta kai dubanta ga Abban Abdallah. Wanda a take mood Ι—insa ya canja ya wani zazzaro mata idanu kamar zai haΙ—iyeta da su. Murmushi tayi da Ι—auke kanta ta cigaba da faΙ—in, “A dalilin son halaka Muhammad na haΙ—u da babban makirin daya Ζ™ara faΙ—aΙ—a Ζ™waΖ™walwata akan Ζ™iyayyarki da zuri'arki. Dan ta sanadinsa ne wasan ya canja salo daga soyayyar Sooraj zuwa wani abun daban. Ba kowa nake nufiba sai Lurwan ga shinan”. Tai maganar tana nuna Abban Abdallah da tun fara maganar tata ya zabura zai miΖ™e a fusace amma Hajjo ta riΖ™oshi cikin fushi.

       Babu wanda bai zaro ido ba a jama'ar falon. Abban Abdallah ya sake zabura yana Ζ™oΖ™arin Ζ™wace hanunsa daga hajjo. “K baΖ™ar annamimiya, makira, azzaluma. dan ubanki sharrin naki da makirci yazo kainane kenan komai?”.

     Dariya sosai Addah tayi tana kallonsa, tace, “Lurwanu ai ka fini iya makirci, dan kaine malamina a wannan fanin kuwa. Da farko ta hanyar malami kawai nake samun nasara akan Firdausi, amma haΙ—uwata da kai ya sani hutawa daga zuwa wajen kowanne irin malami, dan kai kafi malamin hatsabibanci ma. Yau ranace mai kama da ranar hissabi, yanda nasan cewar ayyukanmu bazasu Ι“oyu ba a wannan rana dake jiranmu to ina tabbatar maka yau Ι—in nanma tun a duniya zan fara fallasasu dan kowa ya yaji. Dan wlhy yanda duniya tasan waceceni a yau, Ζ΄aΖ΄ana sukaji shukar danayi, mijina yaji, dolene kaima uwarka da yayanka da matarka da Ζ΄aΖ΄anka da sauran Ζ΄an uwanka susan kai wanene a cikinsu”.

       Sake zabura yay kanta kuwa da Ζ™arfin tuwo ya fisge hannunsa a cikin na hajjo, amma sai Dawood yay azamar shan gabansa da bindiga. “Ka kama girmanka, inba hakaba zan maka irin tabon dake a Ζ™afarta kaima. Ka nutsu ka riΖ™e sauran mutuncinka”.

      Jikin Abban Abdallah rawa yakeyi sosai, dan bai taΙ“a kawowa a ransa tone-tonen Addah zai iso kansaba musamman da yasan irin gargaΙ—in da yay mata kafin ya yarda su fara aiki tare, da kuma kalaman datai amfani dasu a yau wajen shimfiΙ—a labarinta. Yayi zaton zata rufa asirinsa ne.

            A hankali baba malam ya yunΖ™ura ya miΖ™e hawaye na sakko masa akan fuska. Yasa babbar rigarsa ya share sannan ya dubi jama'ar falon. “Inaga dan ALLAH mubar maganarnan gaba Ι—aya, wannan tone-tonen a ganina sam bashi da amfani. Sun aikata abinsu a Ι“oye sai mu barsu kawai da nauyinsu suje can su Ζ™arta. Bana buΖ™atar jin abinda Rudwan ya aikata ku barni haka, n.......”

      “Dolene kuwa kaji Ι—an malam, dan haka koma ka zauna”. Hajjo tai maganar cike da bada umarni. Baya iya Ζ™etare maganar mahaifiyarsa. dan haka ya koma jagwab ya zauna yana mai dafe kansa da hannaye biyu saboda jirin dake kwasarsa.

       Addah tai murmushi mai ciwo da cigaba da faΙ—in, “Lurwanu shiya canja tunanina daga fushin rasa masoyi zuwa na mallakar dukiya, dan huΙ—ubarsace ta fahimtar dani cewa ina dukan taiki ne kawai ina barin jaki, haukana kawai nake akan nafi Firdausi Ζ΄aΖ΄a nafita nasara yanzun. sai dai ashe dukiyar da mijinta ya mallaka a cikin Ζ΄an uwansa ta ninka wadda nawa mijin ke da shi sau fiye da bakwai. Kaso biyu na dukiyar gidan nan mallakarsace, kaso Ι—aya ne na mazajenmu da Hajjo. Gaba Ι—aya komai ya susuce min a lokacin nama nema rasa makamar tunani da hankalina. Amma sai ya dinga kwantarmin da hankali ta hanyar nunamin inhar zan taimakesa muyi aiki tare to lallai dukiyar baba malam zata koma Ζ™arΖ™ashin ikonmu ne. Nace masa ta yaya kenan?. Ya bani tabbacin ta hanyar Abdallah. Tunda akwai shaΖ™uwa sosai tsakanin Nu'aymah da Abdallah hakan na nufin nangaba kaΙ—an soyayya zata iya bayyana a tsakani duk da Ζ™uruciyarsu.  Dan bazaiyi wasaba wajen Ι—ora Abdallah akan matakin daya kamata game da Nu'aymah. Ɗari bisa Ι—ari na yarda da hakan a wancan lokacin. Saboda a yanda ya faΙ—aΙ—a min bayanansa na fahimci inba ta wannan hanyarba babu ta inda zamu mallaki wannan dukiyar. Wannan shine sanadin dunΖ™ulewarmu waje guda ni da Lurwan muka fara aiki tare. Amma wlhy kullum hankalinmu cikin Ζ™ara tashi yake gameda haΙ“aka da dukiyar Sooraj keyi abun tamkar roΖ™o. Shima kuma sake Ι—aukaka yakeyi fiye da sauran Ζ΄an uwansa akan ilimi da soyayyar mutane. Wanda Ι—aukakar tasa itama tana Ι—aya daga cikin abinda ke Ζ™ara Ι—ora Lurwan ga son cutar da shi. Haka muka cigaba da tafiya munama Sooraj *SARAN ƁOYE* da iyalinsa harma da duk wanda tsautsayi ya sakko a tarkonmu. Dan kuwa dai Rabi na Ι—aya daga cikinsu. Mun sakata tana mana wasu ayyukan akan dole wasu ko bama tasan muna amfani da ita munayiba musamman ta wayarta. Akwana a tashi mun cigaba da tafiya wataran muyi nasara akan aikinmu wataran su tsallake tarkonmu. A haka maganar soyayyar Abdallah da Nu'aymah ta fito, har takai Nasir yayi zuciya yabar gidan nan dan shima yana sonta. Da gaske Abdallah tsananin son Nu'aymah yakeyi, kamar yanda itama sonsa takeyi saboda tsananin shaΖ™uwar dake a tsakaninsu, amma a hankali muka fara canja tunanin Abdallah muna kwaΙ—aita masa dukiyar Sooraj. Tun yaron nan baya fahimtar mi muke nufi yana bijire mana harya hau kan hanya saboda Ι—aukesa da iyayensa sukayi zuwa wajensu. Dan mun fahimci zamansa da Firdausi ne ke mana illa komin masa huΙ—uba itake wargaza mana komai ta hanyar Ζ™aunar da take nuna masa ta gaskiya. Gaba Ι—aya mun tattara shirinmu ne akan auren Nu'aymah da Abdallah, shiyyasa duk likitan da aka samo da tabbacin zai mata aiki akan matsalarta sai munbi duk hanyar da zamubi wajan daΖ™ile hakan saboda wani likita ya tabbatar mana da wahala ai mata aikin nan ta tashi, mukuma burinmu muyi amfani da wannan damar sai bayan aurenta da Abdallah aimata aikin ta sheΖ™a mu samu abinda muke buΖ™ata, dan inhar muka gama da yarinyar kauda Ζ™aninta abune mai sauΖ™i a garemu. Har ALLAH yasa burinmu ya cika aka tsaida ranar auren Abdallah da Nu'aymah. Sai dai Abdallah baisan da shirinmu akan bayan aurensa da Nu'aymah so muke ta mutu ba. Wannan daga ni sai mahaifinsa ne muke shirinmu. Amma kash tarihi sai ya nema maimaita kansa tsakanin Adawiya da Nu'aymah tamkar ni da Firdausi. Dan kuwa dai Adawiya soyayyar Abdallah ce tai mata shigar sauri, tanata Ι“oyewa har takai ta gagara hakan lokacin data tabbatar zai kubuce mata. Na jima da fahimtar tana sonsa amma sai na Ι—auka kawai Ζ™uruciyace, sai da aka tsaida rana na fahimci yarinyata da gaske takeyi. Shine fa na samu Abban Abdallah da zancen kozamu samu mafita. Kai tsaye ya nunamin hakan bamai yuwuwa bane. Na harzuΖ™a matuΖ™a, dan ina buΖ™atar farin cikin Ζ΄aΖ΄ana, dan haka nace to kuwa sai dai kowa ya rasa. Da dai ya fahimci zan lalata komai bayan nasara dake tunkaromu sai ya lallasheni akan to na fahimcesa mana, mu bari ayi auren Nu'aymah da Abdallah. bayan komai ya faru Aymah ta mutu wajen aiki duk yanda zaiyi zaiyi a aurama Abdallah Adawiya. Na zauna nayi nazari sosai kafin na yarda da tsarinsa, dan nima a nawa hangen dukiyar da zamu mallaka Ι—in idan Abdallah ya auri Adawiya zata sake dawowa wajenane tunda jikokina sune zasu zama magadan Abdallah, daga haka muka cigaba da shirye-shiryen biki, sai dai kash ana gobe matakin cikar burinmu zai tabbata aka sace Nu'aymah. Ina mai tabbatar muku munfi iyayenta shiga tashin hankali a wannan lokacin, duk da ni Ι—aura auren Adawiya da Abdallah ya Ι—an min daΙ—in da har tashin hankalina ya sassautu. Amma bayyana muku kalar ruΙ—anin da Lurwan ya shiga a wannan ranar ba'a magana. Dan har sai da muka samu matsala kanmu ya rabu, ni haushina Ζ™iyayyar da Abdaallah ya nuna akan yarinyata, shi kuma Lurwan takaicinsa suΙ“ucewar damarmu. Daga baya dai muka dai-daita muka tafi shirya filan b. Iya bincike kuma munyi mun rasa gano yaya akai? ta wace hanya hakan ta faru? Sannan wanene ya aikata mana hakan? Da gaske mun fara zargin asirinmu ne ya tonu, sai dai har Ζ™ura ta lafa bamuga wani alamar hakanba sai hankalinmu yaΙ—an kwanta”.

        Karan farko Hajjo tai murmushi mai ciwo. Amma batace komaiba.

       Addah ta cigaba da faΙ—in. “Mun sake son Ζ™ulla auren Abdallah da Nu'aymah a karo na biyu. Sai kuma ga Naser ya dawo wai shima da soyayyar ta. Da alama kuma tayi shirin amsarsa. Sannan hajjo da Ananah sun goya masa baya a wannan karon. Shi kansa Sooraj mun fahimci so yake ya bama Naser Ι—in. Dan yanda suke takun saΖ™a da Abdallah baisa wani ya taΙ“a nuna goyon bayan Abdallah ba. Muna tsaka da neman mafita Abdallah ya saki Adawiya da Yusrah. Wannan saki shine ya kawo saΙ“ani mai girma a tsakaninmu. Dan nikam dai na tabbatar musu sai Abdallah ya maida Adawiya zan cigaba da basu goyon bayan cigaba da aiki tare. Amma sai Abdallah ya tubure, Ζ™arshema ya gudu ya bar gidan saboda takurawar da mukai masa ni da Abbansa. Sai dai ya tabbatar mana shifa da gaske yanason Nu'aymah ya kuma gaji da biye mana. Hankalinmu duk ya tashi, dan tabbas da gaske munga soyayyar yarinyar a cikin idanunsa. Mun kuma tabbatar da ya daina mana biyayya kenan”.

       “Ana tsaka da wannan rikicine ciwon da nake yawan ji ya takura mani, batare da sanin kowaba Mustapha ya kaini asibiti, a gwaje-gwajensu aka tabbatar mana da ina Ι—auke da ciwon kansar jini, ga kuma ciwon zuciya daya ci jikina sosai shima, wanda na tabbatar yanada alaΖ™a da hana kaina zaman lafiya danai akan Ζ™adarar da ban isa canjataba tunda rubutacciyace daga littafin Firdausi da Sooraj. Lallai jikina yayi sanyi, duk wani kaushina ya sulale, adadin watanni da likitanci sukai Ζ™iyasin bazan zartaba ya ruguza dukkan burikana da zalamata. A karan farko zuciyata ta kwaΙ—aitu da son yin Ζ™yautatawa ga Firdausi koda sau Ι—aya ne a rayuwata”. Kuka yaci Ζ™arfinta da tari. Yanzu kam gaba Ι—aya ta cire Ι—an-kwalin ta tare jinin dake fita da tarin, sai da ta tsagaita da Ζ™yar sannan ta cigaba da faΙ—in, 

         “Na roΖ™i Mustapha ya rufe zancen ciwona harga Ζ΄aΖ΄ana saboda banason Ι—agama kowa hankali, da farko bai aminceba, amma da naita lallaΙ“asa da hujjoji sai ya fahimta. Son kuΙ“utar Nu'aymah daga tarkon Lurwan ya sakani sakebin hanyar wani malami aka sakar mata jini. Ni da kaina na zuba garin magani a zoΙ“o na kai sashensu saboda a gabana Firdausi tasa Rabi ta dafama Sooraj zoΙ“i shima. sai nayi amfani da wannan damar kawai, ni na kwaΙ—aitama Rabi kaima Nu'aymah zoΙ“on Ι—aki lokacin dana shigo sashen da nufin neman cucumber. Sai na aiketa ta faΙ—oma Firdausi zan Ι—auki cucumber Ι—in. Tana fita na zuba maganin. Ina laΙ“e ta bayan kitchen lokacin da Rabi ta tafi kaima Nu'aymah zoΙ“o sai ma suka gamu a falo. Inajin Nu'aymah tace bazatasha zoΙ“on ba na shiga damuwa. Inata Ζ™ulla yaya zanyi kuma sai ga Rabi ta dawo kitchen Ι—in ta Ι—aura shayi. Dabarar bugar glass Ι—in Windown nayi, Rabi ta kalla wajen ta Ι—auke kai. Na sakeyi har sau biyu, shine ta leΖ™o, bataga komaiba da alama, shine na sake bugarsa. Shine fa tai tsaki ta fito domin dubawa. Nikuma nai amfani da wannan damar na shigo na zuba maganin na fita ta falo. Inda na wuce Aymah na kallo, sai  hankalinta bai kau kainaba harna fice da sauri. Na bada awa guda sannan na sake dawowa na laΙ“e jikin window Ι—inta, banbar wajenba harta fara ciwon ciki wanda na tabbatar magani ya fara aiki. Nabar wajen cike da farin ciki. Kafinma na isa sashena ihunta ya karaΙ—e gidan. Malam ya tabbatar min dama kowanne irin bincike likitoci zasuyi ciki kawai zasuyita gani ya zube a jikinta, hakanne kuma ya faru. Da wannan damar zancen ciki na sakeyin amfani na tursasa Hamisu bisa tsoratarwar zan kashe mahaifiyarsa ya kawo hotunan da ni na Ι—auki Yoohan da Nu'aymah su ba shiba, ba kuma Kubrah ba kamar yanda nasan Nu'aymah zatai zargi. Nayi amfani da Hamisu ne saboda kusancinsa dana sani da Sooraj sosai, na kuma san Sooraj ya yarda dashi. Duk da Sooraj da Firdausi sun bani tausayi sosai a wannan halin na danne zuciyata na cigaba da aikata shirina dan nasan shine kawai zai kuΙ“utar da Nu'aymah daga sharrin Lurwan akan kwaΙ—ayin dukiyar mahaifinta...............✍




Post a Comment

0 Comments