TOP HAUSA NOVELS atOptions = { 'key' : '20e08520dad54dbf6d9e963271

Saran Boye page 74

 πŸ’ƒπŸ»πŸ’ƒπŸ»πŸ’ƒπŸ»πŸ’ƒπŸ»πŸ’ƒπŸ»

TEAM----ZAFAFA BIYARπŸ”₯😘πŸ₯°πŸ˜


ALLAH ka gafartama iyayenmuπŸ˜­πŸ™πŸ».

[7/6, 9:39 AM] +234 913 412 2711: *_LITTAFIN nan na kuΙ—i ne. Dan girman ALLAH ki daure ki biya kafin ki karanta, idan kuma bazaki iya biya ba ki haΖ™ura domin ALLAH karki karanta. Idan kuma kin saya dan girman ALLAH karki yaΙ—a manaπŸ™πŸ»_*.



No. 74


............“Dabarata ta jingina ciki ga Nu'aymah, da kawo hotonta ita da Yoohan shine burina Sooraj yay fushi yace sai Yoohan ya auri Nu'aymah. Ta hakanne kawai aurenta da Abdallah ko Naseer zai gagara. Duk da bana zargin Nasir da komai, amma inhar shi Nu'aymah zata aura tsugunne bata Ζ™areba kenan. Amma indai ta auri Yoohan inada yaΖ™inin zai bata kariya. Saboda alwashinsa na ranar da aka kirashi akan wannan batun ya birgeni. Ko bayan babu raina ina fatan ya zama garkuwa ga ahalin Firdausi. Sannan Nu'aymah ma zata samu lafiya ta dalilinsa tunda shine likitan da dama aka basu Number sa muka sace ni da Lurwan. Alhmdllh naci nasara, dan kuwa da bakinsa ya furta son auren Nu'aymah, duk da Sooraj bai bashi goyon bayaba a lokacin saboda jin nauyin Ζ΄an uwansa akan su Abdallah na tabbatar yanason bashi. Lurwan ya shiga ruΙ—anin ganin zai rasa dama ta biyu, hakan ne ya sakashi sake dawowa gareni mu haΙ—a kai a wannan karonma. Ya kuma bani haΖ™uri da tabbacin zaisa Abdallah ya maida aurensa da Adawiya da zarar anyi aurensa da Nu'aymah. Na nuna masa na amince dan na samu a gama maganar auren Nu'aymah da Yahya cikin kwanciyar hankali. Daga haka na cigaba da gayama ALLAH dan agareshi kawai nake hangen samuwar nasarar kubutar da Nu'aymah daga tarkon Lurwan. Hidimar aurar da Ζ΄aΖ΄a kawai nake a zahiri, a baΙ—ini kuwa ba wannan bane a gabana sam, shiyyasa na samu Firdausi da shawarar duk yanda zatayi tayi kar Sooraj ya bama Abdallah ko Nasir Nu'aymah, gara a auramata Yahya bisa wasu dalilan dana lissafa mata a lokacin waΙ—anda Alhmdllh sunyi tasiri a gareta. Sai da ina shirin fitowane naga Sooraj tsaye bayanmu alamar yaji komai da muka tattauna kenan. Hakan yamun dadi, dan insha ALLAHU koba komai inada yaΖ™inin samun nasara”.

      Ta share hakawayenta ga murmushi a fuskarta. Cigaba tai da faΙ—in,

       Jin tabbatuwar Ι—aura auren Nu'aymah da Yahya shine nasarata ta farko da kobayan nabar duniya inason Ζ΄aΖ΄ana su tuna suyi farin cikin aikin alkairi dana taΙ“a Ζ™ullawa a rayuwata ta zaman gidan nan. Ko murnanr aurar da Ζ΄aΖ΄ana guda biyu a ranar banyi murnarsa da tsananin farin ciki ba kamar yanda nayi na Nu'aymah. Amma a baΙ—ini nabar wannan nasarar tawa. A zahiri kuwa na shiga jerin masu shiga Ζ™ololuwar tashin hankali kamar su Abdallah da Lurwan da rayuwarsu ke a gigice. Dan wlhy aranar da aka Ι—aura wannan auren kaΙ—an ya hana zuciyar Lurwan bugawa a gidan nan. Ya kuma sake Ι—aukar alwashi kala-kala akan koma ta halin Ζ™aΖ™a saiya samu cikar burinsa. Wannan furici nasane ya sakani saka Ζ™anwata bin Ζ΄an tawagar kai amarya. Sai da na tabbatar Nu'aymah ta shiga Ι—akin mijinta lafiya ta hanyar ji daga gareta sannan hankalina ya kwanta. Duk da na tausayama yarinyar inda Ζ™addara ta jefata. Amma sai nai mata fatan samun kariyar UBANGIJI da nasarar canjasu dalilin shigowar tata cikinsu. Daga haka na cigaba da Ι“oyayyar jiyyar da mijinane kawai yasan inayi da duΖ™ufa neman gafarar UBANGIJINA ko zan samu sassaucin raguwar zunubaina. Abinda yasa nabiku Austria ganin Nu'aymah saboda kozan samu na nema gafarartane. Ban saniba ko kafin ta dawo Ζ™asar ni na rasa raina. Ta Ι—ayan gefen kuma inason sakama Lurwan idone. dan a yanzu na daina sanin komai daga shirinsa saboda ya fahimci bana tare dasu a yanzu. Ko amincewa da zaman Adawiya da nai gidansa tanamin aikin sakamasa idone. Dan duk wani motsinsa itace ke kirana tana sanarmin batare da ita kanta tasan aiki takeminba dan ban fito fili na sanar mata manufataba”.

      Wannan shine labarina, shine Ζ™addarata, shine kuma son zuciyar SARAN ƁOYE dana aikata muku Firdausi, nasan bazaki taΙ“a yafeminba ke da zuri'arki, shiyyasama bazan matsaba wajen neman yafiyarku. Kai koma ke kin yafemin ALLAH bazai yafemin ba, dan nasan na cutar daku iya matuΖ™ar gaya ta hanyar SARAN ƁOYE. na aminta ku kaini kowace irin kotu a yankemin hukuncin daya dace dani kafin naje na fuskanci babbar shari'ata ga babban alΖ™ali”.

     Ta Ζ™are maganar da fara tari mai tdanani. Sosai yanda take tarin guda gudan jini na faΙ—owa ya tada hankalin kowa a falon. Umm ta matsa gareta ta riΖ™eta sosai jikinta tana kuka. Da Ζ™yar aka samu tarin ya lafa. Duk da Yoohan najin zafinta har yanzu, dan shi baiji wani tausayin taba, duk da Ζ™oΖ™arin Ζ™ulla aurensa da tai da Nu'aymah a Ζ™arshen Ι“arnakun data tafka, amma sai ya bada shawarar a kwantar da ita zata samu sassauci daga yawan tarin. Da shawararsa akai amfani wajen kawo Ζ™aramar katifa aka kwantar da ita Ι—in. Aiko sai tarin ya lafa sosai.

     Murmushi tayi tana kallonsa, murya na rawa tace, “Nagode Yahya, ALLAH ya azurtaku da Ζ΄aΖ΄a nagari da zasuji Ζ™anku, ALLAH ya sauki Nu'aymah lafiya naga gudan jininku kafin nabar duniya”.

     Uffan baiceba, baima nuna yaji mita faΙ—aba, amma jama'ar falon sun amsa mata da amin, duk da wasuma irin zuciyar Yoohan garesu basuji tausayin nataba.


          Abban Abdallah da keji kamar ya tashi ya Ζ™arasa rayuwarta saboda zuciya data kumesa ya yunΖ™ura zaiyi magana Hajjo ta dakatar da shi ta shanyar Ι—aga masa hannu. Dole kuwa ya koma ya zauna yana zare idanu.

        Tai gyaran murya sannan ta gyara Ζ™afarta mai ciwo da dubansu Ι—aya bayan Ι—aya ta fara faΙ—in, “Karma ka wahal da kanka wajen Ζ™aryata abinda duk Fauza ta faΙ—a Lurwanu. Idan bakai tunanin ana kallonku ba yau zan sanar maka cewar na jima da fahimtar kai da ita su wanene a cikinmu. Na barkune saboda na muku talalar zuwan wannan ranar. Na jima ina zargin akwai wani abu a zuciyar Lurwanu game da Ι—an uwansa, dan yasha kawomin sukarsa akan miyasa kaza da kaza dole sai da umarnin Ι—an malam akeyi a gidan nan?, sai dai ina nuna masa Ι“acin rai. Amma ban sake tabbatarwa ba sai bayan tsaida ranar auren Abdullahi da Zainabu. Da kunnena naji dukkan abinda kuka tattauna akan soyayyar da Adawiya kema Abdullahi, tare da shirinku na bayan mutuwar Zainabu zai aureta. Hankalina ya tashi, dan zan iya cewa wannan shi e sanadin girmama samuwar hawan jini na ma. Na riΖ™e komai a raina na kasa faΙ—a har Ζ΄ar uwata tazo diba ni (Ananah) banso faΙ—a mataba. amma na fahimci dolene na samu shawara daga wani kafin lokaci ya Ζ™ure. Dan wannan abune mai matuΖ™ar sarΖ™aΖ™iya. haka na samu lokaci a wani dare mukai maganar. Itama hankalinta yayi Ζ™ololuwar tashi dajin wnanan zance. Itace ta kawo shawarar ai tunda SARAN ƁOYE kukeyi muma yakamata mubi ta ZAGON ƘASA mu kamaku a hannu dumu-dumu. Itace ta kawo shawarar sace Zainabu ranar daren aurenta, dan hakanne kawai zai wargaza auren cikin sauΖ™i. A cikin shirinmu Ameer ya shigo rayuwar Zainabu matsayin abokin Abdullahi. Ameer kuwa abokin Naser ne, dan Naser shine mukaba aikin a hannunsa. Nice da kaina na shiga na haΙ—o kayan Zainabu a Ι—akinta, na kuma jajjefa wasu ta taga. Ina cikin yi Yusrah ta shigo Ι—akin da alama banΙ—aki zata shiga. Na tabbatar taga mutum, sai dai ban saniba kota gane waye ko bata ganeba. Abdullahi yaso lalata mana shiri a ranar saboda jan ra'ayin Zainabu da yay tayi akan suyi hira. Sai dai kuma ta dalilin Adawiya hirar batai tsaho ba. Naser ya samu damar Ι—auke Zainabu ya kaita wani gida. Bamu dawo da itaba sai bayan sati biyu. Daga haka muka cigaba da bibiyar duk wani taku naku. Hatta da sace Number likitan da zaima Zainabu aiki naji a raina wani a cikinkune ya saceta, sai dai banida hujja shiyyasa nai shiru. Ina kan sani na amince da aurama Abdallah Adawiya saboda Ι—ana tarkon farko a gareku, inason kuma tabbatar da hannun Abdallah akan shirinku, kokuwa kuna amfani da shi ne kawai batare dashi kansa ya sani ba?. Na kuma hana Yusrah tarewa dan dama bazan yarda ta tare Ι—inba. Tafiya da Zainabu Umrah yanada nasaba da son sake tabbatar da komai. Na kuma tabbatar Ι—in. Waya da aka Ι—agama Khadijah na hana Abdullahi zuwa Nigeria duk a cikin shirinmu ne. Munsa Nasiru ya dawo rayuwar Zainabu ne daman dan ya sake wargaza magar auren da Abdallah keta naci da son sake ganin ya Ζ™ullu tsakaninsa da ita. Da kuma sanin da nai duk cikin shirinkune”.. 

        “Maman Aaida data zama Ζ™awar Adawiya a saudia duk a cikin shirinmune itama. Mune muka sakata samun kusanci da Adawiya da Ι—orata mataki-matakin kasancewa da Abdallah, a tunaninmu ko zaku dawo hayyacinku ku yarda da Ζ™addara. Amma sai kuka sake tura kanku a cikin ramuka. A tarayyar maman Aaida da Adawiya ne ya bamu damar sake fahimtar bada sanin Abdallah kuke wani abunba. Dan ba komai kuke sanar masa akan shirinku ba, sannan lallai da gaske yana son Zainabu duk da ya raba hankalinsa biyu akan soyayyarta da dukiyar mahaifinta da kuka Ζ™waΙ—aita masa a rai. Ta kuma hakane muka fahimci banzar sana'a da Abdallah yake Ζ™oΖ™arin jefa kansa a ciki. Amma Alhmdllh munyi Ζ™oΖ™arin maidosa hanya ta dalilin mijin maman Aaida Ι—in, wanda ta hannunsa mukejin duk wani motsin Abdallah a yanzu haka. Maganar cikin Zainabu shine ya hautsina min tunani, saboda batare kukai aikinba yasa ban fahimci komaiba a ciki ba, duk da ina zargin kuΙ—inne duk da haka. Koda na tabbatar Zainabu takai mutuncinta gidan aure wannan ruΙ—anin na maganar ciki bai barniba sai yanzu da Fauza ta warware komai akan samuwar ciki da fitarsa. Na kai Uwaliya aiki Abuja ne dama dan Lurwanu yay yunΖ™urin yin amfani da ita kamar yanda Nasiru ya gano mana hanyar da sukebi wajen aamfani da Rabi itama. Na tabbatar alwashin da yahya ya Ι—auka akan gano ko wanene bazai tashi a banzaba. Bakuma zai samu sauΖ™in ganowarba sai da wani a tsakani. Shiyyasa na tura Uwaliya ta fara sauka gidan Lurwanu ta kwana biyu sannan aka kaita wajen Zainabu. Ita kanta batasan amfani zamuyi da itaba, na Ι“oyene saboda fahimtar idanunta a buΙ—e suke dasan kuΙ—u itama. Ko nawa Lurwanu ya bata lallai zata amince tai masa aikin daya buΖ™ata akan Zainabu. Ankoyi sa'a shirinmu ya tafi dai-dai saboda Nasiru ma mutumne mai Ζ™waΖ™walwa da hikima. Hatta da yawan shigowa Najeriya da Abdallah ke yawan yi suna ganawa da Lurwanu duk mun sani dan duk inda yasa Ζ™afa Nasiru na biye da shi batare da yasani ba. Kai hatta binmu da Abdallah yayi Ζ™asar da akaima Zainabu aiki nasani. Dan ko a randa Yahya ya gansu suna magana shi da Lurwanu nima na gansu, sanin da nayi babu ta hanyar da zasu iya cutar da Zainabu saboda tsaron da take samu a wajen yasa na watsar da al'amarinsu. A yanzu haka mijin maman Aaida shine ya taso mana Ζ™eyar Abdallah zuwa Najeriya harya halarci wannan bikin duk da yazone a makare”.

       Ta Ζ™are maganar da nuna inda Abdallah ke zaune kansa a duΖ™e tamkar munafuki. Harga ALLAH da yawan mutanen dake falonma sai yanzu sukasan da zamansa a falon. Hajjo ta sake gyara zamanta tana duban kowa.

       “Nasan wasu zasuce miyasa duk nasan wannan amma na Ι“oye matsayina na mahaifiya ga waΙ—an nan yara su duka?. Amsarku itace duk da ni mahaifiyace a garesu fitowa da lamarin kai tsaye dasa sabuwar fitinace da zatafi wadda muke ciki girmama. Dan inhar da tun a wancan lokacin na fiddo komai zasu kare kansu akan ba haka bane, su jefa zuciyarmu a ruΙ—ani mu duka kokuma su canja salo, ko komai ya Ι“aci duniya tasan halin da muke a ciki maΖ™iyanmu dake a waje su sami Ζ™ofar yin kutse cikin wannan zuri'a su Ζ™arasa Ι“arar da sauran abinda ya rage daga garemu. ƘyaΖ™yΖ™yawar rayuwar da aka gina tsahon shekaru zata wargatse ta lalace kowa ya fita a hayyacinsa. Idan hakan ta kasance banci riba ba. Sannan wahalar da malam ya sha akan son gina zuri'arsa baici riba ba kenan shima. Dukansu ni na haifesu, tun a Ζ™uruciya nasan halin kowannensu. Dama can Lurwanu hatsabibine tun yana Ζ™anΖ™aninsa, a cikin Ζ΄an uwan nan nasa babu wanda baisha wahalarsaba. Kaifin addu'a ne kawai ya ladabtar da shi, sai kuma kawaici da iya zama da su da Ι—an uwansu yayi. Na yarda inhar ka samu Ζ™yaΖ™yΖ™yawar tushiya a cikin yabanyarka da izinin ALLAH zaka azurta da Ζ™yaΖ™yΖ™yawar albarka. Kasancewar Ι—an malam Ι—a nagari, mai haΖ™uri da kawaici, mai juriya da riΖ™e girmansa matsayin babba ga Ζ΄an uwansa shine ya taimaki wannan zuri'a da kaiwa haka batare da mutanen waje sunyi tunanin samun Ι“arakar shigowa cikinmu su wargazamuba. ALLAH yayima Ι—an malam baiwa da Ζ™yautar abubuwa da yawa. Ilimi, hankali, dattako, dukiya, sanin ya kamata, nasaba. Sai dai hakan ba yana nufin zai more rayuwarsa Ι—ari bisa Ι—ari ba tunda ya haΙ—a komai. Shiyyasa ALLAH ya jarabcesa da atsabibancin Lurwanu dana matar Ι—an uwansa Mustapha. Suka dinga wajiga rayuwarsa saboda UBANGIJI ya gwada Ζ™arfin imaninsa. Koni da nake mahaifiya a garesa inajin sha'awar koyi da halayensa na haΖ™uri da juriya duk da zuciyarsa na Ζ™onuwa shi da matarsa da Ζ΄aΖ΄ansu. Wannan kawaicin da uziri shine ya kaimu ga matakin nasarar da a yau gashi su da sukecin dunduniyar sane a gabanmu suna faΙ—in tsiyatakun da suka aikata da bakinsu, miyafi wannan nasarar daΙ—i ga bawa kuwa?”.

       Abban Adawiya ya share hawaye da fadin, “Babu inna, wlhy babu makamancin wannan nasara kuwa, dan hakan yana nuna mana duk mai haΖ™uri da tsayawa akan gaskiya, da adalci gana Ζ™asa da shi, ma'abocin bautar UBANGIJI, ALLAH bazai taΙ“a taΙ“ar da shi ba, ALLAH bazai taΙ“a Ζ™asΖ™antar da shi ba. ALLAH bazai taΙ“a wulaΖ™anta rayuwarsa a hannun azzalumai ba. Ni shaidane akan hakan, dan Lurwan yaso jan ra'ayina sosai akan lamarin Yaya, kullum zancensa shine Yaya cutarmu yake a Ι“oye. wai tayayama za'ai ace a raba mana gado tare, amma yazo ya fimu komai. Yafi kowa kaso mai tsoka a duka kamfanonin mu. Ga wasu harkoki da yakeyi kuma a gefe masu bala'in bashi kuΙ—i. Sannan kuma wai ai muduka munada ilimin addini amma tayaya za'ace kowa yafi sonsa da Ζ™aunarsa dajin maganarsa. Hatta mahaifiyarmu sai abinda Yaya yace takeyi a gidannan. Acewarsa wai Yaya ya asirce kowane kawai amma yake fakewa da malanta. Da farko na fara bin ra'ayinsa. Sai dai ba'ai nisaba ALLAH ya soni da rahamarsa ya fargar dani, danni dai ban taΙ“a ganin wani abu saΙ“anin Ζ™yautatawa ga yaya ba. Da kuΙ—insa na gado ya tsaya mana mukai karatu duk da kuwa muma muna dasu. Da kuΙ—insa na gado ya dinga mana hidimar rayuwa tamkar mahaifi. Idan mukai kuka shima sai kaga Ζ™walla a idanunsa. Idan mukai ciwo shima sai kaga raΙ—aΙ—in a fuskarsa. Idan mukai dariya sai kuga tashi fuskar faΙ—aΙ—e da murmushi mai tsada. Shine ya nuna mana hanyar tashi mu nema na kanmu, dan shine ya fara shan wahalar kafa dukkan kasuwancin da ayanzu sune suke riΖ™e da duk wani motsinmu. Shine ya tsaya akanmu mukai karatu tuΖ™uri bayan ya tattare martabar mahaifinmu ya riΖ™e mana bai bada Ζ™ofar da zamuyi sakacin da zata kufce mana ba. To miyasa son zuciya zaisa zamuyi sakaci ya sargafe tunaninmu?.  Hakan yasani janye jikina daga wannan mummunar a Ζ™idar naita istigifari akan zargin da aka sakani nai masa babu gaira babu dalili. Ashe ya koma sun Ζ™ulle da matata suna cutama yaya da zuri'arsa da basujiba basu ganiba. Minene laifin waΙ—an nan Ζ™ananun yaran da basuma gama sanin rayuwarba balle daΙ—inta. Basai nace komaiba, dan Fauza azabarma da kike ciki ta isheki. kai ko Lurwanu ka jira naka sakamakon kaima, dan duk wanda yaci zalin gwani rabbi zai saka masa da alkairi a duniya ko a lahira”.

        Abba Musbahu yace, “Tabbas haka zancenka yake Yaya Mustapha. Dan koni ma yaso jan ra'ayina. Sai dai fa ka sanni ni, a zuwan farko na shata masa layi duk da kasancewar sa yayana. Shine dalilin da yasa zama waje Ι—aya a Lagos ya nema gagararmu sai da yabi ya lallaΙ“a yaya malam ta Ζ™arΖ™ashin Ζ™asa aka maidasa Abuja aka buΙ—e masa company wanda ALLAH kaΙ—ai yasan irin Ι“arnar da yake a cikinsa shi da abokan aikin nasa. Domin a duk lissafin Ζ™arshen shekara idan mukayi sai mun tsamo yawan cuwa-cuwa da akai da kuΙ—aΙ—en company. Shi Yaya cayake daga ma'aikatanne. Niko nasan Yaya Rudwan ne dama wlhy. Nayi shiarune kawai dan ina fatan Yaya Malam ya kamashi da hannunsa dumu-dumu. To ashe aikin nasama ba anan ya tsayaba duk bala'in da ake kunnama Yaya malam da Ζ΄an Ζ΄aΖ΄ansa biyu da suka rage yanada hannu aciki. Wlhy ko alhakin Ζ™ananun yaran nan bazai barku ku zauna lafiya ba balle kuma haΖ™Ζ™in yaya malam da Umm-Muhammad da a kullum burinsu su Ζ™yautata rayuwar Ζ΄aΖ΄anmu a gidan nan. KaΙ—anma kuka fara gani yanzu kuma”.

          Momyn Abdallah daketa kuka tun Ι—azun tace, “Lallaikam yanzu suka fara gani Musbahu. Wannan wace irin cin amanace haka? Wane kalar son zuciya ce?. Ba yaya kaΙ—ai kuka cutarba ai, muma kammu iyalanku kun cutar damu, kun shiga haΖ™Ζ™inmu. Wace irin ni'ima ce ALLAH bai baku ba a rayuwa amma ku gaza gode masa har sai kun Ι—aura Ι—ammarar shiga haΖ™Ζ™in wani. Alhalin dukiyar da kukema zarin ma kunfi mai ita amfana da ita ku da iyalanku. Wai miyasa Ι—an adam Ι—in da ALLAH yayma ni'ima shike fin tsaurin idon rashin gode masa? ALLAH ya baku ilimi alhalin ga wasu can jahilai ko yanda zasu bauta masa basu saniba. Ya baku lafiya, ga wasu can a gadon asibiti kwance basu da kuΙ—in neman lafiyar. Ya baku muhallin zama. Ga wasu can suna raΙ“e-raΙ“e basu da ko kangon da zasu raΙ“a. Ya muku sutura. Ga wasu can tufafin da zasusa su rufe tsiraicinsu bai wadacesu ba. Ya baku mutunci da daraja a idon duniya, bayan akwai dubunku da suka fiku shekaru a Ζ™asΖ™ance. Ya baku dukiyar da bama kuda iyalanku ba, waΙ—anda suka raΙ“u da ku zaku iya ciyar da mutum sama da Ι—ari a kowanne yini. Ga wasu can iyalansuma basa iya wadatawa. Ya azurtaku da Ζ΄aΖ΄a maza da mata,  ga wasu can suna nema da miliyoyin kuΙ—aΙ—e basu samu ba. Ya azurtaku da iyaye na gari, bayan ga wasu can iyayen nasu a gidajen baΙ—ala. Duk waΙ—an nan ni'imon kuka gagara godema ALLAH a kansu, to mikuke jira UBANGIJI ya muku kafin ku gode masan? Mi kuke nema kukuwa a duniya bayan duk waΙ—an nan tarin ni'imomin da yay muku. Bafa kunfi waΙ—anda basu da shi bane, ba kuma tsoronku yasa aka baku ba. Ba kuma Ζ™oΖ™arin ibadar kuce tasa aka baku ba. Kai jama'a kaicon hannu mai butilcin amsa ga mai bashi. Kaicon zuciya mai baΖ™in cikin cigaban mai Ζ™yautata mata, Kaiconku Rudwan, tabbas bazan yafe muku Ι—oramin yaro akan mummunar aΖ™ida da kukayiba........”

      Kuka ya sarΖ™eta ta kasa cigaba da magana. Shi dai Abban Abdallah ya kasa koda Ζ™waΖ™waran motsi, kansa duΖ™e a Ζ™asa ya gagara kallon kowa. hakan yasa babu wanda zai iya cewa ga a yanayin da yake.

       Baba malam ma dai kansa a Ζ™asa yake duΖ™e. Babu mai shaida yanayinsa. Umm kam ganin al'amarin take tamkar a mafarki zuwa anjima zata farka. Zuciyarta ta kasa gaskata komai akan Abban Abdallah da Fauza. Mutanen da sukafi kowa kusanci da su a gidan. Kai jama'a duniya ina zaki kaimu?.....

      Jin kowa bai Ζ™ara cewa komai ba yasa Jay yin gyaran murya. Kusan duk kallonsa sukayi. Ya furzar da numfashi na takaici da faΙ—in, “To inaga idan kun gama da su zamu kaisu station mu haΙ—a bayanansu sai mu miΖ™asu kotu su amshi hukunci kamar yanda shari'a ta tanadar”.

       Tari Addah ta fara kaΙ—an-kaΙ—an, hakanne ya saka baba malam Ι—agowa ya kalleta ya maida dubansa ga Jay. “Muhammad Jawaad mubar zancen zuwa kotu kaji. Ita wannan kuma miya rage mata a duniyarma gaba Ι—aya. Ai wannan izayar da take ciki kawai ta isheta izina. Sai dai mu taimaketa mu miΖ™ata asibiti kawai....”

     Murmushi Jay yayi yana jinjina kai. “Duk da haka malam ai ya kamata su fuskanci shari'a kodan hakan ya zama ilimi ga Ζ΄an baya masu sha'awar sake aikatawa. Duk da tana cikin halin ciwo bashi ke nuna zata mutu ba, mutuwa ta ALLAH ce, takanzo a sanda taso ga wanda taso. Dan haka zamuje asibitin taga likita amma bisa Ζ™arΖ™ashin kulawar hukuma. Shi ko zamu wuce da shi station”. Ya Ζ™are maganar yana nuna inda Abban Abdallah yake zaune.

      Baba malam zai sake magana Hajjo ta katsesa da cewar, “Ɗan malam hakan shine dai-dai kuma ya kamata. Kaga idanma da mai sha'awar aikatawa a nan gaba sai ya bada himma”.

      Tarin Addah daya Ζ™ara Ζ™arfine ya sakasu duk maida hankalinsu gareta. Da wannan damar Abban Abdallah ya samu ya sulale a hankali yabar sashen. Sauran jami'an dake a waje basusan yaya aka Ζ™areba shiyyasa basu hana Abban Abdallah bi ta gabansuba ya wuce sashensa yaje ya haΙ—a duk wasu abubuwa nasa masu muhimmanci ya zuba a Ζ™aramar jikka ya fito. A gaban jami'an ya shiga motarsa maigadi ya buΙ—e masa gate ya fita batare da shima yasan mike faruwa ba. 

       Daga ciki ma babu wanda ya farga da rashinsa sai bayan an fito da Addah daketa faman zuba aman jini aka saka a mota domin kaita asibiti. Suna wucewa su Jay suka koma kan Abban Abdallah sai yace ku Ι—aukeni inda kuka ajiye. A take suka hau cigiyarsa a lungu da saΖ™o na gidan, sai daga baya sukeji daga bakin maigadi cewar ya fita a mota tun kusan mintuna talatin da suka shuΙ—e.

      A razane Jay yace, “What?!!, shine kuka barsa saboda baku da hankali?!”. Yay maganar wa yaransa. Duk rawa jikinsu ya kamayi suka hau rantse-rantse su basusan mai laifi bane. Ai kota kansu Jay baibiba ya shiga motarsa shi da Bily da Little. Suma duk suka shiga a wacce sukazo. sai da suka tambayi maigadi motar daya fita a ciki da lambarta sannan suka fice a guje.

      Wayar Jabeer Jay ya kira, yana Ι—agawa ya ce, “Jabeer inason a baza zami'ai a kowacce hanyar fita garin kano domin tsaidamin mota mai Number..... Ruwan toka”.

     Jabeer na amsa masa ya yanke kiran, C.P ya kira shima dan ya taimakesu.


__________★★


       A gidan su Nu'aymah kam musalta muku halin da suke ciki Ι“ata lokacine. Dan motocin su Jay na fita a gidan Umm ta yanke jiki ta faΙ—i. Hakama Malam Ζ™arami shiΙ—e musu yayi. Ga kukan da su Adawiya keyi ya taru ya Ζ™ara Ι—aga musu hankali. Baba malam kansa dauriya kawai yakeyi dan gaba Ι—aya jinsa yake kamar kansa zai tarwatse dan ciwo. Gashi su Yoohan sun wuce da Addah asibiti. Hakan yasa dole aka kwashi su Umm ma zuwa asibitin.


   Ζangaren Abban Abdallah kam tunda ya fito anguwarsu kai tsaye hanyar Katsina ya Ι—auka, shi kansa baisan mi yake shirin aikatawaba. Ceton kansa ko gudun kunya? Ko tsoro?. Gudu ya ke na hauka babu wasa a cikinsa. Musamman daya kasance ta gefe-gefen gari yake tafiyar, dan bai yarda yabi ta cikin gariba sam. Yana fara Ι—aukar hanyar Ktn bayan ya gota Dawanau kaΙ—an ko mintuna goma baiyiba ya ga motar Ζ΄an sanda na binsa a baya. A take ya Ζ™ara Ζ™arfin gudun motar tamkar ya manta da kasancewarsa Dattijo. Abu kamar a film suka fara rere tsakaninsa da jami'ai.

       ALLAH sarki rayuwa, duk iyawarka baka isa zarce Ζ™addarar UBANGIJI ba. Dan kuwa dai wannan Ζ΄ar tsere na Abban Abdallah da Ζ΄an sanda sunansa gudu akan igiyar Ζ™addara. Dan kuwa bisa tsautsayi sukau taho mu gama da wata mota dake nufo cikin kano. A take waccan tayi gefen titi, shiko ta Abban Abdallah sai ta kife ta fara wuntsil-wuntsil daga titi ya gangara cikin gona. Tun suna jin yanda yake neman Ι—aukin UBANGIJI har sukaji tsit, motar kuma ta bugi bishiyar dalbejiya ta tsaya cak.

      Cikin sauri Ζ΄an sandan da dama tuni sun fito a mota suka nufi motar domin bashi taimako. Da Ζ™yar kuwa akayi kama-kamar Ι—aga motar aka zarosa a ciki. Gaba Ι—aya jikinsa yayi face-face da jini har ba'a iya gane inane ya bugu koma yanada rai ko ya mutu. Kasancewar sun kira sun sanar sai ogansu ya basu umarnin maza su Ι—akkosa su dawo cikin kano asibiti. Bisa wannan umarnin ya sakasu Ι—akkosa suka juyo a guje.

    Kai tsaye babban asibiti suka nufa, cikin amincin ALLAH kuma akai sa'a can aka kai Addah da su Umm suma. Su baba Malam na tsaka da tashin hankalin abinda ya faru sabon labari akan haΙ—arin Abban Abdallah yazo musu. A take na gida dana asibitin suka sake harmutsewa. 

     A yanda Yoohan yaga al'amarin ya kasance sai da yaji nadamar shigewa gaba wajen wannan bankaΙ—e-bankaΙ—e. Sai gashi da idanunsa ya ga baba malam na rusar kuka. Nu'aymah kam ai sai allurar barci ya danna mata saboda yanda ta birkice kamar dai Ζ™waΖ™walwar ta bata gama dawowa dai-dai ba.

      Lallai wannan ranace da waΙ—aΙ—an nan ahali bazasu taΙ“a mantawa da itaba a jerin tarihinsu. SauΖ™insu ma har yanzu ainahin labarin bai fita kunnuwan jama'ar gariba. Sai dai kawai ana maganar Sheikh Rudwan Hashim jibiya yayi Accident a hanyarsa ta zuwa Ktn yanzu babu jimawa. A take mutane suka shiga jera masa addu'ar ALLAH ya tashi kafaΙ—a, musamman ma mabiyansa.

      Zan iya ce muku yanda wannan ahali sukaga yinin wannan rana haka sukaga dare. Duk da kuwa Alhmdllh zuwa dare an tabbatar da Abban Abdallah bai rasuba. Ya dai samu karaya a kafaΙ—unsa duka biyu da kafafu. Sai manyan raunika da sukai masa kaca-kaca da jiki. Itako Addah barci suka sakata yi. Umm ma Alhmdllh ta farfaΙ—o ita da malam Ζ™arami. Hakama Nu'aymah ta farka.

         Sai kusan tara na dare suka bar asibitin, ba kuma a barsu sunga Abban Abdallah ba dai. Yoohan da kansa ya fiddo Nu'aymah da ga Ι—akin office Ι—insa daya sakata barci. Ananah ta taimaka mata suka Ζ™arasa shiga mota. Baba malam yaso su Yoohan su bisu can gidan su kwana amma suka bashi haΖ™uri akan zasu zauna anan asibitin ne. Badan yaso ba ya barsu.


       Yoohan na ganin motocinsu sun gama wucewa ya sauke ajiyar zuciya mai kauri, A Ι—aya daga kujerun dake a waje ya zauna hannayensa duka dafe da kansa. Sai yanzu komai ke dawo masa a Ζ™waΖ™walwa tamkar almara. Dan Ι—azun su Addah na bayani ne little na fassara musu shi da Umar, duk da shi yana Ι—an jin hausarma kaΙ—an-kaΙ—an yanzun. 

      Kusa da shi Umar yazo ya zauna shima yana sauke nasa ajiyar zuciyar. Yoohan bai motsaba balle ya kallesa. Shima sai bai damuba ya fara magana a hankali. “Haka mafi yawancin mutanen da suka samu Ι—aukaka suke. Sai kaga na nesa da su na matuΖ™ar sonsu da begen kasancewa da su. Amma waΙ—anda ke tare da su mafi yawancinsu ba son gaskiya suke musu ba. Ƙaso Ι—aya bisa uku a ciki zaka samu suna musu Ζ™auna ta tsakani da ALLAH. Kaso biyun kuwa sai kaga suna raΙ“e da sune bisa wannan Ι—aukakar da ALLAH yay musu. A zahiri kuwa su zugasu da nunama duniya babu kamarsu, a baΙ—ini sune masu musu SARAN ƁOYE. lallai waΙ—anan mutanen masu zagon Ζ™asa suna Ι—aya daga cikin jarabawar masu mafi yawan Ι—aukaka”.

      Ajiyar zuciya Yoohan ya sake saukewa. Ya Ι—ago ya dubi Umar a karon farko, idanunsa sunyi jajur. Ga barci ga yunwa ga gajiya. Shi kansa Umar Ι—in a galabaice ya ke. “Zancenka haka yake Umar, bazan Ι“oye makaba al'amarin mutanen nan ya sake saka tsoro a zuciyata gaba Ι—aya, nasake jin tsoron halin mutum da ayyukansa. Wannan wane irin bushewar zuciya ne haka? Su da ya kamata su zauna suyita godema ALLAH bisa ni'imar da yay musu ta rayuwa, su dinga ibada sai suka zama masu butulcewa ta hanyar cutar da wanda shi ya kusan Ζ™are tasa rayuwarne a Ζ™yautata tasu da ta Ζ΄aΖ΄ansu. Umar wai miyasa Ι—an adam keda manta alkairi da yawan butulci ne?. Miyasa Ι—an adam yafi yarda da biyayya wa huΙ—ubar shaiΙ—an akan dokar ALLAH ne?. Miyasa Ι—an adam yafi yarda ya zama mai samu bamai sadaukarwa ba?  Miyasa mafi yawan mutane sunfi sha'awar cutar da wanda suka Ζ™yautata musu amma sunajin tsoron mai munanasu?. Ko addu'a mutum zaiyi, sai kaji yace ALLAH ka tsareni daga sharrin masu sharri. To miyasa bama addu'ar ALLAH ya karemu da aikata sharri ga masu Ζ™yautata mana ne?”.

       “Wannan shine halin Ι—an adam Ι—in da ake faΙ—a Dude, munada son kanmu, duk kuma mutum mai son kasa zakaga shine kullum a cikin wahalar nema da faΙ—uwa. Dan bazai taΙ“a doguwar nasara ba. Daya samu take kufece masa. Amma saboda bushewar zuciya gobe ma sai ya koma sake neman sa'a. Kowane addini akwai na banza akwai na gari. Irin waΙ—an nan mutanen suke ja ana zagin addinin islama bayan shi kuma addinine mai koyar da Ζ™yawawan Ι—abi'u. Ko shekara banyi da shiga musilinci ba, amma wlhy Yoohan na fahimci babu wani addini dake gogayya da shi akan koyar da Ζ™yaΖ™yΖ™yawar rayuwa. Komai musilinci ya haΙ—a. Amma ka duba su da keda ilimin sani a tsahon shekaru sunfi zaΙ“ar su saΙ“ama ALLAH bisa son zukatansu”.

     Sosai zukatansu Yoohan suka Ζ™ara rauni da wannan al'amari. Imani da tsoron ALLAH ya sake shigarsu a zuciya da Ι“argo. Suma kansu dai a wannan dare sunyi barci ne kawai badan jin daΙ—i ba.


*_WASHE GARI_*


        Washe gari aka bama su baba malam damar shiga su duba Abban Abdallah. A lallai duniya abin tsoro. Bawa daina cikama rayuwa baki kai ba komai bane. Duk damar da kaga ka samu a rayuwa da ga rahamar ALLAH ne. Amma wlhy idan yaso ko Ζ™yaftawar ido baka isa gittawa ba. A jiya iyanzu shine zaune tare da Ζ΄an uwa da iyalansa. Amma yau gashi babu ko Ζ™yan gani a fuska saboda tsabar jigata da rayuwarsa tayi. Ita kanta Addah jikin nata babu daΙ—i.

    Duk wanda ya shiga duba Abban Abdallah sai kaga ya fito da kuka. Hakan yasa dama Yoohan bai bar Nu'aymah a wajenba. Suna zuwa ma ya jata wai tazo suje wajen awo. Bata fahimci wayo yake mataba ta bishi. Sai ya kaita office yasa aka kawo mata abinci. Duk da tace masa ta Ζ™oshi, dan basu fitoba sai da Umm ta bata abinci ya dage sai taci. Dole taci kaΙ—an dan ya barta. Sauran kuma ta bashi dan ta fahimci shima yana buΖ™atar a tsaresa yaci abincin.

         

     Zuwa ranar dai dukan ahalin gidan sunsan halin da ake ciki, Ζ΄aΖ΄an Addah dake aure da Ζ™annen Abdallah ma duk sunzo. Ansha sabon kuka dai kam yau ma. Daga Ζ™arshe baba malam dake ta Ζ™oΖ™arin danne tasa damuwar yay musu nasiha da nuna musu muhimmancin Ζ™addara. Ya tabbatar musu da cewar hakan jarabawane. Dan bazai yuwu dama a rayuwa a rayuwa babu jarabawa ba. Ya hana kowa kakkausan lafazi akan su Addah, dan kuwa shi a take ranar ya tabbatarma da kowa cewar ya yafe musu. Sai su cigaba da musu addu'ar ALLAH ya basu lafiya kawai.

     Baba malam ya Ζ™ara kima a idanun iyalan Addah da Abban Abdallah. Musamman ma Abdallah da har ran yakejin tsanar mahaifinsa da Addah. Sunso su gurΙ“ata masa tunani ALLAH ya hana hakan. Dan bayan Addah ta Ι“ale a cikinsu Abbansa sake zaunar da shi yay ya Ι—ora masa sabon karatu akan maido da Nu'aymah rayuwarsa koda ta Ζ™arfin tuwo ne. Wannan shine dalilin da yasa dinga bibiyar rayuwarta. Ko a randa ya bisu shopping mail Ι—in nan da nufin kidnapping Nu'aymah ya je. Sai akai rashin sa'a Yoohan ya gansa tun lokacin da suke faΙ—ansu da Aymah harta faΙ—a a jikinsa. Dai-dai lokacin da yake cemata ta tara musu mutane idonsa ya sauka akan Abdallah Ι—in. Har suka shiga mail Ι—in kuma yana sane da shi. Sannan yana akan sani yabar Aymah a wajen ita kaΙ—ai dan yaga mi Abdallah zaiyi?.

     Lokacin da Nu'aymah taji Ζ™amshinsa da gittawar mutum Abdallah ne, yana gab da isa gareta Yoohan ya jasa baya da Ζ™arfi ya toshe masa baki suka koma ta bayansu. Cikin fushi Abdallah ya hakaΙ—e Yoohan Ι—in yana faΙ—in. “Kai shasha minene haka?”.

     Murmushi Yoohan yayi sannan ya haΙ—e fuska. Cikin Ζ™anΖ™ance ido ya nuna Abdallah da faΙ—in, “Idan ka bari gangancinka ya Ι—ora zuciyarka bisa dokin shiga gona ta. Na rantse da ALLAH Abdallah sai na dawwamar da rayuwarka a dana sani. Na fika hatsabibanci fiye da yanda kake tsammani. Dan haka ka kama kanka kafin na ajiye mutuncin ahalinka da nake gani gefe na Ι“ata rayuwarka. Karka zata bansan wanene kai ba da ubanka. Ka kiyayeni kona fallasaku duniya ta sanku da aiyyukanku akan ahalinku”.

     Yana gama faΙ—a yabar wajen, shine yaje yaja Aymah suka wuce wajan biyan kuΙ—i.

      Tabbas kalaman Yoohan sun girgiza Abdallah. Hakan yasa ya janye daga bibiyar Nu'aymah. Dan dama can shi mutum ne da a rayuwa bai son yawan matsawa kansa, sannan baison fitina sam. Wannan halayyar tasa tasa lokacin yana yaro ake ganinsa matsoraci a cikin yara Ζ΄an uwansa. Dan da gaske tabbas yanada tsoron faΙ—a a rayuwarsa. Dai-dai da film Ι—in faΙ—a Abdallah baya zaman kallonsa sam saboda baya ra'ayin fitina, daya zama saurayune ma dai ya fara canjawa. har zuciyar tasa tai tauri saboda zuciyar gidansu ta gado.

      Ƙin faΙ—ama Abbansa zancen yayi. Amma yayi Ζ™udirin janye jikinsa daga bibiyar Nu'aymah. Daga bakin Abbansa yaji samuwar Uwaliya, dan a randa aka kawota a ranar Abbansa ya tattauna da ita tun a office kafinma a kaita gidansa. Uwaliya akwai son kuΙ—i. jin maΖ™udan Ζ™uΙ—in da Abban Abdallah ya tabbatar mata zata samu akan kaso masa auren Nu'aymah da kawo musu dukkan bayanai a kanta yasa ta amince zatayi. A ranar ya bata rabin kuΙ—in, sauran kuwa sai aiki ya kammala.

      Tasha murna a ranar, ta kuma tabbatar da lallai ta shigo Abuja da Ζ™afar dama. Yo ko Yoohan Ι—in sukace ta bibiya akan waΙ—anan kudin ai ta halakashi kuwa.

       Wannan shine dalilin da yasa ta fara musu aiki. Sai dai abinda bata saniba suna amfani da wayar Rabi da muryartane idan suka kirata.

     Lokacin da aka wuce da Nu'aymah Austria da gaske Abdallah yaje dubatane saboda son da yake mata. Sai dai baiso Yoohan da su baba malam su gansa. Shine yaso su fara haΙ—uwa da Abbansa. koda suka haΙ—un Abban ya dinga masa faΙ—an da har zancen Nu'aymah ya shigo ciki saboda Addah da tazo taga Abdallah ta zata cutar da Aymah zasuyi. Anna ne Yoohan yaji da Hajjo sukaji, abinda kuma basu saniba shine baba malam ma ya gansu, ya kuma jisu. amma sai bai taΙ“a nunawa ko da Umm ba balle su..........✍  

[7/6, 9:39 AM] +234 913 412 2711: *_LITTAFIN nan na kuΙ—i ne. Dan girman ALLAH ki daure ki biya kafin ki karanta, idan kuma bazaki iya biya ba ki haΖ™ura domin ALLAH karki karanta. Idan kuma kin saya dan girman ALLAH karki yaΙ—a manaπŸ™πŸ»_*.




Post a Comment

0 Comments