TOP HAUSA NOVELS atOptions = { 'key' : '20e08520dad54dbf6d9e963271

Babu So page 70

 Chapter: 70 Share:

Report

BABU SO View: 283 Words: 2K

Chapter 70 70

........Wasa farin girki wai amarya da tuƙa

 

 tuwon tiya goma. Ashe rikici a waya tsakanin Mommy da Gwaggo Halima somin taɓi ne. Dan kuwa ba'a rufa awa guda cikakkiya ba sai ga Gwaggo Halima tazo gidan. Hakan yayi dai- dai da dawowar Daddy daga wajen aiki gidan shima. Yay sagade yana kallon Gwaggo

Halima data ƙaraso garesa tana huci. “Halima lafiya kuwa da magribar nan?”. “Inafa lafiya Yaya, Share! ya buɗe ƙwanji ya

shashsheka ma Fadwa mari amma saboda

son zuciya irin na matarka ta goya bayansa

saboda itace ta haifesa”.

Da mamaki sosai yace, “Mari fa dai? Ya

ALLAH mike damun Share! haka? Wannan ba

maganar nan bace shiga ciki nafara zuwa salla

kafin su Abubakar su dawo”.

A maimakon sashen Mommy ko Gwaggo da

da idan tazo gidan take shiga yau sai ta nufi sashen Mom.....

________________★

Rashin fitowarsa har aka kira sallar magrib yasaka Anaam kasa zaune ta kasa tsaye. Tana son zuwa dubashi tanajin tsoro. Gani take kamar itama ɗin marin nata zaiyi. Harga ALLAH tana matuƙar tsoron duka a rayuwarta. Koda wani taga ana duka firgicewa take. Ballema har abada bazata taɓa iya

 

 manta dukan dayay musu ba ita da Aysha. Da sauri ta juyo jin motsin buɗe ƙofa. Sukaima juna kallon cikin ido ita da shi, ita ta fara janye nata tana sauke ajiyar zuciya dajin shakkar

kallon fuskarsa dake a matuƙar tsuke. “Ki tashi kiyi salla”.

Ya faɗa a taƙaice da juyawa zai fita. Harya kama handle ɗin ƙofar zai fita ya tsaya cak, juyowa yay a hankali yana kallonta saboda ganin yanayinta. Sai dai baice komaiba ya juya ya fita. Numfashi ta saki a hankali da miƙewa ta shiga toilet domin ɗauro alwala.

Bai dawo gidan ba sai bayan sallar isha'i, kai tsaye kuma sashenta ya zarto. Tunda ta idar da salla ta kasa tashi a wajen, babu abinda ke mata kaikawo, haka kawai marin nan na ɗazun da yay ma Fadwa ya matuƙar tsaya mata a rai, duk da kuwa ƙararsa kawai taji bawai yinsa akan idonta ba. Harya ƙaraso gabanta bata san da shigowarsa ba, ya kai tsugunne gabanta, tare da ɗago haɓarta. Cikin idanunsa ta zuba raunannun nata da babu gilashi, bata ganinsa fes yanda ya kamata, amma hakan bai hanata tsaidasu a

tsakkiyar nasan ba... “Mike damunki?”.

Ƙoƙarin janye idanunta tai a cikin nasa ya hana hakan, taso kauda kanta gefe nanma ya

 

 hana, saita ƙara tsuƙe fuska da tura baki. A karon farko ya saki murmushi, tare da kai yatsansa ya ɗalli lips ɗin nata. “K wai baki san shekarunki sun girmi wannan taɓaran ba Autar mata?”.

Hanunsa ta ture zata tashi, yay saurin

damƙota yana dariya, jikinsa ta faɗa, dan

haka suka zube ƙasa gaba ɗayansu. Ƙafarsa

ɗaya ya kwanta, tare da jawota ya kwantar a

cinyarsa ita kuma. Ya tokarar da ɗayar ta

jingina kanta. “Nayi laifi ne wai?”.

Hanunsa dake kan cikinta ta kamo, ta saka

babban ɗan yatsan a bakinta ta ciza. “Wai wai

shiii! Wace mugunta ce muka wannan?”.

Dariya ta ƙyalƙyale da shi. “Noorie muguntafa

babu ƙyau sam sam”. Ka ɗan ta murguɗa

masa baki “Punishment ɗin mai yawo ne ai”. “Shi kuma punishment ɗin mai rashin kunya

fa? yaya ya kamata ya kasance?”. “Sai an binciko a littafin shara'a”.

Ta faɗa tana ƙoƙarin mikewa ta gudu. Riƙota yay yana ƙaramar dariya. “Sarkin wayo ai ni tuni na binciko. Yanzu kuma zan ƙaddamar da shi”.

“Wayyo yaya! Wayyo ni yunwafa nakeji, tun safe banci komai ba.”

“Nima ita nakeji ai”. Ya ƙare maganar da manne lips ɗinsu waje guda. Ko sau ɗaya batai ƙoƙarin hanashi ba, saima gudunmawa

 

 data fara bashi, burinta kawai taga ya huce

daga fushinsa. Cikin ƙanƙanin lokaci ta gama

hautsina masa kwanyar kansa, tun yana binta

a salon jarumta harya fita a hayyacinsa ya

ɗauka wata hanya da ban da karatun da ya

kasance mai girma ga Anaam. A yanzu kam ita

ya nema gigitawa, yayinda shi tuni ya fita

hayyacinsa har baya gane ita ɗinfa ƙanwarsa

ce. Sunyi matuƙar shagala a farantama

junansu ring ɗin wayarsa ya shammacesu. Da

ƙyar Anaam ta iya janye jikinta dake rawa

gefe. Shima nashin rawar yake fiyema da tata,

sai dai jarumtar ƴan mazan ta ɓoye haka, ya

rimtse ido da ƙarfi ya sake buɗewa saboda

ganin mai kiran. Ko'a turu a kwantosa bai isa

ɗaga wayar nan ba, dan babu makawa sai

Daddy ya gane halin da yake a ciki. Haka ya

barta harta tsinke wani kiran ya ƙara shigowa.

Yanzun ma kasa ɗagawar yay har saida ta

yanke, da ƙyar ya samu iya ɗan dai-daita

kansa bayan wasu mintuna sannan yay kiran

Daddyn Back.

Koda Daddy yaji muryarsa a shaƙe a zatonsa

duk ɓacin rai ne, dan kuwa yasan wanene Share! idan yay fushi. “Ka sameni a gida yanzun nan kai da Fadwa”. Bai jira cewarsaba ya yanke kiran. Shima ɗin baice komaiba ya koma kwance tare da mirginawa jikin Anaam

 

 data juya masa baya ya rungumota da ɗaura

kansa a gefen wuyanta yana shinshina, ga

sanyin tiles na ratsasu dan harya huda

sallayar tana iya jinsa a jikinta shima haka.. Jin saukar hanunsa a ƙirjinta tai saurin

riƙewa. “Yaya kirankafa Daddy yakeyi”. Iska ya ɗan hura mata cikin kunne da ture hanunta ya ɗaura a inda yay niyya tun farko. “Koratama kikeyi kenan?”.

“Eh mana, Daddy ba abin wasa bane ai,

umarninsa yana sama da muradanmu”. Sassanyan murmushi ya saki da sake

ƙanƙameta a jikinsa, a hankali ya furta *_Ina ƙaunarki da yawa_*”. Sosai tsigar jikinta ta yamutsa saboda yanda yay furucin a cikin wani irin wahalallen sauti. Taja numfashi mai kauri da cije gefen lips ɗinta sakamakon saukar kiss ɗinsa saman wuyanta. Bata iya ta ɗago ta kallesa ba harya fice daga ɗakin. Ta sauke sassanyar ajiyar zuciya da sake kananneɗe jikinta waje guda wani abu mai girma na tsikarar ƙasan zuciyarta....

A sashen Fadwa kan duk da yaji a ransa itace takai ƙararsa wajen su Daddy bai mata magana ba, umarnin kawai ta samesa a mota ya bata ya juya ya fita abinsa. Taja wasu mintuna kafin ta fito dan har ya kunna mota

 

 ma.

Tafiya suke amma kowanne fuskarsa na gefe,

ita tana kallon mutane shi kuma titi har suka iso. baiyi mamakin samun Gwaggo Halima ba, Fadwa ta nufeta ta rungumeta tana sakin kuka. Lallashinta ta shigayi tana shafa bayanta da fuskarta wai tana neman tabon marin. Abin sai ya girmi kan kowa amma babu wanda yay magana sai Mommy ce taja tsaki da taɓe baki. Share! kam zama yay ƙasa a tsakkiyar ƙafafun Abie da Abba. Kansa a ƙasa batare daya kalla kowa ba ya gaishesu. Haka kawai yakejin tsananin kunyar Abie da Mommynsa fiye da kowa a wajen.

Abba da yaga mulmular da Gwaggo Halima kema Fadwa na neman yin yawa ya magana a kausashe. “K Fadwa tashi ki zauna da ƙyau bama son shashanci”.

Tashin tai zaune, sai a sannan kuma take

gaidasu. Iya su mazan kawai suka amsa.

mommy da Gwaggo babu wanda ya tanka.

Gwaggo Halima tai ƙaramar ƙwafa da ayyana

(Zanyi maganinku) a zuciyarta.. Abie ne ya

buɗe taron da addu'a, kafin ya maida

hankalinsa ga Share! cikin serious matuƙa. “Al-Mustapha miya haɗaka da matarka

harda mari? Bayan wannan ba ɗabi'ar dakaga wani a cikinmu nayi a gidan nan bane?”.

 

 Ƙasa Share! ya ƙarayi da kansa, cikin

matuƙar girmamawa. “Kuyi haƙuri Abie nayi

kuskuren aikata hakan, sai dai saida na

umarceta ta tashi tabar inda nake dan bana

son yanke hukunci cikin fushi, amma taƙi yin

hakan har takai nayi marin”.

“Amma banda abinka Babana ai kai

babbane, da taƙi tashi sai kai ka tashi ka bata

waje tunda kasan baka iya controling kanka a

yanayin fushin. Su mata haƙuri ake dasu a

kowane hali, domin hangenka da nasu sam ba

ɗaya bane ba, sai dai sunada sauƙin sha'ani

kuma ba koda yaushe ake cizawa a kansu ba”. “Hakane Abie, insha ALLAHU hakan bazata

sake faruwa ba......”

“Tama sake faruwar mana. Wlhy da kaina zan

rama mata mara mutunci kawai. Kai yanzu

dan baka da kunya Share! har kanada hanun

ɗagawa ka daki Fadwa a gidanka?”. “Yaya Halima! Ya kamata kiyi shiru abi

komai a sannu”.

“Wane kuma sannu Abubakar, bayan kanaji

yana lallaɓashi saboda ba ƴarsa aka mara ba”. Murmushi Abie yay da girgiza kansa. Cikin

dattako da nutsuwar da kowa ya sansa da ita ya fuskanci Gwaggo Halima. “Ba haka bane Yaya Halima. Da Share! da Fadwa da Anaam duka su ɗin ƴaƴanmu ne, bazamu taɓa sakaci da cutuwar ɗayansu ba ai. Da kinyi haƙuri zan

 

 kai inda kike buƙata nima ai”.

Baki ta taɓe da juya kai gefe. Nanma

Murmushin Abie ya saki kawai ya sake maida

hankali kan Share! da ransa ya ɓaci. “Babana

ina jinka miya haɗaku takai ga mari?”. “Ban taɓa fatan dan na samu matsala da

wata a cikinsu sai munzo gabanku ba. Amma

tunda ita tafi zaɓar hakan a koda yaushe fine.

Fita nai a gida tun safe ina wajen matsalar can

data taso a company, na dawo kawai na samu

ta cikamin sashe da ƙawayenta wai suna min

gyara. A yanda suke komai kai tsaye ya

tabbatar min ba yau ce rana ta farkon hakan

ba. Korarsu kawai nai na ƙyaleta domin ita

tasan bana son yanke hukunci cikin fushi,

amma saita biyoni bayan nace ta ƙyaleni a

yunƙurin farko da tai. Taya zata kawomin

wasu ƴan iska sashe, ta san adadin abubuwan

dana ajiye masu muhimmanci a ciki? Ko

bamma ajiye komaiba ita bazatai tunani da

hankalinta rashin dacewar kai wani can ɗin”. “Inafa zata san abinda ya dace tunda a nuna

mata barbaɗa magani shine kawai zaman aure”.

A harzuƙe Gwaggo Halima ta dubi Mommy

mai maganar. “Nafi wlhy ki iya bakinki domin

zai kaiki ya baroki allura ta tono galma”.

“Yo ta tono mana dan ubanta, abu mai sauƙi

 

 bayan ta tono ita galmar ta turbuɗata cikin

ƙansa yanda ko mayen ƙarfe ƙaryarsa sake

ganinta”.

Aifa nan take falon ya harmutse da hayaniya

tsakanin Mommy da Gwaggo Halima. Mamaki al'ajab sukabi suka sanya Share! cikin madaukakin imani. Yau kuma aminai biyune kema juna tujara haka akan abinda suke ganin shine mafi ƙololuwar alkairi a garesu idan suka ƙulla. Kai duniya ina zaki kaimu ne haka?. Da ƙyar su Daddy suka samu sukai shiru. Gwaggo kam tayi kamar bata a falon tai muƙutt da cuno baki gaba ita a dole takai maƙurar ɓacin ran abinda su Mommyn ke aikatawa. Acan ƙasan ranta kuwa dariya taketa kwasa. Yanzu kam Abba ne ya amshe da zancen yana mai fuskantar Fadwa.

“K shashashar inace da zaki bama ƙawaye damar shiga ɗakin mijinki? Haka kikaga iyayenki na mana? Wace irin mace ce ke da baki kishin mijinki? Ai wannan jama kanki rainine ma wajen su ƙawayen naki da shi kansa mijinkin. To saurara ki jini, daga rana mai kama irin tayau, hakan ta sake faruwa ni da kaina zan hukuntaki sannan shima nasa ya hukuntaki tunda koba aure tsakaninku

Yayanki ne.. Kinaji na da ƙyau?”.

Hawaye ta ta share tana jinjina kanta. “Zan

 

 kiyaye Abba insha ALLAHU. Amma Abba dama fa haushina yakeji, dan dama a kwanakin nan banda wulakantani babu abinda yakeyi saboda ya ƙara aure. Baya ganin kowa a gidan sai ita ƴar gwal.....”

“Shiyyasa kuka dage boka da matsubbata ke

da uwarki domin sabautamin ɗa. Su Malika na

kawo miki barbaɗe-barbaɗe kina faman zuba

masa dare da rana. To wlhy babu lallai babu

dole tun kan ai nisa sai ya datse igiyar auren

tunda bake kaɗaice mace ba a duniya......” “Dan ALLAH Nafisa idan baki sakashi ya

datse igiyar aurensu ba baki cika uwarsa ba,

kuma shi din bai haifuba a cikinki...” “Haka kikace?”.

“Eh na faɗa. bandama ƙaddara mi Fadwa

zatai da wani Share! can. Ko dama kun ƙulla

a haɗasu aure dan ku dinga maidamin yarinya

baiwarku”.

“Hahaha yo baiwa kuma ta nawa Halima.

Sai dai wata kuma dan ita kam ta riga ta gama zama labari”.

Ƙara hargitsewa falon yay, da ƙyar yanzu kam Abie da 

Abba suka sakasu yin shiru, dan Daddy dai ya mugun shaƙa zuciyarsa har wani zallo takeyi, gata tokare a maƙoshinsa kamar yay amanta ya huta.............

  End of book




Post a Comment

0 Comments