TOP HAUSA NOVELS atOptions = { 'key' : '20e08520dad54dbf6d9e963271

Sanyi day zafi page 73

 EPISODE 73 

Duk tsaitsaye sukayi kusan Moddibo shine babba agarin, so ana jin maganansa sosai, shi likitan Hawaro ne yace "Modibbo yaya za'ayi yanzu?

Yanda takeda juna biyun nan da mijinta kenan yakamata anemo yan uwanta" dasauri daya daga cikin jama'an yace "binni zamu shiga muje wajen yan sanda mu fadi abinda yafaru" dasauri wani daga cikinsu yace "amman kuma likitoci nada amfani ga al'umma mesa bazamu barta taji sauki ta taimaka mana ba da likitancin zamani, takoyama Hawaro abubuwan zamani na lafiya amatsayin tukuicin cetota da mukayi saita tafi, yanzu rayuwanta na cikin hatsari idan mukaje muka fada mutanen sukazo har nan suka kasheta fa"? Sai abun yakoma wannan yafadi nasa wanchan yafadi nasa gyaran murya Modibbo yayi yace "ku dakata" duk shiru sukayi suna kallonshi, cikeda dattaku yace "na farko dai rayuwan yarinyar nan nacikin hadari gata da kankanin ciki tareda ita, idan kunga gardawan dasuka daukota a tarbama a hadamu mu goma sannan za'a samu daya" yasake yin shiru sannan yace "abarta tafarfado muyi magana da ita da kanmu sannan tafadi mana waye mai gidan nata saimuje da kanmu mu shiga binni mu nemosa yazo ya dauki matarsa gudun kar miyagun su biyota, idan tanaso zata iya koyama Hawaro likitancin zamani saitayi idan bataso saisu tafi kun yarda?" Atare kowa yace "eh" hakan yasa suka zauna suka shiga zantawa yana kara basu labarin yanda yafada kogin.

**

Wasa wasa yau kwana 7 babu Rashida babu labarinta kowa yakasa gane kan Riyad, labari yabi ko'ina afada Sarki na neman haukacewa sabida anyi kidnapping matarsa haryau kuma kidnappers sunki kira, Haleema karan kanta saita fara regretting komi cus attention datake nema wajen Riyad ma tarasa, he's not even himself, komi ya tsayamai chak baya  baya gane komi, sannan komi no fada ya tsaya allbecause of shegiyar Rashida.

Ammi dasu Buba da Muji da babu inda bai shigaba har wajen yan sanda saida yaje yaga koto Jummai ce yaga tana kulle but ansaki Mom yazo yafadi Riyad kanshi baya wajen su Ammi ke mamakin yanda aka saki Mom, an baza hotunan Rashida ko'ina da news da tv ana cigiyanta, Riyad yadawo abin tausayl.

Ahankali take bude idanunta dasuka mata shegen nauyi tana kallon saman bukkan dakin kafin gently tayi yunkurin tashi taji sharp pain akanta dayasa ta daddage ta kwala uban ihu. "Wayyyyyoo kaina" da gudu aka shigo dakin wata yar matace sanye da kayan fulani yaro goye abayanta tana kallon Rashida dake ihu sosai tana kokarin cire kyallen da aka daure mata kan dake mata shegen azaba, da sauri matan takama hannunta tarike tace "yakuri, sannu sannu, Hawaro yace kar abari ki kwance idan kin tashi saiya zo dakansa yakuri" fashewa da kuka sosai Rashida tayi tana rawa da fuskanta tace

"kaina zafiliiii" daidai nan Hawaro ya shigo da dan kofi a hannunshi tareda Modibbo ya duka ata bayanta yakai hannu yana bude kyallen kan yakai cup din yanaba matan ta karba tace "ungo sha maganin zafin zai dena" bakinta takai kofin tana lekawa datagani baki saikuma tace "menene shi?" Dasauri matan tace "magani"? Dasauri Rashida tace

"menene magani?" Dasauri dukansu suka kalleta saikuma matan tace "shine zaisa kan yadena zafi"

Dasauri tabude baki aka samata kofin ta kurba kadan tacire fuska tana yatsine fuska sabida daci daidai lokacin Hawaro yashiga kankare maganin daya shafa akanta daya bushe, ihuuu tayi zata yunkura ta gudu, da idanu yamusu alamu su riketa suka riketa yahau cirewa tana ihu sosai tana kuka, haka yacire ya maida wani madani wajen sannan suka saketa yadauki wani kyalle ya zagaye kan dashi, Modibbo yabata nono a kwarya yace "sha" kallon nonon tayi saikuma tana goge fuska tace

"menene shi?" Ahankali yace "nono sha" karba tayi takai bakinta ta kurba kadan saikuma ta ijiye ta shiga kallonsu yanda suke kallonta suma kaman sun sami tv zafin kan yasoma rayuwan mata, ahankali Modibbo yace "ya sunanki?" Bakinshi take kallo saikuma ahankali tace "sunana?" Saikuma tashiga kallon jikinta tanabin fararen kayan fulani dake jikinta da kallo takai hannunta ta taba kanta kafin takara kallonshi tace "sunana" saikuma tace

"sunana" ijiyan zuciya Modibbo yayi yace "kin manta sunanki" dasauri tace "sunana" tashi

Modibbo yayi kawai yafice waje dasauri Hawaro yabiyoshi, Modibbo yakalleshi yace "zan dauki Liti, da Anas mutafi binni muje wajen yan sanda mu bada sanarwa, banson na je da ita, amman kai ka zauna dasu sabida kar jikinta ya rikice bari muje" gyadamusu kai yayi yawuce su uku suka tafi daga kauyen zuwa wajen gari kusan tafiyan machine awa daya, sannan sukahau mota dazai kaisu Kano about 2 and half hour journey in total, the nearest police station dake nan tashan dasuka sauka suka shiga, ihu yan sanda suka musu ganin su wani kala. "Me kukezo yi nan"? Ahankali Modibbo yace "munzo fadan wani abune daya faru sirri ne gaskiya opisa" wani kallo dan sandan yamusu yace "fada ina jinka" kallon wajen Modibbo yayi saikuma yace "gaskiya muje daga ciki" dan jim dan sandan yayi saikuma yace "okay muje" sukai ciki wani office yabude musu suka shiga yazauna yace "ina jinka" anatse Modibbo yashiga koro bayani sannan yace "yarinyar ina kyautata zaton likita ce tana sanye da fararen rigan likitoci mun batta chan kauyenmu sabida kanta dakuma bamusan ko za'a sami mijin nata ba Ambato rigan likitoci dayayi yasa dan sandan yace

"kujirani" yawuce yafita office na ogansu yawuce ya sanar dashi komi da sauri yasa akawosu office nashi, shigo dasu office na Ogan yayi exact bayani sukamai wayanshi yaciro dasauri yaciro hoton

Rashida yanuna musu yace "itace?" Atare dukansu ukun sukace "eh" wani bala'in farin ciki dan sandan yayi promotion guaranty kenan, dasauri yashiga kiran asalin ogansu kwata kwata ya sanar dashi komi.

Daga Ammi har su Buba dasu Gwaggo da Muji duk an taru ana kan Riyad da aka kasa gane kanshi

Sarkin gida yabuga uwar sallama.

"Assalamuuuuuuuu Alaykum, nazoma da sarkina babban gagaruman sako amin izini" kallon kofan Muji yayi yace "shigo" dasauri yashigo yana gyara malum malum yayi wajen Riyad dake kwance kanshi akan cinyan Ammi gashinan ne kawai ya rame looking sick sosai, zubewa yayi inda Riyad yake da waya a hannunshi ya nuna wayan yace "yanzun nan commissioner na yan sanda yakira masarautan nan" da kyar Riyad yajuyo da kanshi yakalli sarkin gida, sai kawai sarkin gida yafashe da kuka yace "Mai Martaba ana kyautata zaton anga Sarauniya Rashida!" Wani kalan zabura Riyad yayi yatashi yazauna yana kallon Sarkin gida yana kokarin kara gasgata abinda yaji, Muji yace "mene mene? An ganta? Anga Rashida? Aan ina"? Sarkin Gida na kuka yana kallon Riyad yace "wasu bafulatanai guda uku sukazo offishinsu na tashar riya sukace sun tsinceta sany da kayan likitoci ajikinta an nuna musu hotonta sunce itane" wani irin tashi da Riyad yayi sai kawai yadauki key mota daya gani kan table yayi waje da gudu biyoshi kowa yayi harda sarkin Gida da Ammi dake neman lullubi da Gwaggo da Muji yarike tana kuka sosai duk aka wuce aka shishiga mota Sarkin gida na nuna hanyar police station din da akace suke, suna kaiwa parking sukayi Riyad yasauka ya shiga police station din da gudu kowa yabiyoshi Sarkin Gida na ihu "gafaradai gamai Martaba" ana kallon Riyad da babu rawani ko alkyabba ajikinsa.

Babban su ne yataresu yanuna yan fulanin yana farin ciki yace "gasunan mutanen Ranka shi dade dasukazo mana da bayanin" kallonsu Riyad yayi dasauri yayi wajen babban cikinsu bakinshi har rawa yake yahada hannayenshi biyu yace "dan Allah ku kaini wajen Matata!" kallonshi duka suke

Moddibo ya gyadamai kai yace "bismillah mu, muje Alhamdulillah tunda an sameku" yan sandan ma suka dauki mota guda, Modibbo yashiga motan Riyad, sauran suna motan yan sanda aka dau hanya Allah yasa Munir ke tuki cus Riyad can not even drive 2hrs suka bata a hanya motocin nasu ma basu karasa shiga kauyenba haka duk suka sassauka akahau machine harda Gwaggo tace baza'a barta a mota ba.

Har kauyen nasu kafin sukai wajen bukkan duk akai parking suka sassauka dagakan machine yara da manya na zuwa suna kallonsu ganin fuskokin baki, chak Riyad ya tsaya yana kallon Rashida dake zaune kan tabarma agaban bukkan matan Modibbo tana sanye da kayan fulani farin rigansu da zani, babu dan kwali akanta amman an nannade kanta da kyalle har zuwa goshinta, ga kwarya daban daban na abinci agabanta kusan guda biyar wayanda matayen kauyen duk suka kawo mata ganin takicin abinci har yanzu gashi tuntuni ta tashi kuma yunwa takeji, daya tuwo da miyan kuka, daya usulin awaran nono, daya kuma shinkafa da miyan ja, daya namomi cike ne da aka soyamata da manja, sal dayan kwaryan kuma fura, sai kallon abincin take,ayanda take kallon abincin kasan kaman batada lafiyan kal.

Nunata Moddibo yayi da hannu daga inda suke tsaye wajen masu machina da akace su jirasu yace

"gatachan" kowa kasa motsi yayi har Buba, cikin muryan kuka Gwaggo tace "meya sameta naga an daura mata tsumma aka?" Ahankali Modibbo yace

"dana cirota daga ruwa kanta afashe jini na zuba daga kanta, to tafarka muna tambayanta ya sunanta kaman ta mance komi banda haka kuma akwai juna biyu ajikinta yanzu zaiyi sati uku!" Dawani irin sauri Riyad ya kalleshi hakama kowa ke kallonshi jin abinda ya ambato ganin yanda suke kallonshi yasa Moddibo yadaga hannu yakira Hawaro dake cikin tarin jama'an yan kauyen dake kakkallonsu yace

"Hawaro taho" dasauri matashin yazo Moddibo ya nunashi yace "ni kawai na cetota daga ruwa ne amman ga asalin wanda ya ceci rayuwarta dana halittan datake dauke dashi nan Hawaro" yadan sauke ijiyan zuciya yana dafa Hawaro yace "yasan magunguna shine ke bamu magani idan muna ciwo, ya gaji magani daga kakanninsa, Hawaro gayamusu meke damunta".




Post a Comment

0 Comments