TOP HAUSA NOVELS atOptions = { 'key' : '20e08520dad54dbf6d9e963271

Babu so page 77

 BABU SO

Chapter 77

77


........Kaɗan ya rage zuciyar Fadwa yin tsale ta fito, jikinta na rawa tace, “Wlhy ƙaryane, munafukar tsohuwa da bazataga MANZON ALLAH ba”.


  Saukar mari taji lafiyayye daga Mahaifinta. Gwaggo ta jinjina kanta cike da jin daɗi, “Nagode Sadiqu. Ba laifinta bane uwace bata moraba. Yo dama yaushe Halima taga wata tarbiyya balle ta bata. Ai bakai dace da mata ba wlhy”.


  Cikin matuƙar mamaki su Daddy suke kallo da sauraran Gwaggo da alamu suka nuna akwai suɓutar baki a kalamanta. Gwaggo Halima zatai magana Alhaji Sadiq ya dakatar da ita. “Wlhy kikace tak sai kinyi nadama Halima...”


   “Barta tace in ma tanada abin cewar mana. Dan kuwa inada ƙwaƙwaran hujjar ita ta zubar da cikinta da kanta, saboda karya hanata waɗan nan raye-rayeda sukeyi na zamani a wannan abubuwan da kuke kira yanar gizo-gizo ko uwar mima. K Luba kiramin Bibah ta shigo da likitan da ta saka yaymata aikin. Amma kafin sannan fara latso min ita a wayarki su gani”.


   Cikin rawar ɓutiya Hajiya Luba ta latso Fadwa a tiktok ta miƙama Baba Ibrahim dake a tsakkiyar Daddy da Abie, sai Baban Fadwa a gefen Daddy, Abba kuma na gefen Abie. Wani video ne na rashin mutunci da aka ɗauka a ranar kamun Fadwa. Ana gobe ɗaurin aurenta da Shareff kenan. Kayan barcine jikinta riga fingila iyakarta cinyarta amma ta kusa gwiwa, sai gashinta dake a buɗe tama warwaresa akan kafada. A yanda taketa komanta kai tsaye da farko na rawar wata wakar turanci zaka san bata san ana dauka ba. Sai a kusan ƙarshe-karshe take kare jikinta da filo data ɗauka tana masifar miyasa zatai mata video, sai dai anyi cutting sunan wadda ta ambata na mata video ɗin. Bayan shi akwai wasu daban-daban na rashin mutunci, abindama zai baka mamaki kamar an tsinto iya wanda tayi abin ALLAH wadai ɗinne kawai an ɗora a shafin. Hatta wayarsu ta ranar daurin aure da Shareff duk akwai a wajen, duk wani faɗa datai da wani a tiktok ko rawar banza cikin shigar wofi duk sune aka tato aka ɗaura. Harda ma wanda bata kai tiktok ɗin ba


    Komai ya ƙara tsayama Shareff cak, bama shi kaɗaiba hatta sauran jama'ar falon gaba ɗaya. Kafin wani ya samu damar tofa tasa sai ga Bibah da likitan daya zubdama Fadwa ciki. Harga ALLAH tayi matuƙar firgita. Zuciyarta ta dinga tsitstsinkewa lokacin da Gwaggo ke faɗa masa ya faɗi miye alaƙarsa da Fadwa. Kansa tsaye babu fargabar komai saboda an toshe bakinsa da kuɗi ya fara bayani tiryan-tiryan tun zuwan su Fadwa da ƙawayenta Sima da Amal. Baice akwai Bibah da Siyyah ba. Sai yanzu ne Fadwa ta samu damar fashewa da kuka.


   “Wlhy wlhy ba haka akaiba. Bibah kiji tsoron ALLAH, dan kina son auren mijina basai kin ƙullamin sharri ba.....”


   “Sharri kuma. Idan sharri nake miki aiga wayarki a hanunki a amsa a duba agani”.


  Duk da Fadwa tasan duk waɗancan videos ɗin tayisu amma ta goge mafi yawa a ciki saita bada wayar tata, saboda sanin masu dama-damar ne kawai a shafin nata na yanzun. Baba Ibrahim ne ya amshi wayar, sai dai koda aka duba babu wani accaunt akai sai irin wanda Bibah ta nuna.


     “To'ai babu banbanci tsakanin wannan da wanda ke anan ciki”.


  Ba karamin ruɗewa Fadwa tai ba. Harta fisgi wayar a hanun Baba Ibrahim batare da tasan tayi ba. Koda ta duba itama sai taci karo da abinda suke maganarne kawai babuma accaunt ɗinta data sani akan wayarta kwata-kwata. Mamaki da tsoro suka risketa. Takai dubanta ga Bibah sai ta samu tana murmushi, hakan ya bata tabbacin itace tai komai. Wata irin wawuyar mikewa tai ta shaƙi Bibah, nan take kokawa ta kacame Bibah ta fara kakarin mutuwa. Da ƙyar Maheer ya rabasu shi da su Aunty Bintu.


    “Shareff idan baka saki Fadwa ba wlhy wlhy wlhy har abada babu ni babu kai. Yanzu nan ka saketa, dan baka taɓa rayuwa da wadda ta zubar maka ciki ba dan son zuciyarta, sannan ballagaza.”


   Shareff da gaba ɗaya brain da Heartbeat ɗinsa sun tsaya cak daga aiki, ya dago yana kallon Mommy.” “Ba kallona nace kayiba saketa nace, idan kuma bazaka saketaba to wlhy zan......”


   “Haba Nafisa kinada hankali kuwa, ki tsaya abi komai a sannu mana”.


  “Yaya daina wani maganar a sannu, ai tunda Ubansa ya sakeni wlhy shima sai ya saki Fadwa. Dan na tabbatar abinda na aikata bai kama kafar abinda taiba. Itafa ciki ta zubar masa”. Kafin ma Baba Ibrahim yace wani Shareff da dake cikin matsanancin fushi ya furta “Na saketa saki biyu”.


   Tamkar saukar aradu Fadwa taji saukar wannan kalma. Tai baya ta zube ƙasa, ihu take son yi amma ta kasa yi tsabar yanda falon ke juya mata tana ganib bibbiyu, da sauri ta rarrafa gaban Shareff.


   “Soulmate dan girman ALLAH ka saurareni, wlhy ba.....”


  Wani irin hankaɗata yay tai baya ta zube har kanta na buguwa da kujera sai da Abba ya tareta. “Wlhy idan kika sake koda matsoni zan iya shaƙeki ki mutu, ballagaza. ALLAH ya isa ban yafe miki zubarmin da ciki ba, na tsaneki, na tsaneki, bana buƙatar sake ganin mummunar fuskarki a rayuwata har abada. Idan har zaki iya salwantar da ƙyautar da ALLAH ya bamu, abinda ke amsa suna gudan jininki to zaki iya halakani nima, na tabbata zaki iya kasheni saboda cikar burinki. Kin wulaƙanta aure na, kin nunama duniya ke ɗin baki da tarbiya, har wasu banzaye najin wani abu akanki saboda kin nuna musu ke ballagaza ce. Anya Fadwa kinada ilimin addini kuwa? Anya kin san darajar kanki kuwa? Anya kina tuna zaki mutu kuwa?, na godema ALLAH ma da ban haihu da ke ba, dan bana fatan ƴaƴana su taso su kalleki matsayin mahaifiya balle har halayenki su zama naso ga tasu rayuwar. ALLAH ya wadaran mace irinki mai tara ƙawaye da bata da ra'ayin kanta sai nasu, kije ƙawayen naki su cigaba da baki rayuwar da kike buƙata, kije, kije bana son ganinki wlhy”. Idanunsa har tara ƙwalla suke na tsananin ɓacin rai, Shareff nada kishi matuƙa akan duk abinda yakeji ya killace matsayin nashi. Yanzu haka yanajin kamar zuciyarsa zata tsage, babu abinda ke masa amsa kuwwa sai zantukan samarin ɗazun a kanta. Wata muguwar shaƙa ya kai mata jijiyoyin kansa na matuƙar tashi. “Fadwa na tsaneki, bazan yafe miki ba.....” da ƙyar su Abie suka ƙwace Fadwa a hanunsa, sai numfashi take fiddawa da ƙyar na wahala ga Gwaggo Halima na ihu da kururuwar kuka zai kashe mata yarinya. Kansa ya kife a jikin Abie dake kusa da shi, yana mai ƙoƙarin danne hawayensa. Abie ya shiga shafa kan nasa cikin lallashi tausayinsa na ratsashi. Ba Abie kaɗai ba kowama yaji tausayin Shareff ɗin dan abune mai matuƙar ciwo ga duk namijin daya san ciwon kasa. Su kansu sunajin raɗaɗi a zukatansu matsayin iyaye, mahaifinta kam ma ai ya kasa ko motsi dan gaba ɗaya ya tattara laifin a kansa shima, zuciyarsa suka take matuƙa a ƙirjinsa...........”


   *_“Tabbs da ace kayi haƙuri saki bashi bane mafita Yaya MM”._*


  Kusan gaba ɗaya suka waiwaya a inda sautin maganar ta fito. Anaam ce sanye da hijjab har ƙasa. a kallo ɗaya zaka fahimci a barci ta tashi ma. Kuma yanayinta yana nuni da batajin daɗi....


   “Ke kuma a wa, kajimin ƴar iskar yarinya. To ko ubanki Usman da uwarku basu isaba balle ke haihuwar yau”.


   “Badan na isa bane na faɗa Mommy, ba kuma dan iyayena nada wani kusanci da zama masu isa a wannan Family ɗin ba. Sai dan kusan gaskiya ku daina dukan jaki kuna barin taiki (ALLAH yasa na faɗi hausar tawa dai-dai). Tabbas Fadwa bata taɓa ƙaunataba. Kamar yanda Gwaggo Halima bata taɓa ƙaunar iyayena guda uku ba. Haka kema baki taɓa ƙaunarsu ba. Kafin wata rana ina ganin laifinku matuƙa ina kuma jin zafinku mai tsanani, sai dai lokaci ya saukaƙamun hakan sakamakon fahimtar kuma a haka aka raini zukatanku. Zan faɗi gaskiyane a yanzu ma badan ku soni ni da iyayena ba, sai dan ku sani wadda ta raineku ku kanku ba ƙaunarku take ba bawai iyayena ne kawai take ƙi ɗinba. Lallai da sanin Fadwa aka zubar da cikin jikinta, sai dai kuma Gwaggo itace ta tsara komai da taimakon momyn Bibah, su Bibah ƙawayenta su huɗu suka ɗarata a hanya har komai ya faru.....”


   Wani irin harziƙowa Hajiya Luba tayi, amma sai Baba Ibrahim ya dakata mata wata irin razananniyar tsawa. Komawa tai ta zauna daɓar. Anaam tai murmushi mai ciwo da dafe karfen benen takai zaune saboda jiri da take gani. Sai da ta ɗan dafe kanta na wasu sakkani sannan ta ɗago tana ɗan murmushi. “Kuyi haƙuri.” Batare data jira cewar wani ba ta cigaba da faɗin, “Ban faɗa muku wannan maganarba sai dana riƙe hujja, kuma dama irin wannan ranar nake jira dan nasa duk yanda Maman Bibah da Bibah zasuyi da Gwaggo sai sunyi domin Yaya MM ya auri Bibah, kuma Fadwa itace kawai makaminsu da Mommy”. Ta ƙara maganar da miƙa wayarta dan bazata iya tasowa ba saboda jiri. “Gashi komai na'a cikin nan. Ku kira Amrah ma kuji dan tasan abubuwa da yawa itama”.


   Aunty Bintu ce ta amso wayar, ta kaima Baba Ibrahim. Gwaggo ta miƙe a fusace sai dai jikinta rawa yake. Amma sai Gwaggo Halima tasa ƙafa ta taɗota ta koma zaune daɓar har tana sakin ƙarar azaba data ratsa ɗuwawunta. Sosai da mamaki mai cike da ɗunbin razani suka bayyana a fuskokinsu Baba Ibrahim. Dan kuwa dai ga muryar Gwaggo gata Hajiya Luba da Bibah. Su Mommy zasu fara hayaniya Baba Ibrahim ya hanasu, cikin matuƙar razanarwa Baba Ibrahim yace Hajiya Luba ta faɗa kokuma ya ɗauka mataki a kanta. Jikinta tsuma yakeyi, musamman da taga irin mugun kallon da Shareff ke jifanta da dashi, wanda ba ita kaɗai ba, hatta Gwaggo haɗiyar yawu take da ƙyar...


    “Wlhy Yaya mu ba laifinmu bane, kawai dai Bibah ce ke tsananin son Shareff, nayi-nayi Nafi ta fahimci abinda nake buƙata na mu haɗa aurensu taƙi, sai nunawa takeyi da Fadwa za'a haɗa. Har nayi zuciya da hakan sai dai Bibah ta shiga damuwa, shine nazoma Gwaggo da batun ko akwai yanda za'ayi, amma saita nunamin itama bata san zancenba. Ban gajiba muka cigaba da binta har akai auren Fadwa da Shareff, sai lokacinne ta fara saurarena, ta kuma tabbatar min idan har muka taimaka mata cikin Fadwa ya zube zatai duk yanda zatai dan auren Shareff da Bibah ya yuwu”.


   Salati falon ya ɗauka baki ɗaya, yayinda a lokaci guda Gwaggo Halima da Mommy suka kaima Gwaggo shaƙa, da ƙyar aka ɓanɓareta a hanunsu idanunta har sun firfito waje kamar na tsohon kwarto. Nan fa sabuwar hayaniya ta kaure har wani baijin zancen wani, dan Fadwa kam tuni ta turmushe Bibah tana jibga, itama uwarta Hajiya Luba ta turmushe Fadwan. Ƙurace sosai ta tashi a falon, wadda ta saka Anaam ji kamar duniyar na juya mata. Cikin sa'a Shareff ya hangota tana jujjuya kanta. Da sauri ya miƙe yay inda take, cak ya dauketa ya koma saman da ita tana faman jujjuya masa kanta, Mamie da itama ta hangosu tai saurin bin bayansa dan ita kam ma ba komai take fahimtaba a abinda ke faruwa a falon.


   Faɗa sosai ya kaure, duk yanda su Abba sukaso kwantar da abun ya gagara, dan tun anayi a falo har aka koma tsakar gida, kafin kice mi ƴan biki sun fara tururuwar shigowa bama idonsu abinci tunda dama akwai ƙofar dake a tsakanin gidajen wadda basai kaje gate ba. Cirko-cirko mutane sukai sunajin fallasa da tonon asirin da su Mommy sukema juna, yayinda Gwaggo ke neman naɗe tabarmar kunya da hauka. Sai dai fa ganin lamarin yafi ƙarfinta dan hatta Mommy yau la'antarta take ga ƴan biki sai ta nema fita a gidan tana kuka wai su Daddy sun shirya wulaƙantata. Nanfa wasu a munafukai masu son jin ba'asi suka take mata baya, sai dai taƙi sauraren kowa, tana gab da barin layin nasu wani mai mota ya shawo kwana, duk da horn da yakeyi sam Gwaggo daketa faman sambatu da surutai batajisa ba, shi kuma ALLAH ya hanashi damar taka birki, ya kwasheta sama ya direma kasa, yana son riƙe kan motar ina saida taya ɗaya ta dirza ƙafar Gwaggo har ana iya jin karar farfashewar ƙashi. Tun ƙarar azaba ta farko data saki bata sake fahimtar ina take ba ta suma. Dan danan aka rufu kanta, har su Daddy labari yazo musu sun fito, nan fa layin ya cika dankam. Matasa zasu rufu kan mai mota da ƴan biki yazo dauka baba Ibrahim ya dakatar da su. Kamalarsa da dattakon kasancewarsa tsohon arziƙi ya sakasu bin umarni, sai dai an kama Gwaggo da babu alamar numfashi a jikinta an saka a motar mutumin aka nufi asibiti.


    Babu ko tausayi a fuskar Gwaggo Halima, sai ma faffaɗar magana take wai ai ƙarshen Gwaggo kenan. ALLAH ma ya kara sakata a masifa fiye da hakan. Mafi yawan mutane maganganun Gwaggo haliman basu ɓata ransu ba, sai dai duk da mugun halinta baban Fadwa ya kasa haƙuri shima a wajen ya yanke igiyar auren Gwaggo halima biyu. Ai sai lokacin Fadwa da Mommy suka sake tunawa da mutuwar nasu auren fa suma. Nan guri ya kara daukar zafi faɗa ya dawo sabo

 fil da ƴar koke-koke abin zakkunya da takaici...........✍




Post a Comment

0 Comments