TOP HAUSA NOVELS atOptions = { 'key' : '20e08520dad54dbf6d9e963271

Makauniyar soyayyah page 67-68

 *STORY & WRITTEN*



            *BY*



*MARYAM AHMAD PAKI*





*🌈KAINUWA WRITERS ASSOCIATION*🤝🏽




*TA’AZIYYA*


_Ina mik’a sak’on ta’aziyya ta ga family d’in Murjanatu Alhassan wacce Allah ya ma rasuwa a ‘Yar aduwa University a sanadiyar rashin lafiyan da tayi_.


_Allah nake rok’o ya jik’an ki ya gafarta miki, Allah yasa aljanna ce makomar ki_.


_San da naji labarin rasuwar ki ba k’aramin tashin hankali na shiga ba, nasan nayi rashi, ke k’awa ce ta gari da bazan mantaD dake ba_

😭😭😭


_Ina mik’a sak’on ta’aziyya ta ga Hussaina wacce Allah yayi wa mijin ta rasuwa_.


_Halima Mk ina k’ara mik’a sak’on ta’aziyyata gare ki na rasa mijin ki da kika yi_.


_Allah nake rok’o ya jik’an su baki d’aya ya kyautata makwancin su, ya sa aljanna ce makomar su, Allah mu ma ka kyautata k’arshen mu_


_Ina rok’on duk wanda ya karanta wannan page d’in yasa su a addu’a_



 



*QUESTION OF THE DAY*


_Wace surah ce take karantar da cewa duka abubuwan duniya suna da dangantaka da junansu, dangantaka bayyananna ko’boyayya, Kuma zumuntarsu na gudana gwargwadon dangantakarsu da juna_






67-68


Su Abbu kuwa ba k’aramin fushi suka yi dani ba, yaya Khalil ma ya fisu shiga damuwa saboda yadda muka fi shak’uwa dashi, ba wani mai walwala a cikin su tun san da na bar gidan mu.


Dadin su Faruk ya bada cigiya ta a kafafen yad’a labarai, sannan ya kai report police station amma har yanzu shiru ba wani bayani a kaina.


Tsakanin Dadi da Abbu an rasa mai k’arfin gwiwar da zai iya tunkarar Hajiyan Wagini akan rashin gani na da ba ayi ba, tunanin fad’an da za tayi da halin da za ta shiga yasa suka ‘boye mata, sun barshi akan sai an ganni za a sanar mata da komai, a cikin su ba wanda tunanin shi ya kawo can zan tafi.


Yau kwana biyu kenan da wayar da yaya Faruk suka yi da Dadi sai gashi a Kaduna.


Tun san da Dadi ya kira shi yake tunanin dalilin kiran da Dadi ya mishi, yasan in akan biki ne zai sanar dashi a waya, ba sai yace yazo ba.


Bayan ya huta ne Dadi ya kira shi side d’in shi.


Samun shi yayi da Momi a zaune, alamun dake fuskar su na nuna kowa da abin dake damun shi.


Sallama ya musu ya nemi guri ya zauna.


 Dadi ne yayi k’arfin halin amsa masa sallama.


Cikin ladabi yaya Faruk ya ce "Gani Dadi".


Dadi sai da saki ya gauron numfashi saboda tunanin abin da zai fad’a ma yaya Faruk ba mai dad’in ji ba ne kana ya kira sunan sa "Umar!

Cikin sanyi ya amsa "Na’am Dadi".


A ranshi kuwa jinjina abin da Dadi zai fad’a mishi mai matuk’ar mahimmanci ne tun da ya kira ainihin sunan shi.


Dadi ne ya nisa kafin yaci gaba da cewa "Faruk, dalilin da yasa na ce kazo Kaduna shine akan wata k’addara da ta faru bayan tafiyar ka wanda yake da alak’a da kai, ka ga kenan ‘boye maka bai da wani fa’ida".


Tun kan Dadi ya fad’a mishi maganar da yake son fad’a mai, yaji jikinshi yayi sanyi, yanzu jikin shi ya fara bashi ba abu mai dad’i Dadi zai fad’a mai ba.


"Faruk abin da nake son fad’a maka shine yau kwana hud’u kenan ba a ga Fatima ba, ba a kuma san inda ta tafi ba, hakan kuma na da nasaba ne da auren da za a muku da kuma wanda take so shi wannan Dr d’in, ina son ka d’au hakan a matsayin jarabawar ka, shi Ibrahim saboda ranshi a ‘bace yake ya ce ko da ba ta dawo ba zai d’aura mata aure dakai, kuma ni na fahimci dan ya faranta maka zai yi, ni kaina nasan Ibrahim da Aisha suna nuna maka so kamar d’an da suka haifa,sun kansu yanzu suna cikin damuwa da abin da Fatima ta aikata, maganar a d’aura aure ba a ga Fatima bai taso ba, za a k’ara ‘bata Al’amarin ne, gwara in ta dawo a san yadda za ayi, ba na so ka sa wannan matsalar a ranka dan guje ma kamuwa da wata cutar, kayi hak’uri Faruk, nasan Fatima ba ta kyauta maka ba" ya k’arasa maganar cikin lallashi.


Tun san da lokacin da Dadi ya fara labarta mishi wannan mummunan labarin kan shi yake a sunkuye ba tare da ya d’ago kai ba.


Duk wannan maganganun da Dadi yake ma yaya Faruk ji yake kamar ana watsa mishi tafasasshen ruwan zafi ne a zuciyar shi, ran shi ba k’aramin ‘baci yayi da jin wannan labarin ba, jijiyoyin kanshi duk sun tashi, idanun shi duk sun canza launi zuwa ‘bacin rai, bai ta’ba kawo wa a ranshi wannan mummunan labarin Dadi zai sanar dashi, ji yake ina ma mafarki yake yi ya samu ya farkar daga wannan mummunan mafarkin wanda bai fatan ya k’ara yin irin shi, sai dai kash! Wannan mummunan labarin a zahiri Dadi yake sanar dashi, yau ya k’ara tabbatar da maganar da Hausawa ke cewa idan wani yak’i ka wani sai yaso ka, shi da ‘yan mata ke son shi yana ja musu aji, nan ya tuno da Binafa yadda take mishi magiya akan ya so ta saboda yadda ta kamu da son shi, ya samu ya ba ta hak’uri ta hak’ura da sauran ‘yan matan da suka fad’a mishi suna son shi bai kula su, sai gashi an samu  a kanshi na gudu saboda kar na aure shi duk kuwa da irin son da ya nuna min amma ni ban ga hakan ba, na za’bi bare a kanshi, ba abin da yafi tsaya mishi a ranshi shine yadda na dinga mishi yawo da hankalin shi na k’in fitowa a fili na fad’a mishi ba na son shi da wuri, sai daga baya da ya sakankance da cewa ina son shi sannan na nuna mishi da ban yi na’am dashi ba, yanzu ba abin da yake mishi yawo a k’wak’walwar shi shine guduwar da nayi wanda ba a san inda na tafi ba, a yanzu yana ganin ba abin da zai fi mai sauk’i illah ya samar wa kanshi mafita kafin dawowa ta, shi kad’ai yasan matakin da zuciyar shi ke fad’a mishi ya d’auka akan wannan curkud’ad’d’en al’amarin, yana ganin ba wanda yafi cancanta da ya nemo ni dan zartar min da hukuncin da ranshi ke ayyana mishi da ya yanke wanda yake ganin shi kad’ai ne zai kawo k’arshen wannan abun da yake faruwa tsakani na dashi.


Momi da Dadi jikin su ne ya k’ara yin sanyi ganin halin da yaya Faruk ya shiga tun a yanzu wanda ke nuna tsantsar tashin hankalin da yake ciki da kuma ‘bacin rai da ya mishi dabaibayi a lokaci guda.


Falon ne ya d’auki shiru ba tare da kowa ya sake magana ba, kowa da irin tunanin da yake ayyanawa a ransa.


Jin shirun da yayi yawa ne yasa Dadi ya kira sunan yaya Faruk cikin tattausan harshe.


Yaya Faruk ne ya d’ago kan shi wanda yake mishi wani matsanancin ciwo, wani irin nauyi kan yake mishi saboda tsabar ciwon da yake yi mishi.


"Come close to me my son" Dadi ya fad’a cikin lallashi.


Ba abin da yaya Faruk yafi buk’ata a yanzu da ya wuce yaji shi a kwance ko ya samu sauk’in rad’ad’in da yake ji a zuciyar shi da kuma kan shi da yake mishi matsanancin ciwo.


Ba tare da musu ba ya matso ya kwanta a jikin Dadi, a lokacin ne yaji wani irin zazzafan hawaye na fita daga idanun shi, sai faman sauke ajiyar zuciya yake yi kamar wanda yaci kuka ya k’oshi, k’arshe ma runtse idon shi yayi ko ya samu sauk’in halin da yake ciki, sai faman karanta *Inna lillahi wa inna ilaihir raji’un* da *Allahumma ajirni fih musibatih, wa aklifni khairan minha* wannan addu’o’in su yake ta faman maimaitawa a cikin ranshi, a hankali yaji natsuwa ta fara shigar shi, ‘bacin ran da yake tare dashi ya fara raguwa.


Momi na ganin halin da yaya Faruk ke ciki ita ma ta fara zubar da hawayen tausayin shi, tasan daman hakan za ta faru, yaushe rabon da ta ga hawayen yaya Faruk, amma yau a dalili na yaya Faruk na zubar da hawaye.


Dadi na lura da hawayen da Momi ke yi, yasan dole ta shiga wannan halin in dai ta ga yaya Faruk a cikin wannan halin, shi kanshi kawai dauriya yake yi ba wai dana bun bai dame shi ba, a yanzu ba wanda yafi buk’atar lallashi sama da yaya Faruk.


Dadi ba abin da yake faman yi sai shafa kan yaya Faruk yake yi kamar yadda ake lallashin k’ananun yara, a lokaci d’aya yana fad’a mishi sweet words masu kwantar da hankali.

Jikin shi da yaji ya d’au zafi wanda hakan ke nuna zazza’bi ne ya kama shi mai zafi.


Janyen jikin shi yayi daga jikin Dadi, hannun shi yasa ya rik’e kan shi wanda yake ji kamar zai tsage saboda ciwon da yake mai.


Tashi yayi da niyar tafiya, ya fara tafiya kenan, hannun shi na dafe da kanshi, jirin da yaji yana d’ibar shi, nan ya fara tangad’i zai fad’i, da sauri Dadi ya taso dan ya rik’e shi kafin ya fad’i, ko kan Dadi ya k’arasa yaya Faruk ya fad’i a k’asa.


Momi ce ta taso da gudu tana kuka tazo tana jijjiga yaya Faruk.


Anisa ma wanda shigowar ta yayi daidai da fad’uwar yaya Farud da gudu ita ma ta k’araso gurin yaya Faruk wanda yake kwance a k’asa.


Momi kuwa cikin kuka cewa take yi "Faruk ka tashi, ku kad’ai gare ni, daga kai sai Anisa, ku kad’ai Allah ya ba ni, kar ka mutu saboda ‘ya mace, idan ka mutu ban san halin da zan shi ga ba".


Anisa ma cikin kuka ta kwanta a jikin yaya Faruk tana cewa "yaya Faruk dan girman Allah ka tashi, kai kad’ai ne d’an uwana da nake kalla na ji sanyi a raina, kar ka tafi ka barni da maraicin ka, rashin ka zai sa in shiga cikin wani mawuyacin hali, yaya Faruk kaji tausayin mu ka tashi dan Allah…" nan ta k’ara fashe wa da wani irin kuka.


Cikin Momi da Dadi an rasa mai lallashin wani a cikin su.


Dadi ne ya ta’ba yaya Faruk yaji yana motsi, hakan yasa ya fahimci suma yayi.


Da sauri ya wuce gurin d’an k’aramin fridge d’in shi ya d’akko faro water mai sanyi yazo ya yayyafa mishi a jikin shi.


Saukar ruwan da yaji a jikin shi yasa ya saki wata ajiyar zuciya.


Dadi ne da Momi suka samu suka kama shi suka kai shi side d’in shi.


Wayar shi Dadi ya d’akko ya kira family Dr d’in su ya fad’a mishi halin da yaya Faruk ke ciki.


Ba a d’au wani tsawon lokaci ba sai ga Dr yazo da kayan aikin shi.


Bayan gwaje-gwajen da Dr ya mai ne ya kalli Dadi ya ce "Alhaji a gwaje-gwajen da nayi na gano Faruk yana yawan tunani duba da yanda BP d’in shi ya hau, yawan tunanin da ya fara yi mishi yawa ne ya jawo mishi ciwon kai mai tsanani wanda hakan yasa temperature d’in jikin shi ya canza, ciwon kai da jirin ne ya hadassa mishi suma, sannan Alhaji pls a kiyaye fad’a mishi abin da zai sa ranshi ya ‘baci don kiyaye lafiyar shi, yanzu zan mishi allurar da zai sakko mai da zazza’bin, zan kuma sa mishi drip da yaji k’arfin jikin shi, sannan zan ba da maganin da za a bashi yasha, in da hali a barshi ya huta don a yanzu bai buk’atar hayaniya".


"Za mu kiyaye insha Allah" Momi ta fad’a.


Bayan ya mishi allura ne yasa mishi drip kana ya musu sallama suka fita da Dadi.


Tun da aka sa ma yaya Faruk drip yake ta faman barci kasancewar har da allurar bacci Dr d’in yasa mai.


Momi ce ta koma side d’inta dan dafa wa yaya Faruk abincin da zai ci in ya tashi.


Anisa kuwa zama tayi a kusa dashi tana kallon yadda yaya Faruk ya koma a lokaci guda.


Ba abin da take furta wa sai "Fatima why, me yasa za ki sa yaya Faruk a wannan halin da yake ciki" a lokaci d’aya hawaye na ci gaba da zubowa a idanun ta.


Yaya Faruk sai da ya kwashe fiye da awa uku yana bacci kafin ya tashi daga baccin.


A hankali ya dinga bud’e idon shi, Anisa ya gani a gefen shi tana rik’e da d’ayan hannun shi wanda ba a sa ma drip ba, yayin da hawaye ke zubowa a idanun ta.


Ganin yaya Faruk ya farka yasa ta saki murmushi ta ce "yaya Faruk ka tashi, sannu ya jikin, yanzu ina yake maka ciwo, akwai abin da ka ke so ne, ko in kira Momi ne?".


Jin wannan jerin tambayoyin da Anisa ke jero mishi yasa ya girgiza mata kai.


K’ara rik’e hannun ta yayi yana kallon ta, idanun ta da ya gani ya canza kala ya tabbatar mishi da tayi kuka, hannun shi yasa yana goge mata hawayen.


Kwanciyar da ya ji ya gaji da ita ne yasa a hankali ya tashi ya zauna.


Da sauri Anisa ta kara mishi pillow a bayan shi ya jingina da gadon.


Drip d’in da taga ya k’are ne yasa ta cire mishi ta koma ta zauna.


"Me yasa ki kuka?" yaya Faruk ya tambaye ta.


Kamar jira take yi ta k’ara sa wani kukan, cikin kukan take cewa ‘yaya Faruk dan Allah ka daina sa tunani ni a ranka, likita yace BP d’in ka ya hau kuma duk a dalilin tunani, plss ka cire tunanin Fatima a ranka".


A hankali ya ce "Kar ki damu Anisa, komai ya kusan zuwa k’arshe insha Allahu, ki daina kuka kin ji my lovely sister".


"Na daina yaya Faruk".


Momi ce ta shigo da foodflask a hannun ta da flask.


Ajiye wa tayi a kan centre table ta nufi yaya Faruk cikin fara’a ta ce "Ka tashi Faruk, sannu ya jikin".


"Da sauk’i Momi".


"To Allah ya k’ara sauk’i".


"Amin Momi".


Niyar mik’ewa yayi da niyar tashi amma har yau jikin shi ba k’arfi.


Momi ce ta ce "Ina zaka kuma".


Cikin muryar marasa lafiya ya ce "Ina so in je in watsa ruwa ne, jiki na ne nake jin shi ba k’arfi, ga shi ina so in yi sallah la’asar da ban yi ba".


Cikin tausayawa Momi ta ce "Ka bari kaci abinci zaka ji dad’in jikin ka, in yaso sai ka watsa ruwan kayi sallah".


"Bari in je in yi brush in dawo".


"Ok" Momi ta amsa mishi.


Tashi yayi a hankali yake takawa, da alama har yanzu bai gama jin k’arfin jikin shi ba.


Band’aki ya shiga ya d’auraye fuskar shi kana yayi brush ya fito.


Dawowa yayi ya jingina da gadon.


Momi ce ta kalli Anisa tace "Je ki kan fridge ki d’akko plate da cup a zuba mishi ya ci".


Anisa ce ta had’a mishi kakkauran Tea wanda yaji madara a ciki, d’ayan plate d’in kuma farfesun kayan cikin ne a ciki.


Momi ce ta amshi tea d’in da plate d’in ta matsa kusa da yaya Faruk d’in.


Tea d’in take bashi a baki wanda yake shan shi kamar mad’aci hakan yake jin shi a bakin shi, kad’an yasha tea d’in y ace ya k’oshi, ajiyewa Momi tayi ta fara bashi farfesun, yana shan farfesun ne ba wai dan yana jin taste d’in shi a bakin shi ba, sai don kar ran Momi ya ‘baci yasa yake sha.


Dadi ne ya shigo d’akin yayi don ganin jikin yaya Faruk.


Samun shi da yayi ya farka har yana d’an cin abinci yasa yaji dad’i a ranshi.


A hankali ya k’araso gurin su yana Murmushi ya kalli yaya Faruk ya ce "Jiki yayi sauk’i kenan Faruk, Allah ya k’ara afuwa da sauk’i".


Amsawa yayi da "Amin".


Bayan ya gama cin abincin ne ya mik’e yaje ya watsa ruwa yayi alwala yazo ya rama sallolin da ake bin shi kana ya koma ya kwanta.


Dadi ne ya kira su Abbu ya sanar dasu rashin lafiyar yaya Faruk.


Da daddare sai gasu Abbu, Ummu da yaya Khalil sun zo duba shi.


Jikin Ummu ne yayi sanyi ganin da Momi take amsa musu maganar su kamar ba ta so, tasan hakan bai rasa nasaba da halin da yaya Faruk yake ciki wanda a dalili na hakan ya faru dashi, ko waye aka yi wa d’anta haka dole ne ranta ba zai mata dad’i ba.


Anisa kuwa tun bayan gaishe dasu da tayi ta tashi ta bar d’akin.


Shi kanshi yaya Faruk bai ji dad’in yadda Momi tayi ma su Ummu, da yadda yaga Anisa na share yaya Khalil, yana ganin wannan abin da ya faru tsakanin shi da ni ne, bai kamata su ‘bullo da wannan matsalar ba duk da yasan dan saboda shi suke yin haka, suna jin haushin abin da na mishi.


Yaya Khalil ne ya tashi ya bi ta d’akin ta amma ta k’i sauraren shi, a iya nazarin da yayi yasan ba abin da ya had’a shi da ita bare yace fushi take yi dashi, duk wasu kalamai na lallashi da ya kamata ya fad’a mata ta saurare shi amma tak’i, sai ma kuka da ta sa mishi.


Jikin shi ne yayi sanyi da kukan da yaga Anisa ta na yi, shi kanshi yanzu dauriya ce yake yi irin ta namiji, gashi kuma Anisa na so ta d’aga mishi hankali da kukan ta.


Cikin kukan take cewa "yaya Khalil ina rok’onka ka k’yale ni, ka barni na ji da halin da nake na halin da d’an uwa na yake ciki a yanzu wanda ‘yar uwarka ce silar shi shiga wannan halin, yaya Khalil tun da Fatima ta nuna ba ta son d’an uwa na to nima ina ganin babu wani fa’ida a ci gaba da soyayyar mu, nima ina kishin d’an uwa na kuma ina son sa, yaya Khalil ka fita na ce" ta k’arasa maganar cikin kuka.


Sai yanzu yasan akan abin da yasa Anisa take k’in kula shi, tana mishi haka ne saboda ta rama abin da Fatima ta yi ma d’an uwan ta, yasan ko mai zai fad’a mata ba za ta saurare shi ba, abin da ya fi shine ya bari ta sakko, hakan zai fi sa su fi fahimtar junan su.


Kallon ta kawai yayi ya girgiza kai ya fita daga d’akin.


Yana fita ta sake fashewa da wani kukan, wannan lokacin akan abu biyu take kukan, na son yaya Khalil da ke d’awainiya da ita a cikin zuciyar da rashin yi mishi adalci na hukunta shi da laifin da ba nashi da kuma tausayin halin da yaya Faruk yake ciki.


Haka su Ummu suka yi sallama da su Momi kowa da abin da yake damun shi a ranshi.


Ranar haka yaya Faruk ya kwana da tunanin in da na tafi.



Washegari jikin yaya Faruk yayi sauk’i dan ya samu ya fito falo ya zauna, ganin yadda kowa ke nuna mishi kulawa yasa ya saki jikin shi duk kuwa da yadda yake jin zafi a cikin zuciyar shi na abin da na mishi.


Yaya Aminu ma yazo da Anty Jiddah sun zo sun duba shi, yaya Aminu haka ya ci gaba da kwantar mishi da hankali, ya nuna mishi shi kanshi halin da yake ciki na abin da na aikata.


Sun d’an jima a gidan kana suka koma gurin Momi suka mata sallama suka tafi.


Yau kwanan yaya Faruk biyu da zuwan shi Kaduna ya shirya zuwa Wagini gaishe ta, kiran ta da yayi a waya haka ma Dadi ya sanar dashi shima bai samun ta a wayar, hakan yasa ya shirya tafiyar.


Fito wa yayi cikin shigar wani yadi mai laushi kalar ash, in ban da k’amshin turare da yake tashi ba abin da falon yake yi.


Sallama yayi ma su Momi akan ya tafi Waginin, may be zai kwana a can ko ya dawo yau.


Fatan a dawo lafiya suka mishi.



Kasancewar ya sa wa motar speed yasa ya isa Wagini a da wuri.


Hajiya na zaune a tsakar gida tana sauraren radio taji shigowar yaya Faruk.


Sallama yayi yazo ya zauna kusa da ita akan tabarmar da take zaune.


Amsa masa sallamar tayi da fara’a a fuskar ta.


Hajiya ce ta ce "Maraba da mai gidana Soja na kaina, sannu da zuwa".


"Yawwa Hajiya, mun same ku lafiya".


"lafiya lau, ya aiki, ya wajen iyayen naka"


"lafiyar su lau, suna gaishe ki".


"Hajiya lafiya wai ba a samun wayar ki, su Dadi suna kiran ki ba sa samu, nima na kira ba ta shiga sai a ce min a kashe take".


Hajiya dama kamar jira take yi ta fara fad’a "Rashin samu na da ake yi ba zai rasa nasaba da wannan ‘yar buhun ubar ba, ba yadda banyi da ita ta gyara min wayar nan amma yarinyar nan tak’i, idan na ce ta kira min ku a wayar sai ta ce ba ta shiga, haka na gaji na k’yale ta".


Murmushi kawai yayi yace "Wai wace yarinyar ce ki ke magana Hajiya".


"Au kai duk bayanin nan da nake yi ba ka gane wacce nake nufi ba, to amaryar ka nake nufi Fatima…".


Da sauri ya katse da cewa "Wace Fatiman wai Hajiya".


Hajiya ce ta mishi dak’uwa tace "Ungo naka, kaji ni da shak’iyin yaro, yau Fatiman ce ba ka gane ba".


"Hajiya kina nufin Fatiman Abbu, dama tana nan ne".


"Yau kwanan ta kusan shida kenan, na ji kana tambayar dama tana nan ne, kana nufin ba a san tana nan ba ne".


"Tana ina ne Hajiya?".

 

"Tana can cikin d’aki, hala tana can ta kunna kururuwar shed’an tana saurara, yarinya ba ta da aiki sai kunna wak’ok’in soyayya kamar a kanta aka fara".


Bai tsaya sauraren abin jin bayanin da Hajiyan Wagini ta ke mishi ba ya mik’e ya nufi d’akin.


Duk yadda na ‘bata mishi hakan ba zai hana shi jin dad’in tawowa ta nan Wagini ba, kowa tunanin shi bai kawo nan na tawo ba.


Ni kuwa ina kwance akan gado, earpiece ne a kunne na ina sauraren wak’ar Hussaini Danko, sauraron wak’ar na ke yi sannu a hankali kamar ni na raira ta, mai taken _SOYAYYA TA_


Bin wak’ar na fara yi inda mai amshin take cewa _nima soyayya ta zan furta_

 _ba a saka ni rana d’aya in yi gudun ka_, _so d’ammara nayi ko za ya saka min hauka_, _ko mutuwa nai zan so a dalilin son ka , _so ajiya nayi ranar shi tazo zan d’auka_, _idan tafiya nayi an ce da gwani amsar ka_, _nace kai na za’ba_, _har zuci bazan canza ba_, _ba kuma zan k’osa ba…_, _ni kaine burina ba a hana ni zuwa gurin ka_, _so ne jagora na shi ya dasa min k’imarka_, _amsar tambihi na je ka rabe min hujjar ka_, _ya zan yi in k’yale ka in ta zama a cikin cuta_, _so so soyay…_


Sauran baitin ne ya tsaya a iya baki na saboda idanuna da suka sauka akan wanda na gani a bakin k’ofa yana kallo na.


A hankali ya tako ya k’araso inda nake ya tsaya yana ci gaba da kallo na, a yanayin shi bazan iya gane halin da yake ciki ba.


Wata irin kunyar yaya Faruk ne ya kama ni da tsoron shi a lokaci guda, daskarewa nayi a zaune ba tare da na iya motsa ko da d’an yatsa na ba.


Wani irin murmushi ya min wanda na kasa fasalta mai murmushin yake nufi a gurin shi.


"Fatima kenan, ashe nan ki ka tawo a na ta neman ki a gida" ya k’arasa maganar yana min wani irin kallo.


A halin da nake ciki na firgici ba zai bani damar in iya bud’e baki na in amsa wa yaya Faruk tambayar shi ba.


A yadda na lura ma bai da buk’atar amsawa ta a yanzu.


Ci gaba yayi da cewa "Fatima kamar yadda kike buk’atar in barki da masoyin ki wanda ku ke son junan ku ina ganin lokacin yayi, na yarda ke jaruma ce a soyayya da zaki iya fad’i tashi a kanta, in da kika ban kunya a soyayyar taki shine tsoron da kika sa a ranki har yakai ki ga barin iyayen ki wanda ki ka sa su a cikin halin damuwa, a matsayi kin a ‘ya mace ina ganin ba mutunci ki ba ne barin gari dan ba kowa yasan nan za ki zo ba, hakan da kika yi zai sa mutuncin ki ya zube a idanun mutane, anyway ba dogon zance zanyi dake ba illa in sanar dake *FATIMA NI UMAR FARUK NA HAK’URA DA AURAN KI, FATIMA NA HAK’URA DA SOYAYYAR KI  DUK KUWA DA SON DA NA KE MIKI*.


Sauri nayi na d’ago kaina na kalle shi, banyi zaton jin wannan kalamen daga bakin yaya Faruk ba sanin son da yaya Faruk yake min ban yi zaton zai yi saurin yanke hukunci irin wannan ba na hak’ura dani amma sanin halin yaya Faruk in ranshi ya ‘baci zai iya yanke kowane hukunci dan samar ma kanshi mafita yasa ya zartar da hukunci, bai duba halin da zai shiga ba, Kalamen da ya yi amfani dasu wajen yi min magana shi ya bi duk sassan jiki na ya katse min kuzari na da nake tare dashi a wannan lokacin.


A lokacin wani irin tausayin yaya Faruk ne ya kama ni wanda ban san lokacin da hawaye ya fara sintiri a idanu na ba.


Ci gaba yayi da cewa "Fatima ina da power da zan iya auran ki in kuma koya miki so na ko da ba kya so, ba wai wannan abin da kika aikata ne yasa naji tsoro na hak’ura da auran ki, sai dan ni ba mai son shiga rayuwar wani ba ne, ina son ba wa mutum right d’in shi ne a matsayin shi na d’an adam, kin fad’a min wannan Dr ki ke so ban d’au hakan a komai ba, sai yanzu da kika d’auki matakin fara guduwa daga gaban iyayen ki, na ji tsoron a matsayin ki na ‘ya mace kar ki je ki aikata wani abin da bai dace ba duk a dalilin aure na da zaki ko bayan anyi aure na da ke ki je ku ci gaba da soyayyar ku kuna cin amana ta, kin ga kenan zan iya d’aukan ko wai mataki da ya zo min idan hakan ta kasance, hakan yasa na fasa auren ki, Fatima nayi niyar nuna miki kuskuren ki na yaudara ta da kika min, da tozarta ni da kika yi niyar yi a lokacin da bikin mu bai kai sati biyu ba kika tawo nan da niyar guje ma aure na, na so in nuna miki ba kowane namiji ne ake yaudarar shi a zauna lafiya ba, sai dai k’udurin da nake dashi na miki hukuncin na fasa dan ke ‘yar uwa tace, hannun ka ba zai ru’be ba ka yanke ka yar, shi yasa zan barki da halin ki".


Maganganun da yaya Faruk yayi amfani dasu wajen yi min magana sun min tsaurin da zuciya ta ba za ta iya amsar su ba, nasan maganganu ne yake fad’a min a k’aik’aice masu isar da sak’onnin da yake son isar wa wanda Hausawa ke cewa "kukan kurciya jawabi ne".


Wani irin kuka na saka a lokacin, in ban da shasshek’ar kuka na da ya cika d’akin ba abin da ke tashi.


Murmushin takaici yayi ya kalle ni ya ce "Fatima ba ki yi wa kan ki adalci ba da kike yin kuka alhalin ni ban miki wani abu ba, ina ganin in akwai wanda ya dace yayi kuka bai wuce ni ba saboda halin da kika sa ni a ciki, Fatima ni kukan zuciya nake yi wanda yafi na fili ciwo, ni a gani na murna ya kamata ki yi yau na cika miki burin kin a barin ki da wanda kike muradi".


Ni dai ba abin da nake yi sai ci gaba da kuka na da nake yi, wannan maganganun da yaya Faruk yake fad’a min zai fi min sauk’i akan yasa bulala ya zane da wannan maganganun da yake fad’a min.


Ganin Hajiyan Wagini kawai muka yi ta shigo cikin d’akin tana cewa "Haba Soja me kuma kayi ma amaryar taka, ko me ta maka ai kamata yayi kayi hak’uri da ita dan nasan dama ita ce da laifi, ni kaina tun da tazo take sa ni magana, dama ina jin haushin ta’ba min waya da tayi".


Ci gaba nayi da kuka na ba tare da na tsagaita ba, hakan yasa Hajiyan Wagini ce ma yaya Faruk "Mai gida na wai me ka mata ne ta cika mana kunne da kuka".


Wani irin banzan kallo ya watsa min kana ya kalli Hajiya ya ce "Hajiya kukan jin dad’i take yi dan ni ba abin da nayi mata".


Hajiya cikin lallashi ta ce "Wai me aka miki ne ki ke kukan nan".


Cikin kuka na ce "Hajiya dan girman Allah ki ba ma yaya Faruk hak’uri, na mishi laifi ne".


"Me kika mishi?".


 Hajiya ta tambaye ni tana kallo na.


Shiru nayi wannan karan ban bata amsa ba, hakan yasa Hajiya fusata ta fara fad’a tana cewa "Ka ga ja’iran yara, kowa sai tambayar shi nake yi me yake faruwa kun k’i fad’a min sai tamaula ku ke yi dani".


Yaya Faruk ne ya rik’o hannun Hajiya ya ce "Hajiya mu je falo zan fad’a miki abin da yake faruwa" yana gama fad’ar haka suka bar d’akin.


Samun guri yayi ya zauna ya zayyane ma Hajiyan Wagini abun da yake faruwa da hukuncin da ya yanke yanzu.


Hajiyan Wagini na gama jin labarin ta sa kuka tana cewa "Yanzu dama abin da Fatima tayi kenan, shi yasa ta tawo nan, ba yadda ban yi ba akan ta fa’da min dalilin zuwan ta tak’i ta kuma d’au waya ta tayi min wani surkullen da ban da damar in kira mutane ko a kira ni, wannan wace irin hatsabibiyar yarinya ce, yaushe soyayyar zamani ta canza Fatima ta koma haka, to wallahi ba ta isa ba sai ta aure ka ko tana so ko ba ta so, anya Fatima tana da rabo kuwa a duiya tun da ta k’i ka, shi yasa ta ke kunna min wak’ar soyayya ni ina sha duk cikin son ka ne ashe wani barbad’ad’d’en take so ba kai ba".


Duk da ranshi ba ya mishi dad’i amma hakan bai hana shi murmusa wa ba jin Hajiya na cewa wai anya Fatima na da rabo a duniya kuwa?


Jin fad’an Hajiya yayi yawa yasa ya ce "Hajiya kar ranki ya ‘baci akan wannan maganar, ni na riga da na hak’ura da Fatima, kin ga kar a zo ayi abin da zumunci zai ‘baci".


Wani kallo ta mai na anya kasan abin da ka ke fad’a kafin taci gaba da cewa "Anya Soja kana cikin hankalin ka kuwa, ko dai shi wannan Dr d’in da ka ce yana son ta ya maka wani surkulen da zaka hak’ura da Fatiman, in ba haka ba ya za ayi bikin ku bai wuce sati biyu ba kace ka hak’ura da ita, ina ganin ka gwarzon namiji ashe ba haka ba ne, ko da yake bazan yi mamaki ba tun da son da kake ma Fatiman ba zai barka ka d’au hukunci akan ta ba, abin kunya yarinyar da ka ga k’uruciyar ta amma wai shakkar ta ka ke yi, to in  kai ka hak’ura ni ban hak’ura ba, ba wanda ya isa ya kawo min matsala a cikin iyali na in dai ina raye".


Lallashin ta yaya Faruk ya fara yi amma kamar k’ara zuga ta ake yi, maimakon tayi shiru sai ma mik’e wa da tayi ta nufi d’akin da nake ciki.


Tun san da suka fita suka bar ni na ci gaba da kuka na har na gaji, sai faman ajiyar zuciya na ke yi, ba kalar tunanin da bai zo min a raina ba a wannan lokacin.


Fad’an Hajiya ne ya katse min tunanin da nake yi.


"Sannu Fatima, na ji abin da kika aikata, bari in fad’a miki babu wanda ya isa ya lalata min zumuncin da yara na suka dad’e suna yi, a yadda soja yake fad’a min nima za ki iya fad’a min magana in dai akan wannan Dr ne, to ko ke Laila-Majnun ce k’arewar soyayya sai kin hak’ura da shi wannan shed’anin yaron da yake zuga ki, ke ba ki isa ki kunya ta ‘ya’ya na ba, ke in banda sharrin so ai kin san Soja yafi k’arfin ki a komai ma".


Duk fad’an da Hajiyan Wagini take min kaina a sunkuye yake, nasan Hajiya za ta iya min abin da ya fi haka kasancewar duk cikin familin mu tafi son shi da shak’uwa dashi sannan sunan kakan mu ne wanda ya rasu, shi yasa duk wanda ya ta’ba yaya Faruk sai inda k’arfin ta sai ya k’are.


Yaya Faruk ne ya shigo ya ga fad’an da Hajiyan Wagini ta ke min, magana ya mata a kan ta k’yale ni tun da ya hak’ura, jin hakan ya k’ara tunzura HajiyanWagini ta dawo da fad’an kanshi "Rufe min baki, na ga akan Fatima za ka iya dawowa Sallamame sai yadda tayi dakai, kai in ban da ba ka da zuciya har za ka iya sa bakin ka har ka bani hak’uri duk da abin da ta maka, to in kai kana tsoron ta ni ba tsoron ta nake ji ba".


Duk wannan fad’an da Hajiya ke mai bai ce mata komai ba sai ma wayar shi da ya ciro yana daddanawa.


Ganin wayar da yake dannawa yasa Hajiya ta ce "Yanzu Soja duk wannan fad’an da nake yi akan ka shine za ka bad’a min k’asa a ido, maimakon kaima ka nuna ‘bacin ranka ka taya ni yi mata fad’a sai ma wayar ka da ka d’akko kana dannawa, ai shi kenan" nan Hajiya ta k’ara sa wani kukan.


Sanin rikicin Hajiyan Wagini yasa ya maida wayar shi gaban aljihun shi ya ce "Hajiya ki yi hak’uri, ban cika son d’aura ma kaina damuwa ba, likita ya min gargad’i akan haka saboda kiyaye lafiya ta kuma kin san ni ban cika son hayani ba".


Wannan maganar da yaya Faruk ya fad’a ne yasa Hajiya yin shiru daga fad’an da yake min.


Hajiya ce ta fara fita a falon, har ya fara tafiya kana ya juyo cikin d’aurewar fuska ya ce min "Ki shirya yau za mu koma Kaduna in kin gadama, in kuma za ki kira wannan Dr d’in ne ya zo ya d’auke ki ku tafi wani gurin, kina da damar yin haka, za’bin ya rage naki" yana gama fad’ar hakan ya bar d’akin.


Samun Hajiya yayi akan zai koma Kaduna dani, Hajiya na jin haka ta ce itama da ita za a tafi a yi komai a gaban ta.


Yaya Faruk bai mata musu ba ya ce ta shirya zuwa anjima za su tafi.


Abinci Hajiya ta shirya ma yaya Faruk wanda na dafa.


Tun da Hajiya ta zubo mishi abincin yaji bai marmarin shi dan yasan ni na dafa, ba yadda Hajiya ba tayi dashi ba akan yaci amma yak’i, sai ma ce mata da yayi bai jin dad’in bakin shi ne, ruwa kawai yasha da dambun naman da Hajiya ta kawo mai wanda ba ta rabo dashi yaci kad’an.


Haka na zauna a d’aki ba tare da na fito ko falo ba, abincin da na dafa ma kasa fitowa nayi na ci, ko sallah a band’akin ciki nayi alwalata, na san in dai na kuskura na fito falo ba abin da zan fuskanta sai ‘bacin rai, fad’an Hajiya kawai ya ishe ni bare a je ga kallon da yaya Faruk yake min a yanzu, A yanzu ina ganin yaya Faruk ya dawo kamar yaya Faruk d’in da na sani a da, yanzu ga wani tsoron shi da ya sake shiga na a karo na biyu.


San da za mu tafi yaya Faruk ne ya shigo d’akin ya ce in fito mu tafi.


Ko da zan shiga motar tunani na fara yi akan gaba zan zauna ko a baya, had’a idon da muka yi da yaya Faruk ne ya watsa min wani banzan kallo yasa ba shiri na bud’e baya na shiga, Hajiya ma baya ta shiga yaya Faruk ya ja mu muka tafi.




Post a Comment

0 Comments