TOP HAUSA NOVELS atOptions = { 'key' : '20e08520dad54dbf6d9e963271

Sanyi da zafi page 55

 Sanyi da zafi page 55


EPISODE 55

Har yanzu yanada damuwa aranshi but dayama Mrs Bugaje explains komi about 40% na damuwan yatafi gida chan yakoma flat nashi yafada wanka yafito ya shirya cikin wasu kaya daban sannan yadauki laptop dinshi yashiga typing ba kakkautawa kafin yayi printing abinda yagama typing ya dauka ya kalla sannan yatashi yadauki wani envelop yasa aciki kafin yadauki pen da paper yazauna yayi wani rubutu shima yasa a envelop sannan yafito rike da abubuwan guda biyu yawuce side na Haleema.Wuraren 11 ya shiga gidan ya maida kofa yarufe yahayo sama ahankali yabude kofanta yaganta kwance akasa tana bacci awahale sai munshari take shiru yana yana kallonta, ko hayaniyan datayi yau ya isa yasata minshari, he just loves everything about her and overall yana tausayinta kaman me, shigowa dakin yayi yamika hannu kaman yadauketa but yana tsoron karya tadata saikuma yadaure after all kota tashi yanzu yanada plan gently yadauketa ko alamun tashi batayiba dan akwai ta da nauyin bacci sata yayi kan gadon ahankali yakai hannunshi yadaura saman kanta kaman yar yarinya gently yace “I’m sorry about your pain Jewel! I promise I will make it all go away” hannunshi yadaura kan kumatunta cikeda tsantsan so yace “just let me in, you don’t have to go through this difficult time alone, let me in Rashida, let me in please” yayi maganan yana dukowa ya manna mata kiss a goshi sannan yatashi bargo yaja yarufa mata ya kunna AC dakin ya kashe wuta sannan yafito yakoma dakinshi wanka yasakeyi ya kwanta wanda baiyi wani bacci ba yatashi yahau sallan dare da asuba yawuce mosque.

Jin gaisuwa da akema sarki yasa Haleematu ta mike tsaye da sauri tana kwashe plates na abincin dataci tun safe dasuke falon, plate dataci indomie yanzun nan shima yana wajen ta kwasa dasauri but kafin tagama hadawa yabude kofa yashigo suka hada ido kallonta yayi sannan yabi dakin da kallo dasauri tayi kitchen ta ijiye plate din tafito tace “inata kiran Mom tamaka magana kadawomin da bayina bata dauka badai kahadani da ita bane tana fushi dani ba” ijiyan zuciya yayi sannan yazaro envelope din daga aljihu ya ijiye mata akan kujera faduwa gabanta yayi tayi kujeran da gudu tadauka tashiga bude takardan. “NA SAKI HALEEMATU SAKI DAYA!” Reason sabida bani ta dauka amatsayin mijinta a auren mu ba, there’s a third party. Kallonta yayi strictly yace “park your things kitafi gidanku ki koyi zaman aure then give me a call idan kin shirya maidani mijinki sannan kin shirya zaman aure” yana maganan ya bude kofa yafita yana jiyo kukanta. Ahankali take bude idanunta tabi saman dakin da kallo kafin ta tashi zaune tareda taba bango luckily taji switch ta kunna wuta ganinta akan gado bayan tasan akasa tai bacci yasa tadinga mamaki tagumi tabuga saikuma tafashe da kuka tunawa da kashe Mama akayi cikin muryan Kuka tace “why did you sleep kema kikai bacci kaman kin mutu? Anyi poison Mama but bakusan ta yaya ba, kofan ta kalla tunanin a kulle yake yasa ta tafi bayi tabude akwai sabon brush da toothpaste dauka tayi shima dan kawai batajin dadin bakinta brush tayi tai wanka tayo alwala tafito bargon data dauka na gado tun jiya tana salla dashi takara dauka ta kabbarta sai hawaye take sharewa jitake kaman ta ramama Mamanta abinda aka mata, tunawa tai alkawari zata dinga karatun Al Qur’ani yasa tafara karatun daka mulk ta karanta gabaki daya tana zaune ahaka awajen taji an bude kofa ko kallon wajen batayiba, anatse Riyad dake kallonta yace “I’m ready to let you go but kifito falo I have something to tell you” dasauri tadago kanta ta kalleshi yana kallonta shima yace “Ammi tasamiki hijabi in that box kibude ki saka ki dauki takalmi also kifito” yana maganan yajuya dasauri ta tashi box din ta kalla daidai da tsinke nasu bataso amman kuma bazata iya fita ba hijabi ba hakan yasa tawuce box din tasauke ta bude taciro hijabin dayake dark blue tasaka har kasa yakaimata me hula gata fara saiya mata shegen kyau slippers tadauka tasaka shima sannan tabude kofa tashiga saukowa tundaga sama yake kallonta hijabin yamata wani kalan arnen kyau kaman ba gobe idanunta a kumbure gwanin ban tausayi karasa saukowa tayi batare data kalleshi ba ta tsaya wajen wani kujera tace “gani” dan ijiyan zuciya yasauke yadauke envelop na kusa dashi yadauka yabude yajawo papers na ciki guda uku yamika mata daga xaunen dayake yace “read this” kallon hannunshi tayi batare data kalli fuskanshi ba taki motsi, strictly yace “wannan ne ticket naki na amsan saki I will leave you for Good bazan taba tursasaki kiyi zaman aure da ni bakiso ba so gashi” jin maganan dayayi yasa tadanyi jim sai kuma chan cikeda taurin kai ta taho cikin falon yana kallonta babuko kyafta idanu ta taho tasa hannu ta karbe takardan tashiga karantawa anatse babu alamun wasa kan fuskanshi yace “this was drafted by my lawyer” anatse yace “as you said ke ba yarinya bane I can’t forced you to leave with me nor kidnap you tunda ni ba kidnapper bane but I can do one thing shine na karbi duka kudade na dana kashe akanku!” Dasauri Rashida data gama karatun komi na takardan ta kalleshi dan she’s very fast in reading, hade fuska yayi tamau kaman ba shi ba cikeda rashin mutunci yace “tunda na sanki I spent about 22Million naira akanki da mahaifiyarki kaman yanda kika karanta a papers din” Riyad ya gyara zama yana kallonta kyar kaman yanda take kallonshi kallon haka dama kake,  yace “incident daya faru a hotel I had to pay for medical treatment na yarinyar dakika daka and settle parents nata sabida karsukai kara, then Mahaifiyarki” yadanyi shiru yace “Allah jikanta! I spent money a hospital dana kaita, then nazo na kawo muku kayan abinci gidanku, kudin salla, saikuma rashin lafiyan nan datayi last that I paid everything which komi na rubuta kudin akasa, I break down the details inhar you pay me all of this money I will let you go forever!”

Kallon tsantsan tsana Rashida kema Riyad, sabida tace yasaketa shine yake cemata tabiyashi everything daya kashe akanta, tama kasa magana cus kudin slamp head and mouth dinta taji she’s speechless, anatse Riyad yace “your Mom tabani amanarki agaban kowa dudda is not on papers but kaman tayi assigning dina as next of king dinki ne, inhar baki biyani kudina ba you can’t leave my house haka lawyer na yace, idan kin bari kuma I can take legal action against you! Bazan takuraki ba anytime kika shirya biyana you can! But you have to leave with me and under me, while kina living dani bazan taba miki kallon matata ba cus nasan kince kin tsaneni but ni a matsayina na mijinki hakki na kaina ma ciyar dake da tufatar dake that I will do banda haka you are a nobody banmasan kina existing ba, thank god bake kadaine mace aduniyaba! And I have another wife!” Yadanyi shiru sannan yakalleta yace “as long as baki biyani ba kina karkashina the only aiki dana yarda kiyi kuma kije is your school and clinic, ni Sarki ne those shara and washing of toilet you dare not do such!” Yafadi da kakkausan murya yana mikewa tsaye yace “you are free Rashidah ke ba prisoner bane idan kinada anywhere dazaki you can go but dole ki kwana agidan nan inhar baki biyani ba or else duk inda kika shiga zansa akamoki aduniya” yayi maganan yana jefa mata key na gidan kan kujeran dake kusa da ita yace “that’s your key and this is your house bazan dinga zama anan ba inada Masarauta to run” haryahau bene yace “ohh I remembered something” saiya dawo da sauri yana ciro iPhone nata daga aljihu yace “nasa kudin wayan nan a list din so ita yours not mine tunda zaki biyani kudinshi take abinki, ur sim is inside ga school bag naki chan” yawuce sama abinshi Rashida mutuwan tsaye tayi 22Million naira ta ina zata fara biyanshi? Yanzu dama duk abubuwan daya musu ba kyauta bane? Saikuma wani bangare na zuciyanta yace keda kanki kince zaki biyashi ai lokacin saisa, hawaye ta share tasake sharewa tana kallon kudaden she has mugun self respect and she’s not a coward she rather die tana aiki danta biyashi than ta cemai ya yafemata kudin koya yakuri, wallahi bazatayi ba! Bayan hannu takai kan fuskanta sannan tace “Riyad Rashida tamaka alkawari she will pay you this money ko mujima komu dade!” Jakanta ta dauka da wayan tunda yasaka kudin kawai tayi kofa tafice batare data dauke key nashi ba.   DID YOU SUPPORT DECISION DIN RIYAD????




Post a Comment

0 Comments