TOP HAUSA NOVELS atOptions = { 'key' : '20e08520dad54dbf6d9e963271

Babu so page 58

       *_❤‍🔥BABU SO....!!❤‍🔥_*

                 _(Miya kawo kishi?)_




              *_Bilyn Abdull ce🤙🏻_*


*_BABU SO👉🏻AREWABOOKS_*


*_58_*



Assalamualaikum


NAFISAT K ABDULLAHI

Is an actress in the kannywood industry


She's a singer and can sing all types of songs 


You can't afford to miss her newly released song named *KADDARATA* part 1-4 on her YouTube channel *OFFICIAL FEENAT*


You can only click on this link and stand a chance to listen and watch her amazing video 


https://youtu.be/t__84EwU7Fo


Dont only enjoy the emotional video but also *SUBSCRIBE* to anable you to be notified when ever she upload another video


Like and drop your comment under the video to encourage her do more of that .


The only way you can support and encourage her is by *SUBSCRIBING* to her YouTube channel below


https://youtu.be/t__84EwU7Fo


She is used to noticing those following and commenting on her videos .



*GUESS WHAT*?


https://youtu.be/t__84EwU7Fo


Click and see for yourself

Thank you so much

_______________________


........Hanunta take ɗagawa daƙyar tana kai masa ƙananun duka, ya fara ƴar dariya da ƙoƙarin riƙe hannayen nata. Duk yanda yaso su koma barci hakan ya gagara, dan ƙorafinta na zafi da raki ya gagara tsayawa. Ga zazzaɓi mai zafi dake ƙara rufeta bayan sauka ya kamata yayi tunda tasha magani. Dole ya tashi zaune da ita a jikinsa yana ƙoƙarin son su haɗa ido amma taƙi yarda. Bai damu da hakan ba, dan yasan kunya dole ce. Shi kansa wani nauyi yakeji amma yana ta ƙoƙarin ganin ya fuske abinsa..

     “Faɗamin miye matsalarki kuma Noorii na?”.

Shiru ta kasa bashi amsa, sai ƙoƙarin son kauda kanta kuma take yaƙi bata dama. Dole ta buɗe baki muryarta a ɗashe irin ta wanda yaci kuka ya more, dan ko fita batayi da ƙyau. “Inajin zafi mai raɗaɗi, dan ALLAH ka kiramin Mamie ko ka kaini wajenta”.

       A ransa yace, (Ko ɗaya a ciki bazaki samu ba) a zahiri kam wayarsa ya ɗauka zuciyarsa na masa kaikawo akan waya dace ya kira. Har yai dailing number Dr Jamal sai kuma ya katse, text message ya tura masa. mintuna kaɗan kuwa sai ga kiransa. Kamar bazai ɗauka ba sai kuma ya ɗaga da miƙewa ya fice a ɗakin.

     “Malam ba kirana nace kayi ba, Nurse daka aminta da ita nace ka turamin”.

           Dr Jamal yay murmushi da shafa kai daga can, “Oh to ai ko asibitin ban fitaba shiyyasa nace bara na kiraka naji waye babu lafiya?”. Jimm yay na wasu ƴan sakkani, sai kuma ya furzar da huci a hankali ya furta “Juwairiyya!”.

    “Ayya ALLAH ya bata lafiya, mizai hana ka kaita asibiti kawai sai mu haɗu, dan gaskiya a iya hasashena ban san wace Nurse zan tura maka ba indai irin wadda nasan zaka buƙata ce. Amma Dr Bilkisu na tabbatar ta iso yanzu zatafi kulawa da ita da sanin matsalarta kai tsaye inma mune baka son mu duba maka ita..”

     “Kai ka sani”.

Ya bashi amsa a taƙaice da yanke wayar. Daga can Dr Jamal yay ƴar dariya da ajiye wayar ƙasan zuciyarsa na masa kaikawo amma yana turewa dan yayi alƙawarin mantawa da ita, zai cigaba da mata kallone kawai irin na ƙanwa kuma matar amininsa insha ALLAHU.

       Shawarar Jamal ta masa, dan haka ya taimakawa Anaam daketa hawaye har yanzu ta shirya, shima dai a gurguje yay nasa shirin. Duk yanda yaso tai taku daga bedroom zuwa waje ta kasa, ko bedroom ɗin ta kasa iya ƙarasa fitowa zafi kawai take ambata tana hawaye, gashi duk ta langaɓe masa kamar mara ƙashi a jiki. Dole ya ɗauketa gaba ɗayanta ya fito.....


      ★Ranta fes ta tashi yau kamar yanda ta kwanta sakamakon jin ƙwarin gwiwa daga sirrin su aunty Safarah. Gaba ɗaya cikin yaƙini da imanin maganin da suka batan yayi aiki take. Tana idar da salla cike da karsashi ta shiga kitchen da kanta haɗa breakfast. Hakan ba ƙaramin mamaki ya bama maman Abu ba. Sai dai bata iya cewa komai ba dan ta fahimci uwar ɗakin nata tana a farin ciki, tasan kuma yana da nasaba ne da abinda taga tanayi jiya. Sai taji inama zata fahimceta kuma ta isa ta bata shawara akan abinda take kallo ba komaiba. Taji sanda su aunty Safarah ke tabbatar mata maganin matane suka bata, ita kuma ta aminta da hakan saboda bata da ilimin banbancewa, ta sani Fadwa nada rawar kai da ɗagawa, dan duk wanda ya kwana ya tashi a gidansu yasan ita ɗin boss ce musamman akan ƴan aiki, to amma kuma duk da kasancewarta a haka ɗin bata taɓa tunanin ganinta da wani mugun hali da ya zarta waɗannan ɗin ba, tanaji a ranta kuma da wani zai fahimtar da ita abinda su aunty malika suka bata nada banbanci da maganin mata ƙila bazatai amfani dashi ba duk da bata san zuciyarta ba dai.

     Tana aikin gyaran sashen nata ita kuma tana haɗa breakfast mai rai da lafiya a kuma nutse, dan dama dai shiriritarta da son jiki ke hanata yi ɗin a yanda ya kamata bawai dan bata iya ba. Cikin ƙanƙanin lokaci ƙamshi ya gauraye ko'ina, cike da nishaɗi ta kammala ta koma bedroom ta gyara jikinta. A yau zata kawo duk wani iskanci da jiji da kan Anaam a gidan nan, dan babban burinta tai gaba ta barta da mijinta salin alin.

     Ƙarfe takwas da wasu ƴan mintuna ta nufi sashensa dan tasan ya tashi zuwa yanzu, shi ba ma'abocin barcin safe baneba ma, amma a yanzu tunda yana gida ba aiki zai fitaba tasan ko yaya zai ɗan kwanta.....

      

     Fitowar Fadwa yayi dai-dai da fitowarsa ɗauke da Anaam daga sashenta. Babu shiri taja birki ƙirjinta na dukan tara-tara bama uku ba, shi sam baimaganta ba dan hankalinsa gaba ɗaya ya tafine ga kallon Anaam yana murmushi, saboda tsokanarta yake akan raguwace ita tana tuttura masa baki da kauda fuskarta gefe. Anaam ɗin kam sarai ta ganta, duk da halin da take ciki hakan bai hanata ganin wannan wata dama bace, ada taƙi yarda ta riƙesa, a yanzu kam saita saƙalo hannayenta a wuyansa duk biyu tana sake sakin kuka da cusa kanta a ƙirjinsa. Shiko da bai san dalilin yin hakan ba sai ya ɗan manna mata kiss a goshi da sakin siririyar dariya. A hankaki yake taku har zuwa wajen motar tasa, ya dureta ƙasa tare da jinginata da motar. 

       “Ina zuwa”.

Ya faɗa yana barin wajen, batace komai ba sai dai idanunta na satar kallon sashen da Fadwa dake binsu da kallo har yanzu kamar a birkice take. Da sauri Fadwa tai baya alamar bata buƙatar ya ganta, shima da yake ALLAH yasa hankalinsa ba wajen yake ba sai bai lura da ita ba ya wuce yanzu ma. Mintuna da basu fi uku ba ya sake fitowa hannunsa da key ɗin motarsa. Sake wucewa yay abinsa batare da yanzu ɗin ma ya ganta ba dai...

      A gaban idonta ya sake ɗaukar Anaam ya saka a mota, shima ya shiga suka fice gidan. Tai baya kamar zata faɗi maman Abu da itama komai ya faru akan idonta ta riƙota. “Hajiya dan ALLAH ki kwantar da hankalinki”. Maman Abu ta faɗa muryarta cike da damuwa itama. Da taimakonta Fadwa ta koma ciki, ta ɗakko mata ruwa amma sai ta hankaɗar da shi ya zube, wasu zafafan hawaye da sai yanzu suka sami damar fita a idanunsata suka shiga rige-rigen sauka a fuskarta. Maman Abu dai batai fushiba, takai zaune kusa da ƙafafunta a ɗarare ta sake faɗin, “Hajiya dan ALLAH karki ɗaga hankalinki, wannan kaɗanne daga halin maza idan suka ƙara aure. Amma inaga ki bincika kiji mike faruwa tukunna kamar zaifi. Koba komai kin jefa tsuntsu ɗaya da dutse biyu. Na farko dai zaki san mike faruwa, na biyu kuma zaiji kunyarki idan fitar bata da wata babban dalili da farar safiyar nan. Amma idan na shiga hurumin daba nawa ba kiyi haƙuri..”

     Idanu Fadwa ta sake rumtsewa da ƙarfi zuciyarta na wani irin zafi da raɗaɗi, dan tabbas abinda Shareff yayi ya sake zuzuta zafin daya sauka mata lokaci guda, kishi ya rufe idonta ta kasa ji a ranta wata matsalace ta sakasu fita gidan da safen nan bawai lafiya ba.....

     Waya ta ɗauka da sauri ta fara laluben layin aunty Safarah. Bata tsaya ko gaisuwa ba ta sakar mata kuka. 

      “Subahanallahi Fadwa lafiya kuwa?”.

   “Aunty Wlhy maganin beyiba, yanzu fa da safen nan ya fito ɗauke da ita suna farin cikinsu da dariya suka bar gidan nan. Alhalin jiya babu wani kusanci makamancin hakan tattare dasu. Aunty na shiga uku idan hankalinsa ya koma kan yarinyar nan. Jiyafa taimin alwashin indai ya fara kasancewa da ita saina zama ƴar kallo....”

     “Kinga nutsu ki saurareni Fadwa. A yanzu haka gani tare da Aunty (Gwaggo halima) kuma duk tana jinki, dama nazone zan amsa sako da zamuje wani waje saboda ke”.

      Sunan maman ta fara kira cikin kuka, Gwaggo Halima da tun fara bayanin Fadwa wutar kanta ya ɗauke saboda shi babba duk inda yake babba sunansa, tuni zuciyarta ta hasko mata wani abu ya shiga tsakanin Shareff da Anaam kenan, dukan kokarinsu na hana faruwar hakan bai yuwuba kenan, taja numfashi. “Fadwa kinga nutsu kuka ba naki baneba. Karki damu damun bayanin komai na riga na sani domin ni na aiko su Safarah wajenki dama nace ne karsu faɗa miki. Yanzu ki jira zamu kiraki ina zuwa...”

    Kafin tace wani abu aka yanke wayar, ta zube a bakin gado da sake fashewa da kuka mai cin rai....

     

_______


      Cikin ƙanƙanin lokaci suka iso asibitin, yanzu dai taso nuna jarumtar hanashi taɓata amma ina hakan bai yuwu ba. Dan taku biyu kacal ta nema zubewa tamkar ta fasa ihu dan zafi. Dole dai ya ƙaraso ya ɗauketa.

     “Ni dai Yaya ka saukeni zan iya”.

Ta faɗa tana sharce hawayen dake ambaliya akan fuskarta saboda hango Dr Jamal dake nufosu alamar yasan da zuwan nasu. 

    Murmushi yay da kashe mata ido ɗaya “Da wannan tafiyar tonamin asirin ne zaki iya?”. 

      Idanunta ta rumtse kunyar duniya a kanta, dan gani take kowa zai iya sanin miya faru da ita ne. Da taimakon Dr Jamal suka sami ganin Dr Bilkisu a sahun farko. Ganin Anaam taƙi amsa tambaya ko guda ɗaya a gaban Shareff daya tsatstsareta da ido yasa Dr Bilkisu kallonsa da ɗan murmushi. “Alhaji Al-Mustapha ko zaka ɗan bamu wajene dan naga patient ɗin tawa kasancewarka tare damu ya hanata cewa komai”.

       Ido suka sake haɗawa da Anaam. Tai azamar janye nata da tura masa baki. Mikewa yay yana murmushi batare da yace komai ba ya fita. Ko'a bayan fitar tasa ma sai da Dr Bilkisu ta sha fama sannan Anaam ta amsa mata wasu daga cikin tambayoyin nata tana faman sinne kai, a yanda ta fahimci ta kasa zama da ƙyau tai hasashen abinda Anaam ɗin ke faman ɓoyewa. Batace komai ba ta taimaka mata zuwa gadon da suke duba marasa lafiya, ganin tana neman ɗage mata doguwar riga ta riƙe da sauri tana girgiza kanta...........✍     




Post a Comment

0 Comments