TOP HAUSA NOVELS atOptions = { 'key' : '20e08520dad54dbf6d9e963271

Babu so page 65

       *_❤‍🔥BABU SO....!!❤‍🔥_*

                 _(Miya kawo kishi?)_




              *_Bilyn Abdull ce🤙🏻_*


*_BABU SO👉🏻AREWABOOKS_*


*_65_*




........ *_Cikar burina shine ganin irin wannan ranar tare da ke gimbiyar mata, kece sirrin ruhuna, nima inajin raɗaɗi fiye da wanda na gani a cikin ƙwayar idanunki. I'm sorry! ranarki tana zuwa_*. 

      Ta haɗiye yawu da ƙyar, da sake maimata karatun kamar mai bita, dan yayisa ne da yaren maley ta tabbatar batayi kuskuren karantawa ba. Zaune takai dan ƙafarta ta kasa ɗaukarta. Ta cigaba da zaro sauran abinda ke cikin akwatin. Akwai kashi-kashi na ribbons ɗinta, ta gane hakanne saboda matuƙar son da takema wasu, wasu kuwa ta gansu a hotunanta dake cikin albom ɗin can tun tana yarinya. Sai wani ɗan abunta mai kamar kwalba cikinsa da taurari da wata suna yawo, a tsakiyarsu da alkur'ani a buɗe, idan bata manta ba Mamie ce ta bata shi as gift ɗin kammala haddar alkur'anin ta, amma saita nemesa ta rasa a daga baya duk da kuwa a side drawer na gadonta yake. Har kuka tayi na rashinsa, kai tsaye kuma ta zargi mai aikinsu ce ta fasa amma ta ɓoye. Mamie ce ta kashe wutar a lokacin ta sake saya mata wani sai dai yasha banban da wannan ɗin dan haka taita mitar batason sa har sai da Abie ya shiga zancen ya lallasheta. Ashe Yaya MM ne ya sacesa. Ta cigaba da kallon abubuwa da dama nata, kuma masu muhimmanci a gareta data nemesu ta rasa a lokuta mabanbanta, wanda a iya tunaninta ta rasa mai ɗaukar mata su, duk da har su Amrah yaran aunty mimi tasha zarga. Book ɗin ta ɗauka saboda ji a ranta shima ya shafeta. A shafin farko sunanta ne da rubutu kamar haka.

        *_Juwairiyya Anaam! kece matar aurena kuma uwar ƴaƴana da izinin UBANGIJINA. Ni kaɗai aka haifawa ke, zan kuma rayune domin ke insha ALLAHU._*

      Ta buɗe shafi na biyu zuciyarta na tsitstsinkewa. _Da ace wani bawa nada damar tsara labarin rayuwarsa da wanzuwarsa, zan tsara nawane kawai domin ke kaɗai a wannan duniyar. Ina roƙon UBANGIJI ke ɗin karki zama a cikin ƙaddarar abinda ALLAH bazai mallakamin ba, zuciyata bazata iya ɗauka ba, ya rabbi ka zama gatana akowane hali_.

    Haka ta cigaba da karanta abubuwa daban-daban akan rayuwarta da tasa daya dinga rubutawa tamkar labarin littafi. Mafi ƙololuwar ruɗa tunaninta da saukar da hawayenta shine a gaɓar da Mommy ta takura masa auren watanta. Duk wani tashin hankalinsa ya zanashi da fargabar karta suɓuce masa. Zuwanta Nigeria da sunan hidimar ƙasa mafi girman sassauci dajin ƙwarin gwiwar yin biyayya da cusa son Fadwa a ransa matsayin sadaukarwa ko UBANGIJI zai masa tukuyci da samun Anaam. Kukanta ya ƙara ƙarfi jin cewar ya kwanta jiyyane akan jin za'a aurama waninsa ita ba shi ba, harda barazanar kamuwa da ciwon hawan jini daya nema shafar lafiyarsa. “Innalillahi...” ta shiga ambata da kifewa jikin desk ɗin nasa ta shiga raira kuka, wani al'amari mai girma na ratsa dukkan magudana da jijiya ta jikinta. Sai da tai kuka sosai harta gode ALLAH kafin ta ƙarasa ganin wasu zane-zane da yayi wanda duk fuskartace ya zana, kai kace tana tsayene a gabansa yay zanen. Da kyar ta miƙe ta tattare komai ta maida masa yanda yake ta maida a drawer ɗin sannan ta fice jikinta a saɓule.


         Aysha dake zaune a falo tana aikin nata na tiktok data koya gun Fadwa ta bita da kallo. Ganin zata wuce bedroom batare data tanka mata ba ta riƙo hanunta da sauri. Juyowa tai tana kallonta, hawaye masu ɗumi na sauka mata a kumatu, sai kuma ta rungume Ayshan tana saki wani marayan kuka da ita kanta bata gama tantance na minene ba. 

     Hankalin Aysha ya ƙara tashi, ta ɗagota da sauri. “Ya ALLAH blood wai miya farune? Yaya ne ya miki wani abu?”.

    Kanta ta girgiza mata. 

“To minene? Ko dai maganar aurence dai har yanzu? Da zaman wannan gidan?. Dan ALLAH ki kwantar da hankalinki Anaam. Ki saurareni a wannan gaɓar na buɗe miki kanki ta yanda wlhy sai Yaya Shareff ya dawo tafin hanunki ta hanyar soyayya da bin dokokin ALLAH. Na fahimci rashin sanin minene kishi da rayuwar gidan malam bahaushe ke sakaki tafiya a haguggunce a wannan gidan har Fadwa ke jan akalarki da makirci. Ki nutsu ki saurareni Please”.

     Bataƙi ta Ayshan ba, suka koma suka zauna cikin hikima da basirar da ALLAH ya bama Aysha. Da kasancewar ta tashi a rayuwane ta cikin gidan yawa dama salon kishin Mommy da Aunty Amarya. Ga karance-karancen littatafan nan na hausa duk tana taɓawa ta shiga warware mata abubuwa masu yawan gaske. Anaam irin mutanen nanne masu saurin haddace abu idan an faɗa musu, musamman akan abinda ke wahalar da su, ko wani abu da basa ƙaunar a kaisu ƙasa. Hakan ya bata matuƙar gudunmawa wajen fahimtar Aysha daki-daki babu kuskure. Sosai taji daɗin bayanin dan haka ta rungume Ayshan. 

     “Na gode blood, nagode, irin godiyar da babu alƙalamin dazai iya rubutawa. Sai dai ki sani duk abinda kikaga inayi a gidan nan kamar mara wayo ba rashin wayo bane sarai ina lure da komai da binsa daki-daki, sannan akan sani nake aikatawa saboda wasu dalilai nawa. Idan banyi hakaba shi kansa bazan gama fahimtar halayyarsaba balle ita. Tabbas nasan bazan taɓa iya kaiku wayon zama a irin rayuwar da kuka tashi ba, sai dai koba komai ina shigowa cikinku nima ina ganin wasu abubuwan. Daliline ya sakani zaɓar yin duk abinda nakeyi. Sai dai a yanzu kalar rubutun zai sha banban da kalar takardar. A yanzu lokacina ne, kisa a ranki lokacin Juwairiyya Usman MD Shareff zai fara a gidan Al-Mustapha Muhammad MD Shareff. Nayi alƙawarin bazanyi abinda zai cutar da kowa ba, sai dai zan nunama kowa kowacce mace da ilimin zaman gidan aure UBANGIJI ya halicceta, kuma ko wacece ita ko'a ina ta tashi zata rayuwu, ta kuma riƙe kambunta na ɗiya mace. A kwanakin da nayi biyar a gidan nan, na karanci abubuwa masu dama a cikinsu, zan kuma fara sharar fadata da su domin samun damar shimfiɗa mulkina batare da wani datti ya sha gaban cikar burina ba”.

      “Woow vary interesting my blood. Haka nake sonki dan ALLAH. Ki haukata mana Yaya Shareff, ki kuma dawo mana da Fadwa hanya tabar bin karatun su Mommy, ta zama mai ra'ayin kanta”.

   Anaam ta ƙyalƙyale da dariya, zuciyarta fes tamkar an sauke mata dukkan wani nauyi da ƙuncin da takeji a yau a yanzu yanzu. Basai amfaɗa ba, da ni da mai karatu duk zamu fahimci hakan nada nasaba da abinda taci karo da shi wannda a baya bashi take kallo a fuskar Shareff ba. Sun ƙara tattaunawa sosai akan wasu abubuwan da dama da Aysha kafin ta miƙe ta koma sashen Shareff domin gyarawa bisa shawarar Aysha. 

     Bata jin daɗin jikinta saboda ɗinkin da akai mata na sakata jinta tamkar a takure, ga tafiyarta har yanzu bai zama normal ba kamar da. Amma haka ta jure a daddafe na rashin sabon da wahala ta gyara ko'ina na sashen nasa, sauƙin ma babu datti mai yawa. Sai da ta tabbatar ko'ina ya mata da kamshi sannan ta rufe ta fito. Baki ta saki tana kallon yanda Aysha ta ƙara gyara sashenta itama. Ta saki murmushi da harar Ayshan dake tsaye tana karanta mata taje tayi wanka ta ɗauki ado dan Yaya Shareff na gab da dawowa. Akwai tsoro tattare da ita na abunda ya faru, amma gargaɗin likita akan Shareff ya bata ƙwarin gwiwar tabbatarma kanta babu wani abu tunda ko dai baya cikin hayyacinsa ai baya nema wani abu daga garetaba zaren ɗinki na a jikinta. Da wannan tunanin ta faɗa wanka. Koda ta fito tsareta Aysha tai wai sai ta mata kwalliya. Badan taso ba dole ta tsaya kuwa Aysha ta zaneta tsaf dasu jaja leɓe da barbaɗa kumatu na zamani. Turare kuwa har ji take yana hawa mata kai dan khumras nata sun sami haɗine na musamman daga hajiyar sudan, ga kuma *_YERWA INCENSE AND MORE +234 809 521 5215 da miss xoxo tayo mata haɗi da sai ƴar gata ke samunsa😋_*. Hakama na kanti duk masu tsadane da ƙamshi na musamman da aka zuba a lefe. Ƙanan kayan nata taso sakawa, sai dai Aysha ta hanata hakan, acewarta kayanmu na gida sunfi mata ƙyau. Dole badan taso ba ta haƙura ta shirya cikin skirt da riga na lass daya zauna mata a jiki tamkar ka saceta ka gudu. Aysha tai mata ɗauri na zamani daya saka ita kanta kasa rufe baki sai faman kallon kanta takeyi a mirror da ƙyalla hotuna da wayarta.....

     

     A gajiye ya iso gidan bayan idar da sallar isha'i. Ya fiddo ledojin daya shigo da su na fruits kashi biyu. Sashen Fadwa ya nufa, ya sameta zaune a falo ƙafa ɗaya kan ɗaya tanata cika da batsewa. Kallo ɗaya yay mata ya ɗauke kansa dan ko sallamarsa bata amsa ba. Ledar ya ajiye batare daya ce ko a ba yay ficewarsa yana ƙwafa. Dan a yanda ta masa ya bashi tabbacin tana kan sani taƙi ɗauka masa wayarsa. Sashen Anaam ya nufa da ɗayar ledar yanata faman furzar da hucin ɓacin rai......✍




Post a Comment

0 Comments