TOP HAUSA NOVELS atOptions = { 'key' : '20e08520dad54dbf6d9e963271

Saran Boye page 76

 

πŸ’ƒπŸ»πŸ’ƒπŸ»πŸ’ƒπŸ»πŸ’ƒπŸ»πŸ’ƒπŸ»

TEAM----ZAFAFA BIYARπŸ”₯😘πŸ₯°πŸ˜


ALLAH ka gafartama iyayenmuπŸ˜­πŸ™πŸ».





[7/8, 10:16 PM] Sweet Sis: *_LITTAFIN nan na kuΙ—i ne. Dan girman ALLAH ki daure ki biya kafin ki karanta, idan kuma bazaki iya biya ba ki haΖ™ura domin ALLAH karki karanta. Idan kuma kin saya dan girman ALLAH karki yaΙ—a manaπŸ™πŸ»_*.



No. 76


.............Gaba Ι—aya gidan ya hargitse. Su Naser dai sunbi motar data Ι—auki Yoohan a mota, sai dai babu tabbacin zasu iya cimmasu, musamman daya kasance dare ne.

     Afrah da yake tazo wajen sunan ce tai azamar kiran Jay ta sanar masa, shima kansa hankalin nasa ya tashi matuΖ™a, amma sai ya shiga kwantar mata da hankali akan karta damu, indai da waya a jikin Yoohan gano inda ya ke abune mai sauΖ™i, ya kuma tabbatar a duk inda za'a kai Yoohan Deen na wajen insha ALLAH.

     Suna yanke wayar yay kiran su Aliyu ya sanar musu. Tare da tura musu Number Yoohan dan yana son a bibiyesu da sauri kafin suyi tunanin yadda wayar a wani waje ko wani abu daban. Haka kawai a ransa ya kejin wannan aikin papa ne.

       Lallai hikimar Afrah na saurin kiran Jay ya taimaka ainun. Dan cikin amicin ALLAH kuwa ta hanyar bibiyar wayar Yoohan Ι—in da ke a jikinsa suka samu nasarar sanin inda aka kaisa.


_______★


        A Ι“angaren Yoohan kuwa an shammacesa ne. Dan yana tsaka da firgicin jin cewa ba'aga Deen ba, da cewar Nu'aymah ta suma juwa ta nema kwasarsa. Yana dafe kansa kawai yaji an jasa ta Ζ™arfi an tura a mota, al'amarin kamar wani wasan yara. Suna sakashi a motar suka Ι—ora masa bindigu. Binsu kawai yay da kallo Ι—aya bayan Ι—aya ya girgiza kansa. Kafin yace wani abu Ι—aya a cikinsu yace, “Indai kana buΖ™atar Ι—anka a raye ka bimu salin alin”.

       Guntun murmushi kawai yayi ya Ι—auke kansa. Papa yana Nigeria kenan, dan a take ya gama fahimtar su Ι—in yaran papa ne. A ransa yake tunanin shin da papa na buΖ™atar ganinsa sai ya bi ta hanyar sace masa yaro kenan? Minene amfanin yin hakan to?. (tsoron a kamashi mana) zuciyarsa ta raya masa. ‘To ashe kuwa shi da kansa zai damΖ™a papa a hannun huku yau ba sai gobe ba’.

      Ganin baice komaiba yasa yaran Ι—auka yayi ladab ne. A haka suka iso wani hotel. Duk maida bindugunsu sukayi a jiki daga su har Yoohan suka fito a motar. Yaji a ransa zai bisu kamar yanda suke buΖ™ata. Sun shiga cikin hotel Ι—in babu wani alamun rashin gaskiya tattare da su. Hasalima sun shiga a rarrabe ne. Yoohan tare da Ι—aya a cikinsu, suma sauran biyun suka shiga su kaΙ—ai.

       Shi Yoohan sun wuce cikin hotel Ι—in direct, sauran kuma suka tsaya reception kamar dai wani suke jira. Yoohan dai yanata bin hotel Ι—in da kallon nazari har suka Ζ™arasa Ι—aki mai lamba 23 vip section. Knocking Ζ™ofar yayi sau Ι—aya, sai ko gashi anzo an buΙ—e. da ido yayma Yoohan alamar ya shiga. Yoohan yay masa wani gajeren murmushi ya shige Ι—akin, sai y  bisa a baya yanayin Ζ™wafa. Dan yaji haushin murmushin Yoohan Ι—in har ransa.

           Ko kaΙ—an Yoohan baiyi mamakin cin karo da Momy a Ι—akinba. Dan dama ai su zuciyarsa take raya masa gani Ι—in. Ya kauda kansa daga kallonta saboda shegun kayan dake jikinta bata da maraba da tsirara. Takowa tai gabansa tana kwasar dariya da tafa hannaye ta shiga zagayesa. 

      Hannayensa kawai ya tura cikin aljihun wandon shaddarsa ya rumtse idanunsa. Sai da ta zagayasa sau kusan uku kafin tazo gabansa ta tsaya daf tamkar zata rungumesa. Ko motsi kuwa baiyiba, bai kuma buΙ—e idanunsa ba.

     Cikin raΙ—an maganar shaΖ™iyanci da  jin alfahari madam Chioma tace, “Abin mamaki ko my boy, haka muke ni da papanka kullum cikin bama mutane mamaki”. Sai kuma ta Ζ™yalΖ™yale da dariya mai cin rai tana ja baya. Komawa tai bakin gado ta zauna tana wani lashe baki da banΖ™aro Ζ™irji. Tare da jan rigarta sama sosai cinyarta Ι—aya ta fito waje idonta akan Yoohan da har yanzu nasa idanun ke a rufe. Cike da salon iskanci ta sake narke idanu tana lasar laΙ“Ι“anta.

       “My boy karka takura kanka da tunani, dan baka buΖ™atar hakan musamman akan soyayyar jaririnka, oh sorry jikana nefa ashe”. Ta kwashe da dariya sanna ta cigaba da faΙ—in, “Yi haΖ™uri my boy na mantane. Ta hanya Ι—ayane kawai zaka iya cetar my grandson John. Dan nice kaΙ—ai zan iya kaika inda zaka samesa. Hakan kuma bazata kasance ba sai ta hanyar biyamin buΖ™ata ta. Hhhhhh My lovely john dolene fa na Ι—anΙ—ani zumar nan taka da kaketa min rowa, dan itace burina tun kana shekaru sha takwas a duniya. Hhhhhh kaga kuwa ai bai kamata nasha wahalar dakon lokaci ba, kaima nasan zaka tausaya min dear soooon”. Ta Ζ™are maganar da wani salon iskanci tamkar zatai kuka. Sai kuma ta taso zuwa gabansa ta tsaya tana matso hawayen da suka cika mata idanu.

     Hannayenta ta Ι—ora akan Ζ™irjinsa ta fara Ι“alle maΙ“allin shaddarsa tare da cigaba da faΙ—in, “Karka damu duk ma na yafe maka wahalhalun dana sha a waΙ—ancan shekarun kaji baby. Dan wannan daren kawai ya wadatar da cike gurbin duka sauran dararen da suka shuΙ—e”.

      Duk wannan iskanci da madam Chioma keyi Yoohan na tsaye tamkar gunki, har yanzu idanunsa a rufe. Sai da takai Ζ™arshen duka maΙ“allansa tana sambatun haukan zantukanta, ta tura hannunta cikin rigar ta fara shafa Ζ™irjinsa ta saman singlet Ι—insa. Wani irin cije baki yayi ya hankiΙ—ata baya da iya Ζ™arfinsa.

        A take ta saki wani irin wahalalliyar Ζ™ara saboda da gaske ta bugu. Da sauri yaran da suka kawosa wajen suka zagayesa da bindugu. BuΙ—e idanunsa dake a matuΖ™ar jazur yayi akansu, ya wani Ι—auke kai irin ba kune a gabana ba ya maida kan madam Chioma dake kwance Ζ™asa wanwar tana numfashi da Ζ™yar saboda azaba.

       A hankali ya fara takawa gareta fuskarnan kanta tayi jazur kai kace aman wuta zatayo. Suko yaran madam Chioma na biye da shi da bindiga abin nasuma abin dariyaπŸ˜‚.

     Ζ˜afarsa ya taka a samna gadon ya ranΖ™wafo kanta. Wani murmushin tsantsar tsana ya jefeta da shi tare da nunata da Ι—an yatsa. “Na tsaneki, har cikin raina na tsaneki, tsana irin wadda ban taΙ“ama wani mahaluki ita a wannan duniyarba. Indai nine zaki mutu da takaicin rashin samuna har Ζ™arshen numfashinki. Nayi takaici mai yawa akan kasancewarki mahaifiya a gareni. Bakuma zan taΙ“a yafe miki ba har abadan tunda ke karya ce wadda sam bata da zuciya a Ζ™irjinta balle Ζ™waΖ™walwar tunani. Badan ke uwata bece da yau na tabbatarma duniya ke Ι—in dabbace, a cikin dabbobinma kina jerin aladu dan sune basu banbance junansu wajen neman kansu. Wlhy kinji na rantse ko tabon Ζ™warzane na samu a jikin yarona saina halakaki da wannan hannun nawa”. Ya kai Ζ™arshen maganar yana wara yatsun hannunsa da jujjuyasu akan fuskarta.

     Da gaske tsoro ya shigi Madam Chioma, dan tunda take a rayuwarta bata taΙ“a ganin irin wannan fusata da fushin na Yoohan ba. Tsaye ya miΖ™e yana zuba mata wani mummunan kallon tsana da Ζ™yama. 

      Da sauri ta zabura ta miΖ™e duk da azabar da bayanta ke mata. Tace, “Ku Ι—auremin shi, wlhy koda Ζ™arfi saina lashi zumarka John. Kaje kaita tsanar tawa kai ya dama wannan kuma, ni ban tsaneka ba. Ba kuma zan tsneka ba”.

     Kafin Yoohan yay wani yunΖ™uri kuwa suka dabaibayesa da igiya, duk yanda yaso kuΙ“utar da kansa ya gagara hakan sam, dan tsam suka Ι—auresa a tsaye sannan suka kamashi suka ajiye a kujera suka sake Ι—aurewa suna dariyar yanda sukaga yana wani irin huci na zafin zuciya.

      Itama kanta Madam Chioma dariyar take tayasu da iya Ζ™arfinta. Ta tashi tsaye da Ζ™ar tana riΖ™e Ζ™ugu. Gabansa tazo ta tsaya tana cije baki. “John kana wasa dani ko? Na fika hatsabibanci yaro. dan tunkan asan za'a haifeka nake da taurin kai. Ai tunda nayi alΖ™awarin saina cikama rayuwata”.


      Lokacin da su Yoohan ke wancan dabi shi da madam Chioma su Nu'aymah suna shigowa cikin hotel Ι—inne tare da jami'an tsaro. Dan tuburewa tai akan saita biyosu. Ganin yanda ta rikice Ι—inne ya saka Omar bada shawarar aje da ita Ι—in. Sai da jami'an tsaron sukai magana da manager Ι—in hotel Ι—in sannan suka nufi cikin hotel Ι—in kamar yanda alama ke nuna musu dai-dai inda wayar Yoohan take. Wadda toshewar basirar madam Chioma baisa ta kawo a ranta sanadin wayar ballinsu zaiyi ruwa ba.

        Dai-dai madam Chioma ta Ι—ora kanta saman wuyan Yoohan tana shinshina kamar wata mayya ko tunkiya, hannayenta duka biyu na akan jikinsa. wani irin masifar tafasa zuciyar Yoohan keyi tamkar zata faso Ζ™irjinsa ta fito waje. Sai ko faman taunar lips nashi yake da masifar Ζ™arfi, a Ι—aure yake, bashi da wata damar Ι—aukar mataki akan uwar tasa.....

       Da sauri ta Ι—ago saboda jin an buΙ—e Ζ™ofar. Hakama yaranta dake tsaye a gefe kawunansu a Ζ™asa duk zabura sukayi suna rarumar bindugunsu...

       “Ƙasa gaba Ι—ayanku, duk wanda ya taΙ“a wata bindiga anan kuwa a bakin ransa”.

    Ɗaya daga cikin jami'an ya faΙ—a a tsawace yana nuna yaran madam Chioma. Da sauri ta fiddo tata Ζ΄ar Ζ™aramar bindigar jikinta ta Ι—ora bisa kan Yoohan daya buΙ—e idonsa a hankali ya sauke su akan Nu'aymah da ke shigowa tare da Jami'an.

       Cikin rawar jiki data murya Madam Chioma tace, “Ku fita a Ι—akin nan kona tarwatsa masa kwanyar kai duk da kasancewarsa Ι—ana”.

        Da sauri Nu'aymah tace, “Ƙarya kike munafuka azzaluma. K! Ba mahaifiyarsa bace ba. Yah Yoohan wlhy ba itace mahaifiyarka ba Ζ™arya takeyi”. Tai maganar da fashewa da kuka tana zaro hoton nan daga envelope ta nuna masa balarabiyar nan. “Kaga mahaifiyarka nan Yah Yoohan, wlhy ba wannan shaiΙ—aniyar bace. Bana tantama akan har mijinta ba shine ya haifeka ba, akwai abinda suke Ι“oye maka. Iyayenka na gaskiya bazasu sace maka Ι—anka ba. Mahaifiya ta Ζ™warai bazata so tarayya da Ι—anta ba koda kuwa bata da addini, sai dai idan dabbace ita mai juyayyen tunani..........”

       “Hhhh da Ζ™yau tsagera”. Madam Chioma ta faΙ—a tana dariya har yanzu bindigarta na akan Yoohan da zantukan Nu'aymah sukema kai kawo a rai. Ta cigaba da dariya da faΙ—in, “Ashe tsaurin idon naki ya kai haka? Ko da yake ashefa kinsan zafin haihuwa ko? Hhhhhhh. Ashe kuwa za'a kwashi gawa da yawa a hotel Ι—in nan yau”. Tai maganar da haΙ—e fuska ta nuno Nu'aymah da bindigar.

       Cikin kaushin murya Umar yace, “Kibar wannan haukar da kikeyi ki ajiye bindigar hannunki kawai madam”.

      Kallonta ta maida garesa. Cikin yatsina fuska tace, “Richard kake kowama? Kai kuma a suwa shiga family issue?. Maza kama kanka wannan ba shigarka baceba.....”

     Kafin ta rufe baki taji an hankaΙ—ata, sai ga ta ita da bindigar Ζ™asa wanwar. Da sauri Ι—aya a cikin Ζ΄an sandamln ya Ι—auke bindigar, wani kuma yazo ya danna mata ankwa ta baya. Yaran nata ma duk an kamesu. Nu'ayma kuwa da gudu ta Ζ™arasa jikin Yoohan dake a Ι—aure ta rungumesa tana fashewa da kuka. Biyota Umar yayi ya fara warware igiyar da suka Ι—aure Yoohan Ι—in da ita, itama Aymah sai ta miΖ™e tana taimaka masa. Suna gama kwancesa ya rungume abarsa yana shafa bayanta. Sai dai bakinsa ya kasa furta komai saboda irin tafasar da zuciyarsa ke masa. Hoton hannun nata ya zare ya kafe balarabiyar jiki da kallo tare da papa dake gefenta. Jiyay wani abu na tsarga masa tun daga zuciya har zuwa tafin Ζ™afa. Ya kafe fuskar papa yana nazari sosai akansa batare da su Nu'aymah sun fahimci abinda yake nazartarba. A hankali ya janye Aymah a jikinsa yana miΖ™a mata hoton, gaban madam Chioma ya karasa. Babu wani kace nace yasa Ζ™afa ya taΙ—e Ζ™afafunta sai gata a Ζ™asa ta zube. Kasancewar hannayenta Ι—aure suke ta baya da ankwa sai ta faΙ—i a rubda ciki. A take goshinta da hancinta da baki suka fashe, haΖ™oran gaba guda biyu sai gasu a Ζ™asa.

     Wata wahalalliyar Ζ™ara ta saki. Yoohan yasa hannu ya birkitota ta dawo rigingine. Gaba Ι—aya fuskarta ta gama damewa da jinin raunukan data samu, “Ina Ι—ana?”. Wannan itace kawai tambayar daya jefa mata batare da ya damu da yanda jini yayma fuskarta jage-jage ba.

       Kanta ta shiga girgiza masa, cikin rawar murya da laΙ“Ι“a tace, “Nima ban saniba John, Please ka yarda da ni”.

     Uffan Yoohan baice da itaba, sai bindigar hannun Ι—an sanda Ι—aya ya fisge ya Ι—ora mata a goshi. “Humm ke Ζ™aramar Ζ΄ar iskace ashe. Idan kika cigaba da min gardama ba shakka zan tarwatsa Ζ™aramar Ζ™waΖ™walwarki da harsashin cikin bindigar nan. Idan kinada taurin kai tun kan haihuwata, ni ki Ι—auka bayan haihuwar tawa na damaki na shanye. Da kika ganina anan tsageran kainane nima wlhy. FaΙ—amin ina Yarona yake?”.

      Wutar bala'in da madam Chioma ke hangowa cikin idanun Yoohan ya sata saurin faΙ—in, “Zan gaya maka, amma ka taimakeni ka cikamin burina nima, kayi tarayya dani koda sau Ι—aya ne naji sanyi a raina John. Ka tausayama wahalar danasha a kanka ta tsahon shekaru”.

         “Lallai k! a tumakin ma balama ce”. Yoohan ya faΙ—a yana cije baki da Ι—ana kunamar bindigar ya maida bisa tsakkiyar kanta. 

      Jikinta karkarwa ya farayi, tana kuka tace, “Kayi haΖ™uri karka kasheni zan faΙ—a maka Jonh. Na rantse zan faΙ—a maka. Yaronka na a hannun Papanku acan wani gida dake cikin G.r.a, nima ya sakanine na kai masa kai, shine nai amfani da wannan damar domin fara cikama kaina burina a kanka na tsahon shekaru. Na biyo da kai tanan kafin na miΖ™aka wajensa. Miracle ita aka saka ta sace maka yaro a wajen bikin da kukeyi, dan dama muna biye da duk wani motsinku.......”

      Duka ya kai mata a fuska Ι—an sanda yay saurin riΖ™esa. “Cool down Mr Yoohan. Karka damu dolene ta kaimu har inda suke ai. Kwantar da hankalinka kaji”.

      Huci kawai Yoohan ya keyi, tsabar zuciyar dake cinsa sai ga hawaye sharrrr suna sakkowa. Matsowa Nu'aymah tayi ta riΖ™e masa hannu batare da tayi magana ba. Da sauri ya jawota jikinsa ya rungume ko zaiji sassaucin zuciyarsa.


            An tattara yaran madam Chioma zuwa police station da su. Su kuma su Yoohan da sauran jami'an suka shiga motar da aka sato Yoohan tare da madam Chioma bayan an sakata kiran papa ta sanar masa cewar gata ta samo Yoohan harda Nu'aymah ma. Wani ihun gigitacciyar dariya papa ya saki har su Yoohan na jiyosa. Umar da Jami'an sun rufe fuskokinsu tamkar su Ι—inne yaran madam Chioma. Itace ta dinga nuna musu hanya har suka isa anguwar. A daidai Ζ™ofar gate Ι—in gidan suka tsaya. Maigadi na leΖ™owa yaga motar sai ya buΙ—e da tunanin su madam Chioma sun ciyo nasara suma.

        Yoohan da Nu'aymah aka sakama ankwa a hannu suka fara shiga, jami'an tsaron da fuskokinsu ke a rufe na biye da su a baya. Umar ne Ζ™arshe da madam Chioma a gabansa. Acan waje dama tuni Ζ΄an sanda sun gama zagaye gidan dan dama babban burinsu shine kama papa da sauran mutanensa. Abinda suka share watanni biyu suna nema ga dama ta samu a lokacin Ζ™anΖ™ani.

      Da sauri Papa dake zaune cikin kujera su Joshua zagaye da shi duk suka miΖ™e sabida ganin Yoohan da Nu'aymah. Deen na kwance akan centre table Ι—in falon cikin showal Ι—insa. Yayi kukan wahala har ya gaji yayi barci. Gefensa an ajiye sharΙ“eΙ“iyar wuΖ™a.

       Cike da wata irin mahaukaciyar dariya papa ya shiga tafa hannayensa yana kallon su Yoohan.

   Ya tako gabansu a hankali batare da tunaninsa ya haska masa cewar waΙ—anda ke bayansu ba yaransu bane ba. Da dariyarsa ya shiga faΙ—in, “Oh my Son & Darling daughter in-low Ι—ina. Welcome to my new land. Nice meeting you my guys”.

       Da ga Ayma har Yoohan dai kallonsa kawai suke. Papa ya kalli jami'an da yake tunanin yaransa ne yana fa faΙ—in, “Ku cire musu ankwa amfaninta ya Ζ™are ai. Dan game zamu buga da su mai zafi”.

     Babu musu Ζ΄an sandan nan suka cirema su Yoohan ankwa. Komawa papa yay ya zauna a kujerar daya taso. Ya Ι—an taΙ“e bakinsa da dora Ζ™afa Ι—aya kan Ι—aya ya Ι—auki kofin giyarsa ya kurΙ“a yana kallon su Yoohan. “John badan inada Ζ™arancin lokaci ba dana baka wani labari mai ban mamaki da al'ajabi. Amma share kawai muje ga game Ι—inmu. Idan lokaci ya rage mana a cikinsa sai na baka labarin. Daughter in-low karki tada hankalinki kinji, Ι—anki yana lafiya, kingama barci yake abinsa”. Yay maganar da tasowa daga kwanciyar da yayi jikin kujera ya yaye showal Ι—in da deen yake ciki yana lakatar hancin yaron da Ι—an yatsa. “Daughter kin iya haihuwar Ι—a fa”. Ya faΙ—a yana kecewa da dariya su Mike na tayasa. Giyarsa ya kwankwaΙ—a ya ajiye kofin yana haΙ—e hannayensa waje guda. “Oh Sorry my son karka fusata na sanka da zuciya”. Takardun dake a gefen Deen ya jawo ya tura Ζ™arshen tebirin ta sashen da su Yoohan suke. “Wannan takardun sune game Ι—inmu tare da Ι—an jinjirinku Ζ™yaΖ™yΖ™yawa. John kanada zaΙ“i biyu. KuΙ“utar da yaronka ta hanyar yimin signing a duk takar dunnan, ko kummaaaaa nai masa yannnnnkan rago da wannan wuΖ™ar tawa a wannan lallausar fatar tashi”. Ya Ζ™yalΖ™yale da dariya yana Ι—ora wuΖ™ar bisa cikin Deen dake barci a binsa yanata sakin ajiyar zuciyar kukan da yasha. 

       Ko motsi Yoohan baiyiba, haka ma Nu'aymah duk da hankalinta a tashe yake kallon papa kawai take zuciyarta na tunanin anya kuwa wannan mutumin ma mahaifin Yoohan ne?

        Hannunta taga Yoohan ya saki tare da takawa a hankali zuwa gaban papa yana wani Ζ™yaΖ™yΖ™yawan murmushi, dan cikin Ζ΄an sandan nan Ι—aya yay masa alamar yaje. Zuwa yanzu sunsan sauran Ζ΄an uwansu sun gama tattare yaran papa gaba Ι—aya dake cikin gidan. Sannan sun gama nazarin su papa kaf babu wani makami tare da su anan sai wuΖ™ar dake akan Deen. Babu wani alamar damuwa a fuskar Yoohan balle tambayar papa ba'asin yin hakan. Yazo gaban tebirin ya zauna akan Ζ™aton tum-tum dake kusa da shi yana murmushi. Cikin kwanciyar hankali ya Ι—auki pen Ι—in dake saman takardun ya rike a hannu. Shafin farko na takardun ya karanta cike da nazari. YaΙ—an Ι—ago ido ya kalli papa da shima ke kallonsa. Murmushi Yoohan ya sakar masa da taune lip Ι—insa na Ζ™asa ya Ι—age gira Ι—aya da lumshe idanunsa ya sake buΙ—ewa akan takardun. Har cikin jini Murmushin Yoohan ya daki zuciyar papa da su Mike. Amma sai basuyi magana ba. Ɗaya bayan Ι—aya Yoohan ya fara signing takardun. Yana gab da gamawa Mike da ya farga babu Madam Chioma. yace, “Brother wai nikam ina madam ma ne? Ta kawo mana su amma banga ta shigoba ita”.

     Da sauri Papa ya kalli Mike, sai kuma ya kalli Yoohan dake signing yana murmushi da taunar lip dinsa na Ζ™asa. “John mikake kullawa? Ina matata?”.

    Ko motsi Yoohan baiyiba balle ya kalli papa. Sai da ya gama signing Ι—in duk takardun sannan ya kalli papa da tsoro ya fara bayyana masa a fuska. WuΖ™ar kan Deen ya dauka yana faΙ—in, “Ashe kuwa inhar wani abu ya samu matata saina halaka wannan yaron”.

      Murmushi Yoohan ya sakeyi har haΖ™oransa na bayyana. Ya miΖ™e tsaye hannunsa Ι—auke da takardun da yay Signing. YaΙ—an sosa pen din a gefen wuyansa yana duban papan. “Oh my sweet papa ya da karaya haka da wuri?”. Yay maganar da wani shegen murmushin yaΖ™e. Sai sukaga ya girgiza kansa yana Ι—an buΙ—a hannayensa. “Karfa ka damu papa. taya zan cutar da mahaifiyata. Guys Please ku kawo masa matarsa”. Ya juya yana kallon Ζ΄an sandan nan. Umar dake can Ζ™ofar falon bai shigoba ya turo madam Chioma ta fara shigowa bakinta a Ι—aure. Bindiga a bisa kanta.

    Wani irin zabura papa yayi jikinsa na rawa. Kafin yay magana Yoohan yay Ζ΄ar dariya yana faΙ—in, “Oh my sweet papa relaxxxxx!!. Idan ban mantaba kace zamuyi game ko? So karka damu bazan canja ba zamu buga ai. Nasan kana son matarka, ba kuma zakaso rasata ba, gata Ζ΄ar Ζ™yaΖ™yΖ™yawa kuwa”. Yay maganar da wata shegiyar dariya. Sai kuma ya gimtse fuska da haΙ—e hannayensa waje guda yace, “Oh sorry papa bazan sakeba. Ga takardu na maka signing kamar yanda ka buΖ™ata. Sai dai kana da zaΙ“i. Matarka ko waΙ—anan takardun. Idan su kafi buΖ™ata, zan baka, amma zan tarwatsa kwanyar matarka a gabanka. Idan kuma matarka kafi bukata, zaka bani Ι—ana, na kuma wuce da takardun nan a gabanka. Wannan shine game Ι—in Yahyaaaaaa! MuchπŸ’‹! muchπŸ’‹!!, I love you my papa!!”. Suka kwashe da dariya a Ζ™arshen maganar shi da Nu'aymah tare da tafawa.

       Wani irin huci papa ya fara fitarwa kamar zai shiΙ—e. Ya kai hannu zai fisgi wuΖ™ar nan Yoohan yay saurin faΙ—in, “No! no! no no no no!!!! Pastor goshpower. Karka fusata da yawa fa, kasan Ι—an naka mai faΙ—a da cikawa ne. Ai yanzun game ya tashi daga tsakanin takardu da yarona, ya koma tsakanin takardu da matarka ok?”.

     Kafin papa yace wani abu Yoohan ya  fisge handkerchief Ι—in da suka Ι—aure bakin Chioma da shi. Wani wahallalen Ζ™ara ta saki da fashewa da kuka. Cikin roΖ™o tace, “Please Darling ka basu yaronsu, ka taimakeni, na rantse john zai iya kasheni, kagafa yanda ya ciremin haΖ™wara, karkai jayayya dasu nan duk jami'an tsarone ba yaranmu ba”.

     “What!!!”.

  Papa da su Mike suka ambata a firgice. A take duk jami'an tsaron da Omar suka janye abinda suka rufe fuska. Sai ga wasu na shigowa suma akai ma su papa zobe. takawa Yoohan yayi gaban papa yana dariya ya Ι—auki Deen ya rungume a jikinsa tare da sumbatar goshin yaron. Da sauri Nu'aymah ma ta matso garesa ta haΙ—ashi shi da yaron ta rungume. Umar kuwa ya damkama Ζ΄an sanda Madam Chioma ya matso ya Ι—auki takardun da Yoohan yayma Signing yana dubawa.

      “Kai!! Dude!, anya kuwa mutumin nan ma shine mahaifinka kuwa?”..  

     ΖŠagowa Yoohan yayi daga sumbatar kumatun Deeen, yasa hannu ya share hawayen da suka cika masa ido yana miΖ™ama Nu'aymah yaron. Yace, “Goyashi akwai sanyi”. Babu musu Aymah ta juya ya Ι—ora mata Deen a baya ta goyashi, ya gyara mata hijjab Ι—in jikinta sannan ya dubi Umar da yay tambayar da furzar da zazzafan huci.

       “Bana zaton haka Umar, dan abubuwa da yawa sun banbanta tsakaninsa da wanda ke a hoton nan. Sannan waΙ—anan takardun mallakin kaddarorine a cikinsu wanda alamu suke nuna ba nasa bane sam. Dan signing Ι—in cikinsu ba irin nashi baneba. Akwai sirrin da yake Ι“oyema duniya a kaina........”

         “Sirri mai girma kuwa”.

Muryar da basuyi zato ba ta karaΙ—e kunnuwansu a bazata. kusan gaba Ι—ayansu suka dubi bakin Ζ™ofar inda maganar ta fito. *Jawaad Abdul-aziz Yusuf* ne tsaye cikin Ζ™ananun kayan da suka rage masa shekaru, sai dai duk wanda yasan shekarun girma ya kallesa yasan shiΙ—in bana wasan yara bane, (Duk ya girmi masu karatu yanzu, duk da a gabansu aka haihesaπŸ˜πŸ˜œπŸ€£πŸƒ).

         Bayansa jami'ai ne biye da shi. Cikin falon ya karasa shigowa ya zauna a kujerar da ke kallon papa dake a durΖ™ushe bisa gwiwoyinsa yanzu shi da su Anthony saboda zagayesu da akai da bindugu.

       Ζ˜afa ya Ι—ora Ι—aya kan Ι—aya yana wani shegen murmushi, yace, “Hii Goshpower, sai kuma gaka. Hhhh ALLAH sarki. Haka rayuwa take ai, duk iya gudun mai tsere bai isa zarta Ζ™addararsa ba. Dama naji a jikina dole ka dawo, dan yanzu da dukiyar da wannan takardun kawai kake tunanin ka tsira. Kafa birgeni, dan da gaske ka iya wasa. Kana da basira Ζ™warai da gaske. Sai dai kuma kanada daΖ™iΖ™anci a wajen kuskuren lissafi. Da ace bakabar Yoohan a raye ba da lissafinka bazai taΙ“a Ι“ata ba. Sai dai kash a dalilin Ζ™waΙ—ayin abinda baka taraba ka saka kanka a tarko tsahon shekara talatin da biyu. Tsem! Tsemm tsemmm!!! Gaskiya ka bani tausayi. A farkon labarin dai cike yake da birgewa da Ζ™ayatarwa ga marubucinsa. Sai dai a Ζ™arshe an samu dagulewar Ζ™waΖ™walwa ga marubucin. Mai makon yanda aka fara da nasara a Ζ™are da nasarori sai aka Ι“ige da faΙ—uwa Ζ™asa wanwar. Kash matsalar tunani ko Mr goshpower”.

     Jay yay maganar Ζ™arshe yana Ι—age gira da sakin dariya. Ya cigaba da faΙ—in, “Oh sorry bara na taΖ™aita, dan ka sani tafiyar da ban shiryaba a daren nan daga Abuja zuwa kano ga uban sanyi. Maganar gaskiya ma ban yafe ba. Ζ³an jarida ku shirya kayan aiki”. Ya faΙ—a yana shafar girarsa da nuna hanyar Ζ™ofa.

       A take kuwa suka shigo kusan su shida. Duban Yoohan da Nu'aymah da Umar yay ya nuna musu kujerun alamar su zauna suma.

      Zama sukai a sanyaye kamar an doke gwiyawunsu da Ζ™arfuna.

     Jay ya kalli agogon hannunsa sannan ya dubi papa. “Mr Goshpower bamu da isashen lokaci, dan awoyi uku da mintuna ashirin da Ι—aya suka rage alfijir ya keto. Bana son wasana da kai yay tsamari a wannan gaΙ“ar dan daga ni har kai mun jigatu, inason sanin wanene Yahya? Su wanene kuma waΙ—anan na jikin hoton?”.

     Shiru papa yayi ya Ζ™i magana, hakan yasa Jay Ι—inma bai sake magana ba, sai kawai Ζ™arar bibdiga su Aymah sukaji da Ζ™arar papa. RuΙ—ewa Aymah tayi ta Ζ™waΖ™ume Yoohan jikinta na rawa. Ga Deen dake bayanta ma ya farka da wani irin firgitaccen kuka. Taimaka mata Yoohan yayi ta sakko da shi, ya rungumesa a jikinsa yana jijjiga shi. Da kallon papa da Jay yayma harbi biyu a duka Ζ™afafunsa saboda tsabar Ζ™warewa a iya harbi.

      Jay ya girgiza kansa da dafesa. Yace, “Oh kana neman fusatanine Mr Goshpower. Gashi ni kuma hannayena Ζ™aiΖ™ayi sukeyi. Na faΙ—a maka a jigace nake matuΖ™a, karka jani da nisa ana idar da sallar asuba nake son komawa Abuja”.

       Cikin magautar raΙ—aΙ—i papa ya fara magana. Ga wata irin zufa ta jiΖ™esa a take duk da uban sanyin da ake zubawa a garin. Yace, “Shima sunansa Goshpower, shi Ι—in twin brother Ι—inane. Wannan kuma matarsa ce”.

       “Yayi Ι—an gari, haka nake buΖ™atar jinka. Omar a cire masa bullets Ι—in nan”.

       Da sauri Omar yace, “Okay Uncle ”.

       Tsabar son azabartarwa Umar sai ya Ι—auki giyar da papa yasha ya rage ya zuba masa akan harbin. A take kuwa ya saki wata wahalliyar Ζ™ara ya suma. Ko a jikin Omar. Ya amshi First aid box a hannun wani jami'i da sukazo da shi ya cire bullets Ι—in cike da rashin tausayi. Sai da ya kammala komai sannan aka zubama papa ruwa ya farfaΙ—o.

       Sai da suka bashi damar hutun kusan mintuna biyar ya daidaita sannan ya fara bada labari.


       “Ni da shi twins ne. Muna tsananin kamanni har takai jama'a basa iya banbantamu inba mahaifiyarmu ta faΙ—a ba. Duk da itama wani lokacin rikicewa takeyi. Suna Ι—aya iyayenmu suka saka mana wato Goshpower. Takai inhar ka kira Ι—aya a cikinmu sai mu amsa maka mu duka. Mamanmu ta taΙ“a faΙ—a mana kaifin basira da muke da shi da farar fata tasa har ana dangatamu da wasu sunaye. Wasuko na tsoronmu da faΙ—in mama debora ta haifi waΙ—anda ba mayu. Wannan ba sabon a bu bane daga hallayar mutanen Ζ™abilarmu da yankinmu wajen danganta mutum mai fari da Ζ™yawun jiki da suna na tsoro. Mutane basu fara samun basirar banbantamu ba sai da muka fara girma halayenmu suka fara banbanta tsakanina da Ι—an uwana. Mu duka munada kaifin basira da wayo, sai dai kowa da yanda yake gudanar da tashi. Duk inda gaskiya take zaka samu Ι—an uwana a wajen, niko saΙ“anin haka shine zaΙ“i na. Kullum cikin takalo rikici nake wa iyayenmu, Ι—an uwana kuma bai gajiya da bayyana gaskiya idan an tambayesa. A duk lokacin kuma da nai niyyar cutar da shi akan wannan abu da yakemin sai bana samun nasa. Dan ko faΙ—a zamuyi yafi Ζ™arfina. A haka dai muka kammala primary, akwai shaΖ™uwa mai Ζ™arfi a tsakaninmu, amma bamu cika zaman lafiya ba da zama waje Ι—aya na dogon lokaci. Bayan secondary skull muka wuce jami'a, inda anan mabanbantan halayenmu suka sake bayyana. Duk da mu duka muna karatu ni a koda yaushe hankalina nakan mata, sannan duk wani abokin banza zaka samu nawane. Hakan na Ι“atama Ι—an uwana rai, tun yanamin nasiha da faΙ—amin gaskiya har yayi zuciya ya daina, daga Ζ™arshema muka raba Ι—akin kwana, dama ba department Ι—inmu Ι—aya ba. Haka dai muka cigaba da tafiya, kafin mu kammala jami'a na zama riΖ™aΖ™en mara jin magana dan har harkar Ζ™waya na fara, sannan na shiga cikin Ζ΄an Cult. Mun kammala degree Ι—inmu na farko, ta hanyar ogan babanmu muka samu taimakon tafiya Ζ™asar Italy Ζ™aro karatu. Daga nan ne labarin canjawar komai ya fara. Dan watanninmu biyar kacal a makarantar na sake canjawa daga duk yanda aka sanni. Idanuna sun sake buΙ—ewa sosai harna fara harkar cocaine. Ta hanyar wanda na fara harkar Cocaine ne idanuna suka sake bushewa. Ya kutsa dani cikin manyan mutane konace tantirai dake juya duk wani iya shege na duniya. Nasha wahala ba kaΙ—anba wajen karΙ“ar horo daga garesu har takai makaranta ma na daina shiga duk da yawan damuwa da kirana da Ι—an uwana keyi, tare da yawan Ζ™oΖ™arin son sanin abokan mu'amulata. Muna shekarar Ζ™arshe daya kamata mu kammala degree Ι—inmu na biyu Ι—an uwana ya haΙ—u da matashiyar Balarabiyar saudia mai suna Anum. Itama karatu tazoyi, wannan kuma shine zangonta na farko. Sun fara rayuwa kamar abokai a hankali suka rikiΙ—e zuwa masoya. Sam bansan da wannan soyayya tasu ba sai da tai nisa, muna ma gab da kammalawa. ko nace Ι—an uwana na gab da kammalawa. Danni tuni na yaye kaina daga zuwa makaranta. Sai dai nakan shigo lokaci-lokaci saboda harΖ™allar dake tsakanina da Ι—alibai ta kayan shaye-shaye. A wani shiga da nai cikin makarantar ne na haΙ—u da Anum, wadda ina cikin tafiyata tazo tasha gabana, a zatonta Ι—an uwana ne. Da farko na harzuΖ™a matuΖ™a, sai dai Ζ™yawunta yayma idanuna barazana da danne fushina. Cike da tsokana take kallona tana dariyar wai yaushe nasai kayan jikina?, ita dai basu mata ba. Naji haushin kalamanta amma saina fuske na barta akan Ι—an uwan nawa ne. Kiran wayata da ogana yayine yana min neman gaggawa yasa na sulale nabar Anum da nufin zan dawo gareta. Daga haka bansan yanda ta Ζ™areba bayan taga Ι—an uwana. Shin ya warware mata mu Ζ΄an biyu ne, kokuwa ya karΙ“a mata matsayin shine ni?. Kwana biyu da yin haka na dawo cikin skull neman Anum sai dai na samu labarin cewa sun wuce saudia ita da Ι—an uwana. Samakon zuwa da yayunta biyu sukai suka ganta da Ι—an uwana daba musulmi ba”.

        “Duk da bana shiri da shi hankalina ya tashi matuΖ™a, dan kodai babu komai shiΙ—in Ι—an uwanane ai. Duk zatona ko zasu cutar da shi ne? Naso binsu duk da bansan ina suka nufaba sai kuma wani aiki ya sake taso mana zuwa Ζ™asar Germany. Haka na tafi al'amarin Ι—an uwana na damuna a cikin rai. Kamar wasa sai ga wannan tafiya ta jani tsahon wata huΙ—u, lokacin da muka dawo Ζ™asar Italy saina samu munyi graduation, course mate Ι—ina duk sun kama gabansu har Ι—an uwana. Na bincika Anum sai na samu wai itama tabar makarantar. Daga jin haka sai kawai na nufi Nigeria, a zatona Ι—an uwana ya koma gida. Amma kash sai na iske saΙ“anin tunani. An dai tabbatar min yazo wata biyu da suka gabata wajen rasuwar mahaifinmu, nima anta nemana amma ba'a sameniba. Ko damuwa banyi da mutuwar babanmu ba, sai dai jin ogan babanmu ya bama Ι—an uwana maΖ™udan kuΙ—in aikin da mahaifinmu yay aiki a Ζ™arΖ™ashinsa dan yaje ya juya hankalina ya tashi na bukaci sanin ina Ι—an uwana yake?. Mamanmu bata saniba, abinda kawai ta sanarmin shine ya sake barin Ζ™asar, bakuma susan ainahin Ζ™asar daya tafi ba. Yadai bar musu kuΙ—in da zasu ishesu, tare da musu alΖ™awarin nanda shekara guda zai dawo musu da daddaΙ—an labari. Nayi Ζ™wafa kawai bance komaiba. Daga haka na tattara kayana zan koma. Sai dai kafin na wuce na haΙ—a harΖ™alla da abokaina akan zanke turo musu kaya insha ALLAHU suna saidawa su tura min kuΙ—in. Sunko amince tare da min alΖ™awarin bazasu bani kunyaba. Daga haka na tattara na koma inda na fito, babu wani zancen nasarar da naci a karatuna dana zauna naima mahaifiyarmu. dan koma ban faΙ—aba nasan Ι—an uwana ya gama tona mata dukkan zance a kaina”.

      “Ban sake sanin ina Ι—an uwana yakeba, ba kuma mu sake haΙ—uwa ba sai bayan kusan shekara, ana gab da zai cika alΖ™awarin daya Ι—aukama iyayenmu na komawa garesu da daddaΙ—an albishir. A lokacin naje kai kaya Ζ™asar Syria ne. Kwatsam zamu shiga wani shopping mail ni da abokin tafiyata sai ga twin Brother Ι—ina tare da balarabiyar yarinya dana taΙ“a haΙ—uwa da ita a Italy a bazata. Da gani har shi babu wanda baima Ι—an uwansa kallon mamaki ba. Hakama mafi yawan jama'ar wajen kallon mamaki suke mana da al'ajabi. A zahiri dai gashi muna tsananin kamanni, amma a shigar sutura da yanayi bama muyi kama da Ζ΄an yanki Ι—aya ba. Ni na fara sakin murmushi ina kallon jaririn dake rungume a kafaΙ—arsa, sannan na kalli Anum na sake kallonsa. Goshpower kaine anan kuma?”.

      “Shima Murmushin ya saki a karo na farko yana girgiza min kai, yace my twin bro, wannan suna yanzu na bar maka. A yanzu sunana IBRAHEEM ne, wannan matatace Anum, ga yarona Abdul-Maleek. Woow!! Na faΙ—a ina dariya da tafa hannu, kafin na miΖ™a hannun ya Ι—oramin jinjiri Abdul-maleek. Yaro Ζ™yaΖ™yΖ™yawa mai tsananin kama da mahaifiyarsa, sai dai ya kwaso kamannina nima ni da Ι—an uwana kaΙ—an. Ganin dai da gaske munsan juna abokin tafiyata ya barni tare da su yana faΙ—in mu gaisa shi zaije ya kai kayan zuwa anjima saimu haΙ—u. Na amsa masa da jin daΙ—i, dan koba komai ina buΖ™atar keΙ“ancewa dama da Ι—an uwana dan naji yaya batun kuΙ—in daya amso a Nigeria suke. Dan ko kaΙ—an banji wani damuwa da fahimtar ya koma musulmi ba. Kamar ya shiga raina kuwa. Sai ya buΖ™aci mizai hana muje gidansa kawai, ashe nan yake da zama yanzun. Mun shiga danΖ™areriyar motarsa dani da ke wahalar nema da shiga haΙ—arin rayuwa ko wadda bata kamitaba bani da ita. Wannan abu ya sosamin rai, amma sai ban nunaba muka shiga, suna gaba shida matarsa niko ina baya tare da jaririnsu a hannu. Al'amari bai kuma tadamin hankaliba sai da muka isa Ζ™aton gida da yaji kayan more rayuwa a matsayin wai nashine. Lallai nasha kallo, cikin mintuna kalilan kuma matarsa ta gama cika gabanmu da kayan ciye-ciye. Sai bayan munci mun Ζ™oshi mukai gaisuwa da tambayar bayan rabuwa. Bai Ι“oye min komaiba daya shafesa bayan rabuwarmu”.

      Yace, (Ɗan uwana kamar yanda na sanar maka wannan itace matata, mun haΙ—u a jami'ar Italy dakaΖ™i nutsuwa ka Ζ™arasa. Da farko tsakanina da ita abota ce, sai daga baya muka fahimci muna son juna. Sai dai ta tabbatarmin babu yanda aure zai kasance a tsakaninmu saboda addinimu ba Ι—aya baneba. Hankalina ya tashi domin ina tsananin Ζ™aunarta. Nai alΖ™awarin inhar zata yarda mu zama ma'aurata zan koma addininta. Ta sake tabbatarmin indai saboda aurenta ko soyayyar da nake matane zan zama musulmi wannan bazaisa ta yarda ta aureniba. Na musulinta kawai domin ALLAH badan tarayyarmu ba. A hakanma na yarda na amince, a randa muke shirin zan karbi shahada aranar Ζ΄an uwanta biyu sukazo dubata. Sun nuna mata tsantsar Ι“acin rai nayin tarayya dani, harma yanda ake musalta musu a cikin makarantar mun zama tamkar wasu miji da mata. Dagani har ita hankalinmu ya tashi muma. Dan tunda nake da ita ko maganar banza bata taΙ“a shiga tsakanina da itaba. Bata taΙ“a yarda ko zama gab da juna munyiba balle akai ga aikata wani abu mara Ζ™yau. Ni bamma taΙ“a kawo wani mummunan al'amari tsakanina da itaba kamar yanda nasan itama hakanne daga gareta. Kawai dai ALLAH ya haΙ—a jininmune kawai, kuma ina koya mata karatu. Duk yanda mukaso su sauraremu sunki, daga karshe ma suka tattarata wai zasu wuce da ita. Banyi Ζ™asa a gwiwa ba wajen tattara duk abinda nake da shi na bisu batare da sun saniba. Sai da muka dira Ζ™asar saudi-arebia suka fahimci jirgi Ι—aya ma muka shiga da su. Sun nuna jin zafin binsu da nayi, amma sai basu hanani na bisu har gidansu ba. Koda muka isa gidansu sunma iyayensu bayani akan dukkan alaΖ™ar dake tsakanina da Anum. Maimakon nai zaton za'a koreni sai naga saΙ“anin hakan, dan kuwa sun yarda da bukatata ta zama mai salla. Amma babu zancen aurena da Anum, dan suncemin yarinyarsu karatu takeyi. Duk da na shiga tashin hankali saina amince a hakan zan musilinta Ι—in. A take kuma na amshi shahada. Komawata musulmi ya sake canja komai, dan kuwa sunmin gagarumar Ζ™yauta maiban mamaki ta maΖ™udan kuΙ—aΙ—e wai na riΖ™e kaina, tare da haΙ—ani da wani malami dazan dinga Ι—aukar ilimi a hannunsa a Ζ™asar Italy. Satina biyu a saudia na dawo saboda karatuna. Amma daka ganni kasan bana cikin hayyacina saboda rabani da akai da masoyiyata. Duk na rame na fita hayyacina, amma hakan baisa nayi sakaci da karatuna ba. Na cigaba da neman ilimin addini da zana jarabawar Ζ™arshe data rage mana na tsahon watanni biyar. Har muka kammala jarabawa banji labarin kaba. Na bincika ance bakaje Nigeria ba. Hankalina ya tashi matuΖ™a. Amma yaya zanyi. Bayan yin graduation Ι—inmu na tattara zan koma gida Ζ™asata. Amma maimakon nayi 9ja direct saina kasa haΖ™uri na nufi Saudia wajen Anum. Nayi mamakin tarbar dana samu daga iyayen Anum da ita Anum Ι—in kanta daya kasance tazo hutu, dan lokacin karatunta ya dawo nan Ζ™asar Syria. Albishir na farko da suka faramin shine bani auren Anum, ashe dama sun gwadanine dan suga da gaske nakeson komawa addinin islama kokuwa dan son Ζ΄arsu?. Shiyyasa suka haΙ—ani da malamin dake koyar dani batare da nasan bayanai yake basu ba a kaina. Nayi farin ciki nayi kuka dan daΙ—i. Sai dai da aka nema na gabatar da iyayena na fito fili na tabbatar musu  akwai matsala. Dan nasan kaf danginmu babu wanda zai amshi canjawata matsayin musulmi balle kuma auren musulma kai tsaye. Naji tsoron Anum zata sake kuΙ“ucemin sai gashi ba hakaba. Dan duk da abinda na sanar musu sai gashi sun amince sun bani aurenta. Bayan Ι—aurin aurena da Anum an bamu wajen zama kafin ta koma makaranta. Watanmu Ι—aya da tarewa ta koma makaranta, ni kuma naje gida Nigeria, sai dai kowa ya tambayeni ina kake sainace kanacan baka Ζ™arasa naka karatunba sai next year. Na tarar jikin babanmu yayi tsamari, amma sunki kaisa asibiti. Inada kuΙ—aΙ—e masu nauyi a accaunt dana samu saboda musilintar da nayi, dan haka nai amfani dasu wajen kaisa babban asibiti aka fara bashi kulawa. Sai dai kash, kwanakinsa huΙ—u a asibiti ya rasu. Bayan rasuwarsa da kusan sati biyu nace musu zan koma domin yin kasuwanci. Ananne ogan daddy ya bani kuΙ—aΙ—en daddy, wai yace a bamu idan munzo, tunda mune manyan Ζ΄aΖ΄ansa maza. Na amsa kuΙ—i na basu wanda zasu wadacesu na koma saudia. Mahaifin Anum shine ya Ι—aurani akan harkar kasuwanci acan Ζ™asar Syria, ya bani shawarar na koma can kusa da matata ina kasuwancina tana karatunta. Naji daΙ—in wannan shawara kuwa. Tafiyata Syria ta zama tushen nasarata, dan ina zuwa na iske matata na laulayin ciki. Nayi farin ciki matuΖ™a, harma bansan yaya zan musalta makaba. Haka na zauna kulawa da ita tare da fara kasuwancina. Cikin amincin ALLAH sai gashi dan danan na haΙ“aka. Saboda na farane da kuΙ—aΙ—e masu nauyi. sannan kuma ta hannun babban mutum irin mahaifin Anum. A haka cikin Anum ya shiga watan haihuwa, tana gab da haihuwa na sayi wannan gidan da nake ciki, tare da motar hawa. Sannan na zauna na banbance dukiyar da take matsayin mallakina, na kuma fidda wadda ta kasance ta mahaifinmu. Kwanaki uku da yin haka Anum ta haihu namiji, wanda yaci suna Abdul-malik. bansan yaya zan bayyana maka Ι—unbin farin cikinaba Ι—an uwana. Amma babu abinda zancema ALLAH sai godiya. A yanzu haka watan Abdul-maleek uku a duniya, muna shirin zuwa Saudia ne domin nunasa ga dangin Anum dan babu wanda ya taΙ“a ganinsa sai mahaifinta da yazo mana nan sanadin harkar kasuwarsa. Daga Saudia kuma zamu wuce Nigeria na nunata ga dangina, na kuma sanar musu na zama musulmi duk da a tsorace zuciyata take. Dan yanzu haka maganar da nake makama nayi cinikin wani gida a Lagos, idan munje can zamu Ι—an zauna kafin hutun Anum na Ζ™arshen shekara ya Ζ™are. WaΙ—anan takardun sune takardun shaidar company na dana mallaka da dukiyata. Insha ALLAHU kuma zan mallakashi ga Abdul-maleek ne. Dan haka kaima inason ka zama shaida, kaimin signing anan wajen, a duk lokacin da yakai shekaru talatin na girma zan mallaka masa shi. Wannan kuma sune takardun dukiyar mahaifinmu, idan nazo Nigeria mu dukanmu zamu haΙ—u mu saka hannu alamar tabbatarwa da banawa bane ni kaΙ—ai).

     “Rungumesa nai a lokacin, na nuna masa tsantsar jin daΙ—ina da wannan Ζ™oΖ™ari nashi, tare da bashi goyen baya akan zamansa mai sallah. Yaji daΙ—in yanda na bashi goyon, hakama matarsa. Sai dai ni a cikin zuciyata Ζ™ulla ta yanda zan kwashe waΙ—anan takardun nakeyi, tare da damfare duk wata dukiya da yake fankamar ya tara. Banbar gidanba sai dare, na tafi da Ζ™udiri kala-kala a cikin raina da zuciyata”.

     “Washe gari ma naje na samesu, shine ya Ι—aukeni ya zagaya da ni duk inda companys Ι—in suke guda biyu. Na Ζ™ara girgiza da wannan al'amari, dan dukiyace bata wasaba Ι—an uwana ya tara. Tofa sai tunanina ya Ζ™ara faΙ—i da girmama. Dan koda nabar wajensu a ranar kasa barci nayi, har takai na fito na bayyanama abokin tafiyata. Yace na bashi dama zaiyi tunanin ta yanda dukkan wannan dukiya zata zama tawa, amma sai nan da kwana biyu mun gama abinda ya kawomu zai faΙ—amin hukuncin daya yanke. Naji daΙ—i, na kumayi murna. Sai dai wayewar garin ranar al'amari ya canja salo, dan bamusan yaya akaiba aka kama wanda muka kawoma kayan cocaine. Har bincike yazo ta kanmu. Da farar safiya mukaji jiniyar motocin Ζ΄an sandan Ζ™asar. Hankalina ya tashi matuΖ™a ni da abokin tafiyata, cikin zafin nama muka samu nasarar tserewa ta bayan gidan kafin Ζ΄an sanda su gama shigowa gidan. Muna barin gidan muka rabu nida abokina, domin wannan gudune na ceton rai, kuma hakan abune da kowa ya sani daga tsagera. Idan bala'i ya tunkaro kowa takansa yakeyi. Ba'a sauraren dukiyar da aka tara balle abokantaka. Cikin kiΙ—ima na nufi gidan Ι—an uwana, dan duk da wannan bala'i da nake a ciki ban manta da batun takardu ba. Ina isa na samesu a tsakar gida suna hutawarsu cikin kwalliya. Dakewa nai daga ruΙ—anin da nake ciki na amshi jaririnsu, tare da faΙ—ama matarsa nifa inajin yunwa. Dariyar tsokana suka dinga min, Ι—an uwana na faΙ—in to nazo nayi aure, yafimin wannan gararin, danshi sofa yake na dawonan tare da shi mu haΙ—a Ζ™arfi wajen kula da kasuwancinmu. Murmushi kawai nayi, na shiga daga ciki Ι—auke da yaron. Matar ta shigo ta bani abinci. Tana kammala haΙ—amin komai Ι—an uwana ya shigo, kallonta yay cike da so da kauna, yace tunda ga bro yazo kizo muje muyi shopping Ι—in nan da bamuyiba jiya, sai mubar Maleek tare da shi dan harmu dawo da wahala ya farka. A take ta amince da shawararsa. Yayinda ni kuma kaina ya kawomin wuta a take. Jacket Ι—in jikina na cire jin yana faΙ—in bara ya karo riga a saman kayansa. Nace bro indai rigace ga wanann ka saka nasan zata maka Ζ™yau, dan yanzun nan dazan fito na ganta a wani shago na siya. Nama tambayi biyu akace babu. Cike dajin daΙ—i ya amsa, dan shi mutumne mai saukin kai. Sannan bashi da saurin zargi. A gabana matarsa ta taimaka masa ya saka suna dariya da yaba Ζ™yan da rigar tai masa. Murmushi nayi ina dubansa na ajiye yaronsu na tashi ina gyara masa rigar, cikin dabara na saka masa wayata da wallet Ι—ina a aljihu, na zare tasa wayar da wallet ni kuma. Sunmin sallama sun wuce bayan sun tambayeni abinda nake buΖ™ata a siyomin nima, dan yace idan ya dawo zamuyi magana akan zamana a gidan. Suna fita na kulle Ζ™ofar falon, na bar yaron anan na shiga cikin Ι—akinsu binciken takardu dama duk wani abu mai amfani. Duk kuwa da a raina ina addu'a da fatan tarkon dana Ι—ana musu ya zama sanadin tafiyarsu har abadan. Komai na gansa, dan haka na tattare tsaf na hada a jikka, na fito falo inda yaron ke barci na ajiye tare da zaman jiran sakamako”.

      “Mintuna talatin kuwa ban rufa da zamaba saiga babban labarin da nake jiran gani daga television. Ɗan jaridan  dake bada rahoto ne ke magana cikin tsantsar sarΖ™ewar harshe, akan samun nasarar kama mutane biyu da suka shigo daga Ζ™asar Italy da hodar ibilis. An samu nasarar cafke Ι—aya a airport, Ι—aya kuma daidai traffic light tare da matarsa. Sai dai bisa kuskuren guduwa da sukayi na gardamar su basusan komaiba Ζ΄an sanda suka harbesu, wanda bisa tsautsayi suka matu har lahira. Sai ga gawar Ι—an uwana an nuno tare da matarsa kwance cikin jini. Hannayensu riΖ™e dana juna. Ga Ζ΄an sanda na lalube wallet din dana saka masa tare da wayata anata faman bincike. Ko Ι—ar banji a raina na nadamar yin hakanba, dan koba komai asirina ya rufu, zan fara sabuwar rayuwa. A take na Ζ™arasa haΙ—a duk wani abu mai muhimmanci dake gidan, tare da kayan yaron na shiga mota na fice a gidan. Na tabbatar yanzu bazan fuskanci kowacce irin matsalaba, musamman daya kasance hankalin jami'an tsaron ya koma gaba daya akan nasarar cafke masu laifi. Aiko banci karo da kowace matsalaba wajen barin Ζ™asar ta mota. Duk da naci uwar wahala ga yaro nata zubamin kuka ban damuba. Haka nai nasarar fita a Ζ™asar zuwa Ζ™asar dake maΖ™waftaka da su, acan kuma nabi jirgin ruwa, inda anan ne na haΙ—u da Chioma, itama tsagerace ta kanta, dan kuwa kusan duk irin harkokina shi takeyi, sai dai ita oganta a Nigeria take. A dai takaice na samu nasarar komawa Italy tare da jariri da Ι—unbin dukiya da takardun kaddarori da taimakon Chioma. Ogana yayi farin cikin ganina dajin labarin ta hanyar dana kuΙ“uta, dan haka yaymin alΖ™awarin taimakona ta hanyar tabbatar duk waΙ—annan kaddarori na Ι—an uwana a tafin hannuna. Yanda Chioma ke taimakona da rainon jariri dana canjama suna da John ne yay sanadin Ζ™ulluwar soyayya mai Ζ™arfi a tsakaninmu har mukaima juna alΖ™awarin aure. Ta matsa matuΖ™a muyi aure sannan mu koma 9ja dan haka na amince mata saboda nima ina sonta. Bayan aurenmu muka nufi Ζ™asar haihuwarmu cikin danginmu. Wanda zuwa yanzu labari ya gama zuwa kunnen danginmu na rasu ta hanyar kamani ina safarar hodar ibilis ni da wata, dan a haka labarin keta yawo. Kowa kuma yana Ι—auka ni aka kashe, saboda kowa yasan halina. ni kuma nine Ι—an uwana. Munzo Nigeria ne dama da shirin hutu mai dogon zango, dan ogana ya tabbatarmin dolene inyi nesa da shiga kowacce Ζ™asa. Inba hakaba kuwa babu makawa sai an bankaΙ—o ainahin gaskiyar nine mai laifi ba Ι—an uwanaba. Nayi amfani da wannan shawara kuwa, dan haka na yada zango a Lagos gidan da ya sanarmin ya saya ta hanyar abokinsa. A labarin nanfa da nake baku kowa ya Ι—auka dama nine aka kashe, dan ansan nine tsagera, Ι—an uwana kuma shine ni. Dan haka na canja sosai wajen Ι—aukar Ζ™yawawan halayyar Ι—an uwana na yafama kaina akan dole. halena kuma na Ι“oyesu, dagani sai matata muka sansu. Ban wani cika burin Ι—an uwana ba na mallakama mamana da Ζ™annenmu dukiya ba, sai dai naja Ζ΄an uwan nawa a jiki wajen sakasu cikin harΖ™allolina. Bansan yaya akai Godwin ya fahimci banine twin bro Ι—ina ba, sai kawai rana tsaka ya fuskanceni da wannan zance shi da Mike. Na matuΖ™ar tsorata da firgita, amma sai Chioma ta bani dabarun maidasu a hankalinsu ta hanyar Ζ™ara jansu jikina da rufe bakunansu da dukiya mai tsoka da kuΙ—aΙ—enta. Danni a lokacin bawani kudine da niba. Sunko bi sun tsuke bakunansu kuma, tun daga nan suka zama sunsan kowacce irin harΖ™allata, sun kuma san John ba Ι—ana baneba”.

        “Abinda ya faru baisa na daina harΖ™allataba, sai harkokine suka sake buΙ—ewa sabbi dan yanzun dukiyar Chioma muke juyawa, nazama jan wuya anan Nigeria, ta hanyar turomin da kaya da ogana yakeyi. Cikin shekara huΙ—u kacal na shahara, na kuma sakeyin kutse cikin addini har saida na zama Pastor a wata Ζ™aramar church duk da babu wani ilimi da nake da shi. Zuwa lokacin John ya fara wayo, yanada shekara huΙ—u, dan ko ina zuwa yake, ga surutu a bakinsa ba'a magana. Yanda yaron ya shiga ranmu muke tarairayarsa bazaka taΙ“a kawowa a ranka ba dΙ—anmu bane, dan soyayya ta gaske Chioma ke nuna masa. hakan yasa na Ζ™ara sonta a raina, dukda kaf dangina basa sonta dan ta rainasu, su kuma gani suke ta Ζ™waceni ta hanani taimaka musu bayan kuma dukiyarsuce tunda dai kallona suke a matsayin twin bro Ι—ina. Dukiyar Ι—an uwana tazo hannuna, sai dai ba dukantaba, dan wata an tabbatar da dolene sai John ya girma sannan  nasoba kuwa dole na haΖ™ura, na cigaba da juya abinda ke hannuna ta hanyar harΖ™alla daban-daban. A wannan lokacin ne naje Ζ™asar France yin wani couse na watanni tara, dan rashin yawan ilimi nason min tangarΙ—a akan zamana pastor. inda acanne muka haΙ—u da Sooraj Hashim Jibiya. Bayan korarsa da akai a makaranta sanadin dukan da yaymin nai jiyya kusan ta watanni uku, da Ζ™yarma na kammala abinda ya kaini na dawo gida cike da alwashi kala-kala akan Sooraj dama yankin daya fito gaba Ι—aya. Dan nayi alΖ™awarin sanadin abinda ya aikata mani saina tarwatsa duk danginsa da jama'ar yankinsa. Wannan shine dalilin farkon fara sato yara daga yankinsu ana kawomin ina cinikinsu. Sai dai na gaza lalubo a ina Sooraj yake? Dan ko'a wancan karon dama bansan taka-maimai shi Ι—an ina bane, nadai san musilmine Ι—an arewa. a zahiri kuma na lulluΙ“e True color dina da rigar addini, babu mai cewa ni shege ne. Cikin kanΖ™anin lokaci na shahara, dukiya da girma suka zauna saina tattaro na dawo Abuja. Wani halaye da John ya fara nuna mana na Ζ™yamar addini da wasu abubuwan namu duk da Ζ™anΖ™antar shekarunsa yasa hankalina tashi. Dan da alama yaron yanada wata baiwa dake nuna ya fahimci kamar muΙ—in ba iyayensa bane. Mike ne ya bani shawarar zuwa gidan boka a kulle tunanin Yoohan gaba Ι—aya, koda ya girma bazai taΙ“a kawo a ransa muΙ—in ba iyayensa bane koda yaga rashin kamansa da Chioma. Naji daΙ—in wannan shawara, nakumayi amfani da ita. Bayan munje wajen boka ya amsa zai mana aiki, sai dai aikin zai zama sanadin saka ciwon rashin barci ga John lokaci-lokaci. A take kuwa muka amince, akai asiri John ya koma tafin hannunmu sosai. Duk abinda muka sakashi babu tantama yake mana, sai dai ban taΙ“a yarda yasan Ι“oyayyar harΖ™allataba Mamana ma da sauran Ζ΄an uwana nasa akai musu asirin da bazasu taΙ“a tunanin ko kawowa a ransu niΙ—in ba Ι—an uwana bane. Ana haka Chioma ta haihu twins itama, Gebrail da Joy. Nayi farin ciki sosai da samuwar nawa Ζ΄aΖ΄an, amma samun nawa baisa naji tsanar Yoohan ba. Bayan su Joy Chioma bata sake yarda ta haihuba sai da John ya shiga jami'a ta sake haihuwar Victoria. Ta sake Abraham wanda cikinsa yazo mata babu shirin hakan, dan tace daga yaΖ΄a uku ta gama. To ashe da rabon zuwan Abraham. Abinda yasa nasaka Solomon kullum yake tare da John tun bayan gama karatunsa, saboda tsoron kar wajen yawon Ζ™asashensa da aiki ya tilasta masa yin  gamo da wani dangin mahaifiyarsa Ζ™waΙ“ata tayi ruwa. Shiyyasa dukkan motsinsa sai na sani ta hanyar Solomon”.

        “Abu mafi Ι—agamin hankali daya faru shine tarayyarsa da Sheikh Sooraj. Lokacin dana san wannan alaΖ™a hankalina yayi Ζ™ololuwar tashi,  na kumayi murna dan sanadin John maΖ™iyina dana Ι—auki shekaru ina bulayin nema ya bayyana. har Ζ™auye naje mukai zaman meeting da sauran mutanena, dan saboda gudun irin haka yasa na cusa masa Ζ™iyayyarsu tun yana yaro, amma daga Ζ™arshe sai gashi abinda nake gudun ya auku. John ya xama musulmi kamar mahaifinsa. Ranar nayi tamkar mahaukaciya a gidan nan, harma na yanke hukuncin kashesa kawai na huta bayan na sakashi ya sakamin hannu a takardun da naketa a jiya tsahon shekaru, dan company Ι—in yanata haΙ“aka zuwa yanzun, sai dai ina mamakin ta hanyar wa hakan ke faruwa?. Su Mike ne suka haΙ—u wajen bani shawarar mizaisa na damu da musilincinsa. Sun san dai babu ta yanda za'ai ya iya gano shiΙ—in wanene saboda asirin da ke a kansa. Sooraj kuwa amfani zamuyi da kusancinsa da John Ι—in mu yashe masa asusunsa tsaf mubarsa da Ι—imautar Ζ™waΖ™walwa da bugawar zuciya. Amma wai koda na tuntuΙ“i John akan mike alaΖ™arsu sai ya nunamin wani aiki yakeyi akan Sooraj Ι—in. Nafa yarda da shi har cikin raina. Saboda nasan irin horon danai masa tun yana yaro akan wannan yanki. Har raina daΙ—i nakeji zai Ι—aukamin fansa akan abinda Sooraj yaymin tsahon shekaru, dan duk da korar da akai masa a makaranta wancan karon baisa na huceba, na kuma daΙ—e ina addu'ar haΙ—uwarmu amma hakan bai yuwuba sai yanzun. Ban fahimci John folani yake a kwalayeba sai akan aurensa da Ι—iyar Sooraj, idan nace zan bayyana muku halin dana shiga ni da matata dasu Mike a wannan tsakanin Ι“ata lokacine, da Ζ™yar Godwin ya kwantar min da hankali akan na amince da auren, bayan anyi mu kashe yarinyar yanda Sooraj zaiji ciwo sosai a ransa kafin kuma mu yashe masa asusunsa. Wannan shawarace ta kwantarmin da hankali na amince akai aure batare dana yarda na nunama Yoohan nasan ya musulintaba, sanann matata ma ban taΙ“a faΙ—a mata ya zama mai salla ba dan nasan tana son John sosai fiyema da Ζ΄aΖ΄anta, kodan shita fara samu matsayin Ι—a ne kafin ta haifi nata oho. Shigowar Ι—iyar Sooraj cikinmu ta sake ruguza komai na shirinmu, dan yarinyace hatsabibiya. takai ko ganinta nai sai naji matsanancin tsoro na shigata. Bala'in kwarjini takemin kamar ubanta, gata bata da tsoro. Ban sake tabbatar da yarinyarnan abar tsoro bace sai randa ta shigar min Ι—aki, ta kuma nuna ba ita bace. Da gaske nima Ι—in na yarda ba ita Ι—in bace a lokacin, sai daga baya na gane itace ta hanyar cctv dake a falona wadda ko matata batasan da zamanta ba duk da kuwa harΖ™alla Ι—aya mukeyi, kai hasalima na sakatane domin ita dan haka harkarmu take a kullum bama yarda da juna. Bawai ina tunanin itama zata cutar dani bane, dan ina tsananin Ζ™aunarta, na kuma yarda da ita. Ina tsoron kar dai cikin abokan harΖ™alla wani yay amfani da ita ya cutar dani ne dai. Sosai hankalina ya tashi da lamarin yarinyar, da kuma tunanin mahaifintane ya turota leΖ™en asirina. Sai kawai na shirya yanda Doctor Ι—in da zasu mata aiki zasu kashe min ita ta cikin sauΖ™i kafin na dawo kan John Ι—in shima. Naji daΙ—in abinda Gebrail yay mata, dan nasan nesa tazo kusa akan aiwatar da aikina a kanta, sai dai kash Dr Mateo ya lalatamin burina. Naji takaici, naji ciwo, na kuma yanke shawarar halaka John da yarinyar gaba Ι—aya da zarar sun dawo Ζ™asar nan. Zan fara halakata ita da duka danginsu da ubanta kafin shi ma na juyo kansa. Amma taurin kai irin na John da bani da tantama wajen ubansa ya gada sai ya sake ruguzamin shirina. Ya koro Solomon, ya kuma Ι—auketa daga Austria ya canja mata Ζ™asar da bani da damar shiga, dan tuni aka hanani lasisin shiga Ζ™asar U.S. Wamnan shine dalilin yimin katanga a garesu, na zauna dakon jiran dawowarsu ko zuwansu Ζ™asar a tare. A randa John ya dakarmin yaro wai ya shigar masa Ι—aki naji kamar shima na halakashi da hannuna. Amma na taushi zuciyata dan nasan a tafin hannuna yake. Shina Ζ™anΖ™anin lokacine ya rage masa ai. Na tattara komai na ajiyeshine ban masa magana a kaiba dan banason ya zargi komai a kaina har sai randa ya sakamin hannu a waΙ—annan takardun, ya kuma kawomin shegiyar matarsa Ζ™asarnan. Dan nagama shiryawa tsaf akan yanda zan yashe asusun ubanta kaf na maidashi sifili. Wai kawai kwatsam rana tsaka saiga yarannan da ciki sunzomin gida. Lallai naga baΖ™ar rana kuwa, dan da gaske ranar susucewa nasoyi gaba Ι—aya. Randa na gama shirya Ζ™udirin aikata lahira suka baro Abuja batare da ko John ya sanar minba da yake shima tantirin Ζ™wallon shege ne. Nasa a biyota kanon, a daren da zasuzo bisa jagorancin Solomon kuma Ζ΄an sanda suka ritsamin yaro a hanyarsa ta kawomin kaya daga Ζ™asar Cameroon. Da Ζ™yar yasha zuwa abuja, duk sun fasa masa jiki da bullets, amma sai yayi Ζ™oΖ™arin zuwa ya isarmin da saΖ™on na gudu, dan da gaske wanann tarkone babba aka Ζ™ulla a kaina tsahon lokaci. wannan shine sanadin tserema Ζ΄an sanda da nayi, sai da na bada Ζ™afa ta watanni biyu na dawo da baya saboda jin matar John ta haihu ta hanyar wani Ι—an leΖ™en asirina. Na fahimci lokaci yayi da zai sakamin hannu a takardu, daga haka na kama gabana bayan na kasheaa shi da Ι—an da matar tasa. Sooraj kuwa zan dawo masa da nasa shirin bayan Ζ™ura ta kuma kwanciya.......”

       Kallonsa kawai kowa keyi a falon kamar sun sami television. Dan shi kansa Jay makircin na Goshpower ya matuΖ™ar rikitashi. Ashe shine sanadin halakar Ζ™anwarsa da mijinta. Iya bincike sunyi bayan faruwan wancan al'amarin amma suka gagara sanin gaskiya, dan sudai basusan mijin Anum da wani twin Brother ba. Ba komai yaja hakaba sai sakacin rashin bincike danginsa koda a Ι“oyene, duk da dai shi yaso yayi binciken a lokacin mahaifin Anum Ι—in yace a barsa darajar gaskiyar yaron, a bashi dama har ya bayyana mana danginsa suma ya bayyana musu mu. Tunda dai shi sun gwadashi ta hanyoyi da dama basu samesa da wani mummunan hali ba. A lokacin haushi shi Jay yaji yace ya cire hannunsa akan batun, dan ya rasa wane irin so sukema mijin Anum Ι—in. Ganin yanda ya dage da harkar nema da neman ilimin addini yasa shima Jay din Ι—aga masa Ζ™afa ya bashi lokaci zuwa sanda Anum zata haihu, dan yayi alΖ™awarin da zarar ta haihu kosu Ummu sun yarda ko basu yardaba dolene yasan dangin mijin Anum ta hanyar tasa Ζ™eyarsu har Nigeria aje tare da shi. Sai gashi a dai-dai gaΙ“ar da take shirin kawo musu ribar auren nata su gani su kuma je ga dangin mijin nata wannan al'amari ya bayyana. Wanda ta sanadin haka suka rasa Ζ΄ar uwarsu da mijinta da Ι—anta. Suka kuma rasa ainahin gaskiyar zance akan zargin da akema mijin nata. Haka suka haΖ™ura badan zukatansu sunsoba, suka Ι—auka wannan itace Ζ™addararta kuma. Tare da mahaifinta sukaje suka amshi gawarsu wajen Ζ΄an sanda bayan ansha gwagwamaya suka sallacesu aka kaisu makwancinsu. Sai dai basuga gawar yaronba, sai suka Ι—auka wani ya Ι—auke gawar a cikin wannan rubibi. Sai dai a binda ya Ι—aure musu kai rasa muhimman takardun mijin Anum a gidansa. Bayan wasu watanni kuma akazo musu da batun an Ζ™wace duka kaddarorin nasa dake a Ζ™asar ta Syria. Basu da ikon nuna rashin yarda tunda sunsan hakan shine dokar Ζ™asar ga duk wanda aka kama da irin wannan laifin. Badan zukatansu sunso ba daga haka suka rufe babin Anum da duk abinda ya shafeta. Sai kuma gashi kwatsam bayan tsahon shekaru sunci karo da mai tsananin kamanni da ita a Nigeria, tare kuma da mai tsananin kamanni da mijinta matsayin ubansa. Wannan abu ya rikita Jay matuΖ™a, harma yaji a aransa inama Ummu da mahaifin Anum na raye su tayasa wannan al'ajabi.....

     Ta Ι“asan da Jabeer yayine ya sakashi dawowa hayyacinsa daga tunanin daya tafi, Jabeer ya nuna masa agogo da faΙ—in, “Boss asuba fa na gab da shiga, muyi abinda ya dace kafin masu Ζ™arfin faΙ—a aji suce wani abu”..............✍





Post a Comment

0 Comments