TOP HAUSA NOVELS atOptions = { 'key' : '20e08520dad54dbf6d9e963271

Makauniyar soyayyah page 63-64

*STORY & WRITTEN*



         *BY*



*MARYAM AHMAD PAKI*





*🌈KAINUWA WRITERS ASSOCIATION*🤝🏽




*INA SANE DAKU*


_Masoya littafin SILAR KAYAN SALLAH, ina k’ara ba da ku hak’uri akan shirun da kuka ji ni na kwana biyu na rashin posting da wuri, hakan ya faru ne na yadda abubuwa suka yi min yawa, insha Allah zan muku typing d’in shi_.



*QUESTION OF THE DAY*


_Su wa K’urayshawa suka aika lokacin yana mushuriki a lokacin Sulhun Hudaibiyya, da yaga irin son da sahabbai suke ma (S.A.W) ya koma zuwa ga k’urayshawan yace musu ‘Ya ku mutane na, Wallahi hakika na bak’unci sarakuna, na bak’unci Kaisar da Kisra da Najjashi, wallahi ban ga wani sarki shugaba daya da mutanen sa suke girmama shi kamar yadda sahabban Muhammad suke yi ga Muhammadu ba_.




63-64


Yana shiga ya fara ma Anty Jiddah fad’a akan me yasa za ta bar ni in fita gurin Dr, bayan tasan an kusa biki na.


Tabbatar mishi tayi da ba ta san shine yazo guri na ba, da ba ta barni na fita ba.


A lokacin na shigo falon da sallama ta.

Anty Jiddah ce ta amsa min ciki-ciki, da alama ita ma ranta a ‘bace yake.

Yaya Aminu kuwa sai watso min banzan kallo yake yi.


Hakan yasa jiki na yayi sanyi duk da ban san me nayi ba nayi k’arfin halin yi mishi sannu da gida.


Maimakon ya amsa min sai ma nufo ni da yayi.


Ban yi tunanin wani abu zai min ba shi yasa ban gudu ba.


"Daga ina kike" yaya Aminu ya tambaye ni cikin d’aure fuska.


"Abokin yaya Faruk ne yazo, shine ya turo shi guri na ya ba ni sak’o ya kawo min".


Wani irin kallo ya watsa min mai nuna alamar tambaya kana ya ce "Ina sak’on da ya bayar".


Cikin daburce wa na ce "ya… ce… zai…dawo…anjima…yana…sauri…ne…ya …bar…shi…a…".


Ban gama fad’a mai abin da zan ce ya d’auke ni da wani lafiyayyen mari.


Cikin fad’a ya ce "Uban wa za ki raina ma hankali, kina sha ban gane wannan Dr bane, za ki ce min abokin Faruk ne, ban fad’a miki ki rabu dashi kina da wanda zaki aura ba, yau ba gobe ba su Abbu za su ji wannan maganar, na gaji da rufa miki asiri, dama Faruk nasan hak’uri yake yi dake akan abin da kike mai saboda wannan Dr, tun da shi so ya rufe mai ido ba zai iya hukunta ki ba, yau za ki ji a jikin ki, kije ki d’akko jakar ki mu tafi gida".


Kuka na fara yi ina bashi hak’uri akan yayi hak’uri kar ya fad’a ma su Abbu amma bai saurare ni ba.


Ita kanta Anty Jiddah na ba ta haushi, amma ganin kukan da nake yi ne ya karyar mata da zuciya yasa ta fara ba yaya Aminu hak’uri akan ya min hak’uri, ko sauraren ta bai yi ba.


Ganin ban da alamar tashi in d’akko kaya na yasa ya janyo hannu na ya kaini mota ya kulle ya shiga side d’in driver ya ja muka tafi.


Muna zuwa gida ma ya rik’o hannu na kamar wacce ake ma jagora.

Main parlour muka nufa yana ci gaba da min fad’a, yana d’aura laifin ga Dr, wanda ya ce in dai suka had’u sai ya ci mishi mutunci tun da shi yake hure min kunne.


Jin yadda yake aibata Sadik yasa nayi k’arfin halin duk da tsoron dake raina nace Yaya Aminu ka daina ganin laifin Dr Sadik da ni, Allah ne ya jarrabe mu da son junan mu, abu ne mai wuya a ce lokaci guda in cire son shi…".


Maganganun da yaji ina fad’a mai ne yasa shi harzuk’owa ya ficiko AV wire dake manne a jikin DVD ya fara zuga min ita a jiki na.


Dukan da yake min ne yasa na sa kururuwa ina ta kuka, jin kuka na yasa Ummu da Abbu suka fito daga side d’in su suka nufo falon, shi kanshi yaya Khalil yana cikin d’akin shi yana jiyo ihu na, shima a lokaci d’aya suka shigo falon don ganin me yake faruwa.


Yaya Khalil kuwa tun da ya ga dukan da yaya Aminu yake min ya zargi akwai abin da nayi wanda yasa na tunzura yaya Aminu yake min irin wannan dukan, shi yasa bai samu k’arfin zuwa ya cece ni duk kuwa da tausayin da na bashi.


Dukan da suka ga yana min ne yasa Ummu ta daka mishi tsawa.


"Aminu miye haka, wani irin laifi ta maka haka kake mata wannan dukan, so kake yi ka ji mata ciwo".


Jin hakan da yaya Aminu yaji Ummu tayi magana yasa ya dakatar da dukan da yake min ya wurgar da AV d’in, sai faman huci yake yi.


Sai a lokacin Abbu yayi magana ya ce "Ku same ni a falo na".


Gaba d’ayan mu muka nufi falon Abbu, jiki na kuwa ba inda bai min rad’ad’i.


Abbu ne ya kalli yaya Aminu ya ce "Aminu ban ji dad’in irin dukan da kayi ma Fatima ba kasancewar ta mace, kai babba ne, ka fi ta hankali".


Cikin ladabi yaya Aminu ya ce "Kayi hak’uri Abbu, Ummu kema ki yi hak’uri".


Abbu ne ya ce "Ba komai Aminu, dama ba laifi kayi ba, sai dai ina son kasan ita mace a hankali ake bin ta, yanzu fad’a min me tayi".


Yaya Aminu ne ya nisa kana ya ce "Abbu akwai abin da yake faruwa wanda ban fad’a muku ba, ina sha matsalar k’arama ce da ni kaina zan iya shawo kan matsalar ba tare da na sanar daku ba, sai a yanzu nake ganin matsalar ta fi k’arfi na da ya zama dole in sanar daku ita…".


Ummu ce ta katse shi da cewa "Wai wace matsala ce daka ke ta mana kwana-kwana, ka fito ka fad’a mana".


Tun da naji yaya Aminu da gaske ya keyi fad’a musu zai yi, jiki na ya k’ara yin sanyi, ban san yadda za su d’auki maganar a gun su ba, hukuncin da za su yanke min shi yafi tsaya min a rai.


Nan yaya Aminu ya gyara zama ya kwashe duk iya abin da ya sani tsakani na da yaya Faruk da kuma Dr Sadik, da abin da yanzu na fad’a mishi akan Dr.


Shiru d’akin ya d’auka kamar ba kowa a ciki, kowa da irin abin da yake sak’awa a zuciyar sa game dani.


Ni kuwa ina can a ra’be kamar wacce tayi ma sarki k’arya, ba abin da nake yi sai aikin k’ifta idanuwa da nake yi.


Abbu ne ya ja gauron numfashi kafin ya juyo da kallon shi zuwa guri ni ya ce "Fatima, abin da Aminu ya fad’a min gaskiya ne?".


Nasan ko wani abu nake sha bazan kalli idon Abbu in ce mai bana son yaya Faruk ba, na za’bi ba re akan shi, nasan abin da zai min sai ya fi na kowa muni ganin yadda ya d’auki yaya Faruk kamar yaya Aminu, shiru na a wannan lokacin sai ya fi min amfani.


Ummu ce ta daka min tsawa ta ce "Ba dake ake magana ba Fatima kika yi wa mutane shiru, ko mu ma za ki fara gwada mana fitsarar da kika koya ne".


Har yanzu na kasa bud’e baki na in yi magana sai hawaye da ya fara zuba a fuska ta.


Tun san da abin nan ya faru, yaya Khalil bai yi magana ba sai bi na yake da ido.


Abbu ne ya ci gaba da cewa "Fatima ke nake saurare".


Ba ni da wata sauran dabara da ya wuce in fito in fad’a ma Abbu da Ummu abin da yake raina, watak’ila su duba uzuri na su fuskance ni su bar ni da wanda nake so, da wannan na samu karsashin yin magana.


"Abbu kayi hak’uri, nima ba laifi na ba ne, nayi duk wani k’ok’ari akan in sa son yaya Faruk a raina don in faranta muku dashi kan shi yaya Faruk da ya nuna min soyayyar shi har ya zuwa yanzu da ake maganar bikin mu, amma zuciya ta tak’i amsar tayin siyayyar sa, zuciya ta tayi nisa a son Dr Sadik, Abbu da Ummu dan Allah ku tausaya min ku fahimtar da yaya Faruk, nasan zai fahimce ku…" Na k’arasa maganar cikin kuka.


Abbu ne ya kalle ni ya ce "Ina sauraren ki Fatima, yanzu me kike so in miki".


Ba tare da jin tsoron hukuncin da zai biyo daga baya ba na ce "Abbu so nake yi ka ba yaya Faruk hak’uri ya hak’uri ya hak’ura da aure na, Dr Sadik na ke so".


Kowa a d’akin ni yake bi da kallo, a yadda na fahimci kallon da suke min yana nuni da ban san abin da nake yi ba.


Ummu kuwa da ‘bacin ranta ya kasa ‘boyuwa tashi tayi tazo ta tsinka min kyawawan mari lafiyayyu guda biyu, wanda hakan ya haddasa min ganin taurari a fuska ta.


Rabon da Ummu ta kai hannu ta a jikina na manta, bare har ya kai ga ta mare ni.


Yau nasan ran Ummu ya ‘baci kasancewar ta mai hak’uri da sanyin hali, nasan za ta iya min abin da yafi haka in dai akan yaya Faruk ne.


Cike da ‘bacin rai ta ce "In da nasan akan haka Aminu ya dake ki, da ko fito wa bazan yi ba har in mishi magana, Fatima ban ta’ba tunanin hakan daga gare ki ba, ki d’auka wannan maganganun da kike fad’a kamar guguwa ce dan in ta kad’a ta tafi ta riga ta tafi kenan, ci gaba da wannan maganganun zai iya sa ki fuskanci mummunan hukunci daga gare ni, ki kiyaye ni".


Abbu ne ya katse ta daga fad’an da take min "Hajiya k’yale ta ki zo ki zauna".


Ba ta musa mishi ba ta dawo gurin zamanta ta zauna ba tare da ta k’ara cewa wani abu ba.


Kowa idan ka duba yanayin da yake ciki ransu a ‘bace yake.


Abbu ne ya saki murmushin takaici wanda bai kai ciki ba ya ce "Na ji bayanin ki Fatima, ina so ki saurare abin da zan fad’a miki da kyau, wannan maganganun da kike fad’a min wai ba kya son Faruk kina da wanda kike so na d’auke shi shirme ne, Fatima abin da kike so a miki ba mai yiwuwa ba ne, ba na magana biyu, ba ni na had’a ki da Faruk ba bare ki ce za a miki auran dole, hasalima ba ki ta’ba nuna mana ba kya son shi ba sai yanzu da kika ga komai yazo k’arshe sannan za ki bijiro da wata magana mara amfani, ina so ki sani ko da basaid amincewar ki sai kin auri Faruk, ina so ki sani ba ki da wani miji bayan Faruk, zan iya nemar ma Faruk aure a ko ina ne bare ke mallakina, ba ki isa ki lalata mana zumuncin dake tsakani na da d’an uwana da kowa yake sha’awar mu ba wanda tun kan a san za a haife ki muke yin shi, sai ke a rana d’aya da kike so ki wargaza mana shi a lokaci guda, wannan su ne maganganun da zan fad’a miki, shawara ta rage naki, abu na k’arshe da zan fad’a miki shine ban yarda ki k’ara fita daga gidan nan ba sai in ni na umarce ki" Yana gama fad’ar haka ya mik’e ya shiga cikin bedroom d’in shi.


Wani irin kuka na fashe dashi, a lokacin zuciya ta wani irin zafi take min da irin hukuncin da Abbu ya yanke a kaina.


Ummu ce ta d’aura da cewa "Fatima kin bani mamaki, ina ganin ki yarinya mai hankali, ashe ban sani ba kin riga kin canza da yadda na sanki, ki rasa wanda zaki yi ma butulci sai Faruk wanda yake dazumunci da ganin girman manya, za ki nuna kin fifita wani a kanshi, tun yaushe Abbun ki ya raba ki da wannan Dr yace ki bashi hak’uri kina da wanda za ki aura, shine ki ke so ki nuna mishi bai isa dake ba, ki ka ci gaba da soyayya dashi, ko a fuska ki ka nuna ma Faruk wani abu sai nayi mugun sa’ba miki".


 Tana gama fad’ar haka ta bar gurin.


Yaya Aminu mik’ewa yayi ya tafi, ko kallon in da nake bai yi ba.


Ya rage daga ni sai yaya Khalil a falon, ina tunanin zai ce min wani abu, ga mamaki na bai ce min komai ba, a fuskar shi na gane shima bai ji dad’in abin da nayi ba.


Tashi yayi ya koma side d’in shi, a raina ina k’ara mamakin canzawar yaya Khalil, in da a da ne yaga an min wannan dukan a gaban shi, ya dinga bani hak’uri kenan, amma yanzu ko magana bai yi min bare in sa ran zai ba ni hak’uri.


Ganin ni kad’ai nayi saura yasa na tashi na tafi d’aki na dan in gasa jiki na, saboda ko ina a jiki na ba in da bai min ciwo.


Tun daga wannan lokacin na rage fito wa falo, ba kuma wanda ya damu da fitowar tawa tun da fushi suke yi dani.


Yaya Faruk na kira na a waya, sai dai hirar tamu ba ta yin wani armashi, saboda komai ya min magana sai na gadama nake bashi amsa, da ya tambaye ni dame-dame nake so ya sa min a akwati, k’in fad’a nayi, da ya matsa min ne nace duk abin da ranshi yake so, size d’ina kawai na fad’a mai, ba yadda bai yi ba akan mu tattauna akan bik’in, amma nak’i, ganin hakan da nake mai ne yasa yayi fushi ya rage kira na sai ya kama yake kira na.



Nana Khadijah kuwa yanzu shak’uwar su sai k’ara gaba take yi da yaya Faruk, yanzu sukan zauna da ita yana jan ta hira, yawancin hirar tasu yana fad’a mata yadda yake so na, hakan yana ba ta mamaki ganin yaya Faruk miskili wanda bai damu da kula mata ba a yanda ta ji yaya Mus’ab na yawan fad’a sai take mamakin yadda yake fad’a mata yanda yake so na, lallai ta tabbatar da son da yake min ba k’aramin so ba ne, ba ta san bikin yaya Faruk ya kusa ba, sai da taje gidan su yaya Mus’ab ne taji suna maganar bikin da Anty Maryam, tun san da taji maganar bikin ta rasa yadda za ta fassara yadda take ji a ranta, ganin abin zai dame ta yasa ta watsar da tunanin da yake so ya zamar mata matsala.


Lokacin da suka had’u da yaya Faruk ne take mishi fatan alkhairi a auran da zai yi, ta kuma mishi k’orafin me yasa bai fad’a mata bikin shi ya kusa ba, ya bata hak’uri akan mantawa yayi, shi kanshi yaya Faruk yana ganin mutuncin Nana Khadija saboda yadda ta d’auke shi kamar yayan ta, sannan natsuwar ta da kamun kanta da rashin hayaniyar ta na d’aya daga cikin abin da yasa yake ganin mutuncin ta, shima sai yake jin ta kamar k’anwar shi, ko su yaya Mus’ab da Anty Maryam suna mamakin yadda yake zama yana hira da ita duk da dukan su ba ma’abota surutu ba ne.



Yau ina zaune a d’aki na kamar yadda na sabar ma kaina, yaya Khalil ne ya shigo da sallamar shi.


Amsa mishi nayi na kau da fuska, saboda shima yanzu ya shiga cikin sahun wanda ba su damu dani ba.


Murmushi kawai yayi ganin yadda nayi.


"Fatima zuwa nayi in baki shawara a matsayina na d’an uwanki, wanda ya damu da damuwar ki, wanda kuma bai son ki sa kan ki a wani hali".


Jin ban ce komai ba yasa yaci gaba da cewa "Fatima, abubuwan da kike yi sam bai kamata ba a matsayin ki na ‘ya mace, da nayi niyyar in zuba miki ido kamar yadda kike so a k’yale ki, sai na ga bazan iya ba, yanzu har kin manta sharad’in da na gindaya miki in dai kina so mu shirya shine ki so yaya Faruk, ko da yake na lura dake za ki iya ‘bata wa da kowa in dai akan Dr ne, tun da yanzu gashi kin za’bi ki zauna a d’aki ke kad’ai kina ganin in kika yi hakan za a gane kina fushi, to bari in fad’a miki ki ji, ki hak’ura da Dr Sadik tun da su Abbu da Ummu sun nuna sun fi son ki auri d’an uwan ki, ni da yaya Aminu ma mun fi son ki auri yaya Faruk d’in, me zai sa ba za ki duban hakan shi zai fi miki zama alkhairi tun da kowa shi yake so ki aura, duk abin da kika ga yawan mutane nak’i to ya kamata ka hak’ura dashi duk kuwa da son da kake mishi, zai iya yiwuwa abin ba alkhairi ba ne a gurin ka, ko da yake ke kin yi nisa a makauniyar soyayyar da ba za ki fahimci hakan ba, wannan shawarar ina baki ita ne a matsayina na yayan ki, nasan komin daren dad’e wa zaki tuna da shawarar da na baki, nasan a yanzu ba lallai ki d’auki hakan da mahimmanci ba, ki zauna ki yi karatun ta natsu ko dan gudun ‘bacin ran iyayen mu da kuma zumuncin mu da zaki ja ya samu rauni ta dalilin ki, ina fatan za ki yi amfani da shawarar da na baki, na barki lafiya" yana gama fad’ar haka ya bar d’akin ba tare da yaji nawa jawabin ba.


Tabbas nasan duk abin da yaya Khalil ya fad’a gaskiya ne, ni kaina da zan iya amfani da shawarar da suke bani da na bi, sai dai matsalar zuciyata da ta riga ta daina d’aukar shawarar kowa a dalilin son Dr.


Kasancewar takunkumin da Abbu yasa min na hana ni fita, ba k’aramin takura min yayi ba, yanzu ba ni da halin had’uwa da Dr sai dai a waya, na fad’a mishi duk halin da ake ciki, ya nuna min da kar in damu da duk abin da za’a min in dai zamu cin ma burin mu.


Son da nake ma Sadik bai sa na hango illar abin da nake yi ba, ni ko da yaushe shine in kasance da son Dr a raina.


Da wannan nake samun k’arfin gwiwa amma a maganar gaskiya halin da ‘yan gidan mu ke nuna min a yanzu na damu na, dan duk wanda yasan ni a da yasan na canza dan har wata ‘yar rama nayi.


Duk wata kulawa da Ummu da su Abbu har ma da yaya Khalil suke nuna min a da, yanzu babu wannan.


Gashi yanzu shirin mu da Anisa yaja baya, ba wani cika zuwa tayi ba tun san da tazo gidan mu muka samu sa’bani da ita akan maganar yaya Faruk, duk da ina kewar ta kasancewar yadda muka shak’u tun muna yara, hakan ba zai sa in rabu da burin zuciya ta dan in faranta mata, muna waya da ita jefi-jefi.



Ranaku na ta wuce wa inda bikin mu ya kasance yau saura sati uku, a ranar kuma aka kawo akwatina Set biyu aka kawo, dana Abbu da ya had’a da na yaya Faruk, kowane set akwatuna uku ne da kit, haka ma na yaya Faruk, kowane set da kalar sa, kaya ne na gani na fad’a, akwatunan kad’ai abin kallo ne bare aje ga kayan dake ciki, baki ba zai iya fasalta kayan da ke ciki ba, sai dai gani da ido.


A ranar ne na samu na rok’i Abbu akan ya barni in je gidan su Halima, jin inda zani yasa Abbu yasa yaya Khalil ya kaini ya d’akko ni.


Ko da muka je gidan su Halima, da k’yar yaya Khalil na rok’e shi akan yaje ya dawo, da cewa yayi sai ya jira ni.


Ina shiga muka gaisa da Maman su kana muka wuce d’akin ta.


Hira muka dasa ta yaushe gamo, mai aikin su ce ta kawo min kayan abin sha da abinci.


Ko kallon abincin ban yi ba saboda a halin damuwar da nake ciki, nafi buk’atar mai kwantar min da hankali akan wani abinci.


Drinks kad’ai na d’auka na sha.


Halima ce ta matsa min da tambayar dalilin ramar da nayi, ganin abokin kuka ake fad’a ma mutuwa yasa na kwashe komai na fad’a mata har ya zuwa yanzu halin da nake ciki.


Halima ce ta numfasa kana ta ce "Gaskiya Fatima kina cikin wani hali, dole ne a tausaya ma halin da kike ciki, sai dai gaskiya ni ban goyi bayan ki akan ki tafi wani gurin ba, gwara ki ta ba su Abbu hak’uri akan su baki wanda kike so, ki ci gaba da nuna musu yadda kike jin Dr a ranki da halin da za ki iya shiga idan bashi kika aura ba, nasan za su fahimce ki, ko kuma kije ki samu Dadin su yaya Faruk d’in ki mishi bayani, nasan shi zai son farin cikin d’an shi dan ba zai so d’an shi ya auri wacce ba ta son shi, haka kuma ba zai so zumuncin su ya samu rauni saboda wannan auren ba".


Girgiza mata kai nayi kana na ce "Halima ba wata dubarar da zan bi wadda ta fi min sauk’i shine in yi tafiyar, gurin da zani ba mai cutar wa bane, da kunya in tunkari Dadin su yaya Faruk da wannan maganar, gaskiya ba zan iya ba, Dadi da Momi sun nuna min soyayya, su Abbu ba za su saurare ni ba, dan ba ki ga yadda suka nuna ‘bacin ransu akan maganar nan ba ne, yaya Faruk ma ba zan iya tunkarar shi da wannan maganar ba dan ba zan so ya shiga wani hali sabo dani ba, kawai dai ki taya ni da addu’a, Allah yasa komai yazo cikin sauk’i".


Cikin tausayawa Halima tace "Amin dai Fatima, insha Allahu zan dinga sa ki a addu’a ta".


Da k’yar Halima ta tilasta min na ci abincin da mai aikin su ta kawo min, ba laifi na ci abincin dan na dad’e ban ci abinci mai yawa irin shi ba.


Haka Halima taci gaba da bani shawarwari, hak’ik’a na ji dad’in shawarwarin da ta bani.


Kiran yaya Khalil ne ya katse mana hirar da muke yi, sanar da ni yayi ya na k’ofar gida yana jira ma, sallama muka yi da ita, mun yi da ita akan sai mun had’u da ita ta waya.


Ko da muka koma gida ban nuna musu komai ba, Falo nazo aka yi ta hira dani.


A fuskar su kad’ai da na kalla na gane sun yi farin ciki da yadda na sake, da alama na hak’ura da k’udiri na.


Jin dad’in hakan ne yasa bayan na koma d’aki Ummu ta shigo ta k’ara min nasiha tare da bani magungunan da za su gyara ni.


Saboda ban son tayi fushi dani yasa na amshi magungunan nashi ba wai magungunan na da dad’i ba, hasalima wasu da nashi ji nake yi kamar in yi amai.


Abbu ma ya kira ni ya k’ara min nasiha, na nunar mishi da ba komai na hak’ura.


San da Ummu ta ce in zo in ga kayan akwati ban mata musu ba, dan bana son ta zargi ko har yanzu ban hak’ura ba, gaskiya iya had’uwa akwatunan nan ya burge ni, kai da gani kasan mai tsada ne, kayan ciki kuwa nasan kud’i yayi kuka, nasan ko Dadi da Momi kad’ai Allah kad’ai yasan kayan nawa suka zuba a ciki, bare har da na yaya Faruk da yace zai k’ara min.


Ko ni idan na ce kayan bai min ba na fad’i son raina ne, gaskiya sun yi bajinta a akwatinan da aka kawo.


Haka Ummu tasa mai gyaran jiki ta zo ta fara min gyaran jiki.


Anisa ma tazo dan mu tattauna akan yadda bikin zai gudana, na sanar da ita da cewa ba wani event da zanyi sai walima, da ta matsa min ne na ce na bar mata wuk’a da nama, ta tsara duk yadda take so bikin ya gudana, hakan da na ce mata taji dad’i.



Yau bikin mu ya rage saura kwana goma, sai shirye-shirye ake yi ko ta ina kasancewar abin na gida ne, a yau ne kuma muka shirya tafiyar da zanyi ni da Dr.


Kayana na h’ada a irin jakar matafiya, na d’ebi abin da zan buk’ata.


Sai da fito falo na ga ba kowa, dan gudun a sami matsala sai da na je d’akin Ummu na ga tana bacci, dama nasan Iya Talatu ba ta nan Ummu ta aike ta, haka na k’ara fita parking space na ga ba motar yaya Khalil, daman nasan Abbu baya nan.


Da wannan na samu k’arfin gwiwa na d’akko jaka ta na fito cikin sand’a dan kar wani yaji takun tafiya ta.


Cikin sa’a san da nazo bakin gate ba kowa, dan haka da sauri na bud’e k’ofar a hankali na fita.


San da na fito daga gidan ne naji wasu hawaye sun zubo min masu zafi, zuciya ta na k’wa’ba ta akan abin da zan aikata ba mai kyau ba ne, zuciya ta na umarta ta da na koma, abin da nake shirin aikata wa zai iya janyo min fushi a gurin iyaye na da ‘yan uwa na, idan na tuna da in da za ni bai da wani matsala, zan dawo idan lokacin bikin ya wuce, da wannan na samu k’arfin gwiwar tafiya.


Can bayan layin mu maka had’u da Dr kasancewar dashi zamu yi tafiyar.


Ina zuwa ya bud’e min mota na shiga muka d’au hanyar barin garin. 




Post a Comment

0 Comments