TOP HAUSA NOVELS atOptions = { 'key' : '20e08520dad54dbf6d9e963271

Sanyi da zafi page 65

 EPISODE 65

Wayan takara a kunne tana fitowa sabida tazo takarasa goge dinning din tasa wayan a speaker tashiga saukowa daga bene daga dayan bangaren Maimoon tace “Hello Rashida” itafa har yanzu she’s not use to having friends awkwardly tace “uhn” Maimoon tace “bakizo clinic ba, na dubaki ban ganki ba, are you fine?” Ahankali tasake cewa “uhm fine” daidai tana karasa saukowa dinning din taga Riyad na goge dinning din yajuyo suka hada ido dasauri tadauke kai Maimoon tace “but mesa bakizo ba”? Da sauri ta kalli Riyad hada ido suka karayi hakan yasa tajuya tace “uhnn bacci nayi” Maimoon tace “kai wani irin bacci ko nabiyo nadubaki dai? Inane gidan naku?” Tsayawa tayi saikuma tajuyo takalli Riyad hada ido sukayi saitaga ya gyadamata kai ahankali tace “GRA1 House 2B2” dasauri Maimoon tace “to gani nan zuwa gobe munada test I want you to teach me wannan course na pediatric surgery guy din nan wlh nakasa” ahankali tace “toh” dan murmushi Riyad yayi ganin tayi friend dan Mama tacemai batada friends and shima bai ganiba and from the way she’s talking to the girl sef kasan basu wani dade da haduwa ba batama iya kwancen ba karasa goge dinning din yayi yawuce kitchen everything is clean properly arranged murmushi yayi yayi dialing number security shi yana hawa sama yana dagawa yace “my wife’s friend is coming over tazo let her through” dudda tana daki but she heard maganan dayayi yawuce dakinshi books nata taciro daga jaka da pen tafara budewa da dan jitter nata tana ahaka taji karan an taba doorbell nasu da sauri ta tashi rikeda books din tafito tasauka kasa ganin baya falo taji dadi tawuce bude kofan tayi Maimoon na ganinta ta rungumeta tace “Rashidaaa” dan murmushi tayi tace “come in” shigowa tayi bayan tacire takalmi tashigo falon sai kallon falon take kitchen Rashida tawuce takawo mata abinci da drinks abinci tahau ci ta kwaso yunwan school tace “ke kika dafa abincin nan?” Gyadamata kai Rashida tayi Maimoon tace “you’re such a great cook wlh wow” cinyewa tayi tadauki juice tanasha tace “ina mutanen gidan lemme great them” dan kauda kai Rashida tayi ta tashi tana daukan tray tunda tagama ci tace “basa nan” sannan tawuce kitchen Maimoon tabita da kallon ganin kaman she’s hiding something from her, fitowa tayi hakan yasa Maimoon tace “but gidan waye nan din? Tunda kin cemin an saida naku?” Books tashiga dauka tana budewa tace “bazan dade anan ba zanbar nan shima yauwa kinada textbook din ni banda shi” tai maganan trying to kore conversation din dasauri Maimoon itama taciro suna fara karatu duk Riyad na jiyosu dan kawar akwai katon murya tasaki jiki sabida ance yan gida basanan sosai Rashida ke koya musu karatu har aka fara kiran magrib.

 Tashi tayi tana kokarin goya jakanta danzata wuce Riyad yashiga saukowa ahankali gadan ruwa a fuskanshi cus masallaci zashi ko kallon inda suke baiyiba jin sahun tafiya dasauri Maimoon tajuyo ganin wani kyakkyawan guy yasa dasauri dan tanada faram faram tace “ina yini” dan gyada kai yayi alamun yaji kafin chan ciki ciki yace “fine” yabude kofa still bai kallesu ba yafice dasauri Maimoon takalli Rashida tace “dama da wani agidan muketa surutu haka Rashida? Waye this fine Man?” Hakanan Rashida taji wani abu yataba zuciyanta yanda Maimoon tace fine Man sai kawai tai banza da ita tace “bari na dauko hijab na rakaki” wucewa sama tayi tadauko hijab tasaka tasauko suka fice tare har zuwa gate tai waving nata tace “bye” Maimoon tace “bye see you tomorrow a auditorium na CMD za’ayi test din” gyadamata kai Rashida tayi sannan tafice daga gidan itakuma tajuya takoma cikin gida. Salla tayi tasauko wlh sabida kawai baida lafiya ne dakuma masu gadin hakan yasa tashiga kitchen sai kawai ta dafa stair fried couscous tayi salad, tayi chicken pepper soup da juice again takawo komi dinning ta ijiye tadauki kula zatakai waje daidai ana bude kofa hannu kawai yabata tasamai tajuya tawuce sama wanka tayi tai salla tana zaune wayanta yahau ringing around 9 Riyad tagani kin dagawa tayi tunawa da maganinshi sai kawai ta tashi da hijabin har kasa tafito falo ta leka baya ciki hakan yasa tawuce hanyar dakinshi kawai taji batajin yin knocking itama direct tabude kofan wannan karan dagashi sai towel a waist ga karami a hannunshi sannan acire IV line datamai jiya kasa shigowa dakin tayi ta tsaya saikuma ta juya tace “idan kasa kaya ka kirani” dasauri yace “wait bari nasa” tashi yayi yaja wandon pajamas nashi yasaka shi kadai yace “come to” shigowa tayi taki kallonshi magungunan shi tadauka tadauki dripline tahada tace “why did you remove line dinka?” Ahankali yace “zafi yakemin nacire yanzu da ina wanka” bata sake magana ba ranta sai baci yake dük ta tuna maganan Maimoon saida taki kallonshi cus ita bata wani ga fine din da ake fadi ba dalla hannunshi ta karba nan da nan tamai fixing wani line tasakemai injection sannan tasaki hannunshi tajuya tafita yabita da kallo baice mata komiba tasauka kasa tahada maganin tsarin duka tasha, masu dadın da marasa dadin tana tabe baki sannan takoma sama dakinta tabude tashiga tasaka key tai bacci Washe gari da wuri ta tashi tai breakfast lafiyayye ta hada a dinning takoma sama tai wanka abaya black tasaka tasaka lab coat nata dataga an goge again yau sannan tawuce kasa tai microwaving kazam Ammi taci tasha magungunan sannan tai rolling gyalenta tafito goye da jaka harzata wuce saikuma ta kalli kofan dakinshi atleast taduba drip data sakamai. Knocking tayi murya chan kasa yace “come in” bude kofan tayi ganin yariga yacire drip din yasa taki kallonshi tadan juya tace “your breakfast na kasa, natafi school” tajuya zata tafi ahankali yace “Rashidah!” Chak ta tsaya saikuma ta juyo ahankali yace “your driver is waiting for you a compound all the best, your CA” samin kanta da kallon fuskanshi tayi murmushi yasakin mata ahankali dayasa taji gabanta yafadi dasauri tawuce a compound taga wata sabuwan benz fan kujeran da leda gawani dattijo haka yana ganinta yace “barka da zuwa hajiya” dasauri tace “ina kwana” shiga motan tayi yaja suka fita har zuwa makaranta dayake this morning suke da test din auditorium yakaita tasauka yace “ina nan zanyi parking” dasauri tace “katafi” yana murmushi tace “dan aikinki zalla aka daukeni duk inda na kaiki zan kira mukoma tare ranki shi dade” kallonshi tayi ganin student nasu na zuwa wajen yasa tajuya tatafi.




Post a Comment

0 Comments