TOP HAUSA NOVELS atOptions = { 'key' : '20e08520dad54dbf6d9e963271

Makauniyar soyayyah page 43-44

 [4/16, 12:31] Mrs Mansoor: *MAKAUNIYAR SOYAYYA*💝💖💞


🤦🏽‍♀🤦🏽‍♀🤦🏽‍♀🤦🏽‍♀🤦🏽‍♀🤦🏽‍♀🤦🏽‍♀🤦🏽‍♀🤦🏽‍♀



*STORY & WRITTEN*


                *BY*



*MARYAM AHMAD PAKI*



*🌈KAINUWA WRITERS ASSOCIATION*🤝🏽

 




*Wannan shafin na sadaukar dashi ne ga duk wanda yake cikin wata jarabta ko cikin wani hali*


*Allah 🙏🏽🙏🏽🙏🏽na yi tawassali da sunayen ka da kyawawan ayukan mu, ka kawo mana mafita a al’amuran mu, ka bamu ikon cin dukkan jarabawar da ka mana*.


*Alllah dan sunayen ka tsarkakakku, ya ubangijin Sammai da k’assai, ya Ubangijin fiyayyen halitta, Annabi Muhammad (s.a.w) Allah ka bi ya mana buk’atun mu na alkhairi*

🙏🏽🙏🏽🙏🏽🙏🏽🙏🏽


_Plsss fans ina barar addu’ar ku akan wasu buk’atu nawa, Allah ya amsa min da sauran ‘yan uwan musulmai baki d’aya_




*Question of the Day*


_A cikin matan manzon Allah s.a.w, wacece ta lurar da manzon Allah (s.a.w) game da wata dabara da zai jawo hankalin sahabban sa a ranar hudaibiyyah, kuma dabarar taci nasara sosai_

_Menene cikakken sunan ta?_



 


43&44


Bayan na shiga d’aki ne, hirar da muka yi da yaya Faruk a cikin mota da kuma shawarwarin da ya din ga bani game da karatu ya dinga fad’o min a rai.


A yanzu na sa a raina da cewa yaya Faruk ya samu wani matsayi a raina ta ‘bangaren zumunci, wata zuciyar kuma ta na ce min mai zai hana in bashi matsayin da yafi dacewa shine in amince da soyayyar shi, me yasa har yanzu zuciya ta ba ta anshi tayin shi ba?


Wata zuciyar tawa kuwa shawara ta ba ni akan mu ci gaba da zumunci irin na ‘yan uwantaka.


Da wannan sark’ak’en tunanin na tashi na nufi d’akin Ummu.



Washegari ina zaune a falo, ina karanta wani online novel a cikin waya mai suna *Rayuwar yusra da Afshan*, wanda Maryam Ahmad Paki ta rubuta, labarin yayi touching d’ina na yadda soyayya ta canza ma Afshan hali, duk a dalilin soyayyar Muhsin da ta fad’a kuma mijin Yusra wacce ta rik’e ta kamar ‘yar uwarta ta jini, ba ta saka mata da komai ba sai soyayya da Mijin Yusra wanda take son shi kamar ranta, ko yaya labarin zai kasance a k’arshe? Gaskiya na yadda da marubuciyar da tace labarin Soyayya mai rud’ani da tausayi a cikin novel d’in, Shine na k’osa na ji k’arshen labarin.


Sallamar yaya Faruk ne ya katse min karatun da nake yi.


Amsa masa sallamar nayi da sassanyar murmushi na.


Kusa dani yazo ya zauna, yana min kallon gefen ido.


"yaya ina wuni" na gaishe shi.


"lfy amma ba lau". ya amsa min


Kallon shi nayi jin amsar da ya ba ni, a yanayin shi ban ga wani abu da yake damun shi ba.


Shiru na yi ban k’ara cewa komai ba.


Wani tsadadden murmushi yayi kana yace "Teemah ba ki tambaye ni me ya same ni".


"yaya ai ni ban ga alamar ba ka da lafiya ba, na gan ka normal ne".


Kallo na yayi sannan yace "Teemah, ni ko ke rashin lafiya?".


Da sauri nace "Me yake damun ka?" Na fad’a da alamar tausayi.


K’asaitaccen murmushi yayi yace "Ba irin ciwon da kike tunani bane, wannan daban ne, kuma ke ce maganin ciwon nawa".


Gaba na ne ya fad’i, sai yanzu na gane mai yaya Faruk yake nufi, yana so ya d’akko min maganar da muka yi kwanaki ne akan amsar tayin soyayyar shi.


Yanzu in ya tambaye ni mai zan ce mai? Gaskiya bazan iya fito wa direct in ce mai ban yi na’am dashi ba duk da matsayin da na ba shi a guri na.


Katse min zancen zucin da nake yi yace "Teemah!"


 nasan kin gane me na ke nufi, ba komai ke damu na ba illah fama da ciwon son ki da ya min dabaibayi a zuciya ta wanda har yanzu ban san matsayi na a gurin ki ba, ina so ki bani amsa ta Teemah, dan zuciyata ta samu peace of mind".


"An zo gurin".abin da na fad’a a raina kenan.


Zuciya ta ce ke kai kawon me zan ce ma yaya Faruk a yanzu da zai yadda da hujja ta, dubara d’aya ce ta fad’o min akan in lalla’ba shi mu rabu lafiya.


"yaya Faruk, kai ma kasa ba zan k’i ka ba, ko dan darajar ‘yan uwantaka dake tsakanin mu, ko a da damu ke samin misunderstanding rashin fahimtar juna ne, amma yanzu na gano kai mutum ne mai dad’in zama da dad’in mu’amala, sai dai ina neman alfarmar ka yaya ka k’ara min time, saboda kasan har yau ban gama sanin mecece soyayya ba"


Tsura min ido yayi kamar yana so ya gano gaskiyar maganar da na fad’a mishi.


Sunkuyar da kai na nayi dan gaskiya ba zan jure kallon da yaya Faruk yake min.


"Fatima!" ya kira ni da wani irin salon maganar shi da ya banbanta da sauran lokuta.


"Na’am yaya"


Sai da yayi shiru kamar ba zai ce


min komai ba, can ya d’ago ya kalle ni.


"Teemah, zan iya k’ara ba ki time kamar yadda ki ka buk’ata, ina so duk san da na k’ara tambayar ki ya zama kin samo amsar".


Ci gaba yayi da cewa "Teemah, ina son ki wanda ni kaina ban san adadin son da nake mi ki ba, ni mutum ne da ba na soyayya sai akan ki da na fara, akwai ‘yan mata da suke so na amma ni ke ki ka min, ba na so in yaudari mutum, dan haka Teemah ina rok’on ki kar ki yaudare ni, gwara tun wuri ki fito ki fad’a min abin da ke ranki, zai fi min sauki".


Jiki na ne na ji yayi matuk’ar sanyi da maganganun da yaya Faruk ya fad’a min, yanzu gaskiya ba k’aramin girman yaya Faruk nake gani ba.


"yaya insha Allah ba za ka same ni da aikata haka ba".


Murmushin jin dad’i yayi wanda hakan ya nuna a fuskar shi.


"Teemah, kinga kin sa na koyi surutu duk saboda son ki" ya fad’a da alamar wasa.


Dariya nayi nace "Ni ba ruwa na yaya".


Girgiza kai kawai yayi bai ce min komai ba.


Haka muka ci gaba da zance jefi-jefi, yana k’ara jaddada min irin son da yake min.


Tambaya na fara yi ma kaina "wai yaya Faruk wani irin so yake min haka? ni kaina na san ba ni da amsar amma alamu sun nuna ba k’aramin so yake min ba.


Muna cikin haka ne, yaya Khalil yayi sallama ya shigo falon, ka sa ‘boye mamakin shi yayi ganin mu tare da yaya Faruk a kujera d’aya muna hira.


Hannu ya mik’a mishi suka yi musabaha kana ya nemi guri ya zauna.


Yaya Faruk ne ya kalle shi yace "Ashe ba ka nan, shi yasa ban ga motar ka ba"


"Na d’an fita ne, naje gurin friend d’ina" yaya Khalil ya ba shi amsa.


"Ok" yaya Faruk ya fad’a a gajarce.


Ci gaba yayi da min Magana k’asa-k’asa yana fad’a min gobe zai koma Abuja, kar in manta in mishi Samosa da Spring roll d’in in ba Ummu ta ajiye mai, zai biyo ya amsa.


Sauraren shi kawai nake yi ba tare da n ace komai ba saboda na ga yaya Khalil ya maida hankalin shi gare mu.


Shi kuwa yaya Khalil kallo ya bi mu dashi ganin yadda mu ke Magana k’asa- k’asa, yana so ya tabbatar da zargin da zuciyar shi take yi akan mu.


"Tun yaushe yaya Faruk da Fatima su ka shirya? An yaya babu wata alak’a tsakanin yaya Faruk da Fatima kuwa? Duk wannan tambayar da yake yi ma kanshi yasan ba mai ba shi amsar sai Faruk ko Fatima, shi kanshi yasan ba zai iya tunkarar yaya Faruk da wannan zancen ba, gwara dai ya tambayi Fatima.


Kallan tsadadden wrist watch d’in shi yayi wanda ke d’aure a hannun shi, kallan time yayi ya juyo ya kanne min ido ya ce min cikin murya k’asa-k’asa


 "Teemah, zan tafi, nasan gobe in nazo ba zan same ki ba, mai za ki bani wanda zan dinga tuna wa dake" ya tsura min ido yana jiran ji mai zan ce mai, shi ko kunyar yaya Khalil ba ya ji.


Murmushi nayi nace "yaya ni ban san me zan ba ka ba, amma dai zan maka addu’ar Allah ya kai ka lafiya, ya kuma baka nasara a aikin ka".


Lumshe ido yayi saboda yadda yaji dad’in addu’ar da na mishi.


"Na gode Teemah da wannan addu’ar taki, ko ita kad’ai ta wadatar dani".


Had’a ido muka yi da yaya Khalil ya sakar min murmushi, saurin kau da ido na nayi dan nasan yau zan sha tsokana a gurin yaya Khalil.


Mik’ewa yayi yace "Bari in shiga gurin Ummu mu gaisa, sai mun yi waya".


"Ok sai mun yi waya" na ba shi amsa.


Hannu yaje ya ba yaya Khalil suka yi musabaha yace


 "Khalil bari in lek’a gurin Ummu, gobe zan koma Abuja, may be ba ka nan, kana school".


"Gaskiya may be ba za ka same ni ba, gobe da wuri nake so in shiga school".


"Don’t mind, sai na dawo daga Abuja kenan".


"Safe journey yaya Faruk"


"Thanks Khalil" ya fad’a ya nufi d’akin Ummu.


Samun ta yayi tana zaune tana muraja’ar Alk’ur’an, sanye da medicated glass a fuskar ta.


Sallama yayi ya nemi k’asan carpet ya zauna kusa da ita.


Amsa masa tayi da murmushi a fuskar ta.


Gaisawa suka yi ta tambaye shi ya su Momi, Daddy da Anisa.

Amsa mata yayi da suna nan lafiya.


Ce wa tayi ya fad’a ma Momi tana nan shigowa wannan sati.


Hira suka ci gaba dayi, a ciki hirar ne yace "Ummu gobe zan koma Abuja"


"Da wuri haka Faruk, ni ina sha zaka yi mana kwanaki a Kaduna".


 "Ummu da kwana biyu na nemi permission zanyi saboda prospond d’in tafiyar mu da aka yi".


"Allah dai ya taimaka, gwara da ka fad’a min da wuri, gobe sai in maka dambun naman ka tafi dashi".


Yau tsintar kanshi yayi da kunyar Ummu duk da ba ta san me ke tsakanin shi da Fatima ba, yana mai k’ara ganin girman Ummu na yadda take nuna kulawar ta gare shi.


"Ummu da kin barshi, saboda Fatima za ta min Samosa da Spring roll in tafi dashi, gobe zan biyo in amsa".


Dad’i ne ya kama ta ganin ce wa Fatima ce za ta mishi Snacks ya tafi dashi, hakan na nuna yanzu sun shirya kenan.


"Faruk ai Snacks daban, danbun nama daban, ka biyo gobe sai ka amshi duka".


"Ummu na gode, Allah ya k’ara girma".


"Amin Faruk, amma na sha ce maka in na maka abu ba godiya a tsakanin mu".


"To Ummu bari in k’arasa gida"


"Ka gaishe su"


"Za su ji".


Yana fito wa daga d’akin Ummu, d’aga mana hannu yayi ya fita daga falon.


Yaya Khalil ne ya dawo kusa dani yana kallo na.


Ni kaina kallon da yake min nasan akwai Magana a bakin shi, sai ban nuna mishi ba.


Dariya nayi ganin yadda yake min kallon tuhuma yana murmushi.


"yaya Khalil wai lafiya wannan kallon"


Bai ba ni amsar tambaya ta ba, sai ce min yayi "Sister kun sa ni a confusion"


"Ni da wa?" na tambaye shi.


"Ke da yaya Faruk"


"Da aka yi me?" 


Hararar wasa ya min yace "Fatima kinn gane abin da nake nufi, amma tun da kin nuna ba ki fahimta ba, bari in miki filla-filla".


Ci gaba yayi da cewa "Fatima wai yaushe kuka had’e da yaya Faruk ban sani ba? na fara zargin ko akwai wata alak’a a tsakanin ku, sister tell me the truth".


In akwai wanda ya cancanta yasan alak’ar mu da yaya Faruk bai wuce yaya Khalil da Anisa ba, sai dai kash, hakan ba zai yiwu ba, dan muddum yaya Khalil ya ji maganar nan kamar kowa yaji ne a family, hakan na nufin dole in amince da yaya Faruk duk da har yau zuciya ta ba taji wani alamu na kamuwa da son shi ba, ya zama min dole in bar maganar tsakanin ni da yaya Faruk duk da nasan duk daren dad’e wa dole a ji abin da ke tsakanin mu, ina fatan a lokacin na yanke hukunci tsakanin amincewa dashi ko akasin haka.


Yaya Khalil ne ya katse min tunanin da nake yi.


"Sister tunanin me kike yi ne?"


"No ba tunani nake yi ba, ni ba abin da ke tsakanin mu ni dashi, kawai dai yanzu muna shiri ne, shi yasa ka ke ganin kamar akwai wata alak’a a tsakanin mu".


Kallon tuhuma ya min yace "Kin tabbata abin da kika fad’a min gaskiya ne".


"haka yake yaya Khalil".


Girgiza kai kawai yayi amma ba dan ya yadda da abin da na fad’a mai ba.


Tashi yayi yana cewa "bari in je gurin Ummu, na ga ban gan ta a falo ba".


"Ni ma yanzu zan tashi in shirya, lokacin makaranta ya kusa".


"Ok ki biya ma Anisa sai driver ya kai ku, akwai abin da zan yi ne yanzu, zan zo in d’auke ku in time d’in tashi yayi".


"To shi kenan, sai kazo" na mik’e na tafi d’aki, shi kuma yaya Khalil ya tafi gurin Ummu.


Kamar yadda yaya Khalil ya mana alk’awarin zuwa d’aukan mu idan aka tashi, hakan ce ta kasance, shi yazo d’aukar mu.


A hanyar tafiyar mu muka ce ya biya damu bakery ya siya mana ice cream sannan yace mu za’bi abin da muke so.


Beaf bread da pizza na d’auka, Anisa kuma ta d’auki Shawarma da sponge cake, shi kuma yaya Khalil ya d’auki meat pie da burger, gurin biya yaje ya biya sannan ya fara sauke ni a gida kafin ya tafi kai Anisa.


Tun bayan sallar asuba, na fara had’in Samosa da Spring roll, sai da na tabbatar na gama, na d’auki had’in na sa a fridge, ko a lokacin har gari ya waye. 


Wanka na je na shiga, bayan na fito ne na shirya cikin cotton material kalar purple wanda ya sha d’inkin bit work, na d’akko gyale na light purple na yafa, na sa flat shoe, na rataya jaka ta side bag mai launin purple.


Gaskiya ni kaina nasan kwaliyar ta amshe ni sosai.


Fitowa nayi na tarar da Ummu da Abbu zaune a dining area suna kalaci, d’aya daga cikin kujerun dake zagaye da dining table d’in na nemi guri na zauna.


"Abbu Ina kwana, Ummu an tashi lafiya?"


"lfy lau Auta" Ummu ta amsa.


Murmushi Abbu yayi yace "Fatima kin tashi lafiya?"


"lafiya lau Abbu".


Juyawa nayi ina tambayar Ummu "yaya Khalil bai tashi ba ne?"


‘"Ina jin bai tashi ba, dan ban ji motsin shi ba, ina jin bai da lectures d’in safe ne".


Abbu ne ya kalle ni yace "Tun da na ga kin shirya, in kin gama break fast d’in ki same ni a falo, sai in yi dropping d’in ki, akwai in da na ke so in je da safen nan, tun da na ga Khalil bai tashi daga barci ba"


Amsa masa nayi "To Abbu".


Tashi yayi ya koma falo yana kallon labarai.


Kallon Ummu nayi na ce "Ummu, in yaya Faruk yazo, Samosa da Spring roll na cikin fridge sai ki ba shi".


Ummu murmushi tayi tace "Har kin yi kenan, gaskiya kin kyauta".


"Tun bayan sallar asuba na fara yi saboda ina gudun kar in makara".


Dariya Ummu tayi tace "Lallai kin yi k’ok’ari, Auta an shirya da yaya Faruk d’in ta kenan, ba sauran fad’a".


Cikin shagwa’ba na turo baki nace ‘ko da shi yake ja, amma yanzu mun shirya".


"Ai hakan yafi kyau Fatima" ta mik’e ta tafi falo.


Bayan na gama ne naje na sanar da Abbu na gama, tashi yayi muka nufi parking space ya d’auki motar shi muka tafi.


Sai da ya kai ni har department d’in mu ya sauke ni sannan ya tafi.



Can ‘bangaren yaya Faruk bayan ya shirya ya tafi side Dadi, inda ya samu Momi a can.


Yau Dadin bai samu zuwa aiki ba, kasancewar bai jin dad’in jikin shi.

Gaishe su yayi suka amsa.


Sun d’an ta’ba hira sannan ya mik’e da niyyar tafiya.


Addu’a Dadi da Momi suka yi ta mishi da fatan nasara a tafiyar da za suyi.


Kud’i ya ciro a wallet d’in shi ya ajiye ma ta.


Tana matuk’ar son Faruk saboda son kyautata ma iyaye da ‘yan uwa, ga kyauta, fatan ta Allah yasa ya ci gaba da wannan halin nashi.


Momi sai sa mishi albarka take yi irin wacce iyaye ke ma ‘ya’yan su.


Sallama ya musu, ya nufi ma’ajiyar motoci, ya shiga ya nufi gidan mu.


Ko da ya shiga falon, Iya Talatu ya samu a falo tana mopping, gaishe ta yayi ya tambaye ta "Ina Ummu take?"


Amsa mishi tayi "Tana kitchen, ko in kira maka ita ne?


"A’ah ki bar shi Iya Talatu, bari in k’arasa gurin ta".


Kitchen d’in ya nufa ya same ta tana juye dambun naman da ta mishi a plastic mai d’an zurfi.


"Sannu da aiki Ummu"


"yawwa Faruk, ba dai har ka shirya ba ba?".


"Yau da wuri nake so in tafi, akwai abin da zanyi ne in na koma".


"Ka ga ko yanzu na gama dambun naman, bari in d’akko maka Snacks d’in da Fatima ta ma ka"


Wani farin ciki ne ya kama shi a lokaci guda, ganin yadda Fatima ta tashi ta mishi snacks d’in kamar yadda tayi alk’awarin za ta mai, hakan na nuna kenan ta damu dashi.


Bai san lokacin da murmushi ya su’buce mai Abuja


D’akko mishi tayi ta samu d’an k’aramin basket ta jera mai a kai.


Kud’i ya ciro a wallet ya ba ta.


Ummu k’in amsa tayi tace "Haba Faruk, ni kam yau kayi hak’uri b azan amsa ba, tun kullum cikin ba mu ka ke yi, Allah dai ya k’ara bud’i".


"Ummu plss ki amsa ba yawa".


Murmushi tayi tace "Faruk ai ba raina wa nayi ba, wani lokacin na amsa, amma Allah a yanzu ba zan amsa ba".


Bai son suna jayayya shi yasa ya hak’ura, amma ba haka yaso ba, yaso ta amsa.


Sallama ya ma ta ya kana ya nufi Abuja.



Post a Comment

0 Comments