TOP HAUSA NOVELS atOptions = { 'key' : '20e08520dad54dbf6d9e963271

Saran Boye page 72

 πŸ’ƒπŸ»πŸ’ƒπŸ»πŸ’ƒπŸ»πŸ’ƒπŸ»πŸ’ƒπŸ»

TEAM----ZAFAFA BIYARπŸ”₯😘πŸ₯°πŸ˜


ALLAH ka gafartama iyayenmuπŸ˜­πŸ™πŸ».[7/6, 9:38 AM] : *_LITTAFIN nan na kuΙ—i ne. Dan girman ALLAH ki daure ki biya kafin ki karanta, idan kuma bazaki iya biya ba ki haΖ™ura domin ALLAH karki karanta. Idan kuma kin saya dan girman ALLAH karki yaΙ—a manaπŸ™πŸ»_*.



No. 72


...........Washe gari bayan sallar asuba Nu'aymah ta Ι—orama Yoohan karatu kamar yanda suka saba. Daga haka ya shiga Ι—akin motsa jikinsa. Ita kuma sai tayi amfani da wannan damar ta shiga Ι—akinta domin Ι—akko hoton nan. Duk da ta jima bata shigesaba ta fahimci an canja mata zaman wasu abubuwa da dama. Wasuma babusu. Bata bar hakan ya dametaba ta nufi Wadrobe direct inda ta ajiye hoto. Sosai gabanta ya faΙ—i ganin yanda kayanta suka koma a harmutse ba yanda tasan sukeba. Cikin gigita ta shiga tiΙ—osu Ζ™asa tana faman zazzagewa. Sai dai kamar da wasa babu hoto babu labarinsa. Hankalinta ya tashi, har takaita da duba indama tasan bata ajiye Ι—inba amma ko mai alamarsa babu.

        Jagwab ta zauna a bakin gado tanabin Ι—akin da kallo daki-daki, dan sai a yanzune ma harmutsewarsa ba yanda ta barsaba yake dawo mata a zuciya daki-daki. Yoohan ta fara kawowa a zuciyarta. Sai kuma ta girgiza kanta dan bata tunanin zai mata bincike. Can Ζ™asan zuciyarta yace, ‘Omar ne. Bashi kika sanarma maganar hotonba’. Nanma da sauri ta girgiza kanta alamar a'a. Gebrail. ‘Kai bazai zama shiba. Dan shi manufarsa daban data masu hankali. Wannan bashi da man kai akan hakan’. Madam Chioma. Nanma a fili tace, ‘Kai ina bana sata a wannan layin dan kanta baya ja tacika kidahumanci kamar kifi’. ‘To wa zan zarga?. Ko dai papa ne?’. Mikewa tai da sauri tana kaΙ—a kanta hannayenta duka biyu a saman cikinta. ‘Lallai tabbas shine abin zargina, musamman daya kasance ya riga yabi diddigina akan shigar masa Ι—aki da nayi, zai iya kasancewa tunaninsa ya basa zuwa nan yamin bincike. Shin minene wannan mutumin ke Ι“oyewane akan mijina? Lallai ya kamata na sani kafin na sake barin Ζ™asar nan’. Sai kuma ta dafe goshi cike da damuwa. ‘Hoto shine kawai hope Ι—ina. Gashi yanzu Ι—an barahazar ya sace min, bayan na gama baza bayani wajen Abbana da wannan Umar Ι—in. Kenan dolene na sake satowa. (Idan bai Ζ™onaba ko?) zuciyarta ta ayyana mata. Karan farko da matsanancin tsoro ya risketa. Da sauri ta fita a Ι—akin zuwa can cikin gidan. Gidan shiru alamar masu gidan babu wanda ya tashi kasancewar weekend ne. Kitchen ta nufa. Tako iske Blessing kawai tana haΙ—a breakfast kamar yanda tayi hasashe.

       Ko gaisuwar Blessing Ι—in bata amsaba taja hannunta suka shige cikin store. Sai da ta leΖ™a ta tabbatar da babu kowa sannan ta tura Ζ™ofar store Ι—in ta rufe ta juyo ga Blessing da jikinta harya fara rawa. “Please ki nutsu, ba wani abu bane tambaya zan miki, ina fatan kuma zaki bani amsa kamar yanda kike bama Omar... Oh sorry Richard”.

      Cike da tsoro Blessing zata fara rantse-rantse Aymah ta tsaidata......

      “Karki wahal da kanki wajen mani rantsuwa nasan komai daga wajensa. Inason nasan zuwan Richard nawa gidan nan?”.

     Da tsoro sosai a fuskar Blessing tace, kusan bakwai”.

          “Dama can anan yake sauka kenan tunkan aurena da Yoohan kokuwa a yanzune yake sauka anan?”. 

      “Eh dama yana sauka gaskiya, amma sai Oga yana Ζ™asar”.

     Jimm Nu'aymah tayi alamar tunani, sai kuma tace, “Mikike tunanin yana zuwa yi nan gidan?”.

    Cike da tsoro sosai Blessing ta buΙ—e Ζ™ofar kaΙ—an ta leΖ™a, hakan yasa Yoohan daya biyo Aymah yake a laΙ“e saurin komawa ya lafe a bango. sai da ta sake tabbatar da babu kowa sannan ta dubi Aymah murya can Ζ™asa sosai. “Na yarda dake sosai Aunty na, dan tun a zuwanki gidan nan na fahimci ke mutuniyar kirkice wlhy. dan haka zan sanar miki komai duk da nima ba komai Ι—in na saniba”.

     “Okay ina saurarenki”.

“Tun bayan wucewarku Austria nakeji wasu maganganu masu gidan nayi a kanki. Dan akwai randama na taΙ“ajin an bada kwangilar kasheki ta hanyar likitan da zasu miki aiki. To sai dai kwanan mutuwarki bai rigada yazoba dan ke Ζ΄ar baiwane. Sai akazo baki mutuba. Su boss sunje dubaki, bandai san miya faruba bayan dawowarsu Uncle Richard naga ya nacema zuwa gidannan. Sanan yakan sani na masa wasu abubuwa akan boss ko madam Ι—in gidan nan. Sannan ko baya gida zai kirani yaji mi akayi ko mi ya faru. Badai komai nake fahimtaba gaskiya, tunda banida hurumin yin komai. Sai dai matsalar dana fuskanta shine randa su papa suka shiga sashenku ita da Solomon da Madam. Sun miki bincike a Ι—aki sai dai basu sami komaiba suka fita. Bayan hakan Uncle John yazo Ζ™asarnan yaga yanda akai miki da Ι—aki shine ya zane Gebrail a tunaninsa shine ya shigar miki. A zahiri papa baicema Uncle John komaiba akan dukan Gebrail. Amma bayan barinsa gidannan ba Ζ™aramin rikici akayiba tsakaninsa da maman madam dama madam Ι—in. Shima kuma papan naji yana wasu maganganu tsakaninsa da Brothers Ι—in nan nasa wanda ban ganema kansuba sam. Wanann rikicin ne ya saka su Maman Destiny barin gidan nan. Dan sun nuna goyon bayan Uncle Yoohan fiye da Gebrail. Shine yasa akai rikici duk suka wuce. Bayan nan kuma sai Uncle john Ι—in da yazo last time madam Ι—in gidan nan ta shigar masa Ι—.........”

      Da sauri Yoohan dake a laΙ“e ya rin tse idanunsa tare da shiga kiran sunan Nu'aymah tamkar ya shigo nemantane. Rikicewa sosai Blessing tayi, amma Aymah ko'a jikinta saima Ι“ata fuska tayi ta buΙ—e Ζ™ofar bayan ta Ι—ebo noodles guda biyu. 

       “Oh Sweet boo ganinanfa a store. Nazo amsar noodles ne a wajen Blessing shine take nunamin inda take”.

            Cike da mamaki yake jinjina wayonta. Amma shima sai ya waske yana mai dafe kansa da faΙ—in, “Kinsa duk na ruΙ—e na fito ban gankiba a gaba Ι—aya sashen”.

      “I am sorry Hubby”.

“Silly girl yana iya dake. Yanzu yaya za'ai da Noodles Ι—in?”.

     “Zan dafa ne anan”. Ta faΙ—a saboda son ya barta ta Ζ™arasa jin zance a wajen Blessing.

     Fahimtar hakan da yayine ya sakashi hayewa saman kitchen cabinet Ι—in yana cewa, “Okay dafa to mu wuce. Dan kinsan akwaima fa inda zamuji ga lokaci nata Ζ™urewa, Omar ma jiranmu yakeyi tuni. Koma kibama Blessing Ι—in ta dafa miki muje ki shirya data gama sai kici kawai”.

     Duk da Aymah bataso hakan ba sai ta amince kawai. Dan ita bama cin noodles Ι—in zatayiba sam. Blessing ta Ζ™walama kira. Sai gata ta fito da sauri hannunta Ι—auke da abinda zata dafa da rana irin dai shi ta tsaya Ι—ebowa. Sai dai kallo Ι—aya Yoohan ya mata ya fahimci tsoron dake tattare da ita.

    Bata dahuwar noodles Ι—in tayi suka fice. Gaba Ι—aya hankali Nu'aymah akan Blessing yake. Amma Yoohan yay mata tsayuwar sojan badakkare aka komai tare sukayi. Koda suka fito Blessing ta kawo noodles Ι—in catai ta Ζ™oshi. Sai Yoohan Ι—inne yaci tare da Omar. Dama yasan baci zataiba ai. Dan tunda ta samu cikin nan tabar cin indomie sam.

      Koda suka gama ficewa sukai a gidan batare da sunbi takan kowa ba. garama mama debora sun haΙ—u da ita a falo tana shan shayi. Tako hanasu fita saida akaima Aymah addu'oi ita da cikinta. Dan tace ita yanzu ta daina yarda da madam Chioma a gidan samπŸ˜‚πŸ€£.


     Ita dai Aymah yanzu tsohuwar birgeta takeyi. Dan har suka bar gidan batabar murmushi ba akan abinda ya faru.

    Tafiyarsu ta Ι—anyi nisa Omar ya fahimci ana binsu a baya. Shima Yoohan ya gani amma baice komaiba. Dan babu abinda zuciyarsa ke masa sai tariyar zancen Aymah da Blessing. Tunaninsa wane abu ne Aymah ke zargin an shigar mata Ι—aki akansa ana nema? Sannan kuma ashe papa ne da madam Chioma suka shigar masa Ι—akin mata hardama Solomon?. wane bincike Umar keyi akan iyayen nasa?  Mi Aymah ta shiga yi Ι—akin papa a wancan karon daya dage kareta a wajensu amma hardayin Ζ™aryar taga wanda ya shiga Ι—akin ashe itace?  Miyasa mahaifinsa yasa a kashe masa mata? Dolene yasan waΙ—anan tambayoyi a lokacin Ζ™anΖ™ani insha ALLAHU.

    Da wnanan tunani da yakene yasa har Omar ya gudama masu binsu shi baisan yaya akaiba. Sai ganinsu kawai yayi a station Ι—in su Jay.

         Aymah dai har suka shiga tana maibin wajen da kallo tare da jami'an tsaro. Ko Ι—ar batajiba duk da ta fahimci wajene bana wasan yaraba. Yau saΙ“anin ranar Office Ι—in Jay aka kaisu direct, acan suka sami Dawood da Little bee da bily. Sai Afrah da adalilin zuwan Aymah Jay yasa akazo da ita. Dan ita karatun lauyanci takeyi batabi ayarin su little bee ba.

      Duk da a hoto sukasan juna ita da Aymah hakan bai hanasu gane junaba. Suka rungume juna kuwa cike da Ι—oki dan sunyi sabo sosai ta chart da waya. Daga haka Aymah ta gaida little bee dake zaune tanata danne danne a Computer alamar miskilawan na kusa. Dan duk ihun dasu Aymah sukeyi ko kallo basu ishetaba, aikinta takeyi hankali kwance. Gaisuwarma a haka ta amsata. Sai daga baya ta Ι—ago ta kalli Nu'aymah sannan suka gaisa dasu Yoohan.

    Nu'aymah dai bata sake bi takantaba itama ta juya ta gaida Dawood da Miemaa data amsa mata da fara'a da kulawa, dan itama ta taimaka mata ta zauna a kujera. Daga haka ta gaida Jay da a kallonsa sai da gabanta ya faΙ—i. Duk da ba tsananin kamanni suke da Yoohan ba dolene kaga yanayin gittawar jini tattare a tsakaninsu. Duk da ba mutum bane shi mai yawan wasa saida ya tsokaneta kaΙ—an. Har hakan ya bama su Yoohan mamaki. Dan su dai ba taΙ“a ganin dariyarsa sukaiba tunda suke mu'amula da shi.

     Sai da aka lafa da gaishe-gaiahe Jay ya fara magana.

       “So ba shirita ne ya taramu ananba. Inason ku bani hankulanku nan gaba Ι—aya. Da farko dai kece bakisan dalilin zamanmu ananba duk da mijinki ya tabbatar mana ta hanyarki yasan wasu abubuwan. Sai ko Afrah da sanin nata baida muhimmanci daga tushe duk da itama da taimakonta ne muka samu bayanan sirri game da gidanku. So yanzu little zata miki sabon bayani, ke kuma Afrah jeki waje ki jiramu”.

     Sosai Afrah ta Ι“ata fuska kamar zatayi kuka. Cikin magiya tace, “Abie Please ka barni dan ALLAH, wlhy nima zan taimaka muku da wani abun kaimafa ka sani. Duk da ba aikin nan nakeba so nawa ina muku aiki ta Ζ™arΖ™ashin Ζ™asa”.

    Fuska ya haΙ—e zai mata magana Aymah da duk kwarjininsa ya cika mata idanu tace, “Abie dan ALLAH, indai hakan ba laifi bane ka barmin Aunty zanfi samun Ζ™warin gwiwa nima”.

      Kasa cewa komai Jay yayi, ya kai dubansa ga little. Da wani style na Ζ™warewar aiki taima mahaifin nasu alamar roΖ™on yabar Afrah Ι—in. Dan itama tana hasashen tasirin zamanta a wajen.

     ΖŠauke kansa kawai yayi ya maida ga Yoohan dake ta kallonsa kamar ya samu television. Sai kuma ya Ι—auke ya sake maidawa ga little bee alamar ya bata damar yima Aymah bayani.

    Tsaf ta gama yima Nu'aymah bayanin komai. Dan haka taketa duban Yoohan da Umar cike da mamaki. Da damuwa a harshenta tace, “Amma Yah Yoohan baka gudun Abbana kar yaga ba'a Ζ™yauta masaba. Sam baya son laifin jama'ar gidan nan namu, shiyyasa yake Ζ™oΖ™arin maida laifukansu kuskure dan gudun lalacewar zuminci”.

      “Zeeynab inhar muka cigaba da bama Uncle goyan baya akan hakan tabbas sai an salwantar da ran Ι—aya daga cikinsu ko ke ko Muhammad a wannan gidan naku. Dan ni nasan mina ganarma idona a Austria da wasu maban-banta wajaje dangane da ke”.

     Bata iya tace komaiba dan tasan gaskiya Yoohan ya faΙ—a. Bandama ALLAH yasa tanada sauran kwana a duniya ai da tun tana jinjira an aikata barzahu Ι—in. Sannan shima Muhammad Ι—in ai ansha gwada rayuwarsa a mabanbanta lokuta Abba na Ι“oyewane kawai........

     Cikin katse mata tunani Jay yace, “Karki damu akan Sheikh, ni zan masa bayanin dazai gamsu akan hakan. Yanzu zamu tafine kai tsaye akan abinda ya taramu anan tunda kin gama jin bayanan farko. Dan dama munsa mijinki ya dawo dake Ζ™asarnan ne dan zamu Ι—anaki a gidanku ne matsayin tarko. Dawood minene bayani akan binciken wayar matar nan da aka sakeyi?”. Ya Ζ™are maganar da maida hankalinsa ga Dawood.

       Takardun gabansa ya Ι—auka ya fara bayani. “Sir bayanan sununa tabbas ana amfani da wayarta batare data saniba. Kamar maganar yin waya da mai aiki da aka turoma matar Yoohan anan Abuja, sam ba Rabi bace ke waya da Uwaliya. Mun tabbatar da hakane ta hanyar binciken ainahin muryar da aka samu a voice recording Ι—in nan. HaΙ—ine ta hanyar makirci babba na masu ilimin sani akan na'ura mai Ζ™waΖ™walwa. Suna amfani da wani app... Ne da aka saka cikin wayar matar, dama kowacce waya idan ta sake sai suke sarrafa wayar tata daga wajensu batare da ita ta saniba, suna barin mata bayanan abinda sukai da tasu wayar, dan ko an tashi bincke ita za'a zarga kai tsaye. Hakan yana nufin kenan tun fil azal da aka kawota gidan dama akwai manufa a ciki, kokuma daga baya aka fara amfni da ita. WaΙ—anan sune tatattun bayanai akan ainahin contact dake a wayar Rabi wanda suke aiki da saninta. WaΙ—anan kuma sune ainahin waΙ—anda ake amfani da ita ta wayar batare data saniba. Kuma insha ALLAHU zasu taimaka mana mu zaΖ™ulo kosu wanene masu aikata hakan kamar yanda Abdurrahman Sameer Saifudden ya bamu tabbaci, dan shine yay wannan bincike gaba Ι—aya tun daga Ζ™asar india. Ya kuma tabbatar mana idan ana buΖ™atarsa zai iya zuwa koshi ko abokan aikinsa yan uwan tagwaicinsa kenan”.

       Cikin jinjina kai Jay ya amshi takardun yana duban little bee. “Bilkisu! Minene bayanan wajenki akan zaman Afrah gidan?”.

      Juyowa Little bee tayi da kujerar da take a kai tana fuskantarsu. Yoohan ta sake kallo kamar yanda dama tuni shi take kallon a sace bisa Ζ™yaΖ™yΖ™yawan nazari datakeyi akansa tun farkon fara ganinta da shi.

     “Sir! Bayanan dake anan sun nuna wasu sunaye da Afrah ta rubuta akan zarginta, saboda wasu al'amura da suke aiwatarwa a gidan na marasa gaskiya. Akwai Rabi. Mai aikinsu, a yanzu tana a hannunmu. Sai Mai aikin sashen Addah, sai ita kanta Addah da tafi kowa kusanci da Umm a gidan. Sai Nasir wanda asali shi bama Ι—an gidan bane yana zuwane lokaci-lokaci. da wasu sunaye a jerin Ι—aliban Uncle Soorajidden Ι—in. Ta tattara waΙ—an nan sunayen ne bisa dalilai mabanbanta da suka faru akan idonta da kuma yanda labarin yazo garemu. Zamu iya jin bayani daga bakinta gata nan idan da buΖ™atar hakan”.

        A yanzu kam bily ce tai wani gutun murmushi tana kallon Jay. Cike da nuna Ζ™warewar aiki tace, “Boss niko kaga a duk jerin sunayen nan mutum uku kawai naba ayar tambaya. Sauran kuma inaji a jikina basa zaune a cikin gidan. Abinda yasa nai wannan maganar shine duk lokacin da za'a cutar da ita Nu'aymah akan yine lokacin wani taro a gidan. Hakan na nufin akwai mazauna gidan dake zaune a waje cikin tafiyar. Amma Ζ™asurgumin azzalumin yana nan cikin gidan tare da su ko akasin haka. 

     Murmushi Jay yayi a karo na farko. Ya sauke numfashi da Ι—an buga pen Ι—insa akan takardar gabansa. “Tabbas komai zai iya kasancewa. Dan suma sauran ai hasahe mukeyi, tunda ga Rabi a hashe muka samota kuma sai gashi babu laifinta”.

     “Hakane kuma boss. suspect Ι—inmu na gaba sune, Nasir, Ameer, Hamisu, Kubrah, Abdallah. Da iyayen su Abdallah n”.

     Da sauri Aymah tace, “momy!” cikin zaro idanu. sai kuma ta shiga girgiza kanta da sauri-sauri tana cigaba da faΙ—in, “Bazai kasance hakaba Momy. Uncles Ι—ina suna matuΖ™ar son Abbana. Hakama Yah Abdallah na matuΖ™ar sona. Bazasu cutar damu ba sai dai idan Nasir ne”.

     “Relax Nu'aymah. Muma bamun tabbatar bane hashene kawai. Dan dolene mu alaΖ™anta laifin nan da mafiya kusanci da iyayenki dake kanki, shiyyasa zamuyi amfani da wannan lokacin da mukasan duk ahalinki zasu taru a gida saboda bikin aure da saukar yaran gidan marayunku mu Ι—ana musu ke a matsayin tarko wajen damΖ™esu batare da sun fargaba.....”

        Yoohan ya katse Bily da cewar, “Humm tabbas Momy bana tantama akan hakan. Musamman akan Abdallah. Dan ta dalilinsa na sakama sauran ayar tambaya. Abdallah yayi fushi yabar Nigeria saboda ba'a aura masa itaba. Amma kuma a bayan fage yana a cikin Ζ™asar, dan yana yawan shigowa akai-akai. Sannan kuma yana bibiyar al'amarinta dani kaina. Dalilina na biyu a kansa shine wani business da yakeyi a Ι“oye batare da sanin iyayen nasaba. Dalili na uku akwai harΖ™alla akan aurensa da yara biyu na gidan da aka aura masa dalilin sace Zeeynab da akai ranar wancan auren nasu. Ya saki yaran batare da Ι—aya ta tare ba. Wadda ta tare Ι—in bincikena ya tabbatar min da tasha wahalar zama da shi. Zargi na uku. Akan hotona da aka kai gidansu ni da ita. A yanda labarin yazo kakarsu bata bari su Abdallah sunga hotunanba a waccan ranar, amma daga baya sai hotunan suka zo hannun Abdallah harya kaisu office Ι—ina. Hakan na nufin bayan na hannunsu akwai wasu kenan dama a wajensu komi? Zargi na biyar, Abdallah yafi kowa Ι—aukar zafi akan hotunan a gidan, duk da kuwa nasan Uncle da Umm sai sunfi kowa jin raΙ—aΙ—i da zafin hakan game da tilon Ζ΄arsu. Amma sai ya nuna zaΖ™ewa akan hakan harda kawomin abokinsa wai yay Arresting Ι—ina. Zargi na Ζ™arshe, miyasa a duk lokacin da akai tunanin Ζ™ulla aurensu sai wani dalili ya ruguza shi?......”

       “Please Yah Yoohan ya isa haka mana. Miyasa dukanin zarge-zargenka zai Ζ™are akan Yah Abdallah? Kana kishi da shi ba shike nufin komai ka yaya ka aza a kansaba”.

      Sosai zantukan Aymah suka zafi zuciyar Yoohan, dan gani yake matar tasa tana goyen bayan tsohon saurayin natane kawai. Sai dai kuma uffan baice akan hakanba, yama Ι—auke kansa daga gareta kawai.

     Karan farko little bee ta saki murmushi tana kallonsu. Sai kuma ta taΙ“e baki da faΙ—in, “Wannan faΙ—ane da ya shafeku a gidanku Mrs and Mr”.

    Hararta Yoohan yayi, dan dama tunba yauba yana jin haushin yanda take zaman yimasa kallon Ζ™urilla a fakaice. Yana nuna bai gani bane kawai saboda kunyar iyayenta.

     “A'a bar hararata malami, ni yanzu saina sassafa ka a gaban sahibar taka babu ruwana”.

       “Ashe kuwa mijinki ma zai sassafu a hannuna tare da wannan miskilar fuskar taki mai Ζ™inyima mutane dariya”.

      Harara itama little ta zuba masa tana tsuke fuska. “Oh kace dama kullum cikin takaicina kake bana maka murmushi, to Ζ™walelen kare da hantar kura”.

     Baki Yoohan Ι—in ya taΙ“e da Ι—auke kansa gefe yana cije lip. Dan saiya saita yarinyarnan akan layi kafin a gama case Ι—in nan. shi babu ruwansa da wani Ζ΄ar-sandancin ta ehe. (Kuji Ζ™arfin hali irin na Yoohan. Da alama mafa little bee Ι—in zata bashi shekara Ι—aya a duniya, amma wai yarinyaπŸ˜‚lol)

      Babu wanda drama Ι—intasu baisa dariyaba. Sai Jay da Bily basu dara Ι—inba a fili sai a zuciya. Sundaita kallonsu cike da nazarin suΙ“utar harsunan nasu. 

        Kai jay ya girgiza kawai yana katse little dake son Ζ™ara magana. “Kunga ku aje wannan shirmen naku sai kun fita can sai kuyi, idan kunso ku sassafa kawunan naku munada likita a kusa da zai duba ku. Yanzu dai Yoohan dole a yau Ι—in nan Nu'aymah ta wuce kano. Dan aikin nan banason ya shige satin nan bamu kammalashi ba. Maganar Abdallah kuwa na tabbatar jin Nu'aymah na Nigeria zaizo shima koda a Ι“oyen daya saba ne. Yanzu zan baza jami'ai da zasu fara bibiyar lamarin motsin kowa na gidan idan ya fito. Shima Nasir ina buΖ™atar a jawomin hankalinsa yazo kano. Babu sanya a aikinmu, duk wanda mukaci karo da rashin gaskiyarsa zamu kamasane mu tuhumesa kamar Rabi. Za kuma mu maida Rabi itama dan wayarta zata taimaka mana sosai wajen zaΖ™ulo abubuwa”.

     Cike da gamsuwa kowa ya amsa masa. Duk da kuwa Yoohan dai da alama baiso yin nisa da matarsaba. Amma ya fahimci hakan zai taimakesa gameda Ζ™udirin papa kuma a kanta. duk da kuwa a kanon ma wasu kurayen zata tarar. amma gara can akwai jami'ai masu sanya ido a lamarinta.


________★


     Koda su Aymah suka dawo gida bata ga Blessing ba. Hakama Madam Chioma da papa da alama basa gidan ma. Yara kawai suka tarar da Mama debora. Joy ta wuce makaranta, Miracle kuwa mama debora ke basu labarin wai ta haΙ—a kayanta ta koma gida.

     Ko a jikin Yoohan. Aymah kuwa yar dariyar shaΖ™iyanci tayi abinta ta wuce sama cike da tunanin ina Blessing ta shiga. Ɗakinta ta nufa direct, ta fara zame kayanta zuciyarta taf damuwa akan maganar hoton nan. Agogonta data cire ne ya faΙ—i Ζ™asa. ta Ι—an matsa baya tana dubawa ta tillesa da Ζ™afa yay Ζ™arΖ™ashin gado. Abin ya bata haushi, dan harta barsa akan yayta zama sai kuma taji tanason Ι—akko kayanta dan Yoohan ya batashi matsayin Ζ™yauta a ranar da suka cika shekara Ι—aya da aure. Fita tai ta Ι—akko mopping stick dan Yoohan bai shigoba har yanzu yanacan tare da mama debora. DurΖ™usawa tai gaban gadon batare da damuwa da cikin dake gabantaba saboda wauta. Ta kunna fitilar wayarta ta haska. Da Ζ™yar ta iya hango agogon ta saka mopping stick Ι—innan ta turosa a hankali. Sai da yazo dab da ita ta fahimci harda wani abu take jawowa. Hannu ta miΖ™a danta jawosu duka ta kasa. Dole ta sake zungurowa da iccen mofa Ι—in sannan suka fito. Jikinta har rawa yake wajen fara Ι—aukar envelope Ι—in ta buΙ—e. Tai wani irin waro ido na al'ajabi da mamaki. Batama san sanda ta Ζ™waΖ™ume hoton a Ζ™irjiba saboda murna. Jin an taΙ“a Ζ™ofar za'a buΙ—e tai saurin sakin hoton Ζ™asa, kafin Yoohan daya shigo ya Ζ™araso ta tura hoton ciki yanda bazai ganiba.

       Duk da ta masa alamun rashin gaskiya sai bai nuna yama fahimcetaba. Yay baya da fiΙ—in, “Oh ashe kina nan, bara na watsa ruwa saiki shirya kema zuwa biyar na yamma zamu wuce kano. Amma mi kikeyi ma a durΖ™ushe anan? Bayan kinsan bake kaΙ—ai bace?”.

     MiΖ™ewa tai tana nuna masa agogon data Ι—akko. “Kaga abinda na yadda nan na Ι—akko”.

     “Ki kulafa, dan na fahimci har yanzu wautanki na nan”.

    Baki ta kumbura da iska batare datace masa komaiba. Shima sai ya juya abinsa ya fice kawai ya barta batare daya sake maganaba. Sai dai bai rufe Ζ™ofaba. Da wannan damar ya samu zarafin laΙ“ewa kozaiga mitakeyi. Aiko tana ganin ya fita ta sake duΖ™awa ta Ι—akko hoton tana ambaton ‘Alhmdllh ya ALLAH. Da banga hoton nanba da bazan taΙ“a yafema duk wanda ya Ι—aukesaba. Dolene nasan wacece wannan mai kama da mijina Ι—in insha ALLAHU’.

     Dukkan maganganun Aymah a cikin kunnen Yoohan ne. Hakan yasa zancen tsaya masa a rai tare da son jin ganin hoton nan shima. Yayi kamar zai dawo sai kuma ya fasa. Akan idonsa ta maida hoton a Wadrobe. Tafiya yay Ι—akinsa tunda yaga inda ta ajiye. Sai dai kamar tasan yana kallonta. Yana barin wajen ta Ι—auke hoton ta sakashi a Ζ΄ar jikkar data haΙ—a kayan tafiya kano wai dan kar wani ya sake shigo ya sace mata. Tana shiga wanka Yoohan ya dawo duba hoton. Sai dai kuma komai kama da shi bai ganima. sai ma kamashi da Aymah taso yi ALLAH dai ya taimakesa ya gudu. 

      Haka suka kammala shirin wucewa kano mamakin atsabibancin Aymah na damun Yoohan, shi ganima yake ta gansa shiyyasa ta canjama hoton waje.

     Itako Aymah ranta fal baΖ™in cikin rashin ganin Blessing da Yoohan yasa tabar gidan har sai sun wuce dan bayason ta sanamar Nu'aymah abinda ya faru tsakaninsa da Momynsa.


*_KANO TA DABO_*


          Ƙarfe bakwai dai-dai jirgin su Aymah ya sauka a kano. Batare da sanin kowa daga ahalintaba har su baba malam. Sai da Yoohan yasa suka fara biyawa sukai shopping na tsarabar da zata kaimusu sannan suka wuce gidan.

        Ganin Aymah da Yoohan ya saka mai gadi buΙ—e musu gate mai taxi ya shiga har ciki. Nu'aymah zata fita da kwakwazo Yoohan ya riΖ™ota yana girgiza mata kai. “Please kibi a hankali, a ganinama ba gara ki shige babu wanda ya san da zuwanki ba da safe sai kiyi musu surprise”.

    Baki ta Ι—an tura gaba. Sai kuma tai saurin sakin dariya da cewa, “Yes Yah Yoohan kayi gaskiya kuma”.

     Murmushi yay mata da bata sumba a gefen kumatu. Daga haka suka fito a motar. Gidan shiru kowa yana a sashensa, hakan yasa Yoohan taya maigadi kaima Aymah kayanta bakin Ζ™ofa. Sannan ya turata ciki ya sulale ya koma taxi Ι—in suka fice. Dan hotel yake son guduwa kafin baba malam su fito massallaci su ritsashi.

     Umm na zaune a bedroom tana karatu da jiran lokacin sallar isha'i sai ji kawai tai an rungumeta. A firgice ta juyo dan harga ALLAH ta tsorata. Ta waro idanu sabida mamakin ganin wadda batayi zatoba. 

     “Nu'aymah wai kece da gaske?”.

Kukan murnar ganin Umm Ι—inta ta saki tana faΙ—in, “Nice Ummna, I miss you so much”.

       Rungumeta Umm tayi da Ζ™yau a jikinta itama Ζ™walla na cika mata idanu. Kai Ι—a dabanne gaskiya. Sanin ba ita kaΙ—ai bace yasa Umm tadata daga durΖ™uson da tayi a Ζ™asa ta zaunar da ita a bakin gado. Gaba Ι—aya Aymah sai kuma taji kunyar Umm ta mamayeta, sai ta duΖ™ar da kai Ζ™asa tana Ζ™ara lulluΙ“e cikinta da gyale. Dariya abin ya bama Umm sosai. Sai dai bataiba. Saima tambayarta tai ina mijin nata?. 

   Kan Aymah a Ζ™asa tace waje ta barsa ita dai suna kwaso kaya shi da maigadi. Jin haka yasa Umm fita ta leΖ™a. Sai dai babu Yoohan babu dalilinsa sai maigadi kawai dake shigo da kayan Ι—an barandar falonsu. Shine ke sanar mata Yoohan Ι—in ya juya tare da mai taxi akan da safe zai dawo insha ALLAH.

      Kai kawai Umm ta girgiza ta koma ciki, inda ta iske Aymah ta fito daga toilet da alama fitsari tayo. Cike da kulawa tace, “Kinji mijin naki ya tafi wai zai dawo da safe. Dama kunyi dashi hakan?”.

     “A'a wlhy Umm, ni kawai yace na shigo zaije massallaci ne”. Tai maganar cikin Ι“ata fuska. Murmushi kawai Umm tayi ita dai, tace, “To kiyi wanka kawai sai na samo miki abinda zakici ke tunda shi ya gudu. Cike da kunyar Umm Ι—in data aro ta yafama kanta ta amsa da to. Daga haka ta koma toilet Ι—in danyin wanka.


         Babu wanda Umm ta sanarma da zuwan Nu'aymah a gidan sai hajjo. Sai ko Muhammad daya dawo massalaci ya ganta a bazata. Baba malam ma sai da ya sallami Ι—alibansa ya shigo yaci karo da ita a falo zaune ita da Hajjo da Umm da Muhammad dake liΖ™e da ita.

     Tuni Nu'aymah ta manta da kunya, ta miΖ™e da sassarfa ta nufi Abbanta dake kallonta cike da kewa da so da Ζ™aunarta. Gabanta tai niyyar durΖ™usawa ya riΖ™ota yana faΙ—in, “A'a mamana keda ke fama da kanki. Irin wannan zuwa haka na bazata”.

    Hannunta yaja ya maida a kujera sannan shima ya zauna. Kanta a Ζ™asa ta shiga gaisheshi cike da kewa. Shiko yana amsawa da kulawa. Abakin Umm yaji cewar Yoohan ya gudu. Dariya kawai yayi dan ya fahimci kunya Yoohan Ι—in keji da alama.

        Haka sukayi murnarsu su huΙ—u kawai. Ganin dare ya farayi Hajjo taje sashenta danta kwanta. Aymah kuwa a Ι—akin Umm zata kwana tare da Umm Ι—inta data bar baba malam shi kaΙ—ai.

     Aiko maimakon barci sai suka buΙ—e sabon babin hira ita da Umm Ι—in, sai da suka kusan kai asuba sannan barcin ya kwashi Aymah, daga nan itama Umm tayi.


__________★


        Washe gari kam a bazata kowa yaga Nu'aymah a gidan. Kafin kace mi sun rikice da murna da hayaniya. Tun Aymah na Ζ™unshe-Ζ™unshen ciki harta saki jikinta ta shige cikin Ζ΄an uwanta anashan shafta. Zuwa tashin hantsi kuwa sai ga Hajarah tazo gidan, dan ita dama tasan da zuwan nata. Rungume juna sukai cike da farin ciki. Yanda suka nuna Ι—in har mamaki ya bama kowa. Dan gaba Ι—aya salon shaΖ™uwar Adawiya da Nu'aymah ne ya koma kan Hajarah a yanzu.


      A ranar da yamma suma Ζ΄an Abuja suka iso. Ganin Nu'aymah kuma ya matuΖ™ar basu mamaki dansu da suke Abujan ko a labari basusan da zuwan nataba. Har Momy ma sai da ta kasa haΖ™uri tai complain Ι—in cewar Yoohan bai Ζ™yautaba. Suna matsayin iyayen Nu'aymah amma yazo da ita har Abuja bai fara kaita canba sai dai suzo su ganta anan tsulum.

     Daga karshe dai Yoohan Ι—inne da yazo gidan ya kare kansa akan wannan tuhuma. Dan Aymah bata iya cewa komaiba tunda itama tunanin zuwa can Ι—in baizo mataba. ZumuΙ—inta kawai azo kano.

     Ya bama su baba malam haΖ™uri akan rashin tsayawarsa jiya. Acewarsa aikin gaggawa ne ya samesa shiyyasa bai tsayaba. Duk sun masa uziri akan haka. Sannan suka Ι—ora da godiya akan hidimarsa ga gidan marayunsu daketa Ζ™ara nunkuwa a koda yaushe. Akan bikin nanma kawai da za'ai ba Ζ™aramin hidima yayiba.


      Washe gari baΖ™i suka fara cika gidan, Ζ΄an katsina, Ζ΄an lagos da sauransu, kowa kuwa yana sake yaba yanda Aymah ta Ζ™ara girma da canjawa a cikin shekara Ι—aya kacal. Gashi daga gani ansan ta samu lafiya yanzu. Sai dai fatan ALLAH ya sa ta sauka lafiya kuma.

    Da yamma sukaje can orphanage akai walima, anan ta haΙ—u da sauran yayunta su Kubrah. Tayi mamakin ganin yanda Aunty Kubrah Ι—in dukta lalace. Harta kasa haΖ™uri ta tambayi aunty Hajarah. 

    Cike da damuwa Hajarah tace, “Humm Aymah ke dai ALLAH ya Ζ™yauta, zaman natane babu daΙ—i daga ita har mijin da kishiyar. Kwanaki ai kusan watanta biyu a Lagos wajen Abbah Musbahu. Sunyi faΙ—a ya daketa shine taje can”.

     Kasa magana aymah tayi saboda damuwa. Kodai babu komai Kubrah Ζ΄ar uwartace duk da a yauma ta nuna har yanzu ba sonta takeba.

    Duk wannan hidima da akeyi kuwa su Aymah zagaye suke da yaran Jay ta ko ina. Motsin kowa akan idonsu yake faruwa. Tun daga orphanage har cikin gidansu.


    Washe gari juma'a aka Ι—aura auren amare ashirin da takwas maza da mata. Kowa ya kalli su baba malam yasan suna cikin farin ciki. Sai dai ai fatan ALLAH ya basu ladan hidimarsu ga marayun ALLAH babu gajiyawa.

    An miΖ™a amare Ι—akunansu, daga haka baΖ™i suka fara raguwa sai na jiki kawai aka bari. Kamar yanda Jay ya samu tattaunawa da baba malam a ranar Ι—aurin aure a yau suka yanke hukunci bisa shirinsu. Duk da kuwa da Ζ™yar baba malam Ι—in ya yarda da buΖ™atar Yoohan, Jay, Omar Ι—in. Dan basu Ι“oye masa komaiba game da shirin nasu gudun kar a samu matsala.  

      Tun a yammacin ranar baba malam ya fara takalar Umm da batun mallakama Nu'aymah wasu kaddarorinsa dan yasan lallai mai musu laΙ“e na tare da su saboda tuna Nu'aymah tazo garin ya fahimci mai laΙ“en ya Ζ™ara Ζ™aimi wajen yimusu. Ta riga tasan shirinsu, itama sai ta biye masa. Sai dai zancen bai tsahoba suka barshi akan zasu Ζ™arasa da safe dan lokaci baba malam nada uziri..........✍




Post a Comment

0 Comments