TOP HAUSA NOVELS atOptions = { 'key' : '20e08520dad54dbf6d9e963271

Gimbiya hakima page 65-66

 πŸ‘ΈπŸ»πŸ‘ΈπŸ»πŸ‘ΈπŸ»πŸ‘ΈπŸ»πŸ‘ΈπŸ»πŸ‘ΈπŸ»πŸ‘ΈπŸ»πŸ‘ΈπŸ»πŸ‘ΈπŸ»

         *GIMBIYA HAKIMA* 

πŸ‘ΈπŸ»πŸ‘ΈπŸ»πŸ‘ΈπŸ»πŸ‘ΈπŸ»πŸ‘ΈπŸ»πŸ‘ΈπŸ»πŸ‘ΈπŸ»πŸ‘ΈπŸ»πŸ‘ΈπŸ»



*🌎MANAZARTA* 

*WRITERS ASSOCIATION* πŸ“šπŸ–Š️


     *M. W. A* 


```Kungiya d'aya tamkar da dubu. Masu Nazari da Aiki da Ilimi, Burin 'kungiyar a ko da yaushe shine ta fad'akar ta ta kuma Nishad'antar da masoyan ta. πŸ€™πŸ»``` 

https://www.facebook.com/107980080946102?referrer=whatsa 

________________________________



  _STORY AND WRITING_ _BY_ 


    _Jameelah jameey πŸ–‹_ 


    *(Yar mutan kankiaπŸ‘ΈπŸ»)*  


   




*BISSIMILLAHIR RAHMANIR RAHIM DASUNAN ALLAH ME RAHMA ME JINKAI*


_Wannan labarin kagaggen ne, duk wanda yazo daidai da rayuwarshi a kasi ne._ 


```NASADAUKAR DA WANNAN LITTAFIN GA FATIMA ABUBAKAR 

BELLO, ALLAH YA BAR KAUNA YAR UWA RABIN JIKI😍😍``` 




65&66




*×ZARIA×*



Tunda su Gimbiya Zulaha suka dawo daga wajen Turmurturs, Gimbiya Zulaha ta kasa zaune ta kasa tsaye dan gani take kamar boka yana yi mata yawo da hankali amman da ta tuna Turmurturs ne sai taji hankalinta ya kwanta dan boka Turmurturs ta amince yana share hawaye waya ta Ι—auka ta kira Hamad akan komai yake ya ajiyeshi yazo tana san ganinshi. 




"Hakim ya na ganka cikin damuwa Allah yasa lafiya."? 


"Aliyu ina fa lafiya Abba zaiyi man aure." 


"Aure kuma Hakim.''? 


"Wallahi aure zaiyi man wai yar'sarkin kano, maganar da nike yi maka Fulani tace gobe zani je wajen yarinyar.''


"Innalillahi wa'inna'alaihirajiun, Hakim abunda nayi maka gudu kenan shiyasa naso kanemi yarinyar nan Hakima dan wallahi ba Ζ™aramin marching kukayi ba, amman girman kai yana hanaka wai kai cewa ma kake ka tsaneta bayan ga sonta nan cikin idanunka ina gani."



"Allah ya tsareni Aliyu, ai gwara da Abba ya fidda man mata, ni natsi Hakima bansan Hakima ban Ζ™aunar Hakima kai mai ma irin sunan Hakima bani santa da wall... "Da kata haka Hakim, wallahi karya kake ni Aliyu nace karya kake kana san Hakima kuma nan gaba zakace na gaya maka."



Aliyu ya Ζ™arashe maganar cikin fushi dan bala'in haushi yake ji idan Hakim yace baya san Hakima bayan ga sonta yake ta Ι—awainiya dashi wannan abun na bashi haushi gashi har za'ayi mashi auren dole. 



```🀣 niko nace Aliyu kwanatar da hankalinka burinka ya kusa cika```


"Ya isa haka Aliyu enough, taya zaka zo kasani gaba kana gaya man maganganu saboda wata useless girl zaka sani gaba kana yi man tsawa, ka wuce ka ban waje kabarni da abunda ke damuna please."



"Ba inda zani kuma dole nayi maka tsawa Hakim dan wallahi banji dadin auren da Abba yake niyar yayi maka ba, gashi bamu san garin da Hakima take ba da nabita na nemo maka aurenta."




"What are you said?Aliyu kana cikin hankalinka kuwa? To bari kaji zanyi biyaiya na auri wanda Abba ya bani kuma zan koya ma kaina sonta after that kasan bani da budurwa to tada hankali name? Karka kuskura ka sake haΙ—ani da wannna idiot gril Ι—in take note". 



"Hakim wallahi kana yaudarar zuciyarka, kayi kokari ko bayan aurenka ne kaje ka nemo garin da Hakima take ka aure ta dan nasan tuni kadaΙ—e da kamuwa da soyayyar Hakima itama haka Hakimar dan haka is ur on choice ni kaga tafiya ta office kayi tunani."



Haka Aliyu ya tafi yabar Hakim dan tunani, "Tabbas Aliyu bai Ζ™arya ba idanuwana sun kamu da soyayyar Hakima amman zuciyata ba abunda ta tsana kamar haka, how comes taya haka zata kasance? No impossible i hate you Hakima."



Abunda Hakim yace kenan ya tashi ya wuce shashen Fulani ko yaji saukin abunda yake ji a cikin zuciyarshi. 



Tunda Gimbiya Zulaha ta kira Hamad waya ya Ι—auko hanyar zuwa dan ji yanda zasuyi Hakima ta zama tashi dan abun bata samu mafita ba yana aikata komai mudun Hakima zata zamo tashi, dan ya Ι—aukarma kanshi zai iya kashe koda Sarki Abdulmalak ne mudun ya hanashi auren Hakima. 



*(Wai Allah na wata sabuwa anya Hamad yana da hankali kuwaπŸ€”, taya zai kashe ubanda ya haifeka saboda mace, macen da bata san da zamanshi ba, Allah yasa mudace ya bamu zuri'a Ι—aiyabaπŸ™πŸ»).*


Bayan ya shigo royal house Ι—insu direct shashen Gimbiya Zulaha ya wuce dan yaji abunda zata ce mashi, bayan anyi mashi iso ya shiga ya samu waje ya zauna yana saurarenta dan baki Ι—aya hankalinshi wajen mahaifiyar tashi ya maida shi. 



"Hamad kanaji na ko."? 


"Eh ina saurarenki Gimbiya, "yauwa munje wajen Turmurturs amman yace aure dole ya Ι—auru ba yanda zaiyi ya hana auren." 




"To naji kinga tunda shi Turmurturs ya kasa, ni bari yanzun naje na sarema Hakim kai da man naga yana gida tunda naga motarshi"yana tashi tsaye yake maganganun dan da gaske yake zuwa zaiyi ya sarema Hakim kai tunda shi Turmurturs ya kasa. 



"Na  shiga ukuna ni Zulaha, Hamad baka da hankali? Ko dai kayi shaye-shaye ne kafin ka shigo gidan nan".? 



"Ba abunda na sha da hankali na wallahi kashe Hakim zaiyi ba zan bari ba ya auri Gimbiya Hakima ba, wallahi zan iya kashe koda ubantane balle Hakim da daman na tsaneshi komai za'ayi cikin gidanan shi Abba yake sawa saboda shine Ι—an so, to idan na kasheshi uban kowa sai ya huta."



Tas! Tas! Tas!, Gimbiya Zulaha ta wanke Hamad da zafafan marika har guda uku dan gani tayi sai ta mareshi zai dawo cikin haiyacinshi. 



"Gimbiya ni.. "Yi man shiru ko na Ζ™ara wankeka da  mari wallahi sakaran banza sakaran wofi, zaka zauna ko sai raina ya Ι“aci."? 



Haka Hamad ya zauna yana dafe da kuncinshi da ya sha mari, wata sabuwar tsana yaji yana yi ma Hakim dan saboda shi Gimbiya Zulaha ta mareshi abunda Gimbiya ba ta taΙ“a koda dungurinshi ba amman yau shine tasa hannu ta mara becouse of Hakim. 




"Hamad yaushe ka zamo wawa wanda baya aiki da tunani."? 


"Amman Gimbiya, "Amman mai Hamad kasan bala'in da zaka ballo mana idan ka kashe Hakim".?


"To tsaya kaji ni, mudun ka kashe Hakim, to kaima kasa a ranka sai ankashe ka, kaga mulkin da muke jira ya koma hannu Kilishi kenan munyi wahalar banza."



"Amman idan kabi a hankali ba wanda yaji ba wanda ya gani zamu kashe Hakim cikin ruwan sanyi, ba wanda zaice kashe shi akayi, "taya haka zata kasance Gimbiya? Sannan sai yaushe zaku kashe Hakim."? 




"Yanzun Hakim zai aure Hakima, amman boka Turmurturs yace zasu hana Hakima haihuwa da Hakim, suna kashe Hakim kuma sai a maida aurenka da Hakima kaga shikenan mun jefi tsuntsu biyu da dutse Ι—aya."




"Amman ina kishin Hakim ya rigani sanin Hakima a matsayin mace, zanyi hakuri da shawararku Gimbiya ni zan koma aiki."



"To shikenan, karka kuskura na sake jin kalma sai ka kashe Hakim , kajini ko".? "Eh naji na barki lafiya. 



Tunda Hakim ya tafi shashen Fulani ya kasa komai dan ko abinci kasa ci yayi shidai kagashi nan kamar ba shi ba haka yake jin kanshi. 



"Hakim ko baka san zaΙ“in da Abbanku yayi maka."? 


"Aa Fulani wallahi inaso, in ban bi umirnin iyayena ba umirnin wa zan bi, kawai ji nike kamar bani ba yau Ι—ina."



"Ka yawaita addu'a Allah yana tare dakai kaji yaron kirki."? 


"Eh naji Fulani, ni gobe zan tafi kano ni Ι—aya zani ko na tafi da Aliyu."? 


"Aa ka tafi kai Ι—aya ganin juna zakuyi kuma bikin saura wata Ι—aya haka naji Abbanka yace.''



"To Allah ya kaimu, ni zan wuce massallaci na barki lafiya."


Bayan Hakim ya dawo daga sallah Tea ya sha sannan yayi addu'oi sannan ya kwanta dan ya gaji sosai ga washe gari zashi kano. 


_______________________________



Tunda Hakima taji gobe Hakim zaizo bata zauna ba dan shiri take duk da tanajin ba dadi a zuciyata amman haka take Ι—aurewa dan taba mutanan gidansu mamaki. 



Bayan sun gama wani shirin dan Hakima Ζ™ara komawa tayi wajen gyaran jiki aka sake yi mata su dilka sannan ta dawo gida, har yanzun bata samu lokacin waya da Maryam ba balle ta gaya mata ba, amman tana ranta tana san gaya mata, bayan ta dawo wanka kawai tayi sai bacci. 




Washe gari tunda safe su Lantana suka tashi suka fara aikin tarar bako dan suke kamar mai abinci ake kala-kala dan har abun ya fara ba Gimbiya Hakima tsoro dan gani take kamar yau ce ranar bikin dan hidimar da bayin gidan keyi duk dan tarbar bakon da za

tayi a yau kawai. 




_Too My Fans wani kallar drama za'ayi idan Hakima da Hakim suka ga ashe junansu zasu aura? Am watting urs Answers🀣😎_



_BY Jameelah Jameey✍🏻_




Post a Comment

0 Comments