TOP HAUSA NOVELS atOptions = { 'key' : '20e08520dad54dbf6d9e963271

Makauniyar soyayyah page 35_36

 

*Question of the Day*


K’ofofin aljanna guda nawa ne? Lissafo sunayen su.




 

35&36



Maida hankali na nayi gaban allon Tv ina kallon tauraren d’an adam a tashar MBC Bollywood, jefi-jefi nake jin hirar tasu.


Yaya Aminu ne naji yana cewa yaya Faruk "kai ma Soja ya kamata ace ka fito da matar aure, tun da iyayen mu sun nuna suna son kayi aure, in kuma baka fi son azumi in yazo a fara kad’a maka ganga ba"


Murmushi kawai yayi kana yace "very soon insha Allahu zan gabatar da wanda nake so, kafin in koma aiki zan zo in same ka akwai maganar da nake so muyi" cewar yaya Faruk.


"Ok sai kazo" ya bashi amsa.


Yaya Aminu ya mik’e cikin wasa ya kalli yaya Faruk yana cewa "ni zan gudu, nasan madam nacan na jira na, kai ko k’arfe nawa zaka kai a waje ba matsala, ba mai tambayar ka".


Shima mik’ewa yayi yace "nima tafiya zan yi".

Sallama suka min suka tafi.


Kasancewar yanzu ba ma zuwa ko ina tun da muka zana SSCE exam d’in mu, Abbu ne yasa yaya Khalil ya siyo mana form ni da Anisa a Al-Mannar Academy na shiga Mutawassid tun da mun yi saukar Al-qur’ani.


Bayan mun cike form ne muka fara zuwa makarantar.

Daddy form d’in computer training yasa yaya Faruk ya amso mana a Bintalya computer institute.


Sai ya zamana yanzu ba mu da wani time, da mun dawo daga computer training, ba jimawa zamu tafi islamiyya, ba mu zamu dawo ba sai yamma.


Yanzu tsakani na da yaya Faruk ba wani takurawa, ni gani nake yi neman shiri yake yi dani saboda yadda yake d’an ja na da wasa da kuma hira.


Duk wannan abubuwan da yake yi ba wai na sake dashi bane saboda sanin hali.


Yau ranar ta kasance ranar lahadi, yaya Faruk ne cikin shirin shi ya fito ya shiga side d’in Momi, bayan sun gaisa ne yake ce mata zai lek’a gidan yaya Aminu ne, fatan a dawo lafiya ta mai da sak’on gaisuwar ta ga Anty Jiddah da Humaira da Nabil.


Kafin ya isa gidan sai da ya tsaya a wani super market, ya tsaya yayi wa su Humaira da Nabil shopping.


Da isar shi gidan ya same su a falo da yaran suna kallo, su Humaira kuwa sai murna suke yi da ganin yaya Faruk saboda yadda yake kawo musu kayan zak’i da kayan wasa.


Hannu ya mik’a wa yaya Aminu suka yi musabaha kana ya samu guri a d’aya daga cikin kujerun dake kewaye da falon ya zauna.


Anty Jiddah ce ta gaishe shi tana tsokanar shi tana cewa "su Anisa ba su baka sak’o na ba?


Ta’be baki yayi yace "wane irin sak’o ne".


Dariya tayi ta d’aura da cewa "ce musu nayi su ce maka ka bani za’bi in za’bar maka mata tun da kai naga har yau ka k’i fito da wacce ta yi maka".


Murmushi yayi yace


 "Madam kenan, ke kin san class d’ina yafi a ce za aza’bar min mata saboda ba ki ga yadda ‘yan mata ke so na ba a Kaduna da Abuja, infact nan ba dad’e wa ma zaki ga wacce nake so".


"haka muke so Soja, gwara kayi zuciya kayi auren ko ka huta da gori" Anty Jiddah ta fad’a da alamar wasa.


Yaya Aminu kuwa bai ce komai ba in banda dariya da yayi.


Kayan motsa baki taje ta kawo mai ta ajiya ta nufi d’aki ta barsu dan su zanta.


Nabil ne yaje kusa da yaya Faruk ya manne a jikin shi ya fara Maganar shi ta ‘yan koyo yace


 "Uncle Soja ina bindigar da kace ja ka ciyo min".


Kunnen shi ya kama yace "sorry Nabil na manta ne amma in zan k’ara zuwa zan siyo maka".


Tsalle Nabil ya fara yi yana cewa "yeh Uncle soja jai ciyo min bindiga".


Humaira sai faman zun’bura baki take yi ganin ance za a siyo wa Nabil bindiga amma ita ba a ce za a siyo mata ‘yar baby ba (toys)"


"zo nan Humaira" yaya Faruk ya kira ta cikin lallashi.


"Me ya faru ne baby naga kina so kiyi kuka".


Cikin shagwa’ba tace "ba kai bane kace zaka siyo wa Nabil bindiga, ni kuma ba kace zaka siyo min ‘yar baby ba (toys)".


Dariya suka yi shi da yaya Aminu kana yace "ke ma zan siyo miki, an shi wannan ki kai ma Momi ta raba muku"


Cikin murna ta amsa tana cewa


 "Uncle soja mun gode" ta tafi d’akin Anty jiddah da gudu.


 ganin haka ne yasa Nabil shima ya bi ta da gudu.


5 alive na kwali da Anty Jiddah ta kawo mai ya d’auka ya tsiyaya a glass cup ya sha, ya juya kallon shi zuwa gurin yaya Aminu yace "Aminu shawara nazo nema a gurin ka game da yarinyar da nake so".


Yaya Aminu ya yalwata murmushin shi yace "Masha Allah ina jin ka, kace mun kusa yin suruka".


Sai da ya numfasa kana yaci gaba da cewa "Aminu ba kowace yarinya bace na dad’e da fad’a wa tarkon son ta illah Fatima, bazan iya fad’a maka adadin son da nake mata ba, sai dai kawai in ce maka, I really love her".


Da mamaki yaya Aminu yace "wace Fatiman kake nufi?


Gajeren tsaki yayi kana yace "Akwai wata Fatima ce da ta wuce k’anwar ka".


Dariya Aminu ya fara yi yana kallon yaya Faruk wanda ya tamke fuska ganin dariyar da Aminu yake mai.


Wani dogon tsaki ya k’ara ja wanda yafi na farko yace "wai Aminu miye abin dariya, daga na fad’a maka sirrin zuciya ta, ka tasa ni sai dariya kake min kamar kaga wani mahaukaci".


Tsayar da dariyar yayi yana cewa


 "Sorry Bregadier, my inlaw, abin ne da ban dariya da mamaki wai kai kake son Fatima, gashi kana da son girma, baka son raini, ita kuma Fatima ga rawar kai, amma soyayyar nan za ta ba da ma’ana, naji dad’i da Sister ta samu gwarzon namiji kamar ka, congrat".


"Kai matsala na da kai Aminu, kana mai da zance mai mahimmanci wasa, nazo dan ka bani shawarar amma kana d’aukar zancen as a joke".


"Ok sorry, joke aside, yanzu fad’a min shawarar da kake so in ba ka" yaya Aminu ya fad’a.


"Kaga dai Fatima ba ta dad’e da kammala Secondary School ba, nan ba da jima wa ba admission zai fito su fara d’auka lectures, yanzu abin da yake damuna shine har yau ita Fatima ba ta san ina son ta ba, tsoron da nake ji shine kar in bari ta fara high institution ta had’u da wani su fara soyayya alhalin ni ina nan ina jiran ta, kar kuma in fad’a mata yanzu in katse mata karatu tasa soyayya a gaban ta? kai menene shawarar ka".


Yaya Aminu in ban da bin shi da kallo ba abin da yake yi.


 mamaki yake yi wai Faruk ne ya zauna yana expressing d’in feeling d’in da yake ma Fatima, "lallai ya yarda Love is everything, you don’t have any choice to control yourself when you fall in love, ya kuma yarda da son da Faruk yake ma Fatima".


"A shawara ta Faruk, ina ganin ka fad’a mata yanzu saboda tasan kana son ta da wuri, kaga ko nan gaba tasan da kai, ba za ta bari ta sa soyayyar wani a ranka ba, kasan A bari ya wuce shi ke kawo raban wani".


Yaya Aminu ci gaba yayi da cewa 'yanzu kayi amfani da DAMAR KA ka k’ara jan ta a jikin ka na yadda SHAK’UWA CE za ta k’ullu a tsakanin ku, kaga daga nan sai ka nuna mata ZAZZAFAR K’AUNAR da kake mata, I know, she will not reject you, because you are one out of thousand".


Wani murmushin dad’i yaya Faruk yayi saboda yadda yaji yaya Aminu ya bashi shawara da kuma yadda yake fasa mishi kai, hakan yasa ya k’ara samun k’arfin gwiwar tunkarar ta.


Shawarwari yaya Aminu ya dinga ba wa yaya Faruk akan yadda zai shawo kan Fatima ba tare da wata matsala ba.


Canza akalar hirar suka yi kana yaya Faruk yace ya kira mishi Anty Jiddah ya mata sallama ya tafi.


Tun daga wannan time d’in ya zamana yaya Faruk na zuwa gidan mu yana ja na da hira, ga siyayya da yake min akai – akai, yanzu har dama ya bamu wai mu dinga yin chating, ga kira na da yake yi akai-akai.


Ni ko mamakin mai ya canza yaya Faruk a lokaci d’aya nake yi, yadda ya dawo so cool da friendly damu.



Yau da daddare ina zauna a d’aki ina buga game a waya ta, naji alamar shigowar war calling a waya ta.


Sunan yaya Faruk na gani a jikin screen d’in yana yawo, d’auka nayi na amsa mishi sallamar da ya min.


'ki same ni a falo akwai maganar da za muyi" abin da yace min kenan ya katse wayar.


Tunani na fara yi wace Magana ce zamuyi dashi da ba zai bari gobe ba sai da daddaren nan.


Hijab kawai na d’aura akan night gown d’ina da zani akai na nufi falo.

Samun shi nayi a falo shi da yaya Khalil suna hira.


Guri na samu na zauna na gaishe shi.


Ganin bai ce min komai ba yasa nace


 "gani yaya Faruk"


Yaya Khalil ne ya mik’e yayi wa yaya Faruk sallama ya tafi side d’in shi.


Shiru falon ya d’auka na d’an mintina kamar ba kowa a ciki.


"TEEMAHHHH"


Saurin d’ago kaina nayi saboda yadda naji yaya Faruk ya kira suna na wanda ya banbanta da sauran lokutan da yake kiran suna na.


D’aga kai nayi na kalle shi ba tare da na amsa ba.


Shiru yayi kamar mai tunanin abin da zai ce yake yi.


"Fatima! ina so ki bani aron time d’in ki saboda maganar da nake so muyi a yanzu is ver important".


Wannan wace Magana ce kuwa da yaya Faruk yake son fad’a min mai mahimmanci haka? nasan wannan tambayar ba ni da amsar ta sai dai in jira ya fad’a min ba.


"Teemah, duk maganar da zan fad’a miki ki d’auke ta da mahimmancin saboda har cikin zuciya ta haka take, kar ki zata ko da wata manufa zan fad’a miki sai dan in fallasa abin da ya dad’e a cikin zuciya ta yana damu na".


Duk da ban san wace Magana ba ce, sai naji gaba nay a fad’i duba da yadda yake amfani da cool sound wajen maganar.


"Teemah! ba kowace Magana bace da ta wuce in ce miki INA SON KI FATIMAH, I know I am in love with you because my reality is finally better than my dreams".


Gaba na ne ya fad’i na yadda maganar tazo min a bazata da firgita da nayi a lokaci guda wanda hakan ya kasa ‘boyuwa a fuska ta.


"mai yaya Faruk yake nufi da wannan kalamen nashi, ko in ce tatsuniyar da za ayi ta a lokacin a gama, an ya yaya Faruk yana cikin hankalin shi da zai tunkare ni da wannan tsadaddiyar kalma mai wuyar furta wa? ya ma san wacce yake fad’a ma wannan kalmar" na tambayi kaina.


Kamar ya san tambayar da nake yi wa kaina yace


 "Teemah, kar ki yi mamaki ko shakkar maganar da na fad’a miki, kar kuma ki d’auka da wani nufi a raina yasa na fad’a miki haka illah ina fallasa miki abin da ya dad’e a raina, duk wasu abubuwa da kika ga ina miki wanda kike d’auka a matsayin takurawa, ina miki shine dan ina kishin ki da kuma son da nake miki".


Ci gaba yayi da cewa "Teemah! True love doesn’t have a happy ending because true love doesn’t have an end. My love 4 u has no end, farin ciki na shine samun Ki, there is only one happiness in this life, to love and be loved".


Ni dai rasa a wani hali nake ciki, rasa wani hukunci zan yanke ma wannan maganar mai kama da labari shuni ya yi, na yadda namiji bai da kunya, tun da har yaya bai jin kunyar fad’a min abin dake ranshi ba, ya kuma manta abin da yamin a baya, duk ma ba wannan ba, zuciya ta ce tak’i marhabin da sak’on da yaya Faruk yazo mata dashi.


Jin bance mai komai ba yasa yace


 "Fatima zan baki time kije ki yi tunani kafin in koma aiki saboda hutuna ya kusa k’are wa, dafatan zaki yi ma Magana ta duban basira".


Ya mik’e yana duba wrist watch d’in shi yace "Gud night Teemah, na barki lafiya".


Bai jira jin abin da zance ba ya tafi.




Post a Comment

0 Comments