TOP HAUSA NOVELS atOptions = { 'key' : '20e08520dad54dbf6d9e963271

Zazzafan so cmplt (B)

 Cikin k'asa da murya kuma a nutse yace, "kina burgeni Hafsah.

Muryar da kiran sunanta da yayi sukayi tasiri a zuciyarta..

Ina son sunanki, sunan mamana ne dake, fah.

"Allah sarki. "Haka tace kawai.

"Bari na barki kiyi bacci kada na hanaki bacci, Allah ya bamu alkhairi."

Ya kashe ba tare daya jira tace wani abu ba.

Ta zubawa numbobin shi ido, wane ne shi.. wanne irin mutum ne Allah ya hadata dashi, ya sanyata dariya lokaci d'aya ya barta kuma."?

A take, taji ya shiga ranta, duk da wani bangaren na zuciyarta na kwab'arta akan _kada ta zak'e, daga had'uwa baki sanshi ba.!!

_Funny ukhasha._

Haka taga hannunta ya rubuta wajen saving d`in number shi.

Allah ne ya kawo mata shi, lokacin da tunanin Jamila yayi mata yawa, saboda damuwar tana kiran number bata shiga, gashi 'yar wayar da sukayi har yasa ta manta...

Ta runtse idonta, sai taji tana son ta tuno kamannin shi, Ahankali take imagine ( _ayyana shi_) d`inshi, da wani ustazun mutum, mai cikar kamala...

Kwanaki sun fara tafiya, har ta saba da kiranta da yake, su gaisa, amma yawanshi a tak'aice, sai dai ba sa waya su gama bai sata dariya ba. Sai dai wani lokacin idan ya kirata takan share, idan kuwa ta d'aga kiranshi na gaba sai ya nemi afuwar ta, "Ayi hak'uri a taimaka kada a gaji dani d'indai, in sha Allah kin kusa gane wanene ni, don nasan hakane yakesa kike doubting akaina.!!

Wannan wanene haka, ya kware wajen _reading mind d'inta._ Hakika ta matsu ta ganshi, Gashi kullum sai dai yace, mata ta kusa sanin _wane shi,_ amma har yau bai tab'a neman alfarmar zai ganta ba shi, sai ta fara zargin abubuwa da dama..

Abinda bata sani ba shine, ya matsu sosai ya ganta, amma yana shakkar tambayar ta ne kada taga zak'ewar shi..

Yau ta kuduri niyyar kiran jamila a waya, suyi magana ko na mintuna ne ta haka zata gane idan har zata ci nasara akan jamilar.

Bayan missed calls in da tayi mata har wajen guda biyar, k'arshe dai jamilar ta biyo kiran.

'Sun gaisa sosai, sai kuma Hafsah taji kamar ran Jamila a b'ace yake, saboda yadda taji muryar ta.

Gashi kuma gefe guda ta rasa ta yadda zata cigaba da hirar tasu, domin bayan gaisuwar basu ce komai ba.

Jamila ce tace, "Hafsah H Hamid, kin gama school koh."?

"Eh Jamila mun gama Service ma."

Tayi murmushi, "Gud."!

"Kina aiki kenan."

Eh Inji Hafsah, a takaice ta bata amsa saboda tambayoyin yana tuna mata baya ne, kuma sai take ga kamar tono halin da jamilar ke ciki ne a yanzu.

Can ta jiyo Jamilar ta kuma cewa, tana wani murmushi..

"Hmm Hafsah kenan ai zan kawo miki ziyara, Idan na shigo unguwar namu."

Gaban Hafsah ya fad'i jin hakan, saboda batayi tunanin Jamila zatace zata zo gidan su ba.

Amma sai itama tayi murmushi kawai tace, "Okey thanks sai na ganki."

Okey Inji Jamila, sannan tace "Bye."

Ta kashe wayar.

Hafsah tayi ajiyar zuciya kawai, tayi shiru tana tunani, anya abinda take son yi kuwa zai yiwu..?

Ance,

_"Duk wanda yai nisa baya jin kira.!_

Sai taji tana k'ara godewa Allah bisa, yadda ita rayuwarta bata tab'arbare ba..

Tasani ba dabarar ta bace ko kuma dabarar iyayenta, kawai dai shiriyar Allah ce wacce yake shiryar da wanda yaso.'

"Alhamdulillah alaa kulli haal."!

Ta fad'a ahankali tare da yiwa kanta murmushi.

___________________

Yana kwance kan gadonshi, yana kallon sama, ya dafe kanshi da Hannaye biyu, wani irin Ciwon kai yake fama dashi tun tashinshi daga bacci, azuci yake karanto addu,a sannan ya shafe kan nashi.

Ya duba agogo, karfe shida na yamma magriba ta kusa.

Don haka ya mik'e zaune, saboda yamma ce lik'is.

Koda aka kira sallah ma bai fita ba, adakinshi yayi sallah har zuwa daf da isha'i sannan Fadwa tazo tana buga k'ofarshi.

Abude kofar take Don haka ta jiyo shi yana cewa, "Abude yake k'ofar ki shigo."

Duk da bai san wanene ba, yasan bazai wuce ita bace.

Ta shigo da sallama, ya amsa ahankali, yana kwance a dandaryar k'asa, akan dadduma inda yayi sallah.

Ta sami gefe ta dan zauna sannan ta fara mishi magana.

"Sannu Yaya."

Duk da bai fad'a mata ba tasan bashi da lafiya ne.

"Yawwa."

Yace mata.

"Me yake damunka, ya nuna mata kanshi."

"Oh sannu, Hajiya tace baka ci abinci ba, yanzu me za,a dafa maka."?

"Ki dafa min koma mene."

"A,a dai Yaya ka fad'i me zaka ci."

"To ki bari kawai"

Najwa tayi shiru, abin ya bata mamaki da takaici, amma data tuna halinshi sai kawai ta mike ta fita.

Ta fahimci baya son adameshi idan har yana wannan ciwon kan, amma ita ta tambayeshi ne saboda taji irin abinda yakeso, kada tayi mishi abinda baya so.

Har ta tafi sai kuma ta dawo adan tsorace tace, "Um wai kasha magani."?

Yasan babu wanda ya sata ta tambayeshi tunda babu wanda yasan bashi da lafiyar idan ba yanzu da aka ga bai fito ba tun yamma.

"Zansha."

Yace mata kawai.

Ta juya ta fita..

Fadwa rasa abinda zata kawo mishi tayi, sai kawai ta hada mishi kayan tea, ta dafa mishi Indomie, ta kawo mishi.

Ya mike yana kallon abincin, ko nazarin me yake oho, ita ko tana gefe ta zauna.

Har kusan minti 3, sannan taga dacewar ta ta had'a mishi, nan ta hada mishi komai, sannan ta mik'e zata fita.

"Thank you."

Yace mata ahankali.

Bata juyo ba kuma bata, ce mishi komai ba ta fice, tana murmushi.

_Wato zaman da yayi jira yake tayi serving d'inshi ne, amma kuma yaki mata magana._


Ya samu ya ci abincin da tea d'in sosai, sannan ya mike yayi sallar isha'i, ya dan jima a zaune yana jan tasbaha, sannan ya d'akko maganin shi yasha.

Wayar shi nacan gefe tana chaji amma jin kiwuyar dakkota yake yi. Sau biyu yaji kira na shigowa amma kuma bai son tashi bare ya d'akko.

'Wasa wasa Ciwon ya dauke shi kwana biyu, har sai da Hajiya ta matsa aka rakashi asibiti, an mishi 'yan gwaje- gwaje, babu komai, sunfi ta,allak'a hakan, da yawan ayyuka, da yakeyi babu hutu.'

Yad'an sami sauk'i babu laifi, abokan shi sun zo dubiya, ranar ne ma yaji ya k'ara warwarewa.'

Duk kwanakin nan kusan hud'u sam bai kira Hafsah ba, a ganinshi, gwara ya bari sai ya sami sauk'i sannan ya kirata, duk da cewa yasha kewarta sosai da sosai.'

__________________

Itama nata b'angaren tayi mamaki sosai, tunane-tunane dayawa sunzo, cikin ranta ciki kuwa har da fargabar "Shin mai ya jawo shirun nashi haka.."?

Amma cikin k'arfin hali irin nata take ta kokawar, kawar da tunanin, ita ala tilas, bata son ace, abinda takeji game dashi _'Kewar shi ce.'_

Ganin an d'ebi kwanaki haka, yasa har ta fara wani tunani, 'wai ko ta gwada kiranshi ne."?

Nan da nan tayi saurin kawar da wannan tunanin, _yaushe suka dad'e..? Yaushe sukayi sabon da har zata damu haka."?_ Sai taji takaicin hakan ma.

Ak'ok'arin tayi watsi da tunanin nashi ne, yasa ta d`akko wayarta, ta kunna Data, facebook ta fara dubawa inda taci karo da wani abin mamaki... Sunan Yusuf ta gani wai ya turo mata _'friend request.'_

Taji abin wani iri, meye hadin biri da gada kuma."? Kodai bai san ita bace? Kai ya sani.. Yasan sunanta sarai, kamar tayi delete d'in request d'in sai kuma ta fasa, ta fita daga facebook din gaba-d'aya ma.

Bata wani dami ranta da tunanin shi ba, saboda bata da wani damuwa akanshi sam, ta dai san yanzu baya k'asar, don labari baya b'uya, har labarin Basma tana dashi, duk da cewa ba bibiyar rayuwar su take yi ba, amma hakan baya rasa nasaba da yadda har yanzu suna tare da wasu daga cikin 'yan makarantar su ana zumunci.'

Aisha Daheer tayi aure wata biyar kenan da bikin, dama yawancin zantuka a wajenta Hafsah keji.

Duk da ba d'auka take yi ba, takan watsar da zancen ne a inda tajishi, domin ita a yanzu ta kama wani layi daban na rayuwar ta, _kowa tasa ta fishsheshi._

bata da wani abin buk'ata daga garesu ( _Yusuf da b

Basma_ ) dukansu...

__________________

"Hello.!!

Hello, Barkanka da yamma 

Barka dai

" I hope you're fine naji kwana biyu baka picking call."

Ya d'anyi ajiyar zuciya, wato ita dai bata tab'a watsar dashi, duk da yanzu ta k'arfi da yaji ya canja mata ra,ayi akanshi, amma har yanzu sabon nan nata na kiranshi yana nan har yanzu.

"Hmm, Bahijja kenan, bana jin dad'i ne kwana biyu."

"Subhanallah meya sameka.?

"Ciwon kai nake fama dashi amma naji sauk'i sosai ma."

Ta d'anyi ajiyar zuciya ahankali, 

"Allah ya k'ara lafiya sannu fa."

"Yawwa thank you."

Suka d'anyi shiru, can tace, "ko inzo dubiya ne."?

"No naji sauki fa nagode ba sai kin zo ba."

"Hmm, kai dai kawai baka son nazo ne."

"No ba haka bane."

"Hmm, tayi murmushi kawai."

"Okey shikenan Allah ya k'ara sauk'i."

"Amiin k'anwata."

Ita abin ma dariya ya bata duk da gefe guda tana tausayawa kanta, amma sai taji tayi dariya kawai, ya ta iya da kaddara."?

Shima dariyar ta danji yayi, 

"Sai anjimanka."

"Okey thank you."

Kiran nashi da tayi, ya k'ara sashi jin kewar Hafsah, sosai, ya kalli agogo, yanzu ne daidai lokacin da takeyin program d'innan a television, ya mik'e a hankali ya nufi falon Hajiya, cikin d'an mamaki Hajiya ta kalleshi, ya nemi guri ya zauna, sai dai abin taikaici ba tashar suke kallo ba, ya dai daure ya zauna, har zaman ya gundure shi, ya tashi kawai zai fita sai kuma yaga Hajiyar ta dauki remote ta canja tashar zuwa can d'in.

Sai kawai ya dawo ya zauna, nan ma Hajiya ta bishi da kallo kawai.

"Ya jikin naka?"

"Da sauk'i."

Kasha maganin yau."?

Idon shi kan TV yace "Eh Hajiya." 

Allah ya k'ara sauki."

"Amiin."

Ba,a fi minti 15 ba, aka gama shirin, yaji dad'in kallon aranshi sai yaji an sauke mishi wani nauyi daga kanshi.

Ya dan zauna kad'an, sannan ya mik'e ya wuce d'akinshi.

'Sai dare sannan yayi tunanin kiranta.'

Tana falo ita da kowa na gidan kiran nashi ya shigo, mufida ce ta miko mata wayar, ta kalli sunan daya bayyana, sai taji sanyi aranta, gefe kuma ya haddasa mata fad'uwar gaba, ko meye dalili oho.

Tana jin kunyar a kirata ta mike tabar su a parlour ta wuce d'aki, ciki kuwa ga abbansu da Mama, amma tasan ita da kanta tafi samun nutsuwa, idan ta keb'e tana waya, ko da wanene takeyin wayar kuwa.

Ganin wayar zata tsinke ne, yasa ta d'aga tare da mik'ewa tayi hanyar bed room d'inta.



📝 

*HAJEEYAH*

*KHAREEMERH.*



♥️♥️♥️♥️

*ZAZZAFAN SO*

(masoyin k'warai)

*Cigaban littafin Zazzafan so*

*(Guba ne)*

💔💔

*By:*

*Karima Tijjani Mansur*

*(Hajeeyah khareemerh )*

*Dedicated to Unique in your love heart group members.*




📄 *50*








*"Hello"*

Taji yace.

"Hello"

Ta mayar mishi.

Ta taka da sauri tashige bedroom din ta zauna gefen gado.

"Kina lpia."?

Lpia lau,

Kwana biyu kinjini shiru koh.."?

Bata san amsar da zata bashi ba don haka tayi shiru.

"Uhum."?

Yace da ita.

"Um."

Tace dashi.

"Hhum"

Yayi ajiyar zuciya, ya kwantar da murya.

"Hafsah."

Taji kiran ya ratsata, amma sai bata amsa ba.

Shima badon ta amsa din ya kirata ba don haka yacigaba da magana bayan d'an shiru da yayi, cikin nutsuwar murya yace,

"Baki nemeni ba kuma koh."?

Sai taji 'yar kunya, har ta fara k'ok'arin kama kanta da laifi.

"Um um."

Tace mishi, 

"Hmm yayi murmushi mai sauti, 

"Um um kikace."?

Sai tayi saurin kama kanta, kada fa yaga zak'ewarta.

Ya cigaba da cewa, "Bani da lafiya ne!"

Sai taji gabanta ya fad'i.

Takuma jiyo shi yana maimaita,

"Rashin lafiya nayi Hafsah, wajen _5days_ ina ciwonkai."

"Ya salam." Taji bakinta ya furta ahankali.

"Sannu"

Cikin murmushi yace, "Yawwa naji sauk'i alhamdulillah."

"Allah ya k'ara sauki."

"Amiin"

Yace cike da jindad'in yadda ta nuna kulawa.'

Ya danyi shiru sannan yace,

"Ai na ganki kina program d'inki a TV."

Murmushi kawai tayi.'

"Bani da lafiya amma sai da na fito na kalla."

Ta k'ara yin murmushin daya ji dad'inshi sosai cikin kunnuwanshi, har ya furta babu shiri.

"I Miss you!

Jin kalmar tayi bazato, ahankali ta sauke ajiyar zuciya, tare da zamewa ta kwanta.

"Kinji,"?

Yace da ita.

"Uhum"?

Tace, cike da jin nauyin shi.

"Hmm, cewa nayi "I miss you, I miss ur voice.!!

Lumshe idanunta tayi, sannan ahankali ta bud'e, daidai lokacin da yakecewa, 

"Kinji me nace yanzu."

"Um."

Tace, 

"Okey thank you."

yace.'

Ta rasa dalilin godiyar amma taji d'ad'inshi da zata ce mishi, ~_"For what."?_~

Sai kuma tayi shiru.'

"Ina son inzo wajenki, idan zan samu."

Sai taji gabanta ya fad'i.

Na sami sauk'i, naji kawai inason zuwa inganki, kinga da na mutu a rashin lafiyar nan shikenan koh.?

Shiru taji kawai, ta daiji jikinta ya d'anyi sanyi.

"Idan zaki bani dama _Friday_ nazo."?

Tayi shiru tana tuno yaushene ma _Friday_ d'in.

"Uhum"? "ko baki shirya ganina ba."?

Tayi shiru.

Okey ki bani lokaci, duk sanda kika shirya kinji."

"Okey tace mishi."

"Kada na dameki koh."?

"Goodnight!!

"Bye bye."

Tace.

"Okey..

Ya kashe wayar yayin da itama ta janye wayar daga kunne.

Bata motsa daga inda take ba har zuwa mintuna, tana mamakin yadda take jinta kamar bata tab'a waya da namiji ba, idan tana waya dashi, meyasa haka oho."?

Mamakin yanayin da take shiga take, da kuma yadda take, amsa wayarshi da irin biye mishin da takeyi..






*'WANI B'ANGAREN'*

_________________________

'Tana kwance, shiru ita kad'ai tayi tagumi fuskarta cike da damuwa fal sam bata son ta ina zata fara ba, amma dole ne ta samarwa kanta mafita tunda bata da ishashshen lokaci.'

'Ta janyo wayarta, ta danno number shi, ta samu da 

kyar ta shiga.

'Wayar tayi ta ringing amma ba,a d'aga ba, har ta gaji ta hak'ura, sai kuma ta tuna cewa lokaci yana k'ure mata.'

'Don haka ta shiga Email ta fara tura mishi sak'o..'

"I called you but u didn't picked my call.. WHY?? 

Please ka kirani sai muyi magana."

'Bayan ta aika ne bbu jimawa kuma yai mata reply da "Okey" kawai.

'Tayi ta jiran kiran nashi amma babu kiran.'

'Abinda bata sani ba shine, shi yanzu gaba-d'aya ba ta ita yake ba sam, don shi ya gama yayinta.'

'Sai can dare kiran nashi ya shigo, da sauri ta d'aga.

"Hello 

"Hi 

"How are you 

"Am fine, um naga kin kin min Email mene ya faru ne."

'Hum tayi ajiyar zuciya.' sannan ta marairaice ta fara magana.'

"Akwai damuwa ne fah. Yesterday, Dad ya kira ni, yace min in fito da wanda nake so amana aure.. If not kuma yace akwai wanda ya mishi magana so zai bashi dama kawai."

"Tunda ta fara yake sauraronta har tazo nan sannan yace, 

"To yanzu what's solution."?

Cikin takaici tace,

"Hmm you already knew that ba zan iya auren wani ba idan ba kaiba koh.."?

"What.. what are you saying..??

'Wutar kanta ta d'auke ta tsaya cak, au tambayarta yake me take fad'a ma."?

Sai kuma taga asarar ta k'yaleshi don haka tayi k'arfin halin cewa, "Yusuf nasan kaji me nake fad'a maka, amma kake nunamin baka ji ba koh."?

"Hmm.. Yai wani murmushin rainin hankali.. "naji mana... kuma aini murna ma zan miki zakiyi aure koh."?

"Hum, Okey haka kace koh."?

"Hmm, so ya kike so nace en mata."?

"Hmm, thanks 

thank you very much."

'Ta fad'a cike da rashin sanin matakin d'auka.'

"Okay, yace kawai sannan ya katse wayar.'

"Ta saki wayar ta fad'i k'asa, ta dafe kanta da hannu biyu, bata da wani abinyi sam..

'Kogin tunani ta fad'a akan yadda rayuwarsu ta baya ta kasance..'

'Idan ta k'irga zata ga a daddafe tayi shekara d'aya da rabi rabon da taga Yusuf ido da ido.'

'Ta sani, asanda ta mallaki Yusuf ta mallakeshi sosai har tsahon shekaru kusan uku ta shimfida mulki a rayuwarshi tayi sa,ar rabashi da wasu abubuwa muhimmai cikin rayuwarshi misali "HAFSAH."




Tun a wancan lokacin ta tabbatar wa da kanta cewa, "Lallai soyayyar da Yusuf ke yiwa Hafsah, ta gaskiya ce, domin sunsha fad'a akan ambaton Hafsah da Yusuf ke yawanyi tare da zargin kansa akan _'Ya ci Amanarta'_

Yusuf ya kashe mata kud'ad'e da ita kanta bata isa ta kirga su ba, sun shimfida rayuwa mara dad'in bada tarihi.. Don tun tana abubuwan ta ab'oye har takai mamanta ta sani, lokacin hankalin maman ya tashi, amma ta gaza iya yin komai don ta bari sai da abin yafi k'arfinta.'

'Alokacin ta yanke shawarar maida Basman wajen mahaifinta, wanda mamakin hakan ya sashi shakkar karb'arta.

'Da kyar ya yarda ta koma gidan nashi, ya kuma saka ido sosai akanta, ahankali ya fara gano cewa tabbas tarbiyyar 'yartashi ta dade da rugujewa.'

Sanda Allah ya dubeshi sai akayi sa,ar barin Yusuf K'asar gaba-d'aya ya sami aiki.'

Lokacin neh Abban Basma yaga tab'ara kala-kala, wato Basma ta sha auna tserewa daga gida a nufinta na sai tabi Yusuf duk inda zai tafi, akan wani alk'awarin k'arya da Yusuf d'in yayi mata wato zai aure ta acan k'asar da zai koma.'

Lokacin tana level 200, a makaranta

Bayan tafiyar Yusuf d'inne, lokacin Basma ta fara ganin sauyi daga gareshi, sannan ta fara fahimtar cewa lallai sahun giwa ne ya fara take na rakumi, _wato yaje can ya had'u da dai-dai shi.'_

Lokacin kuma ta fara fuskantar rashin kulawa daga gareshi har takai sai su shafe sati bai waiwayeta ba.'

'Ayanzun ma da ta nemeshin, sun shafe fiye da wata d'aya, basuyi magana ba koda a waya kuwa.'

'Ta sani bata da wani tsayayye, wanda zata iya kawo mishi zancen ya aureta, duk tarin samarin nata irin kalar Yusuf d'inne wadanda suka maye mata gurbin shi bayan tafiyarshi.'

'Nour' shine Abba ke son had'ata dashi, duk da bai kamata ta kira hakan amatsayin 'Auren had'i' ba, domin Abba ba d'akko shi yayi yace zai bashi ba, ganinshi yayi a wajenta kuma dake ya gaji da irin take- taken ta sai yai mishi izinin ya turo iyayenshi kawai, kuma akayi dacen shima hakan ne manufarshi.'

'Bashi da wata makusa, d'an manyan mutanene, shekarunshi ba zasu wuce 30, ba, bai wani girmi Basma sosai ba, amma yana da nutsuwa sosai.'

'Basma ta ja tsaki, sanda ta tuno shi, wai ita ake shirin yiwa aure ba tare da son ranta ba.'

'Ta rarumi wayarta ta danna kiran wata k'awarta.'

"Hello Basma."

"Teemah, babu lafiya fa."

"Meya faru kuma."

"Kinga na kira Yusuf yaki ma ya saurareni yadda ya dace bare muyi magana."

"Kinsan me zan fad'a miki k'awata."?

"Ina jinki."

"Wallahi mu,amalarku tayi k'arko keda Yusuf."

"Bangane me kike nufi ba."

"Hmm, ina nufin yadda kuka dad'e tare keda shi, kema kin sani samarin yanzu ba amana ce dasu ba, bare shi da yanzu ma bakwa kusa keda shi."

"Hmm, Teemah, ahakan kike fad'ar haka."?..kin san rabona da Yusuf kusan 2years kenan."?

Koma yayane nidai ina fad'a miki kun dad'e keda Yusuf, kuma ni yanzu shawaran da zan baki shine kawai ki yarda kiyi aurenki don banajin Yusuf zai aureki.!!

"Ke Teemah, bana son wulak'anci, ai ke auren kikayi da kike cewa inyi aure kuma a rainin hankalinki zaki ce in auri wani ba Yusuf ba."??

"Hmm, ni dai gaskiya na fad'a miki, kuma ni ko ayanzu na sami wanda yazo yacemin yana sona da aure, wallahi auren shi zanyi kindai san babu yadda za,ayi kuyi irin rayuwar da kuke da Yusuf sannan kuma yace zai aureki.!!

"Kada ki fad'a min maganar banza, har ni zaki zaga, kice muna rayuwar banza, kema ba irin ta kikeyi ba."?

"Hmm, Basma ni ba cemiki nayi ba ita nakeyi ba, amma kinsan ni bankaiki ba don, ban watsar da mutunci na atiti ba, _kefa dakanki kika fad'amin kin bawa Yusuf komai saboda haka kisan da sani Yusuf ba zai aureki ba zaki ce na fad'a miki.."_

"Ta katse wayar, tabar, Basma na zage-zage tana fad'in k'aryane bazai yiwu ba."

Daga bisani ta mik'e ta nufi, d'akin abbanta, fuskarta babu annuri don amsa kiran da yayi mata.

Tayi sallama a ciki-ciki sannan ta shige ciki.

Yana zaune, akan kujera, yana kallon TV, ta nemi guri ta zauna.



Cikin nutsuwa ya juyo ya kalleta, ta k'ara tamke fuska.

"Basma, ya muke ciki a maganar mu."?

Ta keb'e fuska kamar zatayi kuka, batace komai ba sai kallonshi da takeyi.

"Tambayarki nake don kada na yanke hukunci ki ga anyi miki ba daidai ba."

Bataga alamun wasa a tattare dashi ba don haka ta shiga hankalin ta kada ta tsaya wasa tayi wa kanta.

Ta bude baki ta fara magana, cikin shagwab'a.

"Abba fa munyi magana da Yusuf d`in yace zai zo k'asar nan nan da wata d'aya.

"Wata d'aya."?

"Eh Daddy"

"Hmm Basma ki shiga hankalinki dani, ba maganar wasa nake miki ba, kuma bazan tab'a zaman jira sai wata d'aya yayi zan yanke hukunci ba."

Ta d'ago da sauri ta kalleshi, cikin damuwa, "Allah abba da gaske zai zo."

Cikin fad'a ya fara mata magana,

"Wai ma waye Yusuf d'innan da kike ta fad'arsa, kullum daga anyi magana sai ki kawo zancen wanda baya nan, waye ubansa, ki fad'amin ni naje na same shi."




Gabanta yayi wata muguwar Fad'uwa,

"Ta d'ago ta kalleshi.

"Eh, na gaji da wasa da hankalin da kike min, idan ma k'arya kike babu wani Yusuf ai zan sani ne."

Kawai yaro, yazo da magana amma kina sani ina ta magana biyu, to baki isa ba, kuma kada na sake ganin kin fita daga gidan nan bada sani na ba."

Na baki sati daya idan banga Yusuf a gidannan ba, to dole ki karbi, zabina, shashashar banza kinfi gane kiyi ta gantali ko."?

Hankalinta tashe ta nufi d'akinta, sam ta rasa sanin abinyi, gashi wai har wata dokar hana fita aka sa mata wanda tabbas tasan ba zai yiwu ba.

Kamar an tsikareta ta fizgo wayarta babu shiri, ta danna kiran mamanta, tana d'agawa Basma ta fara kuka, cikin tashin hankali take tambayarta "Lafiya meya faru."?

"Ba kece kika kama kin dawo dani gidannan sai wulak'anta suke gashi sun zuga abba wai aure zaiyi min.!!

Duk da tasan za,a runa, amma maganar ta shigeta da taji cewa, ba zab'in 'yar tata za,a bata ba.'

"Aure, kuma..??

Tab to wa zai aura miki."?

Wani ne daga yazo gurina ya ganshi shine yace ya turo iyayenshi."

"Okay ki kwantar da hankalinki zamuyi maganar da shi bazata yiwu ba."

Ta danji sanyi aranta don haka tace "To Mama."

Maman ta d'ora da cewa, "Wato hajiya Salman ce ke zuga shi ko."? Shikenan dani take zancen, dama ke kika jawo wa kanki ai, badon haka ba me zai kaiki gidannan da zama, I hope bata takura miki ita da samarin 'ya'yan nan nata."?

Basma tasan Indai gaskiya zata bi hajiya Salma a 'ya ta d'auketa, yayyenta maza su uku ne biyu, sunyi aure sai kuma mace guda d'aya "Aunty Meenat."

Sai Basman wacce uwarta ita kad'ai mamanta ta haifa sannan ta fita, sai na'imah sai autar hajiya Salma wato Nuratu.'

"A,a ni bana ma shiga harkarsu, yaya Abdul ne yake samin ido komai nayi sai yayi magana."

"Tab bazai yiwu ba, dole zan mishi magana babu wanda ya isa ya takura miki gida, gidan ubanki ne kema."

"Thank you mum."

Kuma ki maida hankali akan karatun ki, yawon nan da kike yi idan ma baki daina ba gaki ga Dad din naki nan ai."




________________

Yau ne rana ta farko da ya fara yi mata magana a chat. Ya mata sallama da wata number, ta amsar sallamar tare da cewa "wa yake mgna."?

"Hmm yace, tare da tura mata murmushi.

"Okey you don't chat with strangers ko?

"Hmm" tace mishi kawai."

Ta duba user name dinshi _UK_ kawai taga an rubuta.

"Kina magana da ukhasha "

Rasa reaction d'in da zatayi tayi, bata da wannan number d`in, shi kuma yaga ta gani kuma yana jiran amsarta.

"Ok you're welcome!

Tayi saurin lalubo abin cewa.

"Thank you yace mata."

"Ya kike ya gida"?

"Lpia lau"

"Ya ayyuka naki ya fans"?

Sai ya dan bata dariya tayi murmushi.

"Hmm suna lpia."

"Masha Allah.

"Hafsah.!

"Yes."

"Please ina son inzo wajenki Allah.!

"Taji gabanta ya fad'i."

"Hmm tace don ta rasa abin ce mishi."

Plz nasn kina da uzuri.. Amma ki taimaka min da Friday."

"Friday? 

Ta tambaya 

"Yes plz."

"Ina son had'uwar mu dake"

Hmm Okey diz coming Friday?

Eh ina da lkc sosai ranar kene dai bansaniba ko kina dashi.

"Okay zan duba."

"Oh my God yaushe? 

"Soon!

"Plz help mee!!

"Hah, tace.

"Hmm da gske ina son ganinki.

"Koo ?

"Allah.

Okay Gud."

"Plz wallahi n damu dake fiye da tunani."

Okay thank u.

"Kin yanke shawarar."?

"No, Ina duba free time ne."

"Hafsah manya a taimaka dai."

Okay 

"Sai dai sat day. 

"Oh!

"What?

"Nthng en mata, nagode zan katse uzuri na domin ke!

"Hmm..

"Yes kin isa ai"Ngode hakan ma.

"Amma plz ki brni nazo da yamma kinji"?

Yamma.."?

"Eh plz.

Why.."?

Shine nke da time kuma inason ki ganni sosai.

"Hmm!

"Am sorry plz!!

"For..?

"Da nace _ki ganni,_ bansaniba ko bkya buk'atar hkan."

"Hmm, 

"Yes but ni ina so."

"Kna so me? 

"Inganki mana Hafsah en mata."

Ya dan b'ata kunyar kalmar.

"Hmm" 

okey bye.

"Kin gaji ne ko?

"Bacci znyi.

"Ok ki huta have nice sleep!

"Thank u!

"My Dear Hafsah!

Gud Night!!

'Ta kashe Data ta tayi shirin bacci da tunanin hirarsu ko ba komai ya d'ebe mata kewa, ta rufe idanunta tana tunanin ya had'uwar tasu zata kasance."?




📝 

*HAJEEYA*

*KHAREEMERH*



♥️♥️♥️♥️

*ZAZZAFAN SO*

(masoyin k'warai)

*Cigaban littafin Zazzafan so*

*(Guba ne)*

  💔💔


*By:*

*Karima Tijjani Mansur*

*(Hajeeyah khareemerh )*

*Dedicated to Unique in your love heart group members.*






📄 *51*





*Tana* kwance take tuno abubuwan da suke faruwa. 

Wato tun bayan wayar da sukayi da mamanta har take ce mata zata yiwa Abban nata magana. To maman ta sameshi amma kuma had'uwar tasu ba tayi dad'i ba.


 Gashi saura kwana kad'an lokacin da daddynta ya d'ibar mata su cika..



Wato da daddare maman tata, tazo gidan, dake ba wani gaisuwar arziki suke yi da matar gidan ba, sai ta wuce d'akin 'yar tata kai tsaye ta zauna.


Basman na kwance tana danna wayar ta maman ta shigo, ta mike tare da rungume ta cikin farin ciki. sukayi murmushi, mama you're welcome, 

 Basma tace, cikin jin murna, sannan ta sake ta. 


"Yawwa baby na ya kike."? Ta fada yayin da ta nemi guri ta zauna. Sannan ta fara kallon ko ina na dak'in, an tsara d'akin sosai yadda har ta gama kallon k'urillah d'in ta bata gano abin yin k'orafi ba.


Basma ce tayi mata magana.

Mama menene"?

Tayi murmushi babu komai, ya ake ciki."?


Basma ta shagwab'e murya kamar zatayi kuka.

mama, wallahi Daddy yace bazai chanja ra,ayinshi ba, yace min wai one week ya bani.

Sai ta k'arashen zancen da kuka.


Maman tata ta rungumo ta tana rarrashi.

"Sorry my Baby kiyi hak'uri na fad'a miki ki daina damuwa kinji babu wanda zai miki abinda bakya so."


Mama baki ga yadda Abba yake ba wallahi bana tunanin zai chanja.


Basma, ki k'yale komai a hannuna nace ki daina damuwa kinji, tashi ma kije ki fad'a mishi nazo."



Ta mike ta fita, bata jin zuwan maman nata zai yi amfani, yadda Abban nata ya kafe akan lamarin.


"Abba Mama tazo."

Afusace yace, "Tana ina."?

"Tana room d'ina."

"Okey ina jiranta."

Ya mayar da hankalinshi kan abinda yake.



Cikin takun k'asaita ta iso cikin falon nashi, ta nemi wajen da yai mata ta zauna.


"Ina yini."?

Tace dashi fuska babu walwala sai shan kamshi take.



Ya zuba mata ido, har yanzu, tana burgeshi sai dai bazai iya sake zama da ita ba, saboda halayenta, sam bata son zaman lafiya, shi kam bashi da burin raba matanshi.


"Lafiya lau"

"Ya amsa."



Ta shak'i iska sannan ta fara magana.


"Basma ce tazo min da wani bahagon zancen da nake tunanin k'aryarta ce ta shirya."


"Ya d'an tsare gida sannan yace, wanne zance fa."?

 


"Am naji tace wai kace ta fito da mijin aure."


Ya jingina mata kai.

"Eh hka nace kuma sati d'aya na bata."


"Hmm, akan wanne dalili ne yasa hakan.. yarinyar nawa take to ina ma mijin da zata fito dashi."?


Ya kafe ta da ido.

"Dalili kike tambaya ko."?

To ra,ayi nayi nayin hakan.!! Sannan kince yarinyar nawa take, to bata kai ayi mata aure ba amma take gantalin da kika gaji dashi ko."?

Mijin da kike tambaya kuma ki tambayeta ita."


Ya kake neman ka dinga fad'a min magana ne ehe."?

Su sauran yaran naka aure kayi musu."?


"Ita naga dacewar inyiwa."


_Dai dai lokacin Hajiya Salma ta kawo kai cikin d'akin, sam bata san da zuwan Maman Basman ba sai jiyo muryarta tayi tana cewa,_ "Saboda ka kaji da zama da ita ko, an zuga ka yarinya a gidan ubanta amma kamar yar rik'o, shekara nawa Meenat ta bata amma ita bakace ta isheka ba sai ita ko."?


Tana rufe baki ya mayar mata, "Kamar yadda kema ta isheki ba..."



Hajiya Salma tayi sallama ta iso cikin shiga ta alfarma, tasha kwalliya ga sarka da awarwaraye a hannanyenta.


Ta nemi guri kusa da mijinta ta zauna batayi wa maman Basma magana ba saboda, bata son abinda zai had'asu har ta kaisu ga ce-ce ku-ce.


Hajiya Halima (Maman Basma) ta watso mata wani kallo sannan ta tab'e baki.

Ta kalli alhaji Yunus.

"Idan ina tattauna game da 'yata bana buk'atar wani yaji bare ya tsomo min baki."


Yayi murmushin mai sauti, "Halima kenan."

"Waye bare anan."?

Ta tab'e baki sannan tace "Kafini sanin koma waye."? 


Ita dai hajiya Salma bata tanka ba, ko kallon ta ma batayi ba, tana so ta nuna mata cewa bata isheta kallo bama bare ta sami damar yi mata rashin kunya."


Halima, Abu d'aya zangaya miki shine, "Wallahi Billahi bazan sauya akan hukuncin dana yanke ba, dole k'arshen watan nan Basma tana da ranar ta aka, in sha Allah."

"Tabd'i jan wai alhaji meye haka ne ina mutumin da zata aura yake d'in an fad'a maka yaron baya k'asarnan a,a..? kada fa ka jawo abinda bazai wa kowa dad'i ba ni da kai."



"Hm, Halima! bana son maimaita magana kije ki tuntub'eta ai ita ta sani muddin banga yaron da kuke min wak'ar akwaishi ba cikin satinnan to wallahi babu d'agin k'afa."


"tabd'ijan, lallai ma Alhaji Yunus!!" 


Abinda ya fito daga bakin ta kenan.

Domin tama rasa me zatace mishi, ga haushin tunda Hajiya Salma ta zauna bata kulata ba, taso tayi mata magana taga tsan tsar rashin mutunci.


"Kinji dai abinda nace."

"Ya k'ara maimaita mata."

"Hmm k'al"

"Tayi k'wafa.

"Ya bita da wani kallo kawai."



Sai kuma ta juya kan Hajiya Salma,

 "Kada ki d'auka kinyi nasara ne, don munafirci kinzo kin zauna kina kallo na."


Hajiya Salma ta bi ta da wani murmushin _"Kiji da abinda ke damunki."_


Alhajin ne ya d'aga mata hannu tare da cewa, "Halima zancen mu ya tsaya iya mu bana son kina sako Salma ciki."

"Hmmm"

Tace kawai, don tasan tunda ya tanka, zai iya yarfa ta agaban matar shi.


"Idan baki da abincewa zaki iya tafiya.


Ta watsa mishi wani kallo sannan ta gyara zama, _alamar bata da niyyar tafiya._


Abin ya bashi dariya  ma.


Sai ya mik'e k'afarshi yana jijjigawa.




Sunfi mintuna biyar cikin shiru sai k'arar AC dake falon.


Sannan akaji sautin kwafar, Hajiya  Halima, "K'al"


Sannan ta mike ta fice fuu kamar wucewar iska.



Sai bayan ta fita alhaji ya kalli Hajiya Salma, ya girgiza kai, "Kiyi hakuri fa kinsan ta sai ahankali."


Tayi murmushi, "Haba alhaji meye abin hak'uri kuma."?

Yai ajiyar zuciya,

 "Halima sai ahankali, tana d'aukar zance na wasa.."


Ya d'an tsaya, sannan ya d'ora.

"Hmm, mu zuba ni da ita."!!

Ta kwantar da murya, "Don Allah alhaji kabi komai a hankali dai."

Ya kalle ta da kyau, "Kin fini sanin halin da yarinyar take ciki dai."

 

"Nasani amma, ayi komai ba tare da b'acin ran kowa ba ai yafi ko."?


"Haka ne Nagode, amma aure babu fashi."

 Hajiya tayi dariya kawai.

"Allah ya zab'a na gari." tace dashi.

"Amiin". Ya amsa.


Sannan ta mike don kawo mishi abinci, bata son su tsawaita zance akan maganar, don babu ruwanta cikin lamarin.



Hajiya Halima na fita, d'akin Basma ta nufa a fusace, ta tarar Basman na kwance. 

Ta d'a ka mata duka.

"Tashi maza kwanciya bai sameki ba."



Zumbur, ta mike a razane "Mama, me yace."? 


"Hmm" tace, mai makon ta bata amsa sai ta hau tambayarta.


"Ina Yusuf yake yanzu."?

"Baya nan Mama." 

"Dole ki nemo shi."

"Basma ta zaro ido."?

"Tayaya Mama."?


"Ubanki yace aure babu fashi matukar ya wuce satinnan bai ga Yusuf ba kinga ya rage ruwanki."

Basma ta rushe da kuka, "Mama bansan ya zanyi ba munyi waya dashi baki ga wulakancin daya min ba, bashi da niyyar aure yanzu."


"Bansan ya zan miki ba Basma, ke ya dace ki tashi ki kwatar wa kanki hak'k'i kodai a wajen Yusuf ko kuma a wajen mahaifinki,  ya rage naki don babu yanda zanyi da Alhaji, sai dai idan naga abin ya wuce gona da iri kotu zan kaishi"!!


Basma ta waro ido cikin tsoro, "Kotu kuma. Gidan tonon asiri, kamar ita akace iyayenta na kotu akanta ai an gama yayatata a duniya.


"Mama, ya zanyi yanzu."?? Ta fad'a cikin kuka.


"Kiyi hakuri, baki da lokacin kuka yanzu, dole ki san abinyi."


Ta matso kusa da ita, cikin rarrashi take ce mata, "Kiyi hak'uri kinji baby na,  kiyi dabarar da zakiyi Yusuf yazo k'asar nan kinji."??


Basma ta d'aga kai alamar toh."

Yawwa 'yata nasan kina da wayo ai ko."?


Sai lokacin Basma tayi murmushi jin dad'i duk da dai tasan akwai aiki a gabanta, amma ta d'anji sanyi cikin ranta.


"Mama ta mik'e bari in tafi zanyi bak'i."

Ina fatan dai baki da matsala da waccen matar."


Basma ta girgiza kai, "No mama sai dai ta isheni da wa,azi."


"Hahh, hajiya Halima ta sheke da dariya, _"Makira Salma kenan.!"_

Ta nuna, Basma da yatsa alamar gargad'i.

"Kada dai ta baki wani abin kisha."

Basma ta d'aga kai alamar, "Toh"

"Tashi ki raka ni kinji."

Basma ta goge fuskarta suka fito.


Suna tafiya, Hajiya Halima, na k'ara tsara mata yadda za,tayi."


"Ki shawara da Teemah take kowa, K'awar nan taki."

"To Mama." 

Yawwa sai kace ba Basma na ba kina 'yar zamani juya namiji ya gagareki."?

Basma tayi murmushi an fasa mata kai.


Har bakin motar mama ta raka maman, sannan ta shige tana d'aga mata hannu.

"Taja ta ta tafi."




Basma ta dawo gida, ta dad'e cikin shiru domin nemar wa kanta mafita, amma ta rasa.


Tana kwance wayarta tayi k'ara, kirane ya shigo ta duba da sauri, lokaci guda taja tsaki har kiran ya katse.

Yana katsewa wani kiran ya k'ara shigowa cike takaici ta danna _Dismiss,_ tayi _rejecting_ kiran.



"Aikin banza aikin hofi.!!

Ta fad'a.


Basma bata so abinda Teemah tayi mata ba kuma tayi, mamaki da tak`i bata shawara, sai goyon bayan hukuncin abba da take, kuma tana karanta mata ta kyale Yusuf, don haka taji bazata k'ara yi mata zancen ba.

Nan ta shiga tunani, sai ta tuno da wata k'awarta "Hala." 


Wacce bayan dawowarta gidan abbah ne duk gayyar tasu ta watse suka daina had'uwa a gida sai dai duk sanda Basma ta sami dama ta lek'a club to suna had'uwa."



Nan da nan ta rarumi wayarta, zata kira Hala, sai taci karo da text akan wayar tata.


_"Problem"!_

Shine sunan Nour awayar tata.


Ta danna don taga abinda ya rubuto mata.


*Basma abinda kke min bai dace ba, ki tsaya mu fahimci juna don Allah..*

*I luv u..*


"Mts, taja tsaki.

Sannan ta nemo number Hala ta doka kira.


Tana d'agawa tace,

"Basma jama,ar Duniya kina nan kuwa.!!


Cikin damuwa tace, "Yes Hala, ai ni abu ne ke neman kwab'e mini."


"Wanne abu kuma, ke da naga kwanaki kinyi Babban kamu?."


Basma ta d'anyi yak'e, "wanne irin Babban kamu"."?


Gayen da kuka had'u recently mana."

 "Hmm, Inji Basma sannan tace, Akwai matsala k'awata.

"Wacce irin matsala kuma."?

Hala ta tare ta da mamaki.

"Ba zaki gane ba but please gobe idan zaki sami dama kizo please da akwai magana."


"Zan sami time kuwa Basma."? 


"Please k'awata wallahi akwai _big problem ne ina cikin damuwa fah."_


Basma ta fad'a cikin raunin murya.


Hala tace,

Basma zuwa gidanku yanzu _is not easy_ kin sani kema _your brother_ d'innan Abdul yake ko wa,? bana son kallon rainin da yake min."


" _Sorry_ Hala ba zaku had'u ba ma."


"Okey to zanzo, but ki fad'amin abinda ke faruwa mana."?


_"I can't,_ duk a rud'e nake, abin bazai fad'u a waya ba fa."

Hala tayi ajiyar zuciya, "Okey zaki ganni toh."

"Thank you my friend."

"Byee"

Sukayi sallama...






   📝 

*HAJEEYAH KHAREEMERH*



♥️♥️♥️♥️

*ZAZZAFAN SO*

(Masoyin k'warai)

*Cigaban littafin Zazzafan so (Guba ne)*

💔💔


 *By*

*Karima Tijjani Mansur*

*(Hajeeyah Khareemerh)*

*Dedicated to unique in your love heart* 






📄  *52*




*Washe garin* tunda wuri Hala ta iso gidan su Basma, kai tsaye ta wuce sashin da d'akin Basman yake, babu ruwanta da duk wanda taci karo da shi bare su gaisa.



Sanye take cikin riga da skirt na atamfa, sai wani bak'in glass a fuskar ta, sai jaka a hannunta, kana ganinta ka ga yarinya 'yar hutu.




_Sun had'u da Basma ne wajen partyn wani abokin Basman, sun zauna sit d'aya a wajen, bayan sun gama shawa juna k'amshi sai kuma suka jone, ta dalilin wani da yazo wajen Basma ta yarfa shi. Hakan ya burge Hala, don tana son mace da aji (class.)_ Daga nan ta bud'i baki, _"Kin burgeni k'awata."_

Suka tafa ita da Basma.

"Allah kuwa bana son rainin hankali wasu mazan akwai tsaurin ido fa yasan ke fa ba _type_ d'inshi bace."

Suka sheke da dariya har da k'ara tafawa.

_To daga nan abotarsu ta fara, sai kuma akayi dacen halinsu yazo d'aya._

_Shekaru biyu kenan da had'uwar su tun  Yusuf bai bar k'asar ba, yana saura k'iris ya tafi. Don haka bai san Hala sosai ba._



Cikin yauk'i Haala ta shigo falon da Basma take.


Ta nemi guri ta zauna, tana k'arewa ko ina  kallo.


Basma ta fito jin alamun an shigo, kana kallon ta zaka karanci damuwa cikin fuskarta.


Tana ganin Haala tazo da gudu suka rungume juna cikin farin ciki.


Bayan sun saki juna ne, Haala ta kalli Basma tana yatsina fuska. Da mamaki take cewa.


"Big girl kinga yadda kika koma kuwa, meya sameki ne haka"?


Basma tayi narai narai da ido, kamar zatayi kuka, cikin damuwa ta fara karantowa Haala damuwarta.

Har zuwan mamanta da abinda maman tace sai da tafad'a mata ta k'are da cewa, _"Haala na rasa yadda zanyi wallahi ban san Nour zai zaman min k'arfen k'afa ba wallahi.."_


Haala ta dad'e cikin shiru, kafin daga baya ta fara magana.


"Ki daina damuwa k'awata, wannan ba abu bane da zaki damu kanki akai, ai kina da matakin d'auka. Tunda dai Abba ya nuna aure dole to za,ayi, amma fa da Yusuf.!!"

"Basma ta kalleta da mamaki."

Ta k'ara kallon Basma, _"Ko kin shirya escaping kuma toh."?_

Basma ta waro ido. "Noo rufamin asiri, ina zanje.."? So kike na tonawa kaina asiri.."? After that duk inda zani ma sai abba ya nemo ni.!!

 

Haala bata ce komai ba illa wayarta data d'auka. "To bani number Yusuf.


Tace da Basma, babu musu Basma tasa mata number.



 Kasak'e Basma tayi tana kallon Haala yayin da ta saka wayar a kunnenta.


Cikin wata irin murya mai daukar hankali Haala tace, 

"Hello."

Hello akace daga d'aya b'angaren.


"My DEar!

Ta fad'a cikin shagwab'a.

"How're you."?

Yace mata.


Cikin kissa tace, "Baby ka tafi, baka fad'amin ba, then kana tambaya na, ya nake koh."



_Ya shiga rud'ani_ 

"Am sorry Baby.

"Bangane muryanki ba pls tell me wace ne."?


"You say what "?

"Sweet nine ka manta ko."?


Nan ya dan rud'e saboda sunan da ta kirashi _'sweet'_ ta tuna mishi da wata yarinya da yake ji da ita, kafin tafiyar shi ne yayi _missing contact_ din yarinyar, gashi had'uwa irin tasu bai san gidan su ba. _May be_ a irin goge-gogen da Basma take mishi ne a waya ta goge mishi lambar.


"Please Baby tell me mana kinji."

Haala ta k'ara shagwab'e murya, wallahi I won't tell u, tunda ka manta ni shikenan, dama ce maka zanyi na dawo N'ija cikin satinnan."


"Oh Baby am sorry I missed you over, kiyi hak'uri kinji Honey plz."


"Hmm, ban hakura ba fa, ka sami 'yan mata ka manta ni nagode."


"Haba _Honey plz_ kinji mana, wallah _I missed your contact that's why._Amma ina kewanki sosai Honey." 


Hmm, Okey naji zan hak'ura amma fa don kaine.


 "Oh Baby thank you Muah." yai mata kiss ta waya.


"Hmm sweet like kana missing me d'innan."


Yes, baby wallahi I do."


"Wai Baka dawo bane."?

Honey naji dad'i da kika kirani fa, da nan da _2weeks_ zanzo nija amma yanzu zanzo nan da _1week_ saboda ke.


"Wow sweet, Allah kawo ka kaji."


Okey Baby, please amma ki saki jiki idan nazo kinji."


Baka da matsala sweet."


"Wow Baby kin biya ni fa i miss you."

Ina aiki ki jira ni da dare zamuyi video call.

"Okey sweet."

Tace mishi.

Sukayi sallama.



"Basma ta rungume Haala tana ihu." Duk da tana dan kishin wayar da sukayi.


"Kinga cikin sauki yana dira muma muyi gidan nasu koh"?


"Yes inji basma, Kinga ranar saura 1day lokacin da Dad ya dibar min."


"Kada ki wani damu k'awata." Inji Haala.


"But kada ki kira Yusuf ke, ki share shi a zuwan kin bar zancen shi.


Okay k'awata.

 Daga nan Haala ta cigaba da tsarawa Basma yadda zasuyi da Yusuf d'in.





B'angaren Haala kuwa cikin kwanakin ta samu damar Yusuf sosai, duk da cewa, daga baya Yusuf ya gano ta amma, saboda gudun kada ya kub'ce mata sai ta fad'a mishi cewa ta tsinci number dinshi ne cikin wayarta kuma tabbas ada sunyi rayuwa amma ba su dad'e ba ya bar k'asar.




Kan Yusuf ya kulle, to abu ne dayawa, yana da 'yanmatan da bai san adadinsu ba shi kanshi. Don haka sai ya yi mata wata tambaya guda d'aya don ya tabbatar.

"Kin san wata yarinya Basma."?

"Wa ce Basma kuma."?

Ta mayar mishi da tambaya ita ma.


"Hmm, kin santa mana."

Yace mata.


Yes she's my friend. Ta bashi amsa kai tsaye.

"Hmm, Zatayi aure koh."?

"Yes.!

Haala ta bashi amsa babu wani kwane-kwane.


Yayi ajiyar zuciya.

"Bana son idan nazo N'ija, ta sani.!!


"Hmm, saboda me."?


"Zata dameni ne.. Yai wani murmushi  "Hmm yarinyar tana so ta batamin rai ne."

"Kamar Yaya"? Haala ta tambaya.

( _Kamar bata san abinda ke faruwa ba._)


"So take wai na aureta a nata haukar."


Haha Haala ta shek'e da wata dariya.

"Me zai hana ka."?

Hmm, babu aure a schedule d'ina sai nan da 3years idan ma auren ne. And sam bata cikin 'yan mata da zan iya aura.!!

"Hmm.. Haala tace.

"Yes, kota aiko ki ne domin ki sani aurenta koh."?


Ya fad'a kai tsaye yana mata wani dariyar na-gano ku daga baya.!!


Babu b'oye-b'oye Haala, tace mishi "Yes. 

"Hmm sai kuma kika yarda zaku iya koh"?


"Yusuf kana so Basma."? 

Ta tambaye shi maimakon ta bashi amsa.

"Hmm, ki tambayeta ai, we're just  friends ba soyayya muke ba.


"Hahh.. Do you know why I accepted her request data ce nayi convinced naka ka dawo Nija."?


"Hmm ashe hakan ne ko."? So na gane ku ai."

"No..no.. no.. no, I just came for my own reason."

"Idan zaka yarda nima mu zama friends mana."


Ta fad'a kai tsaye babu wata shakka.


Yusuf yaji dad'i a ranshi ko ba komai ya sami wajen zuwa idan ya dawo k'asar.


"Hmm you're welcome."

Yace ita.


Daga nan suka cigaba da hirar su, sosai Yusuf ya saki jiki da ita, domin yana da saurin sabo da sakin jiki Indai ga mata ne.


Ya bata labarin yadda alak'ar su da Basma ta fara.

Cikin 'yan kwanaki suka k'ulla wata alak'a mai k'arfi da Haala, kuma ya tabbatar mata cewa  zai zo Nigeria aranar asabar, kuma a ranar zai shigo kano komin dare.



_____________

Basma tasha tuntub'ar ta akan zancen, amma kullum Haala fad'a mata take babu matsala duk ranar daya dira kasar itama kawai ta dira gidansu kuma zata sanar mata da zarar yazo... Gefe guda abbanta yana ta mata tuni, ya fada mata. Nace iyayen Nurah  su shirya don idan banga idon  Yusuf ko iyayenshi ba ranar asabar toh Lahdi in sha Allah zasu zo su. Kada kice na miki badai-dai ba shiyasa nake baki dama. Ita dai komai ta mayar dashi ga hannun Haala tunda kullum cikin kwantar mata da hankali Haala take, amma abinda ke bata mamaki shine sau biyu Haala tazo gidansu, duk maganganun da suke yi a waya ne gashi gobe wa,adin abba zai cika.!!








   📝 

*HAJEEYAH  KHAREEMERH*



[17/03, 2:37 p.m.] UMAIMA BASHEER: ♥️♥️♥️♥️

*ZAZZAFAN SO*

(Masoyin k'warai)

*Cigaban littafin Zazzafan so (Guba ne)*

💔💔


 *By*

*Karima Tijjani Mansur*

*(Hajeeyah Khareemerh)*

*Dedicated to unique in your love heart*





📄 *53*





*Yau* jin ta take gaba-d`aya kamar ba ita ba, komai tana yinshi ne cikin sanyi. Ba wai damuwa ce ta mata yawa ba, sai dai kawai fargabar  bak'on da zatayi. Ta nemi dalilin damuwar itama ta rasa.

 Ita ba bakin maza ne batayi ba, bare ace rashin sabo ne, takanyi bak'i idan ta kama saboda yanayin aikinta.


Sannan gefe guda tana son sanarwa mama batun zuwan bak'on shima taji ta kasa hakan. Hatta Basheer, ko Zainab ji tayi tana jin nauyin sanar musu bare kuma abba. Sai ta fara tuhumar kanta. _"Zuwan nashi zuwa ne fa na ziyara kawai, ba alak'ar soyayya ce tsakaninsu ba, idan ma zata bashi matsayi zata iya kiranshi da abokinta kawai.._

_To mene ya kawo jin nauyin da fargabar."?_


Wani b'angaren na zuciyarta yace, _"Saboda baki sanshi ba baki taba ganin shi ba.!!"_

Sai kawai ta yardarwa kanta wannan dalilin ne yasa.


Har kusan k'arfe uku da rabi tana d'aki a kwance.  Mufida na ta kai kawo cikin d'akin, sai da ta tambaye ta ma, _"Aunty ko baki da lafiya ne."?_

Ta girgiza kai kawai.

Jin ana kiran sallar La,asar ne yasa dole ta tashi. Tuna cewa, _yace mata da yamma zai zo fah."?_


Sai da tayi wanka sannan tayi sallah lokacin zainab itama ta lek'o d'akin. Ta kirata.

"Zainab zo kiji."

Zainab ta shigo d'akin gaba-d`aya ta zauna kusa da ita, "gani meke faruwa."?

Ta girgiza kai, _"babu komai,_ sannan ta waro ido, don tambayar tasa ta tsargu. _"Me kika gani.?_ Ta tambaya.



Zainab ta girgiza kai. 

"Babu komai gani nayi kin kirani."

"Okey Abba yana nan."?

Hafsah ta tambaya.

"Ya fita tun dazu."

"Basheer fa."?

Zainab tayi mata kallon mamaki sannan tace. "Ya sa kayan kwallo ya fita."

"Okey.."

"Bak'o zanyi neh!!


Ta fad'a a hankali tana kawar da kai.


Zainab ta saki murmushi, dama ta lura da yawan wayar da yayar tata keyi kwanakin nan.

Ta waro mata ido, "Really aunty."?

"Aa to mene kike mamaki don nace zanyi bak'o"?

Zainab ta kuma yin murmushi, "Babu komai, da yamman nan zaizo."?


"Eh, ni duk na kasa komai ma.!!

Ta fada tana k'arasa shafa mai a hannunta.

Zainab ta boye dariyarta. Sannan tace, "Meya sa toh aunty."?

Tana sane tayi mata tambayar.

"I don't really know, kawai bana son ya raina ni, so kuma na kasa komai."



"Kin tanadi kayan da zaki sa."? Inji zainab.

Duba Ki zab'o min.

Zainab ta mik'e ta shiga dubawa, har kayan cikin akwatu, itama tana son ta fito da yayar tata. 


Daga k'arshe dai ta nemi mata, wata pink d`in atampha riga da skirt dinki stone work yayi kyau sai shek'i suke,  ta ciro mayafi, da sark'a d'an-kunne zobe, agogo duka ta ajye mata. 

"Kisa wannan aunty zaki yi kyau."

Ta kalli kayan ta tab'e baki, kawai ni yazo zai tashe ni tsaye wallahi.!!

Zainab tayi murmushi ta gimtse. Hafsah ta mik'e don saka kayan. Zainab Tayi saurin dakatar da ita da tambaya, "Aa yaya ba zaki shafa ko powder bane."?


"Ke kyale ni fa, ba wai kwalliya zanyi ba yana zuwa kuma zai tafi."


Zainab ta zaunar da ita bisa gado. "Please aunty Ki bari na shafa miki powder."

Bata mata musu ba, saidai ta had'e rai.


Zainab ta mata saasauk'ar kwalliyar powder, sai lining na kan ido, da mascara sai can janbaki. Nan da nan farar fuskarta ta d`auki haske da sheki tayi kyau matuk'a. 

Tana mik'ewa da nufin saka kaya, kirashi ya shigo. Taji gabanta ya fad'i, kamar ta share sai kuma ta d'aga.


"Ranki ya dad'e na iso cikin unguwar fah."!!

Ta waro ido, ta kalli zainab.

Number nawa ne ma gidan. Baki fad`amin ba"? 


Batayi magana ba sai ta turawa Zainab wayar.

Zainab ta rik'e, tasa a kunne, dai-dai lokacin yana cewa, "Kiyi hak'uri nasan na takura miki amma don Allah ki fad`amin."




"Hello." Zainab tace, sai yaji ba muryata ba. Cikin muryar tausayi yace, "Don Allah ina take me wayar, please kada kuyi min haka."


Cikin muryar shi zainab ta fahimci nutsuwa a tattare dashi, sai ya bata dariya da tausayi lokaci guda.


"Kana ina yanzu."

Ina unguwar da ta fad`amin.

Ina kenan."?

"Sallari tace koh."? 

"Eh nan ne."

"House no. 35." Inji Zainab.

Thank you, in sha Allah gani nan."


"Amma please ina take."? Ya tambaya da damuwa.

"Bata kusa ne."

Kamar zai k'ara magana, sai kuma yace, "Okey thank you."


Zainab ta kalli, Hafsah, lokacin har ta gama sa kaya. A d`auki d'an kwali zata d'aura mata.

"Yaya ya kusa isowa."

Batace komai ba.

Zainab ta mata d'aurin, yayi kyau sosai.

"Kinyi kyau Yaya."

Ta fad'a tare da mik'a mata mudubi.


Hafsah ta kalli, madubin tayi kyau sosai. Tayi murmushi.

Zainab ta tambaye ta, "Yaya kin fadawa mama."?

Ta girgiza kai, Aa ai ba dad'ewa zaiyi ba kuma friend dina ne fah kawai.

"Hmm, Zainab tayi murmushi.

Sai kawai ta fice.


"Mama, aunty Hafsah wai bak'o zatayi."

"Waye zaizo."?

Nima ban sani ba, inaga wanda suke waya dashi ne.


Mama tayi murmushi, "Ai shikenan tunda bata gayamin ba."



Zainab tayi dariya itama. 


"Idan kinga bata bashi ruwa ke ki kai mishi kinji." Inji mama.

"Toh, zainab tace ta juya ta nufi d'akin da Hafsah take.


Tana zaune jugum, wayarta na gefenta, wayar na ta fara k'ara, amma ko kallonta batayi ba, kafin Zainab tayi wani yunk'uri har wayar ta tsinke.


Ta kalli Hafsah daidai lokacin kuma, wani kiran na k'ara shigowa.

Yaya menene wai, kiranki ake fah."

Ta yatsina fuska. "Ki kyale ni kawai idan zaki d'aga ki d'aga amma fa kyar idan zan fita ma."


Zainab tayi mata wani kallon mamaki, tana so tayi magana amma bata son wayar ta k'ara katsewa ba,a d'aga ba, don haka da sauri ta mik'a hannu ta d'akko wayar, ta d'aga kiran.


"Hello."

Tace dashi.

Cikin murya mai cike da damuwa yace, _"Don Allah kibawa yayarki hakuri wallahi idan zuwana zai zamar mata damuwa, na fasa, zan juya kawai."_


Da sauri zainab tace, "Aa fah, tana wani abu ne. Kana ina ne."?

"Ina kofar gidan da kika fad`amin house no 35."

Okey please ka dan jira. Zainab ta fad'a.

"Okey thank you, amma please ki fad`amin gaskiya meyasa Hafsah taki amsa wayata, kinji, don Allah."



Hafsah ta gyara zama, tana jinsu, tunda wayar kamar hands-free take. Ita kanta batasan dalilin abinda takeyi ba, kawai ta tsinci kanta da rashin son hada id'o dashi.


Allah babu komai fah. 

"Okey thank you."


Zainab ta ajjye wayar ta kalli Hafsah. "Don Allah Yaya ki daina kinga ke fa kika ce mishi yazo."


Hafsah tayi shuru, ta zubawa zainab ido kawai.


Zainab taja mayafinta zata fita.


 "A kujerun waje zaki ce ya zauna."

Hafsah tayi mata magana.

Ta gyada kai ta fita kawai.


Tana bude gate ta hango bayan shi, yana tsaye daga gefen dama na gidan, ya juyawa hagu baya. Babu mota a wajen d`in mota bare ace da ita yazo.


Zainab ta dan matsa har zuwa kusa dashi sosai, sannan tayi mishi sallama.

Assalamu alaykum."

Ya juyo da murmushi a fuskar shi. "Wa alykum salam 

Zainab zuciyarta tace, _Masha Allah, amma wannan aunty Hafsah take wa yanga. Mutum ne mai kwarjini da cika ido, ga kyau mai d'aukar hankali._


"Kaine bakon Yaya Hafsah koh."?


Ya d'aga mata kai.

"Okey, ka k'araso toh."

Tace dashi.

Yayi mata murmushi tayi gaba ya bita a baya, har suka iso farfajiyar wajen can gefe da kujeru a wajen da d'an table.


Zainab ta mishi nuni da kujerun sannan tace, "Ka zauna ga kujera nan, tana zuwa itama."

"Okey nagode, sannu kinji." Ya fad'a a shigen zuci.


Zainab ta k'ara kallon shi sannan ta shige gida.


Yaya Yaya, gaskiya mutumin ya hadu kinganshi kuwa, wallah Masha Allah, gashi da kwarjini da...

"Hmm, Hafsah ta katse ta."

"Don Allah Yaya ki tashi kije kinji."

Ta kalli Zainab, tana son fita, amma nauyi takeji, amma babu yadda zatayi.


Zainab ta d'auki jan jambakin data sa mata dazu zata k'ara mata, ta kauce.


No ki bari zainab haka ma ya isa.

Ta muk'e ta k'arasa jikin mudubi ta kalli kanta, tabbas tayi kyau. 


Zainab ta duba ta dakko mata takalmi me sauk'in tudu, ta sanya.


"Zoki raka ni Zainab." Hafsah tace.

Noo Yaya, kije ke kad'ai, please."

"Aa nace kizo fa."

Please Yaya Allah kikaje ke kad'ai sai kinfi kwarjini a wajen shi.

Hmm, inji Hafsah, a zuciyarta tana cewa, _"an gaya miki so nake na burge shi."_


"Yayah.!!

Zainab ta kirata da k'aguwa.

Ta kalli Zainab ta mata alama da ido, _"mene."?_

"Kina wasting time Don Allah ki tafi kinga babu dad'i fah."


Dole ta bude k'ofa ta  fita, gabanta nata fad'uwa.




Yana zaune, hankalinshi gaba-d`aya nakan, flowers (fulawowin) da sukayi wa farfajiyar gidan ado, don ya gaji da kai kallonshi hanyar fitowa daga cikin gidan.


Ahankali take tafiya,  ta k'ara saka yanga akan alhinin yangar da take tata ce ta halitta, saboda bata son k'arasawa inda zata je.

Tana hangoshi tana k'ara rage sauri. Ga k'aruwar fargaba kuma.

Yana kallon fulawowin har yanzu, gaba d'aya ya bada hankalinshi can, don ya fitar da ran fitowarta kusa.


Hakan da yayi ya mata dad'i bata son ya jiyo sautin takunta, bare ya juyo.


Sai da ta kusa zuwa inda yake sannan ya juyo.

Tunda ya gano me tahowar ya kafa mata idanu, har ta k'araso inda zata zauna, ita kuwa da kyar take iya cira k'afarta. Tayi k'asa da idonta ga barin kallon shi, dama bata yarda sun had'a ido ba. A hankali ta d'an bude baki ta mishi sallama, sannan ta d'an ja kujera a hankali ta zauna.



Sai da ta daidaita a kujerar sannan ya bud'a baki shima ya amsa mata, yana k'ara kai idanunshi fuskarta, "Wa alaikumus-salam."



Sukayi shuru tun bayan sallamar daya amsa. 



Sai kuma taga ya dace ta mishi sannu da zuwa, tunda bak'onta ne.


Cikin rashin daga sauti kamar koyaushe tace, "Sannu da zuwa ya hanya."?

Sai yanzu ya ji dad'i sosai har ranshi, don da har ya fara wani tunani. Ya fad'ad'a murmushi sosai.


"Yawwa, sannu kema, hope na sameki lafiya.


Ta fad'a a hankalin dai.

"Lafiya lau Alhamdulillah."


Suka k'ara yin shuru,  shi cikin nazarin irin had'uwar ta, datsaruwarta komai nata yayi mishi yadda yake so, yafi ganin kyanta ma yau fiye da koyaushe da ya tab'a ganinta. Ita kuma cikin k'aguwa da kallon da yake mata, da tunanin irin haduwar shi shima da kwarjinin da yake da shi, don jinta take kamar gaban wani sarki take, gaba d'aya ta takura.



"Hafsah, yau gani koh, Allah yayi yau kinga ukhashatu.!!


Ya fad'a da murmushi. Itama ta dan murmusa, bata da abin yi ko cewa idan ba murmushin ba.


Yayi yar ajiyar zuciya a hankali.

Alhamdulillah.!!

Taji yace, sannan bayan wani d'an shuru ya furta.



 "Ki yarda Allah ne ya had'ani dake, kuma shiya san alkhairan da zai kulla tare damu, shiyasa na nace miki duk da ke naga kamar takura ne agunki koh."


Ya k'arashe maganar yana k'ara zuba mata idanunshi, ta taga sunyi mata wani _harr_ a nata idanun, kamar wani giftawar haske.

Tayi saurin kawar da idonta gefe tana murmushin zancen shi.


"Da gaske ne kenan ni me naci ne a wajen ki koh."?

Ya fada shigen rad'a. 


Dole ta bude baki don kare kanta.


"Ni bani na fada ba dai.!!

Ta fada tana yar dariya.

Shima dariyar yayi, hmm ai ni nasani, inada naci akan abinda nake so gwara na fada da bakina.


Gabanta ya fadi da kalmar daya fad'a, _inada naci akan abinda nake so.!_


 Sonta yake kenan."?

Ta tambayi kanta, tare da d`agowa ta kalli idanunshi don tabbatar da abinda yace.

Ya jinjina mata kai shikuma, "yes.!!

Ya fad'a.


_Ta kasa tantance me "yes d`in tashi ke tabbatar wa. Kasancewar shi mai Nacin ko kuma kalmar kan abinda yake son, dayace.? wanda maganar kai tsaye tasan akanta ake yi._?


Suka tsaya shuru shida ita, kowa cikin   nazari.


Takun tafiya sukaji daya sa su dukansu juyawa.

Zainab ce rik'e da tray na ruwa da lemo sai _cups._


Ta musu sallama sannan ta ajye.

Bata bata lokaci ba ta juya, wanda hakan bai bawa ukhashatu damar yi mata godiyar da yayi niyya ba. Sai kawai ya juya ga Hafsah. "Thank you.!!

Yace mata.

Ta mishi alama da ido. Tana neman karin bayani akan godiyar.


Yayi mata nuni da tray d`in yana murmushi, sannan yace, "ko ba ni aka kawo wa ba."

Murmushi tayi ita, tace, "hum.."

Kawai.

"Zan iya sha don inajin k'ishirwa.?

Ya tambaya.

Ta d'aga gira kawai.

Ta mishi kyau sosai hakan yasashi b'ata lokaci ya kalleta, sannan ya d`auki ruwan ya zuba a kofi, ya d'aga zai sha.


Ta zuba mishi ido ita kuma, sai taga ya fasa.


Batayi magana ko wani motsi ba taga ya d`auki bottle d`in zai kuma zuba wani ruwan.

"Oh sorry ban tambayeki ba ruwa zaki sha ko lemo. Ni dai nafi ga ruwan."


Batace komai ba, sai mamaki daya bata, _wannan mutum akwai salo!!_

Tace a ranta.


Uhum."?

Ya kuma tambayar ta.

Ta bishi da kallo kawai, sai kawai ya zuba mata ruwan, a cup ya ajye agabanta.

"Gashi."

Yace mata sannan ya tsare ta da ido.

Ala dole tace, thanks.

Tana ganin yanayin murmushin da yayi mai bayyana tsantsar farin ciki.

Sannan a hankali ya daga nashi ruwan ya fara sha.


Bata da bukatar shan ruwa a lokacin, kuma ko da, da buk'atar hakan ba,zata sha agabanshi ba.


Sai da ya shanye, ya k'ara zuba wani ya sha, rabi sannan ya ajye, "Thank you."

Yace mata, wanda kafin ya fad'i hakan sai da ta lura da motsawar bikinshi ya furta, _"Alhamdulillah!._


Sukayi shuru, bai k'ara ce mata tasha ruwan ko wani abu ba. Sai kallon agogon hannunshi da yayi.


Itace ta tuna da wata tambaya da tace zata mishi, don tana san tabbatar wa.

Tana fara magana, ya zubo mata idanu, wanda hakan yasa ta dan rikice sai da kyar takai k'arashen jimlar.

Um.. Kace ka taba ganina a wurare, so ina da inane."?

Ya saki murmushi, sai lokacin ta lura da dimple d`in da yake dashi ya jinjina mata kai.

"Of course naganki sau biyu kafin na ganki a television."


Tana so ta k'ara tambayar shi, "To ina ne."?

Amma bata son ta k'ara tambaya.


"Na ganki a gidan biki, sannan na ganki a titi.!!abinda yace kenan yana wata iriyar siririyar dariya.

Sai ta tafi tunani, Gidan biki kuma.. Titi kuma."?

Da kyar ta samu ta tuno irin gidan bikin da yake nufi, da taimakon k'ara kallonshi da tayi take ta gano shi.


_Mutumin da taji abokan shi sun kirashi da UK ranar bikin Aysha er ajinsu sannan tabbas sunyi magana da Basheer randa suka had'u a titi._


Wato dole yace gidan biki da kuma titi.

Da sauri ta bude baki tace, waye ya baka number ta toh."

A hankali kuma cikin nutsuwa yayi saurin bata amsa,  "Allah.. Allah ne ya bani.!!

"Hmm, koh."?

Ya jinjina mata kai.

Sannan don kada ya bata damar sake mishi magana ya fara wata magana takaitacciya, amma wacce ta rikita komai nata.

"Tun ranar naji kinyi min, naji inason kulla alak'a dake, sai dana rasa hanyar samun contact dinki na gano sonki nake.!!


Ya dago kai sannan ya dora, kiyi hak'uri nasan ba lallai kin shirya karb'ata ko kuma na chanchanci ki soni ba, amma inason ki bani dama mu dinga ko da gaisawa ne don Allah."

Magiyar da yayi ya k'ara sa mata tausayin da yanayin maganar shi ya sakata.



So.."? Yau kuma"? Yanzu, ake furta mata shi."?

Ji take kamar babu wanda ya taba ce mata hakan a duniya.


Taji  zaman

 wajen ya gundure ta, kamar ta tashi bar gurin, amma babu dama.



Gashi shi kuma tun bayan da yayi maganar yayi shuru ya koma kalar tausayi yaki ya k'ara furta mata koda kalma d'aya sai kallon ta da yake ta faman yi...






H hameeed!! Sukaji an kwallo mata wani kira, wanda hakan ya sasu waige waige shi da ita. 


Wata budurwa ce take tahowa daga wajen gate, sanye take cikin riga da skirt na atampha sai wani siririn mayafi wanda iyakarshi kafad'ar ta. 


Da wani irin sauri take tahowa. Da alama ba cikin hayyacinta sosai take ba. 



Tana k'ara isowa kusa dasu Hafsah na k'ara fahimtar wacece. Don haka da saurin ta mik'e saboda mamaki. 


Da gudu ta k'araso, ta rungume Hafsah gam, kafin Hafsan tayi wani yunk'uri, cikin kuka take magana..


"H. Hamid, Yusuf.. Yusuf!! 


Mamaki ya cika ukhashatu, ya lura ita ma Hafsah a razane take, sannan yana lura da yadda take ta kokarin kwace jikinta.



Da k'yar ta iya kwacewa, suka tsaya kallon juna.


"Ukhasha ya mik'e, ya kalli Hafsah, naga kinyi bak'uwa, koh, bari na barku ku gaisa. Thank you.!!

Ya juya, ya kama hanyar fita. Basma ta bishi da kallo.


Hafsah taji kamar ta kurma ihu, wannan wacce irin masifa ce, Basma a gidansu, a irin daidai wannan lokacin da take da bako irin wannan, kuma yake furta mata abubuwa masu muhimmanci."??


Ta bishi da ido har ya isa gate tana gani, sukayi musabiha da mai gadi, yana fita ta juya itama da gudu ta wuce cikin gida, bata tsaya ko k'ara kallon Basma ba.


Aka bar Basman a tsaye tana tunanin abinyi...






     📝 

*HAJEEYAH* 

*KHAREEMERH*

[17/03, 2:40 p.m.] UMAIMA BASHEER: ♥️♥️♥️♥️

*ZAZZAFAN SO*

(Masoyin k'warai)

*Cigaban littafin Zazzafan so (Guba ne)*

💔💔


 *By*

*Karima Tijjani Mansur*

*(Hajeeyah Khareemerh)*

*Dedicated to unique in your love heart*





📄 *54*



*Ganin* zata b'ata lokaci, yasa tabi bayan hafsah da gudu itama.


Acikin gidan kuma Zainab da Mufida na zaune a parlour suka ga Hafsah ta shigo kamar anjeho ta tana hak'i.

A razane Zainab ta mik'e tana dube-dube, zatonta wani abin ukhasha yai wa Hafsan, tana bud'e baki da nufin tambayar hafsah ~meya faru ta shigo haka."?~ sai ga wata ma ta shigo da sauri, Zainab ta ware ido ta kalleta sosai sannan ta fara gano wacece.


Itama mamaki  ne ya sa ta tsaya shuru, babu abin cewa, kafin ita wacce ta shigo d`in ta nufi Hafsah ta rirrik'e ta, H. Hameed baki ganeni ba ne... Basma Yunus ce, kiyi hak'uri abinda nayi miki wallahi sharrin shaid'an ne nima yau na tabbatar Yusuf ba d'an goyo bane, nima yayi min abinda mukayi miki.. Yusuf ya yaudare ni yaci amanatah.. 

Ta fada da iyakacin k'arfinta cikin kuka, wanda sautinta ya tsorata su, sannan har ya isa ga kunnen mama da ke can d'akinta.


Hafsah tasa k'arfi ta ture Basma lokacin da take wasu maganganunta.. Don Hafsan ta gaji da abun, gani take mene had`i kuma yanzu.."? Bata da wata alak'a tsakanin ta da su dukansu d`in.


_Hafsah ki zo, mu yaki Yusuf ki manta da abinda ya faru, don Allah, mu kwatarwa kanmu yanci mu hada kai kinji.. Mu ganar da shi kuskuren sa, nayi alkawari indai kika yadda to zan bar miki Yusuf bayan mun koyar da shi darasi dama ni Abbana aure zaiyi min, zan kyale miki shi wallahi da gaske nake.!!"_


Bak'in ciki ya cika Hafsah, gefe guda kuma abun taji ya bata dariya, _meye kuma haka."? Allah ya tsare ta Ita ta bata lokaci kan wani shudadden al,amari da ya riga ya shud'e a wajen ta."?_ 



Sai lokacin bakinta ya bude cikin fushi ta fara magana.


Ta nunawa Basma hanyar fita. Cikin k'araji tace, Basma Yunus, fita, fitar mana daga gida, kar na k'ara ganinki a nan, an fad'a miki yanzu da ce"? Saboda kin rainawa kanki hankali kike tunanin har yanzu ke da Yusuf you're  part of my business.."? Ke ce kike cikin damuwa, ke kika d`auki Yusuf mutum who worth your wested time, but to me  ( _ta nuna kanta._) YUSUF IS WORTHLESS.!!

Ke dashi bani da had`i da ku, don haka matsalarki ce ni ban san wani Yusuf ba bare ke..!!


Fita!! Ta fad'a da sauti me k'ara.




Shigowar mama kenan taga taga abinda ke faruwa.

Ta tsaya ta k'are musu kallo har da bak'uwar fuskar da bata gane ba.


"Ke Hafsah mene haka."?

Cikin haki murya na rawa ta fara magana. 

Mama Basma ce fah, Basma Yunus, kuma ta rasa sanda zata zo sai yanzu tazo ta korar min bak'ona!!.. ( _bama tasan sanda ta fadi hakan ba._) 

Then tana fad`amin wani rubbish wai Yusuf mene ne had'ina dashi ni ta fita.!!

Zata fara kuka kenan Zainab ta tarota ta d'an rungumo ta, sorry Yaya kada ki bata hawayen ki kinji, bari kiga.


Sai ta saki Hafsah, tayi kan Basma, ta daga hannu zata daketa. Ke banza fice mana daga gida, idan kina da kunya ma zaki iya zuwa gidan nan, nonsense, deceiver, Hypocriter, snatcher.!!

Fita nace kafin musa a fitar mana dake.!!

Zata sauke mata hannu, mama tayi saurin rik'e hannunta. Ke Zainab shiga hankalin ki fah.. Me tayi muku zaku dake ta."?

Ta ruk'o Basma ta zaunar da ita, akan Kujera. Hafsah ma ta zauna.


Wacece ke."?

Mama ta tambaye ta.

idonta cike da k'walla, tace "Basma, kawan Hafsah ce ni."

"K'awar Hafsah, amma ban sanki ba."? Inji mama.

Basma tayi tsuru-tsuru.

"Me kika zo yi gidan nan toh "? Mama ta tambaye ta cikin tsanaki tana son ta gano wani abu itama.

Basma tayi shuru, tana kame-kame, um am.. "Na...na zo ne kawai.."

Hmm, to waye Yusuf da naji kin kirashi."?

Ta waro ido, ana shirin k'ureta.

Ehe.?

Inji mama.

"Sa..saurayin Hafsah ne.!!

"Saurayin Hafsah kuma."? 

Inji mama.

Sai kuma ta juya ga Hafsah. Cikin had'e rai tace, "Ke waye Yusuf."?

Hafsah tayi saurin girgiza kai.

"Ban sanshi ba mama.!

Mama ta, juya, ga Basma.

''Ya'yana basa kula saurayi ba tare da sanina ba, saboda haka bamu san wani Yusuf ba a nan gidan.Don haka kada ki k'ara kawo mana zancen wani cikin gidan nan kinji.!!

Basma ta gyad'a kai jiki a sanyaye kuma a kunyace.


"Mene had`in ki ke da Yusuf d`in tunda kince saurayin Hafsah ne da bakinki."?


Basma ta hau zare ido. Bata da amsar bayarwa..

"Mama ma ta san hakan don haka ta cigaba da magana.



"Duk abinda ya faru ma, basai kin fad`amin ba na sani. 

"Kinsan cuta babu kyau, k'awarki ta yarda da ke, ki cuce ta ki k'wace mata saurayi..kinsani to alhaki kwikwiyone, saboda haka ki tashi ki tafi gidan ku, kuma kada ki k'ara kawo mana zancen wani Yusuf cikin gidan nan, bamu da alak'a dashi.!!


"Kije, kinji abinda yayi miki ma ya isheki darasi, kije Allah ya baki wani kema, amma Hafsah kam bata san wani yusuf ba sam..


Cikin kuka Basma  ta fara magana, Mum Dad d'ina ne yace ya fito ko ya aura min wani, shine yak'i na ya nuna bazai aure ni ba, shine kuma bayan ya dawo na je nemanshi na ganshi tare da k'awata, har mari na sukayi, and he til me bazai taba aure na ba kuma kada na k'ara kula shi.!!


Mama bata da abin cewa da alama kuma taga abin ne yana damun Basman shiyasa har take amaryar dashi, bata damu da korar ta da ake yi ba.


Ta mik'e ta kallesu dukansu, mama thank you, H. Hameed am sorry for give me for what I did to you.!!


Ta juya zata fita sai ta bawa mama tausayi.


Mama ta kirawo ta.

Zo 'yata kinji.!!

Basma ta juyo, ta dawo ta Tsaya.


"Ki bi zabin da mahaifin ki ya baki kinji."

Ta d'aga kai kawai, amma aranta bakin ciki ne fal.

Da alama taji shawarar mama da kunne ne kawai.

"Thank you mama. Tace, sannan 

Ta juya ta fice.

Su Hafsah suka bi ta da kallo.




Ta fita tana cije lebe, tabbas yau taga Tashin hankali, wato har gwara abinda sukayi wa Hafsah ita da Yusuf..

 Da irin korar da Yusuf yayi mata.


Kai tsaye Gidan mamanta ta nufa, taje ta rushe mata da kuka. Da kyar ta shawo kanta.

Kiyi hak'uri kinji 'yata fad`amin abinda ya faru.


"Mama gidan su Yusuf naje nemanshi na tarar ashe ma ya dawo.."

Sai kuma akayi yaya."?

Inji Hajiya Halima.

Cikin kuka tace,  shine naga Hala a gidan suka mini wulaqanci ita da shi.

Hala."? Wace Hala."? Inji maman Basma.

My friend Hala.

Cab!! Me kikayi musu ke toh."?

Inji mama.

Mama, bazan iya dasu ba, baki ga abinda suka mini ba, har sawa yayi servant dinshi suka min wulaqanci, mama Yusuf bashi da mutunci, ban san haka yake ba sai yanzu."


Maman tayi shuru, itama bata da abin cewa, ga shi lokaci ya k'ure musu. Sai kawai ta shiga rarrashin 'yar tata, tana nuna mata tayi hak'uri akwai sauran wata hanyar, dole a koya musu hankali.

Basma ta d'ago ta kalleta, "How mama,  can't you see lokaci ya k'ure gobe fah Abba zaice iyayen Nour su zo, kuma fah kinsan bana son shi mama."


"Kiyi hak'uri zanzo zamuyi wannan zancen, yanzu tashi ki tafi gida kinji, nasan abbanki bai san kin fito ba, kada kija matar nan ta zuga shi ya miki wani abin. Oya!! ki kwantar da hankalinki, babu mai aura miki wanda baki so, nina fad'a miki kinji."


Basma tayi ajiyar zuciya, ta gyara zama bata son tafiya tabar gidan.

"Mama ni bazan koma ba."

Ta fad'a a shagwabe.

Maman ta dan had'e rai, Oya tashi tashi mana, kina son ki b'atamin shiri so kike Abban naki yasan kin fito."? Ba nice dai nace kije babu komai ba."?


Ala dole ta mik'e ta nufi hanyar gida, cikin rashin sanin abinyi, gaba-d`aya duhu take gani, ta rasa wacce irin bak'ar rana ce wannan.


Mamanta kuwa ta rasa abinyi, ta sani alhaji Yunus yafi k'arfinta ba zata iya ja dashi ba, tun da tun farko ita ce ta mayar masa da 'yar, da komai bai faru ba. Mataki d'aya take ganin zata iya d'auka wato na shari,a shi kuma tana shakkar yin hakan nan ma. Amma fa dole tasan abinyi. Duk da wani b'angaren ita kanta ta sani Basma ta isa aure  kuma, auren Basma hutu ne a wajenta, amma damuwarta shine ba zata bari  a aurawa 'yarta wanda bata so ba..




*HAFSAH*

________________



Hafsah duk bayan muntuna tana duba wayarta ko zata ga missed call d`inshi, amma bata gani ba.  Haka kawai taji babu dad'i, bataji dad'in zuwan Basma ba, a irin lokacin, gashi ta tsargu da tafiyar da yayi daga ganin Basma, anya kuwa bai santa a wani waje ba.?



Tayi shuru tunani fal a ranta, a zahiri tak`i bayyana damuwarta amna cikin zuciyarta damuwa ce fal, don Zainab ma sai da ta dameta da tambayoyi. "Yaya ya akayi wai bakon naki ya tafi."? 

"Ke bansaniba nima, dama ba nace miki bazai dad'eba ba."


Amma naji d'azu kina cewa mama, Basma ta korar miki bak'o."?

Hafsah ta zaro ido, Yaushe tayi wannan maganar.

Sai ta mik'a hannu ta d'an daki Zainab.

''Yaushe nace haka, k'arya kike."

"Hmm, wallahi Yaya na fad'a.

Ta mik'e zata hau ta da duka, Zainab ta gudu.


Sai ga Basheer ya shigo, Zainab tayi bayanshi ta boye, "Yaya, Yaya, auntynka ce zata bige ni."

"Mene haka ke, me kika yiwa Yayata."?

Ya fad'a yana matsawa gefe.

Au bazaka boyeni ba."?

Inji Zainab.

"Sai kin fad`amin me kikayiwa auntie nah."

Hafsah ta koma ta zauna,tana jinsu.

Ai kuwa da labari zo kaji Yaya.


Hafsah ta had'e rai, tana hararar Zainab, "Allah Zainab ki shiga hankalin ki fah."

Zainab tayi dariya.

Au nidin, ba zaki bari a fad`amin ba koh Yaya. Inji Bashir.


Hafsah ta harare shi shima. Yau girman ya motsa. Basheer ya fad'a, azuci.

A fili kuma sai yayi murmushi, "Zainab  ki bari zamu hadu ai zamu sa labule.!"

To Yaya. Zainab ta fada cike da tsokana tana kallon Hafsah tana mata dariya..


Bashir yasa Mufeeda ta zubo mishi abinci yana ci suna hira, acikin hirar Basheer yake cewa, "Yaya ni kuwa mun tab'a exchanging numbers da wani, wata rana mun fita har muka danyi clash da wani a mota."?

Gaban Hafsah ya fad'i da sauri tace "Toh menene."?

Basheer ya girgiza kai, "babu komai nasan dai ya kira number ta bai sameni ba kuma na duba number babu akan wayata bata hau kan email ba da nayi saving." 


Sai kawai tace Okey,  wani abin zakuyi kai da shi."?


Baya son ya fada mata ya nuna yana son wata cikin su don haka yace, A,a kawai babu dad'i ne."


Daga nan ya kawar da hirar. Zuwa wata. Ita kuwa Hafsah jikinta tayi dama ace ya kira Bashir d`in taji mai zai ce.?

___________________



Har washegari, zuwa yammaci bai kirata ba.


Ta d`an damu, don haka ta kira Zainab suyi shawara. Bayan Jan kunne da tayi wa Zainab d`in, kan koda wasa kada ta sake ta bawa Basheer labarin bak'onta..

Zainab d`in tace "Toh.


 Sannan Hafsah ta fara maganar da tafi damunta..


"Zainab kinga bai kirani ba, tun sanda ya tafi. Ta fada da 'yar damuwa.


"To Yaya ke ki kirashi mana.!!

"In kirashi."? Inji Hafsah tana d'an hararar Zainab. 

Zainab ta jinjina kai, "Eh, may be fa gwadaki yake yaga idan ma kin damu dashi, kuma tunda shi yazo wajenki you supposed to call him, irin kice ya yace gida."?

Hafsah ta tab'e baki. "Ke tafiya fa yayi babu shiri, kuma yak`i kirana, so kuma sai in kirashi, saboda zub da class."?

Yayah.. Wallah babu wani down da class zaiyi, kuma ma ai da dalili, rashin kiranki da baiyi ba, shi zaisa ki kirashi, kuma ba doguwar waya fa zakuyi ba, just irin ki nuna mishi ya yaje gida, and mai isa ya tafi don kinyi bak'uwa kinga inda ma wani abu a k'asa zaki ji ai..


Hafsah tayi shuru, cikin raba tunani, tana son ta kirashin,  don gaba-d`aya ji tayi tayi wani sabo da shi, ga kuma tasirin ganinshi da tayi, yayi mata sosai taji ya shige ranta cikin k'ank'anin lokaci, amma kuma bata son yaga zakewar ta..

Nan ta d'anyi jim cikin shawarwari....



_____________________________


Shi kwa bayan ya koma gida, tunani ya zauna yi. Me ya hadata da k'awa irin wannan, menene alak'arsu haka, yana so ya gano. Yarinyar sam kana ganinta Kasan babu tarbiyya, amma me yasa ya ganta tazo kamar  Cikin rashin hayyaci, yaji kuma tana ambatar wani, to me ya faru da ita, me wanin yayi mata, ta yuwu fa wani abun ya mata mara dad'i, kuma ta rasa gurin wa zata zo sai wajen Hafsah, in kuwa mafita tazo nema kenan Hafsah aminiyarta ce."? Tunda da amininka kake shawara. Sai yaji baya fatan abin ya zamana haka.

Yayi sauri yayi _Ta,awiziy_ saboda zargi kawai yake, bai tabbatar da ko d'aya daga cikin abubuwan da yake tunani ba, sai yaji ya dace ya sa ido, ko kuma ya d'an yi bincike game da hakan..




_ALHAMDULILLAH naga wad'ansu daga cikin copy da nayi a *clip board*, wasu kuwa sunbi ruwa especially wanda nayi tun daga yau da safe, da kuma na yamma...babu komai وما قدر الله حق قدره... Alhamdulillah alaa kulli haal.!!_👏🏼👏🏼👏🏼


Allah ya kaimu gobe.😊😇

*THNKS*

  *FOR*

  *YOUR*

  *LOVE*

       *&*

*SUPPORT.*

👍🏻👍🏻👍🏻👍🏻👍🏻




  📝 

*HAJEEYAH*

*KHAREEMERH*

[17/03, 2:42 p.m.] UMAIMA BASHEER: ♥️♥️♥️♥️

*ZAZZAFAN SO*

(masoyin k'warai)

*Cigaban littafin Zazzafan so*

*(Guba ne)*

  💔💔


*By:*

*Karima Tijjani Mansur*

*(Hajeeyah khareemerh )*

*Dedicated to Unique in your love heart group members.*



_~Am sorry readers/fans anyi mana rasuwa ne again, yayar mahaifina ce ta rasu.!!~_👏🏼👏🏼👏🏼👏🏼




📄 *55*






*Yana* cikin tunanin wayarshi tayi k'ara, ai kuwa da sauri ya duba, ganin Itace yasa shi wani murmushin jin dad`i.

Ya d'aga kiran tare da saka ear piece a kunne.


Itama ganin ya d'aga ya sa ta d'an so ta rikice, kada fa yaga zakewar ta. Amma  babu yadda zatayi ta riga ta kirashi.


A hankali ta bud'i baki tayi mishi sallama.

Ya amsa muryarshi na bayyanar da farinciki.

"Wa alykm salam."


Sukayi shuru a lokacin, shi cikin jiranta tace mishi wani abu, itama tana jiran taji ya k'ara magana.



Zainab na gefe tana mata alamu da tayi magana mana. Ta aika mata da harara sannan tace, 

Ya kake."?

Caraf ya amsa.

"Lafiya lau hope kema kina lafiya."

"Lafiya lau itama tace."

"Naji dad`in ganinki sosai fah."

Ya fad'a yana murmushi.

Tayi murmushi itama.

Ya d'ora duk da nasan ke ba haka bane koh."?

Hmm, tace mishi don bata abin cewa idan ba hakan ba.

"Hakane kenan gashi nan kin fad'a.!!

Cikin son kare kai tace, "Um Um fah.

Hmm,  ai na sani bani da kyau ko had'uwar da zan burge ki."


Hafsah tayi shuru, a zahiri. Wannan mutum yana son ya dinga sata fadar abinda batayi niyya ba. A lokacin ya dace tace mishi _kayi min mana."_ Amma kuma tana ganin kamar lokaci baiyi ba da zata fada mishi irin haka. Don haka sai ta raka zancen nashi da murmushi kawai sannan tace, "Ai baka dad'e ba ka tafi."


Yaji dad`in maganar, don wannan wata dama ce da zai gano abinda yake son gano wa.

"Ai naga kinyi bakuwa ne."

No don nayi bakuwa, sai ka tafi, itama ba dadewa tayi ba.

Yayi yar dariya, naga kamar tana son ku tattauna ne, am sorry na kula da yanayinta kamar akwai damuwa koh.. Shiyasa na barku ku tattauna."


Hafsah ta d'an tsargu, kuma har yanzu bata kai ga gano cewa, ko yasan Basma ne, bata son zargi ya shiga tsakanin su, tunda bai san tabbatar ba itama ba gama tantance halinta yayi ba, don haka ba tare da tayi wani dogon tunani ba, tayi saurin cewa. "Noo nifa na dad'e banganta ba for long.!!

"Koh."?

Taji yace,

"Yes zamuyi 2years bamu had'u ba."

Ukhasha ya d'anyi jim, baya son ya k'aryata zancenta tunda bashi da masaniya, kuma baya son yaja zancen da tsaho, amma kuma yana son yasan ainihin dalilin zuwanta toh.

"Oh am sorry naji kamar tana kiran sunan wani koh, wani abun ne ya faru."?





Anyi mata rasuwa ne brother nata shiyasa tazo tana irin haka, banjin ma, tasan tazo."


Take yaji ya yarda da ita, sai ya nuna alhinin shi, "Allah sarki Allah ya jiqanshi. Shine naji tana kiran Yusuf koh."?


Hafsah, ta waro ido, Wannan mutum bashi da mantuwa, dole tayi taka tsantsan.

Cikin k'osawar da ya fahimta a cikin muryar ta tace, "Eh."

"I'm sorry na dameki da zancen koh."?

Sai kuma ta d'anji kunya. "Tayi yar dariya.

Ya katse kiran, tuna cewa ita ta kirashi, sannan ya kirata, lokacin sun tafa ita da zainab zainab nace mata, ai dama na fad'a miki Yaya.


Ta d'aga kiran tasa a kunne, muryarshi da sanyi sosai, kuma tayi can k'asa da kyar ta fara jiyo abinda yake fad'a.


"Hafsah.!! Taji wani iri kamar yadda ta saba ji idan ya kirata da sunan ta.


Wallah ina sonki kin burge ni, sosai tun sanda na fara ganinki, bare jiya da na k'ara ganinki kinyi min sosai."


Jin zancen da yake yi, yasa ta bada hankalinta gabadaya kan abinda yake cewa, tana bukatar nutsuwa, sannan bata saba da dinga yin waya gaban wani ba, bare shi da yanzu yake mata wani irin zance, tana bukatar ta saurare shi sosai. Don Allah tayi Zainab nuni data fita.

Zainab tayi mata dariya, sannan ta noke kafad'a.

Zainab ta aika mata da harara, sannan ta mik'a hannu zata kai mata duka, Zainab ta tashi da gudu tana mata gwalo.



Baiji tace komai ba, don haka ya cigaba da magana..


_Ki yarda dani, ban taba jin ina da niyyar wasa da hankalinki ba, zan fada miki gaskiya, wallahi tunda na ganki naji kinyi min sosai, ina son kulla alak'a dake, ina son ki, kuma zan iya aurenki idan kin amince min.. 


Ya marairaice murya, "Don Allah idan har banyi miki ba, ki sanar dani, bana son in d'inga bata miki lokaci..


Thanks  for your time, gud night."


Ya kashe wayar take.






Wayar na kunnenta, ta kasa motsi bare ta cire ta, jikinta yayi sanyi da kalaman shi. 

Kanta ya kulle tamau, ta rasa wanne irin tunani ma zatayi"? Me yasa yake mata haka. laifin waye a cikinsu nata ko nashi."? Ya zaiyi mata magana irin wannan sannan ya kashe mata waya ta ke."? Tunda amsa yake nema daga wajenta to meyasa bazai jira yaji ta bakin nata ba." 

Sai kuma ta shiga kasa musu laifukan ita da shi. 

Laifinta shine jan aji. Inji wani b'angaren na zuciyarta. _"Hafsah kina ja wa mutumin nan aji sosai, yanzu ak'alla kunyi fiye da wata ke da shi, kuna waya, amma kin kasa sakin jiki da shi, magana ma doguwa bayi mishi kike ba, aganinki zai ta zama dake haka ne."?_


Tayi saurin kare kanta. _Tabbas tana da dalili lokaci baiyi ba da zata fada mishi irin abinda yake bukatar ji. Tana da buk'atar sanin wasu abubuwa muhimmai ga me da shi."_


Me yasa zai k'i sanar da ita abubuwan da ya dace ta sani game dashi."? Wannan shine laifinsa.



Na nutsa tunaninta cikin tunano shi, siffofin shi, da kuma wasu abubuwa da ta lura game dashi a had'uwar su.





_Mutumin ya hadu ba shi da makusa ta bangaren halitta. Yana da kyau matuk'a, ga kwarjini komai nashi zai iya burge ko wacce mace._


Yana da barkonci, kuma ta lura bai fiya daga kai ba ko nuna isa. Ya damu da ita matuk'a, sannan shi mai mata hidima ne  ta gani a zuwanshi wajenta. _A yadda ya nuna kenan a zahiri, don bata san ainihin cikin zuciyar shi ba. Tunda sanin gaibu sai Allah.!!_


Wata zuciyar ta tambaye ta. To me kike son ki sani banda wannan kuma."?


A zahiri ma sai da bakinta ya motsa, ta furta babu sauti. _Waye shi."?_


Tabbas akwai buqatar ta san waye shi, dan gidan waye, Matsayin karatun shi, sana,ar shi da sauran abubuwa.




Wani gefe na zuciyarta ya k'alubalenceta da cewa. Yanzu Hafsah  don zaki amshi Soyayyar mutum sai kinsan dan gidan waye."? Har da binciken aikin shi."? Anya kuwa son gaskiya kike mishi, ko ma kina son nashin kuwa."? Lokacin da kika amshi Yusuf AI baki kawo wadannan tunanukan ba sam, ko dan shi bakya sonshi shiyasa kika tsaya tantance wadannan abubuwan, Yusuf kuwa idanunki sun rufe saboda Soyayyar shi koh."?

Sai dai idan ba son gaskiya kike shirin yi mishi ba, kina da abinda kike so kawai.



Gabanta ya fad'i, bata so ace abin ya zama haka, bata son zargin ya fad'a akan cewa sonshi ne da batayi shiyasa haka. Don haka ta lalubo hujja.


_"Tabbas lokacin da ta amshi Yusuf batayi bincike ko tunani irin wannan ba, ta kalli Yusuf ne kawai a matsayin cikakke wanda ya hada komai da take buk'ata. Amma yanzu ta mallaki hankali ya dace ta tantance kafin ta zaba ko dan gudun mamaita abinda ya faru._


Abinda kike son sani wannan bincikene na iyaye ba naki ba. Kawai in zaki amshi soyayya ki amsa, da wuri don shima ya nuna ya gaji da baki lokacin shi.


To idan na shirya amsa ta yaya zan nuna mishi.? Yayi magana bai jira cewata ba ya kashe waya.!! 

Ta tambayi kanta.


_Akwai sauran dama.!!_ Ai bacewa yayi ya daina kiranki daga yau ba, kuma dole ki nemo hanyar da zaki nuna mishi kin amince da shi yadda zai fahimta.






Wayar da ke kunnenta ta shiga k'arar da tasa ta dawo daga tunanin ta take ta kullawa a zuciyar ta.


Tayi saurin zare wayar, sunan Jamila ta gani. 


Ta saki ajiyar zuciya, ta daga kiran.


Hello."

Jamila tace.

Itama ta amsa da Hello

Jamila kina lafiya.

Cikin muryar ta da dama ta dad'e da chanjawa, tace, "I'm fine. "Ya mutanen gidan ya mum."?

Hafsah taji dad`in hakan..

Lafiya lau." tace tana dan murmushi tace, "Bayan kince zaki zo baki zo d`in ba."?

Wallah babu time ne, ina ta son inzo, but zaki ganni, savoda zanje Dubai nan da two weeks so zan shigo unguwar kafin na tafi."


Gaban Hafsah ya fad'i. "Dubai kuma."?

"Kada dai Jamila tayi shaharar zama _International."_


Don haka taga asarar barin Jamila batare da ta nemi k'arin bayani ba. Da sauri tace.

Dubai me zaki je yi Dubai."?

"Zanyi rakiya ne."!! Jamila tayi magana tana wata 'yar siririyar dariya.

Kan Hafsah yayi wata iriyar sarawa.

Tana son ta k'ara tambayar Jamila, _Wa zata raka haka."?_ 

Amma kuma bata son Jamilar taga kamar tana binciken ta ne. Don haka tayi shuru kawai.

Sai ta juyo Jamila na cewa. "Thank you, ki gaida mama, bari na d'aga wani kira.

"Okay thank you bye bye.

Hafsah tace...







     📝 

*HAJEEEYAH KHAREEMERH*

[17/03, 2:46 p.m.] UMAIMA BASHEER: ♥️♥️♥️♥️

*ZAZZAFAN SO*

(Masoyin k'warai)

*Cigaban littafin Zazzafan so (Guba ne)*

💔💔


 *By*

*Karima Tijjani Mansur*

*(Hajeeyah Khareemerh)*

*Dedicated to unique in your love heart*




📄 *56*




_NAILA group 1 ina godia da Soyayyar ku... Espclly #ummita_😊😊

_Sayyada_ kema Inayinki. (NAILA group 2)

 

*Team Ukhasha 

*Team Hafsah.

Inajin dad`in comment d'inku.💃🏼💃🏼💃🏼



*Ranar* da ta biyo baya, bai kirata ba sam tun daga safiya har wata wayewar garin.


Hafsah ta sanya kanta cikin tsarguwa. Amma kuma tanajin ba zata iya kiranshi ba.



___________________

Yau gaba d'aya busy yake, abubuwa sun mishi yawa, bayan dawowar shi daga office, yayanshi Dr. Sunusi yace ya same shi a gida, zasu tattauna.


Yana dawowa abinci kawai yaci, yayi wanka sannan yayiwa Hajiya sallama ya wuce.




Bayan hira da sukayi ta zumunci, Dr. Sunusi ya bujurowa da Ukhasha maganar da yasa ya kirashi.


"Ukhasha."!!

Ukhashatu ya amsa.

"Naam Yaya.!!

Dama wata _share_ ce zan maka talla ko zaka sa kud'inka kaima aciki.. 


Ukhashatu ya bada gaba d'ayan hankalinshi ga yayan nashi.


Dr. Sunusi ya cigaba da magana.


Wani d'an k'aramin company ne, na had`in guiwa mukeso mu bude ni da abokai na mu shidda, to kuma mun duba munga muna da buk'atar k'arin kud'i shine muke bukatar k'arin mutum d'aya.


Ukhasha ya gyara zama. Okey Yaya, kamar nawa ake buk'atar kowa ya saka."?


Ba wai bukata ake kowa sai yasaka daidai da na kowa ba. Zaka iya saka ko nawa kake dashi kawai, tunda za,a dinga raba ribar ne, daidai da yadda kudin mutum yake aciki.


Ukhashatu ya jinjina kai, Okey na gane Yaya, amma kamar nawa kake ganin ni zansa."?

Um..To." Inji Doctor. Sannan ya kalli ukhashatu.

Zaka iya saka 4million, ko da rabi ma.!!


Ukhasha yayi murmushin gefen kunci.


"Doctor, ansan nauyin aljihun fah.

Na sani.!

Inji Dr Sunusi yana murmushi shima.

"Ka saka  4million d`in dai."

Ukhasha yayi ajiyar zuciya a hankali, Dr. ya kalle shi da  alamar tambaya. Ukhasha yace, "da inada wani lissafi da nakeyi ne."


Dr. Sunusi yayi murmushi, wanne tunani kuma."?


Ukhashatu ya sunkuyar da kai, yana shiga matsa k'afar shi, dama a kasa suke dukan su a zaune.

Dariya ya bawa, Dr. ma sai da ya gama dariyar sannan yayi magana.


Aure zakayi."? Bai barshi ya bada amsa ba ya d'ora.

Ka gaji da zaman gwaurontakar kenan...

Ukhasha yayi wani dan murmushi. "A,a fa Yaya."

To mene tunanin naka idan ba shi ba.

Yayi shuru, don bashi da amsa.

Hmm, yanzu dai ka nemo, 4m. kawai kaidai, zamuji dad`in abin fa idan ya kankama.

Okey in sha Allah."

Inji Ukhasha.

Zuwa Yaushe za,a karbi kud'in.

Nan da wata d'aya muke son mu fara shirya komai, amma   muna yin meeting akan yadda abin zai kankama, gobe ma muna dashi, da daddare sai ka shigo muje.!!


Okey, in sha Allah.


Am naji Hajiya na cewa zatayi retire koh."?


"Eh haka tace, nan da wata d'aya ne."

Gud, ai gwara ta huta.!! Inji Dr. Sannan ya shiga wata maganar.

"Yaushe ma Abba yace zamuje gidan gonar nan don na manta.

Nan da sati d'aya ne." Cewar ukhasha.

Ai abin ne da yawa abubuwan sunyi yawa.

"Ana kokari ai."

Inji ukhashatu, Naji yace yana so ne, ya k'ara fad'ad'a wajen."

"Yayi kyau hakan ai, kaga ya dad'e bai je duba gurin ba fah.

Ukhasha ya jinjina kai, "Eh  amma 

"yana tura ni akai-akai ai, kuma naga babu laifi ma,aikatan suna kula da wajen yadda ya dace.!! 

So ko zamu bude namu d'an k'aramine haka koda iya kaji ne, da kifi sai mu saka. Cewar Doctor yana dariya.

Ukhasha ya taya shi dariyar shima. "Hmm Doctor kenan.!!

Cikin nutsuwa yake jawo hakalin Ukhashatu kan abin da cewa, "Ina da wani tunanine, kuma dana bujurowa da Abba shi naga ya nuna jin dad'inshi har ya sanyawa abin albarka ma."

Ukhashatu ya kalle shi irin kallon neman k'arin bayani.

Cikin nutsuwa doctor yace, inaso mu bude wani kasuwanci dukanmu har matan ma, kai hatta mahseem sai ansa mata nata kason aciki.!

Ukhashatu ya waro ido.

Doctor ya jinjina kai, Yes, wannan zai kara kawo had`inkai, sannan kuma gaba ake ji ba baya ba."

Ukhashatu ya jinjina kai. "Hakane..abun yayi kyau.

Baka ga yadda Abba ya d`auki abin ba, daga yi mishi zancen ni na zaci ma yayi  maka zancen.

Ukhashatu ya girgiza kai.

"A,a" Amma waye zai sawa su yaran tunda kace har Mahseem."?

Doctor yace yana dariya. "Abba ne.!! Kuma ai ba wani abu mai yawa zai maka musu ba, tunda kasuwanci ne irin na kayan amfani  irin na kasuwa da kadan zamu fara, kuma za,a saka equal ne babu mace babu namiji kowa _one hundred thousand._ Yayi kyau Yaya Allah ya bar zumunci ya taimake mu, Allah ya taimaki Abban."


"Amiin ya Allah. Inji Dr. Sannan ya kuma kallon Ukhashatu.





A ina ka sami yarinyar ne."?

Ukhasha yayi saurin bude baki, "Am ai bamu gama daidaitawa da ita bama."

"Hmm, koh.."? Baka sanarwa da su Abba  ba kenan."?

Ukhashatu ya daga kai alamar, "Eh."

Cikin nutsuwa doctor yake nusar dashi. "Kayi kokari dai, kayi abinda zai farantawa su Abba."

Ukhashatu ya gyada kai, In sha Allah, bamu dad'e da sanin juna bane shiyasa."

Okey, nagane Allah ya tabbatar da alkhairi.!

"Amin Yaya. Sannan ya duba  agogon hannunshi, "Bari na tafi dare yayi yaya.

Okey, ba zaka shiga cikin ku gaisa ba."?

To bari na shiga naga 'yar rigima.


Sukayi dariya sannan suka mik'e a tare.





Suka shiga da sallama. Fadeel na jin muryar auncle ya taho da gudu yana murna "uncle!! uncle!! Ukhashatu ya d`auke shi, ya daga shi sama suna dariya.

"Kaii Kaii Kaii." kai fa ka girma yanzu, kayi nauyi "Ya Fadeel zan daina d'aukarka kai da "Ãrif. Na'eemah kawai zan dinga d'auka.!! Ukhashatu ya fad'a sanda yake sauke shi.

Suka zauna a Kujera yaron ya zauna kusa da shi."

"Uncle su sunyi bacci."

"Kai meyasa bakayi bacci ba toh."?

"Assignment nake yi, nima yanzu zanyi bacci, aunty dinmu tace ina da k'ok'ari!!

Allah, ai na sani dama _my boy is a gifted.!!_

Suka tafa shida Fadeel d`in suna dariya.


"Au uncle ina yini."?

Inji Fadeel harda d'an rank'wafawa. Doctor da Ukhashatu suka sheke da dariya, doctor yace, "Au sai yanzu aka tuna da gaisuwar."?

"Mantawa nayi Abba.!! Inji Fadeel.

To Lafiya lau, Fadeel d`ina kana lafiya."? Inji ukhashatu. 

Lafiya lau uncle.


Suna cikin haka, maman yaran ta fito daga d'aki.

Au Engr. Sai yanzu kenan ka shigo koh."?

Afwan auntie ina yini."?

Lafiya lau, yasu Hajiya da Abba."?

Lafiya lau suke."?

Ta dan sami guri ta zauna.

"To yasu Fadwa M aryam, kwana biyu basu lek'oni ba."

"Suna nan kalau, bari na wuce ma kada dare yayi min."

Daga shigowa kuma."? Inji aunty Jamila. 

"Dare ne zaiyi min shiyasa"

Eh, kuma kazo kawar taka na bacci koh."?

Eh fa, ai gobe ma zan dawo in sha Allah."

"Tom sai kazo d`in.

Ya mik'e Fadeel ma ya mik'e ya rik'e hannunshi.

Ya kalli, yayanshi. Sai da safe yaya."

Tom ka gaida gida ukhashatu sai goben, ka gaida su Abba da hajiya.

Zasuji, yace, sannan ya juya ga aunty Jamila, Tom aunty sai da safe, Allah ya tashe mu lafiya, agaida Hajiya da mama."

"Zasuji sosai, yace.

Ta kamo hannun Fadeel, oh baby zo kaje ka kwanta kaji.

Ya noke k'afada "A,a ni uncle zan bi."

Ukhashatu yayi dariya, Aa aboki ka bari gobe zan dawo sai muje gidan Abba  amma yanzu kaga dare yayi koh."

Ya daga kai, a sanyaye da alama bai so ba."

Ukhashatu ya sake shi, sannan ya laluba aljihun shi babu, ya zaro 500. "Ungo Aboki."

Ya damk'awa yaron.

Asai chocolate yau na manta ban taho dashi ba.

Yaron yasa hannu biyu ya k'arba yana murna.

Thank you auncle, ka gaida gida.

Aunty Jamila tace, Allah dama ukhasha shiyasa yaran nan suke makale maka, ka daina basu kudi don Allah idan babu alawa a hak'ura.

Yayi murmushi kawai, yana dagawa yaron hannu "Bye bye.

Shima yaron ya daga mishi "Bye bye uncle gud night.!!

Ukhasha ya fita yana murmushi.






__________________

Daya koma gida, 11 na dare ta wuce, kafin yayi wasu al,adu da ya saba kafin kwanciya bacci har sha biyu tayi. Dole ya hakura da kiranta da yayi niyya. Gashi ya gaji likis, yana kwanciya babu jimawa bacci ya d`auke shi mai cike da mafarkanta..




_________________

Tana ta sak'awa da kwancewa akan neman dalilin rashin jin shi gaba-d`aya yau, amma tunanin ta yafi fad'awa kan cewa ya gaji ne, ya yanke hukunci. Hankalinta ya dugunzuma, meyasa bata mishi koda SMS bane bayan wayar da sukayi. Ta shiga yiwa kanta fad'a, tabbatas da gaskiya r shi, su fa ba yara bane 'yan secondary da zata dinga yi mishi abubuwa irin haka.

Dole ne, ta sami hanyoyin fahimtar dashi abinda take ji game dashi.

Ta lalubi wayarta, akan wayar taga dare yayi har k'arfe 11:30pm, taji kamar ta mishi text da _I love you.!_ har ta shiga wajen yin typing message, sai kuma taja dan siririn tsaki, ta fasa.


Sai ta bige da kunna Data, kai tsaye ta shiga wajen sunanshi. Taga rabon da suyi hira, tun randa ya roketa zaizo wajenta, asama taga _last seen_ dinshi k'arfe tun 9:30 na dare.

Nan ma zatayi mishi magana sai kuma ta fasa. 


Ta duba profile d'inshi babu komai ma akai ya cire, takaici ya kamata dama bata taba ganin yasa photonshi ba kamar yadda itama bata sawa kodan mutane. 


Ganin tana bata lokutan ta, akan bibiyarshi da tunaninshi yasa ta matse wayar tata ta kashe ta, gaba-d`aya. Sannan ta nutse kanta cikin bargo wai ita dole sai tayi bacci. Dama kuma tana da fita gobe tana da wani aiki da sassafe.

Data rufe idon sai taji tana son tunano kamannin shi, ji tayi ta kasa, amma abin mamaki sai ta shiga yiwa kanta dole, da haka tayi bacci.




______________

Kwance take ta nutsa kanta cikin pillow tana risgar kuka, ji take duk duniya babu wanda ya kaita bak'in ciki. Gashi a yau d`in dai gaba-d`aya wayoyinta abbanta ya karb'e, ta rasa wanne irin abun bakin ciki ya same ta haka, duk wani da zatayi _sharing_ damuwarta yau ita dashi babu hanya, banda takunkumin hana fita da abbanta ya saka mata, sannan ya dad'a da kwace wayoyinta.?

Duk bayan minti sai ta tuno da wasu bakaken kalamai da sukafi komai muni a xuciyarta wato.

_"Basma yau dai Allah yayi ikonshi na bada ke, in sha Allah aurenki saura wata biyu, kiyi hak'uri kiyi min biyayya, ina kyautata zaton banyi miki zaben tumun dare ba.!!_

Ya had'e rai sannan ya mik'a mata hannu. 

"Bani wayoyinki duka.!!

"Zan baki amma sai lokacin da aka d'aura miki aure.!!"




Tuno wad'annan kalamai da suke muna na, a kunnenta yasa ta bude baki ta kwalla wata muguwar k'ara, wacce lokaci guda kuma tayi saurin toshe bakinta, tuno cewa abbanta na iya jiyo ta, kuma babu abinda zai hanashi hukuntata, koda kuwa da duka ne, don ta kaishi bango.

A hankali take zubar da hawaye tana wani marayan kuka, tana kiran mamanta. Har muryata ta dashe, amma bata daina ba, sai da ta raba dare, sannan dakyar bacci ya sace ta..



_______________


Yau da wuri, ya tashi, bayan ya dawo daga masallaci, ya wuce d'akin abbansu don ya gaida shi.


_Khaady_ Yana zaune yana jan doguwar tasbaharashi, gefe kuma ga wasu manyan litattafai kusa dashi, sai kuma al'Qurani mai girma. Yau shima yana da wata shari,a da yake saka ran yanke hukunci a yau.


Ukhasha yayi sallama, _khadi_ ya amsa.

Sannan ya shiga gaida shi.

"Abba barka da asuba." Cikin sakin fuska ya amsa.

Barka dai malam, ( _kamar yadda yake kiranshi wani lokacin._) an tashi lafiya? 

"Lafiya lau, Akaramakallahu."

"To Masha Allah.





Ukhasha ya k'ara duk'ar da kai sannan yayi magana cikin nutsuwa.


"Abba!! yaya ne yayi min magana akan wani d'an company da zasu bud'e shida abokan shi."

Khady ya bada hankalin yana sauraron shi.

Ukhasha ya cigaba.


"To yace idan ina so nima zan iya saka nawa kud'in."


Khady ya nunfasa sannan ya fara magana, "Eh nasan da zancen, ya fad'a min zasu bud'e companyn sarrafa shinkafa ne koh."?

Ukhashatu ya gyad'a kai, "Eh shine."

"Yayi kyau hakan, nawa zaka saka aciki kai."? Cewar Khady yana kallon Ukhashatu.

Cikin ladabi Ukhasha yace, "Shine nake so a bani shawara Abba."


Khady yayi yar dariya, sannan yace, _malam_ kenan, "To ai  shawara na wajenka, kai kasan nawa zaka iya sawa."


Ukhasha ya d'anyi murmushi, ya sosa kai.


Cikin Hikima Khady yace, "To komai dai za,ayi ayi daidai misali dai, yadda ba za,a takura ba, idan Allah ya sawa abin albarka sai kuga yana ta hab'aka."


Ukhashatu ya jinjina kai.

"Shi nawa yace ka kawo."? Khady ya tambaya.

"Bai kayyade min ba, amma ya bani shawara.

Yace ka saka nawa.

"Million hud'u." Ukhasha ya fad'a yana sunkuyar dakai.

Khady yayi dariya me d'an tsaho.


"Kana da million hud'u Ukhashatu."?

Ukhashatu ya hau shafa kai.

Khady ya cigaba da magana.

"Amma baka fara ginin ka ba koh."?


Ukhasha yayi tsit, saboda anzo wajen.


Khady ya takaita zancen da cewa, "Ka saka million uku kaga babu takura koh, tunda shima million shidda ya bada."


"Nagode, Abba Allah ya k'ara girma."

Ya shiga godiya kamar wanda akayi wa kyauta.


Sannan cikin nutsuwa Khady ya kira sunanshi. "Ukhashatu!! 

Ya amsa a sanyaye.

"Na,am Abba."

Khady bai jira komai ba ya fara maganar da zaiyi.

"Basai an fad'amin ba, nasan kana da isassun kud'in da zaka fara gini, idan aure ya zo maka ma  kuma kayi shi, hakane koh."?


_Yana sane ya maida zancen salon tambaya._


Cikin sanyi Ukhasha ya hau gyad'a kai.


"To ka samu ka fara gininka cikin watan nan. Abba ya fad'a yana d`auke murmushin fuskar shi don Ukhasha ya san bada wasa yake mishi ba.


Cikin ladabi ya shiga d'aga kai, zanyi Abba in sha Allah, a taya mu da addu,a."


"Addu,a ai kullum cikin yi muku ita ake Ukhasha kuma in sha Allah, Allah yana amsawa."


Ukhasha, ya motsa kamar zai mik'e don yin sallama da Abba ya tafi, yaji Abban na wata magana.


"Kaji yau in sha Allah, masu kawo lefen maryam zasu zo koh, kuma za,ayi bikin cikin sati uku"


"Allah ya sanya alkhairi Abba. Inji Ukhashatu.


Amiin ya allah, Khady ya fad'a yana k'ara kallon Ukhasha kamar zai mishi magana, sai kuma bai ce komai ba. Shi kanshi Ukhasha a tsarge yake, Allah-Allah kawai yake a sallame shi ya tafi.


Sai kuma ya tsinkayi abban nacewa, "Yau baka je daukar karatun ba ne."? ( _yana nufin makarantar manya da Ukhasha yake zuwa da asuba, a wani masallaci kusa da su_)

Yayi murmushin jin dad'i, don bai zaci haka abban zaice mishi ba.

Eh Abba, yau ana idar da sallah gida na yo, saboda inason zan fita da wuri.

"Khady ya gyada kai, amma gashi ka b'ata lokaci anan.


Ukhashatu yayi yar dariya, "Aa, Abba, dama inason ganawa da kai d`in.

To yayi kyau tashi maza kada a makara.

Ukhasha ya mik'e.

Nagode Abba a huta lafiya.

Khady yayi murmushi yana bin shi da kallo.




_____________

Fitowar ta daga wanka, kenan tana goge jikinta da towel, wayarta ta shiga yin d'an kida.

Batayi mamaki ba don tayi zaton abokan aiki ke neman ta.


Tayi saurin k'arasawa inda wayar take don dubawa ta d'aga.


Wata iriyar faduwa gaba taji, wacce sai da ta d'an had'a da da fe k'irjinta.

Cikin mamaki tayi saurin d'agawa zuciyarta tana cewa, lafiya kuma kiranshi da sassafe."?

Cikin sanyin murya tayi sallama, sai kuma taji shi muryarshi ras ya amsa mata.

Hakan yasa taji babu wata ragowar damuwa a tattare da ita.

Ranki ya dad'e Barka da safiya, Allah yasa dai bani na tasheki ba da safenan.

Ya fada da nutsuwar murya kamar ko yaushe, wanda tunda ya fara magana take murmushin boye, na jin dad`in muryarshi.

Uhum."?

Taji yace, ta kalli kanta, daga ita sai towel,  sai taji tana jin kunya gani takeyi kamar zai gano ta.


Tayi murmushi mai sauti, dayaji shi sosai har cikin jininshi.


Ga mamakinshi sai yaji tace, ka tashi lafiya."?

Ta gano farinciki tsababa cikin muryarshi sanda yake amsa mata.

"Lafiya lau _my queen,_ ai  da tunaninki na tashi.

Tayi murmushi itama.

Jiya bamuyi waya ba, ji nake kamar mun shekara."

Itama a zuciyarta haka ne amma bata furta komai ba sai murmushi.


Cikin rage sauti yace mata, I miss you dear, you do miss me too."?

Ya fad'a kamar rad'a.

Babu wani tunani ko bata lokaci taji bakinta ya furta _"yeah!!."_

Ukhasha tsaye yake, amma babu shiri ya zauna, a gefen gado.


Really."? Yace mata cikin taushin murya.

Ta toshe bakinta, tana yar dariya, tuno abinda bakinta ya fad'a.


"I have to go to work earlier today, ina son in shirya."

Ta fa ke da fadar haka.

"Dariya, yayi mata shima, yasan dalilinta na fad'ar haka, "me too."

Yace mata, kinga nima shiri nake, amma ina son inji ki..  

"bazan iya aiki ba idan banji muryarki ki da safen nan ba."

Tayi murmushin jin dad`in kalaman shi.

Lokaci d'aya kuma taji yace, kada na tsaida ke koh, bye."


Itama "OK bye" tace mishi.

Ya k'ara mata da "I love you."

To fa anzo wajen sai tayi tsit kamar babu ita.

A hankali taji yace mata, "Kinji."?

"Um." tace mishi.

Cikin marairaice murya ya ce, to ni me zaki ce min."?

Tayi shuru tana tunanowa, wato yau dai k'ure ta zaiyi.

Uhum."?

Ya k'ara tambayar ta.

"Thank you!! tace mishi.

Yayi kamar baiji ta ba, ya d'ora da.

"please Say you love me too, please Hafsah.!!

Ta nemi guri itama babu shiri ta zauna jin yanayin muryarshi.

"Please!! taji ya k'ara fad'a.


Nan ma shuru tayi, 

please Hafsah ki taimake ni!! Ya fad'a murya can k'asa sosai.

(Kiran sunanta da yake ba k'aramin tasiri yake ba.)


"Nan ta shiga tunani akan ta fad'a ko kada ta fad'a."?


Cikin sanyi ta juyo shi, yana cewa "Okey can't you."?

Bata son su kuma maimaita irin na rannan, don haka da sauri wanda shima babu zatonshi yaji tace, _"me too."!!_


a k'age yace, "You too  what.."?

Hmm, tace.

"Ki daina min rowa don Allah wallah kina wahalar dani.!!


Tayi jim na wasu muntuna tana hasashe.


ta jiyo shi yana cewa, idan nine bazan kasa fad'a miki ina sonki ba, wallah I love you with all my heart Hafsah.


Da alama zancen zuci yake, ta fahimci wasu abubuwan suna zuwa bikinshi ne batare da niyyar shi tayin hakan ba, haka kuwa na nuni da zallar soyayyarta ne cikin zuciyarshi.


murya na d'an karkarwa tace don ta huta itama, _ilove you too.!!_



Zo ki ga farin ciki gurin ukhasha, har sai da ya zame ya kwanta.

Yana rik'e da wayar amma yayi shuru.

Itama wani iri take ji, har wani zif-zif take ji a jikinta.

_Anya kuwa tayi wa kanta daidai.?_


Sai da ya gama saita kanshi sannan ya sauke wata ajiyar zuciya a hankali yace, "Nagode, "Nagode Hafsah, in sha Allah by time zaki fahimci irin son da nake miki, kuma in sha Allah bazan taba baki kunya ba, zakiyi farin ciki dani.

Thank you.!!

Ita dai bata da bakin magana, ya san ba zatayi d`in ba, don haka yace..

"Hafsah.! A hankali.

Ta kasa amsawa don bata son ya k'ara jin muryarta a lokacin saboda kunyarshi.


"Ina sonki." taji yace mata, maganar da ta k'ara kashe mata jiki.


Ki shirya kinji, kada na saki kiyi late.. nagode, Allah ya tsare min ke."


Babu sauti amma ta motsa bakinta wajen cewa, "AMIIN."

Don taji dad`in kalaman shi.


Tanajin karar katse kiran shi amma bata motsa ba, ji take kamar ta sauke wani nauyi daga kanta, haka kawai ta yardarwa zuciyar ta, ukhashatu ba k'aramin sonta yake ba, daga jin muryar shi zaka tabbatar da haka.


A hankali ta motsa ta d`auki mai da niyyar shafawa, gaba-d`aya ji take kamar an kwashe mata duk wani _energy_ da ke jikin ta.


A sanyaye ta dinga yin komai, gefe kuma na zuciyarta tana mamakin kanta, da kuma tuhumar kanta kan kalmar da ta furta da sanyin safiyar nan.


Azuciyar ta take fata, _"Allah yasa takai Soyayyar ta inda zata sami kulawa, ba inda za,a cutar da ita ba."_


Bata sami nutsuwa ba, har sai da raunin da jiki da zuciyarta yayi ya kaita da fitar da wata 'yar kwalla, sai da ta goge a hankali, sannan taji ta sami k'wari.



Tun bakwai take shiri, amma saida nawa ta kaita har k'arfe takwas, hakan yasa mama biyota.


Ta ganta zaune ta gama saka kaya, tana d'aura d'ankwali.


Yaya, me kikeyi hakane, keda kika ce da wuri zaki fita kinga takwas har tayi fa.


Ita kanta ba zatace ga abinda ya tsaida ta d`in ba.

"Na gama mama."

"Kiyi sauri kizo kiyi break dai."

Ta gyada kai.

Gani nan mama."


Maman ta juya itama ta fita.





Ukhashatu, tsahon ranar yinin farin ciki yayi, jiyake babu wanda ya kaishi farin ciki a yau. Godiya yake kawai ga Allah don shi ya mallaka mishi ita. Zuciyar shi cike take fal da tsare tsaren yadda rayuwar su zata kasance shida ita.


Bai iya jurewa ba, har sai da kira wayarta da azahar amma Hafsah taki d'agawa, ji take bazata iya mishi magana a yau ba.


Yayi murmushi lokacin da kiran ya yanke.

Kawai sai ya zana mata _text messages_

_"Hmm, dole kik'i daga waya mana dama, kin rikita bawan Allah, kin barshi a rikice kuma.!!_


Text d`in dariya ya bata, ta dinga yinta, har abokiyar aikinta na tambayarta "meke faruwa."?

Sai kuma ta dinga jin kamar da ita yake, domin itace a rikice ai, tun safiyar yau."


Don ta kare kanta ta aika mishi da, _lots of work dear, let's phone to night.!!_


Sanda ya ida karantawa, sai da ya maimaita kalmar _Dear_ a fili.

Ya dinga murmushi shi kad'ai shima, yana fatan daren yayi da sauri.

Amma murnarshi ta koma ciki, daya tuna yana da meeting da daddaren..




    📝 

*HAJEEEYAH KHAREEMERH*

[17/03, 2:48 p.m.] UMAIMA BASHEER: ♥️♥️♥️♥️

*ZAZZAFAN SO*

(Masoyin k'warai)

*Cigaban littafin Zazzafan so (Guba ne)*

💔💔


 *By*

*Karima Tijjani Mansur*

*(Hajeeyah Khareemerh)*

*Dedicated to unique in your love heart*





📄 *57*




____________________

Bai samu ya kuma kiranta ba a ranar, itama kuma sai taji tana da jiran kiranshi, amma bai kirata ba, haka ta hakura har zuwan lokacin baccinta.


Tana mamakin dalilin daya tare shi ga barin kiran nata.




Ranar data biyo baya, sukayi waya, dole ta saki jiki da shi, saboda salon shi, gareta. Duk wani abu da ukhasha zaiyi ya tabbatar mata da son da yake mata yayi shi, wani ta mayar mishi wani kuma ta bishi da murmushi ko tayi shuru, don yanzu ta gama fahimtar dawa take tare. _Wato shi mutum ne daya k'ware a ko ina, yana matuk'ar son yaga ya sakata farinciki kuma._

Daga k'arshe  yake rok'onta akan ta barshi ya k'ara zuwa ya ganta.

Da take tambayar shi, yaushe yake so ce mata yayi.

Ko yaushe kika ce nazo zaki ganni."


Tayi dariya Kawai sannan tace, Aa dai mu bari sai k'arshen sati."

"Babu musu ya amince.

Allah ya kaimu lokacin."

Amiin tace mishi.



___________________


Shiri sosai Hafsah ta dinga yi ranar da ya kama zai zo d`in.


 Har tunani ta shiga yi, me ya dace tayi mishi na tarbarshi."



Ta kasa tunana komai, k'arshe ta yanke shawarar bashi lemo da snacks kawai tunda suna da shi.


Shiri tayi alwashin yi sosai akan zuwan na shi. Ba su kara yin waya ba tun bayan wayar da sukayi, da rana.




Wani abu da ya da ya wargazawa Hafsah shiri, wanda badon zuwan Ukhasha ba babu abinda zatayi farinciki dashi kamar shi, amma sai zuciyarta ta kasu biyu gefe na jin dad`in hakan gefe kuma naga tunanin gudun samun matsala. Wato abin ba komai bane fa ce zuwan _Jamila_ a ranar.



Misalin k'arfe uku da rabi daidai na yamma, lokacin Hafsah na cikin toilet, don tayi alwashin shiryawa da wuri, ba zata b'ata mishi lokaci ba, sannan tayi alwashin zata nuna mishi soyayya daidai gwargwado yadda zai fahimci tana son shi itama.



Tana cikin band'akin taji sallama daga palourn mama kamar anyi bak'uwa.  Bata damu ba take wankan ta a tsanake.


A falon kuma, mama ce zaune ita da mufida, tana mata tausa a k'afa, sukaji anyi sallama da wata iriyar muryar da ta sakasu juyawa duka, don basu gane wanene mai muryar ba.


Mama wata hamshak'iyar  babbar mace ta gani, a cikin falonta, wacce ita a ganinta tafi mata kama da irin mata 'yan siyasa.



Mufida kuwa idonta ne yayi wani harr, sai da mai sallamar ta k'aras Shigowa sannan ta gane ta, don sun ganta Kwanaki ita da su yaya Hafsah.


Mama ce tace mata, "sannu da zuwa, zauna mana."

Ta tsuguna ta gaida maman kafin ta zauna a kujerar da aka bata.

Abun ya bawa mama mamaki matuk'a, kafin ta kai ga tambayarta wacece, ita taji tanacewa.

Mama, Hafsah na nan."?

Eh tana nan inji mama, tana k'ara kallon Jamila.


Sannan ta kalli mufida, "Jeki ki kira Hafsan."


Maman taga alamun kamar mufida tasan bak'uwar, amma babu damar ta tambaye ta, sannan da taji wajen Hafsah  tazo, sai tafi alak'antata da abokan aikin Hafsah. Amma kuma taji kamar tasan muryar, amma ta manta a ina."?


Sanda mufida ta shigo d'akin hafsah na shirin fitowa daga toilet d`in, don haka ta d'an jirata ta fito.

"Yaya kinyi bak'uwa.

Hafsah na tsane ruwan jikinta da wani towel d`in banda wanda ta d'aura, ta kalli mufida. "Bak'uwa kuma."?

"Eh, Wannan da muka gani  a park dinnan ce.!

Gaban Hafsah yayi wata iriyar bugawa.

"Toh, jamila!!

Ta fad'a a hankali.

Sannan ta goge fuskarta kafin ta kuma cewa, "Kice ina zuwa bari na shirya."


Tunda aka, fad'a mata zuwan bak'uwar taji jikinta yayi sanyi.


Da kyar ta tattaro nutsuwa, ta shafa mai sannan ta dakko kayan da tayi niyyar sakawa tasa.


Bata tsaya shafa ko da powder ba, shima kafin ta k'arasa sai da mama ta leko ta.

"Hafsah kiyi sauri mana kin barta tana jiranki."?


"Mama gani nan, yanzu zan fito." Ta bada amsa da haka.

Maman ta k'ara kallonta sannan ta juya ta fita.



Leshin ya amshe ta sosai, tayi kyau duk da bata shafa komai ba, d'an kunne da agogo kawai ta saka, sannan ta fito palourn bayan tayi amfani da turarukan ta.


A palourn sunyi shuru, duka, sai Jamila da jefi jefi take kallon wasu shashi na palourn.

Gidan ya chanja sosai ba kamar yadda tasan shi da ba, an sami cigaba a tsarin gidan da komai ma.



Mama ce ta gaji da hasashen son gano wacece, don haka ta kalli Jamila tana murmushi tace, "Um kema wajen aikin naku d'aya da Hafasan ne."?


Jamila tayi yar dariya sannan tace, Aa, mama baki ganeni ba koh."?

Mama ta jinjina kai, naga kamar na san fuskar koh kina zuwa gidan ne.

Babu jiran komai Jamila tace, "Mama Jamila ce fah."

 Tana murmushi.





Mama kallonta ta tsayi sosai, kallon mamaki da tambayoyi, da k'yar ta d`auke ido, tace tana 'yar dariya.


Laa, ai ban ganeki ba sam, ashe kece."

Daga nan ta rufe bakinta.


A Kofar shigowa daga waje ta palourn, Basheer ne ya shigo da sallama.

Mama ta amsa mishi, ya k'araso ciki, daidai lokacin kuma Hafsah itama ta fito daga d'akinta tana takowa zuwa cikin palourn.


Sai da Basheer yazo Tsakiyar palourn sannan yaga fuskar bak'uwar don kujerar da take kai cikin falon take kallowa, sai kuma yaga Hafsah ta fito tana fara,a cikin shigar da tafi kama data fita, badon bata saka mayafi ba, sannan yaji cikin fara,a tana ambaton  sunan Jamila.


"Ah, Jamila Sannu da zuwa ashe kece.!!


Maganar data saka Basheer, juyawa ya kalli Jamila sosai.



Ta ganshi itama. Amma basu yiwa juna magana ba, ya nemi guri a kujera 1 _seater_ ya zauna.


Yana bin Hafsah da wani kallo na tuhuma lokacin da take cewaJamila, "shigo ciki mana."

Jamila ta mik'e ta bita. Mama bata ce  musu komai ba sai kallo da tabi Jamila da shi, sannan ta k'ara sauke kallon akan Basheer.


Suna nesa dasu, bakin Basheer ya bude rai a b'ace yace, "Mama wai meyasa Yaya zata dinga yin irin haka ne."


Mama ta gane akan me yake magana, amma sai ta cigaba da kallonshi don neman k'arin bayani.



Meyasa dole tace sai ta kula waccan, bata ganin yanzu ba da bace, kinga ta gayyato mana ita gida koh."?


Mama ta danyi murmushi sannan tace, "Haba Basheer ai ba,a gudun mutum a duk halin da yake ciki, kuma ni yarinyar shekarunta nawa rabon da ka ganta a nan gidan, tun sanda akace _tabar gidansu fah._ Ba yawo sukayi da yayarka ba bare kace janta take suna fita."


Basheer ya sake bata rai, "Nidai mama bana son tana kulata bare har ta dinga zuwar mana gida, dama na sani tun ranar da muka ganta a park, Yaya ta wani rikice data ganta, saida taje sukayi magana sannan taji dad`i, shine fa sukayi exchange numbers"


Mama ta d'anyi shuru kafin tace, "Ba fad'a ya dace kayi ba, bayani zakayi mata yadda zata fahimta, amma ka fara zuba ido kaga tunda ai yau ka fara ganin tazo gidan koh."? Kuma ko babu komai Hafsah fa yayarka ce dole ka bi ta a hankali."


Basheer yayi shuru yana had'e rai, _shidai sam bai gamsu da zuwan Jamila ba, kuma har su shige daki ita da yayarshi._



A cikin d'akin kuma, suna shiga Hafsah cikin farin ciki, ta nunawa Jamila gefen gado, "Zauna mana."


Jamila tayi murmushi sannan ta nemi guri ta zauna.


Hafsah cikin rawar jiki ta fito don nemawa Jamila ruwa.


Tana fitowa palourn kai tsaye hanyar kitchen tayi. Basheer ya bita da kallon Takaici, ta zubo mata snacks da dambun nama da basa rabo dashi a, ta had'o da lemo da ruwa. Sai da tazo zata wuce su Bashir yayi mata magana murya a dak'ile.

"Yaya.!

 Bata amsa ba ta juyo.

"Yanzu sai da kika gayyato wannan gidannan koh..."?


Jin abinda yake fitowa daga bakin shi ya sata yin gaba, don bata son ma ta saurare shi.



Basheer ya cije leb'e don matuk'a ta bata mishi rai, ya zabura zai mik'e ya bi bayanta amma mama ta hana shi.


Ta daga mishi hannu, "Bari Basheer kada ka bita."


Ranshi ya k'ara b'aci ya zauna shuru ya jingina sosai jikin kujera, bai fi minti d'aya ba, ya mik'e yayi waje mama ta bishi da kallo.



Niyyar ficewa yayi daga gidan gaba d'aya don haka ya nufi hanyar waje kai tsaye.


Yana bud'e k'ofar  gate d`in wani Napep na tsayawa a k'ofar gidan nasu.

Bashir na k'arasa fita yaga kamar ana d'ago mishi hannu ta ciki. Don haka ya dan dakata har mutumin ya fito, me Napep yayi gaba, shi kuma mutumin ya nufo wajen Basheer.




Basheer yaso gane shi, sannan yana mamakin irin murmushin da yake mishi.


Yana k'arasowa ya k'ara fad'ad'a murmushinshi, sannan ya mik'wa Basheer hannu suka gaisa.


Cikin fara,a yace mishi, Allah ya sake had'amu koh."?

Basheer yayi murmushi tana kallon shi da mamaki.


Kafin yace, "Ai ni sai yanzu na gano ka."

Shima murmushin ya mayar mishi.


Bashir dai kallonshi yake da buk'atar k'arin bayani, kuma yaga kamar bai da niyyar k'ara cewa komai. Don haka yayi gajen hakuri yace. "Ka kira number ta baka samu ba koh."?

"Hmm, kai dai bari nasha wahala fah,

Ya dafa kafad'ar Basheer, yana murmushi, "Ka wahalar dani abokina, meya faru ne."? Cewar Ukhasha.


Bashir ya taya shi murmushin, 

"Wallah a ranar aka d`auke min waya."

Ayya Allah ya kikaye gaba. Ukhasha ya fad'a cike da alhini.



"Amiin inji Bashir, sannan cikin son tabbatar wa yace, "Naga kamar nan gidan kazo koh."?


Ukhashatu yayi murmushi mai sauti, sannan yace, "Eh."

"Nan na zo."!!

Bashir ya mishi kallon mamaki kafin yace, "Gurin abbanmu,? kar dai ka sanshi dama."

Ukhasha yayi 'yar dariya, sannan yace, kai tsaye, "A,a gurin Hafsah nazo.!!


Bashir najin haka ya fad'ad'a murmushi sannan ya mishi nuni, "Aa shigo, zo mu shiga ciki don inason k'arin bayani.


Sukayi dariya dukkansu, sannan yabi Bashir suka samu kujeru suka zauna, Bashir ya bude baki zaiyi magana Ukhasha ya dakatar dashi.


"Eh dama na santa, na ganta wajen bikin aboki na, so ta hanyar shi na sami contact d'inta a wajen matarshi, bayan na kasa samunka a waya."


Tare suka sheke da dariya, don yanayin amsar tashi ya baiwa Basheer dariya.

"Ai nasan abinda zaka tambaya kenan a ina na santa koh."?

Cewar Ukhasha.

Basheer ya jinjina kai "Yes.!


Basheer nason yi mishi k'arin tambayoyi amma baya son ya dameshi.


Da kanshi ya kuma cewa, "Ai nazo wajenta fiye da sati d'aya daya wuce, kawai dai bamu had'u da kai bane."


Bashir yace, "Hakane, sai yau Allah yayi.


Sosai Basheer yake yi mishi wata fara,a ta musamman domin har cikin ranshi murna yake kuma yana godiya ga Allah da Hafsah ta samu Ukhasha a matsayin mai sonta, don  komai ya had'a, kudi, kyau, ga ilimi.


Bari naje na kira maka ita koh."?

Inji Bashir.


Ukhasha yayi murmushi, "Nagode dama na kira number ta tun kafin na sauka ba,ayi picking ba.


Bashir yayi shuru yadai mik'e, amma a zuciyar shi yana cewa, _"Ya zaayi tayi picking tana tare da wannan banzar kawar tata.?_


Ya nufi ciki Ukhasha ya bishi da kallo, gaba-d`aya yaron yayi mishi kuma yaji ya k'ara samun nutsuwa da Hafsah dama gidansu da komai nata..


Allah-Allah yake kawai ta fito ya k'ara ganinta yaji sanyi a ranshi, don tunda ta tabbatar mishi ta amshi soyayyarshi, yake jin wani irin abu na musamman game da ita fiye da na da..




________________________

A cikin gidan kuwa,  komawar Hafsah d'akin kenan ta ajyewa Jamila kayan data kawo mata tana murmushi take ce mata, "Ga ruwa fah."

Jamila tayi murmushi, ta k'ara bin Hafsah da kallon da take ta bin ta dashi tun zuwanta gidan.


"Thank you! tace mata, sannan ta d'ora "Nayi missing dambun nama nan naku da snacks d'innan."

Jamila mamaki ta bawa Hafsah, amma sai tayi, murmushin yak'e kawai tanajin ciwon abin cikin zuciyarta.


"An kira wayarki fah." Jamila ta fad'a sanda ta debo  dambun nama zataci.


Hafsah ta d`auki wayar tana dubawa,

sai taga sunan Ukhasha, ta tsaya jimm, da zata bi kiran amma sai ta fasa. Don tana da yak'inin zai sake kira kuma bata son katse hirar su, kuma bata son tayi waya dashi a gaban Jamila.


"Kinsan da agidanmu aka bani abubuwan nan bazan ci ba.."? Ta dan tsaya, Hafsah kuma ta zubo mata ido. 

"Nan ma don na mugun yarda da ke neh."!!


Inji Jamila tana wani irin murmushi.


Lamarin daya bawa Hafsah matuk'ar mamaki ta kalli Jamila da neman k'arin bayani.


Jamila ta jinjina kai. "Yes, ba komai ake bani a ko'ina nake ci ba musamman ma idan nazo gidanmu, don zan iya ce miki rabona da ko da ruwan gidanmu ne za,ayi shekara biyar ko shidda."



Hafsah ta zaro ido, lamarin ya ba ta mamaki, mamakin dalilin Jamila na kin yarda da abincin gidansu. _Wannan wacce irin jaraba ce!!_

Ta fad'a a zuciyarta.

Kafin tayi magana, Jamila tace, _"Saboda zasu iya min kiranye ni kuma ban shirya komawa gidan ba.!!_


Hafsah ta dan zaro ido, abin yafi k'arfinta. Ashe duk abinda take tunani mafarki ne kawai, Jamila bata da tunanin sauyawa. Saitaji tana shakkar yi mata wasu tambayoyi da, da  tayi niyyar duk randa jamilar tazo zatayi mata su. Don a ganinta Jamila Itace dai wacce ta sani a da,  kuma tafi kowa sanin ta, sannan tana ganin ta isa da ita da har zata yi mata kowacce irin tambaya.


Ashe ba haka bane, tunaninta ne ita a haka, Jamila tayi nisa kuma ta riga ta chanja tsarin rayuwa.....






   📝 

*HAJEEEYAH KHAREEMERH*

[17/03, 2:53 p.m.] UMAIMA BASHEER: ♥️♥️♥️♥️

*ZAZZAFAN SO*

(masoyin k'warai)

*Cigaban littafin Zazzafan so*

*(Guba ne)*

  💔💔


*By:*

*Karima Tijjani Mansur*

*(Hajeeyah khareemerh )*

*Dedicated to Unique in your love heart group members.*


*HELLO FANS KU K'ARA HAKURI DANI BISA RASHIN POSTING... IN SHA ALLAH, ZAN TAK'AITA LITTAFIN*

_BANA SAMUN LOKACIN TYPING NE SOSAI._👏🏼👏🏼



*NOT EDITED*✏️






📄 *58*




*Suka* shuru ita da Jamila na dan wani lokaci kafin Jamila ta k'ara kallon Hafsah.


"H. hameeed, naga kamar shirin fita kike yi koh."?


Hafsah ta d'anyi jimm, kafin tace, "Eh akwai wanda zan gani ne."


Jamila ta kafe ta da ido tana mata wani irin kallo, "Hmm kice an kusa mu fara shiri."


Hafsah ta d'anyi wani d'an murmushi. "Hmm Jamila kenan ina fah.."? Wannan _manager_ inda nake aiki ne, zaizo zamuyi wata magana."


Sanin Hafsah bata k'arya yasa Jamila yarda da zancenta.


Kafin daga bisani Jamila tace, "To gaskiya kiyi kwalliya  a fuskar ki don naga  bakiyi kwalliya ba."

You know mazaa akwai rainin hankali,  musamman manyan ma,aikatan nan."


Abin ya bawa Hafsah dariya.

Yes nake fad'a miki, inji Jamila tana zuge jakarta ta dakko wata powder.


Ta mik'e tana cewa, "ungo shafa ko in shafa miki."!!


Kawai sai ta hau shafawa Hafsan. Haka kawai Hafsah taji tana d'ard'ar d`in hakan, taji tana kyankyamin Jamila ta tab'a ta amma babu yadda zatayi.


_Powder ce mai tsada Jamila ta shafa mata wacce a k'alla kud'inta zai kai 5k, ta kuwa amshi fuskar Hafsah sosai, dama ta farare ce, tunda Jamila ta zama fara sosai itama duk da dama can tana da hasken fata._



Jamila ta ajye powder a gefe, ta kwance daurin d'ankwalin kan Hafsah, bak'in gashin ta mai tsaho ya bayyana.

Jamila ta yarfe dan kwalin tana cewa, "Gashin nan dai na nan yadda na sanshi sai baki daya k'ara.!!


Hafsah tayi dariya, sosai.


Jamila kenan, kina son gashin nan, gashin da naki ma yafi shi yawa "?


"Ta fara zarga mata d'auri tana cewa, Hmm ai nawa fushi ne dashi gashi ba gaba-d`aya ya tafi ba wani yafi wani tsaho."





Ganin suna hira haka ya bawa Hafsah k'warin guiwa wajen yin tambayar data dami zuciyarta. Dama bata son had'a ido da Jamila tayi mata ne, yanzu kuwa tana mata d'auri.



"Jamila wa zaki raka Dubai please."

Hafsah ta dake murya ta tambaye ta.


Jamila tayi murmushi.

"Hmm, H hameeed kenan."


________________________________



A parlour, Basheer ne ya shigo, har yanzu mama na zaune a parlourn, ita kanta ji take bata aminta da shigewar Hafsah da Jamila d'aki ba. Tunda bata san me Jamilan zata fad'a mata ba.



Sallama Basheer kawai yayi ya nufi inda d'akin Hafsah yake. 


Mama ta kira sunan shi, "Basheer."?

Ya dakata, sannan ya juyo, "Naam mama."?


"Me zaka shiga d'akin kayi."?

Ya dan shagwabe murya, Kai mama babu komai fah, Ya Hafsah ce tayi bak'o zan fad'a mata."


"Hmm, da gaske."?

Ya saki murya.

"Allah mama.!

Mama ta maimaita, Bak'o."? "Jeka fad'a mata toh.



Mama a ranta itama bata so bakon Hafsah yaga Jamila ba.



Basheer ya wuce, ya nufi k'ofar d'akin.


_____________________________


"Ai Hafsah badon kina da abinyi ba akwai labari.. Cikin muryar tausayi ta cigaba.


"Bansan ya akayi na yada ke ba, amma cikin in sha Allah idan na dawo daga tafiyar nan zanzo zamu tattauna don ke kad'ai ce zan fadawa magana ki yarda kuma ki bani Shawara tsakani da Allah."


Hafsah tayi shuru tana sauraron ta jikinta ya k'ara sanyi.



Ita har yanzu Jamila bata bata amsar abinda take son ji ba.


Sai ta ji Jamila na cewa, 

"Aunty zan raka, Kinsan yanzu duk duniya bata da kamata Nima bani da ya ita sai dai akwai Matsala guda d'aya nida ita.."!!


Ji sukayi an turo k'ofar babu ko sallama.

Jamila ta juyo, Hafsah kuma ta d'ago.


Yaya."?

Kira sunanta rai a cunkushe.

Ran Hafsah ya b'aci.

Mene."?

Tace mishi.

Ita kuma Jamila ta cigaba da gyara mata d'aurin.


"To kizo kiji mana."

Inji Bashir.


Hafsah ta bude baki cikin fushi.

Bazan zo ba, Basheer ni kake disgracing koh agaban kawata koh ni kake wa haka."?


Muryata tayi rauni, "Shikenan bazan zo ba, ko ma mene bazan zo ba inyaso ka rufe ni da duka.."


Bashir yasan hali don haka ya k'araso cikin d'akin.


Lokacin Jamila ta k'arasa mata d'aurin ta zauna.

"Am sorry my yaya, ba abin zafi bane, kiranki ake a waje."


"Shine Bazaka fadamin ba kake kirana kamar nice mufeeda koh."? 


Shidai Bashir shuru yayi, Jamila kuma ta zuba musu ido bata son tasa musu baki.


Please Yaya ki zo dai jiranki ake."


Yana gama fad'ar haka ya fice.


Yana fita Jamila tayi magana.

"Ki tashi Hafsah, kinga may be ya dad'e yana jiranki, kinga _no wonder_ ma tun d'azun nan ma shi ya kiraki so kada yace kina mishi wulak'anci don ya biyo ki har gida."


Jamila ta mik'e ta d`auki Jakarta ta bud'e, ta zaro wani pink jambaki da powder nan ta d'azu.

Ta mik'awa Hafsah, Ki shafa wannan lipstick, zai miki kyau, wannan  powder shima kuma ki rik'e yana da kyau.


Hafsah ta tsaya saroro tana mamakin Jamila.

Jamila tayi murmushi, ki amsa mana."

Ta ajyewa Hafsah a gefenta.

Nagode Jamila.

Hafsah ta fada, sannan ta d`auki jan bakin ta mik'e ta,  Kalli mudubi.


Ta dinga murmushi ganin yacce tayi kyau matuk'a.


Ta dan goga Jan bakin tana murmushi azuciyarta tana godewa Jamila, don yau tana da burin ta yanki ukhasha da yawa.


Wow Jamila thank you fah, dama kefa kin iya kwalliya, amma wanna daurin like irin makeup artist ce

 ke.!!


Ta bude drawer zata dakko mayafi.


Jamila tayi murmushi.


Hmm, H hameeed, da gaske d`in ita ce.

Hafsah ta juyo da mamaki.


Jamila ta jinjina kai, Hmm, H. Hammed sana,ar da ake zaton inayi ba ita nake ba yanzu, Allah ne shaida ta, shiyasa nace miki zanzo zuwa na musamman ina so ki bani shawara, inaso na inganta rayuwata nima."


Jikin Hafsah yayi sanyi ta matso a hankali ta kamo, hannun Jamila.

Sam Jamila batayi irin raunin da Hafsah tayi ba, Hafsah har kwalla ce ta cika mata ido.


Jamila ta lura, sai tayi murmushi kawai, ta yarda cewa a duniya bata da kamar Hafsah H hameeed.


"Ki saka kwalli mana."

Jamila ta share zancen da fad'ar haka.

Hafsah ta juya ta d'auka.


Jamila ta sa hannu ta d'akko turaren data gani cikin drawer, sannan ta rufe drawer da murfinta.


Aka kuma turo d'akin, wannan karon mama ce.

Fuska babu annuri sosai ta leko d'akin ta k'are musu kallo, Hafsah nasa kwalli Jamila tsaye.

Jamila tayi saurin cewa, "Sannu mama."

Lokacin ta bude baki zata fara magana.

Maimakon ta amsa ta sai kawai ta fara maganar ta.



"Ke Yaya ba cewa akayi kinyi bako ba."?


Kafin Hafsah ta amsa mata. Ta kalli Jamila "Yawwa."

Hafsah ta juyo.

Mama gani nan fah.

"Zo ki wuce toh."

Sannan ta kalli Jamila. Ki jirata kinji."

Aa mama nima ina sauri ne bari mu fita tare."


Mama bataji dadin hakan ba, kawai sai ta juya tabar musu d'akin.


Jamila ta fesawa Hafsah turare itama ta fesa.


Hafsah ta dakko takalmi a hannu suka fito.



Jamila ta durkusa da suka iso palour, "Mama, sai anjima.!

"To ki gaida gida."

Zasuyi gaba, mama ta kira Hafsah.


Suka fara tafiya sun fita kofar palourn har sun nufi hanyar waje, mama ta kira Hafsah.


Hafsah ta dawo tana mamakin kiran.


"Zauna kiji."

Hafsah ta zauna.

Mama tayi shuru, ta shiga wata sabgar ma.





















Kusan minti biyu, suna shurun. 

Awaje kuma Jamila na tsaye.



Hafsah ta rasa dalilin kiranta da mama tayi, gashi bata mata magana ba kuma.


"Tashi kije ma kawai .!!

Mama ta fad'a mata.


Da sauri Hafsah ta mik'e ta fita.



Jamila ta tsargu da kiran da akayiwa Hafsah. Amma da Hafsan ta fito bata nuna mata komai ba. suka had'u a harabar gidan.




Ukhasha tun sanda Jamila tazo ta tsaya ya lura da ita, dake suna daga gefe shida Basheer.


Don ya hana Basheer tafiya sai janshi yake da hira.


 Acikin hirar ne ya gane cewa Basheer k'anin Hafsah ne, kuma ya ji cewa Basheer ba anan yake karatu ba,  kuma shima engineering yake karantawa.




Sannan daga baya yaga Hafsah ta fito, Basheer na ganin fitowarta ya mik'e yayi waje Ukhashatu sallama,

 "Agaida gida yaya nah.!"

Ukhashatu ya tsaya yana kallon shi, "Haba aboki ya zaka tafi kuma."?

"Dama zani wani waje ne."

Ukhashatu ya mik'a mishi hannu sukayi musabiha.

"Okey thanks alot, zan kiraka in sha Allah tunda kayi swapping layin."


"Okey nagode ka gaida gida." Inji Bashir.




Hafsah niyya tayi da ta wuce shi, ta raka Jamila in yaso idan ta dawo taje wajenshi. Amma sai ta kasa samun nutsuwa da hakan.

Tana ji ajinkinta kallontan da yake. Kawai sai ta nufi wajen shi. Ganin haka Jamila ma ta bita amma sai ta tsaya daga can gefe.


Wani shudadden murmushi suka dinga yiwa juna, ukhashatu yaji zuciyar shi fes, kamar an wanke mishi, ganinta yake kamar wata sabuwa, yau tayi mishi wani kyau ne na musamman daya tafi da tunaninshi..


Assalamu alaykum.

Cikin sakin murmushinya amsa mata yana k'ara kallon cikin idanunta. 

Hafsah ta kawar da kai tana murmushi.


Tana tsaye har yanzu. Ahankali taji yace "Queen!! 

Ta amsa mishi da idanu.

Yayi mata nuni da kujera. Sai ta girgiza  kai.

Ya kalleta cikin kwayar ido, cikin marairaice fuska yana neman dalili.


Tayi mishi nuni da Jamila.


"Kawata ne mun dad'e bamu haduba for years yau tazo min so zan dan taka mata ne."


Hafsah ta manta da ukhasha take magana, sannan kafe ta da ido da yayi yaja tayi saurin furta wad'annan kalaman babu shiri.


Ukhashatu ya lumshe ido a hankali, sannan ya zuba su can Wajen da jamila take. Hakika farkon tahowarsu tafi mishi kama da k'anwar babar Hafsah, amma da suka doso shi, xubinta da Yanayin shiga yasa yaji ya kori wancan tunanin kuma yaji yana bukatar jin wacece ita."?



Murmushin ya saki, sannan yace "Okey,  kuma ba zaki kawota mu gaisa ba."?

Ya fad'a da zolaya.

Hafsah tayi murmushi sannan ta matsa ta kira Jamila.


Cikin yauk'i tazo amma yin tozali da idon ukhasha sai da yasa ta gyara tsayuwarta. Shikuma ya sami dama yayi mata cikakken kallon na seconni a lokacin.


"Sannu Barka da yamma."

Cikin sakin fuska yace "Barka dai."

Hafsah koh sai murmushi ta ke.


Daga nan Jamila ta nemi zata tafi, ta hanyar kallon Hafsah sannan batayi magana ba ta fara tafiya.




Hafsah ta d'agawa ukhasha hannu alamun yayi hakuri tana zuwa. Ta bi bayan Jamila tana murmushi.


A hankali ya sauke ajiyar zuciya. sannan a zuciyarshi ya furta k'awarta."?


Hakika dole yayi nazarin akan al,amran. Kada dai ace Hafsah nayi mishi rufa-rufa ne. Banda haka kawayenta biyu kenan wad`anda kana kallon su zaka d'ora zuciyarka _a layin shakku game da su._ Amma me yasa take ce mishi ta dad'e rabon da ta had'u dasu."?

Me take nufi."?

Anya bata zo da rainin hankali ba.?

Ita kanta tasan basuyi kama da qawayen kirki ba sam shiyasa bata son a ganta dasu, shine dalilin kenan daya sa take yunk'urin kare kanta, ko nisanta kanta dasu idan ya ganta dasu.!!

Ahankali ya furta, _dole na nemi sanin dalili._


Baya mata mummunan zato, amma baya jin zai iya zuba ido tana mu,amala da k'awaye irin wad'annan.

Amma koma menene to dole yasan dalilin daya sa take mishi k'arya.

_Na dad`e ban ganta ba for long ko for years!!_




Shafshaf Hafsah tayi sallama da Jamila hankalin ta duk yayi wajen ukhasha, suka tsayar da Matsaya cewa Jamila zata dawo idan ta dawo daga Dubai.





Yanayinshi ya d'an nuna sanyi. D fara,a ta nufo shi sai yaji sanyi cikin zuciyarshi, tabbas Allah ne yayi mishi gam da katar d`in samunta..  Hakika komai nata yayi mishi. Komai cikin nutsuwa da hankali..


Ahankali cike da kulawa yace mata "Sannu fah."

Muryar tayi tasiri wajen sata saurin amsawa tare da sakin murmushi.

"Yawwa ya kake  ya hanya."?

Alhamdulillah hope ban katse muku hira ba.


Hafsah ta girgiza kai.


Noo, dama gaisawa ta biyo mukayi."


Okey, ya fada sannan ya kauda zancen da cewa kamar rad'a. Kinyi min kyau matuk'a, kina da  kyau masha Allah."


Hafsah ta saki murmushin jin dadi.

Sannan taji ya kuma cewa, "Ai da gaske you're beautiful shi yasa kika burkita min lissafi.!!


Hafsah ta saki murmushi, tana dan sunkuiyar da kai.


Bayan dan shuru sannan yace, ya mum ya family."?


Suna lafiya lau.

OK so ya kike kema."?

Ya fad'a cike da kulawa wacce zaka karanta kai tsaye cikin idanunshi.


Ahankali tace "lafiya lau.!!


Alhamdulillah, Kinsan dole nayi taking care, na mai sunan Hajiyata.



Hafsah tayi murmushi, sannan ta gyara daidaitonta a kujerar. 

"Sunan hajiyarka kenan.?

Yes my queen Hajiyata sunan ta kenan kuma tana so na."!!

Ya k'arashe zancen yana mata murmushi.


"Allah ya kara lafiya.

Ta fad'a a hankali shikuwa yaji ta tarr.


Cikin nuna jin dad`in adduar yace, "Amiin Queen." 


Suka d'anyi shuru kafin Hafsah ta dan daga mishi hannu, please "Ina zuwa.!!

Ya girgiza kai yana kallon ta. Ta mishi alamun tambaya da ido.


"Please kada ki tashi.!

"Tayi murmushi, i'm sorry yanzu zan dawo.!!


Yaji dad`in kalmar _i'm sorry_ d`in data ce. Ya saki tattausan murmushi.

 "To kije.!

Sannan ya cukune fuska kamar yaron da aka kwacewa alawa.😀


Ta mik'e tana kunshe dariyarta.


Tana juya baya ya zuba mata ido yana k'arewa tafiyar ta kallo, _cikin nutsuwa take._ yana jin dad`in hakan har ta shige kofar cikin gidan.


Ita da mufida suka dawo, ta rakota da try d`in lemo, ita kuma ta taho da snacks da dambun nama..


Suka mishi sallama dukkan su, ya amsa, suka ajye a kan table d`in, sai faman bin hafsah da ido yake.


Mufida ta gaida shi.

Ya amsa cikin sakin fuska sosai. 

Hafsah taja kujera ta zauna, ta d'anyi kafin ta dago da niyyar mishi magana.

Karaf idanunsu suka had'u dama shi kallonta yake.

Ta dan kalleshi na seconni itama, shi ko ko kiftawa baiyi ba,  hakan ya bata tsoro tayi saurin k'asa da ido ta fasa maganar.


"Itama k'anwarki ce."?

Ta d'aga gira kawai.

Yayi murmushi.

Sannan yace, Hafsah.!!

Ta tsayar da duk tunaninta kanshi amma bata ko motsa ba bare ta amsa.


Ya dace kisan ko ni waye koh."?

Ta saki murmushin jin dad`in zancen.

Ya d'ora "Tun kafin ki gaji dani."

Ta sake yin murmushin dai.


Ya jinjina kai yes, amma kafin in fad'a miki sai kin amsa min wata tambaya.


Ta kalle shi cikin ido tana sauraren shi.


Cikin nutsuwar daya tattaro ya had'a  da rage sauti kai tsaye ya tambaye ta.


Zaki aure ni"?... Ya d'an tsaya sannan ya k'arasa, don Allah ki fad`amin.

Ya saki hannayen shi ya ware su, "nayi miki kalar wanda zaki iya rayuwa dashi."?


Hafsah tayi saurin kawar da kai gefe, bata son wannan titsiyan nashi, yau wato bama a waya ba a fili yake mata wannan zancen."?



Sukayi shuru, sai iskar Yammar dake kad'a su.



"Please ki fad'amin. Don Allah.!

Hafsah ta yi ajiyar zuciya a hankali kafin tace, "Please ka bari mu bar wannan magana kashe lemon ka ga snacks nan."


Yayi mata murmushi, "Nagode da hidima. Sannan ya kalli abincin ya k'ara kallon ta, Babu abinda zaki bani nak'i ci, amma bani da nutsuwa idan banjin amsar tambayata ba please."


I will tell you ai." so take subar zancen a yanzu don haka ta fad'i haka.

"Okay you promised koh."?

Tana murmushi ta girgiza kai.

Hmm, Allah sai kin fad`amin. Ya fad'a sannan babu jira ya shiga zuba lemon a cups. Yau ma guda biyu ya zuba nata da nashi, ya mik'a shi gabanta sannan ya d`auki nashi ya fara sha haka, kafin ya fara had'awa da cake."


Kallonshi Hafsah kawai take yi da wani shauk'i. Kadan yaci ya koma ga dambun naman, ya fara ci yana mata hira.


"Mama na tana son abin nan, gaskiya yayi dad'i thank you my queen."


Ya d'ago ya kalle ta, "Kisha mana."

Ta girgiza mishi kai.

Why."?

Naka ne ai.!!

Nawa ne to ai nina baki."

Hmm, nima ai nina baka."


Baisan sanda ya sa dariya ba. _Dama tana magana haka kamar shi."?_




A fili yace, "Hmm kina da wayo... Kin fi ukhasha wayo.


Tayi murmushi itama.


Ya d`auki toilet paper ya goge hannunshi.

Bayan ya motsa bakin shi azuci yayi hamdala sannan ya zubo mata idanu.


Nagode Hafsah na, na gode da hidima, duk da ke bakya min karar na baki abu kici.!!

Tayi murmushi ta kawar da kai.

"Ai baka ci da yawa ba."


"Ya isheni, nagode, ganinki yana k'ara min koshi.!!


Suka yiwa juna dariya.


Kafin ya tattaro nutsuwa yace, "Hafsah.!!

Itama ta bada hankalinta kanshi.


Zan fad'a miki gaskiya tsakani ga Allah ina sonki, kuma ina son in aure ki...



Yayi shuru yana karantar yanayinta.


Kinyi min a matsayin mata komai da komai.


"Ni ba wani bane, haka mahaifi na, sunan mahaifina Khady Abubakar, yana aiki da ma,aikatar shari,a. Hafsah banyi zurfi a boko ba masters kawai gareni..Sannan ina aiki a wani company, civil engineering shi na karanta.!!


Ya tsahirta anan yana kallonta sosai, Hafsah tayi shuru ita dai, bata da dogon buri akan auren hamshakin mai kud'i, amma tana da burin samun miji wanda yasan darajar ta, wanda zai kula da ita.

A ganinta ukhasha zai iya hawa wannan matsayin.. Tabbas bataji makusa a tattare dashi ba sam.




"Ban miki ba ko  Nayi miki."?

Ya kalleta da wani salo yana tambayar ta.


Murmushi tayi.

Indai banji amsa ta ba nan da gobe, to banyi miki ba. Ya fad'a yanayinshi na bayyanar da gaskiyar abinda yake cikin zuciyarshi.



Hafsah ta yi Jim, sai ta kau da zancen da cewa, "K'annenka nawa toh."

Ta bashi dariya ma, sai ya kalleta da murmushi, ke naki guda nawa ne.

Kai tsaye tace "Four.

Ya jinjina kai, "Tab ni kam tsoho ne.


Ta zuba mishi ido.

"Ni ina da ya ma."

Ya fad'a.

Hafsah ta tsare shi da idanu.


So take ta gane ko da wasa yake.


Sai taga ya nuno mata photon a wayarshi, sun d'auka shida wata akan kujera, 'yar wacce bazata wuce shekaru biyu da rabi ba, ta zagayo ta bayansu ta dafa shi.

Hafsah ta zaro ilahirin idanunta.


Sunyi kyau matuk'a, amma sai kishin macen kusa dashi ya hanata ganin haka.



Ta d`auke kanta, ukhashatu ya lura da yanayinta da ya sanya shi cikin wani nishad`i mara misaltuwa. _Ashe ana kishi nah."!_

Ya fad'a a zuciyarshi a fili kuma ya kuma hasko mata photon.

"Kinga mamanta."

"Bata kalla ba tare Allah ya raya.!!

"Amin Nagode.

Yace mata.


Sukayi shuru babu magana tsahon muntuna.



Sannan ta ji shi yana cewa,  k'annena suna da yawa nine na uku a gidan mu.


Hmm,  tace mishi kawai.


Kin zaci nine dan fari koh."?

Yace da ita, azahiri haka ne amma saboda takaicin shi take yasa tace, "Noo, ni bana raya kai na nawa ne a gidanku, kamar yadda banyi hasashen kana da aure ba.!!


Ba k'aramar jarumta ukhasha yayi wajen hana kanshi tintsurewa dadariya ba. 

Kiyi hakuri, mantawa nayi ban lissafo miki da shi ba.

Takaici ya hana ta tanka mishi.



Suka k'ara yin shuru, sannan yace, kin gama service d`in koh.

"Um."

Amma naga kamar still kina aiki a wajen.


"Sun d'auke ni ne.!!

Ta fad'a mishi kai tsaye.

"Okay Masha Allah Allah ya sanya alkhairi."

"Amin."

Ta fad'a fuska babu annuri, tunda ta d`auke shi tun d'azu bai dawo ba.


My queen, ukhasha ya fad'a yana yar dariyar da ya rik'e.


Sai taji ya bata haushi ma.


Sun dad'e cikin shuru kafin yace a hankali, _ina sonki wallahi."_


Taji ya k'ara bata mata rai, Azuciyar tace, _k'arya ne.!!_

_Agurin Hafsah gani take Soyayyar mutum biyu bata had'uwa azuciya lokaci d'aya._


"Please ki fad`amin." Ya katse mata tunani da cewa haka.


A dakile tace mishi what."?

"You loves me, ba kin fad'a min ba rannan inaso ne na tabbatar."


Da k'yar Hafsah ta mayar da k'wallar da ta cika mata idanu.


Ukhashatu ya fuskanci raunin da tayi sosai don haka ya tausasa murya.


"Please inason naji don Allah please I love you my queen."


Maimakon ta ba amsa sai ta sunkuyar da kanta tana dan cije leb'e.


Ukhashatu ya shagala da kallonta a haka.


Kyakykyawar farar mace, komai nata madaidaici, ga yangar halitta komai cikin nutsuwa, sai raunin da yayi zuciyarta yawa, ga _k`i fad'i_


A hankali taji shi yana wata Siririyar dariya me jan hankali.


Ta d'ago a hankali.

"Kiyi hakuri na daina.!! Ya fad'a yana daga mata hannu alamun rok'o.


Bata fahimci me yake ce mata ya daina ba amma zafinshi da takeji bazai barta ta iya mishi magana ba.



Suka sake yin shuru dai, ya dakko wayar shi yana dannawa.



"Ki tura min photonanki please koda ta Whatsapp ne inason na dinga ganin ki Hafsah na.!!


Taji yace haka.


Bata tanka mishi ba.


"Ya share babin ya k'ara cewa, Ki fad'a min abubuwan da kike so da wanda bakya so."


Ya fad'a a k'ok'arinshi na kawar da wannan Yanayin da ta shiga, wanda a bad'inin zuciyarshi ba k'aramin kona mishi zuciya shurun nata yake yi ba, dauriya kawai yake, don yana son jarraba ta sosai.



"Bana son k'arya!!

Yaji ta fad'a kai tsaye baiyi zaton zatayi magana ba sam, sai gashi tayi cikin d'aure fuska.


Ya saki tattausan murmushi, yana girgiza mata kai, don yasan dalilin ta na fad'ar haka.


Nima haka Hafsah, bana son karya kuma in sha Allah ba zaki same ni maiyi miki itaba..


Ya tsura mishi ido, Shikuma ya d'aga mata gira, cikin k'asa da sauti yace, _"sai dai ina da zolaya.!!_


Ba tayi dogon tunani kan abinda ya fad'a mata ba, banda haka da ta d'ora wasu zantukan nashi a ma,aunin zolayar dayake yana dashi.

_Misali auren daya ce mata yana da.._



Hmm, tace mishi kawai. Sai ya kalleta itama ta zuba mishi ido sai ya b'ige da yi mata wasu dogayen zantukanshi masu sanyaya mata jiki.


Kiyi hak'uri idan a zuwan nan da nayi nayi wani abu daya bata miki rai, babu zuciyar da zan so in sata farin ciki kamar taki, sai dai idan ina tare da ke bana iya control d`in kaina, ina iya yin komai ne domin na burge ki, sai dai a samu akasin ke a wajenki ba abin burgewa bane, tunda ban kware wajen karantarki ba tukuna.



Nagode, da irin hidimarki gareni, amma ina son inji amsata ko da a waya ne, don Allah idan banyi miki kalar wanda zaki aura ba ki sanar dani.!!


Ta bi shi da kallo, shima ya k'ura mata ido.


Bari na barki kada na cika ki da surutu, Nagode Allah ya huci zuciyarki..


Lokaci guda ya mik'e itama sai ta mik'e d'in. Ji tayi zuciyarta na tafasa, sam bata tsammaci  tafiyar shi yanzu ba, 

Ji tayi kamar, hasken wajen ne zai d`auke idan ya tafi..



Bata ankara ba taji yana ce mata kiyi hakuri ki karb'i wannan, ta dawo da kallonta gunshi, kud'i ne sababbin 'yan dariya biyu, _wrapper_


Ta tsaya sororo tana kallon shi, kafin tayi yunkurin yin magana ya rigata.


Bance don kina da buk'atar su ba ko wani abin, sai dai inason na dinga kyautata miki nima da iya abinda nake da iko, kamar yadda kike min.


Ya ajjye su akan table d`in sannan ya daga mata hannu yana murmushi mai tsaya mata a rai.

"Bye bye.!!


Ya juya ya nemi hanyar shi ta fita ya barta daskare a wajen ta zubawa kud'in idanu....





  📝 

*HAJEEEYAH KHAREEMERH*

[17/03, 2:54 p.m.] UMAIMA BASHEER: ♥️♥️♥️♥️

*ZAZZAFAN SO*

(Masoyin k'warai)

*Cigaban littafin Zazzafan so (Guba ne)*

💔💔


 *By*

*Karima Tijjani Mansur*

*(Hajeeyah Khareemerh)*

*Dedicated to unique in your love heart*




*IN SHA ALLAH ZAN TAKAITA BOOK D`IN CIKIN 3PAGES. DALILI SHINE MUN KOMA MAKARANTA KUMA KARATU YA KANKAMA..*

_SAI AYI HAKURI DA YADDA LABARIN ZAI ZO ATAKAICE._👏🏼👏🏼👏🏼👏🏼





📄 *59*




Ukhashatu na fita motar Abban su Hafsah na sako kai, don haka ya dakata aka bud'e mishi ya shigo, lokacin ita kuma Hafsah lokacin ta gaji da tsaiwar ta wuce ciki cikin sanyin jiki..




Abba yaga ukhashatu kuma ya yayi mamakin ganinshi tunda yasan ba abokin Basheer bane.


Sai da yayi parking ya fito, ukhashatu dake rakabe a gefe ya k'arasa wajen shi.


Har k'asa ya tsuguna ya gaida shi, Abba ya amsa cikin sakin fuska yana mishi alamu da hannu 'da ya mik'e.'


Ukhashatu cikin ladabi ya mik'e zai juya. Abba ya buda baki ya mishi magana cikin sakin fuska. "A to ai a shigo mu k'ara gaisawa koh."?


Ukhashatu cikin ladabi ya dawo yana murmushi, Abba yayi gaba, shi kuma yabi bayan shi.


A sit room suka yada zango, bayan dukkansu sun zauna a gurin da shi abba yaiwa kanshi mazauni, da kuma gurin da yayi wa ukhashatu nuni daya zauna tun f

Kafin shi Abban ya zauna, amma sai da ukhashatu ya bari Abba ya zauna sannan ya zauna a k'asan kujerar da aka mishi nuni da ita.



Abba yaji dad`in wannan ladabin. Ya fuskace shi kuma da murmushi a fuskar shi.


"Ya mutanen gidan suna lafiya."

Ukhashatu yayi murmushi, yana dan sunkwi da kai.

Lafiya lau Abba.

Abba ya d'anyi gyaran murya.


"Sai dai ban shaida fuskar ba daga ina ake."


Ukhashatu ya k'ara k'asa da kanshi.

Nassarawa."

"To Masha Allahu." yana murmushi yace,  "Za,a fad'a mana sunan mai Gidan ko nafi ganewa."


Ukhashatu yayi murmushi shima, Eh, "Alhaji Abubakar Khady."


Abba ya fad'ad'a fara,arshi.

To Masha Allah, Khady dai da na sani mai sharia na majestry court"?


Ukhashatu ya jinjina kai cikin ladabi.

Abba cikin fara,a Alhamdulillah. "Ai Khady na mu ne, Allah ya k'ara mishi lafiya."

"Amin Abba." 

 Cewar ukhasha.

Sannan Abba ya d`an shaki numfashi kafin yace, "To wajen Basheer aka zo ne."?

( _baya son ya mishi tambayar gurin wa yazo cikin yayanshi mata kai tsaye._)


Ukhashatu ya sosa k'eya  yana gyara zama cikin jin nauyin abba yace, "Eh Abba mun gaisa dashi kuma nazo wajen mun gaisa da Hafsah ma."


Abba jira kawai yake yaji alak'ar Basheer da Hafsah.

Cikin son mishi wayo irin nasu na manya yace, "Wajen aikin ku d'aya kenan."?

Ukhashatu ya girgiza kai, fata yake kawai Abba ya fahimta basai ya fito b'aro-b'aro ba.



"Am um dama ina zuwa ne muna gaisawa."


Abba yayi murmushi, cikin matsanancin farinciki, "Alhamdulillah ya furta a fili."


Yana yiwa Allah godiya, da ya bawa Hafsah miji irin wanda yake mata fata. _(Dan gidan manyan mutane ba girma irin na naira ba, sai dai duka kuma Allah yayi an had'a kudi da sanin yakamata ga kyakykyawan asali)_


Ukhashatu yana iya karantar irin farin cikin daya bayyana kan fuskar Abba.


"Masha Allah, Allah yayi albarka."

Kai tsaye yace, Za,a iya yiwa manyan magana sai a zo agaisa koh."?


ukhashatu ya gane me Abba yake nufi, cikin farin ciki, shima ya ke zuba godiya.

"Nagode Abba Allah ya saka da alkhairi."

"Amin Amin."

Sai a bani number shi Abban naka koh."?

Abba ya ciro wayar shi ya mik'o.

Ukhashatu ya karb'a da hannu biyu ya rubuta number, sannan ya mik'awa Abba.


Abba yayi saving, sannan zana tashi number akan wayarshi, ya k'ara mik'awa ukhashatu.


"To gashi, koh sai a d`auki tawa saboda a sanar idan an shirya zuwan."


Ukhashatu ya karba yasaka, a wayarshi.

Sannan ya mik'awa Abba wayar.

Yana fad`in "Angode Abba."

Abba yayi murmushi sannan ya mik'a mishi hannu sukayi musabiha, yana fad`in agaida mutanen gidan, naga magriba ta k'arato.

Ukhashatu ya mik'a bayan sun saki hannun juna, "Na Barka lafiya Abba."




Ya fita cikin matsanancin farin ciki, ji yake kamar ango ne shi.

Godiya yake ga Allah daya sauk'ak'a mishi komai. Ya sani ba dabarar shi bace Allah ne ya saukaka mishi komai yadda zai sanya mahaufanshi cikin farin ciki.

*______________*

A wani masallaci ya tsaya a hanya yayi sallar magriba inda babu wani jira ya, k'ara tarar napep Kai tsaye ya wuce gidan abokin shi, da k'yar ya lallabashi kan ya taso ya raka shi gadon k'aya gidan Baffa..Babu irin mitar da Mubarak bai mishi ba a mota.  _kai ka cika zumudi daga haka sai ayi haka, wa yaga farin shiga."? Banda na matsu kayi aure nima da babu abinda zai hana ni zamana a gada. Kawai ka taso mutane suna hutawarsu._


Shidai ukhashatu kus yayi yana jinshi don yana cikin farin ciki, baya son ya tanka mishi ya ce bazai raka shi ba.


Yanayinsu da Baffa ya gani ya tabbatar mishi da akwai magana, kuma shima ya sakar musu fuska kamar yadda ya gansu cikin farin ciki.

Bayan gaisuwarsu kamar ko yaushe, _ta musabiha._

Baffa cikin fara,a yake tambaya.

Ya akayi ne, ya Abban naku."?

"Yana lafiya lau Baffa."


"To Masha Allah." Suka k'ara yin shuru.

Baffa ya k'ara tambaya.

Komai kalau dai koh."?

"Lafiya lau Abba suka fad'a cikin ladabi, Mubarak ya gyara zama, ganin dare ya farayi ya fara magana.



"Baffa ayi mana afwa munzo da daddare."


Baffa ya gyada kai, yana murmushi, "Ai ku ba bak'i bane, babu komai, ai shi ya sha amsa kiran dare ma a gidan nan." Ya kalli Ukhashatu yana k'arashe zancen.


Ukhashatu shidai kanshi na k'asa.


Sannan baffa ya juya ga Mubarak  yana, tambaya. "Me ya faru ne."?


Mubarak ya gyaran zama ya fara bayani.


"Dama Baffa, akwai gurin da Ukhasha yake zuwa amma bai jima ba, to yau d'innan sai mahaifin yarinyar yace a turo magabata." 


Tunda ya fara magana Baffa najinshi yana gyada kai, sai da yakai k'arshe sannan suka ga wata fara,a da basu taba gani ba musamman ukhashatu a fuskar Baffa.

Masha Allah Alhamdulillah Allah ya tabbatar da alkhairi, ai wannan abu ne da muke nema."


Sannan ya juya ga ukhasha da kunya ta cika yace, "Har kwananka nawa da fara zuwa zaka ce, baku dad'e ba."


Kai a k'asa yace, wata d'aya zuwa biyu, amma zuwanta na biyu kenan gurinta."



"Baffa ya ca fe, ahaf ai tunda kun daidaita kuma har tana saurarar ka ai zance ya k'are."


Ya juya ga Mubarak, "Abban nashi ya sani."?


Mubarak ya girgiza kai.


"A,a Baffa ai yanzu ne akayi maganar."


"OK tom babu komai."

"Sun bada number ne da zaayi magana."?

Mubarak ya kalli Ukhashatu, shi kuma da sauri ya lalubo wayarshi a aljihu, ya danno number _Abban Hafsah_ ya mik'awa Mubarak.


Cikin ladabi Mubarak da hannu biyu ya mik'awa Baffa.


Baffa ya amsa yana murmushi yana cewa, "Ai kuwa gaka anyi dabara da aka bada number."



"Sai ayi magana yadda ya dace."


A wanne unguwa suke. Mubarak ya amsa, "Sallari."

"To ya sunan shi mahaifin yarinyar da yarinyar."?


"Alhaji Habeeb Hamid."!!

"Ita kuma Hafsah."

Duk Mubarak ne ya bada amsa.


"Masha Allah, "Allah ya tabbatar da alkhairi.

"Amin." Inji Mubarak.



"Zamuyi magana da Yayan." Baffa ya fad'a.

Ukhashatu ya d'an tab'a mubarak alamun ya tashi su tafi.


Mubarak ya mik'e shima ya mik'e, cikin ladabi suka mishi sallama.

"Baffa zamu tafi kada dare yayi." Inji su.

Tom Allah yayi albarka tunda har kun mik'e ku gaida gida, an gode kaji Mubarak."?



Suka fita, kowa fuskar shi da murmushi.


A waje mubarak yake ta tsokanar Ukhashatu, "Aikin banza ka wani zama silent a ciki don gulma koh."


Ya gyada kai Eh mana, ni wuce ka kaini gida malam.


Cab bazai yuwu ba wallahi, sai dai na ajyeka a titi, kawai na baro iyali na salon ka hura min wuta kai kana kokarin gida naka gidan."?


Dukansu sukayi dariya, Ukhasha ya zagayo ta daya barin yana cewa "Eh naji saukeni a titin."


Suna zuwa titin kuwa yayi parking. Ukhashatu ya mishi godiya ya fice ya tari Napep yayi gida.


_______________

D'akin Hajiyarshi ya nufa daga shigowar shi gidan, fara,ar shi ta musamman a lokacin, yana nufo d'akin, Mahseem ta nushi da gudu ta d'ane shi,  "Yaaya!!

Ya daga ta da k'yar.

Kin girma fa "Mahseem na daina daukar ki daga yau."

Ya sakko ta ya rik'e hannunta suka k'arasa cikin gidan.


Yayi sallama ya zauna.


Hajiya ta kalleshi.


"Ina kaje ne haka tun yamma."?


Ya sunkuyar da kai, "naje gidan baffa hajiya."

"Acan ka dad'e haka."? Hajiya ta k'ara tambaya.

"A,a naje gidan abokinah..."

Yana cikin fad'a Fadwa ta ca fe, tana dariya "Hajiya zance yaje fah."


Ya aika mata da wata hararar data sa ta saurin to she bakinta da hannu.


Ya jinjina kai sannan ya mik'e, hajiya ta bishi da kallo, to ya Hajiyar ka baro su lafiya."?


"Lafiya lau Hajiya." 

Mahseem ta biyo shi ta rik'e hannunshi suka nufi d'akin shi.

"Yaya tasbahar da kace zaka siyo min."


Yayi murmushi, Eh na siyo miki "Mahseem har da chocolates ma."

"Yawwa brother nagode."


Ya bude d'akin suka shiga, mahseem na mishi tambayar da ta saka shi juyo wa.


"Yaya wai da gaske zance kaje."


Ya tsaya ya kalleta har tasha jinin jikinta kafin yayi murmushi.


Museem ki min addu,a kinji Allah ya zaba min abinda yafi alkhairi.


Tayi murmushi, "Tom Yaya inayi."


Ya bude drawer ya dakko mata ledar, ungo kije ki kwanta, kice  maryam ko Fadwa su kawo min abinci kinji."

"Tom Yaya sai da safe." "Yawwa Mahseem. 

Yace da ita.



Sai da yazo kwanciya bacci ya tuno yadda suka rabu da Mutuniyar tashi, nan ya dinga dariya kamar bazai daina ba,  Yanajin kewarta a zuciyar shi daga k'arshe, ya lalubi number ta amma tak`i d'auka.

Yayi murmushi a fili yace, "Hmm yarinya na kusa mallakar ki na huta.!!


_____________________________


Khady yayi mamakin jin batun da, k'aninshi yazo mishi dashi, _wai ukhashatu da neman aure.!!_ Bayan cikin kwanakin nan ma ya mishi maganar amma ya nuna ba wani shiri da yake.


Badon bikin maryam sati biyu kawai sukayi saura ba, da babu abinda zai hana yace a had'e.


Ya nuna jin dad`in shi ga kanin nashi, sannan suka shawarta yadda abubuwan zasu kankama, sun tsara zasuyi bincike kafin suyi magana da mahaifin yarinyar.



Sukayi sallama kowa cikin farin ciki da mamakin Ukhashatu.



___________________________



Maman su Hafsah ta lura da kalar farincikin da Abban Hafsah ya shigo dashi d`auke a fuskar shi, itama sai ta tare shi da hakan.



Sai da ya nutsu yake mata jawabi yadda zata fahimta.

Amina, naga wani yaro yazo wajen Hafsanki, kuma na yaba dashi har na nemi daya turo iyayenshi."


Mama ta waro ido, "Abba da wuri haka."?

Ya gyd'a kai to me za,a jira tunda Allah ya kawo."?


Kuma yaron dan gidan sanannun mutane ne, amma duk da haka zanyi d'an takaitaccen bincike, kedai ki taya ta da Addu,a Allah ya mata zabin alkhairi.

"Amin."


Inji mama, taji dad`in hakan amma kuma tana tsoron gaggawar da akayi kan al,amarin."



"Kada Ki sanar mata har sai sunzo, sannan zan sanar mata da kaina."


Mama ta gyada kai alamar "Toh."



Sanda Basheer ya shigo ya shiga d'akin Abban don tsaigun ta mishi bak'on Hafsah.


Shima Abba a k'age yake yana son jin zancen daga bakin Bashir d`in tunda bakon ya tabbatar mishi sun san juna shida Basheer.


Akwai magana ne malam Bashari."?

Basheer ya sosa kai sannan yace,


Am Eh Abba dama naga wani yazo wajen aunty Hafsah ne yau kuma naga kamar tana sauraren shi itama."

Abba yayi murmushi.

"Nasan zancen, na gamu dashi kuma har nace ya turo iyayenshi ma."


Bashir ya d'ago da sauri yana mamaki, Abba yayi murmushi.


Ba yace min yasan ka ba."?


Bashir ya labartawa Abba had'uwar su da Ukhashatu sannan ya dora da cewa, amma sun dad'e da aunty sunfi wata d'aya zasuyi biyu ma, kuma yace min zuwan shi na biyu kenan."


"To masha Allah Allah yayi jagora."


Bashir yace Amiiin, shima yaji dad`in abinda mahaifin nashi ya yanke.



____________________


Hafsah cikin tunani, barkatai da takaicin Ukhashatu ta kwanta, shiyasa tana ganin kiranshi amma ta share, takaicin ta d'aya matar daya boye mata yana dashi.



Har kwalla ta zubar, meyasa sai da ta fara sonshi sannan zaiyi mata wannan tozarcin, gaskiya maza basu da amana.





Share shin da take ya fara azabtar dashi, don haka ya shirya kalaman ban hakuri masu sanyaya zuciya da taushi ya turo mata.



_Kiyi hak'uri Queen idan nayi laifi, ni mai matuk'ar son ganin farincikinki ne, joking with you inpresses me ina son wasa dake amma wallah bani da mata bare 'ya na nuna miki k'anwata ne da 'yar yayana, am sorry dear na zabtu bzn kuma ba, kiyi picking call kiji wani abu kinji gimbiya.!!_





Sanda text d`in ya iso wayarta, da daddare ne, amma tana dubawa bazan san sanda ta saki wani dan ihu ba, da saida Zainab ta ankarar da ita _dare ne,_ sannan ta nade tabarmar kunya da hararar Zainab.

Zainab itama ta harare ta a wasa ta juya tana kus kus.


Ta jira kiranshi amma bai shigo ba, ita kuma tanajin kunyar kiranshi da kanta.




♥♥♥♥

*ZAZZAFAN SO*

(Masoyin k'warai)

*Cigaban littafin Zazzafan so*

*(Guba ne)*

  💔💔

*By:*

*Karima Tijjani Mansur*

*(Hajeeyah khareemerh)*


*Dedicated to Unique in your love heart group members.*





📄 *60*




#Not edited 

*Kuyi hakuri da typing error.*



______________________________



*Farar* Safiya ce misalin k'arfe takwas na dare, gidan yayi shuru kasancewar _*Mazauna Gidan* (Haermebaererh novels_)

basa nan, Abba anyi mishi wata rasuwa ta Babban abokin sa, a daren jiya daya saka shi fitar sassafe don ya sami Jana'iza. 


Ita kanta matar gidan ta fita, wani uzuri nata, yayin da sauran 'ya'yan gidan suka fita nasu harkokin. Sai su biyu da suka rage a gidan kamar idanu.



Ita kadaice a d'akin ta, jin shurun gidan ya k'aru ya tabbatar mata da cewa mutanen gidan basa nan.




Gani tayi wannan wata dama ce ta samu na gabatar da abinda take ganin maslaha ne gareta. Wanda kuma take ganin zai dakatar da abinda ake shirin yanke mata.


_Bata shirya amsar aure yanzu ba don haka bata jin zata yarda da katsalondon irin wannan._



Doguwar riga ce ajikin ta, ba tare da bata lokaci ba ta d'ora wani mayafi da taga yafi kusa da ita, kawai ta kwashi takalma a hannu cikin sand'a ta fara takowa tana waige waige kamar _barauniyar data shigo sata._


Cikin sa,a babu wanda taci karo da shi. Har zuwa kofar fita, shima a sa,a babu mai gadi a wajen, da Alama ya zagaya wani wajen.


Da gudu ta k'arasa ficewa sai lokacin taji ta sami sukunin watsar da takalman hannunta a k'asa sannan ta saka, jikin ta na rawa ta fara tafiya.


Cikin layin ta hango napep ta tsare amma ya girgiza kai alamun Aa, cikin k'osawa ta kara sauri tana mita,  a zuci.. 

Ta d'anyi yar tafiya kafin ta hango wani, kamar ta kifa take tsayar dashi.. Aikuwa ya tsaya. 


Ta kara sauri sannan ta afka ciki cike da jindadi,  har da ajiyar zuciya. 


Sannan ta sami sukunin sanar da shi inda zai kaita. 

Tarauni zaka kaini.!! 


Me Napep  ya juyo ya kalleta, sanye yake cikin wata riga wacce ta dan dame shi, mara hannu, (sleeveless)  blue color,  sai farin wandon jeans iya gwiwa,   (three-quater). Kanshi ya tara gashi.  Yafi  kama da matasa wadanda ake kira _'yan swagger._


Ta yatsina fuska ganin ya k'ura mata ido har da daga gira. 



"Okey, yanmata."

Yace da ita, sannan ya juya ga tuk'insa. 



Ta kuma yatsina ffuska,  da takaicin kiranta da yanmata da yayi,  sai kuma taji fargaba tuno cewa bata sami damar dakko kudi ba bare  _purse._


Me Napep gudu dinga yi da ita, yanayi yana bin wakar daya kunna musu. 


Da sauri suna isa, unguwar sannan tayi mishi nuni daya kaita cikin wani layi,  babu musu ya kaita har k'ofar gida. 


Sannan ta bude baki,  cikin yauki' saboda taga ta dawo cikin nutsuwarta tace,  "Am na manta kudi na a gida, so zan dan shiga ciki na amso maka kud'in."


Ya bita da kallo kafin ya jinjina kai babu magana. 


Ta juya ta shiga gidan,  shiko ya bita da kallo. 




Kai tsaye dakin maman ta nufa, tana kala mata kira,  Mama!! Mama!! Maman ta yi saurin fitowa suna had'u a palour,  da sauri cikin faraa, ta rungumeta "Yawwa my daughter.!! 


Cikin jin dadi itama ta k'ara rungume matar kafin tayi saurin sakinta tace,  "Oh  mum nabar Napep  a waje so bani 500 na bashi."



Okey,  inji matar,  ta duba gefenta kan kujera,  ta dauki Jakarta ta dakko ta bata.  Da sauri  ta fita,  ta tarar da shi ta mik'a mishi,  ya amsa yana lalubo chanji,  yaga tana kokarin juyawa,  "Wallahi   kin burgeni fah."


Ta zaro ido lokaci guda tare da jan tsaki. Sannan ta juya da sauri, tana fad'in Nonsense.!!




Ta dawo cikin gida,  abinda ya kawo ta ya fi karfin ta tsaya tuna abinda mai Napep  din yayi mata. 


Tana zama maman ta tare ta da tambaya.


Ya akayi kika fito."? 

Sun fita ne duka,  anyiwa Abba rasuwa. 

Okey good. 

Sannan ta saita murya itama ta yar ta bata hankali. 


"Shawara daya na yanke wacce nake ganin itace matakin k'arshe.!! 

Indai mukayi haka to dole a fasa auren nan,  kuma zamu aiwatar da komai ne a yau,  don bamu da wani lokacin daya dace idan ba yau ba."


'Yar ta jinjina kai, maman ta d'ora, "Ai kinsan gidansu koh."? 

Ta jinjina kai. 

Eh,  ya taba kwatantamin. 

"Can zamuje.!! 

Ta fada kai tsaye. 


Yar ta zaro ido,  uwar ma ta kafe ta da nata idanuna,  tare da nuna ta da yatsa. 


_matukar baki yadda mun dauki wannan matakin ba,  to sai dai ki zauna ki aure shi kuma kada ki sake,  mini complain akan bakya sonshi._

Ta dire zancen cikin daga murya tace,  ko kin fara sonshi ne,  kin yadda zaki aure shi."? 


Tayi saurin girgiza kai. 

Uwar ta mike tare da sab'ar jakarta, sannan ta mik'o mata hannu. 

"Taso muje."

Babu musu ta mike ta bita, suka shiga motar uwar suka dauki hanya. 

Jikin yar duk a sanyaye ko menene dalili oho. 


Lura da hakan da uwar tayi yasa ta shiga yi mata wasu jawabai. 

_ina raye bazan zuba ido ayi miki auren dole ba,  tunda shi ya rantse bazai janye kudurinsa ba, ni ina da yadda zanyi. 

   Idan  su gidan su yaron suka ce basayi ko shi yaron su ai ba zai musu dole ba koh."? 


Ki kwantar da hankalin ki,   ayau zuwa gobe zakiji batun auren ki babu shi kinga sai ki auri duk wanda kike so koh."? 


Sukayi murmushi a tare,  sannan sukayi shuru kowa da nashi tunanin. 



Sub iso unguwar, sai da suka had'a  da  tambaya sannan aka nuna musu gidan. 


_"Babban gida kalar gidan manyan mutane.",_



Matar wacce zatayi kimanin shekaru Hamsin 

ko da d'oriya,  na zaune a palournta, tayi shuru a zuciyarta tana lissafin wani abu. 

Wato batun auren babban d'anta dake k'aratowa. 


Ita ba tunanin hidindumu ne ya dame  ta ba, Aa sai dai wani rad'e-rad'i daya ke ta isowa ga kunnenta a kullum, Wato  _wai kalar yarinyar da d'anta ya dakko._


Bataji wanda ya yabi yarinyar ba sam, Sai  dai kushe, amma ta daure abun,  tunda ta tambayi mijinta kuma ya bata yak'inin tabbas mahaifin yarinyar mutuminki kirki ne kuma ya bawa 'ya'yanshi tarbiyya. Don haka ta yanke wani hukunci cikin tunanin da take na, _zata tuntubi dan nata sannan zata sa itama ayi mata binciken sirri._

Tunda indai  kaji anfiya batu kan abu guda toh akwai magana.



Tana tunanin ne ta sami sakon cewa,  wai tayi bak'i, abinda,  ta fara yi shine duba agogo. 


K'arfe 11:00am,  don haka sai tayi tambaya "Su wane"? 

Dan aiken yace,  Hajiya dana tambaye su cewa sukayi,  su ba baki bane,  surukaine don haka in barsu su shigo. 


Kamar zata sake magana sai kuma k'aguwa ( _eager_ ) taga su waye,  yasa tayi saurin cewa shigo dasu kawai. 


Suka shigo da sallama kamar,  gaske, hajiya ta dago ido tana kallonsu da murnushi. 


Duk abinda  Hajiya Halima ta had'iyo sai taji tana shayin matar kuma tayi mata kwarjini, _mutum a gidansa kenan_


Sukayi shuru, bayan ta basu gurin zama, tare da musu tarbar da murmushi had'e da musu _sannu da zuwa._

Itama cikin son tuno ko ta sansu yasa take ta bin karamar da kallo,  don ita tafi yi mata kama da _idon, sani._


Ta gaji da hasashen da kuma shurun da bak'in sukayi tace, cikin murmushi,  _"Naso na shaidaku kuma na kasa,  ko zaku min bayani."?_


Sai lokacin bakin Hajiya  Halima ya bude,  ta sami kwarin gwiwar yin abinda take ganin shiya  dace,  kuma zai jawo fasuwar al, amran."


Yes babu lallai ki sanmu,  especially ma ni.. 


Hajiya ta zubo musu ido, don taji maganar kamar babu _salama_ cikin ta. 


Kafin tace wani abu hajiya Halima  ta nuna 'yarta, 

Wannan 'yata ce Basma,  itace danki yake shirin aure,  to shine nazo na sanar muku gaskiya,  _ni da ita bama son auren nan ubanta ne ke shirin kullawa,_ kinga kuwa gwara a hak'ura kada anayin batacciya don yata ba so take ba. 


Ta kalli Basma, "Basma  ko kina so."? 

Duk rashin kunyar Basma sai taji tana shayin matar itama, kuma tayi mata wani irin kwarjini, amma don kada ta kunyata uwarta sai ta girgiza kai. 

Hajiya Halima  cike da k'warin guiwa ta dora, to kinji dai daga bakinta,  yarinya bata so don,  haka sai azan abinyi gaskiya, idan da zaki tambayi yaron ma,  shi kanshi yasan... 


Hajiya Rabi , bata bar Hajiya Halima ta k'arasa, zancen ta ba, ta daga mata hannu, sannan ta kafe ta da ido, da yanayin fuskarta da ta ke ta sauya zuwa kalar matsanancin fushi. 


Ya isa, kin fad'i magana, kuma, sako yazo, saboda haka zancen ya yasheni haka."


Abin mamaki kuma sai ga Hajiya Halima ta kasa,  mayar da martani sai shuru da tayi kawai tana jiran taga mai Hajiya  rabi zatayi, don taga ta dauki wayarta. 


Cikin tunanin t tsinkayeta tana cewa cikin wayar, "Kazo   palour ko me kake yi."

Bayan d'an shuru kuma taji, tace, cikin fada nace kazo koh,  babu ruwana da me kake, ko aya kake idan ba zaka zo ba tom... "

Sai ta katse kiran. 

Minti baifi daya ba, sai sukaji sallama, ta bayansu, basu waiga ba, shikuma shigowarshi kai tsaye gun mahaifiyar shi ya nufa,  cike da jin kunya. 

_Dama mama tasan da baki tasa ya fito a haka babu wata cikakkiyar riga."?_


_Ya fito daga wanka ne, yana shirin fita, yana sa kaya ta kira shi, yasa wando,  baisa riga ba sai singlet._ Abinda yake fada mata a waya kenan Cewar, _kaya yake sawa._ amma sai ta nuna fushi.


 _Ashe bak'i tayi take son su gaisa.??_ Shidai yayi mamakin dalilin mama na azalzala haka,  ya dan dosanu gefen ta, cike da kunya, sai lokacin ya lura da su wa ke zaune a wajen. 

Ciken da rudu, ya fara magana, "Ba Basma..!!??


Mamanshi ta daga mishi hannu. 

Dakata.!! 

Kasanta ne."? 

"Ba bas,  Basma ma cehh ma mama.!

Ya fada cikin  in'ina. 

Uwar ta jinjina kai,  sannan ta mike tsaye shima ya mike, gabadaya ya rud'e. 


Uwar ta nuna shi da yatsa sannan ta nuno Basma. 

"Tabbatar mata ka fasa aurenta kaima."

Cike da rud'ewa ya hau rarraba ido kamar baya gani, tsakanin mamanshi da su Basma. 


Uwar ta k'ara  daga murya,  sannan ta nuna Hajiya  Halima da yatsa, Me kikace game da 'yarki. "? 


Hajiya Halima ta mike tsaye. "Basai kin nuna ni da yatsa ba, cewa nayi ni da 'yata bama son auren nan idan akayi shi za,ayi b'atacciya.!!

Ta kalli,  Basma ta k'ara cewa, ko kina so."? 

Basma ta girgiza kai kamar d'azu. 


Hajiya rabi ta kalli danta,  cikin daga murya tace,  zaka aureta ko ka fasa kaima"? 

Nour ya zubowa Basma idanu, itama shi take kallo, yana k'ara kallonta,  tanajin wani rauni yana shigar ta a hankali.


Ahankali shima ya bude baki yace,  "Nima  na janye, na fasa auren ki.!! 

Yana fadar haka ya dauke idonshi daga kan Basma ya juya ya kalli mahaifiyar shi, kwalla fal idanun shi.

Hajiya Halima ta bude baki, "Ahto gaskiya kunyiwa kanku.... 


Dakata ke!! 

Hajiya rabi ta fad'a da daga sauti sai da ta razana Basma,  sannan tasa Hajiya  Halima  dakatawar babu shiri.



Hajiya rabi ta nuna su duka tare da cewa,  tunda abinda ya kawo ku ya wuce, to ku bace daga gidannn kafin na gwada muku kalar nawa ikon, don ba ahaifi yar da akanta, za, ayi min dibar albarka ba. Idan kuma kuka k'ara koda minti cikin gidan nan to tabbas zaku gane inda kuka zo.!!! 


Ta juya ga d'anta tana mishi wani kallo. 

Jeka karasa shirinka kaji dana. 

Nasan baka da damuwa koh.'? 


Cike da dakiya ya kirkiro murmushi ya jinjina kai.


Abinda ya bawa Basma madaukakin mamaki kenan. 


Ina tarin naci, da dumbin son da Nour ke mata.??



Har suka koma gida jikinta a sanyaye,  ta kasa nutsuwa da abinda suka aikata ita da mamanta. 


"Anya kuwa batayi abinda zai zame mata nadama ba."? 

Wata zuciyar tace, _wacce iriyar nadama bayan kin rabu da alakakai."??_


_________________


Agidansu Nour kuwa, bayan fitar su Basma, Nour ya fada kan kujera,  ya dafe kai,  kuka yake shirin yi amma kukan ma yaki zuwa, yana mamakin abinda ya faru kamar a mafarki yanzun nan. 

Ya sani bazai iya bawa mahaifiyar shi kunya ba, a yadda ta hak'ik'ance zai goyi bayanta,  a lokacin da ake nuna mata iyakarta akanshi. 


Itama Hajiya Rabi zama tayi kusa dashi, tana son ta bashi baki.  "Kayi hakuri kaji Nour, ka d'auka komai kaddara ne,  kada kaga agabansu nace ka fasa aurenta. Bani da iko akan aurenku haka suma,  Allah  shike kaddara komai Idan ya nufa sai Anyi ko basa so. Amma hakan bazai sa na bada damar su ci mana zarafi ba har cikin gida,  saboda kana son 'yarta,  kaima kayi taka tsantsan kaji, ka nemi zabin ubangiji,  amma ka girmama kanka, kada ka wulakanta kanka inda baza,a taba ganinka da daraja ba, bayan Allah  ya girmama ka ( _amatsayinka na dan adam._)  


Zanyi maka addu,a kada ka damu kaji.. "?  Zamuyi magana da abbanka,  tashi kaje, kayi fitarka kaji, Allah  ya zaba maka abinda yafi alkhairi. 


"Da kyar ya ambata Amiin mama."

Ya tashi babu k'wari ya nufi d'akinshi,  fitar da tasha ruwa kenan, don ya samu rauni matuka ajiki da kuma zuciyarshi. 



Da daddare Abbansu Nour,  na dawowa,  Hajiya Rabi tayi mishi bayanin komai, sannan  ta dora da nata ra,ayin. 


_"Alhaji ina ganin tun da har abin ya zama haka,  to gaskiya a hak'ura, tunda har suka magantu, kuma abin yakai ga anzo har gida to ina ganin Nour ya hak'ura Allah ya bashi wacce tafita, don idan har yarinya ta furta bata so to za,a sami rashin jituwa._


Alhaji ya jinjina kai jin duk bayananta,  sannan ya bude baki, baya son ya nuna mata ra,ayinshi,  a lokacin don haka yace,  "Tom duk naji abinda kikace kiyi addu,a Allah  yayi zab'in alkhairi, zan tuntubi shi Nour din da kuma mahaifin yarinyar."


Daga nan bai sake bata damar k'ara yin magana ba.



______________


Abban Basma yayi mama kin yadda ya dawo yaga Basma bata gidan. Aikuwa ya sauke fushin kan ya ya yayar Basma da ita kanta Hajiya salman, inda ya dora musu laifi duka. Sai da ya sassauto sannan ya fara binciken inda zai samo ta, sai ya fara da Halima.


Ya kirata a waya a fusace, itama tana ganin kiran  ta share. Ya kara kira karo na biyu sai taga ma gwara ta daga suyi ta ta k'are.


"Hello ya akayi ne." Ta fada a fad'ace. 

Halima ki dawo da Basma, don ba muyi dake  zata zo wajenki ba."

Hmm, bazan dawo da ita ba da yake jaririya ce ita da zakace na dawo da ita.!!


Nace ki dawo da itan da waye yace ki zo ki dauke ta.

Tayi dariya au ni na d'auke ta ma koh."?

"Hmm, Alhaji Yunus yarinya fa ta girma sannan ba a kauye muke ba bare kayi mata auren dole tunda tace bata so to fa bazan zuba ido ayi ba. Sannan dawowa ba zata dawo ba.

Haka kika ce koh. "?

"Eh, haka nace.!!

Cikin fusata ya kira sunanta.

"Halima.!!

Ki shiga hankaliki dani wallahi ke kin isa ki hana ni iko akan 'yata."?

To bari kiji ko kinki ko kin so aure sai na aurar  da Basma, sannan koma komawarta wajenki bazai sa na fasa daura mata aure ba, sai dai in bata numfashi.."!!

Hajiya Halima ta sheke da dariyar data bashi takaici. Take ya katse kiran tunaninshi ya kira Basma, sai ya tuna cewa ya kwace wayoyinta. Yayi jigum yana tunani tabbas akwai aiki gabanshi. 




Wani abu daya bashi mamaki shine kiran Abbah Nour daya gani da daddare. 

Da sauri ya daga yana fatan Allah yasa lafiya.

Suka gaisa cike da girmama juna. Kafin  Abban Nour ya fara magana.


Am Alhaji dama inaso ne ka bani dama ko zuwa gobe ne ina so nazo na ganka.

Fargaba ta kama Abban Basma. Ya bude baki da sauri yana tambaya "lafiya  dai Alhaji."?

Cikin  murmurshi yake magana, "lafiya lau, ina so ne mu tattauna wata magana ne.

Da kyar Abban Basma ya kwantar da hankali sannan ya bawa abban Nour dama daya zo gobe su tattauna din.




Yammaci nayi Abban yayi sallama, a gidan su Basma. Abban Basma ya mishi iso a falon bak'in shi.


Ya tarbe shi da ruwa da abin sha. Sun gaisa sosai. Abban Basma yayi jugum cikin fargaba, yana fatan Allah yasa zancen kawo lefe ne ya kawo shi.



Alhaji mukhtar ya muskuta, sannan ya fara  jawabi. Yayin da alhaji  Alhaji Yunus ya bashi duka hankalin shi.


"Am Alhaji dama wata magana ce nazo da ita saboda maslaha, kuma naga ya dace muyi magana daga ni sai kai.


Ya danyi shuru, ya lura da dan tashin hankalin dake kan fuskar Alhaji Yunus. Sai kawai ya kauda kai ya cigaba da magana.


Wato wani al,amari ne ya faru jiya da maraice. Ita mai mai da dakinka da ita yarinyar da ake nema sun zo har gida sunyi magana   kan cewa basa buk'atar wannan aure.!!


Sannan  an tambayi yarinyar agaban ita mai  dakinka shin tana bukatar auren tace bata so, sannan ta jaddada hakan agaban shi Nuran bayan mahaifiyar shi ta kira shi."

"Innalallahi wa in inna ilaihi raji,un."

Shi Alhaji Yunus yake ta maimaitawa, ji yake kamar yayi  hawaye, wannan wane irin wulak'anci ne halima tayi wa yasan iya abinda taje tayi musu a gidan mutane."? Halima ta zubar masa da k'ima.


Ganin  yanayin da ya shiga na tashin hankali yasa abban kokarin kwantar mishi da hankali, 


To shine nace Alhaji kada azo ayi abu da son zuciya, ya dace a tsahirta a samu amincewar tasu tunda ita yarinya dai da ita za,a zauna, kuma auren nan fata muke ayi ya d'ore. Saboda haka shima yaron zan bashi dama idan ya iya shawo kanta toh, Allah ya tabbatar da alkhairi, zamu gani zuwa wasu lukuta ko ya kace alhaji."?



Abban Basma yasa Handkerchief din sa,  ya goge gumin daya tsatstsafo masa. 

Rauni sosai cikin muryarshi wanda zai yake nuna tsananin tashin hankalin da yake ciki.

"Don Allah Alhaji kayi hakuri don manzon Allah wallahi ban san  abin nan ya faru ba...!!


Alhaji Mukhtar ya dakatar dashi yana fad'in, "ashsha.. ashsha  Alhaji ya da magiya haka."? 

Wallahi maganar nan saboda maslahar yaran yasa nazo maka da ita ko kadan ni ban bata raina ba akai, don bana nan ma suka zo dake da safe ne. Kayi hakuri ka dauki komai a sannu, su sha'anin mata sai a hankali. Kada ka dawo Alhaji. 


Abban Basma ya kara gyara zama..

Dole na roki afuwarka Alhaji. Domin wannan cin mutunci ne, ya za,ayi  azo har gida saboda rashin hankali haba ai abin babu mutunci. Don Allah kayi hakuri wallahi bani da masaniyar hakan. Kuma ita matar ba ma tare da ita shiyasa take kokarin hana auren. Amma kayi hakuri don Allah a bawa mutanan gidan hakuri suma don Allah."!!


Cike da kunya alhaji mukhtar yake magana domin  bai so yasa abban   Basma cikin wannan halin ba. 

Babu shiri ya mike da shirin tafiya. Kayi hakuri kaima don Allah sannan kabi komai a sannu. Wallahi babu komai a wajena wannan abin ba komai bane illa neman samun maslaha, kuma mu cigaba da addua Allah yasa alkhairi dama harkar aure dole ana samun kalubale. Amma wannan abin ba komai bane balle kuma kasan sha,anin mata sai su. Ayi hakuri dai Allah ya tabbatar mana da alkhairi."

Ya mik'a mishi hannu jikin  abban Basma a sanyaye sukayi musabiha.


Ya mike da kyar ya raka Alhaji Mukhtar  cike da kunyar shi. Don abin da Halima tayi yaja mishi kunyar manyan mutane irin su  Alhaji mukhtar. Kuma yasan ta gama zubar mishi da k'ima. 


Tafiyar abban Nour kenan Alhaji Yunus ya shigo gida. 

 Yanayin sa ya tada hankalin Hajiya Salma  ta bishi dakin shi da sauri..


Ta tarar ya yaye babbar rigar shi, ya cillar a tsakar dakin yana shirin juyawa zai fita. Alhaji lafiya ta tambaye shi.

Sai da ya juya zai fice sannan yayi mata magana a fusace yana huci.


Billahil-aziim sai Halima ta gane wanene ni.!! Ya cigaba da tafiya bai kara magana ba.

Hajiya Salma ta bishi da sauri kiranshi ta tsorata da yanayin nashi amma ina tuni ya fice.  Ta biyo shi har Harabar gidan tana kira amma ya fice ko mota bai dauka ba.


Ta dawo gida cike da rudu tana tambaye tambayen da babu amsarsu. Fatima meya faru da Abban ku. Ina tunanin gidan halima zaije  fa. Ina tsohon abinda zai faru ko me tayi masa oho."

"Kinga dakko hijabin ki muje wallahi ban aminta da fitar Alhaji zuwa gidan ta ba. Fatima ta taso  babu shiri. Itama hankalinta duk ya tashi.




________________

Mamaki da razani ne suka tarar tararwa  Hajiya  Halima ganin Alhaji Yunus a gidan ta kuma babu neman izini daga sallama ya shigo cikin falon.

Ta mike  tsaye  a dan tsorace, ya nunata da yatsa. Sannan ya rigata fara maganar da take shirin yi cikin fushi.

"Halima kinyi abinda kikayi kinji dadi kuma yayi kyau bazan ce kinfi karfi naba, don idan nayi niyyar   daukar matakin zakiyi mamaki amma zan nuna iko a inda nafi ikon sosai, don wallahi baki isa kin iko akan yata ba kuma aure babu fashi.!!

Kan tayi wani yunkuri ya wuce ta ya nufi bedroom dinta.

Aikuwa sukaci karo da Basman daya shigo nema don tajiyo muryarshi tana shirin fitowa taga me zaiwa mahaifiyar tata.


Ai kuwa ya kife ta da mari kafin ya jata fii ya zubar da ita a kasa.

Cikin tsananin fushi yake maganar.


Kinje kinyi abinda kukayi  ke da uwarki yayi muku kyau wallahi idan hakan ya zama silar fasuwar auren ki Basma hakkina sai ya biki don nayi iya kokari na kuma bazan sake saka hannu akan al'amarinki ba. Don na sauke hakki na a kanki.  



Meye haka me kake ji dashi ne zaka shigo min gida kana min hayaniya kuma don wulak'anci har uwar daka me kake nufi.


Ya juyo a fusace komai ma ina nufi.. Don baki isa kin hanani iko akan yata ba.

"To wallahi ka fita kafin na tara maka jama'a."

Ya daga muryarshi ya fuskanto ta shima.

Ki tara mini jama,ar Halima sai me aini kin gama zubda min da k'ima kuma sai Allah ya saka min abinda kikemin ina yiwa  yata tarbiyya kina rusawa."


Hankalin Basma ya tashi har taji ta dan fara nadamar abinda tayi. Don  bata san abin zai zama haka ba. Yau abban ta har cikin uwar daka saboda ita."? Shida da wuya ma ya shigo cikin  gidan tun da can ma idan yazo ganinta."?


"Hmm, kada ka manta ba kai kayi min nakudar ta ba ehe kuma wallahi ka kara tabata sai sharia ta  rabamu don baka isa ba ka nuna mini iko."


Bai tsaya komai ba saboda xuciya.. ya rufe Basma da duka tana ihu. Yana fad'in idan  na karya ta sai naga naki matakin..wallahi Halima  nayi nadamar haihuwa tare dake da kika haifa min abinda zai bujure min.


Basma cike da nadama take bashi hakuri tana kuma yayin da hajiya Halima ta kasa kwa kwatarta duk kurinta.. Don abban mahuci yasaka da ya gani a gefe sai da ya kakkarye sannan ya kyele ta. Lokacin Hajiya Halima ta fita waje neman dauki inda ta hadu da hajiya Salma suka ranks rankaya babu  tsayawa ce-ce-ku-ce.


Huci yake yana ta  sababi. _"Saboda baki dauke ni mahaifi ba kinfi son ki ta garari kina wayo a gari kina son ki lalace ko." Kina biye mata tana doraki kan hanyar banza. Wai har ke kinsan ki je gidan mutane kuyi musu cin mutunci don kawai dansu na sonki.? Cewa nayi miki Alhaji mukhtar sa,a nane ko itah matar tashi sa'ar uwarki ce."? Idan daraja da mutunci ne kin isa ku nuna musu."? Saboda ki nuna baki da tarbiyya yar mace  ce ke koh"?_


_To Allah ya gani bada yawuna kuka je ba kuma mutunci na da kuka zubar na barku da Allah kuma illa kanki kikayi wa..._



Hajiya Salma ta dakatar dashi. Don Allah Alhaji kayi hakuri kada ka aibatata. Kayi hakuri kazo mu tafi tun farko bai dace kazo bama. Basma  yarka ce ka dinga mata  adduar shiriya ba fada ko aibatata ba.


Ya goge gumi ya juyo ya kallesu. Mataki daya zan dauka ko ta bini ko kuma idan bata bini gida yau ba to na rantse bazata kara taka min cikin gidana ba.


Aikuwa bazata bika ba. In yaso ka cireta cikin yayan naka  sai me."?

Cewar  Hajiya Halima kenan cikin fushi.


Zai tanka mata, matar shi ta tsaida shi. Sannan ta bige  da rokon sa kan ya fito sun zo da mota. Don ita damuwar ta shine ya fito daga cikin gidan.


"Don Allah Alhaji kayi hakuri kajira mu a waje yanzu zamu fito da ita din."

Dakyar ya juya zai tafi yana hararar Hajiya Halima. 


Itama hararar ta jefa masa kafin  tace, "kasani baka daki banza ba don wallahi sai na dauki matakin sharia kan ci muni mutunci da kayi har gida.!!

Cikin kaushin murya shima ya maida mata martani.


Ki kaini kotun koli!! Kuma indai baki barta  ta biyo ni ba kada ta kara kirana ubanta."

Fatima ce ta hau mishi magiya.

Don Allah Abba ka fito kayi hakuri.


Ya juya ya fita a dakin.

Ya bar Halima tana ihun sababi.


Hajiya Salma ta sunkuya tana wa Basma nasiha duk da har yanzu bata san  abinda tayi ba.


Hajiya Halima ta janye ta tana magana cikin gadara. "Malama zoki  bar gidan nan munafuka asirin da kikayi yayi saura ki jira nawa martanin.."

Hajiya Salma tayi murmurshi, "Hmm Halima kenan ke kika san asiri da kike ambatarsa amma kiyi wa kanki fada yarki macece.!! 


Bata jira cewar ta ba itama ta juya saboda bata son tashin hankali. Tana cewa Basma, Kibi mahaifinki dai Basma don da uba ake ado sannan aure shine darajar mace.!!


Tanajiyo Halima tana  zaginta amma sai tayi murmurshi kawai don bata da lokacin ta.



"Bayan fitar su Halima ta koma gun yarta  tana rarrashi tare da kara hure mata  kunne  tana kara nuna mata  ubanta ya tsane ta ne kawai don an rabasu da ita."



Basma taji nadamar abinda tayi amma tana tsoron bin mahaifinta. Don ta daku a wajen shi.



Amma dukan da yayi mata yayi tasiri matuka  wajen shigar da ita hayyaci har ta fahimci tayi  kuskure sannan kalaman shi sun tsorata ta.




Su hajiya Salma kuwa, sunje gida cike da hikima take shawo kan mijinta  har ya dan sakko sannan ta nuna mishi illar zuwa gidan Halima sannan ta taushe shi kan ya dinga yiwa 'yartashi addua.


Sai daga baya ya sakko har ya sanar da ita a binda Halima ta aikata.

Hajiya Salma ta dade da mamakin abin daga karshe ta nuna mishi kada ya damu.



___________________________



Hajiya Rukayya  ta zaunar da Nour sosai take tausar shi..ta karanta mishi abubuwan da take guje mishi akan auren macen da bata yi dashi da kuma illar auren mace mara tarbiyya da kuma yar mace. Ta bashi misalai da dalilai kala-kala  sannan ta shiga nusar she shi abinda take gudu.


_Nour ni mahaifiyar ka ce, ko kana son ka auri mace n da zata rabani da kai.."?  Ya kalleta ta jinjina  kai. Tabbas bakasan son mace yana rufe idanu ba har a dinga hango laifin uwa imma ta hanyar kissa ko kuma ta asiri."? Mata da yawa sun rabamu maza da iyayen su. Ko kana son a dinga wulak'anta min kai ko yaushe ka zama baka da kwanciyar hankali."? Wallahi na tabbatar idan ka auri yarinyar nan sai kaji dama baka aure ta ba tunda har abin ya fara da haka._ "Ka tuna fa yadda babu kunyar ido na ko naka amma ta bude baki tace bata sonka haba nour ai so ba hauka  bane.. nidai ina rokonka kuma ina baka hakuri don Allah ka cireta a zuciyarka badon bana sonta ba ko  don na hana sunna, sai dai don a zauna lafiya kuma in sha Allah, zaka sami wacce ta fita kaji. Allah yayi maka albarka ya baka mace ta gari.


Amin mama inji Nour.


Don bata barshi ba sai da ya yaji ya cire kaso  mafi yawa na son Basma daga zuciyar sa. Don yana matuk'ar son mahaifiyar shi idan ya tuno d'awainiyar da ta sha dashi yana k'arami. Don yasha jinya typhoid data sarke shi yana d'an shekara sha uku. Sai da yayi shekara daya yana fama. Babu wanda ya zaci zaiyi rai ma. 

Ya saki jiki sosai kuma ya tabbatar wa da mahaifiyar tashi cewa ya bar abin.


Don haka lokacin Abban ya tuntubeshi da zancen yana fada mishi sunyi magana da mahaifin yarinyar yayi hakuri ya cigaba da shirye-shirye kada wannan abin ya dame shi.


Nour ya gyara zama yana zayyanowa mahaifin shi jawabi.


_"Abba dama bansa damuwa ba.. kuma abbah ni nama hak'ura na janye._ ya fada yana sosa kai.


Alhaji Mukhtar ya tareshi  da fad'a. "Menene haka Nour."? Ita hajiya rukayyan ce tace maka ka yanje."?

Nour yayi saurin girgiza kai.

"A,a Abba kawai na hakura ne, zan nemi  wata kawai."


Haba Noura so kake ka kunyata ni."? 


Bayan munyi magana da mahaifin yarinyar nan ma kana so ka maidani karamin mutum kaima koh."?

Nour ya girgiza kai. A a Abba wallahi dama na hakura ne kawai bana so ayi mata dole."


Cikin fada Alhaji Mukhtar yace, "to a wanne dalilin zaka hakura da tunda kuke tare ka taba cewa baka so sai yanzu. To ma ai saika saka hankali a zancen. Ita yarinyar anya ba tilas ta ta akayi ko kuma zuga ba."? Don da bata ce bata so ba sai yanzu."?

Nour ya gyara zama ya zayyanowa mahaifin shi abinda ke faruwa tun asali kuma ya fada mishi cewa dama bata aminta dashi ba mahaifinta ne ya yanke mata hanzari yace ya turo amma dama bata son shi."



Alhaji Mukhtar ya yi jimm kafin ya samo abin cewa. 

"Eh duk da haka dai kayi hakuri za'a  san abinyi sannan ya dace kaje dai ku sasanta kai da ita don fasa aure fa ba karamin al'amari bane."


Nour yasan mahaifinshi don haka ya amince zai je. Kuma dama yana son yaje yaga Basma face-to-face don ya tabbatar mata shima dan halak ne.




Washe garin da yaje gidan su Basma yadda Abbanta ya tare shi yasa sai da yaji tausayin mutumin sannan Abban Basma da kanshi ya dinga bashi hakuri har Nour yaji kunya. Yana fad'in babu komai Abba. 

A take Abban ya fad'a mishi cewa tana gidan mamanta.

Sannan ya roke shi. Don Allah kaje kaji Nour ka dinga hakuri da Basma.

Sannan yace ya jirashi.

Ya shiga ciki ya fito ya mik'a mishi wayoyin Basma gashi ka bata kaji.  Amma da sharadi idan  har ta yarda dakai kuma ta baka hakuri.

Nour ya karba da hannu biyu yana wa Abba bank wana. Abban sai albarka yake sa mishi yana ta kara bashi hakuri, tare da gode masa sosai. Nour ya nufi gidan cike da kwarin guiwa.


"Babu musu Basma ta fito da kace ana kiranta don bata zaci Nour bane tunaninta yafi bata Yusuf.


Sai da gabanta ya fadi da ta taganshi. Kuma yayi mata wani kwarjini na musamman.


Ta tsaya tana fuskantarshi. Ya k'are  mata  kallo duk zantukan mahaifiyar shi suka dawo mishi kunne, _babu abinda Basma zata nunawa sauran mata._

Zuciyar shi ta raya mishi wai ace wannan ce zata wulak'anta mishi mahaifiya, take yaji takaicinta ya kama shi.


Ita kuma wani tunani ne ya tsarga mata a zuciya.


_Tabbas Nour mai tsada ne kawai son xuciyarta da kuma yusuf yasa ta kasa fahimtar hakan, bayan haka ma gidan su da ta gani ta sha mamaki bata zaci sunkai haka ba._


A hankali ta fara lura da kallon kaskancin daya fara yi mata.


Ta bude baki zatayi mishi magana. Niyyar ta ta kira sunan shi. Amma ga mamakinta sai ya dakatar da ita.


Cike da izza yace.

Bana buk'atar magana Basma ina maman ku."?

Tayi mamakin maganar amma taji sanyi  aranta zatonta wani abin ya kawo Nour.

Ta nuna mishi ciki.

Sannan ta mishi nuni da su shiga. Babu musu ya bita  yana murmurshi.


Hajiya Halima bata gane Nour ba ita dai Idonta ya hango mata Basma da wani yaro wanda da alama yana cikin jin dadi kayan jikin shi sun bayyana haka, haka fatarshi.


Ya nemi kujera shima ya zauna. Amma hajiya Halima tayi mamakin yadda baiyi  yunkurin gaida ta ba sam. 


Basma kallon shi take sosai tana mamakin shi.


Hajiya Halima ta saki murmurshi ganin ya bude baki zaiyi magana, don tana mamakin yadda take mishi kallon sani. To kodai Yusuf ne.!!


Ya kalli Basma sannan ya kalli maman ya fara magana.


Am yadda kuka je gida kuma kuka sanar so nima nazo na sanar.

Ya kalli Basma ido cikin ido.

"Da ina sonki tabbas amma ni ma yanzu sam  bana kaunar ki, don haka kamar yadda kikace idan na aureki xaayi  Batacciya so bama zan aureki ba bare ayi haka.

 Ina nufin na fasa aurenki but kudin na bar miki. Sannan  ya ciro wayoyin a aljihun shi. Ya dire  su ak'asa.


Wannan sakon abbanki ne yace na baki idan kin aminta da aure na amma ni babu buk'atar ki amince a gareni. Saboda haka gasunan."


Ya mik'e bai kara koda Kalma daya ba ya nemi hanyar fita.


Hajiya Halima ta kasa motsi.


Sai da ya iya fita sannan ta miko hannu kamar me neman abu. Bakinta kuma ya bude.

"Am dama wannan ne Nour din."


Basma bata iya bata amsa ba ta mike ta bishi cike da rashin sanin dalilinta ma na binshi, kawai dai taji ta babu nutsuwa. Bata taddashi ba sai ihu da kurar motar shi.



Kamar ta rusa ihu haka ta dawo gida. Hajiya Halima taji jugum babu bakin magana. Bata taba zaton yaron  da gidan su sunkai haka ba. Bata jin Yusuf zai  nuna mishi wani abu. Sai taji wani iri a jikinta itama amma sai ta nuna bata babu komai a ranta, tayi murmurshi ta kalli tace. "Hmm ya ga dama ya baki wayoyin kenan."


Basma ta tamke rai, ko kallon maman tata batayi ba ta debe wayoyin tayi _bedroom_ don idan ta kalli maman wani takaici mara iyaka takeji. Kuma ta rasa dalili.


Ta bude wayoyin babu chaji sosai amma duk da haka sai da ta lalubi number da take matuk'ar buqatar kira.

"Ai kuwa an d'aga."


Muryarshi kamar mai bacci taji shi yana "Hello, wanene."?


Abin ya bawa Basma takaici matuk'a, take ta bude murya sosai sannan tace. "Wanene"?

Yusuf ni kake tambaya wanene."?

"Do you mean that you delete my number."?

Cikin murya babu tashin hankali yace, "Please kada ki dameni fa.. ni nayi losing contact naki and please mind ur own business naga aure zakiyi  so ki daina kirana."

Niba aure zanyi ba idan ma zanyi bazan daina kula ka ba bare kuma an fasa."

"Hmm, ya wartsake daga baccin.

Yayi wata siririyar dariya.

"Hah..tell the dull, but not me."

Cike da takaicinshi tace, look Yusuf wai zanyi maka k'aryane.

Nooo I know baki yin k'arya..but forgot kawai da wani yusuf don yanzu  ba dashi kike magana ba bye.!!

Ya katse wayar.

Ta cije dan yatsanta ta kifa kai kuka takeso tayi amma ta kasa, yau dai ta tabbata _loser_ din data kira Hafsah. Babu Yusuf babu Nour. 


Ta rasa masifar dake bibiyarta wato tun data ga Nour a gidansu take jin wani abu game dashi bare kuma yanzu data kara ganin shi a yau kuma ta mishi kallon tsaf. Gaskiya Idonta ya rufe. Gashi shi wanda take komai domin shi ya riga ya gama yayin ta, bata jin zai kara sauraronta aikuwa idan hakane bazai yuwu ta kyale Haala da Yusuf haka ba, kuma tabbas dole tayi da gaske wajen ganin batayi _biyu babu ba_ Dole ciki ta samu daya ko Yusuf ko Nour.!!🤔 


Kwanakin da suka biyu gabadaya uwar ta kasa gane kanta duk ta daina walwala kuma ta daina hira da ita. Tana janta ajiki amma taki sakin jiki dole ta zuba mata ido. Tana kiran Yusuf kullum amma gabadaya ma ya daina daga kiranta.. daga baya ma ta daina samun shi da alama ya sakata a blacklist. Tana mamakin yadda Yusuf yai mata irin wannan watsarwar kuma tanajin ciwon hakan a ranta gefe ga damuwar Nour da take neman zamar mata jaraba. Don ba karamin mamakin hakan takeyi ba ita kanta.


Abinda bata sani ba shine; "Shi Yusuf sam baya son abinda zai kara hadashi da ita don yana ganinta yake tuno Hafsah haka kawai, kuma yana tuhumar  kanshi da Basman kan Musgunawa Hafsah, ga mafarkanta da yake ta faman yi yanzu a kullum. Gashi sam bashi da wata kafa da zata hadasu kwata-kwata don taki accepting friend request dinshi a facebook.




 Maman ta taje har gidan Alhaji Yunus ta debo mata kayanta. Taji dadin hakan amma bata nunawa maman a fuska ba. Amma kuma tana tunanin abbanta aranta tasan ta mishi laifi kuma har yanzu bai sakko ba amma batayi tunanin neman gafarar shi ba sam.






____________________

Yau da wayar shi ta karya, cike da jin dadi ta d'aga tanajin nauyin shi.

"Morning madam." Yace mata.

Itama tace morning..

Ya saki dan murmurshi tare da cewa can't u call me oga.!!?

Ta danyi yar dariya itama.

Hmm bazaki ce min ba koh, saboda ba oganki bane ni koh."?

Tayi shuru.. uhum."?

Ya kara ce da ita. Sai ta girgiza kai. Kamar ya gani. Yace "Hmm, cikin rage murya yace Hafsah."

Tayi shuru bata amsa ba.

Ashe dama kishi me dake haka."?

Taji nauyin shi sosai.

Sai tayi yar dariya.

"Ai kin hukunta ni da yawa kinga nima bana kuma ba koh don Allah."? 

Ya fada da wani salo kamar yaro.

Dariya ta danyi.

"Kiyi magana please kina min rowar muryarki Hafsah.!!

A hankali itama kuma da niyyar jan hankalinshi tace, "A'a fah.!!

Aikuwa tayi nasara don Ukhashatu har gyara zama yayi.

"To yaya ne uhum."?

Babu komai fah ta fada.

Thank you Hafsah na please ki so ni kinji."?

Taji ya fad'a a maraice.

Tayi jimm tana nazari. _me zata mishi me ya fahimci ta fada tarkon shi._


Bata gama tunanin taji yace please, don annabi  (saw) badon ni ba.

A hankali tace "Okey don mind."

Yaji kamar ta sauke mishi wani nauyi don haka ya sami sukuni wajen kara tambaya.

"Please say you love me.!!

Ta sauke numfashi a hankali wanda har cikin  kunnen shi zuwa zuciyar shi.

Please durling.!!

ya kara rok'a. 

Cikin  siririyar murya ta ce, "Okey I love you."!!

Yaji dadi sosai har da gyara zama sannan yace, please "say it again."!!

Tana so ta tabbatar mishi da son da take mishi don haka babu jira ta kara fad'a. "I love you.!!

Dadin kalmar yakeji akunnen shi kamar me don haka ya kara nema.

Once again dear.!!

Cikin shagwaba tace "Nooo sau it to me."

Babu musu shima ya fada da taushin murya nashi ma har da salon tabbatarwa. "I love only you.!!


Ta sauke siririyar ajiyan zuciya. Hadi da cewa thank you dear.!! 


Yaji dadin godiyar.

Don haka yace _you deserve more dear.!!_ taji dadi sosai sai dai kuma wannan kalma yana daga cikin kalaman da Yusuf ke fada mata.

Amma ji tayi kamar yau ne aka fara fada mata.


Zaki fita aiki koh."?

Ya tambaye ta.

"Eh."

Okey  kada nasaki kiyi late koh."? 

Tayi shuru sai agogo data kallah.

Okey ki shirya my dear sai kin dawo please ki  kulamin da kanki."

"Okey u too tace mishi."

Thnk you Queen bye."

Sukayi sallama ya katse wayar yana murmurshi itama haka.


_______________________

Abban shi ya kirashi sannan ya nemi karin bayani akan zancen daga karshe ya bayyana mishi komai. Abban ya nuna jin dadin shi kafin  ya zarce da kalu-balentar shi.

Yanzu idan auren nan tazo cikin gaggawa ina zaka zauna Ukhashatu."? Tun da saboda haka nake nuna maka kayi gininka amma kaki.

"Afwan Abba bansan abubuwan zasu zo min haka bane."


Babu komai ai haka al'amarin Allah yake  sai ku zauna a gidajen nan na estate ko baka so."?

Ukhashatu cikin ladabi yace inaso Abba an gode Allah ya kara girma."


Amin ya Allah

inji khady.




Duk wani shiri anyi shi angama su Abba suka tsaida ranar zuwa.

A ranar Hafsah babu aiki amma sai ta wuce gidan auncle abdullah don suna dasawa da matar shi sosai tana da kirki. Hafsah bata san dalili ba amma taga mama ta nuna tana son taje can  din yau, duk da ta zaci ko wani sakon mama zata bata amma bata bata komai ba banda sakon gaisuwa.


Su kansu su Zainab sunyi mamaki da suka ji wai neman auren yayarsu za,a zo.


To dai anyi komai cike da mutunta juna, su Abban Ukhashatu sunzo don har da Abban Ukhashan saboda  matuk'ar son da yake Ukhashatu.


Basu tafi ba sai da suka cake kudin aure kimanin naira d'ubu d'ari.


Basu tsaida rana ba dai amma a yadda suka tattauna abin bazai wuce wata uku zuwa hudu ba saboda kada Abbah ya shiga harkar zabe.


Yau farin ciki na dabanne wajen Ukhashatu, abbanshi, hajiyarshi da kowa na gidansu, haka abban Hafsah da duk yan gidan banda Hafsah da bata san abinda akeyi ba.


Bayan shigowar abbah cikin gidan shida yan uwanshi su biyu; sunyi suka gabatar da kudin ga hajiya Amina _maman su Hafsah._

Tasa albarka sannan tayi addua. Bayan tafiyar yan uwan Abba, Abba ya gargadi su Amira kan kada su shaidawa Hafsah halin da ake ciki a waya su ta dawo shi da kanshi zai sanar mata.


Abban Ukhashatu sun tafi suna yabon karamci irin na su Alhaji Habeeb, adduar alkhairi kawai akewa juna.


Zuwa dare duk wanda bai san da zancen neman auren Ukhashatu ba a wanda da ya dace su sani to duk sunji labari sai fatan alkhairi ake kawai.



Ukhashatu jinshi yake kamar ango a ranar yayi godiya ga Allah babu adadi sannan yaji kwarin guiwar aiwatar da wasu abubuwa game da Hafsah wadanda ya dade yanaso ya aiwatar toh dama dama yake jira saboda kada aga ya zak'e  ko ya wuce _makad'i da rawa._



Washe gari dai yayi niyyar fara bujuro mata da kudurin.



Ita kuwa bataji komai ba sai dai yawan faduwar gaba da ta dinga ji tana gidan auncle abdullah. Auncle yasan da zancen amma daya dawo baiyi wasu alamu da zasu nunawa Hafsah wani abu ya faru ba sai dai ya nemi data kwana tunda dare yayi mata kuma ta amince sannan ya shaidawa abbah cewa zata kwana.

Mamakinta a ranar sunyi waya da Ukhashatu har ta dinga mamakin yadda yake farin ciki sannan Kuma ya kirata da wani suna wai, _Amaryata!_ 


Bata kawo komai ba sai dai ta fuskanci cikin nishadi yake matuk'a kuma ranar motsi kadan taji yace, "Allah ya kai mu ranar aurenmu amaryata.!!

Ranar dai tasha ruwan kalamai da tarairaya.


Amma wani abin mamaki sai Washe gari daya kirata inda yayi mata wata magana da tasa ta fusata don aganinta bashi da hurumi akai..


Da safe ne misalin karfe 11:30pm.




Sun gama break ita da yan matar auncle da dansu guda daya Hamid ana ce mishi daddy sai yar da take goyo ita kuma sunan hajiya ne da ita wato kakar su Hafsah.



Tana kashinkid'e tana tunaninshi a lokacin. Abubuwa da dama take tunowa game dashi. Yanayinshi yadda yake nuna damuwa da ita sauk'in fushinshi, da kuma kirkin shi. Komai dai yayi yadda take so sai abinda ba'a rasa ba ma'ana  a wani abin ya cika 100% wasu kuwa sai 90% ko 80% tunda dama duk d'an adam ance _tara yake bai cika goma ba._ 


Idan zata kasafta halayenshi da dab'inshi data fahimta da sauran mu'amala na yanayin shi da cikar d'an adam taka ta dorasu a mizanin burinta ( _akan irin mijin da take fata._) zata iya cewa Ukhashatu ya cika 89% cif cif. Tayi amanna zasu iya zama inuwa daya tunda baka taba samun mutum yadda kake so _hundred percent_ sai dai sauran tana kiyastawa da kuma fatan koda gaba azamansu tana iya tsintar cikon 15% d'in tunda bata gama tantancewa da kuma karanta komai nashi ba.

 Tunda kana iya samun mutum da dabi'ar da baka mishi zato ba wacce zaka fi sonta fiye da wacca kake fata. Hafsah zata so Ukhashatu ya cike gurbin 15% d'inshi ya kara su a adadin _SOYAYYA DA KYAUTATAWA_ a gareta.


Ta lumshe ido saboda baccin safen da yake neman d'aukar ta.


Wayarta ta sata bude idon saboda k'arar da takeyi mara cika kunne sosai.

Ta dauki wayar tare da mishi sallama.

Ya amsa mata.

Sannan yace, I hope ba bacci kike na  tasheki ba amarya.!! 

Tayi murmurshi tare da sa hannu ta murje idanunta sannan tace "No ba bacci nake ba."

Okey sannu 'yan mata.

"Yawwa." Tace. Sannan ta tambaye shi. 

Ya mum da sauran family.

"Mama na lafiya lau." Zan baki ita ku gaisa in sha Allah anjima da dare.

Tayi murmurshi sosai Okey thank you."

Suka d'anyi shuru sannan yace cikin nutsuwar murya da jan hankali.

My Hafs.!!

Na'am ita ma ta amsa tare ta tashi zaune gaba-d'aya.

Don Allah wata magana nake so muyi dake please ina so ki fahimce ni and ki bani amsa kinji."?

 Ta danyi jim tana son ta hasaso wanne zance yake son yi mata haka."?

"Kinji please taji yace sannan ya dora da k'arin bayani."


Kada kice na miki shishshigi amma ina buk'atar neman karin bayani ne kan abin kiyi hakuri kinji."


Cikin k'aguwa tace "Okey fad'a min toh.

Promise ba zakiyi fushi ba.

Abin ya bata dariya to mene haka yake mata k'unbiya-k'unbiya."?

Tana dariya tace "Okey go ahead."


Ya saita murya sannan yace, am kwanaki na ganki da k'awarki ranar da nazo har kike ce min kun dade baku had'u ba please ina son sanin wane alak'ar k'awance ke tsakanin ku, kinsan before naga wata ma and itama kince min kun dade baku hadu ba for long. Please mene hadin ki dasu and meyasa kike ce min kun dade baku hadu ba."? Am sorry please tell me.!!



Hafsah tayi shuru, tana son tayi tunani kada tayi saurin fushi ko yanke hukunci saboda haka ta yanke hukunci gwara ta bashi amsa la'allah bayan jin amsar kalmomin shi da zasu biyo baya su bayyana mata dalilin tambayoyin nashi.

"Kinji."

Yace mata saboda gajiya da shurun da ita.

Ta danja numfashi kafin tace "Okey but nima inason sanin dalilin tambayoyinka akan su.

Da sauri yace in sha Allah zan fada miji please kedai ki bani amsa don Allah har sunan su inason ji."

"Hmm tace dashi sannan ta kara da cewa kodai kasan su neh."?

Noo wallahi bansan ko daya ba kawai inason in sani ne.. tunda kince kunyi shekaru bakwa had'uwa amma kuma gashi sunzo gidanku  yanzu.

Hmm inji Hafsah sannan ta dora. "You mean baka yarda da abinda na fada maka bane koh."?

"Noo ba haka bane please ki  fahimceni."

Tana so ta kama shi da hujja  don haka ba bude baki tace. "Okey d'aya ta farkon Basma  daya kuma jamila. And duk mun dade bamu hadu ba because dama makaranta ne ya hadamu  da Basma and Jamila kuma na fada maka already bata nan so tazo garin nan ranar shine taxo mu gaisa." 

Ta karasa tana sauke dogon numfashi na takaicin tambayoyin da kuma haushin doguwar maganar data biye mishi tayi.

Ukhashatu yayi murmurshi sannan yace, Okey nagode amma please kiyi hakuri idan tambayar ya bata miki rai.

Hmm tace mishi sannan tace "Nooo mene abin fishi."?

Yayi dan murmurshi "babu!!

Sannan ya sake bujuro da wata buk'atar cikin taushin murya.

Don Allah idan  na roki wata alfarma zakiyi min."?

"Inajin ka." Tace da shi.

Please ki taimaka ki fahimce ni bada niyyar bata miki nazo miki da zancen nan ba kuma naso sai nazo mun tattauna amma na kasa"..Ya danyi shuru. 

"Idan kin amince zanzo mu tsara yanda zaayi."

Cikin k'aguwa tace, "Okey menene fadamin toh."?

Ya dan gyara murya sannan  ya fara duk da shima yana shakkar abinda zai fito daga bakin nashi.

"Alfarma guda biyu nake nema a wajenki na farko akan wadanan k'awayen naki please ki takaita mu'amalarki dasu badon ina zargin wani abu bane ko kuma nace kina kulasu sai dai am sorry to say zuciyata ta kasa aminta da yanayinsu bana son suna kulamin anaryata sosai."

Bai bata damar  tayi magana ba ya dora zancen shi na biyu.


"Sannsn ki taimakeni don Allah badon ni ba..ki yarda ina kishinki Hafsah da zaki iya min wannan alfarmar ki ajiye aikin da kike yi idan yaso sai mu nemi wani..bana son ana nuna min ke duniya suna kallon ki please ki amince.!!!



Wani irin yanayi na takaici da bak'in ciki Hafsah ta shiga wanne irin dama mutumin nan ya samu da zai dinga mata irin wadanan zantukan. Wasu sharadai akan abinda ya shafi rayuwarta."? Me ya maida ta shi yake iko da ita ko me har yake sa mata ido da wasu zantukan shi kan wai ya ganta da kawaye.. Yarinya ce ita  da zai mata wannan ikon da a gida ma sam ba'ayi mata shi."? Nufin shi ita mutuniyar banza ce kenan.!!!

Yanayinta ya sauya har wani kankance ido take, so take kawai ta amaryar da abinda ke ranta, so take ta sosa mishi rai yasan bafa classless bace ita da zai dinga mata irin wannan abubuwan ko dan yaga tayi saurin aminta dashi. Haushin kanta da nashi ya turnik'eta ta fara magana cike da tsiwa tana magana wata na ingizo wata saboda ta shak'a da yawa.


"Ban gane me kake nufi ba!! Ya zaka dinga min magana kamar kana da wani iko dani."? Nace maka dole kayi mu'amala danine bare ka kafa min sharadai na mutanan da zanyi mu'amala dasu ko kana da iko dani ne har kake fadamin na saki aiki nah saboda kai ke da ikon komai a kaina ko kai kasakani tun farko."??


Ya kasa samun damar mata magana saboda maganganun da take yi. shima sai yaji ranshi ya b'aci.


Dama haka yarinyar take."?

Daga yazo mata da magana cikin maslaha shine zata dinga fada mishi maganganu irin haka."?


Ita ma ta zaci zai tanka amma taji shuru sai itama tayi tsit ta kama kanta.


_Ni kike fadawa wadanan maganganun ko Hafsah."?_

Yasa kara jin takaicin shi to mene don ta fada mishi _da gaske ai bashi da ikon  akanta."_

"Nagode ya sake ce mata sannan ya kashe wayarshi."


Ta ajiye wayar a gefe tayi shuru tana tunani. "Ya bata mata rai matuk'a amma zuciyar ta ta kasa nutsuwa da maganganun data fad'a masa.


Aduniya bata son a dauke ta amatsayin mara mutunci ko kuma mara kunya.


Amma ita kanta tasan fusata tayi maganganun shi ne suka ingiza ta don tana ganin bashi da hurumi da al'amran rayuwarta da zai dinga tuhumar ta kan batun mutanen da take mu'amala dasu har gwara batun aiki wannan kamar shawara ce ya bata.


Ta dafe kai tana son ta tuno irin maganganun data fada masa amma sai ta kasa. Ta damu kanta kan abin kuma ta rasa dalilin damuwar.


Kusan awa d'aya dayin hakan kiran abbanta ya shigo wayar. Ta dauka da hanzari. Taji shi cikin farin ciki sosai, bayan sun gaisa yake ce mata.

Munyi kewarki sosai Yaya..gashi kinyi zaman ki ke..ki dawo yau mana kinga Bashir gobe zai koma makaranta fah."

"Da gaske Abba."? Ta tambaya bata son Bashir ya tafi.

Ki dawo kedai Yaya zanyi miki wani albishir nima." Cikin farinciki tace toh Abba gani nan yanzu zan taho ma."

To Allah ya kawoki lafiya.!!

Matar auncle abdullah babu yadda batayi da Hafsah ta zauna ba zuwa la'asar amma taki haka tayi wanka da tsakar ranannan. Auntyn ta bata wasu doguwar riga tasa tunda batazo da kaya ba.


Tayi mata sallama cike da zumudi ta dawo gida.

A dakin Bashir ta tsaya. Ya dake labulen yana ta shirya kaya. 

Yadda taga farawa fara'arshi abin ya bata mamaki gashi sai sai kallon ta yake kamar bai santa ba.

Ta gaji ta tanka.

Bashir wai fara'ar mene haka kai da zaka tafi sai faman kallona kake kamar baka sanni ba."?

Bashir yayi murmurshi kawai.

Zaka je ka tarar da sisin ka kana kallon mutane."

Sukayi dariya ita dashi.

Sannan ta tambaye shi "Abba na ciki."?

Yace mata, "A'a ya dan fita amma ba nisa yayi ba."


"Okey tace, bari na shiga cikin."

Tana shigowa taga kowa ya rude ana "aunty.!! Abinda ya bata mamaki shine har da mama.

Ita dai ba dadewa tayi bata nan ba bare ace.

Ta tare su itama da fara'a ta gaida mama sannan ta nemi waje ta zauna.


Suka ma sannu da zuwa suma. Babu jimawa Zainab ta karasa girkin da take. Ta zubo musu su duka sukaci.

Bashir ma ya shigo aka hadu ana hira sosai ana raha.


Sai daf da sallar la'asar Abba ya shigo bayan yaci abinci babu jimawa aka kira sallah suka fita shida Bashir sukayi sannan suka dawo Abba yayi dakin shi sannan yasa aka kira mishi Hafsah, tana jin kiran ta tuno da albishir d'in daya ce zaiyi mata don haka ta mike da sauri ta nufi dakin. Sai kuma ta ganshi shida mama su biyu a d'akin ta zauna a kasa kafin tace, "Abba gani."


Yayi gyaran  murya tare da gyara zama yayi mata wata tambaya da ta sata cikin mamaki.

"Yaya banda Ukhashatu waye yake zuwa wajenki kuma.?

Tayi dif tana kalli mama sannan ta kalleshi shi abban.

Jin batayi magana ba yasa yace.

"Shikenan koma mene ne lokaci ya riga ya k'ure."

Ina fatan zaki karb'i komai a yadda yazo.

Mamaki ta shiga na irin kalaman Abban. Me yake nufi kada dai Ukhashatu ne ya hada ta da Abban. Duk da tasan bai taba ganin abban su bama.

Tana wannan tunanin taji Abban na cewa. 

Yaya kinsan burin ko wanne iyaye shine 'su aurar da 'ya'yansu."

Hakika na dad'e ina saka ido a kanki da yadda kike Mu'amala da mutane kuma naga kinki bada damar da har wani zai shigo har ya nemi aurenki.

Sai dai ina muku addu'a dukan ku kan Allah ya baku mazaje na gari. To dai ganina da Ukhashatu na tabbatar addua ta ta karbu nayi fatan Allah yasa kin aminta dashi.

Kiyi hakuri Hafsah na tabbatar cewa lokacin aurenki ne kawai yazo shiyasa Allah ya kaddara komai ma. Bani ne na sa ayi haka ba iyakaci na nemi ganin iyayenshi ne sai kuma gashi cikin ikon Allah daga  zuwansu sun nemi na basu aurenki kuma na basu.!! 

Ya dire dogon zancen anan don hutawa. Yayin da Hafsah ta shiga motsi da kafafuwanta idan ta fahimta Abba ya bada aurenta ga Ukhashatu kenan."?

Ya akayi abin ya faru haka kamar a mafarki wai yau itace akayi haka ake cewa an bada ita. Maganar Abba ta dakatar da tunanin ta inda yake cewa.


Na ganshi rannan nace inason ganin iyayen shi cikin ikon Allah sunzo jiya kuma sun nemi a bawa dansu ke...manyan mutane ne su, saboda hakane da karfin Allah da kuma yak'inin ba zaki bijure min ba na karbi kudin aurenki naira dubu d'ari. Kuma in sha Allah sun nemi asa lokacin aure wata hud'u."


Hafsah nason ta d'ago ta kalli Abba amma kuma ta kasa _tanajin nauyin shi._


"So take ta tabbatar  da gaske ne Abba ke fada mata ya bada ita ga Ukhashatu."?


Ki amshi  zabin Allah kinji  Hafsah Allah ya yi miki albarka ya kai mu lokacin."


Mama tace "Amiin sannan itama ta gyara murya ta shiga nata jawabin.

"Nidai abinda zan fad'a miki shine "Kiyi hakuri kiyi biyayya ke macece lokacin ki takaitacce ne Hafsah shekarunki sunja ki duba kannenki su kansu sun isa aure. Don Allah kada ki watsa mana kasa a ido. In sha Allah zakiyi alfahari da zabin mahaifinki."


Hafsah tayi shuru tana d'an nazari.

_"Ita kuwa me iyayen ta zasu nema wanda bazata yi musu shi ba."? Ko da ace wani can suka dakko ba Ukhashatu ba suka bata ba zata iya yin musu ba, bare kuma suna da  hujja, itace ta kawo Ukhashatu har Abba ya ganshi."_


Abba da mama suka katse mata hanzari wajen cewa. "Kiyi magana yadda zamu tabbatar kin aminta da zab'in mu.!!"


Abba ya kara da cewa, ban yanke hukunci ba sai bayan binciken da nayi kuma anyiwa yaron kyakyawa shaida nima kuma ina mishi kyakyawa zato.!!

Kiyi hakuri kinji yaya."


Ta  kara kasa da kanta a kunyace tace 'Abba nagode Allah ya tabbatar mana da alkhairi."

Ta fadi haka ne kawai don ta kori shakkun su akanta amma a lokacin ba zata iya cewa ga taka takamaimai yanayin da take ciki ba, banda na tunane tunane barkatai.


Fara'a ta bayyana a fuskarsu suka shiga sa mata albarka da fatan alkhairi.

Nauyinsu yasa ta mike babu shiri ta fita. Ta barsu cikin farin ciki.


Ita kuwa tunanin yadda suka rabu da _angon_ ne ya dawo mata sai kuma ta tuno da salon da ya dawo kiranta dashi daga shekaranjiya wato _amarya_ Sai ta fara jin wani irin tausayi da kunyar shi don sai data baro gabansu amma _emotion_ din ya motsa.. Allah sarki ashe dama gani yake babu wanda ya kaishi iko da ita shiyasa ya dinga mata wadanan zantukan."? Amma me yasa yaki fadamata cewa ta zama mallakinshi."?


Ta fada tunanin tuhumar kai kan abinda tayi mishi, ta takura kanta har saida ta fidda wata yar kwalla. _Da wanne ido zata kalleshi... shikenan ta zubar da k'imarta a idon shi zai dinga mata kallon mara kunya.. me ya kaita ma tayi mishi haka."?? A yadda take so bazata taba barin wata b'araka ga mijin aurenta ba yadda zai dinga jin ta mishi ba  daidai ba tun kafin a shiga daga ciki..bata son ya sanya shakku a kanta._


Amma inaa aikin gama ya gama.!! Tana nan jigum tana shawarwari yadda zata gyara abinda ta bata. Gashi sam bai kuma neman ta ba tun d'azun. Gefe guda kannenta sun dame ta duk wani motsi nata suna ta kiranta "Amarya!! Ko kuma aunty Amarya.!!

Tana ganin kalar farincikinsu har take mamakin ashe dama haka suka damu tayi aure."?


Duk bayan minti sai taji fargabar da wanne ido zata kalli Ukhashatu."?

Wata zuciyar ke fada mata ta kirashi ta nuna kamar wani abu bai faru ba. Amma sai ta kalubalenci hakan gani take wannan kamar _nade tabarmar kunya da hauka neh"!!_


Ya dace tun farko daya kawo mata zantukan ta bishi a hankali  (ta boye fushinta) Sannan cikin hikima ta bishi da _toh din da ba'a aikatawa_ amma sai ta nuna ita macece mai aji kuma bashi da hurumin yi mata haka.

_Kuma idan zata kalli zancen shi ta wata fuskar tabbas ya fada mata gaskiya ne Basma da Jamila kowa ya gansu tabbas zai sa musu a alamun tambaya daga yadda suke yanayin shigar su._


Sannan ta kuma tuhumar kanta kan rashin tsayawa tayi mishi jawabi yadda ya dace ma'ana ta fada mishi gaskiya gashi ta jawo akan k'awance da babu shi a yanxu  (musamman ga Basma.) ta shiga matsala.


Har bayan magriba bata samu matsaya mai sunan mafita ba.

Sai kuma tana kwance taji kira a wayarta. Gabanta ya fadi da taga shine.

A sanyaye ta daga.

Tana dagawar ya mata sallama tare da cewa, ina kofar gidanku don Allah ki fito kinji."


Tayi jimm ko motsawa batayi ba.

Ya zatayi ta iya kallon shi a yau dai."? Bayan haka tana fargabar abinda zai fada mata ta idan sun hadun.


Sai ta tuna bai kashe wayarba kuma jiran cewar ta yake yi.

A hankali tace "Okey"

Tana tararrabin yadda zata fita tunda ta tabbatar  kin fitarta hakan zai tabbatar mishi cewa tana kan bakar ta ne.!!...



📝

HAJEEYAH KHAREMERH


*Wannan shine page na biyun karshe.*👏🏻👏🏻




♥♥♥♥

*ZAZZAFAN SO*

(Masoyin k'warai)

*Cigaban littafin Zazzafan so*

*(Guba ne)*

   💔💔


*By:*

*Karima Tijjani Mansur*

*(Hajeeyah khareemerh)*


*Dedicated to Unique in your love heart group members.*


📄 *Last*


*Ta sauke* wayar jiki a sanyaye haka ta mik'e ta sanya mayafi akan kayanta ta fito falo, gaba-d'aya tunani ya cunkushe mata zuciya _me zataje tace mishi."?_

Sai da ta leka d'akin mama sannan tace mata a kunyace tana yan soshe-soshe "Mama wai shine yazo."

Mama ta gane sai ta bita da kallo. "Haba Yaya kisa kwalli mana."

Hafsah tayi d'an murmushi ta juya ciki. Ta d'auki kwallin ta saka kuwa ta d'an fesa turare, ta shafa powder.

 Data fito kuwa a palour taga mama, Mama ta mata magana daf da zata gifta ta.

"Saura kiki bashi ko da ruwa ne."

Hafsah ta toshe bakinta tana dariya amma Mama bata gani ba.


Yana Harabar gidan daga gefe ta hangoshi tana fitowa.. shima tana fitowa ya hangota aikuwa tana ganin  ya ganta duk ta k'ara rikicewa taji k'afarta tayi nauyi da kyar take dagata saboda kwarjinin daya mata.


Tana k'ara doso shi tana gano yanayin fuskar shi, sam  bazata ce akwai alamu na farinciki ko akasinsa a tattare dashi ba sai kyau da ya kara had'i da wani kwarjini cikin shigar shi ta voil na maza me kyan gaske sai agogon shi silver colour da hula. 


Ya gyara tsayuwarshi sanda ta iso daf dashi, ya dan saci kallonta ya kawar da kai.

Ta hard'e hannu a kinji don samun kwarin guiwar tsayawa yayin da shi kuma nashi hannun guda daya ke cikin aljihun shi.


Ahankali ta sanya k'warin guiwa a muryarta ta mishi sallama.


Sai ya amsa a take babu wani jira amma daga amsawar bai k'ara ce mata komai ba.


Ta kalli gefe inda kujeru suke amma kuma bai zauna ba.


Cikin sanyin murya tace, "Baka zauna a kujera ba."

Ya girgiza kai "Noo nan ma is  Okey."

Ta gyara tsayuwa ita dai ba gwanar tsawaita tsaiwa bace sannan tafi buk'atar su zauna d'in zasu fi fahimtar juna kuma ita kanta sai ta fi sakewa."


Tana wannan tunanin taji yace "Zuwa nayi na baki hak'uri ai... ya d'an dakata.. 

"Bansan xanyi laifi ba idan nayi miki wannan zantukan amma yanxu na fahimci na wuce gona da iri kiyi hak'uri."


Kafin tayi yunk'uri sai kawai taga yana k'okarin juyawa.

Baki na rawa ta bude zata kirashi sai dai ita kanta bata san sunan da zata kirashi ba.

Sai kawai taji bakinta yace,

 "Allah ka tsaya!!

Haka ta iya cewa kawai, shima sai ya tsaya din kuwa.

Ta d'an kara takowa ta matso ya gama karanta raunin da take ciki.

"Ka zauna don Allah kaji..

Ya danyi jim, sai kuma

baiyi magana ba ya nufi kujerun itama ta bishi suka zauna kusan tare.


Wannan karon shiya fara magana. "To me kuma kike so  Hafsah ko baki hak'ura bane."?

Murya a dashe ta sauke numfashi sannan tace, "I'm sorry please wallahi ni bansan..."

Sai kuma tayi shuru.

"Baki san me ba."?

Sai ta kama bakinta don zancen bashi da k'arashe. Ce mishi zatayi batasan an bashi ita ba ko me."?

"Kiyi magana mana."

Tayi shuru don bata da abin cewa.

Shuru ya mamaye gurin sai shi ya zuba mata ido.

"Bai zaci zata iya mishi abinda ta mishi ba, kuma yanxu yaji tana bashi hakuri to me hakan ke nufi."?


Ya katse shurun da dan yin gyaran murya.


"Me yasa kikayi shuru uhum.."? Bai jira cewarta ba shima ya shiga fad'ar abinda ke ranshi.


"Ni ina tunanin kamar mun zama daya ne, zan iya fad'a miki ra'ayi na a kanki."

 Ya zubo mata idanu.. "Ba dole nayi niyyar miki ba Shawara na baki.. nima fa ina da k'anne mata Hafsah wallahi bazan aureki na cutar dake ba ki fad'a min duk wasu burikan ki in sha Allah  zanyi kokari wajen ganin cikarsu..amma fa har ga Allah zan kara fad'a miki banason aikin gidan TV."


Kanta na kasa bata d'ago ba tace.. "Kayi hakuri.."

Ya kalleta da mamaki.

"Meyasa kike bani hak'uri ne."? Ai ra'ayinki kika nuna ba fa laifi kikai ba."


Ya tausasa murya don ya lura neman kuka take amma yana mamakinta.. _kamar ba itace ta mishi fada a waya ba to mene dalilin rauninta a yanzu.?_


A hankali ta kara bude baki zatayi magana sai kuma ta fasa.

Cikin sanyi shima yace "To kiyi hakuri kema na aibata miki k'awaye.!!

Ta rasa abin cewa sai tayi murmurshin jin kunya tana kawar dakai.


Suka k'ara yin shuru..ita tana matuk'ar son ta cire mishi shakku akanta amma kuma ta kasa ta yadda zatayi ta mishi bayani.


A yadda ta karance shi har yanzu abinda tayi mishi yana ranshi kuma tabbas ya saka ayar tambaya akanta.


So take ta kalleshi don ta k'ara fahimtar shi don haka ta dago da idonta sosai a sanyaye suka had'a ido ta kauda ido gefe.

Daidai da mik'ewarshi.. "Zan tafi," yace da ita.

Tayi shuru babu magana  bata son ya tafi bata fahimtar dashi wani abu ba amma kuma ta kasa.


Sai ta lura da wani abu da yake mik'o mata, ita kuma tana can tunani.

Tayi sauri tasa hannu biyu ta amsa babu musu duk da tana shakkun karb'a.

"Ki gaida su mama."

Yace da ita tare da fara takun shi don barin gurin.


Sukaci karo da Bashir a tsakiyar gidan daidai lokacin shigowar shi kenan.

Bashir ya fad'ad'a murmurshi suka yi musabiha. Ukhashatu ne ya fara magana.. ya akayi mutumina baka tafin ba ne."?


Wallahi gobe nake shirin d'agawa.

Suka fara takowa zuwa inda Hafsah take, bisa dole tabar wajen.


Suka zauna suna fuskantar juna.. Ukhashatu yace "zamuyi missing dinka fa aboki."

Basheer yayi murmurshi, "Sosai fa especially mutuniyar taka.!!

Ukhashatu ya zubo mishi ido da wani kalar murmurshi akan fuskarshi wanda ke bayyana zallar shauk'i.


"Hmm to zamu hanaka tafiya." 

Sukayi daria a tare..


Sunyi hira mai tsaho wacce yawancinta ta zancen makarantar da Bashir yake yi ne. Ukhasha yake kwatanta mishi wani abokinshi wanda yake matsayin HOD a makarantar Bashir bai gane shi ba don haka suka rufe zancen da cewa..zan mishi nuni da kai ince qanina ne yana da kirki mutumin.

Bashir ya amsa da "Toh nagode Yaya.

Ukhashatu ya duba agogonshi. "Bari na wuce kaji."

Bashir ya mik'e suna takawa har qofar gida in da yabar motarshi.. _HONDA ACCORD._ motar da Hafsah bata ma san ya na da ita ba.


Sukayi musabiha bayan Ukhashatu ya shiga mota. "To qanina Allah ya kiyaye hanya kaji."

"Amiin, inji Bashir.

Ya motsa da niyyar juyawa Ukhashatu ya kirashi. "Bashir na manta Ungo wannan."

Bashir zaton shi sak'on Hafsah ne don haka ya mik'a hannu. Ukhashatu ya mik'o mishi kudin. Bashir yayi jimm, "karbi mana." Inji Ukhashatu.

Bashir ya amsa yana kallonshi da neman k'arin  bayani.

"Ka kara guzuri dashi nagode ka gaida su Abba.


Bashir yayi jimm jiki a sanyaye yana buda baki zai ce mishi "angode" ya  ga har ya fara tada motar duk da haka sai da ya fada "angode."

Ukhasha ya d'aga mishi hannu kafin ya ja motar ya wuce..

__________________

A palour ta fada kan kujera sanda ta koma cikin gida. Mufeedah ce da amira a palourn babu Zainab suna ganinta suka maida hankalinsu kanta da alama tana cikin damuwa.


Kamar ta rusa ihu haka take ji.. ya akayi tayi sakaci har ya tafi bata wanke kanta ba a wajen shi."?


Ta bata mintuna a daskare hankalinta na can ga tunani, sai da mufida ta kirata.

Yaya baki tab'a nuna min ya Ukhashatu ba aunty Ameera ce kawai ta sanshi.

Da zata share ta sai  kuma ta bude baki a hankali tace.. Idan ya qara zuwa zan kiraku ku gaisa."

Cike da fara'a Mufeedah tace "Yaushe zai k'ara xuwa eh yaya."?

"I don't know! ta fada a kufule.

Mufida ta kama kanta don taga kamar a sama yayar tasu take.


Kamar an tsikare ta yi zumbur ta duba gefenta inda ta ajye ledar data shigo da ita.

Ta dauka da sauri cikin zakuwa take son taga menene aciki.


Da sauri ta zaro abinda taci karo da shi..wani dan box (akwatu) ne shima ta buda shi da sauri ta zaro zoben da ta gani ciki sai shek'i yake.


A hankali ta zame zoben hannunta.. wanda idan zata tuna shine na Yusuf daya kawo mata dake ba sashi take ba sai lokaci zuwa lokaci saboda haka yana nan kar kasancewar shi _Gold_ shima na yanxun gold ne mai matuk'ar kyau. Ai kuwa tana zame shi tayi cilli dashi. Idanun qannenta tun dazu akanta don haka tana yarwa mufeedah tayi zaraf ta samu. Har suna fada da Zainab.

Yadda take zura zoben a hannunta a hankali ta kuma wani irin shauk'i tana jin wata iriyar k'auna na shigar ta.


Yayi mata kyau matuka a a hannunta tana gamawa ta maida akwatun cikin ledar sai ta lura da wata yar takarda a ciki da sauri ta dakko ta a dan nannad'e take don haka ta yi saurin bude ta yar qarama ce sosai. Da rubutun biro kuma da hannu (handwriting) me kyau taga an rubuta _"I love you.."_

Ta ja wata doguwar ajiyar zuciya da tunanin dalilin kyautan haka a halin da suke ciki..


Zainab da mufida har yanzu basu daina sa'insa ba akan zoben yayin da Hafsah ta kulle bakinta kawai taki ta kanta musu bare ta raba gardama.

Mama ta fito daga d'akinta.

Ku lafiya meye haka."?

Mufida ta mayar da jawabi "Maman wai aunty Hafsah ne ta cillar da zoben ta shine na tsinta wai ya Amira sai na bata.

Mama bata bi ta kansu ba sai ta kalli Hafsah da ta jingina kanta jikin kujera. Yaushe kika dawo."?

Ahankali tace yanzu.

Wanne zoben kika yar suke fada akai."?

Mufida tayi zaraf ta nuna mata "Kinganshi wai ya Ukhashatu ne ya bata wani.."


Mama ta kalleta da kyau sai Hafsah taji yar kunya.

Ta zaro zoben a hankali ta dakko box din ta mik'a wa mama. Maman ta amsa tana murmushi wani irin farin ciki takeji. Angode tace sannan ta mik'a mata.

Hafsah ta amsa cike da kunya, bata mayar dashi hannunta ba saboda mama dake wajen.


Mama na shirin zama Bashir ya shigo da fara'a ya nufi mama. A takaice yake mata bayani yadda zai zata fuskanci shi.

Mama ya Ukhasha ne ya ban wannan.

Ya mik'a mata kudin yana  k'ara mata bayanin yadda akayi kudin suka zo hanunshi.

Mama tayi murmurshi masha Allah an gode."


Hafsah ta mik'e zumbur ta  bar musu palour Bashir ma ya tashi ya bita aka bar mama na zaman shari'ar zobe.


____________________________

Yaya Allah mutumin nan naki akwai kirki.

Inji Bashir.

Hmm tace mishi ta nemi waje cikin drawer tana adana zoben ta.


Allah yaso lokacin muna hutu za'ayi bikin ku da wallahi ko babu hutun sai nazo gida nayi two weeks.


Hafsah ta bishi da kallo kawai.

Kinga 5k ya bani and yace zai had'ani da friend dinshi wani HOD a school din mu.

Sai yanxu tayi magana Okey good.


Bashir ya gyara zama..

Yaya baki fad'a min yadda zanyi da yarinyar nan ta school dinmu ba fa.. Allah ni itace damuwata.

'Ka daina sakar mata fuska!!

Ta fad'a a takaice.

Kuma fa haka za'ayi. 

Sannan ya gangaro kan hirar abinda yafi damun shi.

Yaya me da me zamu tsara a bikin naki ne.. nafison ayi shagali sosai wanda ba'a taba yi ba.

Hafsah tayi murmurshin da babu shiri. Wannan wane irin zumudi ne Basheer keji da shi, bama shi kadai ba duka kannen nata haka. 


"Hmm.. kai sai kace abin ya zo daf." 

Yazo mana Yaya ni tun yanxu zan tsara saboda bana nan xa'ayi tsare tsaren kada yaran can suyi ma shirme.

To ka je kuyi tsare tsarenku da su Zainab ni ku daina sa ni a ciki."

Bashir ya sheke da dariya hmm au na manta fa "Yaya ashe ke amarya ce dole kiji kunya."

Hafsah ta kai mishi duka ya mike da sauri yana cewa bari naje kitchen Zainab nayi min baking cake in taya ta tunda kin koreni.. _Amaryar Ukhasha_

Tayi murmushi taji dadi sosai sunan nan daya kirata da shi.

Fitar shi ya bata damar baje tunanin dake ranta. Menene ma'anar zoben daya bata da kuma wannan takardar mai jaddada soyayyar shi."?

Hakan na nufin babu sauran fushinta a zuciyarshi ko kuma me."? 

Ya akayi ma ta kasa fahimtar dashi komai.

Ta tuhumi kanta tare da jin haushin kanta sosai har daga k'arshe ta bige da buda wayar ta ko zataci karo da sak'on k'arin bayani akai.

Babu wani text message daya shigo. Data buda data kuma bai online kwata-kwata sai dai wani abu daya dauki hankalinta..wato chanjawar profile dinshi zuwa photon shi da yayi matuk'ar kyau.


Ta bata mintuna tana k'are mishi kallo tare da kissima abubuwa da dama cikin zuciyarta ciki harda tsananin soyayya da jin kishin shi mai zafi ya tsarga a zuciyarta. _Allah ne kadai yasan iya adadin yan matan da yayi soyayya dasu kafin ya iso gareta._

________________

Da komawar Ukhashatu gida ya kara amsa kiran Abban shi. 

Ya gurfana gabanshi cikin ladabi, bayan ya gaida shi abba ya fara kwaro jawabi.


Kaga saura kwanaki uku su fara bikin Maryam so nake yi ana gama bikin a fara shirin naka kuma ma'ana ka fara shirin gyaran gida da sauransu. 

Nasan dai baka da matsalar masu yi maka aikin haka kayan aikin kasan masu inganci sai dai kada a saka shiririta aciki don Allah idan akayi kammala gyaran kaga anrage aiki sai a fara kuma shirin had'a lefen koh.

Ukhashatu ya gyada kai hakane Abba. 

Yawwa Malam zan tura maka kud'i sai a fara shirin.

Ukhashatu ya dago kai Aa Abba za'ayi hidimar biki fa, in sha Allah ina da abinda zai isa.

Take fuskar Abban ta chanja ya fara magana fad'a fad'a, nasan ba zasu ishe ka kayi komai ba nima kuma nasan kana dashi din kuma na baka to ka karba kawai.

To angode Abba  Allah ya kara girma Allah ya saka da alkairi."

Yawwa ko kaifa."?

Tashi kaje kayi shawara dai da yayan naka.

"Toh Abba a huta lafiya.

_________________________

Hafsah ta tsumayi kiranshi har zuwa washe gari amma shuru babu ko da text..


Da kanta tayi wa kanta fad'a _ai itace a k'asa kuma itace mai laifi_ don haka ita ya dace ta neme shi ko dan ta nuna mishi  jin dadin kyautar shi.


Kiran da ta mishi bai dauka ba sam..sai ta kara  shiga damuwa don haka a lokacin ta tura mishi da _"Thnks my luv"_

Cike da zak'uwar ganin reply dinshi amma har bayan awa d'aya shuru..


Sun raka Basheer inda zai hau mota cike da rashin jin dadi musamman ga Hafsah don zata rasa abokin hira. Sannan ga tunanin idan ya sake dawowa basu da wannan damar sosai kamar tayi kuka takeji. Haka ta yini sukuku babu kuzari ga damuwar Ukhasha _anya ba matakin kuntata mata ya dauka ba."_


Tana wannan tunanen tunanen taji k'arar shigowar sms a wayarta

_You deserve more my dear!_

Ta lumshe Idonta tana murmushin jin dadi don gaskiya ya sham shammace ta, sai kuma taji tana son suyi waya dashi amma sai ta share tunda shima bai kirata ba..


Hidima ta yiwa Ukhashatu yawa har takai yau kwana uku kenan bai kira Hafsah a waya ba. Shirye shirye yake na abubuwa da dama kamar su lefen sa, wanda yawanci yayarsu ce dake abuja zata had'o sai kuma shi da duk sanda zai wuce wani shagon sai da kayan mata baya rasa abin  shiga ya dakko mata.


Sai kuma hidimar fara aikin gidan da kuma harkokin da suka shiga shida yayanshi ga bikin Maryam wanda shima ya bada tashi gudunmawar shiyasa yake mamakin Abbanshi yadda ya bashi kudi a irin wannan lokacin. Baya samun zama sam sai dare kullum cikin zirga-zirga ga zuwa wajen aiki, lokaci d'aya yayi yar wata 'ra ma' sannan kuma yayi duhu.


Suna hirar Hafsah da hajiyarshi idan ya shigo wajen Hajiyar. Ya nuna mata ita kuma tayi fatan alkhairi sai dai shima tayi mishi magana kan idan  sunyi aure yayi k'okarin chanja mata wajen aiki, ya gyada kai to hajiya in sha Allah.

Yawwa kaga hakan zai fi ko."?

Hakane Hajiya in sha Allah za'ayi hakan.



Hafsah ta kissima abubuwa da yawa a ranta na yadda Ukhashatu yayi watsi da ita har kwana uku, zuciyarta har ta fara inkarin soyayyar da yake cewa yana mata sannan dad'in dad'awa ta gano wato ramuwa yake. _"Shi kalar tashi ramuwar kenan."_ Ta fad'a a zuciyarta cike da neman abinyi. Bata jin zata kirashi dai amma zata k'ara mishi kwanaki.


Har dare sannan wani abin mamaki ya faru...


_Sanda take zaune tana sak'e-sak'en ta wani yaro da yake musu yan aikace- aikace ya shigo ga mamakin ta yace mata aunty ana kiranki bata tambayi ko wanene ba ta kimtsa fuskarta ta fita._


Bata ga kowa ba a harabar gidan, ta d'an tsaya waige-waige sai ga yaron ya fito daga cikin gida da plask d'in abincin shi a hannu.

"Jamil Ina yake ne."?

Ta tambaye shi.

Yana waje aunty bai shigo ciki ba ai."

Ta d'anyi jimm kafin ta fara tafiya.

_Wato bashi da niyyar shigowa ciki ma kenan."_

Mota ce mai matuk'ar kyau a 'fa ke'  a kofar gidan..akwai haske ta ciki  n kwayayen da sukayi wa bangon  gidan ado a tsakanin fulawowi da kuma bangon sun haska wajen yayi kyau yadda zaka iya ganin mutum sosai.



Motar mai bak'in glass ce Hafsah bata iya gano na ciki ba sai dai ta tsargu da bata lokacin da yayi bai sauke glass din motar ba.


Shiko dama ya samu ya k'are mata kallon kewa cike da wani irin shauk'i tare da tuno abubuwan baya masu yawa ji yake yi kamar ya maida hannun agogo baya.


Tunawa da yayi zata iya juyawa ta barshi, yasa shi cikin sauri ya dan zuge glass din motar sannan ya bude da sauri ya fito.


Lokacin Hafsah ta fara waige-waige tana son gane ko dai ba shi ya aika kiranta ba.


Sanye cikin  K'ananan kaya ya k'ara k'iba kadan da haske gami da k'aruwar goge wa.


Juyowar Hafsah kenan idonta ya gane mata shi ta d'an so tsorata kad'an.


Yana ida fitowa daga motar ya nufe ta kai tsaye ya tsaya daf da ita ita kuma ta d'an matsa.


Ya d'an kalleta na seconni cikin muryarshi mai bayyana matuk'ar rauni daga k'asan zuciya yace.

Assalamu alaikum."

Bakinta ya kulle gam ta ma kasa motsa shi bare ta amsa sai ma kallon gefe da tayi taga idan da hanyar wucewa.


Ya d'an fahimci manufar ta don haka ya buda baki ya fara magana da muryarshi wacce ba zata tab'a mantawa ba _har yanzu Hausar shi a juye take."_


Hafsah please help me and forgive me Don Allah wallahi na rantse I regretted all what  I did to you..shedan ne yasani..plz"

Cikin sauri ta motsa da niyyar barin wajen ya maraice yace.

Don Allah karki tafi ki tsaya badon ni ba."


Ta kuwa tsaya d'in aranta  babu dad'i tanajin zafin shi amma kuma tana mamakin yadda abin ke faruwa kamar a mafarki duk wani wanda ya gujeta ma yanzu suke dawowa me yasa."? Sam bata so ya riske kamar da ba ( _babu aure_) gani take kamar zaiga zaman jiranshi ne yasa.


Amma sai kuma tayi saurin ture wannan tunanin bisa wata ankararwa da wani bangare na zuciyar ta yayi mata.

_Hafsah kada kiyiwa Allah butulci hak'ika rayuwarki gaba-taci ba baya ba. Kuma yanzu you're engaged kin yiwa Yusuf nisa._


Ta daga kanta ta kalleshi ya kuwa k'ura mata ido kallon ta na tuno mishi abubuwa da dama.


Me ya kawo ka wajena."?

Ta fad'a da kaushin murya.

Bani da hanyar contacting dinki ina miki magana kina share ni kiyi hakuri, na zo ne na baki hak'uri... ya d'anyi shuru kafin yace _and to tell you that my father had died._


Tayi jimm sai yanxu taji d'an tausayin shi saboda a yadda tasan Yusuf da yadda yakeson iyayenshi kuma suma suke son shi.


"Ahankali tace Allah ya jik'anshi."

Yayi wani bushashshen murmurshi ta kuma lura da kwallar data taru a idanunshi.

"Amiin ya amsa sannan ya dora cikin sanyin muryar.


Please Hafsah ki yarda muyi aure mana wallahi na daina duk.."


Ta daga mishi hannu cike da b'acin rai.

Nooo never.!! Kada ka kara mini wannan zancen and kada ka kara zuwa wajena.."


Tana shirin juyawa gida taji cikin daga sauti yace...

Don Allah ki taimakeni Nasan kina sona fah Basma ne ta rabamu kuma nayi regret abinda ya faru..please Hafsah I lost my dad kada na rasa ki kema.."

Ga mamakin ta sai taga yana share hawaye ta tsaya jimm cikin takaicin abubuwan wacce kaddara ce ma tasa ya dawo gareta..ita ta manta dashi ta manta duk wata rayuwar da sukayi a baya imma dad'in ta da wahalar ta duk ta manta. To kuma me zaisa ya dawo mata da wannan zancen gani takeyi ma k'arya yake lokacin yayi tsaho ace da ragowar son ta a zuciyar shi..


Ko ita da tayi sha fama _Zazzafan son_ shi ta warke kuma ta manta bare kuma shi da take da yak'inin wasu abubuwa ne game da ita ke tafiya dashi bawai zallar sonta bane.


Tana tsaye har wata motar ta zo ta dallare ta har sai da ta kare idanunta da hannu motar ta zo gefenta tayi parking sannan aka zuge Glass din ta hango na ciki.


Gabanta ya yanke ya fad'i taji kamar ta sume don fargaba..meyasa abubuwa suke zuwar mata a haka ne."?


Babu shiri ta nemi hanyar barin wajen yayin da Yusuf ya biyo ta yana kira "please Hafsah.!!

Rasa inda zata dosa tayi wurinshi ko kuma gida sai ta tuno da akwai wata kwabar kuma sannan ta kuma kwaba wata jikin ta babu k'wari ta nufo motar babu wata wata ta buda zata shiga koma meye ayi ta ta k'are.


_Yau kawai tunda ya yini yakejin shi babu k'wari sakamakon rashin samun damar yin waya da ita da yake yaji a ranshi bai kyauta mata ba hakan yasa yau ya taho afujajen duk da yana ganin kamar dare yayi amma yayi niyya yazo minti goma ne yayi shidai yasa ta a idanunshi..amma kuma yayi bak'in gamo._


Duk da wani bangare na zuciyar shi na cewa ya mata uzuri ko abokin aikin ta ne amma kuma kishi da kuma abinda ya tayi mishi game da aikin nata ya hana wannan tunanin nashi tasiri. Wato dama saboda irin haka ne ba zata bar aikin ba kenan.!!

Ta kasa mishi ko da sallama sai zama da tayi sukayi jugum shi da ita kana kallon fuskar shi zaka karanci matuk'ar damuwa da bak'in ciki.


Yusuf yaga inda ta shiga kuma yaji shakkar binta don haka ya tsaya cak ya bata lokaci yana kallo motar tashi yayin da shi kuma Ukhashatu yake k'are mishi kallo shima.

Sai cam kuma Yusuf din ya matsa ya koma jikin motar shi yadda Ukhashatu baya iya hangoshi.

Matsawarshi tayi daidai da budewar bakin Ukhasha..



Ya kallo ta gami da zuba mata idanunshi da suka tsorata ta taga zallar kishi da fushi a cikinsu. 


"Na sani nayi laifi tun farko nine na miki katsalondon ban tsaya na nemi yardarki ba kafin na zurfafa akan son aurenki amma ki sani ba laifi na bane kawai Allah ne yayi lokacin yazo."


Ya tsaya ya had'iye wani abu  mai matuk'ar tauri. Sannan ya bayyana mata zallar abinda ke ranshi domin yanayin fuskar shi ya bayyana mata hakan.

Sai da ya kira sunanta ta bashi dukkan hankalinta kafin ya fara maganar kamar an tilasta mishi murya a dusashe.


_"Don Allah idan kina damuwa akan tarayyar mu ki fada min, in sha Allah zaki same ni mai hakuri.. Zan dauki kaddara  don nasan indai Allah baiyi zamuyi aure ba ba zamuyi ba.. Don Allah kada ki damu idan kinji banyi miki ba a matsayin mijin da kikeso ki sanar dani koda a text ne wallahi zan janye.!!_


Yana kaiwa nan ya gimtse baki yana kauda kai don da kyar ya k'arasa zancen.


_Shurun shi daidai da rushewar kukanta lamarin daya daga mishi hankali gefe guda ya kuma b'ata mishi rai._

_Shi a ganinshi wannan ba wani abin tashin hankali bane ashekarunta ma ta wuce irin haka tana da zab'i dama abu ne na Eh ko Aa."_


 Zuciyarshi ta hana shi koda kallonta ne saboda Ukhashatu yana da zuciya wani lokacin sai kawai ya kawar dakai yana jijjiga k'afa."


Amma ta wani fannin kukanta yana tasiri sai dai bai san yadda zaiyi mata bane kawai.



Tayi mamakinshi don haka  ta rarrashi kanta cikin hawayen tace.

Kayi hakuri nima ba'a son raina komai ke faruwa ba."?


Ya juyo ya kalleta da fargaba da kuma neman karin bayani.

Hafsah tasa mayafi zata share hawaye yayi saurin mik'a mata Handkerchief d'inshi ta kuwa amsa.

Ta share hawayen sannan ta   fuskance shi sosai. Ta yanke shawarar fada mishi komai don ta kauda shakku daga zuciyarshi.


_"Bansan za'a mana engagement ba ranar da akayi ma bana nan har lokacin daka kirani kake min zancen nabar qawayena da aiki nah..wallahi ba rashin daraja ka ne ko nuna baka isa ba yasa na fada maka abinda na fada maka ba..kawai dai naga kana fassara ni ne kan ba yadda nake ba kuma kana nuna kamar ina maka_

_boye boye amma kayi hakuri."_


Tare suka sauke ajiyar zuciya.


Ukhashatu yaji dadin batun da tayi shi a takaice amma ya wanke mishi zuciya jira yake kawai yaji matsayin shi a wajenta.

Cike da murmushi yace,

"Na yarda dake.!!

Tayi d'an takaitaccen murmurshi kafin tace..

"Kai zabina nane kuma zabin Abba nah.."

Farinciki mara misaltuwa ya bayyana a fuskar Ukhashatu yayi mata kyautar tsadadden murmurshi.

Nagode mai sunan Hajiyata."

Sai lokacin bakin shi ya bude ya samu damar tambaya. Cikin hadewar rai kamar bashi yayi mata murmurshi yanxu ba.

Waye wancen toh."?

Ta dan zaro ido kafin ta saduda tace "He's my ex!!

Don  bata iya k'arya ba.

"Exxx"??

Ya tambaya yana jan kalmar.

Hafsah ta danyi murmurshi.. ina mamakin yadda kake had'uwa da mutanen da suka dade da barin rayuwa.

Ta tausasa murya believe me wallahi duk randa kuke had'uwa nima ranar nake qara ganinsu bayan tsahon lokaci.!!

Ya jinjina kai kafin yace "Zaki bani labari but ina zuwa.!!


Ta kalleshi da mamakin abinda yake shirin yi sanda ya fita.

Shiko gun Yusuf ya fita kai tsaye ya mishi sallama  Don bazai iya bashi hannu ba saboda kishi.

_Yusuf wanda nutsuwa ta fara zuwar mai sai abinda ba'a rasa ba wanda ya zamar jiki_

Ya amsa asanyaye.

Babu bata lokaci yace.

Kaine kaxo wajen Hafsah koh."? 

Yusuf ya jinjina kai da sauri yana k'ara kallon Ukhasha yana tunani ai kamar dai Hafsah bata da yaya namiji.


_"She was like she's the first born kamar dai haka ya santa ya manta dai."_


*"Kayi hakuri an mata miji kada ka sake zuwa neman ta!!*

Inji Ukhashatu cikin  maganar shi mai kama da gargadi wanda ta girgiza Yusuf ya kasa katabus.



Ukhashatu na k'are zancen yabar mishi gurin.


Yana dawowa Hafsah ta zuba mishi ido.

Cikin mamaki ta tambaye shi "me kace mishi."?

Ya dan harare ta "ina ruwanki mai kuka."?


Ta kawar da kai cike da kunya..

Yayi kasa da murya.. me yasa a lokacin baki tambaye ni ba kin ce.

"Malam shin an baka ni ne da kake kafa min dokoki."?

Gaba-d'aya suka sa dariya.

Ukhashatu ya kalli hannunta dake bisa cinyarta babu zobe ko daya ajikin yatsun zai jan kunshi a iya yatsun daya saka sukayi kyau.. baisan sanda yakai hannu ba yayi kamar zai tab'a sai ya fasa ita kuma tayi saurin dauke hannanyen. Ya hada hannaye alamun  Afwan ta dan hade rai.

Sannan yace "Ya baki saka zoben a hannunki ba ko baiyi miki ba."

"Ai baka ce nawa bane ta fad'a da zolaya."

Ya nunata da hannu. "Kinganki koh."?

To ki saka... ya rage murya ko sai na sa miki."?

Tayi saurin girgiza kai a kunyace shima yayi dariya sannan ya duba ya juya can sit din baya ya dakko wata leda ya mik'a mata yana fad'in "Ungo amarya.!!


Lokacin ita kam ta nutsa cikin tunani kan abunda suka faru yanxu.. wato attempting (yunkurin ) taba hannunta da yayi sai kuma cewar zai sa mata zobe da yayi.. abin ya tuno mata da  da sanda Yusuf yasa mata zoben shi.. 

Ta tambayi kanta..

_"Me yasa abin yaso maimaita kansa"?_

Bata zargin Ukhashatu da komai tana mishi kyakyawan zato sai ta ta'allaqa hakan kan yadda suka kebe a guri mai irin mota su biyu. Dama addini ya hane mu da haka. 

Astagfirullah!!

Ta motsa baki ta fada.

Acikin karamin sauti yace tunanin me kike neh uhum"?

Tayi saurin juyowa tasa hannu biyu ta amshi ledar da abinda ke ciki daya fi kama da ice-cream.


Bai magana ba ya bude motar.

Ya fita sannan ya zagayo ya bude mata itama ta fito suka fuskanci juna..

Bari na tafi kada dare yayi min amma in sha Allah gobe zanzo ki bani labarin kinji."?

Ta gyada kai sannan yasa hannu a aljihun shi ya ciro katina ya bata "Gashi wannan    na bikin Qanwata maryam tace na kawo miki in sha Allah gobe zan taho dana Abba."

Shima tasa hannu ta amsa.

Ki shiga gida sai in tafi yace mata.

Ta mishi murmurshi sannan ta juya cike da farinciki ta wuce.

Yayi murmurshi shima komai kan idon Yusuf. 

Har kwalla yaji ta zubo mishi.


Har Ukhashatu yabar wajen Yusuf tsaye.

Sai da ya gaji da kanshi yabar wajen.



Bacci mai cike da farinciki Hafsah tayi bayan ta koma cikin gida sun baje ice-cream d'in sannan ta mik'a wa mama katinan.. Amira ce tace "amma dai yaya ba zaki je ba koh"?

Bata ce komai ba saboda mama dake wajen..

___________________________


Yusuf ya koma gida jiki a sanyaye ya rasa me yake mishi dad'i yanxu shikenan ya rasa Hafsah."?


In ko hakane zai jinginar da zancen aure duk da yana buk'atar auren a yanzu.

Wato abinda ya nutsar dashi  kan batun aure shine:

Tun lokacin da mahaifinshi ya rasu wata daya baya sanda aka k'are zaman makoki wasu daga cikin dangi suka hadu suke ta mishi nasiha da misalai iri.

Sun nuna mishi yadda mahaifinshi ya rasu ba tare da yaga jikanshi ba. Sun nuna mishi yadda rasuwar taxo bag-tatan wanda shima Yusuf ba karamin kaduwa yayi da batun rasuwar ba gani yake kamar a mafarki.. wai daddyn shi ya rasu.

Sun mishi misali da shi kadai ne wajen iyayenshi haka babanshi shi kadai kakarshi ta haifa."?

Duk da ada hakan baya damunshi amma yanzu ya damun ko dan mahaifiyar shi zata so taga ya'yanshi ita.


Sannan sun nuna mishi girma ya fara kamashi don akallah zaiyi shekaru talatin da abubuwa.


Tunda akayi rasuwar ya rage hulda da yan matan shi kuma indai ba gaisuwa zaki mishi a waya ba baya bari kuyi hira. 

A lokacin rasuwar mahaifiyar shi taga tarin yan mata kala-kala wanda ta rasa daga ina suke.

Wai don ma kadan daga ciki kenan masu raguwar tarbiyya da tausayawa da suka zo mishi gaisuwar.

Sai lokacin kuma hankalin ta ya tashi tasan d'anta ya wuce tunaninta a kallah kullum ta kanga bak'in yan mata biyu zuwa uku har akayi bakwai kuma suna zuwa cewa suke "ina Yusuf."?



Yusuf bai k'ara saduda ba sai da yaga sun dawo kwana shida mum d'inshi kadai a gidan sai yan aiki gashi mum din kullum cikin kuka yake.


Babu wacce ke yawo a kwanyar shi kullum kamar Hafsah.. amma yana tsoron tunkarar ta. Ita  kadaice yaji zai iya aura ba tare daya sa shakku akanta ba a ranshi.



To yau ga abinda ya tarar. Duk da bai sa ran zai ganta ba amma ganin nata ya haifar mishi da damuwa mara misaltuwa.


Ya raba dare babu bacci yana saka yadda zaiyi ya samu Hafsah amma ya rasa mafita. Gashi zuciyar shi ta kasa hak'ura. Ya zauna sosai ya dinga tariyo rayuwar da sukayi a baya cike da shauk'i da yanda komai ya dinga faruwa kamar Film, zuciyar shi na kara ingiza shi.. _shiya san yarintar ta don haka shiya dace ya aure ta!!_



Da kyar ya rik'i wani abu da yake tunanin shine mafita.


________________________

Yau tunda Hafsah ta tashi take jinta cike da nishadi ji take babu sauran damuwa.


Yau abin mamaki sai taga abban ta har dakin ta bayan ya mata knocking tana jinshine taji wata fargaba lafiya Abba har d'akinta yau.

Shiko cewa yake Yaya bude kinji muyi wata Shawara."


Ak'asa ta zauna ta dukar da kai da fargabar wane muhimmin abu ne yasa abban takowa da kafarsa."?


Abban ya zauna gefen gado.. ya fara da nasiha da rarrashi kafin ya fada wa Hafsah abinda ta k'agu taji.


Aure ba abin wasa bane Hafsah babu lallai mijinki ya yarda ki cigaba da aikin gidan TV saboda haka kiyi hakuri ki ajye in sha Allah Allah zai baki wani.. nima bana goyon bayan ki zauna babu wata sana'a ko wani aiki."

Ta dago a hankali ta kalleshi wato zancen Ukhashatu dai..badon tayi imani bazai iya yiwa Abba wannan zancen ba da sai tace shine ya roki Abba, amma tasan basu hadu ba kuma bazai wa Abba zance a waya ba.


In sha Allah Abba zan ajiye zan rubuta resigning zuwa qarshen satin nan.

Ya fad'ad'a murmurshi Allah yai miki albarka in sha Allah da kaina zan sama miki wani.

Tayi murmurshi nagode Abba. Duk da gefe tanajin babu dad'i saboda sabo da mutane..



Bayan fitowar Abba daga dakin nata cikin mamaki yaji labarin wai yayi bako a waje.


Da fitar Abba yayi mamakin ganin saurayi Abba ya mik'a mishi hannu suka gaisa.

Babu jira Yusuf ya fara bayani.


Abban nazo wajen Hafsah ne shine take cemin wai anyi mata engaged kuma wallahi yanzu da gaske nake aurenta zanyi ina sonta Abba."


Abba ya tsaya sororo yana kallonshi wane irin yaro ne wannan magana babu ladabi babu iyawa haka ake neman auren."? Shida yasan Hafsah bata kula kowa to shi daga ina yake kenan."?


Waye kai."?

Abban ya tambaya.

Nine Yusuf Abbah, I dated Hafsah years back har kace na turo..lokacin ban shirya bane..

Abba ya gane shi wato yaron daya hargitsa masa rayuwar gidanshi ne yaso ya hure wa yarshi kunne. Abin  ya bawa Abban dariya har sai da ya dara sosai lallai yaron bashi da ta-ido wato har jawabi yake. Gefe guda kuma Abba ya gode wa Allah daya ga wannan yaro ido da ido.

Take ya tuno komai da sanda yasha gwagwarmaya da Hafsah.

Abba ya dan hade rai saboda ya takaita koma meye yace..

Wato sai yanzu  ka shirya koh."? To anyi mata miji kaji.. kuma ka dakata da zuwa wajen ta."

Nan Yusuf ya Shiga magiya Abba ya daga mishi hannu kaje gida Allah ya baka wata kaima. Daga nan Abba ya juya ciki.

Aka bar Yusuf kamar ya fasa ihu.



Abba ya shiga gidan yana dariya, yasa a ranshi ba ma zai fadawa Hafsah ba sai dai kuma zai bawa Amina labari.


Sun kuwa sha dariya sosai shida ita.

_Kinga abu kamar mafarki ko amina."?_

Ta gyada kai.

Yace alhakin kine dana yarki ke ya dinga sawa shakku da kokarin sa miki hawan jini ita kuma tana matuk'ar sanshi shiko yana k'okarin bata ta.

Mama ta d'ora "sannan ya yaudare ta ba ai dama na roki Allah sakayya."!!

Ya kalleta suka sa dariya.



Ukhasha yazo kamar yadda yayi alqawari sun sha soyayyar mu shida Hafsan shi a hankali cikin hikima da wayo yadda bazai zargi wani abu a ranshi ba ta bashi labarin rayuwarta ta baya wacce ta kunshi Yusuf da Basma da Jamila. Daga karshe ta nuna masa yadda Basma tayi mata snatching. 

"Kaga ina na d'auke ta aminiya ashe saurayina take so."

Hafsah ta fada mishi hakane don bazata iya fad'a mishi zahirin abinda ya faru ba da yadda Yusuf yake ko don gudun zargi..


To ya akayi kika gane ta kwace miki shi."?

Tayi wani murmurshi kafin tace naje gidansu ne naga yazo zance wajenta."

"Hmm..yace..

Ku fa mata haka kuke waya ce miki zance yaje."?

Ta kalleshi kallo mai kama da harara.

Yayi murmurshi "To ai gashi Allah ya baki ni koh."?

Tayi murmurshi.

Hakane."?

Ta gyada kai.

Ukhashatu yayi k'okari ya nusar da ita yadda rayuwa take. Sannan ya nuna mata ta dauki komai yadda yaxo kada tunanin baya yasa tace zata kusanta kanta da Jamila domin yanzu ba da bace.. _"wasu mutanen zama dazu sai shafa maka bak'in fenti ne kawai.."_ 

Idan tazo wajenki kada kiki saurarar ta amma kisan irin mu'amalar da xakuyi. Dama irin haka a rayuwa dole a dinga samun shi. Muma suna nan  wadanda munyi yarinta tare dasu amma yanzu mu da su sai dai Hi hi tunda kowa akwai layin daya dauka. Kuma kowa da yadda Allah ya tsara mishi rayuwa..



Hafsah ta yarda da duk zantukan shi 100% kuma ta kuma tabbatarwa da kanta lallai Ukhashatu shine ya dace da ita kuma shi _Masoyin k'warai_ ne.


Daga nan suka shiga wata hirar yana tambayarta.. me zamu tsara ne na bikin mu uhum amarya.?

Cike da kunya ta kawar da zancen da cewa.

"Resigning.!!

Ya kalleta yana dariya.

"Ai mun gama maganar ranki ya dade."

Wannan umarnin Abba ne."

Ta fada."?

Cike da zumudi yace Allah."?

Ta jinjina kai.

Kaii Allah ya k'ara nisan kwana gaskiya na gode zanyi wa Abba godiya.

Anjima ma za'a turo kanina  ya kawo mishi Invitation Abba yace bazai bani ba wai  gwara ya aiko takanas tunda ni na zama dan gida."?

Hafsah ta kalleshi "ka fiya zolaya Allah."

To ba haka bane."? 

Hakane.

Tace mishi.

______________________


Yau Hafsah ta k'ara karbar ba k'uncin jamila sai dai cikin wani yanayi na daban wanda Jamila tazo dashi abin tausayi domin da kuka ma ta shigo.



Sai da Hafsah tayi da gaske sannan Jamila tayi shuru ta fara sanar da ita abinda ke faruwa.


"Hafsah na dawo gida yau..Uwar dakina ta rasu yan uwanta sun kwashe komai nata gidan da muke ciki ma sun koro ni dole na dawo gida."

Hafsah ta zaro ido da mamaki "Innalillahi tun yaushe ba kince tafiya xakuyi ba."?

Da ita ne dama kuma ba muyi tafiyar ba ma ta rasu.

Tausayi ya mamaye Hafsah ganin yadda Jamila ke kuka.




D'akin yayi shuru sai da Jamila ta sha kukanta sannan ta bude baki tace fara bawa Hafsah labarin yadda rayuwarta takasance bayan barinta gida.



Hafsah ta bata dukkan hankalinta Jamila kuma ta bude baki ta fara.



"Hafsah nasan kema kina min kallon wacce take zaman kanta koh."?

Duk da hakan ne bani da maraba  tunda ba gaban iyaye na nake ba... labarin nada tsaho amma tunda ya riga ya wuce babu amfanin tunawa sai dai zan fada miki wasu abubuwan a takaice ne..


_Bayan barina gida. Nasha gwagwarmaya ta rayuwa ga ciki ajiki na (don nasan kinji labarin komai.)_

Nayi rashin mahalli da tudun dafawa har takai ina na rasa inda zan nufa.


_Tunani na ya gushe na manta da k'awa ta ta makaranta._


_Da kyar na samu abinci a yammacin a wani wajen cin abinci. Wanda na zama tamkar mabaraciya a wajen._


Sai da na ci abinci sannan tunani na ya dawo. A lokacin  na tuno da k'awar tawa "Samha" 



_Da kyar na ari waya na kirata a rikice. Tayi min kwatancen gidansu. Bani da kudin mota haka na fara takawa a k'afa. Wanda daga karshe dai da kyar na  hau abin hawa wanda sai bayan dana sauka ne nake ce mishi ya min taimako bani da ko sisi. Don ba'a barni na  fito da ko biyar ba daga gida. Mutumin nan har Allah ya isa yayi min don yace kamata babu yadda zaayi akalleni ace bani da kudi. (Sanda na sami dama na mishi sadakar kudin shi.)_



Ta girgiza kai sannan ta d'ora.


Na tarar da Samha cikin wani irin yanayi a gidan su. Da alama ba mahaifiyarta ce a gidan ba. Kuma na tabbatar da hakan bayan nayi kwanaki a gidan saboda yadda naga suna fada da matar gidan kamar sa'ar ta. Kusan kowa na gidan basa shiri dasu kuma ta raina su.


Ranar dana isa gidan ma suna ce-ce-ku-ce da matar gidan. 


Na bata labarin duk abinda ya faru dani a gidanmu da yadda 'sir Garba' ya yaudareni.

Amma sai naga ita hakan bai zama damuwa a wajenta ba.


Ta nuna min babu komai har da bani shawarar "na zubar mana ai ba kaina farau ba.


Ban yarda da hakan ba amma bansan me ya faru ba na wayi gari cikin ciwo kuma bayan munje asibiti aka tabbatar da zubewar ciki na. Nayi jinya sosai ta watanni duk a gidan su Samha. Ni kaina ina mamakin gidansu babu ruwan kowa da rayuwarmu ni da ita shiyasa nake zamana cikin kwanciyar hankali a wajenta.


Na zargi Samha kan zubewar ciki na amma sai nabar abin cikin iya zuciyata saboda itace ci na itace sha na.



Na zauna gidan su tsahon watanni da suka kusa rufa shekara.


Samha kullum sai tace in shirya nasa 'spare' uniform dinta muje makaranta amma sam naki saboda na tsani makarantar ma gaba-d'aya. Sai dai na bata sak'o a   wajen Sir kan cin asabar daya min duk da  baya makarantar yanxu  amma ta isar d'in.



Nabar gidan su Samha bisa dalilai da dama na yau da gobe da kuma halayen Samha wanda na kasa ganewa.

Na fahimci Samha tafini wayewa da budewar idanuwa kafin daga bisani na fahimci ta shallake tunanina tunda har takan iya maida mata maza a wajenta.


Bansan tana da wannan dabi'ar ba sanda muna makaranta sai dai babu tabbaci kan ko batayi ne a lokacin amma sanda gwada min haka take lokacin naji bazan iya cigaba da zama da ita ba.


Rayuwar danayi a unguwar su yasa na saba da wasu makobtansu ciki har da wata mata maiwa yan aiki hanya.


Na je har gidanta na roketa kan ta samamin aiki na gaji da zaman gida.

Bayan dogon kallo daga matar sannan ta min shagub'e kan me zai kaini aikatau bayan ina k'awar Samha."? Duk wayewar mu. Domin babu wanda a unguwar baisan ni ba kawar Samha bace.

Wani abin mamaki shine yadda babu kunya matar ta ke tambaya ta. "Kodai abin ya daina karbar ki ne."? Inada wani malami da zai dawo miki da tauraruwar ki."!!


Banyi fushi ba kuma ban nuna mata ba haka nake ba tunda bani da mafita. Sai dai na nuna mata matuk'ar buk'atar aikin wanda daga k'arshe ta yarda zata kaini sai dai ta yanka min wasu kudade da zan biya ta idan na fara aikin. Ta nuna min tasan inda zata kaini. Bangane nufin ta ba sai dai naji tace..

Na fahimci k'afa kike nema so zan kaiki inda zaki k'ara goge wa dama haka irin ku kuke lumbe-lumbu kuke kuyi kwanton bauna ku goge sannan ku gagari masu gida.."!!


Sai ta sheke da dariya.


Na rok'eta hadi da bata cin  hanci kan kada ta fad'awa Samha ina neman aiki. Ta nemi dalili ta rasa. Wanda da kyar na samu ta yarda duk da tana ta mamakin dalilin boyewa ta.


Mun saci jiki sau da dama munje gidanmu nida Samha na kwaso kayana sanda mahaifina bayanan. Mahaifiya ta nuna tsayawar ta duk da sanda baba zai koreni bata nuna wani abu ba domin tasan halin sa zai iya hadamu ya kora.



Nasha gwada in koma gidan mu amma babu damar hakan har mahaifiyata ta gwada min in saduda.



Daga karshe dai matar nan ta samar min aikin kuma nayi mamakin gidan da ta kaini. Gida ne na mata masu zaman kansu.


Takamaimai bansan wa zan dinga yiwa aiki agidan ba sai dai an fada min aikina.

Share-share da wanke-wanke da aike shine aiki na.



Sanda suka ganni sunyi complain kan nayi musu girma harda masu cewa ni uwar mata ce ko suce sumumu-kasau... da kyar suka yarda na fara aiki wanda dole nazama tamkar wata doluwa.


Nasha wuya sosai agidan nan mara dadin tunawa.

 Domin mata ne su wajen goma sha amma babu yadda za'ayi wata ta sani aiki wata bata sani ba idan nabar na daya nasha zagi har da duka. Maza ke tururuwa a gidan ba dare ba rana haka kawai ake kyara ta wai mazansu na kallo na ni munafuka ceh..

Sun sha cewa zasu koreni amma ina basu hakuri har da kuka..


Azaman da nake a gidan ne tunanina ya fara sauyawa kan irin rayuwar da suke anya nima bazan fada ba domin neman mafita ta."?

Amma wallahi dana tuno ki sai inji bazan iya ba.



Nayi akallah shekara agidan kafin wani mutumi da yake zuwa wajen wata ya yaudare ni.

 Mutumin ya dade yana nuna min wasu abubuwa har saida yasan yadda yayi ya fita dani a motar shi kan zan karbo wa uwar dakina sako a wajen shi.


Mutumin ya kasance mutum na biyu wanda bazan taba mantawa dasu ba a rayuwata. Zan sa shi layin wadanda suka taimaka wajen gurbacewar rayuwata.



Ya huren kunne da hilata kala kala wanda tun bana yarda da shi har na fara sakin jiki.



Naci duka sanda suka gane haka a lokacin ne suka nemi su koreni...

Aunty sadia kawarsu ce don tana yawan zuwa gidan. Allah ne ya kawo ta Aranar ta ceceni itace ta tafi dani gidan ta lokacin ina ga ina da shekaru 18 lokacin tasan yan ajinmu sunyi candy.



Na kasa gane irin rayuwar da take ko irin tasu ce. Nasan dai tana business sai sai yawan bak'i maza a gidan ya zarce misali.


Ta nemi taji tarihi na daga bakina da kuma gaskiyar abinda ya faru dani. Na fada mata komai a lokacin ta gargade ni kuma tayi min fada mai shiga zuciya.



_Ke yarinya ce kinyi kankanta kisa rayuwarki cikin wannan abubuwan kada in kara jin hakan ya faru.. tunda komai daya faru a rayuwar ki ki d'auka kaddara ne mu idan zaki ji namu tarihin zaki ji  naki ba komai bane._


Tayi min  jan ido wajen cewa duk ranar da taga wani abu shigen wanda nayi acan to zamana ya k'are.

Tayi min wani gargadi da cewa "Ki bar manya suyi ke yarinya ceh."

Na kasa fahimtar me take nufi sai dai na gimtse abun nabita yadda taxo min. Nidai nasan na wuce sahun yara kuma zuwa lokacin nasan abubuwa da dama..



Mun zauna nida ita tana kula dani har yau bazan manta da ita ba.

Jamila ta share hawaye.


Ta yi kokarin maida ni gida sanda tayi wani tunani a kaina amma baba ya koremu. Cewar shi naje na k'ara tambadewa sannan zan kara dawo mishi gida. Har Allah ya isa yayi hadi da tsinuwa idan har na k'ara zuwar mishi gida. Duk abin matan gidan sai da suka bashi hakuri amma yaki hak'ura. 


Mun rayu da ita babu tsangwama tayi min komai ban rasa komai ba amma kullum gargadinta dani akan na fita harkar maza ne.


Tana yawan fada min cewa "Maza mayaudara ne badon yaudarar su ba da bata zata tsinci kanta cikin wannan rayuwar ba."


Bata taba ban labarin ta ba har muka rabu amma nasan tasha wuya fiye da tawa.

Mamakina shine yadda yan uwanta ke zuwa gidan ciki harda mahaifiyar ta kuma suyi hira sannan su tafi da kayan arziki.


Na goge da rayuwa a zamana da ita tayi min komai sai dai bata taba min tayin maida ni makaranta ba kuma nima ban zarge ta ba.

Tayi min abinda iyayen a basu min ba ina sa mai kyau inci mai kyau sai dai na fahimci yan uwanta basa k'auna ta.


Na gane ne da irin kallo da kyarar da suke min.


Munyi shekaru a kallah uku kafin dole Aunty ta sallama ni nake tsayawa da samari. Sai lokacin na sake fahimtar yadda mutane suka bata rayuwar su. Yawanci basa zuwa da alak'ar gaskiya Sao dai kowa da manufar shi.


Sanda na lura aunty ta rage tara maza a gidan ta ma'ana sun rage zirga-zirga shine sanda wani mutumi ya nuna yana son zai aureta. Tayi murna sosai nima kuma naji dadi sai dai kash sai da komai yazo daf da daf komai ya ruguje..

Mutumin yasan komai game da ita sai don bazance zaman da take yi ne ita daya  bai sani ba. Sai dai lamarin ya tsayawa jama'a da dama aransu musamman k'awayen ta yadda suke ganin zata daga ta barsu.

Ban taba ganin matar nan cikin tashin hankali ba kamar lokacin nan tasha kuka wiwi a gabana. Ta dinga fadamin maganganu kamar ba cikin hayyaci ba kamar ta manta dawa take maganganun.


"Jamila nasan nayi rayuwar da bata dace ba amma na dade da dainawa na tuba yanzu ba da bace halak d'ina nake nema amma meyasa mutane zasuyi min haka."?

Maganganu ta dinga furtawa wasu ma sirrikan ta ne. Nima babu abinda nake sai kuka da bata hakuri.


Anduki lokaci mai dan tsaho kafin aunty ta dawo daidai.


Takan barni nayi mu'amala ta da samari na sam bata hana ni fita da samari. Har mu fita.

Sai dai a kullum zancen ta daya "Kiyi taka tsantsan."


Har kamar ranar da muka hadu dake. Amma nida kaina nake baya baya da mutanen saboda yadda suke nuna min wuce makad'i da rawa.


Aunty da kanta ta sama min hanyar samun kudi a cewarta dogara da abin wani ke jawowa komai ke faruwa.


Na koyi kwalliyar zamani wato makeover da ita nake yiwa kaina abubuwa da dama. Lokacin na k'ara tunowa da gidanmu. Dole na k'ara nemar gida domin bani da wanda inda ya fishi. Ina kaiwa mahaifiya ta alkhairan da wataran har shi mahaifina ake ciki domin komai ya k'are mishi. Kowa a gidan ta kanshi yake.


Da wannan abin nake samun damar zuwa gidanmu kai tsaye.


Sanda nazo wajenki lokacin aunty tayi min  alkawarin zuwa dani Dubai domin siye siyan kaya. Nima tace na k'ara gogewa da sanin rayuwa.


Shine tafiyar da na sanar miki zanyi rakiya. sai dai kash mun shirya komai amma Allah bai nufa ba aunty ta rasu bisa wani hats ari da tayi a motar ta bayan ta fita babu jimawa na samu labari kamar a mafarki.


Jamila ta rushe da wani irin kuka mara misaltuwa. Sai da tayi mai isarta kafin tayi shuru wanda har Hafsah itama sai da ta share hawaye.


Hafsah a lokacin na rasa mutane biyu uwar dakina da kawata Samha wacce akace wata iriyar cuta ce ta kashe ta. Duk da ina ganin kamar nayiwa Samha butulci amma ita ta Nemo ni har take nuna min ko in kula kan gudar ta da nayi sai dai tace min. "Ai Jamila ko ina kika shiga sai na gano ki." Wato kin gama gadin gidan magajiyar shine kika dawo nan."?

Karaf a kunnen aunty ranar kuwa ta mata tatas ni kaina tun lokacin nake shakkar aunty domin ban dade gidanta ba hakan ta faru..


Hafsah rayuwata ta shiga garari yanxu haka babana yana kwance rai a hannun Allah dawowa ta gida ta kara kwantar dashi duk da yayi ikrarin cewa ya yafemin domin korata bai mishi amfani ba. Nima don da karar tsanata da aka dasa mishi a zuciyarsa ne. Domin bayan ni yayyena  wanda muke uba daya har shegu biyu suka ajiye mishi acikin gidanshi kuma babu yadda ya iya dasu dole duka suna gidan.


Hafsah nayi mamaki dana ganki ba kiyi aure ba kema kuma banyi murna da hakan ba ina Yusuf din."?


Da sauri Hafsah ta mata nuni kan tayi shuru don bata son ko jin sunan Yusuf.


Jamila ta girgiza kai ta d'ora.

Hafsah wallahi aure nake so shine kawai burina.. saboda sam ban amfani rayuwata ba na rasa yadda akayi rayuwata ta zama haka bane cika koda daya da yaga cikin burikana ba..


Hafsah nayi asara dayawa a rayuwa ta..aure kawai nake son yi shine zan san na ribaci kuruciya ta sai dai ina tunanin ko  za'a barni nayi Auren."? Duk da bani da wani tsayayye da zance yana sona da aure.


Hafsah ta numfasa. Ki yi hakuri ki daina kallon ayuwarki a baya kowa da irin yadda aka tsara mishi rayuwa Allah yana sane dake ki gode masa domin kinfi wasu."


Jamila cikin hawaye tace Allah Hafsah banyi irin k'azamar rayuwar da mutane ke zargi na ba imma hakan ne a farkon bari na gida ne amma kada ki so kiga yadda mutane suke kallo na."!

Hafsah tayi shuru Allah yaso bata zargi Jamila ba ita dai tasan bata gidansu kuma koda ta bawa Ukhasha labarin ta  ce mishi tayi "tabar garin ne zuwa wajen dangin mahaifiyarta.

Bata soma fada mishi cewa Jamila garari ta dinga yi ba ko dan k'are nata mutuncin.. Domin maza akwai zargi.



Sunyi jugum Hafsah na bawa Jamila baki kan ta tsananta da addu'a. Bayan nan Jamila  ta dame ta da zancen Yusuf ta damu ta bata labarin rabuwar su.


Da kyar Hafsah ta mata a takaice kawai ta nuna mata Abbanta ne ya rabasu saboda karatu kinsan dama lokacin bana kula kowa.


Jamila ta girgiza kai Allah sarki kuma yayi aure koh."?

Hafsah ta girgiza kai bansani ba gaskiya bani da alaqa dashi yanxu.

Jamila ta fahimci Hafsah bata son zancen don haka tabar zancen sukayi shuru. Inda Hafsah taga dacewar ta je ta duba baban Jamila don ko ba komai uba uba ne don haka tace. In sha Allah gobe zanzo duba Baban.

Jamila ta nuna jin dadin ta.

Hafsah tasan sai tayi magiya Sannan mama zata barta don haka tace sai gobe.


Tana son sanarwa Jamila batun bikinta amma kuma tana jin nauyi don haka fa bari sai abu ya matso sosai..



Ita ta raka jamila har waje sannan ta dawo jiki a sanyaye  tana tararrabin yadda rayuwar Jamila ta kasance kuma tana k'ara gode wa Allah..


🔚🔚🔚🔚🔚🔚🔚🔚🔚


Kwanci tashi babu wuya a wajen Allah yau bikin Hafsah da Ukhasha ya rage saura wata daya da sati biyu.


Sun sha gaisawa da Hajiyarshi a waya haka 

Wata rana idan zai zo yakan zo mata da "Najwa" Tayi ta sa Hafsah dariya tayi ta bata labarin su ya  Fadwa da yadda suke tsokanar Ukhashatu.


Mama ta d'auke ta takanas ta maida ta gidan Hajiya Nafisa wato maman ya Nazeer.


Komai da ya dace maman tayi mata sosai Hafsah sai taji rayuwar da tayi agidan da gwagwarmayar da mama ta sha da ita ya dawo mata sabo kamar yanzu. Ita da kanta sai tayi ta dariya ita kadai tana qara gode wa Allah.



Takan yi wani tunani wato 'komai dai da lokacin shi.' Idan taga yadda ya'yan Nazeer su biyu suke cika gidan da hayaniya. Da tuni fa yaranta ne. Sai tayi saurin kwab'ar kanta "Kada ki zama mara godiyar Allah Hafsah kowa da wanda Allah ya rubuta  zai aura a rayuwa.

Amma tana tuno Ukhashatunta da yadda yake sai taji wani farinciki mara misaltuwa har ta _kirashi da daya tamkar da dubu!!_



Tanajin kunyar mama yadda take zaunar da ita tana koya mata abubuwa babu wata shakka.


Ya zame mata dabi'a kullum kafin su fara gyaran jiki sai tayi mata nasiha da nusar da ita yadda rayuwar aure take.


Takan fada mata ko yaushe.

_Rayuwar aure  wata iriyar rayuwa ce wacce ba zaki taba gane ya take ba har sai kinyi ta. Tana da matuk'ar dadi sannan akwai wahala da kalubale acikin ta amma idan har kika saka hak'uri komai zaki same shi da sauki._ Ita zaman ibada ne dole ki hadu da abubuwa masu dadi da kuma akasinsa. Amma matuk'ar kika sa aranki ibada kike to zaki sami komai da sauk'i.



_Kuskure da yanmata kuke yi shine kunfi fifita soyayya akan komai cikin rayuwar aure._

_Duk da tabbas itace ginshiki amma kuma hak'uri da biyayya sune makaman yaki da kowacce irin fitina._


Ina son ki rike abubuwan nan da zan fada miki.


Ki rike tsafta da kamshi 

Sai kuma ki zama mai ka mun kai da biyayya kada ki zama mai girman kai ga mijinki.



Hafsah ta koyi abubuwa cikin sati hud'un da tayi tun daga girke girke data k'ara gogewa dasu sai kuma dabarun zama da miji da zamantakewar rayuwa ita kanta. Adduoi kuwa kullum cikin yin su take babu dare babu rana.


Bata iya sanarwa da Ukhashatu cewa bata gida ba saboda nauyinshi da take ji sai dai idan ya nuna yana son ganinta ta bashi uzuri. Ya k'osa sosai har yake fad'a mata.


"Don Allah ayi hakuri amarya adaina jamin rai ina son ganinka Allah."


Babu abinda take mishi sai dariya wanda da ya gaji sai ya sami lokaci yaje gidan.

Mufida ce ta fada mishi tana Kabuga.

Ya dawo gida asanyaye.

Yana dawowar kuwa ya kirata.


Tana dagawa taji yanayin shi kamar ba shi ba.

"Kin kyauta nagode."

Take tasha jinin jikanta.

Cike da fargaba tace hubby me ya faru kuma."?

"Hmm baki sani ba."?

Um."

Tace dashi.

Okey ya wuce nagode kawai.!!

Tayi shuru tana tunani me tayi toh."?

Sai ta marairaice.

Please Dear meya faru ne."?

"Hmm nace miki babu komai fah."

Please ta sake cewa.

Wai da gaske kike baki ce san me kikayi ba."

Murya cike da rauni tace.

Allah bansani ba I'm sorry plz tell me."

Ya danja dogon numfashi sannan yace.

"Meyasa zaki je unguwa baki sanar min ba."?


Take annurin fuskar ta ya dawo tace cikin shagwaba.

"Dear mama ne fa ta aikani sati na daya ma tace sai biki saura sati biyu na dawo."?

"What.. ina kika je haka ya fada a tsorace."


Abin  ya bata dariya har tayi ta afili sannan tace "ina Kabuga gidan Yayar Mum dinmu.

"Hmm baki fad'a mini ba koh."?

I'm sorryy luv."

Ban hak'ura ba.

Tace plzzz"!!

Ya d'anyi shuru kafin yace.

To fad'amin me kikaje yi haka da har zaki dade kuma baki fad'a min ba."?

Hafsah ta bude baki sannan ta rufe kafin ta lalubi abincewa don bata son tayi b'aran b'arama.

Dear sallama naje mata fa.


"Hmm kuma har 1month koh."?

"Oh my God!! ta fada a zuciyarta. Yau na gamu da dan Jarida.

Dearrrh!!

Ta ja sunan kamar ta k'osa.

Shima yace uhum."?

Na zauna gidan fa da so mum bazata bari na yi kwanaki kadan ba.

"Okeyy shima yace.

Yaushe zan ganki toh plzzz kada ki hanani ganinki nayi missing dinki so bad dear plzzz"

Tayi mishi yar dariya.

"Really fah kike min dariya dama ke baki damu ba koh."?

ta shagwabe tace "Noo Dear.!!

"Umm bawani nan..in zo gobe ba don hali na ba."?

Tomorrow!!?

Yess"

Yace.

"Ka bari sai day after goben."

"Ok" yace mata sannan yayi dif.

Tasan fushi yayi don haka ta mishi dariya itama. 

"I'm joking Dear kaxo goben kaji nima inason ganinka.

Ukhashatu ya lumshe ido saboda jin dadi.

"Thank you WiFi.

"U wlcm Data.!!

Tace mishi.

Suka sheke da dariya "Hmm ke koh..??

"Me kike so in taho miki dashi.

Ta girgiza kai kamar yana ganinta. "Nothing Dear.

"Ban yarda ba."

Tayi murmushi "Okey You You and You.!!

Yayi murmurshin jin dad'i "Amarya me wayo.!!

"Come with you alone." Ta sake  fad'a.

Ya kara darawa "Nak'i din."

"Idan kukazo ba yanda nace ba zaku koma.!! tace.



Lokacin kuma tajiyo mama na kiranta sai lokacin ta tuna girki take duk da dama su aiki amma Mama sata take don ta saba sosai.


"Mum na kirana byee.

"Ok dear kije ki gaida mum."


__________________________


Biki saura sati biyu Basheer ya dira. Duk wasu shirye shirye sun tsara shi babu tsawwalawa saboda amaryar da angon basu san bid'a. Duk wani wanda ya dace yasan da bikin zuwa lokacin ya sani. Hafsah ta tura katinan gayyata ga contact d'inta.


Kowa na mata fatan alkhairi. Musamman Aysha Daheer dake da 'yaya biyu a lokacin. Su Nasreen sune organisers na komai.

Za'ayi kamu ne had'i da kauye Day sai Dinner sai kuma mother's eve. Ranar asabar k/ amarya.


Banda murnar Abbah data fi ta mama fitowa fili ita saboda kunya. Babu wanda za'ace yafi kowa farinciki da bikin kamar Basheer.

Har siyayya yayo wa Yayarshi da kudin shi shima a tashi bidi'ar ya kirkiro da wani event Arabian night."

Dole aka saka shi a manhaja.


Za'a fara bikin ranar Laraba a gama Asabar.

Batun had'uwa wajen amarya babu misaltuwa tayi kyau sosai tasha gyaran jiki.

Sai ana saura sati biyu sannan aka kawo lefe.


Masha Allah baby k'arya aciki anyi abune daidai karfi akwatuna set biyu golden da silver colour.


Kaya sunyi sosai Auntynsu Ukhashatu tayi kokari na had'o kaya masu inganci.

Kowa sai sa albarka yake ana yabawa.

Jamila tazo taga kaya tasa albarka tayi murna sosai itama.


Har zuwa satin biki inda ango yayiwa amarya wuyar gani haka itama saboda hada-hada.



An fara Biki cikin nishadi da nasara Hafsah taga Masoya tako ina haka Ukhashatu har wadanda batayi tunanin gani ba sai da ta gani bata bige da mamaki ba sai da taga Basma a wajen dinner ta ya kayi ta samu card admit oho ko kuma babu mamaki tunda katin yaje hannun yan makarantar su da dama.


Bikin yayi dad'i an gabatar da GAME na amarya da ango inda suka kayatar da jama'a. Biki yabar tarihi.

Daga k'arshe ranar asabar misalin k'arfe 11:00pm aka shaida daurin auren *UKHASHATU ABUBAKAR KHADI DA HAFSAH H HAMID.*


Farin ciki wajen ango baya misaltuwa ya gaza boye hakoranshi kowa albarka yake sa mishi da fatan alkhairi.


Su Fadwa an samu k'awa Amira tun farkon kayaniyar bikin suka jone saboda halinsu yazo kusan d'aya.

Amarya tasha kuka musamman sanda aka daura mata aure inda ta tabbatar yau ba ita babu kwanan gidan Abbanta.


Hajiyarsu  (kakarsu) ke ta tsokanar ta wai ana so ana kuka don itama ba karamin farinciki take da auren ba.


Da yamma yan daukar amarya suka zo. Amarya tana rizgar kuka haka maman ya Nazeer ta sata tayi wanka ta shirya tasha wankan turaruka har suka fara damunta.

D'akin Abbanta aka kaita wanda Dakyar ya daure ya iya yi mata takaitacciyar nasiha da addu'oi wanda shima daga karshe rauni ya hana shi k'ara sawa. Hakan yasa Hafsah kara fashe wa da kuka..


Mama kam babu abinda ta iya ce mata. Amma dole jama'a suka sa ta ta sa mata albarka. Tasha adduoi.


An kaita gidan khady inda Hajiyar Ukhasha ta bata kyauta ka sun karb'i amarya hannu bibiyu sannan ta bada wata tsadaddiyar alkyabba su Fadwa suka d'orawa amarya akan kayanta.


Daga k'arshe an kai amarya gidan ta bisa rakiyar yan uwa abokan arziki.


Gida ya tsaru kowa sai yabawa yake amarya tasha kaya sai godia ga iyaye.


An barta ita kadai yayin da kukanta ya kara tsananta don ma gidan estate ne ba ita kadaice a ciki ba. Maman   ya Nazeer ce ta hana abar kowa saboda akwai tazara kuma dare ya fara.



Amarya tayi jugum cike da tsoro shuru amma ango ba zo ba.

Shi kam yana can Abba na mishi nasiha sai daga karshe abokan shi suka taho domin raka shi. Sunyi musu takaitacciyar nasiha agurguje saboda dukka sun baro iyali. 

Daga karshe ango ya tafi raka su ya dan Jima kafin ya dawo. 



Ya dawo ya tarar da amarya a rakub'e saboda tsoro yayi murmurshi sannan ya nufe ta cike da wani irin shauk'i ji yake kamar bashi ba. A bude min fuskar mana amarya....




Hafsah ta tsinci kanta cikin wani yanayi  mai dad'i cikin rayuwar aurenta..sosai angonta ke tattalinta da nuna mata kulawa ta yardar wa kanta tabbas Ukhasha shine dai dai da rayuwar ta kuma zabin Allah ne.

Ba zata tab'a kwatanta soyayyar shi da k'warewar shi wajen iya nakaltar komai nata da iya sata nishadi da Yusuf ba sam.. tana godewa Allah duk sanda ta budi ido ta tuna Ukhasha ne amatsayin mijinta.


Ko yaushe shi maiyi mata hidima ne ta ko wanne fanni ga barkwanci da sata nishadi..sai dai kasancewar shi dan adam itama ta fahimci abubuwa da dama game dashi. 


-Yana son mace ta dinga mishi hidima.

-Sannan yana da fushi sai dai ya iya mallakar fushin shi. Ba ko yaushe ne idan yayi fushi take fahimta ba a da sai daga baya ta gane duk sanda ya tambayi abu sannan a lokacin kuma ya nuna abarshi, koda fuskarshi bata nuna ba to abadini fushi yayi.



Hakan yasa dole ta koyi abubuwan da suke saurin sauke fushin shi kuma ta zama jaruma wajen iya sarrafa shi. Shi kan shi baya iya dogon fushi da ita. Takan jin jina mishi kan komai dayi mishi godia akan komai yayi mata. Da kanshi yakan tsokane ta idan ya siyo mata koda ice-cream ne kafin ta fada sai ya mak'e murya ya tsokane ta yadda take magana.

"Thank you mu luv."!!

Sai ta harare shi tace "wa ce."?

"Mrs Ukhashatu mana.!!

Sai tayi murmurshi.



Yayan shi ya shirya musu fita kamar yadda ya shirya wa kaninshi sanda akayi bikin shi shima


Ziyara ce ta kasashe biyu Saudia da Dubai inda sauyi Umra sannan su wuce Dubai.

Jin dadi wajen Hafsah babu misaltuwa tayi godia ga Allah. Sun biya ta gidan Aunty babbar yayar su Ukhashatu a abuja saboda ta can zasu wuce sai da suka kwanan mata daya sannan suka wuce.

Ta nuna wa Hafsah soyayya matuk'a da tarairaya..


Jirginsu ya daga inda Hafsah ke cike da farinciki. Taji dadin tafiyar sosai kuma tafiyar tabar mata tarihi mara misaltuwa ta k'ara tabbatar da matsayin ta a zuciyar Ukhasha ya bar mata (memories) da dama da soyayyar shi da bazata iya kwatanta ta da komai ba. Taga kulawa da tarairaya..


Sun shafe watanni biyu a tafiyar..


_______________________

Jamila jira take Hafsah ta dawo (domin taji labarin tafiyar su) so take tayi mata albishir da mijin data samu itama kamar abin wasa a wajen bikin Hafsan sai dai yana da mata amma yayi mata sosai iyayen ta sunyi farin ciki itama.


Basma ta kammala karatu amma shuru duk cikin samarinta babu na aure..Duk da aranta har yanzu tana jin kaunar Nour domin sonshi ya zame mata jaraba amma babu damar mallakar shi tasan ya riga ya mata nisa sai yanzu take nadamar abinda suka aikata. Nadama mara amfani.

Mahaifiyarta tayi aure mutumin kiri kiri yake nuna wa Basma banbanci da kyara. Dole ta koma gidan mahaifinta shima babu yadda ya iya dole ya yarda ta zauna. Duk da zaman gidan babu dad'i aure kawai take so tayi.


Domin anyi bikin auntynta Fatima tun lokacin nata sa ranar, ashe tare Abba yayi niyyar aurar dasu amma ta bujure. Bak'in cikinta shine yadda yawanci mate dinsu sunyi aure da 'ya'yayensu tsurari ne suka rage..



Yusuf sai da ya tabbatar anyi auren Hafsah sannan  ya rarrashi zuciyar shi dakyar ya shiga neman aure bisa damuwar da maman shi ta nuna sosai kan hakan. Yasa a ranshi bazai auri watststsiya ba. Haka ya binciko wata yarinya mai siffar kamilai ya kuwa mutu akan sonta. Ashe kara da kiyashi ce daukar mara sani. Bayan chajar shi da suke ita da uwarta akayi auren Sannan ya tabbatar da lallai  Dara ce taci gida.

Daga lokacin zaman su ya dawo babu dad'i kullum cikin fada da cin mutuncin juna. Yana kiranta mara tarbiyya ita ma take buda baki tace ai jirgi daya ya debo mu tunda ka ganni haka Allah ne kadai yasan iri n ayar daka sheke.

Dama ya dawo da komai nashi Nigeria saboda haka sai ya fice sabgar shi da ta dade bata sashi ido ba. Kullum sukayi fada sai ya tuno da Hafsah ya sani yayi babbar asara..


__________________


Hafsah sun dawo daga tafiya lafiya sunyiwa yan uwa tsara ba tayo wa Hajiyar shi tsara ba ta musamman.


Kowa yayi murna da dawo war su inda suka dawo da murnar samun Baby  tun acan dama aka tabbatar tana dauke dashi.


Lokacin Ukhashatu ya maida hankalin kan tsara musu gidansu a gabanta yake tsara zanen yanayi yana tambayarta ranki ya dade yayi nan yayi.."?


___________________


Rayuwarsu abar sha'awa ga kowa. Yadda suke tattalint juna da yadda suke taka tsantsan da juna. Hafsah tayi imanin wannan abin yana samuwa ne sakamakon sirad'in  na tarkon Yusuf da ta fiye mishi da babu wannan jin dad'in a rayuwar ta. Tabbas ta gani kuma ta amincewa zuciyar ta cewa *"THE VIRGINITY OF GIRL IS HER DIGNITY"!..*


Da ta zama watsatstsiya da tuni bata da wani sauran k'ima a idon mijinta da mutane ma baki daya..wai idan ma ta samu mijin auren kenan..



Hafsah ta kuma yarda lallai yawan tarin dukiya bashi ke kawo kwanciyar hankali da jin dad'in rayuwa ba. Soyayya amincewa juna mutuntawa da tattalin juna sunfi komai taka muhimmiyar rawa. Duk da haka tasan mijin ta kuma bai rageta da komai ba, bata  nemi komai ta rasa a wajen shi ba. Sai dai idan ta kwatanta da irin burikan yan matan yanzu da yadda suke hangen rayuwar wasu da dogon buri zasu kwatanta Ukhashatu cikin tsaka-tsaki (middle class) ta fannin kud'i da tara abubuwan jin dad'in rayuwa. Amma a wajenta Ukhashatu k'arshe ne babu wanda ya fishi.


Sai yanzu take k'ara ganin abubuwa da dama wanda maman ya Nazeer ta dinga nusar da ita sanda tayi zaman gidanta. A lokacin data ke k'okarin dawo da ita hayyaci.

Bazata manta ba ta tab'a fad'a mata cewa.

_"Zaki samu wanda yafi Yusuf har kiyi alfahari dashi."_


Tabbas Yusuf baifi Ukhashatu a komai ba ta fannin wayewa, kyau Nasaba, da kuma iya mu'amala.


Abubuwan da za'a iya  kira da 'banbanci sune kamar rayuwar turai da Yusuf yayi wanda ita a wajenta ba wani abun gani bane tunda babu abinda zai kara mata sai ma nisanta mutum da al'adunshi idan ya zama mai sakaci ma da rashin kula sai su jinkirta yanayin addini. AMMA FA GA WASU..MISALI IRIN SU YUSUF. wadanda iyaye ke sakarwa ragamar rayuwar su tun suna yara suyi yadda suke so...amatsayin Yanci.



Kwanci tashi babu wuya Ukhashatu ya kammala musu ginin dankakaren gidansu 'nagani a yaba'


Ranar da yakai Hafsah taga gidan k'asa magana tayi acikin gidan gidane da babu kalar macen da bazata zauna ciki ba. Ya baje barisa wajen tsara ginin gidan.



Sannan a ranar dai duk yayi mata albishir da offer daya samo mata ta aiki a wata ma'aikata ta gidan Jarida sai dai ya fada mata zata fara aiki ne bayan ta ajiye mishi Baby da watanni."


Ta rasa yadda zata nuna mishi jin dadin ta.. sai kawai  ta bashi ~warm hug~sosai yake jinta shima.

_Thank you my luv u're really such a good caring and loving husband.._

"Kiyi shuru mace ta gari..ni da ke babu godia fa."


Haka yake fad'a mata yawancin lukuta idan tana mishi irin wannan godiyar.


Sun dawo gida. Hafsah ta sanar wa da Mama an kammala gidan ta tura musu photonan sassan gidan. Mama  tayi murna sosai  dasa albarka gidan ya kawatu a wajenta matuk'a ta kuma gode wa Allah yarta ce zata zauna cikin shi.



Hafsah taji godiyar da tayi bata mata ba don haka suna zaune suna daddana wayoyinsu ta ta fa "Thank you dear husband.'

Ya ga abin kamar gizo sunan ta ya bayyana ta turo mishi text. Ya duba ya kalleta sai ta mishi murmurshi. Ya nuna ta da yatsa kin ganki koh."

Sai ta kumshe fuska tana dariya.



Haka suke tafiyar da rayuwar su cikin jin kulawa da gujewa b'acin ran juna su kanyi duk wani abu da zai sa musu nishadi. Misali a lukuta irin na weekend ko sanda bashi da ayyuka sosai in yana gida Hafsah na kirkirar musu abubuwa funny things da zasu sashi nishadi."

Takan ce ya karanta mata ko it ta karanta mishi wani Littafi sai ta kwanta tana sauraron shi tanajin dad'in muryarshi da yanda yake furta turancin.. Yana iya daurewa ya karanta mata da dan dama? kafin tana ganin ya tsaya ko ya chanja yanayin shi zata kwaikwaye kafin ya fada ta rigashi." 

"Na gaji ban iya karanta abubuwan nan naku fah."



Ya nuna kanshi ni kike tsokana koh. Tayi saurin girgiza "A'a..Aa."

Tasan halinshi yanzu zai mata mugunta ko ya matse mata hannu  ko baki, kuma bilhaqqi tanajin zafi. Ta ma kasa gane shin soyayya ce ko kuma mugunta irin ta maza ko baisan tanajin zafin  bane."? Ko laifi ta mishi wani lokacin da haka yake hukuntata har sai tayi ihu sannan ya nuna ya tsorata harya bata hak'uri. Shi  yana son ya kwaikwaye ta amma ita baison yaji ta kwaikwaye shi sam indai tayi haka sai yayi amfani da wata hikima wajen hukunta ta. Misali yayi ta sata K'ananan ayyuka dakko wannan dakko wannan har sai ta gaji ita kuma b'ata kinyi. Idan kuma ta mishi complain ko ta nemi ya mata 'massage' (tausa) sai yai ta mata dariya sannan cikin wasa yaki yi mata sannan ya nuna mata ai punishing dinta yayi. Sai yaga zata yi kuka sannan ya hau yi mata waqa sai kuma yayi mata.






Yana taimaka mata a komai saboda cikin jikinta.. har wata rana sun dawo daga siyayya yake son gwada ta don ya san raguwa ce ko da ma bare yanzu. Ya dauki wasu  kayan sannan yayi mata nuni data dakko wata dundumemiyar jarkar mai.

"Please biyo ni da wannan store maman biyu.!! Yayi nuni da jarkar. Ai yadda ta zaro ida ya bashi dariya yaje yakai ya dawo Sannan ya kinkimi jarkar. Hafsah cike da tsokana ta dunkule hannu alamar jinjina tace "kaga mazaah"!

Ya waro mata ido yana mata wani irin kallo.

Ya dakata Sannan yace mazaje koh."? Tom bara na dawo kiga."

Babu shiri ta rufe baki da zura da gudu zuwa bedroom.

Ya bita da kallo cike da k'auna yana dariya yana girgiza kai tafi ahankali kada kimin asara..!!!!



Ya ajye jarkar ma shima ya bita.....




ALHAMDULILAH ALHAMDULILAH.


HAK'IKA NA DAUKI DOGON LOKACI FIYE DA SHEKARA DA FARA WANNAN TYPING SAI YAU ALLAH YAYI NA HATTAMA..

ALLAH NA GODE MAKA..

INA ROKON ALLAH YA SA MU AMFANA DA A BINDA KE CIKI KUSKURE KUMA ALLAH YA YAFE MANA...




*To readers*📔📚


NA GODE BISA SOYAYAYYA ALLAH YABAR ZUMUNCI..

KUMA INA FATAN ZAKU DAUKI ABINDA YAKE MAI AMFANI ACIKI KU ZUBAR DA MARASA AMFANI.. SANNAN KUYI HAKURI BISA YADDA KARSHEN  LITTAFIN YAZO A TAKAICE.


NAGODE..

ALLAH YA KAWO MANA KARSHEN WANNAN MUSIBA DA TA ADDABI DUNIYA AMIIN DON ALFARMAR ANNABI (SAW)

NAGODE.



*Karima Tijjani Mansur* 

*HAJEEYAH KHAREEMERH* 


Like Karima Tijjani novels on Facebook.

Follow on instagram @ Hajeeyah-khareemerh Tee-em.


Thnk you all

*Saturday 18/04/2020*



TARIHIN WRITER A TAKAICE..


_An haifi Karima Tijjani Mansur a garin kano ashekarar 1998 a watan April. Tayi karatun ta duka na addini da na boko a garin kano. In da yanzu take karatu a jami'ar Yusuf mai tama Sule YUMSUK (NRTHWST KANO.)_


ZAZZAFAN SO Shine littafin ta na farko wanda ta fara futarwa amma kafin shi ta fara rubuta wasu amma ba'a buga ba ko a online ko publish..

Karima Tijjani matashiya ce yar kimanin shekaru 22.

Kuma ta fara rubuta Littafi tun tana kimanin shekara 15. Sai dai bata fitar da shi ba..




Post a Comment

0 Comments