TOP HAUSA NOVELS atOptions = { 'key' : '20e08520dad54dbf6d9e963271

Gimbiya hakima page 75-76

 


πŸ‘ΈπŸ»πŸ‘ΈπŸ»πŸ‘ΈπŸ»πŸ‘ΈπŸ»πŸ‘ΈπŸ»πŸ‘ΈπŸ»πŸ‘ΈπŸ»πŸ‘ΈπŸ»πŸ‘ΈπŸ»

         *GIMBIYA HAKIMA* 

πŸ‘ΈπŸ»πŸ‘ΈπŸ»πŸ‘ΈπŸ»πŸ‘ΈπŸ»πŸ‘ΈπŸ»πŸ‘ΈπŸ»πŸ‘ΈπŸ»πŸ‘ΈπŸ»πŸ‘ΈπŸ»




 *🌎MANAZARTA* 

 *WRITERS ASSOCIATION* πŸ“šπŸ–Š️


     *M. W. A* 


 ```Kungiya d'aya tamkar da dubu. Masu Nazari da Aiki da Ilimi, Burin 'kungiyar a ko da yaushe shine ta fad'akar ta ta kuma Nishad'antar da masoyan ta. πŸ€™πŸ»``` 

https://www.facebook.com/107980080946102?referrer=whatsa 

________________________________




  _STORY AND WRITING_ _BY_ 


    _Jameelah jameey πŸ–‹_ 


    *(Yar mutan kankiaπŸ‘ΈπŸ»)*  


   





*BISSIMILLAHIR RAHMANIR RAHIM DASUNAN ALLAH ME RAHMA ME JINKAI*



 _Wannan labarin kagaggen ne, duk wanda yazo daidai da rayuwarshi a kasi ne._ 


 ```NASADAUKAR DA WANNAN LITTAFIN GA FATIMA ABUBAKAR 

BELLO, ALLAH YA BAR KAUNA YAR UWA RABIN JIKI😍😍``` 





75&76





_______________ 


Tunda Hakim ya tashi ya ansa kiran da Maimartaba Abdulmalak yake yi mashi, duk da yaji dadin yanda ya bashi umirnin ya shirya yaje Kano ayi duk wata al'ada da akeyi dashi amman kuma sai yaji ba dadi tunda Hakima ba sonshi take ba kuma bata Ι—aukin zuwan nashi tunda ya dawo daga gidansu Hakima bata kirashi waya ba duk da yasan bata da numbers Ι—inshi, amman ai ba zasu yi mata wahalar samuba tunda Maryam Ζ™awartace kuma Maryam tanada numbers Ι—inshi kamar yanda su Maryama suke da duka numbers dinshi. 



Bayan ya koma shashen shi ya Ι—auki waya ya kira Aliyu yake gaya mashi ya shirya zasu biki, dan basu dawowa sai da Amarya, bai damu da duk saigantakar da Aliyu yake yi mashi ba ya tsinke wayarshi ya kira Maryam yace ta turo mashi number Ι—in Hakima, Maryam taji dadi sosai da Hakim ya tambaye ta number Ι—in Hakima,tasan cewa ko sunyi aure Hakim ba zai biye ma Hakima ba suyi Ζ™arantar da sukayi ba a school. 



Tura mashi number din tayi sannan yace ta shirya zasu kano biki itada su Maryama amman kar ta kuskura tace dasu Maryama zatazo balle shi, haka ko akayi Maryam tace mata zasuzo biki amman itada wasu course mate Ι—insu zasuzo, tunda maryam ta gaya ma Hakima take murna dan itaji dadi sosai ta samu kawar shawara da ita Ι—aya da Azima kawai take shirinta tunda babu age mate Ι—inta a masarautar baki Ι—aya.



Haka suka gama shiri suka Ι—auko hanyar kano shida su Maryam. 


___________



Yau tun safe bayi ke aiki tukuru saboda yau ake hawan daba, shiyasa kowa da yake masarautar ba zaune yake ba yana aikin da shuwagabannin bayi suka bashi. 



Harta Hakima bata gida tana wajen make_up, kwaliya ake yi mata tana gani ta faΙ—a dan da ka ganka sai kasan kudi sunyi kuka bisa fuskar nan tata, yau su Maryam da wasu friends Ι—insu zasujo bikin, shiyasa tun safe bakin Hakima yake bude ta kasa kulleshi dan batayi tunanin Maryam zatazo mata biki ba, amman abun yayi mata dadi sosai. 



bayan angama shiryata ta fito Amaryarta sak,marron material aka sa mata sai alkalbarta itama marron takalminta marron color ne dan kyai ko Hakima tayi shi dan Ι“ata lokacine wajen tsayawa na gaya maku kallar kyaun da Hakima tayi sai dai kuyi imaging  da kanku πŸ˜›. 



Angama haΙ—a komai yanda ya dace dan su Hakim su iso har abinci sunci a shashen Yarima Annas Hakim da Aliyu suka sauka dan nan zasu zauna har agama hidimar bikin baki Ι—aya sanann, Yarima Annas da kanshi ya kai su Maryam Shashen Hakima sunce abinci sanan sukayi wanka suka hau kwaliya suna cikin yin kwaliya Hakima ta shigo hauka ne kawai batayi ba san murnar ganinsu da tayi, bayan sun gama kwaliya suka jera suka fito da amarya dan kowa ya hallara banda Amarya. 



Tun daga nisa Hakim yake kallon Hakima yana gaya ma Allah, dan tunda yake a duniya bai taΙ“a ganin mace mai kyau ba kamar Hakima, dan komai nata daban yake dana sauran, haka dai har suka iso wajen da zasu hau dokuna ita da Hakim suyi yar rere. 



Hakima keda farin doki Hakim yanada bakin doki, kasa hawan dokin Hakima tayi, tayi kokarin taga ta hau amman ta kasa, Koda Hakim yaga ta kasa hawa sai ya sauko daga bisan nashi dokin ya je wajen Hakima dai dai setin kunnanta yace mata, "Idan kinsan baki iya hawa ba ai sai kice a taimakamaki yan mata, ba sai kinyi nukunuku ba."yace yana kashe mata ido Ι—aya. 


Bata ankara ba taji mutun ya Ι—agata sama ya Ι—aurata bisa dokin yana Ι—age mata gira Ι—aya yana mata nuni da shine boss, wata kunya da takaici ya turnike Hakima wai ita Hakim zai Ι—auka, sai kace wata Ζ™awarshi da zai Ι—auketa kuma gaban su Yarima Annas da Maryam dan ya kama rainata, ita bama Ι—aukarma dariyar da suke yi tafi bata haushi dan suka Ζ™ara koΙ—a mashi kai, bayan ya Ι—aurata shima ya sake hawan nashi sannan akayi masu counting one-three sannan suka ba dawakansu wuta. 



Hakim abun mamaki ya bashi yanda Hakima ta zage tana san ta wuce ita a dole ta yo na Ι—aya ba Hakim ba, shikuma Hakim daya ga haka sai ya Ζ™ara ma dokinshi wuta in munite ya taddo Hakima kallon-kallon suke ma junanshi na Hakim yace mata, "Yarinya ke nemi alfarma a Ι—aga maki ki wuce dan wannan wasan na jarumaine ba na Ζ™anannan kiyashi ba."gwallo yayi mata sannan ya rage gudun nan Hakima ta wuce tayi na Ι—aya, nan fa Ζ™awayen Hakima suka hau murna sunyi na Ι—aya, bayan sun gama hawan dawakan akaci abinci kowa ya wuce masaukinshi. 




Bayan Hakim ya huta ya Ι—auko wayarshi ya lalubo number Ι—in Hakima, ya daΙ—e yana kallon number sanann daga baya ya fara tura mata textmassege kamar hakaπŸ‘‡. 


_"Yarinya ki fara shirya zama da maΖ™iyinki, dan kinsan Yarima Hakim ba sonki nike ba kuma kinsan ke ba zaΙ“i na bace, nan gaba zaΙ“i na zata shigo ku zauna da ita dan haka take note."_


Tunda shigowar massege Ι—in a wayar Hakima ta Ι—auka ta karanta bada damu da abunda Hakim yace mata ba dan daman tasan ba son juna suke ba, dan haka itama ta mayar mashi da answer Ι—inshi dan bata iya Ι—aukar gaya magana marar dadi. 


_"mtssssss, daman wa ya gaya maka ana sonka, kaima ka shirya zama da maΖ™iyarka wanda bata sonka bata kaunarka kawai biyaiya zatayi ta aurenka, kuma in katashi ba Ι—aya ba ka kawo uku bayan ni duk matsalar ko baka san sai ana son mutun akeyin kishinshi ba to ni bani sonka balle nayi kishinka take note, sannan kuma kayi gaugawar goge number ta cikin wayarka."_ 


Shigiwar massege Ι—in Hakim ya karanta take yaji baiji dadi ba ,da man shi yasan Hakima bata taba sonshi, daman yayi message ne yaga ko zata damu amman ga abinda ta mayarmai da answer, shi dai Hakim gashi nan dai dan baiji dadin jikinshi tunda Hakima ta turo mashi answer, kwaciya yayi yana juye juye dan da ya kulle idonshi sai ya hango daukar da yayi ma Hakima ya daura ta kan doki, ko kuma da ya kulle idonshi sai ya tuno fadan da sukeyi a school, murmushi kawai yake dan abun yana yi mashi dadi sosai haka dai bacci ya daukeshi. 




Itama Hakima bayan ta turama Hakim da answer suka cigaba da labarin duniya ita dasu Maryama dan daman can sun san juna shiyasa, sune basu kwanta ba sai wajen biyun dare sanan ko wancansu ta kwanta bacci. 




Yau za'ayi wanki, wani program ne da ake gidan sarauta mai suna *WANKI*, wanki dai suna nufin wankin lailen da akayi ma Amarya, dan haka da wuri suka tashi suka shirya ba Ζ™aramin kyau Hakima da Ζ™awayenta sukayi ba, karfe hudun rana aka fara gudanar da wanki, gaskia ko Hakima taga gata wajen wanki dan ba Ζ™aramin kudi a zubda mata ba sai mangrid sannan a ka tashi. 


Wanka kawai Hakima tayi ta kwanciyarta bacci, duk da ba baccin take ba tunanin zaman da zasuyi da Hakim Yanzun yake neman hanata bacci gashi gobe ne Ι—aurin aurensu, tuna message Ι—in da Hakim yayi mata ya tada ma hankali batasan sanda hawaye suka fara zuba a idonta ba, dan tasan zata sha wuya wajen Hakim dan ma saukinta gasu Maryama nan da Sadiya tana da abokan Ι—ebe kewa, gashi yan jere sunjr sunce a shashe Ι—aya zasu zauna da Hakim, harda haka yake Ζ™ara tada ma Hakima hankali, parlour Ι—aya ne babba sai bedrooms da suka zagaye da parlourn kitchen kuma Ι—ayane toilet ne kawai basu haduwa da Hakim sai bedroom dan suma ance suna da yawa a shashen nasu, haka dai ta kama juyi tanajin su Maryam suna lissafa kudin da suka samu yau wajen Wanki, har suka gama laissafi suka kwanta bacci amman ita idonta biyu tana tunanin rayuwar da zata shiga daga gobe. 



Shima haka takasance Hakim, tunda suka dawo kasa cin abinci yayi yana mamakin yanda Hakima ta tsaneshi da yawa har haka, yana san kasancewa da Hakima inuwa Ι—aya koda ko zasuyi faΙ—an dasuka saba, duk da yasan cewa ba sonta yake ba amman yana san yaganta kusa dashi, sai yanzun ya Ζ™ara amincewa da kunnunwanshi da idanuwanshi suna son Hakima, amman zuciyarshi bata son Hakima, yana taΖ™aicin yanda ita Hakimar batajin haka a taitare dashi, da tana jin haka da tayi kishi jiya da ya tura mata message zai mata kishiya amman a banza ko a jikinta, daΙ—inshi Ι—aya ma shashe Ι—aya zasu zauna ma dole ne zasu ringa ganin juna ko wani lokaci bacci kawai zai rabasu ko wane zaitafi Ι—akin baccinshi, a haka dai ya kama tunaninshi yana hangon kyaun da Hakima tayi wajen al'adar bikin nasu, duk da yasan cewa Hakima kyaukyawace amman tayi mashi kyau sosoi haka har bacci Ι“arawo ya kwasheshi. 



Yau masarautar kano ta fara sanin zatayi hidimar biki, dan sarakuna da yan siyasa yan kasuwa da duk wani mai faΙ—a a ji a nigeria sai da ya hallaci kano dan kawai Ι—aurin auren Gimbiya Hakima da Yarima Hakim, da yake Ι—aurin auren 1pm za'ayi shiyasa jama'a suke samun damar zuwa ayi dasu tunda Ι—aya ne za'a Ι—aura auren. 



"Haba Hakima dan Allah ki tashi ayi maki make-up Ι—in nan kinsan one za'a Ι—aura wannan auren naku kuma gashi yanzun 12 tayi amman kinΖ™i tashi ayi maki make-up haba please."



Itadai Hakima bata ce ma Maryam komai ba, sai dai ido ta tabita dashi, kuma bata tashi ba, ji tayi an bugar mata cinya sannan tayi ajiyar zuciya tana cewa, "Maryam wallahi banson auren nan, banson Hakim kinfi kowa sani bansan ya zanyi ba."



Ta sowa Maryam tayi ta zauna kusa da Hakima, tana zama su Maryama na shigowa suma direct wajen suka zauna dan sun san komai suma, dafa Ζ™afarta sukayi su duka ukkun sannan Sadiya ta fara magana, "Hakima munsan cewa baki san Yaya Hakim, amman kisani Yaya Hakim yana sonki yana kaunarki, Yaya Hakim yana yi maki so wanda har yanzun baisan adadinshi ba a cikin birnin zuciyarshi ba."



"Ta..., "dakata Hakima mu gama gaya maki waye Hakim, da mai-da mai Hakim yake so da wanda bai so, koda baison ki idan kina yi mashi abubuwan da muka gaya maki wallahi zaki juya Yaya Hakim kamar ranwa, Hakim zai zama mijintane daki juyashi yanda kike bukata, domin zai soki kamar ranshi, amman idan kinbi shawarar da muka baki."



"Yaya Hakim mutun ne maison a girmamashi, yana son kwaliya more expecially yaga kinsa jan baki, yana son yaga mace yar'kwaliya da kisisina da shagwaΙ“a, baya cin abincin bayi dan haka ki shiga da niyar ke zaki ringa yi ma mijinki sauwa , ki tabbbatar da ke gwanace wajen iya girki da kwaliya, Hakima tsafta tana gaba wajen sace zuciyar Ι—'a namiji yanga da jan aji ko yayake ko, dan kitson nan da kunshi zu zama abokanarki Hakima suma suna Ζ™arama mace martaba a wajen mijinta, ki rige Ibada da neman tsarin wajen ubangijinmu Allah, wallahi Hakima idan kika rige abubuwan da muka gaya maki sai kinzama zara a wajen Yaya Hakim, sannan naji watarana a lambu yana gaya ma Yaya Aliyu idan mace na cin chingum tana taso mashi da shi'awarshi dan haka sai ki tafi da kwalin chigum, wannan zaman da zakuyi ki kasance mai yawan cin chigum amman a gabanshi kina sa Ζ™ananan kaya masu masifar Ι—aukar hankalin Ι—'a namiji zaki sha mamakin yanda Yaya Hakim zai nemi ku sasanta kanku ku zauna lafiya mudai muna maraba dake muna kaunarki a matsayinmu na Ζ™annan Hakim."



"Nagode sosai Sadiya, kuma insha Allah zanyi duk abunda kuka gaya man, amman mai Hakim yafi so wajen abinci."? 



"Yafi son tuwon shinkafa miyar kuka, sannan kuma yanason dambu sosai, "nagode Allah ya bar zuminci, "Amin ya Allah Hakima, ku taho ayi make-up Ι—in sha-biyu da rabi har tayi fa."


Nan aka yi ma Hakima kwaliya, wata atamfa tasa mai ratsin ja da baΖ™i atamfar tayi mata kyau sosai, sannan ta Ι—aura alkarba sama ana Ι—aura aure za'a tafi da amarya gidan mijinta, shiyasa ta shirya. 



Kutsawa nike cikin mutune dan na kwaso maku rahota wata kallar kwaliya ango Hakim yayi, wai na samu na ganoshi shida friends Ι—inshi, farar shidda yasa tasha aiki masha Allah ga babbar riga duk ya Ι—aura a bisa rigar aikin Ι“akin zare aka yima atamfar abundai masha Allah kawai zamuce. 



Da kaga Hakim kaga ango dan bakinshi yaΖ™e kullewa dan murna, dan koshi kanshi yana mamakin yanda yake farin ciki har haka sai kace wanda zaiyi auren soyayya, amman shi yasan yau babbar ranace a wajenshi, ya rasa yanda zaisa kanshi dan murna duk da tsokanarshi da Aliyu yake amman bai damu ba shidai ya kosa ma a Ι—aura auren bak Ι—aya, dan ji yake inama ya matso da time Ι—in. 





Hausawa sunce rana bata karya sai dai uwar Ι—iya taji kunya, to haka ta kasance dan yau aka Ι—aura auren *YARIMA HAKIM ABDULMALAK DA AMARYARSHI GIMBIYA HAKIMA ABDULHADI*  a kan sadaki naira dubu Ι—ari biyar, mutane da dama suka shida wannan Ι—aurin aure, bayan angama Ι—aura auren aka fara taya Hakim murna shidai kawai kallon mutane yake dan abun mamaki yake bashi wai shi yau aka Ι—aurama auren da kuma Hakima, abunda yana bashi tsoro da mamaki, haka dai haka gama komai aka fara shirya ma amarya dan kanta gidan mijinta. 



Wa'azi tasheshi wajen iyayenta guda uku, tasha kuka kamar ba gobe da Lantana da Bilkisu da Azima kawai ta tafi gidan miji, haka suka Ι—auki hanyar Zaria domin kai amarya gidan mijinta.





_By Jameelah Jameey✍🏻_




Post a Comment

0 Comments