TOP HAUSA NOVELS atOptions = { 'key' : '20e08520dad54dbf6d9e963271

Gimbiya hakima page 63-64

 πŸ‘ΈπŸ»πŸ‘ΈπŸ»πŸ‘ΈπŸ»πŸ‘ΈπŸ»πŸ‘ΈπŸ»πŸ‘ΈπŸ»πŸ‘ΈπŸ»πŸ‘ΈπŸ»

         *GIMBIYA HAKIMA* 

πŸ‘ΈπŸ»πŸ‘ΈπŸ»πŸ‘ΈπŸ»πŸ‘ΈπŸ»πŸ‘ΈπŸ»πŸ‘ΈπŸ»πŸ‘ΈπŸ»πŸ‘ΈπŸ»πŸ‘ΈπŸ»




 *🌎MANAZARTA* 

 *WRITERS ASSOCIATION* πŸ“šπŸ–Š️


     *M. W. A* 


 ```Kungiya d'aya tamkar da dubu. Masu Nazari da Aiki da Ilimi, Burin 'kungiyar a ko da yaushe shine ta fad'akar ta ta kuma Nishad'antar da masoyan ta. πŸ€™πŸ»``` 

https://www.facebook.com/107980080946102?referrer=whatsa 

________________________________




  _STORY AND WRITING_ _BY_ 


    _Jameelah jameey πŸ–‹_ 


    *(Yar mutan kankiaπŸ‘ΈπŸ»)*  


   





*BISSIMILLAHIR RAHMANIR RAHIM DASUNAN ALLAH ME RAHMA ME JINKAI*



 _Wannan labarin kagaggen ne, duk wanda yazo daidai da rayuwarshi a kasi ne._ 


 ```NASADAUKAR DA WANNAN LITTAFIN GA FATIMA ABUBAKAR 

BELLO, ALLAH YA BAR KAUNA YAR UWA RABIN JIKI😍😍``` 





63&64



*×KANO×* 





Washe gari Gimbiya Hakima ta Ι—auki hanyar shashen Maimartaba itada su Lantana suna take mata baya suna labari dan yanzun Gimbiya Hakima ta yarda da maganar Fulani da tace mata inma bata fiddo Lantana ba matsalarta, ta yarda da wanann maganar dan yanzun bata san abunda zai Ι“atama su Lantana rai saboda suma basu san suga Ι“acin ranta. 




A bakin shashen Maimartaba suka haΙ—o da Yarima Annas na suka shiga tare su kuma Lantana suka tsaya suna gaisawa da dogarawan Annas. 




"Yaya Annas wai neman mai Baffah yake yi mana."?



"Hakima nima ban sani ba, amman may be maganar Aure zai yi mana da man wannan ranar tana nan zuwa tunda mun gama karatu." 




"Maganar Auren kuma Yaya Annas."? 



"Eh, amman ai ce maki nayi may be ko."? 



"Wai har naji hankalina ya kwanta, insha Allah ba maganar auren zai yi mana ba dan miko ban shirya aure yanzun ba."



"Allah ko Hakima."? 


"Sosai ma Yaya Annas, "Ok Hakima Allah ya bamu sa'a dai, "Amin ya Allah Yayana."




Haka suka shiga parlourn Maimartaba amman Annas yana mamakin yanda Hakima take furta bata shirya aure yanzun ba bayan tasan Maimartaba ba Ζ™yaleta zaiyi ba, ko shi Maimartaba ya Ζ™yaleta to shi ba zai Ζ™yaleta ba haka suka shiga suka samu waje a kasa suka zauna shi kuma Maimartaba shida su Yakumbo suna bisa three siter suna kallon yaran nasu yanda suka haΙ—a kansu hakan yana yi masu dadi, bayan sun gama gaidasu sannan Maimartaba ya fara magana. 




"Mamana."



Sai da gaban Gimbiya Hakima ya tashi da taji da sunan ta Baffah ya fara kira bana Yarima Annas ba, kasa magana tayi sai dai Ι—ago kanta da tayi tana kallon Baffah jira take kawai taji abunda zai gaya mata, koda Maimartaba ya fahimci sarautar har ta hau kanta ba ansawa zatayi ba amman hankalinta baki Ι—aya yana wajen shi sai ya cigaba da maganar shi. 




"Hakima na fidda maki mijin aure nan da kwana biyu zai zo kuga juna sai ayi biki Ι—an sarkin Zaria ne."



"Nagode Baffah, Allah ya saka da Alkhari, nasan ba zaka zaΙ“e man abunda zai cutar dani kuma ya zama dole na bi Umirninka dan kaine mahaifina kafi kowa iko da ni, ina godiya Baffah Allah ya Ζ™ara girma da Ι—aukaka."




"Allah yayi maki albarka Mamana,nasan bazakiyi kuka ba akan zaΙ“in da nayi maki Allah ya baku zaman lafiya ya baku zuri'a Ι—aiyaba wanda zasu taimaki al'umma baki Ι—aya."



"Amin." 


Baki Ι—aya parlourn suka ansa banda Hakima ta da duΖ™e kanta kasa tana wasa da zoben zinarin dake maΖ™ale a hannunta bata damu ba dan Baffah ya fidda mata miji ba ita dai fatanta Allah ya basu zaman lafiya.



"Allah yayi maki albarka Daughter, nasan Baffahnki ba zai zaΙ“a maki abunda zakiyi kuka ba."




Ita dai Gimbiya Hakima ba tace komai ba, amman tana mamakin wai ita za'ayi ma aure yarinya da ita. 



*{hahahha! Team Hakim kunji wai Hakima bata isa aure baπŸ˜‰}*



"Sai kuma kai Annas kaima ka zama cikin shiri dan aurer da kai zanyi ina nema maka mata dai-dai dakai, dan haka ka zama cikin shiri."




"To Baffah godiya muke, Allah yaja da tsawancin kwana, "Amin zaku iya tafiya Mamana ki fara shirin zuwan baΖ™on naki, "To Baffah insha Allah mun barka lafiya." 




Bayan sun fito suka wuce shashen Gimbiya Yakumbo baki Ι—ayansu, bayan sun zauna Yakumbo ta fara magana."




"Daughter Allah yayi maki albarka, gaskiya kin burgeni Daughter kuma nasan Hakim yaron Ζ™irkine bazai cuceki ba, sannan mahaifiyarshi mutuniyar Ζ™irkice sai dai kun kula dan masarautar zaria ana tungu da surkule dan haka sai kin kula da hannunki."




"Momy da man Yarima Hakim Baffah zai ba auren Hakima."? 



"Ehmana Yarima Hakim ne, da man kasanshi? Dan nasan rabonsu da nan masarautar tun haihuwar Hakima dasuzo sunan Hakima." 



"Eh nasanshi sosai muna mutunci sosai da shi muyi zama dashi a dubai."




Ita dai Gimbiya Hakima batace komai ba, kuma bata kowa komai a ranta ba duk taji sunce Hakim amman bata kowa prof Hakim ba dan ta manta dashi ma. 




*{gaskiya Hakima bata kaunar Hakim tunda ta iya mantawa dashi, salan naji Team Hakim kunce ba haka bane😎}*



Bayan sun gama maganarsu dan Gimbiya Yakumbo taba Hakima shawara sosai yanda zata zauna masarautar su Hakim ta gaya mata shirin masarautar sosai har suna mamakin yanda Yakumbo ta san masarautar har haka. 




"Momy ni wallahi har na fara tsorata taya zan iya da halin su Gimbiya Zulaha? Bayan ni ban taso naga gidan mu ana haka ba."? 




"Zaki iya Hakima sosai ma, abunda zakiyi shine karki yarda kice wani abu da ya fito daga hannu baiwar gida ko kuma hannun su Zulaha da Kilishi, karki yarda da ko wace baiwa sai wanda zaki tafi dasu daga nan masarautar suma da mutun uku zaki Lantana da Bilkisu sai Azima suma dan na yarda dasu amintaitun bayine nasan basu yarda a haΙ—a baki dasu a cuceki ba."





"Sannan karki shiga sabgar kowa, kuma nace maki Gimbiya Kubrah bata da matsala dan matace mai kawaici da mutunta mutane dan haka sai ki yaye Hakima, nasan ki baki Ι—aukar rainin bayi to karki yarda wata baiwa daga cikin masarautar ta ringa shigarmaki shashen har zuwa cikin Ι—akuna dan haka su azima su zasu gyara Ι—aki da girki kinjini ko."? 




"Eh Momy, naji kuma insha Allah zanyi abunda kikace man, dan ba zan yarda ba su Gimbiya Kilishi su raina ni nafi karfinsu da ayar Allah, amman Momy taya kikasan sirin masarautarsu har haka."? 





"Nasan sirinsu wajen Gimbiya Zulaha, da aminatace sosai saboda amintakar da ke tsakanin mijina da mijinta, lokacin daga ni har ita bamu samu haihuwa ba taso taja ra'ayina wajen bin bokaye da malamai nice ban bata fuska ba muna cikin haka sai Sarki Abdulmatalak ya bujuro da auren Gimbiya Fulani Kubrah, hankalin Gimbiya Zulaha ba Ζ™aramin tashi yayi ba dan ba wajen bokon da bataje ba amman bakinsu Ι—aya aure sai anyi ba, bayan anyi aure Allah mai iko yaba Fulani Kubrah ciki daga zuwanta nan ma Gimbiya Zulaha ta fita ta shiga taga cikin zube amman babu nasara har aka haifi Yarima Hakim, bayan haihuwar Yarima Hakim Gimbiya Zulaha itama ashe tana Ι—auke da ciki, Hakim yana da wata biyar a duniya Gimbiya Zulaha ta haifi yaronta namiji shine akazo dashi wajen walimarku Sunanshi Hamad, Hamad yana da wata biyu na haifi Annas tunda Gimbiya Zulaha taga Hakim shine magajin sarki Abdulmatalak ta tada hankalinta shine take bin bakoye dan har yanzun tana kan bakarta na Hamad sai yayi mulkin Zaria ba sirihin da bata yi ma Hakim amman Allah ya kareshi daga sharinta, Gimbiya Kilishi kuma su Hakim nada shekara biyu a duniya sarki Abdulmatalak ya aureta da basu yar ga maciji tsakaninta da Zulaha daga baya da suka fahimci halin su Ι—aya suka zama Aminan juna dan tare suke komai nasu ita kuma Kilishi ita ta haifi Yarima Humad kinji taΖ™aitacen labarin gidan surukanki Hakima zaki shiga gidan sarauta mai rikici dan haka sai kin iya takunki karki kuskura ki nemi bokaye dan haka ki riΖ™e Allah da ibadodi sune gatanki dan ita addu'a takobin mumunice."





"To Momy insha Allah, amman Momy taya kuka bar Abokantaka keda Gimbiya Zulaha."? 



"Lokacin da Baffahnki zai auri mahaifiyarki, dana gaya mata shine ta nunaman naje wajen boka a hana bikin, ni kuma nace ban Ζ™aucema Allah saboda Ι—'a Namiji naje nayi saΙ“on Allah dan haka ban hana Abdulhadi aure koda mata uku zai aure nidai fatana muyi zaman lafiya, shine tace ba ita bani tunda ba halinmu Ι—aya ba,daga ranar bata Ζ™ara zuwa wajena ba sanan ku za'azo wannan masarautar bata zuwa ko sunanki ba ita tazo ba Gimbiya Fulani Kubrah tazo sunanki ita da Yarima Hakim kawai sukazo suna kinji abunda ya rabamu." 




"Mutane saboda san duniya da san zuciya sai suyi abunda zasuyi da nasi nan gaba, Allah yasa mu dace, "Amin Hakima." 





Nan dai suka gama maganganunsu sannna kowa ya wuce shashen shi. 




_______________________________



*×ZARIA×* 







πŸ’ƒπŸΌπŸ’ƒπŸΌπŸ’ƒπŸΌπŸ’ƒπŸΌπŸ’ƒπŸΌπŸ’ƒπŸΌπŸ’ƒπŸΌπŸ’ƒπŸΌπŸ’ƒπŸΌ

*YAR UWA KADA KI WUCE BAKI KARANTA BA DOMIN KUWA AKWAI ƘARUWA A CIKI*

 


      *_πŸ—£️ALBISHIRIN KUπŸ—£️_*



*JAMA'A KO KUSAN MATASHIYAR MARUBUCIYAR NAN WATO JAMEELAH JAMEEY WANDA AKA FI SANI DA YAR'MUTAN KANKIA TAYI SHIRI TSAF DOMIN FITO MAKU DA SABBABIN LITTATAFANTA GUDA BIYU.*


*SANADIN LINK*



*_HAHAHA YAR UWA DAGA JIN SUNAN WANI BOOK BASAI NA FAƊA BA KINSAN ZA'A SHA SOYAYYA. _*




*IZZA KO MULKI*



*WAI WANNAN KO BANSAN MAI ZANCE BA KUNSAN DAI YANDA LABARIN GIMBIYA HAKIMA YA KASANCE TO GA WANI NAN KUMA DAN SHI DABAN YAKE DA SAURAN☺️*




*TAKU CE JAMEEY YAR'MUTAN KANKIA MARUBUCIYARπŸ‘‡*




Post a Comment

0 Comments