TOP HAUSA NOVELS atOptions = { 'key' : '20e08520dad54dbf6d9e963271

Gimbiya hakima page 73-74

 πŸ‘ΈπŸ»πŸ‘ΈπŸ»πŸ‘ΈπŸ»πŸ‘ΈπŸ»πŸ‘ΈπŸ»πŸ‘ΈπŸ»πŸ‘ΈπŸ»πŸ‘ΈπŸ»πŸ‘ΈπŸ»

         *GIMBIYA HAKIMA* 

πŸ‘ΈπŸ»πŸ‘ΈπŸ»πŸ‘ΈπŸ»πŸ‘ΈπŸ»πŸ‘ΈπŸ»πŸ‘ΈπŸ»πŸ‘ΈπŸ»πŸ‘ΈπŸ»πŸ‘ΈπŸ»




 *🌎MANAZARTA* 

 *WRITERS ASSOCIATION* πŸ“šπŸ–Š️


     *M. W. A* 


 ```Kungiya d'aya tamkar da dubu. Masu Nazari da Aiki da Ilimi, Burin 'kungiyar a ko da yaushe shine ta fad'akar ta ta kuma Nishad'antar da masoyan ta. πŸ€™πŸ»``` 

https://www.facebook.com/107980080946102?referrer=whatsa 

________________________________




  _STORY AND WRITING_ _BY_ 


    _Jameelah jameey πŸ–‹_ 


    *(Yar mutan kankiaπŸ‘ΈπŸ»)*  


   





*BISSIMILLAHIR RAHMANIR RAHIM DASUNAN ALLAH ME RAHMA ME JINKAI*



 _Wannan labarin kagaggen ne, duk wanda yazo daidai da rayuwarshi a kasi ne._ 


 ```NASADAUKAR DA WANNAN LITTAFIN GA FATIMA ABUBAKAR 

BELLO, ALLAH YA BAR KAUNA YAR UWA RABIN JIKI😍😍``` 




73&74


Washe gari bayan su Gimbiya Zulaha sun gama shiryawa suka Ι—auki hanyar Kano dan zuwa kai lefen Gimbiya Hakima da Yarima Hakim. 



"Kilishi yau dai zamuga wannan Hakimar da Hakim ke yi ma rawar kai". 


"Aiko dai yayi ya gama dan shekara Ι—aya zaiyi ita, ta zama ta Hamad baki Ι—aya har abada kuma ta haifamana sarki". 



"Hhhhhh! Kilishi kina sani farinciki wallahi shiyasa nike sonki, insha Allah zuri'ata ta dunga zama sarki kenan har abada Kilishi ". 



Wani kallon banza Kilishi tayi tana aiyanawa cikin zuciyar ta itace zata kama ganin sarki a cikin zuri'atar , dan wannan komai da komai da Humad ya dace basu Hamad ba. 



*Niko nace bawan Allah Humad shi baima san Gimbiya Kilishi na wanan wahalar ba dan bai damu da mulki ba🀣* 


Haka dai suka kama yan maganganun su har suka iso masarautar Kano. 


Baki sake su Gimbiya Kilishi dan sunga tarba ta girma, sunga idan akeyin abun girma da nuna arziki duk da Gimbiya Zulaha tasan masarautar Kano amman rabonta da masarautar Kano tunda da Sarki Abdulhadi zai auri Fulani bata sake zuwa ba ita acewarta ba halinta Ι—aya da Gimbiya Yakumbo ba shiyasa suka rabu. 



Bayan angama ansar lefe suka wuce shashen Gimbiya Yakumbo, da yake a shashen Maimartaba Sarki Abdulhadi aka anshi lefen, zasuje suci abinci sannan su wuce gida. 



"Sannunku da zuwa Gimbiya Zulaha, ashe rai kanga rai".?


"Gimbiya Yakumbo gashi kuwa, ya na samaiki keda Ι—ana Yarima Annas ".?  


"Lafiya lau kika samaimu, harda ma Ι—iyarku Hakima ita da mahaifiyarta duk muna lafiya". 


"Haka nike san ji, yau dai saura yan kwanaki akawo mana Amaryar mu, "eh daga gobe zamu fara aladar bikukuwan sarauta insha Allah ". 



"Da kyau, ina ita Amaryar take bata zuwa ta gaidamu".? 


''Aa fa Zulaha kin taΙ“a ganin ida Amarya ta fito ranar da ake kawo lefenta".? 


"Ai nasa zaki kirata tazo mu gaisa ba wanda yaji ba wanda ya gani". 


"Aa ni ba haka nike ba, kuma Hakima bata gidan ma baki Ι—aya kuyi hakuri ta kusa dawowa masarautarku baki Ι—aya ma". 



"Shikenan muna maraba lale da zuwan ta Amarya Gimbiya Hakima ". 


"Yauwa haka nike san ji daga gareku, kuci abincin mana, "to yanzun ko zamuci". 



Bayan sun gama cin abinci suka Ι—auki hanyar komawa gida, bayan sun koma gida basu ce ma kowa komai ba ita dai Fulani Kubrah bata damu da rashin gaya mata yanda komai ya kasance ba daman bata ran za'a gayamata ba. 


Yau ake fara hidimar biki dan yau ake sa Amarya laile hidima ake kamar kama hannun yaro tun safe aka tafi da Hakima shashen Gimbiya Yakumbo aka fara shafama amarya laile, wanann yana farkon al'adar masarautar Kano kafin a fara biki za'a fara sama amarya laile sannan zasu cigaba da yin sauran al'adun. 



Tunda aka fara shafama Hakima laile take bakin ciki dan ba haka ta so ba, ita da ba san Hakim take ba amman sai wani gyara ake yi mata sai kace gidan wanda take so da kauna za'a kaita. 



"Momy dan Allah ki barni haka ko ina fa naga kun shafaman".


"Gidanku Daughter, idan bamu gyaraki ba mai kike san ayi maki".? 


"Amman Momy tunda akayi baiko kuke duraman abubuwa cikin cikina,sannan kuma kuke man shafe-shafe Momy". 



"Wannan shine gatan, nidai Daughter dan Allah karki bamu kunya ku zauna lafiya keda wannan baiwan Allahn, kinga dai yanda Hakim yake da hakuri kema banjinki Daughter fatana ku zauna lafiya kuba mariΖ™a kunya". 



"Insha Allah Momy ba zan baki kunya ba zani kasance mai yi maku biyaiya har tsawan rayuwa nayi maki wanan alkwarin". 


"Allah yayi maki albarka Daughter, sannna ban yarda ki sake da kowa ba inba uwarmijinkina ba da Ζ™annansa, amman ban yarda ki yarda dasu Gimbiya Zulaha ba". 


"To Momy, wai jiya su suka kawo lefe ko".? 


"Eh sune sunso su ganki ni na hanasu, so suka yi su ganki abun ya zama gori nan gaba suna cewa baki da kunya dake aka anshi lefenki, shiyasa na hanasu basu san Ζ™ar nake kallonsu ba, kuma halin Gimbiya Zulaha ba wanda ban sani ba tana iya aikata komai saboda kishi da hassada". 



"Allah ya kiyaye dai Momy, "Amin ya Allah Daughter. 



Ana sama ta laile Gimbiya Yakumbo tana bata shawara dani shirin zama da miji, kuma Hakima tana Ι—auka duk da ba wani san Hakim take ba amman duk abunda Yakumbo ta gaya mata suna cikin kanta dan ta rigeshi sosai. 


Bayan ta wanke lailen kuma ta fara zuwa shashe tana kai gaisuwa duk inda taje sai anbata tukunci haka ta gama yi har dare yayi sannan ta wuce shashen ta duk ta gaji sosai. 



Wanka kawai ta shiga, shi kanshi ruwan wanka ba Ζ™aramin kayan haΙ—i ya sha ba ruwan sai kamshi yake kamar anyi Ι“arin turere cikin ruwan, saboda da kanshi da ruwan yake ga kuma zafin da yake dashi shi yaba Gimbiya Hakima dama daΙ—ewa sosai tana gasa jikinta sai da taji ta dawo dai dai sannan ta fito. 



Mai kawai ta shafa ta kwanta, da Azima ta lura da uwargijiyar tasu ta gaji sai suka kama yi mata tausa suna bata labarin mai dadi har bacci ya kwasheta ba tare da ta sani ba, sai da suka tabbatar da tayi nisa cikin baccin sannan suka tashi suka tafi shashen su dan gobe za'ayi hawan daba. 



_____________________________


"Hakim ya maganar biki damai damai ya zamuyi naga har yanzun baka gaiyaci friends Ι—inmu ba".? 



"Aliyu ni ba wanda zan gaiyata kuma ba abunda zaiyi ai hidimar biki tana wajen Hakima tunda itace Amarya". 



"Duk da haka Hakim, ya kukayi da Hakima mai take bukata kudi ko wani abu".? 



"Kash ni ko number Ι—inta bani da ita, amman nasan bata bukatar komai". 



"What".? 


"Eh Aliyu bani da number Ι—inta, ko laifi nayi naga ka tsareni da idanu sai kace wanda yayi laifi".? 



"Baka kyauta ba gaskiya Hakim, ai at list ko wayace kun ringa yi haka zai kawo maku shakuwa kafin bikin". 



"Ni ban damu da na shaku da Hakima ba Infact nasan ba sonta nike ba itama ba sona take ba zaman biyaiya kawai zamuyi kaga ba amfani kenan".? 



"Kace ba Hakim ina gaya maka gaskiya amman bakaji ko".? 


"Wata gaskiya kake gayaman wanda ban ji ba Aliyu ".? 



"Ehmana gashinan Hakim, wai har sai yaushe zaka gane ka yaudarar kanka, Hakim ka fidda girman kai ka rungumi matarka hannu biyu ka nunamata kallar soyayyar dakake yi mata hakan zaisa itama taji tana sonka tana nuna maka irin nata son da take yi maka". 



"Naji Aliyu zanyi yanda kake bukatar ni zan shiga wanka, "ok shikenan Hakim nima bacci nike ji na wuce mu kwana lafiya angon gata". 



"To goron gata, kaima ka yi fushi ka shigo layinmu a daina ce maka goro". 



"Gaskiya ne Hakim tun kafin akawo Hakimar har ka fara kirana da goro ina da ka shiga daga ciki".?



Hmmmm! Abunda Hakim yace ma Aliyu kenan ya shigewarshi wanka yana murmushi, shi dai baisan dalilin dayasa yake san Aliyu yana yi mashi maganar Hakima sai yaji wani dadi wanda bai iya musulta irinshi. 



Bayan ya fi

to wanka sallah yayi sannan yayi addu'oin bacci ya kwanta yana nishaΙ—a dan yana son a anbaci sunan Hakima gabanshi hakan na yi mashi dadi. 



_By Jameelah Jameey✍🏻_




Post a Comment

0 Comments