TOP HAUSA NOVELS atOptions = { 'key' : '20e08520dad54dbf6d9e963271

Zazzafan so cmplt txt (A).

 [10/10, 9:57 PM] Gambosy: ♥♥♥♥

  *XAXXAFAN SO*

     (Guba ne)

   *The broken* 

   *heart story*

    💔💔 






 🌟STARS WRITERS ASSO🌟🖊✨

(Home of special and extraordinary writers)






Story and writing by:

*Karima Tijjani Mansur*

*(Hajeeyah Kareemerh)*


*Dedicated to: Unique In Your Love Heart Members*


*بسم الله الرحمن الرحيم و صلى الله على النبي الكريم*




📄 *1*


Durkushe take a gaban mahaifinta wanda yake xaune akan daya daga cikin kujerun dake dakin,hannunshi rike da jarida akwai glass fari akan fuskarshi hankalinshi akan Jaridar.. kusan minti 3 tana xaune sannan ya ajiye jaridar kan wani dan table dake gabanshi y dubeta fuskarshi babu yabo babu Fallasa ya miko hannu

"Bani takardar"

Ya fada cikin muryar bayyana takaici. 

Hannu biyu ta saka ta mika mishi a sanyaye.

Ya karba da sauri ya warware ya fara dubawa.. Wajen mintuna biyar yana nazarin takardar sannan ya dago ya kalleta,tayi sauri ta sunkuyar da kai  jikinta sai bari yake. Ita kanta tasan batayi abin kirki ba ajarabawar.. ya d'an ja fasali sannan ya fara magana ahankali 

"Bansan me yake damunki ba hafsat, Allah ya gani ina iyakacin k'ok'arina kan karatunki amma kink'i ki mayar da hankali".. "Kayi haquri abba" ta fada tana hawaye. "Ba kuka nace ki min ba, na dai fada miki ki gyara kafin in fara nuna bacin raina akanki. Ya dace a hankalce ke da kike daukar 1st position amma duba fa bata biyu ba,ba ta uku bama har ta biyar koh? To yayi kyau"

"Kayi haquri Abba" ta kuma fada.. "Hmm tashi kibani guri" tayi xumbur kamar kan qaya take sum sum sum ta nufi kofa "zo ki tafi da takardarki" 

ta dawo jiki a sanyaye ta karba ta wuce kamar wacce kwai ya fashewa aciki.




[1/11, 12:09 AM] Hajeeyah Karimah (Writer): ♥♥♥♥

*ZAZZAFAN SO*

     (Guba ne)

 *A broken* 

 *heart story* 

   💔💔




Story and writing by:

*Karima Tijjani Mansur* 

*(Hajeeyah Kareemerh)*


*Dedicated to :Unique in Your Love Heart members.* 



📄 *2*


Dakinta ta nufa wanda ita kadai ce mamallakiyar dakin sai 'yar qaramar qanwarta ta hudu, Mufeedah. Ta tura qofar dakin a hankali ta shiga, ta tarar da mufeedah tana bacci kan dan qaramin gadonta, kasancewar dare ne. Nata gadon ta nufa tayi cilli da report sheet d'in a qasa ta fada kan gadon tayi shiru cikin rashin sanin tunin da ya dace tayi,ta dafe kanta kawai da hannayenta biyu..

Wayarta ce ta shiga ruri wacce ke cikin drawer ta kayanta. A hanxarce ta mike don ta manta bata sanya wayar a shiru ba (silent). Ta nufi drawer ta bude ta dakko wayar.

Ba wata babbar waya bace Samsung ce mara memory 'yar qarama, wacce ko radio bata da shi *"DEAR"*

shine akan screen din wayar ta lumshe Idonta hadi dayin ajiyar xuciya ganin wanda ya kira wayar, ta danna 'Green' (mab'allin amsa waya) 

Ahankali tace "Hello"

"Ya akayi ne 'yan matana?" 

"Humm!!

Tayi ajiyar zuciya ta nufi gadon ta dan kashingida. 

Daga can akace 

Me ya faru ne baby naji kinyi wani ajiyar heart? ".. Uhum? 

ta dan girgiza kai.. 

"Bbu komai fa"

"Are u sure? "

 "Yess"

"Ban yarda ba fa!

"Me yasa?"

"Haka kawai dai may be kina boyemin wani abu ne Koh? "

"No, I just missed your sweet voice throughout today..am shine yasa.."

"Hmm dagaske kinyi kewa d'ina  baby? "

Ya fada da wata irin hausarshi kamar bai K'ware a hausar ba.

Ta juya kwanciyar ta zuwa rub da ciki "ka daina mamaki"

Ok nagode yaune ina busy baby, mum ce ta sanyani wani aiki wai don rigima ni nayi driving enta xuwa meeting,then ta wani sanya ni na xauna jiranta tun3 12pm har 4:30pm sannan muka bar wajen."

"Dear"

Na,am

Mommynsu ce kake cewa tana rigima? 

Hahh Kijiki kema baby so what's this in ba rigima ba? Ni duk ta tare min schedule ena na yau, hmm mum akwai rigima fa

"Tom shikenan!

Ta tak'aita hirar saboda bata son yana fadan irin wannan kalaman ga iyayen shi, amma shi kamar bai dauki hakan wani abu ba.

"Baby me zan samu ne Uhum"? 

Motsi taji kamar za,a bude k'ofar d'akin don haka tace "Am sorry bacci nakeji" 

"Ok kin gaji dani Koh? "

Kafin tace wani abu ya katse wayar.

Daidai lokacin Mamansu ta shigo dakin 

"wacce irin kwanciya ce wannan? 

Tayi sauri ta tashi zaune. Mama ta Kalli wayar dake gefenta, "waya kike koh"?

 "A,a" ta fad'a a d'an tsorace tana girgiza kai. 

"Yayi miki kyau, kinyi sallah ne "?

"Yanzu zanyi"

"Yayi kyau"

ta d'an Kalli wasu sashi na d'akin sannan ta juya ta fita.

 Hafsa kuma ya mik'e ta nufi band'akin dake cikin d'akin don yin alwala.

[1/11, 12:09 AM] Hajeeyah Karimah (Writer): ♥️♥️♥️♥️

*ZAZZAFAN SO*

(Guba ne)

   *A broken* 

   *heart story*

    💔💔




Story and writing by:

*Karima Tijjani Mansur*

*(Hajeeyah Kareemerh)*


*Dedicated to: Unique In Your Love Heart Members*


*بسم الله الرحمن الرحيم و صلى الله على النبي الكريم*




📄 *1*



Durkushe take a gaban mahaifinta wanda yake xaune akan daya daga cikin kujerun dake dakin,hannunshi rike da jarida akwai glass fari akan fuskarshi hankalinshi akan Jaridar.. kusan minti 3 tana xaune sannan ya ajiye jaridar kan wani dan table dake gabanshi y dubeta fuskarshi babu yabo babu Fallasa ya miko hannu

"Bani takardar"

Ya fada cikin muryar bayyana takaici. 

Hannu biyu ta saka ta mika mishi a sanyaye.

Ya karba da sauri ya warware ya fara dubawa.. Wajen mintuna biyar yana nazarin takardar sannan ya dago ya kalleta,tayi sauri ta sunkuyar da kai  jikinta sai bari yake. Ita kanta tasan batayi abin kirki ba ajarabawar.. ya d'an ja fasali sannan ya fara magana ahankali 

"Bansan me yake damunki ba hafsat, Allah ya gani ina iyakacin k'ok'arina kan karatunki amma kink'i ki mayar da hankali".. "Kayi haquri abba" ta fada tana hawaye. "Ba kuka nace ki min ba, na dai fada miki ki gyara kafin in fara nuna bacin raina akanki. Ya dace a hankalce ke da kike daukar 1st position amma duba fa bata biyu ba,ba ta uku bama har ta biyar koh? To yayi kyau"

"Kayi haquri Abba" ta kuma fada.. "Hmm tashi kibani guri" tayi xumbur kamar kan qaya take sum sum sum ta nufi kofa "zo ki tafi da takardarki" 

ta dawo jiki a sanyaye ta karba ta wuce kamar wacce kwai ya fashewa aciki..

[1/11, 12:09 AM] Hajeeyah Karimah (Writer): ♥♥♥♥

*ZAZZAFAN SO*

(Guba ne)

*The broken* 

*heart story* 

  💔💔


Story and writing by:

*Karima Tijjani Mansur* 

*(Hajeeyah Kareemerh)*

*Dedicated to*

*Unique In Your Love Heart group Members.*





📄 *3*



*Tana* idar da sallar ta miqe ta nufi drawer ta dakko wata doguwar riga, ta bacci ta saka, ta kashe fitilar dakin, sannan ta kwanta..

Ita kanta tasan tana buqatar ta nutsu tayi tunani,amma ji takeyi gaba daya xuciyarta a jagule ba xata iya yin wani tunani ba,duk da da akwai buqatar tayi naxarin abubuwa da dama wanda suka faru ayau din. 

Misali; yaune akayi musu hutun makaranta kuma aka basu sakamakon jarrabawarsu wanda ya dad'e tana d'aukar na d'aya ko na biyu,sai gashi ta tsallaka har mataki na biyar,wanda tun kafin araba musu result d'in da kwana biyar, tasan matsayinta. Malamin ajinsu shiya kirata yake mata fad'a a ranar.

"Hafsat H Hamid. me yasa kike wasa da karatunki ne yanxu? Na lura gaba d'aya yanxu hankalinki baya kan karatu.ke yarinya ce yanxu kike tasowa ya dace ki bawa karatunki muhimmanci fiye da komai hakanne xai gina miki rayuwarki ta gaba."Ki cire shirme da shashanci sannan ki daina batawa kanki lokaci kan soyayyar banxa.."

Tayi saurin dagowa ta kalleshi..

Yayi murmushi "yes abinda yake damunki kenan, kin dauka bana gane duk halin samarin kuke ciki. Don Allah ina baki shawara amatsayina na kamar mahaifinki ki dauka yanxu lokacine na kiyi karatu ba soyayya ba.soyayya a gurinki a yanxu bata lokaci ne, ko kina ganin ba abin kunya ne ace kin mik'a wa mahaifinki 5th position naki ba a wannan term d'in."?

Ta waro ido "Sir 5th kuma?"

Ya d'an hade rai "yes, wa ya miki exam d'in?"

A hankali tace "Nice "

"To tashi kije ,amma kiyi tunani kada ki dinga bari yara suna miki wasa da xuciya."

"Thank you sir"

Ta fad'a a k'agauce.

Ba wai nasiharshi ce bata d'auka ba,amma ta yaya zaice wai tabar soyayya?!

*Hafsah da dad'i wallahi kicigaba*☺

Na biyu kuma fadan da abbansu yai mata yau d'in, wanda ya zamo na farko a tarihinta.Ita yabo kawai ta sani a al,amran karatunta, amma yau gashi Abba da kanshi ya kushe k'ok'arinta?🤔

na uku kuma wayar da sukayi da yusuf d'axu. Duk ciki shine taji zata iya yin tunani a kai,ba wai fad'an abba ko tunanin gyara akan karatunta wanda amma yi musu dogon hutu har na sati hud'u ayau.

Ta mik'a Hannu ta d'akko wayarta ta danna numbobinshi sannan ta kira.

wanna Karon sunan daya bayyana shine 'My dream'

ba,a d'aga wayar a kira na farko, sai a Kira nabiyu wanda aka d'aga wayar sannan akayi shiru daga can b'angaren (ba,ayi magana ba) 

Ita ce ma tace "Dear am sorry kaji!?

(sai yanxu yaga damar yin magana)

"For what "? ba kedai baki da time ena ba,? "Nima Yanzun am busy doing something important than receiving your call."sai anjima kinji? "

yayi saurin katse wayar.

"Oh my God! 

"Me yasa haka yusuf? 

Tama rasa abinyi, ita dai tana cutuwa da wannan saurin fushi na yusuf, shi dai kome yakeso shi za,ayi mishi.

Ta tsorata da fushinshi na yanzu, don haka ta kuma danna kiranshi har tagama ringing ba,a d'aga ba,amma karo na biyu kuma da ta sake kira yai rejecting d'in kiran..

Tayi cilli da wayar tayi shiru, wani zafi zuciyar ta ke mata.

tana ta hura iska daga bakinta a hankali, ta fad'a a fili "Am so sorry my yusuf bana son b'acin ranka, me yasa kake fushi da nine..? 

Ta kuma daukar wayar dole ne ya mishi text na ban hak'uri don tasanshi fushinshi zai iya d'aukansu wani lokaci mai tsaho, idan batayi da gaske ba.

"U mean everything for me kasan kuma you're my only one..

I can't sleep bayan kana fushi da ni. 

am sorry ba ina nufin b'ata ranka bane. d'axun mama ce ta kirani.

kayi haquri please!"

Tana gama typing d'in ta tura mishi ko k'ara karantawa ba tayi ba.

kusan mintuna biyar sannan delivered message ya shigo.Tayi ajiyar xuciya bata saka ran reply ba don tasan bazaiyi ba...Amma taji sanyi aranta, sai yanxu takejin zata iya yin bacci...

*"Hmm Hafsah kenan er Soyaya*

😜

[1/11, 12:09 AM] Hajeeyah Karimah (Writer): ♥♥♥♥

*ZAZZAFAN SO*

(Guba ne)

*A broken* 

*heart story* 

  💔💔


Story and writing by:

*Karima Tijjani Mansur* 

*(Hajeeyah Kareemerh)*


*Dedicated to:*

*Unique In Your Love Heart Members*




📄 *4*



*Wanene yusuf ne da Hafsah ta damu akanshi haka*??


Yusuf Aminu kyakykyawan matashin saurayi ne d'an kimanin Shekara 27 yaro ne dangata wanda ya taso cikin gata gaba da baya.

Mahaifinshi professor ne wanda yake kan ganiyar shi,bayan yayi aiki a Nigeria na en shekaru, sannan ya sami aiki a k'asashen waje inda yake lecturing a jam'i,ar akasar 'California'.

Mutum ne shi daya zaga k'asashen duniya k'asashen ma irin na turawa, saboda haka al,adunsu sun zauna mishi sosai, hatta shigarshi yafi yin irin tasu, fiye da irin ta 'hausawa'.


Ya hadu da Matar shine Layla a k'asar Canada..lokacin tana qoqarin hada digirinta a fannin 'business' wato (kasuwanci).Budurwace ita y'ar kimanin shekara 27, a lokacin.

Ta taso cikin gatan mahaifiyarta,wacce Itace ke daukar duka nauyinsu ita da k'anwarta kasancewar mahaifinsu ya rasu tun bata fi shekara goma ba a duniya. Koyarwa mahaifiyar tata keyi,Wanda da wannan albashin suka dogara.sai tallafi da takan samu daga 'yan uwa da kuma zawarawanta. Bayan layla ta kammala karatune sukayi auren ita da professor lokacin ya dawo Nigeria daga Canada, babu jimawa kuma,suka tafi london, inda acan aka haifi yusuf daga baya kuma suka dawo California.kafin su dawo Nigeria gaba d'aya bisa umarnin mahaifiyarshi na 'ya zauna cikin danginshi kusa da ita.' tunda shi kada'i ta mallaka.

Yusuf ya taso cikin gata domin shi kad'aine iyayenshi suka mallaka, ya samu gogewa da dabi,un turawa, domin acikinsu ya taso. 

Mahaifiyarshi sam bata kwabarshi,aganinta abar yaro yayi abinda ranshi keso shine 'Yanci'.

Ta bangaren ilimin addini kuwa a iya cewa yusuf bai wani abu sami abin azo a gani ba. Shima bayan dawowarsu Nigeria ne 'Dada' wato kakarshi ta wajan Mahaifinshi ta matsa suka kaishi wata islamiyya.sannan ta ta kan matsa mishi da tambayoyi akan addini kuma tana koya mishi wadansu abubuwan. 

Bayan dawowarsu Nigeria ne da shekara uku Allah Yaiwa kakar tashi rasuwa.alokacin kuma yusuf ya kammala karatunshi na secondary. Yusuf yasan yayi rashi sosai, domin duk sanda aka musu hutun makaranta wajanta yake xuwa inda ta sanya shi dole yake xuwa makarantar dare.A wajanta yusuf ya koyi wadansu daga cikin al,adun hausawa kamar gaisuwa,da kuma yanayin shigarmu (ta hausawa) yakanyi ne saboda sha,awar hakan.

Bayan wasu watanni ne kuma aka samar mishi gurbin karatu a jami,ar California inda zai karanta engineering.

*yusuf a sauka Lpia* ✈

[1/11, 12:09 AM] Hajeeyah Karimah (Writer): ♥♥♥♥

*ZAZZAFAN SO*

(Guba ne)

*A broken* 

*heart story* 

  💔💔


Story and writing by:


*Karima Tijjani Mansur* 

*(Hajeeyah Kareemerh)*


*Dedicated to:*

*Unique In Your Love Heart Members.*





📄 *5*




*Sun* hadu da Hafsah ne da a rana wata litinin d'in watan August wacce ta kama daya ga wata. A safiyar ranar anyi ruwa sosai kafin xuwa hantsi ya dauke. 

Su hafsat sun sami damar xuwa makaranta a ranar wanda driver (Nura) wanda babansu ya ajye musu yake kaisu makarantar a wata motarsa data d'an kwana biyu HONDA CARINA.

Uzurin daya tare driver ga barin xuwa d'aukar su yasa hafsat jan hannun k'annenta. Bashir da Zainab wa'yenda suke 'Secondary' wanda ya samu yaxo daukar Amira (k'anwarsu) wacce take a primary kuma ana riga tashinsu. 

A jere suke a bakin titi suna jiran su tsayar da 'adaidaita sahu' su hau. Duk yunwa ta damesu, ga gajiya, ga kayan Jaka da suka goya da iyayen littattafai a ciki.

Hafsah taja tsaki "Mts" sannan tace Bashir niko mutafi a k'afa ne?

Bashir ya kalleta "yaya a k'afa kuma ?

Eh mana na gaji kuma yunwa nakeji"

Bashir yace nima haka wallahi,amma ai da nisa koh?

Ya Kalli Zainab yace "wai muje a k'afa"? Ta cuno baki "A,a ni dai gsky."

Suna cikin haka wata mota taxo ta wuce ta gabansu. Har tayi gaba sai aka dawo, daidai saitin Hafsah aka tsaya aka zuge glass d'in motar wani matashin saurayi ne aciki wanda baxai wuce shekara 26 zuwa 27 ba. Ya dan lek'o yace "kinga wa kuke jira ne? 

Hafsah ta Kalle shi ta kau da kai. Ya kuma cewa "Haba dake fa nake kika yi min shiru". Yana rufe baki Zainab tace "kaga mota muke jira, driver baixo daukar mu... Hafsah taja hannunta sukai gaba tana cewa "ina ruwanki da shi"? Ya kuma matsowa dai dai saitin su yace "kunga kuzo in kaiku"

Ta d'an daure fuska tace "A,a mungode" sai suka had'a baki ita da bashir wajan fad'ar hakan,wanda sai alokacin shi yayi magana.A daidai lokacin kuma bashir ya tsare musu wani daidaita suka shige da sauri...

Shima ko baiyi wata -wata ba yaja motar shi ya bi bayan abin hawan da suka shiga .kofar d'an wani madaidaicin gida aka sauke su. Anyi wa gidan k'awa da adon fulawoyi a gefenshi sai farin gate da ya haska gidan ga futulun kwai masu kyau wadanda suke walwali da dare sun k'awata bangon gidan. Hafsah ta mik'a mishi kud'inshi tun kafin su fito, suna fitowa sukayi wuf suka shige ciki basu lura da wani na shirin yin parking a k'ofar gidansu ba.

A parlour suka cillar da jakunkunan su cike da yunwa da gajiya.suna mitar yau Nura ya shanya su. 

Mamansu tace "A,a ku bazakuyi wa mutum uzuri ba? Yanzu da kuka dawo mai ya sameku? Kuzo kuci abinci kuyi sallah ku tafi islamiyya."

A k'ofar gida saurayin murmushi ya saki bayan sun shige zuciyar shi cike da murmushi, da alama gidan babu maigadi da ya mishi wata tambaya. 

Ya gyada kai yaja motar shi yayi gaba.


*WASHEGARIN*

*RANAR*

*DA YAMMA* 


misalin k'arfe shida na yamma dawowarsu Hafsah kenan daga islamiyya sunzo zasu shiga gida. Mufida har ta tura gate sukaji anyi musu horn.

Hafsah ta juya mota ce a gefensu, suka share zata shige kenan taga ya taho yana nufo ta. Chak ta tsaya yayin da k'annenta tuni sun shige gida.


*Ni ko nace Hafsah meye na tsayawa kuma*😅


Cikin wata irin tafiya yake takowa, wacce bazakace sauri yake ko kuma yanga ba.

Ta k'ara gyara zaman jakar dake kafadar ta. Sai lokacin taga rashin alfanun tsayawarta.

"Ashe harma ya iso wajenta..🤔

"Sannunki Koh?

Shine ya tabbatar mata isowarshi kusa da ita. 

Ad'an daburce tace "Am um yawwa"

Ya matso daf da ita wanda sai da numfashinta yai sama ya sauka.

"Nine yusuf. Am kuma na ganku ne jiya lokacin kuna cikin uniform har nayi miki magana amma kika yi ignoring me"

Ta dan yi shiru tana wasa da yatsun hannunta. Ba wai nasiharshi kasa tuna jiyan bane, sai dai kawai yanayin hausarshi yasa ta kasa fahimtar rabin zancen.

"ko ba kene bah?"

"Nice mana" 

"Gud"

"ya sunanki ma?

"I mean your name"

A zuciyarta ta d'an dara, wanne yaren ne zai fassara mata wani?

Hausar ce zata fassara mata turanci ko kuma turancin ne xai fassara mata Hausar..?

"Ina ga ba bahaushe bane.."

ta fad'a tare da jin wata mummunar fad'uwar gaba ganin motar abbansu na nufusu....

*I need your comment to encourage me!*👏🏼👏🏼

urs a kullum *(Hajeeyah Kareemerh)*

[1/11, 12:09 AM] Hajeeyah Karimah (Writer): ♥♥♥♥

*ZAZZAFAN SO*

(Guba ne)

*A broken* 

*heart story* 

 💔💔


Story and writing by:


*Karima Tijjani Mansur* 

*(Hajeeyah Kareemerh)*


*Dedicated to:*

*Unique In Your Love Heart Members.*


*Godiya ta musammaman Gareku unique ladies dama littafin naku ne, haqiqa ina alfahari daku*


*💋Hajara madaki* 

*💋Salma*

*💋Aysha yahya*

*💋Pheenah*

*💋Shamsiyya Abdullahi*

*💋Jamila Kd*

*💋Fateemah target (Teemah)*

*💋Hawwancy*

*And so on kunsan kanku*👏🏼




📄 *6*



*Alhaji* Habib Hamid kenan Director a Ministry of work housing and estate ta jihar Kano.


Ya iso ya gifta su yana binsu da kallo daya bayan daya. Mamakin ganin hakan yake.


Ya fito ya tura gate d'in sannan ya shige ya barsu.

"Am kinyi shiru koh"? Yusuf ya fada yana kallonta.

Ta d'an k'ak'alo murmushi sunana "Hafsah"

"Nice,sunanki yamin dad'i"

"OK ,nagode to"

"Zan shiga gida, abbanmu ya dawo"

"Bani phone number ki"

"Bani da waya ai"

Ya zaro mata ido "Baki da waya hmm"

"Da gaske fa"

"Ok"

"Sai anjima"

Ta fad'a sannan ta juya ta shiga gida cike da fargaba.

A falo ta tarar da dukka en gidan nasu, har da mamansu sai dai bata ga abbannasu ba sabda ya shigo wanka. Ta nemi waje ita ma ta zauna tana satar kallon mamansu ko zata ce mata wani abu. Amma taga ita hankalinta ba,a kanta yake ba. Suna jin motsin fitowar abban kuma maman ta tashi ta barsu a falon ta wuce bed room.


To har wajen isha'i babu wani sak'on kira daga abba, don haka Hafsah ta saki jikinta tana harkokinta zatonta ko ya manta ne.

Ta Kalli k'annenta da duk hankalinsu ke kan TV dake falon tace "Ku d'akko Assignment d'inku mana."

Nan suka mik'e harda rige-rige.

Nan ta hau nuna musu yadda xasuyi,sannan ta basu lokaci su gama su bata ta duba.

Littafin zainab ta karba taga duk tayi shirme.

A karo na uku ta kuma nuna mata ta kasa. Ran Hafsah ta b'aci sai ko takai mata duka,ta sameta a fuska.Aiko ta kwalla ihu.

Kukanta abbansu ya jiyo shi da mama wadanda suna falon abban.

Dukkansu suka nufo d'akin 

"Zainab me akai miki? Abban ya fad'a yana kallonta.

kafin tayi magana Amira tace abba yaya Hafsah ce ta dake tana ana ta nuna mata yadda xatayi assignment ta kasa, nifa har na gama nawa".

Ya d'an yi shiru, kafin yai magana Mamansu ta saka baki "Au shine zaki dake ta, bada koyo ake iyawa ba?"

Ta fad'a tana kallon Hafsah. "Mama wallahi fa ko a makaranta wasa take."

Abba ya Kalli maman kamar zaiyi magana sai kuma ya fasa. ya wuce ta nufi falonshi. Itama Maman binshi tayi ta zauna kusa da shi. Ya kalleta ahankali yace "Amma dai kinsan halin Zainab d'inkoh?

"Bana son tana dukansu ne"

Ki daina yi mata fad'a a gabansu,sai su rainata ai. 

Ya fad'a ya juyar da kai gefe.

Ta kalleshi "To na daina in sha Allah"

"Ayi haquri"

Ya juyo yana murmushi "Nace kinyi laipi ne? 

tayi dariya "ai an tab'a maka 'yar lelenka." Yai dariya 

"Haka kika ce kenan."

Ya kwalawa Zainab kira. Ta zo 

Tayi sallama sannan ta durk'usa.

"Abba gani"

Ya d'an tsare gida

"Ke ba kya ji Koh? 

A haka kike son zama doctor d'in kina wasa? 

Cikin muryar mai son yin kuka tace "Abba ba wasa nake ba"

To me yasa ba kya Mai da hankali, kina so ace sunfiki k'ok'ari Koh?

"Kayi haquri Abba"

Ya d'an sassauta murya

"To ki daina wasa kifisu ko'kari kinji ni nasan abinda xan baki"

"Kije ki ba yaya Hafsah haquri, kuma kice nace tazo"

"To abba"

ta tashi ta fita.

Hafsah taji kamar fad'uwar gaba da Zainab tace kije inji Abba.

Ta d'an zauna a d'osane. "Abba gani"

Ya zubo mata ido.

"Me kika tsaya yi a k'ofar gida d'axu? 

"Babu komai abba"

"Babu komai? 

"Um"

"Wa na ga kina ma magana."??

Ta kwaso in'ina tace

"Am wa wai cewa yayi tambayata zai yi."

Ya jinjina kai.

"Ki daina kawai daga yau, kinsan na hanaki kula samari Koh?

"Allah Abba ban sanshi ba"

"Ya isa tashi kije na dai fad'a miki."

Kuma kuyi addu,a kafin ku kwanta.

"To mama sai da safe"

"Allah tashe mu lpia"

Ta baro falon cike da Murna. bata zaci fad'an abba zai tak'aita a iya haka ba....

*Need your comment to encourage me* 👏🏼👏🏼

*Idan anga kuskure ayi haquri ajizanci na d'an adam.sannan ni sabuwa ce a wannan fage!*


*HAJEEYAH KAREEMERH ce dai*👌

[1/11, 12:09 AM] Hajeeyah Karimah (Writer): *ZAZZAFAN SO*

(Guba ne)

*A broken* 

*heart story* 

 💔💔



Story and writing by:


*Karima Tijjani Mansur* 

*(Hajeeyah Kareemerh)*

*Dedicated to:*

*Unique In Your Love Heart Members.*



📄 *7*


*A WANI B'ANGAREN*


wani madaidaicin gida ne na k'asa, acikin wata unguwar da kai tsaye za,a kirata ta talakawa.

Wata budurwa ce wacce baxata wuce shekara 17 ba (sa,ar Hafsah) ta fito daga d'aki sanye da uniform na makarantar gomnati a jikinta.

Ta leqa d'akin babarsu wacce ke zaune ita da uban a d'akin "umma zan tafi"

Ta tab'e baki "Sai kin dawo." 

Ta Kalli babannata Baba kud'in makaranta?

"Bani da shi"

Kai tsaye ya fad'ar

ta langab'ar da kai tom na tafi"

"Shashashar banza! 

Dama zama kikai kina mata tallan kunun da kun sami kud'in kashewa, mtss wai ke 'yar Boko!

Ita dai ta fita cike da takaici.

Tana fita titi ta hango motar su hafsah na tawowa xa,a kai su makaranta.

Hafsah ma ta hangota tace wa Nura "Don Allah kaga Jamila can mu d'auketa yace "Tom."

Suna parking ta bude motar ta shiga.

Bashir kusa da driver sai Hafsah, Zainab da Amira a baya.

Hafsah ta kalli jamila "Ya naga idonki yai ja?"

Hawaye ya zubo mata "Babu komai.

"Kiyi hak'uri"

Inji hafsah. 

"Na gaji wallahi Hafsah wai Salim ma... Sai ta sa kuka..

"Ki daina sanya damuwa.

Daidai lokacin anxo k'ofar makarantar su jamila.

Hafsah nagode yau xan shigo da wuri kafin lokacin islamiyya.

Ta fad'a tana goge fuskarta..

"Tom jamila" ta mik'a mata wata leda snacks ne aciki da ake musu gida saboda zuwa makaranta.

Ta karb'a tayi godiya 

Ta bude motar ta fita. 

Hafsah ta girgiza kai cike da tausayin jamila.

Mufida ta Kalli Hafsah "yaya wai wannan k'awarki ce? 

"Eh"

"Amma naga uniform d'inta duk squizing?"

"Ke ina ruwanki?

cewar Hafsah.

Ahaka har suka isa makaranta, driver ya sauke su. Hafsah ta nufi ajinsu SS 2, Bashir SS 1, Zainab Jss 2, Mufida primary 5.


Bayan an taso kuwa babu da'd'ewa jamila tazo gidan. 

Yau mama bata nan.

Suka k'ule a d'akin hafsah.

"Hafsah. Rayuwar gidanmu na bani mamaki kamar ba gidan iyayen da suka haifeni ba.

Don kawai ina da son karatu? 

Ta d'anyi shiru sannan ta d'ora.

Duk gidanmu babu wanda ya zarce primary yaya Habu, yaya jamilu Babu abinda suka sani sai shaye-shaye. 

Ahaka rayuwar su rukayya ga su shafi,u (k'annenta) xata cigaba? ko fa makarantar allo basa zuwa... Kinga banda 'yan d'akinmu ga 'yan d'akin su Ummi Banda talla da yawo..

ya isa jamila komai yai farko zai yi k'arshe ki ci gaba da addu,a Allah ya taimake ki ki ci qualifying."

"Allah yasa hafsat"

"Rayuwarku na ban sha,awa iyayenku masu kud'i...

Hafsah ta d'an dake ta a baya "Kinjiki" "ke ina salim"?

Hawaye ya ciko a idanunta 

"shekaranjiya ya zo yace min Mamansu tace wai 'yar k'anwarta zai aura... Ta fashe da kuka..

"Ya salam"

inji hafsah.

Hafsah ina son salim, wallahi tunda aka rabamu ji nake bani da wani sauran buri a rayuwata. Kinga duk da shi d'an masu kud'i ne (rufin asiri) yana sona har cewa yayi zai d'auki nauyin karatu na, duk da talaucina ahaka yake sona, amma an raba ni da shi... Bikin nashi ma baifi wata biyu ba.. ta kuma fashewa da kuka..

Hafsah ta d'an daddaki bayanta kiyi hak'uri ki dinga addu,a Allah ya baki wanda ya fishi.

ki daina kuka kinji...

Hafsah ta mik'e ta zubo musu abinci shinkafa da miya da Naman kaji fal,

"Ki tashi ki wanko fuskarki ki zo ki ci abinci"

Cewar Hafsah tana ajye plate d'aya agaban jamila..

ta mik'e ta shiga toilet don yin yadda Hafsah tace..

Suna cin abincin jamila tayi wani murmushin takaici tace "Rabon da Inci nama wajan wata d'aya kafin salim ya daina zuwa wajena... Kin san har 'yan rahoto ne da babarsu a unguwar mu wanda in yazo ake xuwa a fad'a mata"

Hafsah tace "tab"

Akwai Sa,idinai"

Hmm abinda ya sa ma yaxo jiya ya fad'an kada inji labarin bakinshi a gari (hawaye ya xubo mata) ta girgiza kai "Allah sarki salim d'ina wai an raba mu?? 

"Wai aure xai"?

Ta kifa kanta kan gadon Hafsah.. 

Hafsah ji sakwato tana kallonta mamaki abin ya bata 'tana cikin cin abincinta kuma sai kuka??

"Jamila don Allah ki cire shi a ranki!'

Kamar an tsikareta ta d'ago cikin hawaye tace "Hafsah baki san so ba shiyasa. Banjin xan tab'a daina son salim har abada..

Naji ki k'arasa cin abincin mu tafi islamiyya kinga lokaci ya k'ure."


Ta fad'a batare da ya bawa furucin jamilar na k'arshe muhimmanci ba don bata ga wani abin damun mutum ba alhalin uwarshi bata so!

Abu d'aya maganar tata ta tuna mata 'Saurayin da yazo jiya'

Ta d'an tab'e baki,sai kuma tayi murmushi da ta tuna hausarshi..

Aiko suna fita suka ganshi a k'ofar gida aiko ya nufo su..

Hafsah ta cake ta tsaya "yan mata"

Ya fad'a ad'an tsorace tace

"wai kai meye ne?

"Gobe ne zan koma schl kuma bamu sami time na magana ba koh? 

Ta k'ank'ance ido ta Kalli jamila.

ita dai jamila tayi kasa fahimtar su.

"Am kaga please kada ka k'ara xuwa wajena kaji? 

ya waro ido why, please baby why..? 

"am tawo mu tafi"

ta jawo hannun jamila,suka fara tafiya.

yabi bayansu 

"plz baby when kike so naxo?

Hafsah ta juyo tsoro take kada yau ma Abba ya ganta 

"I don't know!

suka cigaba da tafiya yana binsu a baya har suka kusa zuwa islamiyyar.

jamila tace "Hafsah wannan baturen naki bai bar binmu bafa?

"shi yaga zai iya"

"Aiko Hafsah wannan ba kalar wukak'anta wa bane "

"Mts to me zanyi mishi?

to ki Sallame shi don Allah"

dai dai lokacin ya kuma cewa

"Please baby yaushe xan dawo?

cike da shak'iyanci tace "Sai bayan wata bakwai

"Mene kika ce? 

"after seven months ehe. 

suka shige cikin makaranta suka barshi yana kallonsu.

yayi murmushi ya juya zai koma k'ofar gidansu inda ya bar motar sa.

ya tafe yana tunanin gobe zai bar k'asar don k'arasa karatunshi wanda zai d'aukeshi wata bakwan da ta ambata mishi.

yayi murmushi 

"I will come back to you again!...


*Hajeeyah Kareemerh ce*

*I need your comments to encourage me!*👏🏼👏🏼

[1/11, 12:09 AM] Hajeeyah Karimah (Writer): ♥♥♥♥

*ZAZZAFAN  SO*

 (Guba ne)

*A broken* 

*heart story* 

 💔💔



Story and writing by:


*Karima Tijjani Mansur* 

*(Hajeeyah Kareemerh)*



*Dedicated to:*

*Unique In Your Love Heart Members.*



Wannan page naki ne aunty nah *AYSHA NIGER* ALLAH YABAR ZUMUNCI AMIN😘




📄 *8*


*BAYAN WATANNI BAKWAI*




*A* bubuwa da yawa sun faru cikin wad'annan watanni bakwai a rayuwar Hafsah, yusuf da kuma jamila..

Yamma ce mai cike da ni'imar hazo daya mayar da yanayin garin kamar hadari, kamar kuma duhun magriba..

Tafiya Hafsah take yi cikin rashin kwarin jiki, kana ganinta kasan akwai rauni acikin zuciyarta..

Ta tura gate d'in gidan su ta shiga.

Bayan tayi sallama tare da cewa "Mama na dawo"

(yau su bashir sun rigata dawowa)

Kasancewar daga islamiyya take..

D'akinta kawai ta nufa, don alokacin babu abinda take so sai kad'aici..

Ta ajye Jakarta a ma,adanarta ta cire hijabin sannan ta sauya shigarta daga uniform zuwa, 'yar doguwar riga mara nauyi.

Ta kwanta akan gadonta shiru tayi, wani abu take son tunowa na kamar shekaru biyu baya...

Ahankali ta rufe idonta tana tuno lokacin.


*HADUWARSU DA JAMILA*


Wata rana suna tafiya ita da bashir an taso su daga islamiyya, ranar kawai sai suka biyo ta wani layi..

Sunzo daida k'ofar wani gida wata ta fito da gudu daga gidan da bokiti akanta (ruwan garai) kullin kunu ne aciki.

Zasu gifta ita kuma ya fito aiko sai ta tank'ad'e bashir, saura k'iris ya fad'i..


"Kai Kai Kai"..kika bugeni?? 

Bashir ya fad'a yana mata kallon k'askanci.


,"Don Allah kuyi haquri wallahi biyo ni akayi ni bana son tallar nan.."

"Mts"bashir ya ja tsaki. 

Hafsah ta kalleshi "Haba bashir ka hak'ura mana.. 


"Hmm, kina ga ta buge mutane..hmm

Shikenan dai."

"Ta Kalli Hafsah tayi murmushi da hawaye a fuskarta. 

Ina son islamiyyar nan taku, nima xan tara kud'i in shiga."

"Tab da kud'inki sai kace baki da iyaye?? 

Yusuf ya fad'a cike da izgili. Hafsah ta harare shi, Kai bashir ina ruwanka?

Sai da suka isa titi suka rabu tace wa Hafsah "In sha Allah. xan shigo islamiyyarku ina so ki zama qawata"

Hafsah tai mata murmushi. "Shikenan to bye bye".

Da suka isa gida bashir ya fad'a wa mama Wai "yaya Hafsah ta zama k'awar mai kunu. Sai da ta taka mishi birki sannan ya daina tsokanarta.

Ba,a fi sati biyu ba aka kawo jamila islamiyyarsu Hafsah cikin sa,a kuma ajin su hafsan aka kawo ta.

Hafsa na son jamila sosai, duk da haka fahimci jamila 'yar talakawa ce amma tana da k'ok'ari da son karatu.

"Zan dinga zuwa gidanku kina koyamin turanci, ni makarantarmu ba,a mana.."

Cewar jamila, lokacin da suke tafiya bashir yai wa Hafsah magana da turanci

"wllhi yaya, am tired!"

Hafsah tace "To sai dai alhamis da juma,a bayan an taso daga makaranta Koh? 

"Eh"

"Ajinki nawa inji hafsah"

Jss 1 nke

Nima haka "we are d same."

Jamila tayi murmushi.

Tun daga ranar jamila ke xuwa wajen Hafsah duk ranar alhamis da juma,a, mama tun bata so harta hak'ura dama abba bai san da ita ba.

Azuwan da take ne in suna hira take bawa Hafsah labarin gidansu.

'Shidai mahaifinta irin mutanen nan ne 'yan gargajiya da babu ruwansu da harkar addini balle Boko.. 

Ya tara 'ya'ya a kallah 23,da mata uku.. Banda wadanda suka shigo suka fita. Mahaifiyarta, kuma irin matannan ne wad'anda suka d'auka cewa amfanin 'ya mace a wajensu shine 'ta nemo musu kud'i.'

Jamila yarinya ce mai hazaqa da baiwa(ko wanne d'an Adam na da baiwa)

Yawancin yaran gidan talla suke yi inda iyayen su mata ke d'ora musu. Jamila ta tsani talla shiyasa tayi bak'in jini gurin mahaifiyarta.

Yawan shige shigen mak'ota da kwad'ayi halin yan gidansu ne saboda basa wadata da abinda ake basu. 

Jamila naso taga rayuwarta ta chanja kullum burinta Allah ya sa ta xama mai kud'i. Tana da himma ko wajen karatu takan zo ta biyar ko ta shida, akwaita da son kwaikwayon abinda taga wani yayi ya burgeta imma a film ko a rayuwar xahiri. Amma dake iyayenta basu da damuwa kan cigaban rayuwar 'ya'yansu basu lura cewa jamila 'Kadara' bace! ko abar a lura da karatunta bace.

Tana primary 6 aka kawo musu wani Malami d'an Tp. A irin surutun jamila ya gane irin rayuwar gidansu haka yasa ya sanya a ransa xai kaita gaba da secondary. Ya ko kaita..

Wanda haka ya q'ara jawo tsanarta a wajen iyayenta kiri-kiri xa,a ce ta d'auki tallah tace ita dai makaranta xata. 

Mutsiyaciya! 'yar iska ni halin wannan yarinya kamar bani na haifeta ba! 

Iri-iren aubun da take samu kenan daga bakin mahaifanta duk da ba ita kad'aiba kowa ma agidan yanayin laifi bai wuce a dake shi ace "tsinannen yaro, shege Mutsiyaci! 

Ai ko tsiyar na binsu tunda duk yaran babu na mora. 

(iyaye a kula da furuci ga 'ya'ya)

A hakan jamila ke rayuwarta cikin k'unci har lokacin da ta shiga Jss 3, inda suka had'u da 'salim' yana taimakawa rayuwar karatunta sosai tana matuqar sanshi har xuwa lokacin da aka rabasu.. take fad'awa Hafsah..

"Nifa Hafsah xuciyata tayi k'ek'ashe, duk gidanmu babu wanda ake ganin d'abi iska sai ni.. Bayan ga yayyena mata nan duk suna yawonsu abinsu, amma wai ni ake cewa salim ya lalata shiyasa yake kashe min kud'i akan bokon k'arya.."

Wallahi Hafsah in kinga yadda in salim yazo baba ke korarsa sai kin d'auka bashi da zuciya a k'irjinsa shiyasa yake dawowa"

Ni ba wannan ba ma aibun da suke ja min "Wai in je indai duniya ce xan gani!"..

Wallahi idan suna min kallon 'yar iska ji nake kamar in bar gidan in tabbatar musu da hakan!!

"Ke jamila don Allah ki yi ha'kuri ki saba da irin wannan rayuwar kada ki k'ara ja wa kanki masifar yawon duniya.."

Shikenan Hafsah amma wallahi rayuwar gidanmu na rasa da sunan da xan kirata, ace babu wanda zai fahimceni? Babu mai gane cewa ina son kawo mana sauyi ne? Ta fashe da kuka.. Kinga ya Habu duk da yana shaye-shaye shi kad'aine ke tausayin yana cemin

"ai su baba ne ya cucesu,tun farko ba ruwanshi da makarantarsu sai dai daga yaro yayi 15 yace ya cire mishi kwano daga gidan ya fita ya nema.. "Gsky kiyi karatu "a dama da ke kema!! 

Haka fa yake fad'an Hafsah..

"Allah y kyauta.. Abin Hafsah ke iya fad'a kenan idan jamila tana mata halayyar k'orafin gidansu, don bata da abin cewa d'in... in ba haka ba.

...Yanxun da take tunanin nan wani labari ta jiyo a islamiyya '

wai Jamila tayi cikin shege babansu ya koreta'

Xata iya tuna rabonta da jamila wata d'aya kenan bata xuwa islamiyya kuma bata xuwa gidansu.. ita kuma Hafsah ba xuwa gidansu take ba, mama ma ba xata barta ba.

A yadda aka bata labarin wai cewa akayi jamilar wani malaminsu ne a makarantar boko suke soyayya har ya yi alk'awarin kawo mata kud'i..to kuma sai yace xai biya mata kud'in Waec da Neco don bataci qualifying ba. Ance har fita sukeyi da ita da shi..

Labarin dai ruwaya kala-kala.

A iya sanin Hafsah jamila ta fara bata labarin 'sir Garba' bayan kamar wata d'aya da bikin salim.. 

"Hafsah yanxu wani malaminmu ne yake so na,kuma yana da mutunci saurayine black beauty, kuma ya Had'u,Allah sai naji duk ya sa na manta da tabon da salim yai min.."

"Allah ya tabbatar da alkhairi"

Abinda Hafsah tace kenan.

Bayan haka kuma jamila tazo mata da k'orafi..

Hafsah sir ya fiya wayewa da yawa "ko dan English ya karanta?.. bai da buri sai na ya rik'e Hannuna, ko yace na mishi kiss!!"

"What?? 

"Jamila ki rabu dashi"

Tai mata kallon rashin fahimta 

"Tab Hafsah kin san son da nake mishi kuwa..?

Wallahi ko baba wannan karon baxan yarda ya tabani da 'Sir Garba' ba, d'an gayu nah"


Shikenan jamila ni na rasa me kike ji a soyyaya"


"Haha Hafsah, yaushe xakuyi biki ne a familynku ina son bikin 'yan gayu wallahi"


Hafsah ta harareta "ke mayyar biki ce!"



Daga lokacin halayyar jamila ta d'an so ta chanja Don 'idan Hafsah ta lura jamila ta rage fad'a mata tsakaninta da sir, sannan ya sai wa jamilar waya, kuma xa,a ganta cikin kaya masu kyau, Wanda da Indai ka ganta da suturar arziki to kwancene Hafsah ta ba ta..

Hafsah ankawo wata yarinya ajinmu SS 2 d'innan kanta na hayaki..bata kallon kowa da gashi kinganta kuwa tasha bleaching..Amma ni kuma muna mutunci da ita. 

Gata komai taxo dashi sai ta bani kamar dai yanda muke dake.. 

"Hmm Hafsah tace.

Hafsah wai don felek'e yarinyar nan har tambayata take wai  "Ance wancan Malamin saurayinki ne?"

ni ko nace mata ''eh mana"

"Wai keko me kika gani mai xai Baki? "

Niko nace "bansaniba" 

shine harda ban hak'uri yanxu ko da ita muke xuwa wajanshi ma?

"Wajanshi kuma? 

Eh mana karbar pass questions muke xuwa."

yanxu kuma tace min 

"Wallahi bai da aibu musha soyyarmu"

To tun daga ranar jamila bata kuma xuwa gun Hafsah ba yau wata d'aya kenan..

Kiran sallar da ake ne ya dawo da ita daga tunanin da yasa ta jik'e sharkaf da gumi.. Me yasa sai yanxu? Saida jamila ta fara tasawa a sha,anin rayuwa sannan xata b'ata rayuwarta..?

Sai da taci fiye da rabi na gwagwarmayar ta sannan xata b'ata shirinta? 

Duk wad'anda suka taimaka mata abaya bata basu kanta ba sai shi??

Ita ko bata ga amfanin soyyayya ba tun da bata da rana.. Ta share hawayen fuskarta ta tashi ta d'akko Diary d'inta ta fara rubutu acikin cikin k'unar xuciya da takaici. 


*The day I will never forget*


Haka ta rubuta sannan ta cigaba da rubutun..

Mamansu ta turo k'ofar d'akin "Au na dauka a kwance kike.. To anyi sallar magariba ma ki ajiye shirmen nan.

"To mama"

Ta rufe ta Mik'e ta shiga toilet tayo alwala, tasa hijabi ta tayar da sallah..

Ta da'de tana addu,a bayan ta idar har da hawaye, ta nemi dalilin aikata haka da jamila tayi ta rasa don aganinta 'Talauci ba hujja bane.'

Tana zaunen kuma tana tunane - tunane barkatai bashir ya shigo cikin magana kamar rad'a yace "Yaya Hafsah yanxu xan shigo gida wani d'an gayu yace in kiraki don Allah"

Ta zaro ido ta dafe k'irji "Ni kuma bashir.?

"To waye? 

Ya had'u fa gayen, ki fita ki gani tunda abba baya nan..


"Ni irin motarshi cema tamin." Ya fad'a yana dariya..

Ta shige toilet kamar antsikareta ta wanko fuskarta 

Ta chanja doguwar rigarta xuwa b'akar after dress mai kauri ta yafa bakin mayafin abayar ta fesa turare..


Tana fita falo ta hango mama acikin kitchen (kitchen en a falon yake)

Kamar mara gaskiya sai ta tsorata da suka had'a ido..

Ina zaki daga yin magariba?

cewar mama da ta d'an hade rai..


*I Need your comments to encourage me!*👏🏼

[1/11, 12:09 AM] Hajeeyah Karimah (Writer): ♥♥♥♥

*ZAZZAFAN SO*

(Guba ne)

*A broken* 

*heart story* 

 💔💔


Story and writing by:


*Karima Tijjani Mansur* 

*(Hajeeyah Kareemerh)*


*Dedicated to:*

*Unique In Your Love Heart Members.*



📄 *9*



*"Am* mama gidansu Ummi xani wani littafi zan k'arbo."

"To kiyi sauri ki dawo "

"Tom mama"

Ta fita cike da son ganin wanene wannan yake nemanta da farar magriba..

Tana tura gate ta hango motar a gefen dama na gidansu..

Motar ta had'u kamar yadda bashir ya fad'a mata.

An d'an bude murfin motar. Na ciki ya d'an fito da k'afarshi waje.. 

B'akin takalmi ne a k'afarshi da farin jeans.

Ahankali take takawa har ta isa kusa da motar. 

Shiko hankalinshi na kan wannan wayarshi yana latsawa..

Ta d'an tsaya na kamar minti 1,sannan cikin sassanyar murya tace 

"Assalamu alaykum" 

Hakanne ya sa shi d'agowa ya kallo gefen da take..

Farin kyakykyawan saurayi,mai manyan idanuwa, dogon hanci gami da bak'in gashi sid'ik..

Ahankali ya dago fararen idanuwanshi kamar madara masu zara-zaran adon gashin ido (eye lashes) Ya mata sanyayayyen murmushi da jan leb'enshi madaidaita.

"Wa alaykissalaam"

Ya amsa sallamar. wanda muryarshi tasa Hafsah fad'uwar gaba.

Ahankali ya amsa kuma cikin nutsuwa yadda ita kada'i sautinshi ya jiyar.

Ya mik'o k'afafunshi gami da fitowa gaba d'aya daga cikin motar..

Ta danja gefe daf da bango ta tsaya. mamaki ne cike da xuciyarta to shikuma 'daga ina'?

Takowa yayi zuwa inda take ahankali cikin nutsuwa ya na fuskantarta har ya isa kusa da ita ya tsaya.

Ya hard'e hannayenshi a k'irji. wani tsadadden agogone a hannunshi gami da wani zobe na azurfa. a d'an yatsanshi na tsakiya.

Murmushi ya kuma mata, sannan ya lumshe idanunshi ya bud'e.

"Hafsah nah"!!

Gabanta ya fad'i taso ta tuno mai irin muryar nan a wani waje..

Ya kuma kallonta 

"Am back to you again!

"Ina tunanin "This is the right time to you to accept me!

Kinga kene kika bani wannan lokacin..pls kada ki k'i karb'ana."

Ya fad'a yana had'e hannayenshi biyu alamar rok'o. 

Ya k'ara cewa "kinji..? "pls..

Tayi shiru na wasu lokuta wato shine tabbas, saurayinta na 'Seven months'

Ita abinda ya bata mamaki shine: 'Meyasa a wancan lokacin bata lura da kyau da had'uwarshi ba?

Wannan ma ai yafita kyau..

Sai ta tuno da maganar jamila wancan lokacin.

"Hafsah wannan fa ba kalar wukak'anta wa bane"!!

Tabbas jamila taga abinda ita bata gani ba a lokacin.

"Baby kinyi min shiru "

"hum.. Tayi murmushi "AI nayi tunanine sai yanxu na gane ka"

Murmushi yayi na yin dad'i "da biki gano ni ba koh"?

"Yes."

"Yanxun fah? 

Na gane ka, sai dai baka fad'amin sunanka ba wancan time en"

Ya d'an daga kai ya rufe ido sannan ya bud'e.ya naushi iska 

"Oh shut!

Ya kama leb'enshi na k'asa ya d'an matsa.. 

"Lefin baki nane, amma ai kene u didn't even listen to me.!

Ta rufe bakinta da hannunta "No a lokacin islamiyya zamu ne.

"Ok so my name is Yusuf".

Ya fad'a kamar rad'a.

"Ok Nice name" tace.

Am mu shiga mota "mana koh? 

Kamar ta musa sai kuma ta kasa don gaba d'aya salonshi da komai nashi ya tafi da ita..

Motar kuwa suka shiga duk da ad'an tsorace take.

Abba yayi tafiya amma tace wa mama baxata dad'e ba.

Nayi long waiting fa anan, since 5:55pm nake. Ya fad'a yana kallon agogon hannunshi. sannan yace 6:15pm.

Ta zaro ido "Sannu gaskiya,may be ina shiga gida daga islamiyya kazo. 5:50pm na dawo.

"No, don't worry , all this is because of you"

Ya fad'a yana kashe mata ido da'ya.

Kan tace wani abu taga ya dakko wata led'a.

Ya bude ledar kwalin wayoyi ta gani guda biyu. 

Ya bud'e ta farko "I phone ce" 

Ya mik'a mata wayar yana cewa "I missed you over" ko waya bakya dashi bare mu d'anyi hira Koh?.. To ki amsa wannan to"

Ta girgiza kai cike da tsoro.

Ya kalleta, ya Kalli wayar

"why baby? 

"Ka.. Ka barshi abbanmu zai bban wayya..ai"kuma wanna tayi girma.."

"No ni sai na baki"

Ya fad'a cike da shagwaba.

Ta girgiza kai 

"Thank u"

"Bakya so na Koh? 

Ya fad'a yana nuna kanshi da d'an yatsa.

Ta girgiza kai kawai.

Ji take kamar tayi kuka, wacce kaddarar ce ta sata shiga ma cikin motar? 

"Ok"

Ya fad'a yana cije lebenshi.

Ya Mayar da wayar tayi dakko d'aya karamar ko bude ta baiyi ba ya mik'a mata ita ya had'e rai sannan yace.

"You should accept this one"!

"Just for receiving my call."

Sai kuma ya sassauta murya cikin muryar bayyana damuwa yace. 

"Don Allah"..

Kinga bamu da way of communicating.. Kuma fa nasha wuya da bana nigeria saboda Kefa!

Ta sa Hannu ta karb'a.

"Thank you"

Ta fad'a 

"U deserve more my baby"! Ya fad'a Yana murmushi gami da lumshe idanunshi saboda jin dad'i.

Pls anjima xan kira wayar ki kunna ta.

'OK'

"Bari na shiga gida Koh? 

Ta fad'a tana kallon shi.

"Uhum Uhum yana girgiza mata Kai"

Kamar yaro.

Hankalinta a d'an tashe saboda kada mama ta gane tace.

"Pls kaga mama bata san na fito ba"

Ya zubo mata manyan idanunshi 

I won't let u go wallahi until..

A k'age tace" until what?

"U say u luv me!! 

Ya fad'a cikin rad'a 

To fa..

"I can't"

"U can't and I won't".

Ya fad'a ya na kashe mata ido da'ya.

Ta Kalli glass d'in motar ta ciki ta gane duhu yayi sosai.

Zatai magana kenan ta hango bashir yana tahowa ta dafe k'irji.

Ta kalleshi k'ok'arin kunna musu wak'a ma shi yake.

Bashir ya karaso ta b'angarenta yace yaya kizo inji mama"

Ta "kalleshi mama fa na kirana."

Shima yaji. 

ya kalleta "U are lucky."

Ya bude mata motar ta fita.

Ya d'ago mata hannu "Bye bye."

"Na shiga uku bashir mama ta gane Koh? 

Ya girgiza kai "a,a,

Yaya meye wannan"? 

"Waya ya bani"

"Waya kuma??

Eh.. Bashir bannsan ya xanyi ba cewa yayi dole sai na karb'a dafa iPhone ce." ta fad'a tana zaro ido. 

"Kaii yanxu fa?

Samsung ce k'arama.

To ki bo'ye.

"Yanxu mama tana ina?

Da xata aiko ni dai tana falonta kuma naga kamar wanka xata shiga.

Hafsah tayi ajiyar xuciya "Alhamdulillah"

B'oye wayar nan xan. 

"Kema aunty mai yasa kika karba?

Daidai lokacin kuma sun shigo cikin gida, cikin sa,a kuma mama bata falon. 

Tayi sauri ta shige daki ta yiwa wayar kyakykyawan b'oyo.

Sannan ta dawo falo cikin k'annenta suna kallo.

Can mama ta fito.

Me yasa kika dad'e.?

"Um wanka takene danaje" ta fad'a cike da rashin gaskiya.

Wai wanne littafine ma keda ba makarantarku d'aya ba.. 

"Um English ne wani assignment xan duba"

"Ki Fad'awa abbanku ya sai miki bana son are - are"

"Tom."

Mama ta kuma kallonta kamar wata ce wani abu xai kuma tayi shiru.


*Hajeeyah Kareemerh ce*


_I Need ur comments to encourage me!!_ 👏🏼👏🏼

[1/11, 12:09 AM] Hajeeyah Karimah (Writer): ♥♥♥♥

*ZAZZAFAN  SO*

(Guba ne)

*A broken* 

*heart story* 

 💔💔


Story and writing by:

*Karima Tijjani Mansur* 

*(Hajeeyah Kareemerh)*


*Dedicated to:*

*Unique In Your Love Heart Members.*


*GODIYA TA MUSAMMAMAN GAREKI BABBAR YAYA Bilkisu Tijjani Mansur THANKS FOR YOUR LUV AND SUPPORT*👏🏼😘 

*Wannan page naki ne sai wanda kika ba*😜



📄 *10*



*KO* da Hafsah ta kwanta bacci tunani uku ne ya had'ar mata.. 

Na farko mummunan labarin data samu akan jamila ya tsorata ta sosai ya sanya mata tsoron shiga soyayya..

Na biyu kuma saurayinta na 'Seven months' daya dawo yau, hak'ika ganinshi da tsarin surarshi da wayewarshi ya chanja mata tunaninta akan soyayya... Da ta rufe idonta shi take gani,yayin da kalamanshi ke mata yawo a kunnuwanta.. 

Ahankali ta furta "My new found love"!!

Tayi murmushi tare da k'ara rungume pillow a k'irjinta lallai tayi farin gani ayau,bata tab'a tunanin samun kamar yusuf a cikin rayuwarta ba... 

Sai dai me?? 

Gabanta ne ya fad'i da ta tuna da kyautarshi gareta wato (wayar daya bata)

"Innalillahi"

Ta fad'a ahankali wato wannan ne lokaci na farko data tab'a mallakar wani abu ba tare da sanin mahaifanta ba.

Bata daga cikin yara masu b'oye wa iyayensu komai.. Duk da wasu daga cikin 'yan ajinsu nayi... Misali sau dayawa idan ana hira zataji 'Basma yunus' tace "wannan wayar wani ne yaba ni amma ko maman mu batasan ina da waya ba.."

Ko wani zancen makamancin haka.. 

Sai take ganin "Ina iyayen nasu suke ??

Baxata tab'a iya b'oye wa mama komai ba..don koma ta b'oye mata sai ta gane, don mama bata da shamaki da ko ina a d'akin tana xuwa ta bud'e komai..

A hankali taji an turo d'akin..mama ce bisa al'adarta takan lek'o su duk tsakiyar dare domin duba su.

"Bakiyi bacci bane Hafsah"?

"Um yanxu dai na farka"

" Kin yi addu,a dai Koh? 

"Eh"

"To kiyi k'ok'ari ki koma bacci gobe dai kin san da makaranta."

"To mama"

"Sai da safe" mama ta fad'a tana jawo mata k'ofar ta fita.

"Hum!!

Hafsah tayi ajiyar xuciya. 

Wato yusuf dai ya had'u ko ta ina..duk yadda take bukatar mijinta ya kasance (A siffofinshi) Yusuf ya kai har da k'ari..

Ita kadai tayi murmushi tana lumshe ido,ahaka bacci ya sace ta...


*Washe Gari*

*A Makaranta*

Aji ne mai d'auke da dalibai kamar guda 30 ne kuma duka, mata ne kawai class SS 2b kenan.. Wanda SS 2a ya kasance na maxaa xallah.Haka tsarin makarantar yake..

Row d'in tsakiya desk na biyu shine maxaunin Hafsah, Itace a tsakiya.Su uku ne a desk d'in hajara Umar, sai Hafsah H. Hamid sai Fatima Mukhtar.

Saman desk en kuwa wata d'alibace Mai matsakaiciyar ki'ba fatarta coffee colour, uniform d'inta sunsha goga..

Surutu kawai take ta zubawa.. 

'Basma yunus kenan.' uwar rawar kai da gigi..

Tsit ajin yayi sakamakon shigowar Malamin English d'insu teacher Ahmad kenan 'Gajere Sai Fad'in Rai'🤣

Sunan da suka lak'aba mishi kenan..

Sam basma bata san da shigowar shi ba surutunta kawai take xubawa..

"Hey stupid !!

Go out from my class!!

Ya fad'a cikin wata tsawa daya sa ajin yin wani tsit, kamar babu halitta mai motsi acikinshi.

"Dim" basma ta duro daga desk en sannan ta tsaya chak a tsakiyar ajin ta kalli malamin ta wurga mishi wata uwar harara..

"I say get out"

Ya fad'a yana zare ido..

"Humm" basma ta fad'a tana hura hanci..ta k'ara galla mishi harara sannan ta fita..

Malamin ya d'auki marker sannan ya fara magana *to day our lesson is..*



Teacher Ahmad Ya iya koyarwa sai dai baya son raini, kuma baya son wasa da alama jininsu bai hadu ba da basma.Don ta tsani ya shigo,shi kuma ya tsani surutu..

Da aka fita break ne suka had'a dandalin hira. Duk da Hafsah bata fiya yawan magana ba,amma takan saka baki a hirar tasu wacce yawancinta ta samari ce ko kuma ta wani party ko birthday na wata da xa,ayi.

Basma ta d'ãkawa Hafsah duka abaya..

"Ku H. Hamid fa munafuka ce, sai dai ta zauna taji cikin mutane, amma ita baka tab'a jin hirar saurayinta!!.

Suka yi dariya "Hahh, gaskiya ne fa, ko dai rowa take mana ne.. 

"Hmm.. Hafsah kawai tace, sannan ta jawo basma ta rad'a mata a kunne..

"Ke biki saniba jiya nayi wani har ya kawomin I phone nak'i karba sai Samsung shima a gida ba,a sani ba..

Kut m... 😠

"Gaskiya H Hamid Baki da hankali.."

Basma ta fad'a cikin karaji.. 

(Kuji min ita da ake mata rada)😒


"Me ya faru? 

Dukansu suka tambaya.

"Wai don iskanci a bata I phone ta mana bak'in ciki"?😏

Ta fad'a tana dungurewa Hafsah kai.

Hafsah ta toshe mata baki, "ke basma ki bari don allah..

Sai lokacin Fatima Mukhtar tayi magana 

"to Menene kawai daga bata waya sai ta karb'a?

"Eh mana, meye aciki?

Inji basma.

Babu ruk'ayya ta fad'a.

Basma taja hannun Hafsah zo muyi sirri k'awata.

"Yanzu ina wayar?

Inji basma sanda suka isa can layin baya suka keb'e.

"K'arama ce fa wayar, ni tsoro ma nakeji."

"Kinjiki tsoron me?

"Abbanmu." 

ta d'anyi shiru sannan ta d'ora.

"Ya hanani kula samari fa"

"Hmm to ke bari zaki yi ya gane?..

"Ni dai gobe kizo da wayar." 

"K'ilama yana ta kiranki kinki kunna wayar.. Ki kunna idan kinje gida dallah."

"OK zan kunna saboda kada yaji shiru ya k'ara dawowa don yau abbanmu zai dawo."

"Ki dai zauna ayi babu ke" basma ta fad'a tana dariya..

"Hahh" Don dai kawai ya had'u ne gayen, da babu ruwana dashi.

"Hahh" ta daki bayan ta. "H Hamid anji guys"!!

To bayan ta koma gida, aiki ta tarar mama nayi na tabar abba (wanda yayi wata 'yar tafiya zuwa Abuja na kwana biyu) ta zauna sukayi aikin ita da mama ko islamiyya bata samu zuwa ba. 

Suna aikin mama najanta da hira Kala -kala kamar k'awarta.

Da la,asar abba ya iso suka tare shi suna mishi Sannu da zuwa ita da mama.

"Yawwa, sannunku ku ma." 

Ya sauke kallonshi kan Hafsah "Baki je islamiyya bane.?"

"Aiki ta taya ni" cewar mama suna k'arasowa falo, sannan suka shiga wata k'ofa wacce shine falon mama had'e da bed room d'inta. 


"Kije kiyi wanka kema"

Inji mama sannan suka shige d'akinta ita da abba.

Gidan yayi shiru dama k'annen nata suntafi islamiyya.

Mama da daddy kam suna da'aki.

Bayan tayi wanka a toilet d'in d'akinta ta d'an yi shafa sannan ta saka wasu pink d'in riga da wando jeans saka wata pink d'in turban ta d'aure kanta dashi sai tayi kyau sosai.

Hafsah kenan doguwa ce bata da k'iba kwata-kwata kuma ba siririya bace, tana da hasken fata mai ja,

tare da bak'in gashi dogo amma bai cika yawa ba.

Bud'e wardrop d'in can k'asan kayanta ta bincika ta d'auko ledar da kwalin wayar ke ciki.


 Ahankali ta k'arasa ta sawa d'akin key. Sannan ta dawo ta zauna.

Akan gadonta ta mik'e k'afarta mai zara-zaran yatsu. 

Ahankali kuma cikin tsoro take bud'e kwalin wayar 'yar k'arama ce mai kyau. 

Ta kunna ta..minti kad'an ta kunnu.


Da SIM card akan wayar sai dai babu chaji kara d'aya ne kawai.

Ta saka wayar a vibrations sannan ta d'auki chajar wayar ta jona ta achaji ta koma ta kwanta tana jiran taji ankira wayar..amma shiru har lokacin sallar magariba.Ta mik'e ta nufi toilet don yin alwala...

Bayan isha'i ne mama tazo ta kirata. Allah yaso lek'owa tayi bata shigo ba.

"Ki zo ki raka abbanku shopping keda bashir."

Ta saki k'ofar data rike ta juya. 

Ajiyar xuciya Hafsah tayi sannan ta mik'e ta d'ora after dress akan kayan jikinta tayi rolling da mayafi sannan ta d'auki wayar ta maidata kwalinta sannan ta mayar inda ta bo'ye ta da farko.

Jin muryar mama tayi a bayanta tana "kiyi sauri fa" 

Ta tsorata sosai.Mama ma taga hakan sai dai bata ce komai ba.

Al,adar abbannasu ce zuwa dasu shopping musammaman ita da bashir idan k'annensu suna buk'atar wani abin suna fad'a musu idan xa,a shopping a tawo musu dashi.

Yana jan hafsah ajiki sosai duk da ita ba namiji bace..amma yana hira da ita ya bata labarin Yarintar shi da yadda sukai karatu a boarding school (makarantar kwana) yana nuna mata al,amran rayuwa sosai, niyyar shi shine ta sami kyakykyawan tarbiyya da kwaxo ta zamewa k'annenta kamar uwa.

Abba nason Hafsah sosai ya kan fad'a mata ma wani lokacin "Hafsah ina son ki" (idan tayi wani abu ya burgeshi) yana nuna mata ita wata ce kuma tana da girma Shiyasa yakan kirata da "Yaya." (wasu lokutan idan zai kira ta) yakan ce mata idan k'annenta sun mata laifi ko bashir ya kawo mata raini wani lokacin "Haba yaya aikece babba kiyi hak'uri mana, duk abinshi kin dai girmeshi. Kokuma "Ke fa babba ce, kiyi ha'kuri dole babba sai yayi ha'kuri kinga kece zaki zame musu abin koyi, ki kula da rayuwarki Hafsah kada ki dinga shashanci da shirme"..

Wannan ne irin kalaman abba yawanci a gareta, wanda suna tasiri matuk'a azuciyarta har suka sa mata nutsuwa da girma fiye da shekarunta, don baka tab'a ganin ta tana abu na shashashanci ko rawar kai irin na 'yan matan yanxu, musamman wad'anda iyayensu ke da sukuni irinta..

Komai takeyi cikin nutsuwa take yinsa, bata gaggawa, shi yasa ake ganin kamar tana da 'yanga'. 

Ki dinga nutsuwa Hafsah mace da nutsuwa aka santa ki daina gaggawa a al,amra domin gaggawa aikin shed'ance"..

Wannan ne kalaman abbanta ko da Yaushe.

Tsaye ta tarar da abban a falo yai murmushi "To mu tafi koh"?

Sunzo fita daga layinsu kenan taga motarshi zata shigo. gabanta ya fad'i, ta dafe k'irji

"ya salam"

To sunje sunyi siyayya sosai, mama kuma ta bata sautu don tace yau basai taje ba.

Sai wajen 9:00pm suka dawo.

Yaran sai murna suke dama abban baizo da tsaraba ba.

Dariya kawai take so take ita dai ta wuce d'aki ta duba wayarta.

Abba ya kalleta.

"Ko kin gaji ne yaya?

Ta kad'a kai 

To maza je ki kwanta ta mik'e ta nufi bedroom d'inta.

Sai da ta d'an watsa ruwa sannan tasa kayan bacci. Ta dakko wayar ta kashe fitila ta kwanta.

5 missed calls ta gani akan wayar.

Sannan da text akan wayar tana cikin dubawa, sai ga wani kiran..

Ta d'aga ta kara a kunne "Hello."

Muryarshi mai sanyi da dad'i ta daki kunnenta. Ta d'an muskuta, kafin tayi magana yace cikin shagwabar nan tashi.

"Haba baby nayi miki laifi ko na kiraki kink'i picking then nazo kuma kika cemin bakya nan, pls mena miki ne..??

Ta bude baki xatayi magana kenan, taga haske ya baibaye d'akin tayi saurin juyowa mama ta gani idonta akan wayar hannunta.. 😳

Shigowa tayi ta tambayeta waye yazo nemanta d'azu? sai ta fara kunna fitila so take suyi magana kan kada ta soma kula wani tunda tasan abbanta baiso..

To kuma tana kunna fitila taga abinda da bata tab'a zato ba... Hafsah da waya to waye ya bata?? dawa ma take wayar??

Ku biyo ni..😇


*Hajeeyarku ce*👌🏼

*Pls idan kunga typing error ko kuskure kuyi hak'uri ni sabuwa a harkar. Wanna ne first novel di'na..👏🏼*

*Ina Godiya fans ☺*

*Pls I need your comments to encourage me!*👏🏼

[1/11, 1:33 AM] Hajeeyah Karimah (Writer): ♥️♥️♥️♥️

*ZAZZAFAN SO*

 (Guba ne)

*A broken*

*heart story*

  💔💔


Story and writing by:

*Karima Tijjani Mansur* 

*(Hajeeyah Karemerh)*

*Dedicated to:*

*Unique in your love heart group members.*




📄 *11*



*Tsawa* Maman ta daka mata tare da kai mata duka, wanda yaja tsoro yasa wayar fad`uwa a kan gadon.

Caraf mama tasa hannu ta d`auka abin yana bata mad`aukakin mamaki bata tab`a zata ba. 


Uban wa ya baki wayar nan."?


Iya rudewa Hafsah tayi ta har ta kasa bada amsa. 

"Tashi zaune."

Ta qara daka mata wata tsawar.


Ta miqe cike da fargaba yayin da maman ta zauna gefe gadon.


Ta kafe ta da ido sannan tace, "Ki fad`a mini wanda ya baki wayar nan tun muna mu biyu, idane ba haka ba zan hadaki da abban ku. "

Zufa ta ketowa Hafsah, ya zata yi idan wannan zancen yaje wajen Abba, ai ta ka d'e 


Gwara ta fad`i gaskiya tun suna su biyu da maman tunda an kama ta dumu-dumu ai bata da wata mafita.


Cikin Hawaye ta labartawa maman yadda wayar tazo hannunta, Sannan ta qare mata ta kalaman kare kai.


"Wallahi Mama ajye min yayi ya tafi shiyasa na karb`a, kuma Allah ranar na fara ganinshi."



Tana gama zancen, taji mama ta kama kunnenta kamar zata tsinka.

"Ki kiyaye ni Hafsah, wallahi duk ranar da  na kuma ganin makamancin haka sai ranki yayi mummunan b'aci, shashasha, kuma yanzu ma zan iya fadawa abbanki matuqar na qara ganin abin me kama da wannan. Kuma wayar na kwace bazaki qara ganinta ba. Kuma duk ranar da kika sake naji labarin kin k'ara kula yaron nan to ki tabbatar kamar abbanku ya sani ne."


"Bazan qara ba mama kiyi hak'uri."

Binta mama tayi da kallo kawai, sannan ta fice cike da mamaki.


Ta boye wayar sannan ta saita nutsuwar ta kada Abban Hafsah ya gane, sam bata son tada mishi hankali da irin wannan zancen ba.


Da alhinin k'wace wayar Hafsah ta kwana har ta kasa yin isashshen bacci. Allah Allah take safiya tayi taje makaranta ta sanar da Basma. 



"Na shiga uku Basma, mama ta kwace wayar nan fah."


"Basma ta d`aka mata duka ke garin yaya, banza."


Tsautsayi Basma, waya nake tazo ta tadda ni, Allah ya rufamin asiri ba Abba bane ya ganni da na shiga uku.!!"


"Hmm, gaskiya ke doluwa ce, idan nice wallah bazan bayar da wayar ba."



Hafsah ta zaro ido. Kaii Basma tafa riga ta gani.

"Hmm, kedai tunda kinyi sakaci ai shikenan. 

Please Basma, help me Mama tace kada ta sake ganin yazo na fita, wallah ina sonshi Basma, ya zanyi in dinga ganinshi gashi babu waya."?

"Please help me.!!

Dariya Basma tayi me isarta sannan ta kamo Hafsah tayi mata rad'a a kunne.

_"Ke dallah can appointment zaki dinga hada muku."_

Hafsah ta zaro ido, kamar a ina kenan nifa bana fita kinsani.

"Nonsense ki zo gidanmu mana."

"Kaii Chab Mama bazata barni ba."

"Hmm, kina da abin haushi H Hamid."

"Ba kina zuwa islamiyya ba."?

Eh ina zuwa."

"Why not kuna had'uwa idan kin fita.

Hafsah tayi shuru tana tunani, can kuma ta tuna tabbas babu mafita idan ba hakan ba don haka ta rungume Basma tana godiya.


Sanin da Hafsah tayi basma na zuwa da waya yasa tace,

"Please ki bani wayarki, na tura test Allah yaso n riqe number d`in.


"Hmm, ungo badon halinki ba. Ta ciro wayar daga aljihun uniform ta ba ta.


"Dear it's Hafsah, Mama na ta kwacen waya, ina son mu hadu, yau a bayan layin mu by 2:00pm plz kada kazo Gidan mu.


Minti kad'an ya kira, ta d'aga.

Baby me kike fad`amin, mamanki ta kwace waya.

Eh okay, mun had`u na baki wani.

"Noo dear thank you."

Aa zan taho miki dashi..

Ta katse wayar saboda tsoron kada a kama su da waya.

murna take sosai babu sauran damuwa.



Hakan ne ya faru kuwa, bayan Hafsah ta koma gida tayi ta nuk'u  nuk'u har qannenta suka gaji da jiranta, mama tace suyi tafiyar su.

Dama haka take so don haka Basma ta tsara mata.


katon hijab ne har qwauri sai doguwar riga, sune uniform d`in. Ta sab'a Jakarta ta cewa mama ta tafi.



Yana ta kai kawo a layin, tun qarfe 1:30pm yake wajen har ya fidda ran ganinta.


Ya saki ajiyar zuciya sanda ya hango ta, ya nufi motar shi da nufin ya kunna su shiga ciki amma ta mishi alamar daya bari.

Ta gabanshi tazo ta wuce, sannan ta mishi inkiya (signer) da ya biyo ta.

Ahankali suke tafiya, har zuwa _lokon su Jamila, dake lokon_ babu Mutane sosai, kuma dama suna bin hanya biyu ko su bi tanan ko subi titi street.


A Wani dakali suka yada zango.

Ya kura mata ido yana murmushi, ya mata kyau sosai, taji ta a wata sabuwar duniya, _Lallai babu abinda ya kai soyayya sanya nishad`i._

"Baby I miss you."

Ya fad'a a hankali.

murmushi tayi itama.

Really"?

Yes ya fad'a yana jinjina kai.

"Me too my dear.

Itama ta fad`a.

Ya sakar mata murmushin daya sa ta shagala da kallon shi.

Bata ankara ba taji ya kamo hannunta, dole ta farga, tana kokarin kwacewa ta tuno basma.

_"Saura kuma ki nuna mishi qauyanci!._

Bata fahimce ta ba a lokacin amma Idan hakane dole tayi kyauyanci kuwa, yaushe zata bari haka na faruwa.


Ta zame hannunta a Hankali ta sannan ta miqe tana rungume, hannu a qirji, amma kirjinta sai bugawa yake da sauri da sauri don tsoro.

"Dear lemme go kada nayi late."

Ya kura mata ido, baiyi magana ba dai.

Ya miqa mata qaramar wayar hannun shi.

Okay take this."

"Noo dear."

Please ki karba mana, da me zanna contacting dinki."

Mama zata bani wayata.

Ta fara tafiya don ta fara tsorata da makarar da tayi.

Ya bita suka jera.

"Plz mana baby."

"Am sorry dear, zan amso nawa nace maka."

Ya karanci tsoro a idonta don haka ya kyaleta.

"OK ki dinga kirani a wayan friend dinki.

"Okay."

Sai da ya kusa rakata makaranta sannan suka rabu, ya miqa mata wata Leda dake hannunshi.

Da zata k'i amsa, ya 

had'e ranshi sosai.

Dole ta karb'a saboda bata son su tsaya ja'inja, taqara bata lokaci, sannan tana tsoro kada idon-sani ya ganta."

"Thank you dear."

"I love you." Yace mata.

"Me too dear."

"Bye see you later."

Ya fad'a yana kallo ta.

Suna ta waiwayen juna, cike da farin ciki Hafsah take, gaskiya ya had'u bata tab'a zaton samun saurayi kamar wannan ba.


Gefe guda, tana fargabar riqe hannunta da yayi, Allah yasa dai ba haka yake ba.

sai kuma fargabar makarar data tafka, don ma ansan bata makara...




 .[1/11, 12:09 AM] Hajeeyah Karimah (Writer): ♥♥♥♥

*ZAZZAFAN SO*

(Guba ne)

*A broken* 

*heart story* 

 💔💔



Story and writing by:

*Karima Tijjani Mansur* 

*(Hajeeyah Kareemerh)*

*Dedicated to:*

*Unique In Your Love Heart Members.*



📄 *12*





*Ko* da Hafsah taje islamiyya acan ta rabar da abinda yusuf ya kawo mata..

Ice cream ne sai tarkacen kayan ciye -ciye..

Bayan ta dawo gida ne tana d'akinta mama ta kira ta ta dawo falo. 

Tun daga rannan mama bata barin ta ta keb'e ita d'aya a d'aki idan ba lokacin bacci ne yayi ba..

Da safe suna isa makaranta layinsu Basma ta nufa, sai dai cikin rashin sa,a ranar gaba d'aya Basman bata zo makaranta ba.

Haka hafsah tayi zaman makarantar babu wata walwala.

Fatima ce ke fad'amata "Hafsah wallahi kwana biyu kin chanja, ko son zaman cikin class bakya yi.."

"Hmm, ruk'ayya wani abu ne ke damuna wallahi..

"Kuma kike rasa dawa zakiyi shawara sai Basma Yunus koh?"

Hafsah ta d'an sha jinin jikinta sai kawai ta kawo mata wani zance.

"Fatima ba wani abu bane kinsan k'awata jamila da nake fad'a miki? 

"Eh"

Nan hafsah ta shiga labarta mata abinda ya sami Jamilar..

"To yanzu neman yadda zaku nemota kuke ko me??"

Hafasah bata da amsar bata don haka tace bazaki gane ba Fatima"

"To Allah ya taimka"

"Amin" inji Hafsah.

A ganin Fatima Basma ba k'awar da za,a zauna shawara da ita bace.. Ina ma taga hankalin da zata hango abinda Hafsah bata gano ba,?.. Ita damuwarta ma wai me suke tattaunawa ne?? 

Don bata yarda da abinda Hafsan ta fad'a mata ba.

A saninta Basma ba wata k'awar hafsah bace, hasalima abokiyar takararta ce don idan hafsah tayi sakaci wani lokacin Basma ke k'wace mata 1st position d'inta.

Basma akwai shishshigi da bani na iya.. Tana son shiga al,amran da babu ruwanta..

Tatasone agaban mahaifiyarta don tun tana shekara 5 suka rabu da mahaifinta. Sanadin haka yasa yake sakarwa maman tata kud'i har 'albashi' yake biyanta wai ladan d'awainiyar da take da 'yarshi duk wata dubu d'ari..

Mahaifiyar Basma business takeyi, kuma tana yawan yin tafiye tafiye sai tayi fiye da sati bata gari ko kuma ma k'asar gaba d'aya.

Don haka koyaushe basma na gidan k'awayen mamanta (Can take kaita idan tayi tafiya). 


Don bata da kowa a kano duk danginta na kaduna, amma tunda tayi aure take zaune a kano, ita kad'ai sai 'yan aiki sai abokan hul'arta mazaa da mata da kullum suke zarya a gidan.. 

Idon Basma a bud'e yake sosai, domin idan mama tayi tafiya, haka manya- manyan samari ('ya'yan k'awayen mama) suke d'aukarta zuwa yawo, sune club, sune park, sune party.

Duk da haka mamanta na sata tayi karatu dole. (kuma don ma tana da kwakwalwar karatun ne.)

"Kiyi karatu basma ki dogara da kanki, kinfi k'arfin raini..

"ki daina la,akari da babanki yana da kud'i.."

Ahakan kuma take hanata kula samari, amma duk da haka bata hanata zuwa wajen wani party ko wani taro idan ya kama...

To,Hafsah bata samu damar tattaunawa da basma ba sai washe gari lokacin, malaminsu na lissafi zai shigo ajin suna hango shi suka fice, Basma na cewa "Mts yanzu zai damemu da wani revision."

SS 1a suka shige suka nemi guri suka zauna acan baya..

"ya kukayi H Hamid?

"Um,Basma yazo na fad'a mishi. Amma ba shine matsalar ba."

Ta fad'a cikin damuwa. 

"To Mene matsalar?

Tayi k'asa da murya sannan tace

" Yusuf yana son rayuwar turawa, yana k'aunar ya tab'ani.. Wai haka yace min na mishi kiss"😳

"Mtsss"

Basma ta ja wani dogon tsaki.

"To sai me? Ke da irin local soyyaya zaki nuna mishi, wallahi kin bada ni"

Ni duk kinsa ma raina ya b'aci."

Hafsah dai tayi shiru ita yaushe zata fara wannan watsewar??

tab' Allah ya tsareta.

Amma dake kamar tana tsoron basma ne sai tace 

"Basma yanzu an fasa kiran nashi kenan? 

"Hmm ai kece, ta mik'a mata wayar tana cewa ungo saka number d'in..

(Al,adar Basma ce zuwa da waya makaranta.)

Ringing biyu aka d'aga.

"Hello" yace 

Hafsah ta kalli Basma, bata san me zata ce ba.

Basma ta harareta.

Sai ta dawo kan doka da oda.

"Am, dear iam Hafsat"

"Oh my gosh!

Ya fad'a cikin wata k'ara my baby I miss u alot"

Ta daure tace "Me too"

"ya kake?

"Fine but thinking of you, wai when ur mama zata baki wayarki ne?

"Um very soon in sha Allah."

"Um um ni dai ban yarda ba kawai mu had'u anjima na baki wani"

"No, ka barshi yau zan karbi wayar"

"OK thank you my baby, yaushe ne zanzo my eyes want to see u kinji.?

Dam gabanta ya fad'i ashefa bata fad'a mishi an hanata kula shi ba..

"Um, am.. Ka bari mama ta bani wayar, 

"Nooo ni dai I can't wait, pls baby nah"!

OK ina school kaga yanzu ka bari zamuyi waya, but pls kada kazo sai mun kuma yin waya."

"OK, bye bye i love u" 😍 

"Thank you"

Gama wayarsu kenan, Geography teacher ya danno ajin, kuma shine form master d'in su Hafsah (shine ma ya gansu ran nan)

Suna ganinshi suka mik'e ya kallesu kawai..

"Again?

Ya fad'a yana rik'e haba..

"Yunus and Hamid What are you doing here??

"Am.. im Nothing sir"

"Ok, very good".

Ya fad'a yana kad'a kai.

Suna fita Basma ta Shek'e da wata shashashar dariya..

Tana wani abu da fuskarta kamar ta ga wani abin tsoro, look at your reaction H. Hamid, when Teacher catched us,...😱😨🤥 uhum kamar kinga zaki" hahh 😂😂

A gida kuma mama tunani takeyi akan, Kodai ta bawa Hafsah wayarta ne, a tunaninta, hafsah 'ya macece wacce Yanzu shekarunta sun kai 17, bai dace a matsa mata ba, don takai munzalin tsayawa da saurayi. Don ma abin ya zo da zamani da dane ai da tuni tana d'akin mijinta..

"Ai kuma ya dace ki nuna mata kuskurenta"

Wata zuciyar ta fad'a mata...

'Zan bari zuwa suyi hutu'

Haka mama ta kudurce a ranta..

To kusan kullum a makaranta sai Hafsah sunyi waya da Yusuf, kuma kullum zancen shi d'aya yaushe zai zo? 

"Ka bari dear, ka bani two weeks"

Haka ta fad'a mishi wata rana, lokacin sun fara jarabawa.

"What? Mene kina cewa?? 

"Ok bakya sona ne I realized, ok I will leave you kawai"

Ya fad'a, kawai ya kashe wayar.

"Na shiga uku Basma kinji wani abu kuma"??

"To ya zan miki an baki shawara kink'i karb'a, ba saiki bari ya kub'ce miki ba."

Ta fad'a cikin rashin nuna damuwa da zancen.

"To aini basma tsoro nakeji..

"To ai shikenan"

Ta kuma kiran number ba,a d'aga ba.

"Oh my God! dama haka yake da fushi?.

So bata kuma samu sunyi waya ba sai ana gobe hutu (Bayan malaminsu ya kirata ya mata fad'a akan karatu )

Da k'yer ta samu ya hak'ura, amma yace mata dole ne su had'u cikin wani satin.

Aranar da aka musu hutu, ranar ne kuma bayan ta dawo, mama ta kira ta suka zauna a falon maman..

"Hafsah kinga kin girma, ki nutsu kisan abinda kike yi, zan baki wayarki..

Ta d'ago cike da murmushi,

"Nagode, Mama.

Ba wannan ba, kada ki bari abbanku ya ga wayar nan, sannan kiyi taka tsan -tsan da samari, bance ki kula kowa ba, tunda abbanki baya so,.. Kuma kada ki k'ara karb'ar abu makamancin wannan a hannun wani."

"Nagode Mama, in sha Allah zan kiyaye."

Ta mik'a mata wayar,

"ungo ki b'oye, k'awayenki kawai na yarda ki kira"

Cikin zumud'i ta karb'a..

Baki 'nunamin result d'in naki ba."

Tsoro ya cikata, babu yadda zatayi haka ta dakko ta bata.

"Kaii, ya akayi haka Hafsah??

Bari abbannaki ya dawo, wato don an hanaki kula samari shine zaki k'i maida hankali kan karatunki koh?

(A tunanin Mama kenan)

"Kiyi ha'kuri Mama wallahi ba haka bane."

"Yayi kyau"

Tashi kije kya had'u dashi ai"

Tana zuwa daki'n ta tura mishi text zuciyarta cike da farin ciki.

"My phone is with me.. But don't call me now, let's have phone by night..

I love you!!

*To shine fa wayar da tayi yau, bayan ta dawo daga wajen abban ya mata fad'an karatu, shine kuma wayar da mama ta kamata tanayi a darenna..(Page 1 to 3 )*👏🏼👏🏼


*Muje zuwa muji wannan soyyaya ya zata kaya..*😇


*Hajeeyah Kareemerh ce dai*👌🏼

[1/11, 12:09 AM] Hajeeyah Karimah (Writer): ♥♥♥♥

*ZAZZAFAN SO*

 (Guba ne)

*A broken* 

*heart story* 

  💔💔


Story and writing by:


*Karima Tijjani Mansur* 

*(Hajeeyah Kareemerh)*


*Dedicated to:*

*Unique In Your Love Heart Members.*

😘😘😘👍🏻👍🏻👍🏻

*Jinjina gareku ZAZZAFAN SO NOVEL GROUP*

🍒 *Farida (Farisam*)

🍒 *Gimbiya Bilkisu*

🍒 *Basma A adam*

*فا طم*

🍒 *Ummi M shehu*

🍒 *Amina Yusha,u*

🍒 *Umman Aryan*

🍒 *Maman husna*

🍒 *Mufy expensive*

🍒 *Mummy khali*

👏🏼 *Ina yinku 💯 kamar yadda kuke yin novel d'ina*😘


📄 *13*



*Nunkuwar* shak'uwarsu da yusuf, nunkuwar soyayyarshi azuciyarta..don a kullum soyayyar yusuf k'aruwa take a zuciyar Hafsah. 

Ahakan kuma waya, kawai suke shima ab'oye, amma kullum cikin lallab'ashi take akan lokaci ya kusa da zai zo wajanta..

Wata hira da sukayi, wata rana da daddare suna waya. Ya saisaita murya, dai dai yadda yafi jawo hankalinta gareshi.

"Baby"

Tace "Na,am dear"

"Ina son yi miki wani question ne"

"Ina jinka"

"Wai kina sona kuwa?

Ta d'anyi shiru sannan tace

"Haba dear me yasa kamin wannan tambayar? 

Yai k'asa da murya "Am sorry bana nufin b'ata miki rai, ina tunanin, ni kad'ai ke wahalar son ki ne"

Ta marairaice.

"To Ba haka bane wallahi, u know my friend Basma koh, har cewa take wai 

'Me yasa nake sonka da yawa ne?

Ya gyara kwanciyar shi, "To wane answer kika bata? "

Haka nace mata, "kanada abubuwan da nake so ne,..an then ka iya soyayya"!!

sai taji yayi dariya ahankali.

"Hahh da gaske ina da abubuwan da kike so kuma na iya soyayya??

Ta gyad'a kai kamar a gabanshi.

"Exactly yadda nake son mijina ya kasance, to haka kake."

Yai ajiyar xuciya "Thank you my hafsat!

Ya fad'a da wata kasalalliyar murya.

"Meya faru?" Ta tambayeshi.

Ya kuma ajiyar xuciya sannan yace "Am bacci nakeji, and abinda kika fad'a yasa naji wani 'Laziness' ya saukar min. 

'Kasala kuma'??

Ta tambaya da mamaki.

"Oh, no kada ki damu, ki gaidamin da k'awar taki.. Gud night"Ya kashe wayar.

Sai kawai ta yi kissing d'in wayar, abinda bata tab'a yi ba a tarihin soyayyar su..

Wata ranar juma,a hafsah ta shirya cikin wata doguwar rigar atamfa fiffted. Tayi kyau sosai ta yafa d'an k'aramin mayafi. Batayi kwalliya ba sosai.

Ta fito falo, tace wa mama "Mama zan tafi, "

Maman har da bata kud'in mota.

"don Allah Hafsah kada ki dad'e har abbanku ya dawo"

"In sha Allah"

"Ki duba ta. 

"Tom"

Ta rayata jakarta ta fito."

Cewa maman nata tayi wai ' Mamansu basma ce bata da Lpia zataje dubota, wai har asibiti ta kwanta.. 'Wannan shawarar basma ce, da Hafsah ta dame ta ya zatayi da yusuf?'

Tana zuwa unguwar ta kira basman a waya. Don bata san gidan nasu ba, layin ta kwatanta mata, da number gidan. Tana zuwa ta tarar Basman ce kad'ai a gidan sai 'yan aikinsu, maman tata bata nan.

Gidan nasu ya tsaru babu laifi..

Basma ta ruk'unk'ume ta,

" H, Hamid a gidanmu lallai ina da Manyan bak'i.

A falo suka zauna wanda ya had'u da gujeru da adon fulawoyi.. 

Basma ta sa aka kawo mata kayan ciye ciye..

Kad'an taci. Ta Kalli agogon dake falon.

"Kinga bai Kira ni ba har yanzu, gashi mama tace kada na dad'e."

"Hum, kema ai baki shirya ba"?

Hafsah ta kalleta cikin rashin fahimta.

"Kinga ni tashi muje ki shirya dallah, ahaka zai ganki"?

Taja hannunta, babu musu ta bita.

Wani dak'i suka shiga daya tsaru sosai basma ta nuna mata toilet.

"Ki shiga ki wanke fuskanki"

Ta shiga tayi yadda tace d'in.

Tana fitowa taga rashin ajye mata wasu riga da wando (pencil) iyakacinshi guiwa rigar kuma T. Shirt ce amma bata da hannu.

Ta nuna mata kayan "kisa wannan"

No, basma sunyi k'anana gaskiya"

Ta d'an b'ata fuska 

"Kinjiki ai"

Ta mik'a mata wata powder shafa wannan"

Ta karb'a, Hodar ta amsheta sosai.

Ta mik'o mata sauran kayan kwalliyar 

"Gasunan bari nayi wanka."

Ta shige toilet.

Hafsah ta yi kyau sosai.

Tana gamawa Basma ta fito d'aure da towel ajikinta da kuma wani d'an k'arami hannunta tana goge jikinta dashi.

"Wow kinyi kyau"

Yanzu dai ga wani humra ki shafa saiki sa kayan."

Ta dakko mata wani towel a drawer ki d'aura wannan sai ki cire gown d'in.

"Hafsah ta kalleta Nifa gaskiya Basma bazan iya fita gurinshi da wannan kayanba"

"So wai meyasa?

Kawai,ki barni da wannan gown d'in yayi ai"

"Nooo, bazaki fara zuwa wurinshi da dressing na wani atamfa ba gaskiya, dole ne ki chanja malama."

"To gaskiya sai dai a chanja wani."

"OK ai ga drawer d'innan duba wanda ya miki.' 

Ta fad'a tana nuna mata wardrobe d'inta.

Suna cikin haka wayar Hafsah tayi k'ara, da d'auka da sauri.

"Hello"

Am baby nazo unguwar wane link ne? 

"Om..

Ta mik'awa basma ta kwatanta mishi.

"Sai kiyi sauri ki nema wanda zaki sa."

Ta fad'a tana mik'a mata wayar.

* * * * * 

* * * * *

Wani kyakywan had'ad'd'en saurayi (First Class) Basma ta yi tozali da shi..

A zatonta da yadda Hafsah ke kwarzanta mata yusuf bata ta'ba zaton yakai Kwatar hakan ba.

(Colour of my dream)

Ta fad'a a zuciyarta.

murmushi kawai yake sakarwa Hafsah, tare da wani irin kallo wanda ya so rikitata.

suka isa wajenshi..

Hafsah ta nemi gefenshi shi ta tsaya.

Ahankali tace mishi 

"You're welcome my dear"

Ya zuba mata idanu "Thank you my baby"

"Am mu k'arasa ciki Koh? 

Basma ta fad'a.

Sai lokacin ya kalleta. yace 

"Sannunki fa" 

Tayi wani murmushi cike da gogewa 

"Am yawwa..

Basma na gaba suna bayanta..

Wani d'aki ta bud'e musu dake farfajiyar gidan, sanyin AC ga kuma wani daddad'an k'amshi dake tashi..

A wata kujera ya zauna three seater, 

Hafsah ta zauna a 'me kallonshi' suna fuskantar juna.

"Am ina zuwa.."

Basma ta fad'a, sannan ta fita, sai wani rangwad'a take.

Falon ya d'anyi shiru, kusan mintuna biyu, sai kawai kallonta da yusuf yake..

"Can taji yace " you look so cute my baby".. Kinyi min kyau."

"Thank you"

Kazo lpia? 

"Lpia lau, but full of kewanki amma."

Ya fad'a yana wani d'age gira.

Tayi 'yar dariya. 

"Gani nan kam yanzu Koh?? 

"Ya mamanku"

"She's fine"

Ya d'an gyara zama sannan yace

"Baby baki son ganina koh,? duk na rame, kin hana in ganki..

"Am sorry ba haka bane, na fad'a maka abbanmu ba zai barni fitowa ba, sai nayi candy."

"Hum long distance, u mean bazan dinga ganinki ba koh?

"A,a mana, yanzu ai mun had'u koh?"

"Yes, but this won't satisfy me.

ya zuba mata ido

"Ko dai zaki zo gidanmu ne kawai sai muna hira acan".

Ta d'an zaro ido.

Yayi wata siririyar dariya wacce taji ta har cikin ranta.

"Ba zaki zo ba koh.."?

Ta rufe idonta d'aya da hannunta tana kallonshi da d'aya idon..

'Kallon yayi tasiri a zuciyarshi.'

"Bazaki zo bane Koh? 

Tayi shiru 

"Uhum..? 

Ta kuma yin shiru 

"Talk to me mana kinji..?

Basma ce ta shigo da Tray a hannunta taja wani center table ta d'ora akai..

Ta Kalli Yusuf 

"Ga drink koh?

"Ok thank you"

Leb'enshi kawai ta kalla ta gane me yake fad'a, saboda a hankali yayi maganar.

'Hafsah ta kalleshi.

"Dear ga Basma fa"

Ya jingina kanshi jikin kujerar, sannan ya kallo Basma, yana jijjiga k'afa.

"Am sannunki koh? 

"How are you?

Kut..😒 (Basma ta fad'a azuciyarta) "Rainin sense" wato gayen nan wani nauyin kai ne dashi..😅 

Ok bari na zo mishi ta yadda yazo min..


~'To Basma ya kike so ya miki? Koh kece Hafsan ne'*~🤔


Tayi wani murmushi a d'an share tace "Am fine"..

yace "Gud"

"Am yau dai kaga hafsan naka koh??

Yai murmushi sosai wani b'oyayyen kyawunshi ya bayyana 

"Of course, alot of thanks to you."

"No ai ana tare ne Koh,?..

Ta Kalli Hafsah.. 

"Ai kamar sister na take."

"Gud!"

Ya Kalli Hafsah wanda dama Basma ta lura rabin hankalinshi na kanta dama.

"Baby friend enki nada kirki fa."

"Sosai ma, kuwa inji Hafsah"

Sannan ta mik'e ta zuba mishi lemon a cup.. Basma idonta kir tana kallonsu..

K'okari take ta gano a ina ne Hafsah ke da rauni.?

Amma duk kwakwarta bata gano ba.

Sai ma wani sirri data gano a wajen Hafsan.

Wato yadda yanayin 'Movement' motsinta yake da banbanci da na sauran 'yan mata. Bata abu da gaggawa sannan bata da sanya.. komai takeyi cikin nutsuwa take yinsa, sannan tana da shiga rai sosai.

Ta mik'a mishi lemon ya karba yana murmushi.

Ta zuba itama sannan ta dawo ta zauna tana sha..

Am bari na barku haka koh? 

Ta Kalli

"Yusuf ka gaida gida"

Ok bye bye"

Hafsah sai kin shigo.

Bayan fitar basma, Yusuf hira ya fara yi mata ta rayuwarshi a k'asashen waje, k'arara yake nuna mata 'banbancin' dake tsakanin can da nan. 

Misali acikin labarin shi tsaf yake fad'a mata irin rayuwar shi da 'yan matan shi acewarshi (School mate enshi ne) ko da cikin labarin yakan ce mata "She hugged me and then.." ita dai Hafsah sai dai tajishi da kunne ko tayi murmushi, itama bata son ta nuna mishi 'Gidadanci' kamar yadda yake d'aukar hakan, sai dai a hirar tasu ta fahimci wani abu..

'wato, Yusuf sam bai san wani abu wai shi 'Babu ba' duk da itama ba wai wahalar tasani ba, amma shi batajin yasan da wata abu wai ita wahalar rayuwa.. 

Tsoron da take ji shine kada 'Banbancin' dake tsakaninsu ya kawo musu matsala acikin alak'ar su.

"Baby meyafaru ne? 

Babu komai.

"Sure?

"Yes"

"OK please close your eyes for me! 

I have a surprise for you! 

Ya fad'a yana kashe miki ido.

"Am ok"

Ta rufe idon..

Tsayawa yayi ya k'arewa fuskartata kallo tun daga saman goshinta har zuwa k'asan hab'arta.. Ahankali yace

"My Baby is beautiful!

Hafsah ta gaji don haka ta bud'e idonta 

suka had'a ido.. tare sukayi murmushi "plz baby ki rufe fa"?

"Ok"

Ta kuma rufe idon..

Ya taso ahankali ya iso gabanta.. sunkuyo dai dai saitin fuskarta.

Numfashinsa daya sauka kan fuskantarta yasata saurin bud'e idonta bata shirya ba.

Ta zaro ido.

Yai wata dariya me sauti..

Uhum.. "Calm down"

Ya fad'a cikin rad'a"

Ita dai shiru ta kasa magana.

Hannunta taga ya Kama wanda hakan yasa jikinta b'ari..

Zobe ya ciro daga aljihinshi Gold ne mai kyau, ya fara sa mata ahankali.. tana son ta k'wace hannunta, amma kuma ta kasa, bata

son ta bada kanta da yawa.. Amma azuciyarta Allah Allah take yanayin ya shud'e, gabad'aya nutuwarta bata tare da ita..

Shiko fuskarta kawai yake kallo yana mata murmushi..

Ya gama sa mata amma kuma yak'i sakin hannun na ta.

K'okarin kai hannun nata bakinshi yake.. Ta zaro ido

*"Kiss wai yake shirin min?*😳

(ta fad'a a zuciyarta)


Tayi zumbur ta mik'e sai gata atsaye, ta k'wace hannunta. 

"Please stop it"

"Hmm ok"

"Am sorry I don't mean to hurt you"

Ta gyara tsayawarta ta Kalli zoben yai mata kyau sosai.

"Thank you"

Tace dashi.

"U deserve it"

"Baby kada dare ya min fa..

(Har yanzu a tsaye suke.)

Ya nuna kanshi 

"ok kina korana ne koh?

"No, you know, Wanan plan ne koh, kaga mama bata bani time da yawaba."

"OK you're right"

Tare suka fito ita da shi..

"Baby kije kuyi kuyi sallama ki mu tafi"

No, ka bari sai next haduwar mu.

"Bakya so Koh? 

A,a ba haka bane.

"Ok"

"Muje na raka ka koh.. ?

Suka jera har wajen motar shi.

Ya shiga ya zauna.

Ta rik'e murfin motar..

"Baby sai yaushe?

"Zamuyi, waya.

"Ok bye bye, I love you"

"Cool story dear"

Ya mata wani murmushi ya d'aga mata Hannu

"Bye Bye.

Sai da taga tafiyar shi sannan ta juyo.

A falo ta tarar da Basma tana danna waya. 

Ta d'ago ta kalleta tayi dariya "woo Hafsah Hamid kina wuta.. Irin wannan azababben guy haka?? 

Wallahi wannan mai zafi ne, gaskiya fa kin faso gari.!!

Murmushi kawai Hafsah tayi, "Hmm, Basma kenan akwai tsokana.

"Kinga"

Hannunta ta nuna mata.

"Kaii, wow.

Gaskiya yai kyau.

Am kinga bari nazo na wuce..

Ok kina shiga bed room ki chanja kayan.

Bayan ta fito ne tace 

"To basma nagode, fa sosai, zan tafi ki gaida mamanku"

OK zataji.

Har waje ta rakota

Suna tafiya suna hira. 

"Saura 2 weeks a koma school koh?"

"Inji Hafsah. 

"Eh, yanzu sai yaushe to?"

"Inaga sai an koma schl gaskiya"

"Ok shikenan munyi waya."

Sai da tahau napep sannan ta dawo.


Hafsah na isa gida 

ta tarar da dukka k'annenta da mamanta a falo. A tsarge take da kanta.. don haka ta kasa sakin jiki. 

Ta nemi waje ta zauna.

"Mama, na dawo.

Ok, ya jikin nata.

"Da sauk'i"

Make damunta ne 

"Ulcer ne."

"Allah ya sawwaqe"

"Amin"

Dai dai lokacin idon mama yakai kan, hannunta. Ahankali ta kirata cikin dakakkiyar murya.

"Hafsah?

A d'an razane ta d'ago wanda maman ma ta ga hakan.

"Zoben wane a hannunki"?

Tayi saurin d'ago hannun da zoben ke jiki,

"Am na Basma ne mantawa nayi ta taho da sh.

Hum Gold d'in kika taho mata dashi?

"Meya kawo shi hannunki."

"Um nunamin tayi wai mamansu ce ta taho mata dashi daga Dubai, shine muka manta na tawo da shi."

"Hmm to kawoshi kada ki b'atar mata "

Kamar ta rusa ihu haka taji,

jin wani son zoben take...

Tunda Yusuf d'in ya saka mata taji babu abinda zata bari ya raba hannunta da shi.

Mama zan sa mata fa a drawer, wallahi bazan b'atar mata ba fa"

Ta fad'a da 'yar shagwaba.

Mama ta d'an tsare gida.

"Ki kawoshi nace"

Ahankali take ciro zoben, tana tuno lokacin da yusuf d'in yake sa mata zoben, sai kawai ta yi murmushi.

"Mama ta kalleta da mamaki.

Ta mik'a mata.

Dai dai lokacin kuma wayarta tayi k'ara.

(Tunda ta je gidansu Basma ta cire wayar daga silent, don kada yusuf ya kira basu ji ba.)

Mama ta bita da kallon tuhuma.

Ita ma fargabar wayake kiranta take.

Bashir kuma tsorone ya kamashi, bai san maman tasan da zaman wayar ba. 

Amira ce tace 

"Laa Yaya waya sai miki waya.?..

Dai dai lokacin tana cikin yin maganar abbansu yayi sallama a falon ita ko wayar sai k'ara take...


[1/11, 12:09 AM] Hajeeyah Karimah (Writer): ♥♥♥♥

*ZAZZAFAN SO*

(Guba ne)

*A broken* 

*heart story* 

 💔💔


Story and writing by:


*Karima Tijjani Mansur* 

*(Hajeeyah Kareemerh)*

*Dedicated to:*

*Unique In Your Love Heart Members.*


*Khareemerh Naji daku:*👏🏼

🌷Sumayya hadi(tauraruwar mace group)

🌷Zulaihart (kundin novel group )

🌷Khadeejah (kundin novel group)

🌷Umme marafa (sirrin mijinki..grp)

🌷Fateemah (jidda Tijjani novel)

🌷Maman afnan (zazzazan so nvl grp)

🌷ZEE Aliyu (Zazzafan so nvl grp)

🌷Aeeshart Umar (zazzafan so nvl grp)

*Am proud of you Masoya sune komai* 👏🏼👏🏼


📄 *14*



*"Sannu* da zuwa"

Mama tareshi dashi ta mik'e ta karb'i jakar shi. 

Baiyi Magana ba akan wayar duk da yanajin ringing kuma yasan bana wayar Mamansu bane. Yaran ma sannu da zuwa duka yaran suka mishi.

"Abba Sannu da dawowa"

Cikin sakin fuska yace musu 

"Yawwa sannunku koh"

Suka shige falon Mama.

Yaso yace mata wacce waya ce take ringing a 'Main parlour'? domin baiga alamar anyi bak'i ba. 

'To sai kuma wani abu ya d'auke hankalinshi gaba d'aya..'


♥♥♥♥♥♥♥♥♥♥


Basma ta d'auki wani salo na yawan zuwa gidan su Hafsa, suyi ta hirar su. Dama ita ba wasu k'awayene da ita ba, Jamila ce kawai..

Kwanaki sun shud'e, har su Hafsah sun koma makaranta, Yanzu tana Aji na k'arshe a secondary wato SS 3.

Wanda tun ranar da suka had'u da Yusuf, agidan su Basma basu k'ara had'uwa ba. Sai dai waya ce koyaushe suna yinta duk dare da kuma sanyin safiya..

Hafsah sosai takan tsaya tayi tunani akan soyayyarsu da Yusuf..

Dole ne ta kirashi da 'First Love' d'inta (Saurayinta na farko) ita dai tasan ko ada bata da saurayi, irin soyyayyar nan ta makaranta da akeyi da class mate duk batayi kwata-kwata.

Shiyasa take jin wani abu na musammaman game da Yusuf.

Misali aduk randa bai kirata ba sai ta tsinci kanta cikin kewa da damuwa, sai taji kamar ma bata da lafiya.

Ko tunashi tayi sai 

taji wani nishadi a tattare da ita.. Sau da dama Mama tasha kamata tana murmushi ita kad'ai, idan ta tambayeta "Ke lafiyarki?

Sai ta ce mata "Hmm Mama babu komai."

Mama ta kance "Allah ya shirya"

Hafsah na ayyanawa ('imagine') kanta irin rayuwar da zasuyi da Yusuf idan sunyi aure..

Ko da a makarantar boko idan ana hira, irin ta aure kamar yadda 'yan matan yanzu kanyi, (musamman yara 'yan secondary)

Takan nuna ra,ayinta akan Miji mai kula da matarshi ('Caring husband') a ra,ayinta bata son Namiji mai nuna halin 'ko-'in-kula' (I don't care attitude).

Lokacin suna tare da Jamila.

Wata rana Jamilar ta tab'a d'aukar Diary (Na Hafsah). Da yake Jamila akwaita da son bincike da kuma neman sanin duk abinda bata sani ba musammaman akan harkar 'Gayu'.

Hafsah wai me kike rubutawa anan ne?? 

(dake lokacin a yarinta ne) kuma ba wani abu ne cikin Diary d'inba banda shirme irin na yarinta. Hafsah ce mata tayi

"Ki bud'e ki karanta mana"

Jamila ta hau bud'e Diary d'in page by page.. Abubuwa take gani kala-kala aciki kamar:

*"My first-day at school*

To day is the first day of my secondary school..

Wani shafi (page) daya burge jamila shine Wanda taga an rubuta.. 

*I WANT MY FEATURE HUSBAND TO BE...*

Beautiful, Tall, and Mid obese.

'Colour of dressing: English wears..'

Behavior: I want him to be: Humble, caring, sociable, Cool-temfered and Good- hearted,

That would scriface everything to me!

*And then "Wanda baxai zai min kishiya ba!*😅

And I want to him to always say 'I love you'!

Jamila tayi dariya 

Hahh Hafsah kenan Allah ya baki"

"Amin Jamila.

"Ni fa kafin ma in aure ka sai na tantanceka"

Jamila ta kalleta "Koh? 

Na tsani 'Mugun Miji'

Wallahi biki ga aunty na yadda mijinta ke mata wulak'anci ba!

"Allah ya bamu nagari" inji Jamila.

"Amiin. Aini kullum nayi sallah sai na rok'i Allah ya bani Miji na gari." inji Hafsah.

(Yana da kyau ga kowacce budurwa ma rok'i Miji na gari wajen Allah SWT) # khareemerh.

Hmm Hafsah ki bani wannan littafin mana. Tana nufin Diary d'ina.

Kai Jamila ai nawane sai dai in munje store da abbanmu zan d'akko miki in sha Allah..

"Au d'akko wa ake"?

"Kiji ki, I mean I will bought it for you"

"Au nagode sosai Hafsah.

Aminci sosai Basma da Hafsah sukeyi yanzu, wanda kowa acikin ajin yake mamakinsu.

Wata ranar Asabar Mama tasa Hafsah ta shirya taje gidan 'Hajiyah' wato kakarsu ta wajen uba. Ta dad'e bata je gidan ba.

Kwana d'aya zatayi ta dawo.

A unguwar ja,en gidan yake ta shirya tun wajen 11:00am.

Hajeeyah Amina dattijuwa ce 'yar kimanin shekara 70. Tana da halin dattako, Shiyasa da wuya ka ganta gidan d'anta (Abbansu Hafsa) tana da kawaici bata saka baki a cikin al,amransu. Sai dai hakan bai hana idan taga b'arna ta nuna musu hanyar gyara ba.

Fara ce ita, kyakyauwa da 'yar furfura akanta. Tana da tsafta, kuma ita kad'aice a gidan nata, sai wata yarinya me mata aiki sai kuma autanta dake shirin yin aure nan da wasu watanni wato k'anin abbansu Hafsah 'Auncle Abdallah'

Hafsah tayi sallama cikin falon da Hajiya ke zaune.

'Wa alaikumussalam da Hafsah na"

Hafsah ta shiga cikin falon ta ajye Jakarta a gefe.

Ta zauna a k'asa Hajiya na kan kujera.

"Hajiya ina kwana"

Lpia lau Hafsat.

"Kece yau a gidan kenan? 

"Gaskiya kin rabu da zuwa kwana biyu"

"Saboda school shi yasa"

"Eh hakane kuma"

"Ya Mamantaku da sauran k'annen naki?

"Suna nan lpia lau suna gaisheki."

"To madallah"

"Ki shiga ciki ki ajye jakar taki mana"inji Hajiyah.

Hafsah ta mik'e ta d'auki jakarta ta shiga wani d'aki dake falon.

Katiface shinfid'e a daki'n kawai.

Ta ajye sanna ta cire mayafinta ta fito.

Hira suka d'an farayi da Hajiyar.

"Nace ko kuna dai yin k'okari a makaranta Koh?

Hafsah ta d'anyi dariya 

"Sosai ma Hajiya"

"To Allah ya taimaka"

"Ni nafi son ma kiyi karatun likita."

"Hah ai Hajiya ni ba a science class nake ba, sai dai bashir, shine ma yake son ya zama Doctor"

"Hajiya ta kalleta to ke me zakiyi?

"Law zan karanta"

Menene kuma haka?

"To lawyer zan zama!

Hajiya ta harareta "Ke dahalla bana son shirmen banza mak'aryaci ya kike so ki zama ?

Hafsah ta Shek'e da dariya.

Hajiya lawyer fa ba mak'aryaci bane"

"Ke rufe min baki."

Shi Habibun (Tana nufin Abba) ne yake so ki karanta wannan karatun k'aryar ko me?

"A,a ni nakeso dai Hajiya.. 

"To kwa idan na isa bazakiyi ba.."

Hafsah ta k'unshe dariyar ta. (Wannan rigima ta Granny ta fad'a a zuciyarta)

Ni ko sanda Hamidu (kakan su Hafsah) ya fito zai aure ni, dama ya gama sakandara (Secondary), da yace min karatun 'Loya' (Lawyer) zai cewa nayi indai yayi na fasa aurenshi.. Shine fa ya fasa ya koma Malamin makaranta..

"Hahh,Gaskiya Hajiya kice kin ja mishi class"😅

"Ke ja,ira fad'i da Hausa muji"

Cewa nayi

"Ashe tun da ma 'yan mata suna juya saurayi?

Gidanku kin d'auka muma Irinku ne.. Saiki ga yarinya ta na bin saurayi unguwa don rashin kamun kai.. Mu ada ba sai yazo nak'i fitowa ba ma, kuma dole ya aikomin da kud'in zance!!.. Ku ko yanzu da ko kwandala basa baku??😒

Hafsah tayi dariya

Hajiya ai yanzu ba da bane.. 

"Kyaji da shi dai ni dai ki kawon shi murmushi gaisa.."

Hafsah an tab'o mata inda ke mata k'aik'ayi '.

Ai Hajiya yau ma zai zo gidannan.

"Au haba"?

"Yayi kyau ai"

Tashi kije kitchen akwai farfesu ki d'akko ki ci.

"To Hajiya."

Da daddare Hafsah tayi kwalliya sosai saboda zuwa da yusuf zai yi..

Hajiya ce harda bata turare ta fesa..

"Ku dinga sa turare sosai, saboda maza nason k'amshi."

"Kin ganki yanzu kin yi kyau sosai, shiyasa kike burgeni bakya yin kwalliyar nan ta aljanu da kuke"

Hafsah tayi dariya "Gayu ne fa hajiya"

"Ke ina wani gayu?

Ungo saka kwalli sai ku dinga barin ido fari fat"

Hafsah ta karb'a tasa.

Lokacin kuma wayarta tayi k'ara alamar Yusuf ya iso kenan..

INA FATAN KUNA JIN DAD'IN WANNAN LITTAFI *ZAZZAFAN SO*

DOMIN COMMENTS KO GYARA KO NEMAN K'ARIN BAYANI 09072802875

*HAJEEYAH KAREEMERH CE DAI*👌🏼

[1/11, 12:09 AM] Hajeeyah Karimah (Writer): ♥♥♥♥

*ZAZZAFAN SO*

(Guba ne)

*A broken* 

*heart story* 

💔💔

Story and writing by:


*Karima Tijjani Mansur* 

*(Hajeeyah Kareemerh)*

*Dedicated to:*

*Unique In Your Love Heart Members.*


*MUCH OF LOVE TO YOU MY AUNTY Maryam Adam Gid'ad'o. (MAMAN ASLAM) ALLAH YA RAYA SWEETIE*👏🏼😘😘





📄 *15*




*Ad'akin* Auncle Abdallah ta sauke shi, tunda suka zauna ya kura mata ido ko kiftawa bayayi..sai lumshe su kawai da yake..

Hafsah taji gaba-daya ya cika mata d'akin wani kwarjini yai mata. Gashi yau shigarshi ta yi mishi kyau sosai.

Ta gaji da shirun daya mamaye d'akin.. Ahankali ta d'anyi murmushi cikin muryarta mai dad'i tace.

Dear mai ya "samekane kayi wani silent da kai."

Yai ajiyar zuciya ya shafa summary kanshi, ya k'ara zubo mata fararen idanuwanshi da suka juye suka zama wani kala daban sosai(Sexy).

Sai taji wata fad'uwar gaba, tayi k'asa da kanta ga barin kallon idanunshi.

Can tajiyo shi cikin wata sassanyar murya k'asa k'asa yace "Hafsah!!

Tanajin yau ne rana ta farko daya kira sunanta.. Taji kiran ako ina najikinta.

Ta d'an dago ahankali batason kallonshi bare kuma kallon da yake mata. 

"You're killing me!

Your eyes is killing me, your smell, your smile.. 

I love you..

Ya d'an yi shiru sannan ya d'ora.

"Today is a special day for us.. "

"Yau ne first August ranar dana had'u dake one year ago.."

Ya d'anyi shiru sannan yaci gaba..

"Am Please I need some thing from you idan zan samu?

Ta kalleshi a hankali tace "Menene shi"?

Yai murmushi.

"I have a gift for you, and I want you to give me something special."

Tayi murmushi "Dear me Kake so to?

Yai ajiyar zuciya ahankali ya mata murmushin gefen kunci ya kalleta ta gefen ido.

"Everything is ok"

"No Ni dai ka fad'amin me Kake so..

"No, ki duba abu daya dace dani mana koh?

"Ok"

"So ka bari next idan kazo zan baka"

"Nooo ni dai yanzu nake so Pls I will see idan kina k'aunana"

Haba Baby wa ya ce maka bana sonka.. 

"I love you"

Hmm Ya lumshe ido 

Thank you 'My darling'

"Ya rufe idonshi am waiting you"

Shiru Hafsah tayi tana tunanin me ya dace ne ta ba wannan rigimammen saurayin nata"

Kawai sai wani tunani yazo mata.

Ta kalleshi yar Yanzu idonshi rufe suke ya d'an daga kanshi sama..

Hakan ya bata damar kallonshi sosai, sai taji jikinta yai wani iri, Yusuf nada kyau mai d'aukar hankali.

Murmushi yake yi ahakan idonshi rufe..

Ta ayyana da tana da babbar waya photo zata mishi a hakanshi..

Sannan hakan da yayi yasa mata wani tunani da shaukin

'Wai dama ace sunyi aure shi mijinta ne..'

Ta Kalli jajayen leb'unanshi da yake motsa su ahankali..

Azuciyarta tace k 'Kamar ba d'an hausawa ba'

Dai dai lokacin yai wani juyi yana jujjuya kanshi kamar wani yaro

"Baby am still waiting, am tired am tired" 

Ahankali kuma kamar cikin rad'a yace "Please,.. Please."

Sai da ta firgita da abinda yayi, banda kuma shauk'in daya jefa ta ciki..

Da kyar ta samu tace

"Am sorry."

Ta Mik'e ahankali ta nufi kujerar da yake zaune, kusa dashi ta zauna sannan tace

"Baby please open your eyes first.."

Ai kafin ta rufe baki ya bud'esu ya zubo mata su har da k'ara kwalalo mata su..

Sannan ya d'an so rud'ewa bai zaci tana daf da shi ba, a cikin idon shi ta fahimci haka..

Tayi ta maza ta fara mishi magana ahankali,

"Baby kace kai yanzu kake so koh?"

"Ya gyad'a mata kanshi"

Tall d'an marairaice 

Plz can't u even allow me to enter the house to get something for you"

Ya girgiza kai 

"Kina nan nidai u won't move even a step"!!

"Wash,..hmm.."Ok"

Ta fad'a sannan ta d'anyi shiru..

Can tace mishi 

"Are ready"

"Yes" yafad'a kamar rad'a.

"Give me attention plz"

"All ears, eyes on you"

Ahankali ta bud'e baki Yusuf ya k'agu yaga me zata mishi..

Wak'a ta fara mishi cikin sassanyar muryarta mai dad'i..

Wak'ar celinedeon "I love you"

Ita ta fara mishi..

Babu abinda yake kallo sai yanda take motsa leb'unanta..

Yayin da sautinta ke ratsa dukka Sassan jikinshi..

Cikin wata irin sassanyar murya mai karamin sauti take mishi wak'ar.

Sai da tazo inda ake cewa "I..loove..youu.. Please  say you loove me too.."

Sai tai dif..

Shiko lumshe idonshi yai, shiru kusan minti d'aya sannan ya gama sai ta kanshi ya d'ago..

Ajiyar zuciya yai a hankali da sautinshi da dama can baya d'aga shi bare kuma yanzu.

I love you my dear.. 

Ya d'anyi shiru..

I love your sweet voice 

I love your melodious song..

"And I love your sweet lips"..

"Hmm" ta iya cewa. Kawai

Ya dage mata gira 

"Really"

Sannan ya k'ara kiranta. 

"Baby!

bata iya amsawa ba 

Sai ta kalleshi kawai.

"What's next? I need more pls..

Ta d'ora d'an yatsanta akan leb'enta so take ta tuno me kuma ya dace..

bata son ta gaza, ko kuma ta b'ata mishi rai..

Tana tunanin taji yace

"Still thinking, why you always think b4 kimin abinda nakeso?

Ta girgiza mishi kai, kawai.

Hmm da nine kinsan me zan baki?

"No"

Cikin rad'a yace "Sudden hug"

"And then hot kiss"

"Hum" hafsah tace Shiko dariya yai..

"Am waiting you.

"OK"

"I Give you a chance to see your face through my Eyes for a 2 minutes"

"Humm gud Story"

"But with one condition" inji Yusuf.

Uhum what's it?

"Kada ki kiftamin idonki, sai time d'in ya cika.."

"OK I agreed"

"OK let me set a timer".. Right?

"Yes"

Ya saita a wayar shi sannan yace..

"Ok"

"Mun shiga time enmu."

Wani irin kallo ya fara mata, yayin da kawai ita kamannin shi take gani suna sauyawa..

Basufi second 30s ba aiko ta kifta.

Tana k'ifta wa taji ya rik'o kuncinanta (cheeks) da hannayenshi biyu, ahankali kuma yana k'ok'arin had'a fuskokinsu..😳

Ayya! Tuni ta k'wace da wata azama ta mik'e shima sai gashi tsaye, dai dai lokacin kuma Auncle abdallah ya sako kai cikin d'akin, ya gansu tsaye, kamar kuma tsaiwar tasu bata shiri bace don idonshi ya nuna mishi kamar wurgo Hafsah akayi..??

Shi ba ma wannan ba, yasan tabbas yayanshi baya barin hafsah ta kula samari to ya akayi hakan ta faru, wato sai anan zata zo tayi zancen,kuma meye nayin irin wannan tsaiwar daf da daf haka?

(Don Yuduf daf da ita ya tsaya ya fuskantota kamar sa had'e)

'Shikuma gashi sai huci yake (Yusuf)'

Auncle Abdallah ya tsaya yana k'are musu kallo so yake ya gano dalilin tsaiwar tasu a tsakiyar falon alhalin ga kujeru, sannan ya tabbatar ba shigowarsu d'akin kenan ba, don Hajiyah ce ta sanar mishi suna d'akin.

Yayin da Hafsah bata zaci ganinshi ba, sai gashi yazo a wata gaba, gabanta ya tsananta fad'uwa,musammyanda taga ya bud'e baki yana shirin yin magana..

Tsoron abinda zai fito daga bakinshi take, da kuma matakin da Abba zai d'auka idan asirinta ya tonu...

👏Yours a kullum 

*(Hajeeyah Kareemerh)*🍒

*I need your comments just to encourage me!*👌🏼

Love you all My fannnss😘😘😘

[1/11, 12:09 AM] Hajeeyah Karimah (Writer): ♥♥♥♥

*ZAZZAFAN SO*

(Guba ne)

*A broken* 

*heart story* 

 💔💔


Story and writing by:

*Karima Tijjani Mansur* 

*(Hajeeyah Kareemerh)*

*Dedicated to :Unique In Your Love Heart Members.*

*بنت أبوبكر*

hak'ik'a kina k'aunar wannan novel ina godiya.👏🏼




📄 *16*



Sallama ya musu, Yusuf ya amsa.

Sannan ya matsa kusa da su ya mik'awa Yusuf hannu suka gaisa..

Sai lokacin Hafsah ta sami damar matsawa daga kusa da Yusuf, ta d'an wayance ta gaida Auncle Abdallah.

Ya amsa cikin sakin fuska, sannan ya kalli Yusuf yace.

"Kuyi hak'uri fa, na shigo muku babu shiri"

Kafin yayi magana Hafsah tayi saurin cewa..

"Auncle dama, mun gama raka shi zanyi ya gaida Hajiyah"

"OK shikenan to"

Ya fad'a yana binta da wani kallo da bata san na meye ba..

Ta kalli "Yusuf mu tafi koh?

Ya bita da wani kallon shima, sannan ya bi bayanta.

Auncle Abdallah ya k'ara binsu da kallo.

Yarinyar na da hankali bai jin zata saka rayuwarta cikin irin wannan soyyayar ta zamani.

Sannan me ma ya kaishi zarginta shida kawai shigowa yayi ya ganta tsaye??

Yai A,uzubillah" azuci. Amma kuma yana da yak'inin bata zance Yarinyar ko dai yau suka had'u ne?..

Ya san dai ba zata taba gangancin kula wani bada sanin abbanta ba.

To ko Yaya Habeeb d`in ya sakko da raayinsa ne"?

Ya kasa gano amsar, kawai sai ya bar wannan tunanin, ko ma dai menene ai yarinyar ta girma..


♥♥♥♥♥♥♥♥♥♥


Da sallama suka shiga falon Hajiya, bayan Hafsah ta shiga ta fad'a mata zai shigo.

Yusuf ya zauna akan kujera Hafsah kuma na kusa da Hajiyah..

"Granny, ina yini"

Yusuf ya gaisheta.

"Lpia lau" ta amsa cikin fara,a.. Sannan tace 

"Ya mutanen gidan duk suna Lpia?

"They are all fine wllhi"

(sabon-salo🤔)

Hajiya ta fad'a a zuciyarta.

Suka d'anyi shiru sannan Yusuf yace

"Ajiya (Hajiya) you remembered me my grandma,.. Kakana Dada, she was old enough like you before she died.."

Hajiya dai cewa tayi 

"Allah sarki.

Ya kallo Hafsah da tayi shiru ya mata kallon da ya saba.

"Baby, let me go home"

Ya mik'e sannan ya kalli Hajiyah ya had'e hannayenshi biyu alamar girmamawa (kamar yadda indiyawa suke) sannan yace.

"Stay strong and blessed grandma."

(wai fa shi nan addu,a yai mata)😅

"A sauka lafiya."

Hajiyar tace masa.

"Bye bye"

Ya d'aga mata Hannu.

Hafsah ta mik'e ta bishi..

Suna fita taga ya wani had'e rai.

Tuni tana d'an sha jinin jikinta.Ta rakashi har waje, inda ya ajye motarshi.

Har yanzu ko k'ala baice mata ba.

Suka tsaya a bakin motar, ta d'anyi murmushi sannan tace,

"Baby me ya faru ne?

Ya d'an kalleta ya watsar. Sannan yace.

"OK, ke biki san abinda kika min ba koh?.. Is good, ai nine nazo gidanku ai,..This gave you opportunity to disgrace me!".. Ok let's see if you will see me here again!"

Take tsoro ya kamata. Ta tausasa murya.

"Haba Baby, me kake fad'amin ne ? Me aka maka kuma koh Hajiyah c..

Bata k'arasa ba ya shige motar shi ya figa da gudu ya bar ta da k'ura.

Ta d'aura Hannu aka tare da cewa "Oh my God, me ke shirin faruwa da ni ne?

Tana tsayen uncle Abdallah ya fito daga gida, dole ta bar wajen.

Ta shiga gida zuciyarta a jagule.. Wannan wacce irin al,mara ce?

Yanzun idan Yusuf ya rabu da ita ai ta kad'e.. Take kwallah ta ciko mata ido.

Har yanzu bata gano me yasa ya chanja mata ba, a cikin abinda baifi mintuna biyu ba.

To koh don ta kaishi wajen Hajiyah ne.? Ko kuma yanayin da Hajiyar ta karb'e shi ne bai mishi ba?? 

Yace wai tayi 'Disgracing' d'insa?

Bata lura ba ashe har ta shigo falon Hajiyah, tayi saurin goge fuskarta, kawai sai ta nufi hanyar d'akin kwananta.

Muryar Hajiyah taji tana ce mata,

"Ke Hafsah zo nan"

Dam.. Gabanta ya fad'i, yanayin yadda Hajiyar ta kira ta ya nuna mata akwai wata a k'asa.

Ta tako ahankali ta zauna a k'asa gefen Hajiyah.

"Gani.

Hajiya ta fara magana fad'a-fad'a.

"A ina kika samo wannan Yaron?.. bata jira cewarta ba ta d'ora.

"Yaro kamar ba d'an bahaushe ba, sai wani turancin k'arya yake yana wani b'ab'bata hausa?..

"Kuma don rashin d'a,a ya wani gaisheni yana kan kujera koh..? 

Wai ku 'yan boko har yana cemin wani 'Bebai' (bye bye) saboda raini😠

" wato don ina kakarki ba zai girmama ni ba. Ko ance mishi wasa nake da ku?..

"Kiyi ha'kuri Hajiyah"

Hafsah ta fad'a tana share kwallah.

"Ke hak'uri ya kama." 

Hajiya ta fad'a tana kauda kai gefe..

"Yo ni Allah na tuba meye abin yabawa a wannan yaro abu kamar 'Karan-bawul'🤣

"Yaro sam babu hankali a tattare da shi.?

"Shi habibun har yana ina kike kula wannan d'an?"

Gaban Hafsah ya fad'i. Ya zatayi idan Abba yasan da wannan magana?

Sai yanzu ta gane kasada tayi fa ta kawo Yusuf gidan hajiya, sam ta manta zancen zai iya zuwa kunnen Abba, idonta ya rufe buqatar ta kawai ganin Yusuf, nan fargaba da tsoro suka cika ranta.

"Don Allah kiyi hak'uri Hajiyah."

"Hmm Ni me akayi min ki tashi kije ki kwanta.

Zumbur ta mik'e dama Zaman ya isheta, to da wanne zataji?

Ta fad'a kan katifa ta kife kanta, tana tuno maganganun Hajiyah..

"Wai Yusuf bai da d'a,a?? 

To me yayi wa Hajiyan?

Ita bata ga me yai mata ba? Meye abin kushewa a Yusuf?

Ahankali taji haushin Hajiyah na shigarta. Yanzu idan taja Abba ya rabasu ai an cuceta..

Sai yanzu take danasanin kawowa Hajiyar shi.

wallahi ba don dare yayi ba babu abinda zai hanata tafiya gida.. Haka kawai don jininsu bai had'u ba sai ta hau aibata shi?

(A tak'aice dai idanun Hafsah sun rufe, so ya hanata ganin aibin Yusuf.

Ta manta abinda babba ya gani yaro baya iya hangoshi.

Zatonta k'iyayyar Hajiyah da 'Boko' ne yasa ta aibata Yusuf, wanda azahiri Hajiyah bata k'in boko sai dai tana kyamatar dab'iun turawa da yaran yanzu ke ara yawanci, wanda ita sam 'ya'yanta da jikokinta Allah ya tsare su.

Kana ganinsu kaga wayayyu wad'anda Bokon ya ratsa sai dai kuma wayewa irinta addini da sanin rayuwa da kuma addu,ar iyaye ya hanasu su kaucewa hanya.

Sab'anin irin Basma ko Yusuf wad'anda basu sami wannan gatan ba. Amma Hafsah sam ZAZZAFAN Son data ke yiwa Yusuf ya hanata ganin hakan.)

Tunaninta ya tsaya data tuna yadda suka rabu da shi Yusuf d'in..

Tayi saurin mik'ewa ta dauki wayarshi ta danna kiranshi.

wajen sau biyar bai d'aga ba.. Sai a na shidan ya d'auka

"Mene ya faru?

Da haka ya amsa wayar..

Cikin kuka tace:

"Haba Yusuf yanzu na chanchanci haka a wajenka?..Please me na maka? Baka ganin irin son da nake maka Koh?

"To me zan miki ne while kink'i ki min abinda nakeso, mene amfanin relations enmu, kina wulak'anta ni, So I think kawai mu rabu, am tired with this meaningless relation. Wanda babu wani abu da kike min and u always claiming kina so na!?.. A ina son yake?


*Nikam nace azuci yake Yusuf*😇🏃🏼‍♀


Ya cigaba u can't even allow me to kiss you?.. Wanne irin Soyaya ne kina min?..

Sai yanzu Hafsah ta gano zancen.. Tab' al,amra sun Chakud'e.

'Anan ya dace ta fahimtar dashi wani abu, amma kalmar 'su rabun' daya fad'a shine ya rudata ga kuma tasirin soyayyarshi a zuciyarta bata son ta kuma bata mishi, don haka ta kwantar da murya ta shiga rarrashinshi.'

please kayi hak'uri ni ba ina nufin komai ba ne,..

please ka daina fad'amin cewa mu rabu, numfashi na ba zai d'auka ba." please am sorry.

"I know I hurt u but

trust..

"Noo ya katseta, I need to rest, ki kyaleni kawai.

Ya katse wayar.

Tafi minti biyar bata motsa ba, bare ta cire wayar daga kunnenta..

Ya akayi Yusuf ya iya fushi haka shi baya lura da cewa hakan bai dace ba?

Baya tausaya mata da irin son da take mishi har yake ik'irarin su rabu??

Wai Ita meye mafitarta a wannan al,amari, zata kwa iya yin abinda yakeso?.. Wata zuciyar tace

"Idan har shi kad'aine mafita ba!!

To ldan tayi haka kuwa laifi nawa tayiwa iyayenta, musammaman ma abbanta?

Ta mallaki waya bada saninshi ba.

(Duk da tana da yak'inin lokaci yake jira ya mallaka mata ko da iPhone ce idan tana so)

Tana tare da Yusuf bada saninshi ba.

Sannan ta zo taci amanar tarbiyyar daya mata??

Wata zuciyar tace,

"Hafsah idan fa kika rabu da yusuf kin rasashi fa har abada... Ki tuna gogewarshi da wayewarshi ga kud'i kuma, duk matan garinnan ke kad'ai ya zab'o kina da yaki'nin ('Assurance') baya kula kowa sai ke.

Secondary level kike , amma haka ya zab'o ki..

Yusuf ya fiki sanin rayuwa amma ahaka yake sonki. Shin ma ya zaki iya jurar rashinshi bayan shine daidai da burinki?

"Hafsah idan fa kika yi asarar Yusuf ba zaki sami wanda ya fishi ba..

*Ku biyo ni don jin ko Hafsah zata bi layin da jamila tabi ne??*

*Taku HAJEEYAH KAREEMERH*🍒👏🏼👏🏼

*I need your comment to encourage me!*

[1/11, 12:09 AM] Hajeeyah Karimah (Writer): ♥♥♥♥

*ZAZZAFAN SO*

(Guba ne)

*Abroken* 

*heart story* 

💔💔


Story and writing by:

*Karima Tijjani Mansur* 

*(Hajeeyah Kareemerh)*

*Dedicated to:*

*Unique In Your Love Heart Members.*



💐 Doctor Hauwa,u Ibrahim Umar (Gambosy)

💐 Maman chappa 

Aysha Naseer sheriff 

And kawar rai da rai _AYSHA D'AHEER ADAM_

💐💐💐💐💐💐💐💐💐💐

*And also My lovely sister Sadiya Lawan Abdullah*

*"I love you from the bottom of my heart."*♥♥♥





📄 *17*




*Tunani* ya hanata sakat, da k'yar ta samu bacci ya d'auketa.

Da asuba tatashi tayi sallah, amma ta kasa komawa bacci. Tana kwance kawai shiru har yanzu takasa samun mafita akan al,amarin.

Hajiya dai bata kuma yi mata maganar Yusuf ba.

Da la,asar ta hau shiri. Hajiyah ta kalleta "To Yanzu Hafsah sai yaushe kenan?" k'ak'alo 'yar dariya. 

"Hajiyah sai an kwana biyu dai"

"To shikenan, sai na ganki"

Bayan ta gama shiryawa ta d'auki jakar ta.

"To Hajiyah zan tafi. To shikenan ki gaida mutanen gidan"

Kyautar atamfa da turare Hajiyar tayi mata.

Bayan taje gida ma tunanin ne ya dameta, ta kira Basma amma wayar ta bata shiga ba.

Gashi yar yanzu Yusuf bai kirata ba, ita kuma tsoron kiranshi take, bata san abinda zai ce mata ba. Ahankali hawaye yake bin kan kumatunta, wani zafi zuciyar ta ke mata.

Kwance take bisa filo akan gadonta.ta d'aga kanta sama..

Zancen Jamila ta tuna *"Hafsah baki so bane shiyasa*

Tabbas lokacin hakane, shiyasa taji haushin Jamila alokacin don taga tana kuka akan _rashin-masoyi..._

Ta shafa kumatunta taji hawaye wato dai da gaske kuka take akan wani..?

Ahankali ta mik'a hannu ta d'akko wayarta, text ta rubuta mishi kamar haka:

*I have committed a sin to make you sad,*

*and am realizing that am very bad,*

*so, plz forgive me* *to lessen the grief,*

*ur forgiveness will led to a relief,*

*So plz forgive me*

Ta tura mishi, sai lokacin tayi ajiyar zuciya.

Bashir ya shigo cikin d'aki nata.

"Yaya kizo Abba ya dawo yace ina kike."

Tilas ta mik'e ta nufi hanyar toilet d'inta,

Bashir gani nan"

Fuskantarta ta wanko sannan ta fito ta zari dankwalinta bayan ta b'oye wayar ta ta fita.

"Yaya. Abba ya kirata bayan ta zauna. Ta d'ago ta kalleshi.

"Na,am ta amsa a k'asan mok'oshi.

Baki da lafiya ne? Ta girgiza kai "A,a"

"To ya kika baro min Hajiyata.

"Tana nan Lpia tace tana gaidaku"

"Gobe in sha Allah zanje in gaidata, kwana na uku kenan ban je ba" 

Ya fad'a yana kallon mama.

"Ai shiyasa na tura Hafsan saboda an dad'e ba,a je mata ba." 

Inji mama.

"Ai kin kyauta"

Ya Kalli Hafsah cike da kulawa. 

"Ko dai baki so baro gidan Hajiya ba ne?

Ta d'anyi murmushi "A,a Abba"

"Kinga yaya katin DSTV d'innmu ya k'are kinga babu kallo yau, ki karanta mana wannan kinji.

Ya fad'a yana mik'a mata littafin 'Magana Jari ce' (Na Marigayi abubakar Imam)

Ta sa hannu biyu ta k'arbi littafin.

"Abba wanne za,a karanta?

"Ki Karanta mana mai dad'i,ko wanne ma."

Mufida tace "Abba ni ma zan karanta."

Bashir ya harareta "sai kace iyawa zatayi.

Abba yai murmushi "Wa yace maka mamana ba zata iya ba? "

Labarin 'HASSADA GA MAI RABO TAKI'

Shi ta fara karanta musu, tanayi abba nayi mata gyaran hausa saboda Hausar irin ta da ce me sarqaqiya.

Labarin nada tsaho da kyar ta k'arasa.

Ko babu komai Hafsah ta d'an manta damuwarta zama cikin 'Familynta' ya d'ebe mata kewa da kuma damuwa.

Abba ya d'anyi musu sharhi akan labarin, Mufida ta dameshi da tambaya

"Abba Menene 'kusumbi'?

Abba yayi dariya kije ku kwanta da safe zan fad'a miki.

Yasan idan ya fad'amata sai ta k'ara k'irk'iro mishi wata tambayar.

Suka mik'e suka nufi d'akinsu.

"Ayi addu,a dai, inji Abbah.

"To Abba" Mufida ta fad'a.

Babu laifi Hafsah ta sami nutsuwar zuciya, damuwarta ta d'an ragu game da Yusuf. Yanzu ta juya akalar tunaninta izuwa nema musu 'Mafita'

akan al,amarin.

Meyasa Yusuf yake haka ne?? wai dama haka halinshi yake ko kuwa jiya ne kawai yai mata haka?.. 

Ko dai dama bata fahimci halayyarshi bane?

Duk wani saurayi na k'warai mai yin so tsakani da Allah ba zai tab'a yunk'urin zubar da kimar wacce yake so ba, zai iya jure komai saboda ita. Amma shi kodai manufar soyayyarshi ita ce 'Neman wani abu daga gareta'??

Tayi saurin korar wannan tunanin daga cikin zuciyarta.

*'So hana ganin laifi'* 😇

Wani b'angare na zuciyarta ya k'alubalanci zarginta akan Yusuf.

Hafsah biki yiwa Yusuf adalci ba. Shekara d'aya yana jiranki, da haka yake nema daga gareki ke kad'ai ce mace a duniya? Amma haka ya zauna jiranki... Kuma kirasa shaidar da zaki masa sai wannan? Saboda ansami 'Akasi' na lokaci d'aya??

Hafsah ki tuna waye Yusuf, murmushinshi, kalamanshi, soyayyarshi gareki.. Bakya tunanin idan kin rasashi kin tafka 'asara'?

Zuciyarta ta cigaba da karanto mata,hakan ya tilasta mata d'akko laifukan kacokan ta d'ora su akanta...

Meyasa take yi mishi kwalliya?

Meyasa ma jiyan tasashi kallon cikin idanuwanta, tabbas itace ta jawo koma menene. Ai kowanene ma dole ya sami rauni, balle kuma da tasiri soyayarta. 

Dole ne ta chanja tsarin mu,amalarsu...

Wannan ne matakin farko da Hafsah ta d'auka duk don tsoron kada Yusuf ya tsere wa samunta.

Bata samu bacci da wuri ba.

Da asuba Abba ya shigo tashinta, bayan ta yi sallah ta koma ta kwanta, cikin sa,a ta samu bacci mai nauyi.

Bashir ne ya shigo d'akin yana dukan filon (pillow) da take kwance.

"Yaya wai mama tace, ki tashi munyi late wai ko baki da lafiya ne?

"A,a yanxu zan shirya."

"Ok Yaufa har 7:00am tayi."

"Ok Kujira ni."

Agurguje ta shirya ta fito.

Amakarantar babu laifi ta d'an saki jiki, tunda a ganinta ta samo maganin matsalar, sai dai damuwarta d'aya ce 'bai kirata ba' sai kuma tunanin, ya zatayi ta dawo da mu,amalar su kamar da, don tasan Yusuf da tsawaita fushi..

Tana cikin Aji bata fita break ba. Tayi shiru taji an daki bayanta.

"Shegiya H. Hamid wa ya had'a miki tension? Ta fad'a lokacin da take zagayowa kujerar kusa da Hafsah ta zauna.

Hafsah, ta d'ago da sauri jin muryar Basma yunus.

"Au dama kinzo yau najiki shiru a class"

Tai dariya cikin muryarta mai karad'i tace,

"Wallahi nazo.

Kin san in dai 'Gajere' na class ba,a jin kaina."

Hafsah tayi 'yar dariya.

"Hah Basma Yunus baki bar kowa ba"

"Wallahi kuwa har Daddy"

Hafsah ta bud'e baki zatayi magana sai kuma ta fasa, abin ya fi k'arfinta.

Basma ta d'ana mata duka a cinya.

"Ke wai me ya dameki ne?.. Jiya fa naga mutuminki a wajen wani party har mun gaisa"

Gaban Hafsah yai wani irin bugawa tace 

"Yusuf d'in.?

"Yes"

"Hmm i'm telling you, ai yaro ne tsadadde biki ga 'yan mata First Class ba, yadda suke rububinshi.

Hafash dai jinta kawai ta ke amma tunaninta na can wani waje.

'Wanne irin party ne haka?

Ta daure tace

"Ke me ya kaiki partyn meye?

Basma tayi dariya.

"You know, ina da wani friend Ahmad. So shine yai inviting ena na graduation en wani abokinshi, so ashe abokin Yusuf ne ke graduation en"

"Wallahi Yusuf ya iya rawa biki ga ba, kinyi dace k'awata. Ina ma kaina 'wishing' in samu kamar Yusuf."

Ran Hafsah ya d'an sosu taji kishi ya d'arsu a zuciyarta.

Tai ajiyar zuciya kawai.

Ta bud'e jakarta ta d'akko musu snacks da lemo, 

"Muci ni yunwa nakeji."

"Akwai abinda ke damunki fa"

Cewar Basma.

Hafsah tace 

"Hmm ke dai bari. "Munsami misunderstanding ne da shi"..

"What, Meya had'aku.?

Hafsah sai taji ta kasa fad'a wa Basma.

"OK, tunda bazaki fad'a ba.

"Kinzo da waya.?

Hafash ta girgiza kai.

Basma ta ciro wayarta.

"Am bari mu kirashi saka number en. Banyi serving ba.

Hafsah tasa number tana cewa "Sai dai ki mishi magana idan yaji nice ba zai d'aga ba."

"Ok"

Yana d'agawa Basma ta kashe murya.

"Hallo,Basma ce k'awar Hafsah."

"Ok how are you"

"Very fine" 

"Am mene ya had'aku da Hafsah ne?

"Hmm, Basma your friend dont' care about me" 

"Bata damu dani ba ne"

"No,ba haka bane meya faru?

"K'awanki bata sona, tana guduna ne she disgraced me! " she dn't allow me to touch even her hands, not talk about kissing.."

Ya fada bbu ko kunya.

""Hmm, I get an opportunity"💃🏼

Basma ta fad'a aranta.

A fili kuma cewa tayi, "Am sorry, this is not a problem to worry about."

"What? Me kina nufi? "

"Calm down kasan yanayin ba da'ya ba, So I think my friend don't have interest about it"

"Hmm ok" Thank you"

"Kayi hak'uri fa"

No I know how to deal with her.

"Ok Gata to"

No ki rabu da ita.

"A,a dai"

"Ok"

Ta mik'a mata wayar.

"Hello,

"Hum, Hafsh me yasa kike min haka ne? 

"Am sorry please I don't mean to hurt you my dear"

"Hmm, ok zamu yi waya to night."

"Bye"

Hafsah ta rungume "Basma thank you my friend"

"Me ya ce miki ne? kinsan wayar ba a hands-free take ba."

"No, ki share tunda yace komai ya wuce.

"Ok"

Hafsah dai wasai take jinta,sun shirya da Yusuf d'inta.

ina sonka Yusuf d'ina Allah ya tsaremin kai!!

Basma ta bita da kallo..

To da yamma bayan abba ya dawo daga wajen aiki gidan Hajiya ya wuce, bayan sun gaisa tasa aka kawo mishi abinci.

Yana gamawa akayi kiran sallar magariba yai al,wala, 

"To Hajiyah daga can zan wuce."

A,a ka dawo dai"

"To Hajiyah.

Bayan ya dawo ya zauna a k'asa, yana fuskantarta, yasan da akwai maganar da zasuyi.

"Na dawo Hajiya"

"To madallah."

Dama cewa nayi shi wancan yaron da yake zuwa wajen Hafsah an daidaita ne?

Abba yaji abin banbarakwai,

"Wanne ake magana Hajiyah?

"Au to ,baku kirashi ba kenan."

"Wani yaro ne haka Mara k'iba. Shekaranjiya ya kirata a salularta (waya) ya zo ma nan sun gaisa."

Kan Abba ya kulle amma gudun kada Hajiya ta gane yace

" Oh to, eh saboda bata gama Makaranta, bane shi yasa"

"To yadai dace a tuntubeshi aji idan da gaske yazo."

"To za,ayi hakan Hajiya."

Yayi mamaki da Hajiya ta ambaci waya, amma don ya sake tabbatarwa sai yace.

"A wayarta kenan ya kira, sannan yazo Koh?

Hajiyah tace,

"Eh mana, kasan zamani cigaba yazo, da ya iso ma kiranta yayi ta fita."

"To Hajiyah ni zan koma."

"To ka gaida mutanen gidan."

"Allah ya kiyayeku Allah ya tsareku, daga mugun ji da mugun gani. Allah yai muku albarka."

"Amin Hajiya, Amin".

"Sai da safe"

"Allah ya tashe mu lafiya"

"Amin"

Abbah tuk'i yake amma gabadaya ranshi ab'ace yake, ya kasa yarda da abinda Hajiya ta fad'a mishi, yama za,ayi ayi haka? 'yarsa?..Hafsah?.. Ta mallaki waya bai sani ba? Ta dinga zance da saurayi wai duk bai sani ba?

Yasan tabbas da sanin mamanta.

Lallai zai nuna mata b'acin rai in dai haka ya tabbata.. 

Abin ya bashi madaukakin mamaki fa, inda badon hajiya ce ta fada ba zai taba yarda ba.

Wanne irin sakaci yayi har haka ke faruwa a gidansa??

Huci yake sosai da ya isa gidan. Mama na ganin yanayinshi tasha jinin jikinta...






.

[1/11, 12:09 AM] Hajeeyah Karimah (Writer): ♥♥♥♥

*ZAZZAFAN SO*

(Guba ne)

*A broken* 

*heart story* 

 💔💔

Story and writing by:

*Karima Tijjani Mansur* 

*(Hajeeyah Kareemerh)*

*Dedicated to:*

*Unique In Your Love Heart Members.*





📄 *18*





Ahankali yayi sallama, mama ta amsa tana shirin mik'ewa ta karb'i jakar shi, taga ya nufi hanyar d'akin shi, tayi mamakin hakan.

Baya shiga d'akin shi daga dawowarshi, sai dai idan suna fushi da juna..

Ta Kalli yaran hankalinsu na kan kallo. Ta mik'e a sanyaye ta bishi.

Da sallama ta shiga, yana zaune akan gadonshi ya zubawa carpet d'in d'akin ido.

Ahankali ta nemi guri kusa da shi ta zauna.

"Sannu da zuwa"

Bai mata magana ba kuma bai d'ago ba.

Ta d'an sha jinin jikinta.

Ta d'an yi shiru, Mintuna kamar biyu sai tayi tunanin ta kawo masa ruwa.

Ta mik'e kenan ta fara tafiya taji ya kirata a hankali.

"Amina!!

Ta juyo ta dawo ta zauna wajen da take da.

"Me yasa kakai min haka?

Mamaki ne ya cika ta har yasa ta bud'a baki tace 

"Menayi abban..

Ya tare ta cikin b'acin rai.

"Ok me kikayi kike tambayata koh? To 

zaki fahimta idan na d'auki mummunan mataki akanku!!

😳 

Subhaanallah ta fad'a a hankali.

Sannan ta kwantar da murya,

Haba Abban Hafsah, don Allah kayi hak'uri, Allah ya wuci zuciyarka."

"Hmm dole ki ce haka mana, amma fa kin bani mamaki wallahi.."

"Please kayi hak'uri don Allah, ka fad'amin Meyake faruwa?

"Hum"

Kawai yace.

Sai kuma yayi wani tunani.

'Ya lura ta kasa sanin meye laifinta, shi kuma ba shi da lokacin b'atawa wajen zaman fad'amata'

Don haka yace:

"Sai ki kirata tunda ai da sanin ki takeyin komai."

Ba zata ce bata fahimci da wa yake ba don tasan da 'Hafsah yake'

Ta mik'e cikin azama ta nufi d'akin Hafsah, abinda ya so firgita ta,

'waya ta ganta tana yi.

Ta Kai mata duka, ta sami wayar ta fad'i ak'asa.

Hafsah ta juyo a razane,

Maman ta watsa mata harara sannan tace,

"Sai ki taso abbanku na nemanki"

Hafsah ta razana da jin kiran.

Tuni ita maman ta fice.

Ko hijab bata sa ba itama ta nufi d'akin Abban.

Tayi sallama ta zauna.

Bata ga fuskar gaida shi ba.

"Ke waye ya baki waya??

Tambayar taso ta ruguza kanta kamar saukar aradu haka taji tambayar.

"Da ke nake"

Abban ya fad'a yana nuna ta da yatsanshi.

Hawaye ne ya fara biyo kankuncinta.

Shikenan yau ta kad'e. wacce k'addara ce ke neman afka mata Ayau.

"Zaki yi min magana ko kuwa sai nayi ball da ke a wajen nan."

Abban ya fad'a lokacin da yake kawo mata wani bahagon duka da hannunshi.

Mama tayi azamar tare hannun nashi. Abinda ya hana dukan sauka akan fuskar Hafsah kenan. Don la shakka daya sauka da babu abinda zai hana hak'oranta zubewa.😳😂

Abba ya juyo a fusace, yana huci b'acin ranshi ya nunku, ya kalleta fuskarshi cike da b'acin rai..

👏🏼👏🏼👏🏼

*Am sorry kuyi haquri da wannan*

[1/11, 12:09 AM] Hajeeyah Karimah (Writer): ♥♥♥♥

*ZAZZAFAN SO*

(Guba ne)

*A broken* 

*heart story* 

  💔💔



Story and writing by:

*Karima Tijjani Mansur* 

*(Hajeeyah Kareemerh)*

*Dedicated to :Unique In Your Love Heart Members.*

😘😘😘😘😘😘

*Kai jama,a, ni mai zance da masoya wannan novel ne??*🤔🤔

*Sai dai in gode muku kawai*👌🏻

*INA GODIYA DA ALFAHARI DAKU INA MUKU FATAN ALKHAIRI.*

*KARIMA NAJI DAKU😇*

*ZAZZAFAN So NOVEL GROUP:*

🌹 ummu al,amen, Adam's Fudiyya, Maman affan, Ramcy, Hajara ayuba, Sarauniya Bilkisu.👏🏼👏🏼👏🏼

*UNIQUE IN YOUR LOVE HEART GROUP:*

🌹 Zeena Khalid, pure baby and the whole members👏🏼

*JIDDA TIJJANI NOVEL GROUP:*

🌹Deejah, Lawisa tanaskha, Binta musa salisu (Mamana), Maman Hanan, Nana Hauwa,u, juwaira lukman. And also Aysha Tukur (Maman Teemah and Ahmad)👏🏼👏🏼

*RAYUWAR SUMAYYA NOVEL GROUP:*

🌹 ummu muhd, bintu muhd, Habiba abdul k'adir.

*SIRRIN MU:*

🌹 Ummu hibban 'yar baba, zaujatu muhibbuha, Mrs naseer.👏🏼

*NOVEL ZAFAFA:*

🌹Mr Otu, sumyhala2017.👏🏼

*MATAN AURE NOVELS:*

🌹SUA, Zeenah Khalid, pure baybee. 👏🏼

*NIDA K'AWATA FANS:*

🌹 Nadiya sadou, S ubanduma, maman umar, Aisha ya,u.👏🏼

*KUNDIN NOVEL GROUP:*

🌹Zulaihart, Maman Hafsah, Khadeejah.👏🏼

*TAURARUWAR MACE GROUP :*

🌹Sumayya hadi and Mami boy.👏🏼

💘💘💘💘💘💖💖💖💖💖

*Am totally in love with you.. Kun gane ai*😊👏🏼👏🏼👏🏼




📄 *19*




*Kafin* yayi magana ta riga shi,

"Haba, Abban Hafsah, don Allah d'auki al,amran nan da sauk'i."

Ya kalleta da kyau.

Ta karyar da kai.

"Don Allah"

Yayi shiru sannan ya dawo ya zauna.

Ya Kalli Maman.

Kinsan da zaman wayar?

"Nasani" a ta fad'a a tausashe.

Yaji zafin hakan sosai, don me zata dinga b'oye mishi, abinda ya shafi rayuwar 'yarshi. Yaso rufeta da fad'a sai ya tuna da 'yarsu a wajen..

Ya danne axuciyarshi. Sai fushin ya koma kan Hafsah da dama Itace mai alhakin laifin."

Afusace ya kalleta Yaushe ya baki wayar,? meya sa ma kika kaishi gidan Hajiya?...Wato ni ban isa ki kawo min shi ba koh? Hafsah har kin isa ki yi abu irin wannan bada izinina ba koh?

Hawaye suka biyo kuncinanta.

Meya sameta? tabbas tasan batayi wa kanta adalci ba.

"Abba Don Allah kuyi hak'uri wallahi bazan sake ba."

"Hum, hak'uri kike bani Hafsah?? Dama shi yasa kike sakaci da karatunki koh? Kika sa wasa a zuciyarki, saboda kina yin wani shirme can koh?..

'Tashi ki d'akkomin wayar stupid!!

Ya fad'a cikin wata tsawa.

Ta mik'e a hanzarce gudun kada ya daketa ta nufi d'aki ta dakko wayar.. Har yanzu hawaye bai daina zarya a kan fuskarta ba.

Ta durk'usa ta mik'a mishi da hannu biyu, ya karb'a ya ajye a gefenshi.

Mama dai tayi shiru, don babu damar yin magana.

"Kun dad'e dashi dama ban sani ba?

Abba ya jefo mata tambayar.

Hafsah ta girgiza kai.

"Magana zaki min,"

Ya fad'a cikin tsawa.

Cikin rawar murya tace, "A,a.

Abba ya kalleta sosai,

"Kice masa yazo ina son ganinshi"

Ba Hafsah ba har Mama sai da gabanta ya fad'i. Takai kallonta ga abban, yayin da shi kuma ya k'ara tamke fuska.

Sai ma ya kalli sashin da Hafsah take.

"Tashi ki bani guri"

Ta mik'e sum sum sum ta fita.

Shiru ya mamaye d'akin sai zuciyar kowa da ke sak'e-sak'e. Shi Abba jiran cewar Mama yake yayin da itama take jiran ya sauk'le fushin akanta. Sai kuma tunanin yau yasa taji kunya a gaban 'yarta, don basu tab'a haka ba agaban 'ya'yansu.

Can taji yayi ajiyar zuciya, had'e da juyo da kallonshi b'arin da take, itama lokacin ta kalloshi sai suka had'a ido.

Ya tsaya ya kalleta sosai, kallon daya k'ara raunana zuciyarta cike yake da tuhuma da kuma mamakin abinda tayi mishi, duk ta karanta wannan a idanunshi.

Ahankali tayi k'asa da idanunta, ta dafe kanta da hannu biyu.

Yace, Cikin k'aramin sauti,

"Amina!

Taji amma ta gaza amsawa.

Shikuma yayi shiru, tasan jiran amsawarta yake.

"Amina"

Ya fad'a a karo na biyu.

Muryarta a disashe tace. "Na,am"

Bai damu da rashin d'agowarta ba, ya fara magana.

"Kin san hali na, kuma kinsani idan nace 'eh' bana cewa 'a,a."

Ya d'an yi shiru sannan ya cigaba.

"Kinsan tsari na, kuma dake mukayi magana, ban fad'a miki kada ki bari hafsah ta kula wani yaro ba?? bance miki sai tayi candy ba?

Ahankali tace

"ka Fad'a"

To meyasa kika k'i bin abinda nace?.. Ko dan bake Allah zai tuhuma ba idan ta lalace koh??

Ta girgiza kai.

"Amina me kuke so wanda bazan yi muku shi ba?"

Ya d'anyi k'asa da murya.

"Idan kina son ta rik'e waya me yasa bazaki fad'amin ba.. Sai ki goyi bayan ta k'arbi abin hannun samari koh?

"To Allah ya gani dai ban hanaku komai ba!!..

Maganar daya fad'a ta k'arshe tayi wa mama zafi, sannan ta sa ta taji 'tabbas batayi dai dai ba..

Yau mijinta ne da kanshi yake fad'a mata wai ya fita hak'k'insu??

Kwallah ta cika idanunta.

Shiko bai k'ara kallonta ba ya mik'e ya shige toilet enshi ya murza key.

Bai sake mata magana ba tun da ya fito, kuma yak'i bata damar yi mishi magana ko hak'uri ne ta bashi.

Tana son ta fita ta duba 'ya'yanta tana tsoron kada ta fita ya kulle k'ofarshi, don tasa a ranta dole anan zata kwana.

Shine ma ya mik'e ya fita, dakunan yaran yasasu yin fitsari, sannan ya dawo falo yayi zamanshi.

Shiru Mama na zuba idon dawowarshi.

Sai can wajen d'aya 1:00am sannan ya tashi ya koma d'akin.

To Kwanan ranar dai haka sukayi shi babu d'adi dai...

B'angaren Hafsah kuwa kuka take yi gurshek`e..

Abubuwa ne da yawa suka had'ar mata, na farko nadamar zama silar samun sab'anin iyayenta, domin tasan da wayonta bata tab'a ganin hakan ba gabanta, sannan bataji dad'i Abba ya kamata da laifi irin wannan ba.

Na biyu kuma jimamin k'wace wayar ta da Abban yayi.

Sai kuma babban wato tunkarar yusuf da maganar abba.

Tunani dai shiya cinye rabin darenta.



♥♥♥♥ ♥♥♥♥


Kwance yake akan gadonshi daga shi sai singlet da gajeren wando. Ya kwanta rub da ciki. 

Wani tunanin shima yake yi daban.

Yana jin dad'in yadda yarinyar take sonshi sosai, shima kuma yasan yana sonta, amma matsalar yarinyar 'Local ce' 

Yusuf kenan ke tariyo (tunanin) irin rayuwar da sukeyi shi da Hafsah. Abin na bashi mamaki wani lokacin kuma yana jin takaicin hakan.

Kamanninta ya shigo tunowa. 

Kyakykyawa ce, shi dai ta mishi kyau! yana son komai nata, amma me yasa bata mishi soyayya irin wacce yake so?

Ta iya kalamai masu sanyaya zuciya (sweet words) ta iya kwalliya, ita d'in kalar manyan yara ce.

"Her smile kills me! 

Ya fad'a a hankali.

Yusuf yana son ya samo musu mafita ne akan k'in yarda dashi da Hafsah keyi.

A ganinshi "zama cikin mutane d'aya masu yare d'aya, al,ada d'aya, addini d'aya shiya sa ta rashin wayewa. A ganin shi Hafsa nayin rayuwar _kifi acikin rijiya ne._

Matsalalolin ya kasa kashi-kashi da niyyar samo musu mafita.

Na farko shine 'Rashin yarda dashi da Hafsah keyi, wanda ya danganta shi da 'rashin wayewa'..

Yasani cewa fushinsa na rikitata, saboda haka ya d'auki aniyar nuna mata fushinshi a duk sanda tayi mishi hakan, tare da yi mata barazanar rabuwa da ita, har lokacin da zata bada kai...

Yayi murmushi samun nasara don yasan Hafsah bata da jarumtar jure fushinshi.

Na biyu kuma Rashin wayewarta da zama waje d'aya, mafitarsu a wajensa shine d'aukarta su dinga fita yawon shak'atawa lokaci zuwa lokaci.

Sai kuma sauran banbance banbance dake tsakaninsu wanda zai mayar da hankali wajen sace zuciyarta, hakan zai sakata zama daidai da ra,ayinshi.

*TSOKACI*

Sau da dama zama baya yiyuwa idan ra,ayi ko kuma hali bai zo d'aya ba, sai dai idan d'aya ya rinjayi d'ayan bisa ga bin ra,ayinshi.


Akwai banbance - banbance da yawa tsakanin yusuf da kuma Hafsah. Wanda silar su shine samun dace da iyayen kirki da kuma tarbiyya, sai kuma aka sami akasin haka daga b'angaren 'Yusuf'

Haka fahimtar da suka yiwa soyayya ma da akwai banbanci.

A wajen Hafsah ta d'auki soyaya ne irin ta saurayi da budurwa a matsayin : 'Musayar kalaman soyyaya a tsakanin masoya sai kuma kyautatawa da kuma sadaukarwa ga juna da kuma fatan zama a Inuwa d'aya wato 'Aure'

A wajen Yusuf kuwa yana ganin soyayya Itace farantawa juna da kuma zama d'aya babu banbanci.

'Duk da addini da al,ada sun nuna banbancin inda aka saka wani geji 'iyaka' tsanin Mace da Namiji a wajen mu,amala.'

To shi Yusuf bai ga wannan ba gurinshi ma idan dai 'True Love' ake yi babu zancen wani addini ko kuma al,ada kawai a zauna a bi ra,ayin zuciyoyi.

Domin a wajen shi 'Sacrifice' wato sadaukarwar da Hafsah ke ik'irarin tana masa ba ita bace, tunda ita ganin ta bashi 'Dukkan yarda' shine ta sadaukar mishi komai.

Shi kuma yana ganin idan gaske ne sadaukarwar tata ya dace ya gani a aikace ba ik'irarin da kalmomin baki ba. Shi yasa yake tantama bisa son da take mishi.

Rashin dacen Yusuf da iyayen kirki yasashi fad'awa cikin wannan hali da kuma gurb'ataccen tunani.

Wato tun yana yaro d'an kimamin shekara goma sha biyu, ya tashi cikin wata 'wahalalliyar rayuwa', wanda shi yasanta kuma zai kirata da wahala.

Wato iyayenshi kanyi wasu abubu

agabanshi wanda sun d'auke shi shi yaro ne. Ba ruwan su, kasancewarshi a kusa da su baya hanasu yin wani abu daya shafi mu,amalar aurensu.. Sannan yana zuwa gidan abokanshi 'Turawa' yana ganin yadda suke yi.

Tunanin shi ya kulle da son gano hakan menene? Amma saboda k'arancin shekaru ya kasa ganowa, sai lokacin daya kai munzalin wasu shekaru 15 -16, kuma akayi rashin dacen yana da yanayin buk'atar hakan sosai. Alokacin ne kuma ya bazama nema wa kanshi mafita.

Yusuf nada k'awaye mata a makaranta wanda suke mu,amala tare, kasancewarsu turawa sai ra,ayinsu ya dace da na juna.

Sukanyi mu,amalarsu kamar babu banbancin 'Jinsi' a tsakaninsu.

Yusuf a lokacin nada budurwa 'Jessica' wacce suke soyayyarsu ta yarinta.

Mummy shi ta b'ata bude Diary nashi wata rana.

Yayi rubutu a cikin abin gwanin takaici, wanda ita hakan ya burgeta.


*'My Love Jessica and I'*

Our first time kiss was at school garden..

Rubutu ne sosai yadda abin ya faru, tsaf mummynshi ta karanta, amma ta share abin tayi murmushi.

Wai d'anta ashe ya girma haka?? 😡😒

Da irin wad'annan abubuwa ne kuke ganin rayuwar Yusuf da Hafsah zata tafi a Inuwa d'aya bayan kuma gefe ga Abba na shirin kafawa ya tsare??🤔

Anya ba ko dole wani daga cikin su yayi watsi da nashi ra,ayin ya bi na d'an uwanshi ba?

Idan hakane wa kuke ganin zai sauke nashi ra,ayin zuciyar YUSUF KO KUMA HAFSAH??🤔🤔

Muna Jiran ra,ayinku.

[1/11, 12:09 AM] Hajeeyah Karimah (Writer): ♥♥♥♥

*ZAZZAFAN SO*

(Guba ne)

*A broken* 

*heart story* 

  💔💔


Story and writing by:

*Karima Tijjani Mansur* 

*(Hajeeyah Kareemerh)*

*Dedicated to :Unique In Your Love Heart Members.

*AUNTY KHADIJAH (MK MAKEOVER💄💋)..GODIYA NKE,👏🏼 _KUMA MUNA BOOKING IDAN BIKIN HAFSAH DA YUSUF😅 YA ZO,_ KE ZAKI MATA KWALLIYA.*


Zamu hadu a page dinki na instagram #MK makeover.


*And also*

*D'AYA AUNTYN.*

*(AUNTY FATIMAH, MAMAN LITTLE MAMIE).. ALLAH Y A RAYA WANNAN BABY YA KUMA BATA GASHI IRIN NA FILLO KAMAR NAKI..*👍🏻👏🏼👏🏼




📄 *20*




*Washe gari* da asuba, abban ne da kanshi ya shigo ya tashe ta, kamar babu abinda ya faru..

A al,adarshi 'knocking' dama yake mata sai kuma ya tabbatar ta tashi ta bud'e kofa, sannan zai wuce masallaci.

Gabanta ya fad'i lokacin da taji shi yana kiranta, amma kuma hankalinta ya kwanta da taji yanayin kiran, dama baya d'aga muryarshi da asuba..

"Yaya,..Yaya, ki tashi kiyi sallah."

Ahankali ta mik'e ta bud'e kofar. 

Tun da yaga ta bud'e ya juya.

Tayi hamdala a zuciyarta bata son had'a ido da abban nata.

Akan darduma ta zauna bayan ta idar da sallah ta, tunano ta ina zata fara tun karar Yusuf da maganar abbah ta ke.

Gashi ya k'wace wayar bare ta kira shi. Ta mik'e ta bud'e wata jaka ta dakko zoben da Yusuf ya bata, ta dawo ta zauna.

'Tun ranar da aka koma makaranta ta karb'a a wajen Mama tace mata, zata mayarwa da Basma, shine ta boy'e shi.'

Ta kur'a wa zoben ido, tana tunano wanda ya mallaka mata shi, ahankali kwallah ta cika idanunta.

Allah ka taimakeni.. Allah kasa kada Abba ya rabani da farin ciki nah!!

'Idan na rabu da Yusuf na rasa komai.

Ta janyo Diary d'inta da yake akan 'Bed side drawer' (gefen Gado)

*'Together forever'*

_Our love is built up with scriface and devotion.._

_I will not let it be possible..!!_

_And.._

_I promise you to be

_with you forever no matter what difficult and challenges I'm_ _gonna face.._

" _I love you my_ _Yusuf!_


Ta rufe Diaryn ta ajye, sannan ta mik'e ta nufi kitchen wajen Mama, tasan ita ma babu dad'i ta kwana.

Maman tana kitchen d'in kuwa.

Tayi sallama tare da cewa,

"Mama,Gudmorning"Maman ta kalleta 

"An tashi lpia" 

"Lpia lau."

"Bari in fere miki dankalin."

"Ok kiyi sauri to, kinga kada ku makara a school."

"Ta k'ara kallonta.

Idan kin gama kije ki bawa abbanku hak'uri."

"To Mama"

Tana gamawa ta mik'e ta nufi d'akin Abban, gabanta na fad'uwa.

A tsaye ta tarar dashi a falon shi ya rataya jakarshi yana shirin fita.

Tayi saurin durk'usawa har k'asa. 

"Abba barka da safiya"

Ta fad'a kanta sunkuye.

"Barka, dai kun tashi lafiya?

Ya fad'a babu yabo babu fallasa.

"Lpia lau.

"To madallah"

ya fad'a yana shirin cigaba da tafiya.

Ahankali tace "Abba, don Allah kayi hak'uri kaji"

Ya d'anyi murmushi.

"Hmm, yaya kenan kinyi laifi ne?.. Ba kina ganin abinda kika yi dai dai ba ne koh?

Cikin raunin murya tace.

"Wallahi Abba ba haka bane, don Allah kayi hak'uri."

Ya juyo, ahankali ya kalleta sosai, sannan ya dawo ya zauna.

"To Me yasa kikayi haka? 

"Babu komai"

" Um, dama na nunawa mama fa wayar"

"Tambayar ki nayi me yasa kikayi haka?

"Um babu komai"

" To a ina kika sanshi?

Anan ta d'an fad'a mishi yadda suka had'u da Yusuf d'in.

Da yadda ya bata waya.

Amma bata fad'a mishi sun tab'a had'uwa a wani waje ba, sai ma ta nuna ranar da suka had'u gidan Hajiyah shine ganinta na biyu ita da shi.

Abban ya d'anyi shiru sannan, fara mata magana cikin nasiha, don ya fahimci ita take buk'ata.

"Hafsah ke har yanzu yarinya ce, baki san me duniya take ciki ba.

Ba wai ina hanaki yin wasu abubuwa bane da nufin k'untata miki..Kin manta ni mahaifinki ne?.. Ki daina tunanin zanyi wani abu da niyyar takura miki kinji?

Ta gyad'a kai kawai.

"Ya cigaba.

"Idan kina son abu ki dinga tambayata ko menene shi, kinji yaya? Da kin fad'a min kina son waya da tuni na sai miki..

"Ina son kiyi karatune kinji.. Ko kin fi son in miki aure yanzu?

Tayi saurin girgiza kai.

"To, ki maida hankali kan karatunki kawai, in sha Allah zaki sami mijin da zakiyi alfahari da shi.

Ya mik'a mata wayarshi.

"Ungo saka min number shi.

Hannunta na rawa ta karb'a. Ita dai tana tsoron kada Abba, ya kira Yusuf.

Ta rubuta, ta mik'a mishi.

"Yauwa, yaya."

"Allah yai miki albarka.

Ahankali ta amsa da "Amin"

Ya mik'e.

"Maza ta shi kije kiyi shirin makaranta,nima yau da wuri zan fita.

"Abba a dawo lafiya"

Allah yasa.

Ya fad'a yana fita daga cikin falon.

Daya zo fita ta babban palour, yaran nata hayaniyar shirin Makaranta.


Suna ganinshi suka hau gaidashi. Abba "Gud morning".. "Abba ina kwana?

Ya amsa cikin fara,a yana shafa kansu

Mama ta fito da d'an sauri, daga kitchen.

"Barka da asuba"

"Barka dai."

"Am fita zakayi ne?

"Eh sauri nakeyi"

Bataji dad'in hakan da yayi mata ba, amma sai ta hadi'ye har da yi mishi murmushi.

"Adawo lafiya, Allah ya tsare."

"Amin.

"Sai na dawo.

"Ok bye"

Ta koma kitchen.

Yaran ma suka fara, "Bye bye abba Adawo lafiya.

Shima bai ji dad'in hakan ba, amma kuma so yake ya nuna mata laifinta. Don ya fahimci hafsah bata da laifi tunda da saninta take komai, kuma akwai k'uruciya atattare da ita.

Hafsah bataji dad'i ba Basma bata zo makaranta ba, taso ta kira Yusuf, ta fad'a mishi yayi shirin amsa kiran Abba. Kuma tana son neman shawarar Basma akan al,amarin.

Da yamma bayan abba ya dawo gida. 

Mama ta ta tare shi. Babu laifi ya d'an saki jiki har yaci abinci.

Da daddare ne ta sameshi, yana d'akinshi yana wani aiki a computer.

Ta zauna kusa da shi.

"Abban Hafsah don Allah ka saurareni akan maganar nan.

Ya d'an tsaya da abinda ya ke ya kalleta.

Ina jinki.

Ta Kyautata muryarta.

Dama fa wallahi bada wani manufa na bata wayar nan ba, and wallahi na rantse bansan yarinyar nan tana zance ba."

Ya ajye Laptop d'in a gefe.

"Me kike son fad'amin, baki san tana zance ba, ya zanyi in yarda dake?

Bayan ke ta nunawa wayar?

"Eh ta nunamin"


_(kaji uwa😇👍🏼) love u mama nah_😘 #karima.

"So, sai na k'wace na kuma ce kada ta sake kulashi, yanzu lokacin yin karatu ne.

"Me yasa baki sanar mini ba.??

Kayi hak'uri bana son ina kawo maka damuwa ne, kuma lokacin ka dawo ne daga tafiyar dakayi, bana son ka damu kanka bayan kuma ga stress na office, then na zaci "I can handle it"

Amma ayi hak'uri.

"Hum! Yai ajiyar zuciya sanan ya d'anyi murmushi.

Mata kenan!! wato saboda ba,ason damuwata, sai akasa fad'amin matsalar da zata jawo babbar damuwa. #zancen zuci.



Afili kuwa ce mata yai. "Okey, ya akayi kuma kika bata wayar?

"Um, gani nayi ba babba bace wayar, kuma kada ta zaci ko ina zarginta ne, shine yasa na bata."

Ya d'an dara (dariya) kad'an. "Hmm Mrs habeeb kenan.

Sannan ya tausasa murya.

"Iya hangenki kenan, mata kuna da raina abu. Yanzu baki ga bata wayar da kikayi ya sa ta sami hanyar contacting d'in shi ba?

"Allah ya rufamin asiri iya gidan Hajiya appointment din nasu ya tsaya."

Ya fad'a yana 'yar dariya.

Baki san wani abu ba Ameenah, yanzu Hafsah gani take bata wayar nan da kikayi, kin bata damar contacting d'in yaron ne.

"Tayi shiru, yace 

Baki gane hakan bane Koh??

Tayi d'an murmushin jin kunya, ita ina tunanin ta yakai nan.!

Sai kawai tace,

"Wai kana nufin sai Hafsah ta iya zuwa wani waje da saurayi??

"Hm, kina mamaki koh? 

Ta gyad'a kai.

"Bana zaton zata iya yin haka"

"Hm, ki bar yaran yanzu Amina!

Ya saita muryarshi ta dawo 'Serious'

"Ni dai ina rok'onki da kuma baki umarnin, don Allah kada ki sake b'oyemin lamari makamancin wannan, domin idan matsala ta afku na rantse sai kinfi kowa shiga damuwa."

"In sha Allah zan kiyaye, ka k'ara hak'uri da ni"

"Idan kika yi hakan kin gama min komai."

Ya d'ora.

"Ina tsoron sha,anin samarin yanzu ne, akwai abinda nasani wanda ke baki sanshi ba, ki d'auka kula da kuma hak'k'ina ne dole in saukeshi, in sha Allah babu matsalar da zata gagareni kinji? 

Ya k'arashe maganar da d'an murmushi.

Tayi ajiyar zuciya

"In sha Allah baza,a sake ba."

"Nagode sosai zaujaty!!, wasu abubuwan bazaki fahimta ba sai nan gaba. Yanzu kiramin Hafsan kiga wani abu."

Tace "To" sannan ta mik'e ta fita.

Tare da Hafsan suka dawo, ta zauna kusa da Mama.

Abban ya kalleta cikin sakin fuska yace, 

"Hafsah kin fad'a mishi ina neman shi?

Ta girgiza kai ahankali.

Ya d'an had'e rai.

"To Meyasa?

"Abba babu waya,.. Kuma..

Sai tayi shiru.

"Hmm kuma me? 

Da ya ake kike had'uwa da shi wato don ba naki ba ne kiran koh"?

Kwallah ta taru a idonta.

"Allah abba ba haka bane bansan inda zan ganshi ba."

"Hmm, kije gidansu mana."

Ya fad'a fuskarshi babu wasa.

Kwallah ta fara bin kuncinta tana zarya.

'Menene abba ya ke nufi kenan?? 

Kada dai har ya fara zarginta da zuwa gidan su Yusuf. 

Sai yanzu ta yi nadamar k'in sanarwa ko da mamace tsakaninta da Yusuf, tasan zata fahimce ta.

Gashi yanzu hakan ya zame mata matsala cikin tarayyar su.

"Bazakiyi magana bane.?

Cikin kuka tace Allah Abba bansan gidansu ba."

Au,? Duk dad'ewar taku baki san gidansu ba.?

"To wacce unguwa yake?

Ta girgiza kai. 

Sai yanzu ta tuna basu tab'a maganar inda gidansu yake ba.

Abba wallahi bansani ba.

"Alright."

Ya fad'a yana mik'a mata wayar shi, daya danna kiran Yusuf.

"Ungo yi mishi magana ta nan."

Mama dai idone nata kawai.


Ta karb'a tasa a kunnenta, sam bata san me zata ce mishi ba ma.

"Hello" taji ance daga d'aya b'angaren.

Ta d'an daburce.

Um am, hell.. "Salamu alaykum"

"Wa Alaykumussalam."

"Am Hafsah ce"

Oh! My sweet baby, mene ya sami wayanki ne, kin barni ina missing naki." 

"Hmm, ta fad'a.

Sai wani rarraba ido take tana kallon abba da Mama.

"My baby inaso zanzo wajenki kawai ni dai yau"

Ta Kalli Abba wanda ya tsare gida.

Babu damar tace mishi kada ya zo, don bata son abba ya fahimci hirar da suke.

"Um, dama abbanmu nason ganinka"

"You say what?

Tayi shiru.

"Talk to me mana, Baby, mesa abbanki keson ganina?

Bata da mafita illa ta katse wayar, don haka tace "Okey, nagode, sai anjima."

A tare abba da Mama suka tambayeta "Meyace miki"?? 

Cikin in, ina tace,

"A wai yace in sha Allah zanzo."

Abba ya kalleta sosai.

'Ita Mama tuni ta yarda da zancen.

"Hum, shikenan tashi kije to"

Inji Abba.

Ta mik'e

"sai da safe.

Tana fita Abba ya kalli Mama, 

"Bafa zuwa zaiyi ba!

Mama ta kalle shi da son neman k'arin bayani.

Ya tari numfashinta.

"Ki zuba ido ke dai"

A can B'angaren Basma kuwa..

Tana kwance kan gadonta shiru, wani tunani take. Ko na meye oho!

Wayarta da ke gefenta tayi k'ara.

Taja tsaki tare da mik'a hannu ta jawo wayar.

Ta ware ido lokacin da taga sunan mai kiran nata, akan 'Screen' wayar.

"H. Hamid'slove"

Tayi murmushi har da yin gyaran murya.

"Hello"

"Basmah gud evening"

"Hw are you"

"Am fine, 

"Ok, please akwai magana da zamuyi dake, if you have time.

"Ok, no problem go ahead"

"Thank you.

"Am friend enki ne fa, she has a problem, bata saki jinkinta dani. I mean she always wants to make a difference between us, she always want to create a distance between us."

Basma tayi murmushi.

"Hmm, please be patient with her, I told you many times that Hafsah bata son kana mata abinda kake mata b'cause bata saba,ba..And yanayin naku ba d'aya ba.

"Nooo, I already know this, but why not if she loves me! ?

Basma tayi dariya.

Haha, no she loves you but she don't take care of you, as you want. And she will never do!!

Gaskiya na fad'a maka.

"Oh my gosh''.. Meyasa kka ce haka."? "Hmm k manta neh am her friend I know her more than you.."

Aransa yaji cewa gaskia ta fada.

"Kinaji nah,

Yanzu ma wani another problem enne, kinga fa yanxu munyi waya da ita, and she's telling me that daddy nata nason ganina!"

Cikin nuna mamaki sosai tace.

"To me yasa kun sami misunderstanding ne? 

"No, 

"Wllhi I don't know why yake son ganina."

"Hmm may be he wants to know Something about you, kasan ya hana ta kula samari, then itama naga bata son kana mata irin wannan abubuwan, so may be zaice ko kafito ne ayi muku aure"!!

Whatt??..are you telling me??..Hmm, impossible, I know I love her, but aure not yet gaskiya, barin fad'a miki bazan iya zuwa wajen abbanta ba"

Basma tayi wata irin dariya. 

"Why not. kafito kawai musha biki!

"Hmm am telling you as her friend, please ki nuna mata she have to change her attitude, cause am tired da abinda take min, kuma I don't think zan k'ara zuwa wajenta, sai dai tana meeting ena somewhere na gaji fa"!!

Basma ta kisma wasu abubuwa wanda nima ban san su ba. (Sanin gaibu sai Allah)

Amma afili naji tayi dariya sannan tace,

"Alright" wannan shine solutions" Amma Advicebly kada kaje gidansu couse nasan halin abbansu!!

Anya Basma!! 🤔🤔

Thank you alot bye bye.. I zanje club at 12:00am

"Ok, hope to meet you there one-day!!"

"Kina zuwa ne?

"Yeah, 

"Hafsah fa? 

"Hmm, kana da son jan zance, ya za,ayi kaga wannan a club??

"Oh shut!!

Basma ta Shek'e da wata dariya.

"Bye bye" 

"Ok, thank you u are important in my life."

"Hmm, kada ka damu"

Kawai tace.

Amma azuci cewa tayi.

"Sai ma na sami wata damar..

Ta ajye wayar tare dayin wani d'an ihu,

Sannan tace,

"Saura k'iris"

🤔🤔🤔

To me take nufi??





.

[1/11, 12:09 AM] Hajeeyah Karimah (Writer): ♥♥♥♥

*ZAZZAFAN SO*

(Guba ne)

*A broken* 

*heart story* 

💔💔



Story and writing by:

*Karima Tijjani Mansur* 

*(Hajeeyah Kareemerh)*

*Dedicated to:*

*Unique In Your Love Heart Members.*




📄 *21*



*Yau* da Hafsah taje makaranta, ta samu damar keb'ewa da Basma. Itace ta nemi su tattauna, 'don yau sai wai Basman ta nuna kamar bata santa ba. Itama Hafsan, sai ta d'an share, tasan ta da shariya wani lokacin. Sanan kuma fad'an Abba akan karatu ya shige ta, tunda ta daina yarda suyi hira da Basma, in dai ba 'break' aka fito ba.

Sannan kuma ga jarrabawar k'arshe dake tunkaro su.

Ita taje sit d'in su basman, basman na yin kwantan note d'in da bata zo jiya ba.

"Basma please ina da magana, akwai matsala ne fa"

"Hmm, H. Hamid kenan 'Queen of love"

ta kuma kallonta sannan tace, cikin rashin kulawa da zancen Hafsan,

"Kinga ina yin note ne, so ki bari sai anjima"

"Okay, but please hurry up it's urgent need wallahi"

"Hah, baki da dama!

Haka Basman kawai tace.

Hafsah ta mik'e, 

"Bari nayi break kafin sannan kin gama."

"Okey" Inji Hafsah.

Ta tafi tana mamakin Basma. A saninta da ita note baya hanata hira, zata iya ajyeshi suyi hirar su, ko kuma tanayi suna hira.

"So ko itama mamanta ta mata fad'a ne?? Tayi tambayar azuciyarta.

Bayan ta dawo Basman tace bata gama ba, sai kawai ta rabu da ita.

Wasa-wasa har sati ya zagayo, kullum da uzurin da Basma zata kawowa Hafsah. Yanzu damuwar Hafsan ma d'aya ce, wato Yusuf, ta daina jinshi gabad'aya, tun ranar da ta fad'a mishi Abba na nemanshi, gabad'aya kewarshi ta dameta, har wata 'yar rama tayi.

Yau Monday kuma baifi sati biyu a musu hutu ba, sannan, cikin hutun ne zasu fara jarabawar 'WAEC'

Yau Hafsah tasawa ranta sai tayi waya da Yusuf d'inta don haka ta, je wajen Basma,

"Please B. Yunus, aramin wayarki wallahi I miss my dear very much, kinga abbanmu ya k'wacemin waya then, mun dad'e bamu had'u ba"

"Hmm, H. Hamid, yau banzo da wayaba fa"

"Oh my God!, yazanyi ne?

Mik'ewa tayi da sauri ta nufi d'aya raw d'in.

Wajen Aysha Tahir taje, tasan itama tana zuwa da waya lokaci zuwa lokaci.

"Pls Aisha help me ina son aron wayarki"

"Ok babu matsala, ta bud'e jakarta ta d'akko wayar. 

"Ungo,

Hafsah ta karb'a. "Thank you, nagode sosai"

Aysha tayi murmushi ita bata da matsala, kuma jininsu ya had'u da Hafsah.

Can bayan ajinsu Hafsah ta zagaya. Guri ne mai shuke- shuke, tasan kuma ba,a fiya shiga ba don baya b'ullewa.

Fito da wayar ta sa numbobin Yusuf. Har wani rawar kai takeji yau zata ji muryar Yusuf d'inta.

Lokacin daya d'aga kiran ta kashe murya, 

"Hello my dear"

Shima yaji farin ciki jin muryar Hafsah, yana sonta shima.

Ya d'an shagwab'e muryarshi.

"My Baby, kin yada ni, baki sona koh?

Cikin muryar jan hankali. Don yau sai taji ta rage jin nauyinshi, saboda kewarshi da ta dad'e cikinta.

Haba my baby, ina missing naka, wallahi baka ga yanda na damu ba, duk fa na rame, ko dai ka daina sona ne?

"Hmm, u always say that bayan kin koreni"

"Oh God, wane ni korar ka, haba baby please ka daina fada kaji"

"Gaskene fa, yanzu yaushe, rabon da mu had'u."

Sai yanzu ya tuna mata.

"Baby kak'i amsa kiran Abba fa, kullum sai ya min fad'a kuma ya tambayeni ina kake"

Please baby ki share, i can't, barin iya zuwa ba"

"To Meyasa?

"Abbanki zai min maganar auren koh?

"Noo dear, it's not wallahi kaga kawai yana son yasanka ne, aini Abba, bazai min aure ba a early shekaruna.

Yai ajiyar zuciya, "Gud, but ki share kawai in mun had'u sai na nemi ranar da zanzo."

"Thank yooouu"

"Yaushe ne zamu had'u to?

Yai k'asa da muryarshi sosai I missed you over, and I need you in ma side"

"Uumm, ta d'anyi shiru bata son ya mata magana da irin muryar, sai taji gaba-daya ya sanyaya mata jiki.

"Please Baby nah! 

Ya fad'a cikin marainiyar murya.

"Oh, Kafad'amin lokacin da zaka zo wajen Abba."

Nace idan mun had'u, I will tell you, in kuma kink'i so I swear to God bazan zo ba."

"Oh, rufamin asiri dear, abba ya matsa min fa"

What do you mean by 'Ya matsa miki'??

You, I don't understand Hausa well,"

Hahh, tayi dariya sosai, sannan tace, "oh, ma British boy I love you,"

So I mean yana damuna akan maganar."

Yayi 'yar dariya, "Okeyy"

"Coming Friday, muna biki so, I think mu had'u can."

"No, u know fa banason taron jama,ah.

Idan kazo zan fito daga 'Hall' sai mu had'u.

"Gud idea ma baby I want you!

"Hmm,

Where is your friend, "Basmah"

'Tana class'

Okay please extend my greetings,"

Hafsah taji wani iri azuciyarta.

Kafin tace wani abu ya cigaba,

"She care about us,"

"Hmm, inji Hafsah, don abin ya isheta"

Yace ,

"Me zaki bani ne my Baby, please don't reject my request"

"What do you want?

"Please blow me some kisses!"

"Tad'anyi dif.

Bata son b'ata mishi rai a wannan lokacin. Muryarshi ta katse ta,

Ya d'an chanja murya, 

"Why you always want to hurt me?

'Tayi shiru okay,

"Hmm, Okay, thank you..

Gabanta ya fad'i tayi saurin cewa.

"Am sorry my dear, I don't mean that, am sorry"

"Hm, kina ja min class fa"

"No,ba haka bane.

"I'm just trying to do..

Hmm, you are trying koh, sai kace zaki yi shooting da bindiga koh,?

Tayi dariya, kad'an tayi k'asa da muryarta kamar rad'a.

"Please forget it my baby, enjoy this "Muaan"😘

(😳 Hafsahh??🤔)


Shiko wani shauk'i yashiga, that's my baby girl I love you,"

Please need more"

"Tayi dariya am sorry, 

"Bye,

"Thank you see you on Friday."

"Am gonna miss you baby nah! 

"Bye!'

Ta lumshe ido, ta gaza cire, wayar daga kunnenta.

Ahankali ta k'ara furta "I love you my Yusuf!!

Ta janye wayar tana shirin b'oye wa ta hango english teacher na nufo wajen,

"Hey, what are you doing here?

"Am..nothing sir.

"Ke Banyarda ba, 

Fito min da hannunki" Ya fad'a cikin tsawa.

Bata da mafita Illa ta fito da wayar ya kar'ba yana cewa "Stupid Girl"

Jiki a sanyaye ta dawo cikin aji, d'an farin cikin da Yusuf, ya sata duk ya gushe.

Ta nemi guri kusa da Aysha ta zauna.

Ta dafa hannunta.

Aysha ta kalleta kin gama wayar ne, ko fad'a kukayi"

Hawaye ya zubo mata kan kuncinta.

"Teacher Gajere ne ya k'wace wayar!!

Basma dake can baya ta riga ayshan magana, 

"Tab' kema dai H. Hamid, doluwa ce sometime, kuma sai ki ka bashi.?

Hafsah dai tayi shiru, ita tsoron ta ma Abbanta, ya zatayi idan aka kirashi? Kenan anyi ta kamata da laifuka kenan? 

Me Abba, zai d'auketa?.. In na lillahi wa innah ilaihiraji,un"

Muryar Aysha ne ya katseta tana cewa,

Wai ke H. Hamid meye na yin wani kuka? Kefa kin fiya abu, wallahi.

Ta sunkuyo ta rad'a mata a kunne,

"Please kiyi shiru, kin san fa, Basma 'yar rainin sense ce, sai ta rainaki yanzu ma fa sai wani murmushi naga tanayi"

Hafsah ta d'ago gami da goge hawayenta.

Ta mik'e

"Ina zuwa"

Office d'in malamai maza taje ta sami Class teacher d'insu. Ta tsugunna, 

H. Hamid meya faru?

Sir please ka taimakeni, wallahi ban tab'a zuwa da waya ba, yau ma, Maman mu akayi admitted to hospital, shine na tawo da wayar, naji ya jikinta"

Ya tsaya yayi nazarinta sosai sannan yace,

"How can I believe you, ?

"Please ask my brother bashir."

Ta fad'a tana fargaba.

"Hmm, Who seized the phone.??

"Teacher Ahmad"

"Hmm, Hafsah ina miki fad'a don Allah kada ki b'ata rayuwarki da shashashanci, ke nutsatstsiya ce, ki nutsu, kisan dawa ya dace ki yi abota."

Zan karb'ar miki wayar, amma kin san fa dokar makaranta koh?

Tayi murmushi,

"In sha Allah sir I will not repeat it again! Thank you".

"Ok please take care."

Idan an tashi kizo ki karb'a.

"Thank you sir"

Ta mik'e ta nufi ajinsu. Cikin fara,a take cewa "Fatima in an tashi sir yace naje na karb'a.

"Okey" munyi sa,a.!

Hafsah ta koma wajen zamanta ta dafe kai, ko dai alhakin kiss d'in data mishi awaya ne ya fad'a mata.

sai yanzu abin ma, ya fad'o mata arai, bata tab'a yin haka ba sai yau.

Afili tace "Astagfurullahal aziim"

"Allah na tuba!

K'walla ta cika idanunta.

Bata tab'a zaton zata iya yin haka ba, masuyin haka ma basa burgeta, wai Itace da yiwa saurayi kiss a waya, ahalin da ake ciki na nasihar da Abba ke mata"

"Anya son da nake mishi bai yi yawa ba?? 🤔

'Ta tambayi kanta.'

Ni Kareemerh na ce "Hafsah kya tambayi kanki kuwa!!😇

Nima kamar dai naga hakan...🙊

*Yours @ always Jikar waziri Ahmadu*👌🏻

[1/11, 12:09 AM] Hajeeyah Karimah (Writer): ♥♥♥♥

*ZAZZAFAN SO*

(Guba ne)

*A broken* 

*heart story* 

 💔💔


Story and writing by:

*Karima Tijjani Mansur* 

*(Hajeeyah Kareemerh)*

*Dedicated to :Unique In Your Love Heart Members.*

🌿🌿🌿🌿🌿💐💐💐💐💐💐💐

*My Family My Pride!!*

*GAISUWA, JINJINA HADE DA* *GIRMAMAWA GA DUK WANI MEMBER NA 'WAZIRI AHMADU MAI* *SHAHADA FAMILY'*

*Aduk inda kuke,* *Allah ya k'aramarku had'e k'anmu..Amiin ya jik'an iyaye da kakanni!!* 👏🏼👏🏼👏🏼👏🏼


FANS AYI HAKURI DA TYPING ERROR BANA EDITING 👏🏼👏🏼


📄 *22*



*Data* koma gida Abba ya kirata. Cikin taushin murya yake cewa.

"Hafsah, kinga abinda nake nuna miki koh? Kin ga yak'i yazo koh?

"Abba zaizo fa"

"Hmm, yaushe? Fiye da sati da mishi maganar.

"Wallahi yace zaizo ne"

"Yaushe ya fad'a miki haka?

"Uhm.. 

Abba ya d'anyi murmushi, shikenan ina zuba ido"

Ya sauya zancen zuwa wani.

"Ya shirin jarabawa?.. Ki k'ara karatu kinji,?" 

Ta gyad'a kai "To abbah" 

"Yawwa Allah ya miki albarka."

"Amin Abbah"

"Ki turomin Bashir," 

To Abba.

Aranar bikin Auncle Abdallah, sun shirya duka 'yan gidan don zuwa wajen bikin.

Tayi kwalliya sosai tayi kyau cikin ankon bikin, tana cikin 'yan matan familynsu 'ya'yan yayyen abbanta mata, suna ta shan hira, ba,a cika ba lokacin. Ita dai gabad'aya tunaninta yana ga ina zata sami waya ta kira Yusuf'?

Gasu 'yan matan dai yawancinsu suna da wayoyi.

Hirar makaranta suke sai kuma hirar

samari. 'Nasreen ce tace mata Kefa Hafsah baki da saurayi koh?

'Hmm, anta'bo mata inda yake mata k'aik'ayi.

Ta Kalli Nasreen d'in tace " kin tuna mini wallahi yau mukayi zamu had'u." 

"Allah?

Hafsah tayi murmushi.

Nasreen tace 

"So ki kirashi mana.. Oh ashefa baki da waya, ungo nawa kirashi."

Ta Karb'a "Thank you sisterrrh"

'Hello"

My Baby how are you?

"Am fine.

Nace, "Ka tawo ne?

"Yeah give me just a five minutes"

"Ok".

Sannan Yai k'asa da murya, cikin sanyi yace.

"My Baby"

"Yes..

"Please..

What? Inji Hafsah.

Ya d'an ja numfashi, 

"Forget it.

Sai ta d'an rud'e.

"Please tell me"

"No,ki barshi kawai.

"A,a nidai.."

Yai ajiyar zuciya.

Hum, Ok"

"Ina nufin kin shirya zuwana.?

"Hmm, dear sosai ma"

"Hmm, to me zaki bani please I need some thing special,.. Because kawai ni dai bani son nazo kina min wani abu!

"Dear menayi kuma? 

"Hmm nothing, saina zo."

"Ok"

Ta ajye wayar a sanyaye. Sauran sukayi shewa "Hahh Hafsah ana zuba love".

"Bari yazo muganshi ko ya had'u."

Tayi murmushi "Hmm, Zaku ganshi ne, but my Yusuf is a king dole ku gaidashi then kada wadda ta kalleshi fiye da sau d'aya"...

Ta fad'a har cikin ranta, amma su azatonsu wasa take. Don haka suka Shek'e da dariya.

Hah kajita tab' k'anin namu zamu gaida?..lallai kina da tsaurin ido, Hafsah mun girme ki fa dukan mu"..

Haka suka cigaba da hirar su har lokacin da Yusuf, ya kirata a wayar Nasreen cewa gashi nan'.

Ta mik'e harda k'ara murza powder..

Ya had'u sosai cikin irin shigar daya saba, na k'ananan kaya.

Yau Motar daya d'akko fara ce ta had'u.

Ya bud'e k'ofar motar, kallon ta yake cike da wani shauk'i yana mata murmushin shi dake k'ara adadadin sonshi a zuciyarta.

Ahankali ta k'arasa wajen shi. Ta sakar masa murmushi, 

"Hi my dear!

Yai murmushi.. har da lumshe ido"

"You're welcome Baby" 

Ta shiga cikin motar ta zauna.

Wani k'amshi na musamman, ne ya ziyarci hancinta.

Yanayin taji ya mata dad'i fiye da koyaushe. 'Wato duk sanda take tare da Yusuf, tanajin wani abu na musammaman a tare dashi.. Bare kuma na yau ya nunka koyaushe. Bakinta taji yayi nauyi wajen kasa furta koda kalma 'You're welcome dear ' ne kamar yadda ta saba.

Ahankali ya juyo da kallonshi zuwa gareta, ya k'ura mata ido shima, yana karanta mata wani abu dake cikin zuciyarshi..

Taji wani nauyinshi.. Sannan kuma ta gaji da 'Silent' d'in da sukayi..

Ahankali ta kai hannunta saitin idanunshi ta yarfe su, kamar zata, tsone mishi idon..

Tad'anyi kamar ya furgita.

Yai mata wani 'Sudden smile' daya rikita mata 'yar nutsuwar tata, da k'yar ta samu tace, "Dear wannan kallon fa?

Ya lumshe ido sannan ya bud'e ya kuma zuba su akanta. 

"Always beautiful to me"..

I.. love..you!!

Ya fad'a, wanda motsin leb'enshi kawai ta gani ta gane me yake fad'a..

"Hum, tayi ajiyar zuciya, Ahankali ya mik'o hannunshi babu zato taji ya tab'a mata leb'enta na k'asa da d'an yatsanshi.. "I love your lips..!

Gabanta ya fad'i tsoro ya d'an kamata. Wurin, wuri ne na zirga zirgar jama,ah sannan kuma glass d'in motar ba bak'i bane '(Tinted')

Yaso ya karanci sauyin yanayinta cikin idanunta, amma ta d'an dake har da k'ak'alo mishi sassanyan murmushi, wanda iyakacinshi kan leb'enta..

Wai duk a k'ok'arinta na gudun b'ata mishi rai..🤔


Shikuma yak'i cire hannunshi sai tafiyar tsutsa yake mata a kan leb'e.😅

K'asa k'asa take jiyo hayaniyar su Nasreen suna neman su, tayi saurin juyawa d'aya gefen ta wayance, ta kira 'Nasreen d'in.

"Sister Nassy"

Cikin hayaniya Nasreen tace,

"Oh, kun gansu ashe" 

Su hud'u ne suka k'araso suka gaisa da Yusuf,

"Yakake, 

"Am fine,"

"Ya gajiyan biki?

Na'ima tace,

"No I yanzu aka fara.

"Hmm Gud" 

Hafsah taji dad'in yadda ya musu sai wani arahan murmushi yake musu.

Sautin kid'an da aka fara ne yasa suka, gudu.

"Hafsah sai kin taho kinga amfara".

"Okay sai na taho,"

'Nasreen ta lek'a kanta ta cikin glass d'in ta yi wa Hafsah rad'a a kunnenta.

"Ke irin wannan azababben guy haka??..Kin kwaso babban kai fa.

'Suka tafa'

Hafsah taji dad'i an yabi 'Sahibul Khalbi'🤣

Yusuf ya zaro wrapper na dollars ya mik'a ma Na'ima dake ita ce ab'arin da yake take' 

"Take this kunyi lik'i dashi."

"Ta karb'a thank you."

'Suka ce suka tafi suna murna, suna jinjina had'uwarshi.

Acikin hall ana ta shagali,yayin da Hafsah da Yusuf, suke ta tsinkar fure...

Hira tayi hira, Yusuf ya kalleta yace.

Baby, jiya munyi waya da friend enki Basma, and ta fad'amin a week en da zakiyi graduation zatayi birthday, so she asked me to attend."

Taji wani kishi ya toshe mata hanyar numfashinta,.. 

Basma kuma? Awanne dalili??.

"What's wrong with you Baby? Ya fad'a cikin kulawa.

"Hum.. Nothing"!

'Ta fad'a a share'

"Please tell me" ya d'an nuna damuwa.

"Hmm, haba dear, 'mene ya had'aka yin waya da ita..

"Hmm, oh sorry, she just called me, mun gaisa ne fa"..

Ran Hafsah ya k'ara b'aci jin wai Basma ce da kanta ta kirashi..

Ta juya kanta d'aya gefen..

Cikin taushin murya da k'aramin sauti yake mata magana. 

"Please Baby calm down, just forget it.. Babu komai ne fa, I respect her because she is your friend, and she care about me!!..

Tayi saurin juyawa da mamaki afuskarta. 

Cikin b'acin rai ta maimaita.

"Becouse she care about you.. Ok.. Ta fad'a tana girgiza kai.

"Am sorry dear I don't mean it, i mean she care about us"

"Hmm ta fad'a tana shirin bude ficewa daga motar.

Yayi saurin jawota ta dawo ta zauna babu shiri.

Ta juyo tana kallonshi, sai kuma tayi k'asa da ido, da suka had'a ido.

Ya girgiza mata Kai kanshi,

"Please baby.. 

Ahankali taga yasawa motar key, ya ja ta da gudu suka fice.

Zuciyar Mama ta buga dam, ankira ta ne a waya bataji, cikin shine ta fito waje don amsa wayar. Kwatsam kuma sai ta ga mota ta fita da wata mai irin ankon bikin a gaban motar.. Haka kawai zuciyarta ta raya mata kada ace dai Hafsah, ce.

Da k'arfin muryarta ta furta innalillahi,!

Sannan ta kashe wayar.

Cikin rashin sanin abin yi ta koma cikin Hall d'in.

Acan tsakiyar filin rawa ta hango Nasreen tayi gurinta da sauri, ta jawota, har Nasreen d'in ta tsorata.

"Ina Hafsah,?

Tambayar da ta k'wallah mata a kunnenta kenan, wacce tasa hantar cikinta kad'awa,..

Tama rasa k'aryar da zatayi tasan da 'Wijdaan ce (Yayarta) da tuni ta ninke mama a baibai..

Innalillahi, Hafsah ba bata zance koh? 

Ta fad'a a zuciyarta. To me zata cewa Mama,??.. Tana wajen wani suna zance ko kuwa??

ku bata shawara💁🏼‍♀😇😂

*Hajeeyah Kareemerh ce*👏🏼

[1/11, 12:09 AM] Hajeeyah Karimah (Writer): ♥♥♥♥

*ZAZZAFAN SO*

(Guba ne)

*A broken* 

*heart story* 

 💔💔



Story and writing by:

*Karima Tijjani Mansur* 

*(Hajeeyah Kareemerh)*

*Dedicated to:*

*Unique In Your Love Heart Members.*


Mmn Nussey 

Ayush 

Aysha Ibrahim rahmat 

Ayshert D

*Thanks for your love.*😘😘😘



📄 *23*



*Cikin* in'ina tace "Am, um, Mama bamu ganta ba"

"Don Allah duba min ita" cewar mama ad'an rud'e.

Nasreen ta fita da sauri, ta nufi wajen parking d'in motoci har, tagama zagayenta bata ga motar Yusuf ba.. Ita bata kawo wani abu ba zatonta ko sun gama ne, Hafsah ta koma cikin Hall d'in'

Abakin wajen shiga ta tarar da Mama. Ta tareta da tambaya, "Kin ganta?

"A,a Mama, banganta ba"

Cikin rud'u mama tace" Subhaanallah, to Ina Hafsah ta tafi ne?"

"Mama may be fa tana cikin Hall"

Cewar Nasreen.

"Na duba kowanne table bata nan."

Mama ta Kalli Nasreen sosai sannan tace "Nasreen baku ganta da wani ba"??

Cikin Nasreen ya kad'a. Tayi saurin girgiza kai,

"A,a mama, Nidai sanda kuka zo tana wajenmu, sai dai idan tare da bashir suka fita, saboda d'azu muna tare yace sai shiga store d'in opposite nan ya..

Bata k'arashe maganar ba suka hango bashir d'in na nufosu, yana k'arasowa mama ta tare shi da tambaya "Bashir baka ga yayarku ba?

"Na ganta"

Mama ta zaro ido.

"A ina??

Sai kuma yayi wani tunani, 

"Oh mama na daiga wata kamar ita."

Mama ta galla mishi harara "Kai bashir ka kiyayeni!?

"A ina ka ganta"

Ya d'an hau in'ina Um a.. a.. afa tiittin nan ne"

Ya fad'a yana nuna hanyar waje.

Cikin tsoro Mama ta furta 

"In na lillahi wa inna ilaihiraji,un"

Nasreen ta yi tsuru, 

Mama ta jinjina kai sannan ta juya zuwa cikin Hall hankalinta a tashe.

Tana shiga kiran Abba ya kuma fitowa da ita, ta d'aga kiran ga mamakinta ce mata yayi ,

Amina ina hafsah" 

Dam gabanta ya fad'i, am ta d'an fita daga Hall d'in".. 

"Ina taje? Ya katseta da wannan tambayar..

Ta.. ta. tafi ne Nemo min ruwa".

Muryarshi fal da takaici yace "Ok gani nan zuwa zan kawo hajiya." 

Cikin far gaba tace "Ok sai kun iso"

Idon Abba har wani ja yayi, Allah yaso Hajiya bata ga Hafsan ba. Shine ya hangota sunfito daga layin wajen bikin. Sunyi b'arin dama yayin dashi yake daga b'arin hagu.

Babu abinda zuciyarshi bata raya mishi ba na game da Hafsan, tsoro da fargabar abinda zai sameta suka cika shi. Babu shakka ba don da Hajiyah, suke ba babu abinda zai hana shi binsu..

"Hasbunallahu, Yake ta maimaitawa acikin zuciyarshi.

Yana sauke Hajiyar, ya kirata ta fito.

Ta karanci halin b'acin ran daya chanja yanayinshi sosai,

"Wato Sakacinki ya kai har tabar cikin gurin nan baki sani bako??

Da kalmomin da ya tare ta kenan.

Wanda kafin ta gama tantancesu

Ya kuma jefo mata wata.

"Wallahi idan naji wani abu sab'anin tunani na, sai nayi mummunan sab'a miki.. "

Ya shige motar shi ya fizga da gudu..

Yabar Mama daskare a wajen.

Acan kuma Yusuf, bai tsaya ba sai a wani wajen shak'atawa, tun a mota take son mishi magana amma tsoron gudun da suke shek'awa ya hana bakinta bud'ewa.

Da kanshi ya fito ya bud'e mata motar. Ta fito a tsorace, bata gama tsorata ba, sai da suka fito, ya kamo hannunta cikin nashi ya rik'e, gam, ta dinga motsa hannunta da nufin ta k'wace amma ta kasa." Yana jin yadda take motsa hannun amma ya bagaras da ita, sai ma wani murmushin k'auna da yake mata... Haka bisa wajibi ta ta hak'ura, suke tafiya har suka isa wurin wasu kujeru, suka zauna.

Sunyi shiru, yayin da ita ahankali take sauke numfashi,..

Ahankali ta bud'e baki murya ak'asa tace cikin k'aguwa..

"Please Dear me, me muka zo yi nan ne?

Ya zubo mata fararen idanuwanshi, please ki kalla nan mana kowa na kulawa da babynshi amma, mu always kina had'a distance between us".. Please why?

Sai da ta sanya tunani da hankali sannan ta nemo inda zancen shi ya nufa... Alokacin tsoronta 'na ta baro Mama wajen party' ya gushe, sai taji alokacin ya dace tace wani abu da zai fahimtar da Yusuf, d'in manufarta akan soyyayyarsu.

Ta tattaro dukkan nutsuwarta, sai da ta kalleshi na fiye da mintuna 2, yayin da shima itan ya zubawa ido yana murmushin zaton yau buk'atar shi ta karb'u.

"Dear, ta furta ahankali.

Ya d'aga mata gira.

"Yess"

"I don't want to hurt you.. Don Allah mu daina maganar irin wannan relation, please let it be in our feature'..

Ya kalleta da alamar tambaya In Our feature?.. When ?

Cikin k'warin guiwa tace "I mean when we got married."

Yayi wata dariya wacce ita bata ga amfaninta ba.

"Hmm, baby you're talking about long time' let me tell you 'honest to God "I CAN'T WAIT".. So please allow me to get a solution to my self... Yai k'asa da murya, "Baby i promise to marry you but In sha Allah I will never beg you again!"..But kome ne ya faru kinsani kece kika ja...

Ta d'anyi shiru cikin nazarin maganarshi, ta kalli agogon hannunta, 5:30pm, 

Ta mik'e da sauri, "Please let me go,.. "No, ki bari sai anjima mana.

Hankalinta gaba d'aya yayi can tace "No please let me go. And please dear when will you come to meet Abba"?

Yai murmushi hmm, Im afraid, but i will tell you soon."

Ya taso ya biyota ahankali suka fara tafiya..

"Baby ki karb'i wani wayar mana, i miss your goalding voice."

Ta d'anyi murmushin takaicin rashin wayarta, "No thank you dear."

Badon tsoron Abba ba babu abinda zai hanata karb'a

Ya bud'e mata motarshi, ya mata alama ta shiga.

Ta girgiza kai 

"No barni na tafi"

"Please baby ki shiga na maidaki"

"No thank you.

"Ok, 

"Please ki kirani idan kinje school."

"OK,

Ya rakata bakin titi, ta shiga mota sannan ya juya don shiga motarshi ya tafi.'

Tana fara tafiya a Napep d'in, taji fad'uwar gabanta ya tsananta. Allah yasa kada mama ta lura bata nan.

Tana isa ta fito ta bashi kud'in.

Ahankali take takawa, har cikin Hall d'in. 

Da Amatullah ta fara cin karo, wacce ta tsoratata da cewa, "Hafsah, wai ina kika je ne? Mama sai Nemanki, take." "Innalillahi da gaske?

"Wallahi yanzu ma ta kuma fita nemanki."

Hafsah tayi shiru, amatullah ta ja hannunta suka yi ciki tana cewa, "Ansha rawa babu ke".. Har amarya da ango sunzo.

Filin rawar suka shiga 'yan matan family da samari anata chashewa."

Itama ta shiga akayi da ita, bashir ya matso dai dai kunnenta "yaya, wallahi Mama sai nemanki take, wai ina kuka fita?..nima na ganku fa!

tayi shiru kawai don bata da abin ce mishi.

Wajen mintinta 20mins, da dawowarta mama ta dawo. Tana hango ta tazo ta finciko ta, suka yi waje.

Mari Maman ta wanka mata.

"Ina kika je?

Ta rik'e kunci. Tayi shiru..

"Bazaki fad'amin ba, Mama ta fad'a tana shirin k'ara mata wani marin."

Cikin kuka ta ke mata bayani 

"Banje ko ina ba"

"K'arya zaki yi min"?

Wallahi Hafsah ki shiga hankalinki zan tattaka ki anan wajen.."

Haba Amina, menene nayin hayaniya a nan wajen, ai bai dace ba."


Haba yaya wannan yarinyar idan kinga maganar da take d'akkomin sai kin tausaya min, ya zata dinga ja min laifi a wajen sa..

"Ya isa haka,.. Ta matso ta dafa kafadar Maman, kiyi ha'kuri kuje gida sai kiyi mata fad'a Allah ya shirya mana su."

Aunty Nafeesah ce 'Yayar Mama' wacce su Hafsah ke ce mata (Maman ya Nazeer,) daga ita sai baffa usman abbansu (Amatullah) sai Maman su Hafsah.

'Tana aiki ne a 'Ministry of women affairs' sannan malama ce ita a fannin addini, tana kuma da wajen gyaran jikin amare,

 wanda yaranta keyi.'


Ala dole mama tayi shiru. Tana aunawa Hafsah uwar harara.

'Maman ya Nazeer, taja hannun Hafsah suka koma ciki, yayin da Mama wayar ta tayi k'ara kiran Abba ne.

"Hello"

"Ya ta dawo?

Eh, to maza ki tattarosu ku tawo.

"Tom"

Dama an kusa tashi, biki kuma yayi dad'i ga wad'anda hankalinsu ke kwance irin su 'Nasreen'

Ba Hafsah ba bashir ma yasha jinin jikinshi. Aunty Nafeesah ce tasa drivernta ya dawo dasu.'

'Hafsah dai sai rab'e tab'e take.'

Suna yin sallama ta shige d'aki.

Fatanta Allah yasa mama bata fad'awa Abba ba.'

Tana cikin bed room d'in tajiyo fad'an Abba a palour yana cewa,

"Ina take?? Ta fad'a miki inda taje?..

Mama tace cikin tsoro itama tana d'akinta..

Bata rufe baki ba, ya nufi d'akin Gadan -Gadan, Hafsah na shirin danna key taji ya banko k'ofar da k'arfi. sunayin ido biyu, ya shiga dukanta da bulalar hannunshi.

Ihu Hafsah take ba na wasa ba, saboda abba laftar ta yake sosai kamar wani k'aton yake duka..

Tana ta bashi hak'uri "Don Allah abba kayi hak'uri wallahi bazan sake ba" na shiga uku, wayyo mama, Abba, Innalillahi.."wayyo zan mutu"!!

Kamar zuga shi takeyi. Wato bakya jin magana koh? So kike ki lalace ne?, saboda kin zama 'yar kanki koh, shine har zaki dinga fita da wani, wato duk nasihar da nake miki bakiji ba ko?

Gidan uban wa kika je??

Ihu ta kuma, saki tama kasa magana sai karkarwa da muryarta take wall lahi.. Abb.. Abba"..

"Mufida har kuka ta fara tana, rik'e hannun Abba. Yaran ma sai hak'uri suke bashi. 

'Mama tayi rok'on amma ina yak'i kyaleta.'

Ganin yana shirin kashe mata 'ya yasa ta yi azamar fincike ta, da karfi, tana haki muryarta na rawa take cewa, "Wallahi sai mu bar maka gidan, kashe min ita, zakayi?.. Ko me tayi ba sai ka kyaleta ba?" wasu Maganganun ma bata san tana fad'ar su ba.

Abba ya tsallake Hafsah, dake kwance shame -shame, ya fice daga d'akin ko kallon mama baiyi ba.

Cikin azama mama ta figi mayafinta da jakarta, tacewa bashir,

"Kamota mu fita da ita..

Sai gunjin kukan Hafsa kawai akeji. Ya kamata, ta mik'e da k'yar, ya rirrik'eta da k'yar take takawa, sukayi har yar gate' Mufida ta biyo su, mama zan biku"

Maman ta daka mata wata uwar tsawa daya sa ta koma babu shiri..

👏🏼👏🏼👏🏼

*Hajeeyah Kareemerh ce*

👍🏼👍🏼👍🏼

[1/11, 12:09 AM] Hajeeyah Karimah (Writer): ♥️♥️♥️♥️

*ZAZZAFAN SO*

   (Guba ne)

*A broken*

*heart story*

  💔💔



Story and writing by:

*Karima Tijjani Mansur*

*(Hajeeyah khareemerh)*

*Dedicated to:*

 *Unique in your Love Heart Group members.*




📄 *24*



*Adaidaita Sahu* (Keke Napep) suka tare suka yi wani d'an k'aramin Asibiti, da ita, aka duba ta sosai sannan suka bata magunguna, suka ce sai nan da kamar awa biyu zasu sallame ta..Sai wajen tara na dare suka dawo gida.. Jikinta duk shatar bulala, dak'yar tayi sallar Magrib da Isha'i sannan ta kwanta, mama na d'ankin a kusa da ita, don yau haushin Abba takeji. Don da suka dawo ma yana parlour shida su Mufida, amma ko kallonshi mama batayi ba. Banda sallamar da tayi a ciki-ciki.

Ita bawai laifin Hafsah ne bata gani ba, amma wannan dukan yayi yawa, sai kace wacce ya kama a gidan karuwai??

Tana d'akin har wajen goma sha d'aya na dare 11:00pm.

Ita ko Hafsah shiru tayi ta lumshe ido kamar mai yin bacci, tana jin kunyar mamanta, don bata so ta k'ara yin irin wannan kalan laifin ba, bayan abinda taga Abban yai wa maman rannan.

Sannan takaicinta shine,

'Tasan yanzu Abba zai mata dokar hanata fita..' Gashi bata da wata hanyar contacting d'in Yusuf, hawayen kewa suka zubo mata, masu zafi.. Ga jikinta da ya addabeta da zafi sai abin ya had'ar mata ya sabbaba ('Cause') mata, ciwon K

kai mai zafi wanda ya hana ta bacci.

Mama sai wajen 1:00am ta bar wajenta,.. Sai bayan nan ta d'an samu bacci.

Da safe tunda tayi sallah ta koma ta kwanta, tanajin hayaniyar su Zainab a parlour. Har wajen 10:00am, Sannan zainab ta shigo d'akin tace mata, "Yaya, wai mama tace ki zo kiyi break"

Ta d'aga mata kai.

Dak'yar ta iya mik'ewa saboda tsami da jikinta yayi,.. Duk k'annenta na tare da maman, yau akan dining ma suke, ta wuce ahankali, yaran suna, mata "Sannu Yaya" sai taji wajen na mata nauyi, mussamman da Mama keta aikin kallonta, sai ta tuna cewa bata gaida maman ba.

Cikin dashashshiyar muryarta tace, "Mama barka da safiya"

"Sannunki ya jikinki?, maman ta amsa mata cike da kulawa.

Ahankali take cin abincin, har suka gama, tana shirin mik'ewa Abba ya k'walo mata kira, cikin rud'ewa ta amsa "Na,am", ta mik'e a hanzarce ta nufi d'akinshi, ya gama karyawa, kwanunkan na gefen shi akan 'Tray' da shirin shi na fita daurin aure. tanayin, sallama tun kafin ta zauna yai mata nuni da su, ta sunkuya ta debe su, ta fita, kitchen ta kaisu tana fatan 'Allah yasa kiran da yake mata kenan'.

Ta dawo a salub'e ta durk'usa a gefenshi, kanta a k'asa saboda tana tsoron su had'a ido, cikin sanyin murya tace, "Abba ina kwana"

"Lafiya lau," kawai yace. Tayi shiru, shi kuma ya k'are mata kallo, sosai sannan ya bud'e baki ya fara mata magana.

"Ina kikaje jiyan"??

Ta yi shiru, saboda tsoron amsar da zata bashi take, 

Ya daka mata tsawa, 

"Ba zaki fad'amin ba"..

Jikinta ya hau rawa, wallahi babu ko ina.. 

K'arya zaki min, zan tattaka ki anan wajen, ki bud'e baki ki min magana, shashashar banza"..

Ya fad'a yana shirin mik'ewa ya d'akko bulala.

Cikin hawaye ta fara magana, Don Allah Abba, kayi hak'uri wallahi, bansan fita zamuyi ba, shine ya ja motar,..

Ina kika je na tambayeki,"

"Park". Me kikayi acan?? Wallahi babu komai,"

Wato saboda baki da kamun kai koh, ? To yayi miki kyau, ban tab'a yi miki dukan da kika suma, bane shiyasa. Ya nuna ta da yatsa, wallahi wallahi Hafsah ki shiga hankalinki akan abubuwan da kika k'irk'irowa kanki, idan ba haka ba, zakiyi mamakin abinda zanyi miki, shashasha kawai." kuma daga yau kada na k'ara ganin kinfita ko da k'ofar gidane, ko makaranta ma kin daina zuwa!!"

Ta d'ago a razane ta kalli, abban, wanda uwar hararar daya galla mata, yasa tayi saurin mayar da kanta k'asa.

"Innalillahi, shikenan ta, kad'e ta jawo wa kanta, Abba ya hanata zuwa school, babu batun, karatunta kenan? saura fa sati d'aya su fara 'WAEC' , yanzu ya zatayi kenan, babu zancen fita? Wane irin k'unci zata shiga.??

'Zufa ta wanke mata fuska, babu shakka zata iya cewa k'addara ce tasa Yusuf, ya fita da ita, banda haka, me sukaje yi wannan waje?.. Su basu sai komai ba, hasalima, a gurin Yusuf, baiyi yunk'urin tab'a ta ba, bare tace alhakin hakan ne' Kawai Tsautsayi dai.!!

"Tayi shiru, tana nazarin rayuwar da zatayi babu fita.

Wallahi idan baki sauya tunani ba, zaki matuk'ar shan wahala a wajena."

Tashi ki fitarmin "ana!

Kalaman Abba, kenan da suka katse tunaninta.

"Cikin kuka tace Don Allah kayi hak'uri wallahi bazan.."

Ya kuma daka mata wata uwar tsawar "Fita nace",

Ta mik'e jiki babu kuzari ta fita.

Tana fita parlour, mama ta ga yanayinta, sai ta mik'e sai d'akin Abban,..

Ta nemi kujera ta zauna.. Fuskarta fal da takaici.

Abba ya karanceta tsaf, kafin tayi magana ya riga ta.

"Amina kin bani, mamaki, wato bazatayi laifi a hukuntata ba koh,.. kin fiso abarta tayi tayin abinda taga dama babu kwab'a.. Bakya fargabar abinda zai je ya zo Kennan."

"Ni ba cewa nayi kada a hukuntata ba, amma ai dukan da kayi mata yayi yawa, macece fa"

Abba yai murmushi mai sauti, kina nufin kin fini sonta ne, ko kuma me? 

Tayi shiru azuciyarta tace "Ai hakanne" _lol_

'Jin tayi shiru ya cigaba da magana cikin son fahimtar da ita, don ya fahimci itama cikin fushin take, ba zata tab'a fahimtarshi ba idan shima ya nuna mata fushinshi.'

"Amina, kullum fata na shine in sauk'e nauyin hak'k'inku dake kaina, Hafsah fa 'yata ce, bazan yi abinda zai cutar da ita ba, komai ina yin shi ne don ta sami kyakykyawar tarbiyya, ina roko'nki idan bazaki tayani ba, to ki daina adawa da duk hukuncin danayi mata."..

Ta d'ago da niyyar tayi magana amma ya hana ta, ta hanyar daga Mata hannu"

"Dakata, wallahi kema na tabbatar jiya bakiyi baccin kirkiba, saboda tunanin meyafitar da ita, ita da wani?.. Ki bar yi mata shaidar tana da hankali ko kamun kai, ni bana zarginta da komai amma, wallahi _ba,a shaidar yaran yanzu..._ kuma kema nasan daga yanzu hankalinki bazai k'ara kwanciya ba matuk'ar tafita daga cikin gidannan har sai ta dawo."

Mama tayi shiru tabbas kalamashi gaskiya ne'.

Kuma sunyi nasarar sauke fushinta akanshi, don haka ta shiga bashi hak'uri, 

"Kayi hak'uri to, na fahimceka, insha Allah bazaka k'ara jin bakina, akan lamarinta ba"

Ya girgiza mata kai, "A,a ai 'yarki ce, kema kina da hak'k'i akanta,.. kiyi ha'kuri kema, ki dinga yi mata addu,a kawai."

Ta d'aga mishi kai, "To in sha Allah",.. Ni dama kawai dukan da ka mata ne, ya tsoratani kuma kasan fa duka baya gyara"

Yayi murmushi harda jijjiga k'afa "Nasani"

Cikin nutsuwa ya kuma ce mata, 

"Na hanata fita, koda zuwa makaranta ne, don haka kisa mata ido, sosai.

"Tom, shikenan"

Bata da musu akan matakin daya d'auka..

Kuma ta fahimceshi sosai, saboda haka ta bar wannan zancen, ya miqe zan fita wajen daurin aure Adawo lpia Allah y tsare, 

ta miqe don rakiyar shi. Kmr ban ita ke fushi da shi ba..

Hafsah ta, dawo rayuwa kamar mujiya acikin gidan, kullum tana d'akinta, babu dai wanda yake k'yararta acikin gidan amma duk ta tsargi kanta, kuma babu wanda ya damu, da hakan.

Akan idonta su bashir suke shiryawa su tafi makaranta itako ko oho, sai bashir dake Cemata "Yaya 'yan ajinku suna ta tambayata nace musu baki da lafiya ne.

'Hakan shi yafi damunta, gashi tun ranar nan, Abba, yayi watsi da ita gaisuwar ta kawai yake amsawa. Gefe kuma kewar Yusuf da tunaninshi sun addabeta, hakan yasa tayin wata 'yar rama, tayi bak'i.'

Haka har sati ya zagayo ranar lahdi, kuma washe gari zasu fara exam, kuma Abba yasan da hakan, Amma, har ya dawo babu wata magana daya yi mata...

*Kuyi haquri da wannan*👏🏼👏🏼

*Hajiyar ku ce*👌🏻

[1/11, 12:09 AM] Hajeeyah Karimah (Writer): ♥♥♥♥

*ZAZZAFAN SO*

(Guba ne)

*A broken* 

*heart story* 

 💔💔



Story and writing by:

*Karima Tijjani Mansur* 

*(Hajeeyah Kareemerh)*

*Dedicated to:*

*Unique In Your Love Heart Members.*



📄 *25*



*Sai* da safen mama tashigo tace mata, 'ta shirya zuwa makaranta. K'arfe 9:00am ne, exam d'in, don haka, da 'Nura' yazo, Abba cewa yayi ya kaisu bashir, ita idan lokacin yayi ya dawo ya kaita.

'Tunda ta jita a mota taji wani farinciki ya ziyarceta, tana son tajita cikin k'awayenta, sannan tana son ganin Basma.'

Sanda taje ana daf da shiga, saboda haka bata sami ganin Basma, ba. Kuma cikin rashin sa,a ajin da suke exam daban ne.

Suna fitowa daga 'Papper', Aysha D'ahir ta nufo ta.

Suka cafe hannu.

"H Hamid ya jiki..? Wallahi har kin rame!"

"Hafsah dai tace Da sauk'i kawai"

Ke wallahi mutuminki ya dameni, kullum sai yacemin in had'aku 

a waya idan nazo school,..So na fad'a mishi baki da lafiya, ne but ya damu fa sosai"

Hafsah taji dad'in hakan har da lumshe ido,

"Oh Allah sarki My Yusuf, nima nayi missing nashi wallahi"..

"Please ki had'amu"

"Am sorry to say "Na baro wayar a gida because naga exam za,a fara, kada ayimin seizing, but don't worry in sha Allah tomorrow zan Had'aku".

Hafsah ta rungume ta "Thank you my friend!!"

Muryar Nura (Drivern su) taji, yana cewa, "Hafsah, kiyi sauri don Allah"

Ta rik'e hannun Aysha, "See you tomorrow bye"

sai taji zuciyarta ta d'an k'untata 'Ashefa yanzu ba da bane'.. (Wato abba ya bawa Nura umarnin idan tana da paper biyu, matuk'ar bazata wuce awa 4 biyar a exam ba, Nura ya jira ta tagama sanan ya dak'k'ota, wannan doka ce akanta, idan kuma ta haura lokacin gama exam yace mishi laifinshi ne'

'Haka tanaji, ta shiga mota bata sami ganin Basma, ba.'

Wasa-wasa har sunyi rabin exam d'in, amma bata sami had'uwa da Basma, sun zauna ba. Suna had'uwa a duk lokacin da ta zo su gaisa. Watarana suna d'an fara hira, ake shiga 'Exam'..

Sanan hirace irin ta group, bata samun keb'ewa da Basman, kuma mafi yawanci tana riga su basma fitowa, kuma, da Nura ya k'yalla ido, ya ganta zai ce suyi gida..'

Haka Aysha ta bata hak'urin, rashin had'ata da Yusuf, saboda ta daina zuwa da waya. Agabanta, aka k'wace ta wata... Hafsa amma kiyi ha'kuri in sha Allah gobe ki shigo da wuri zan had'aku."

Haka kuwa, akayi dama exam d'in ta karfe tara ce, kuma Abba ma yana da copy na timetable d'in, tun daga dare take shirya irin k'aryar da zatayi, abarta yau ta bi su bashir'.

Taje ta sami Abba, afalo. Saboda ita yanzu da wuya ki ganta a falo, ko yasa yaushe tana 'Bed room'.

"Abba"

"Na,am,

Ta d'an yi shiru..

"Ya akayi".

Inji Abban'

"Um, dama ance gobe mu shiga da wuri saboda, jibi, zamuyi 'Catering' ne, to wai akwai abinda malamar zata koya mana.

Ta k'arashe maganar tana kallon Abban don taga ya k'aryar tata ta karbu'?..

Abba ya kalleta sosai, ya nazarci yanayinta, sannan yace ,

"To ki shirya ku tafi da su bashir".

Tayi murmushi "Nagode, Abbah"

Har takai bakin k'ofar d'akinta yace mata, 

"ki dinga yin addu,ar neman nasarar Exam d'in dai."

"To Abba" 

'Ta shige d'aki'

'Cike take da farinciki, da tunanin gobe ya zata kasance da Yusuf, d'inta a waya.' Hakan ya bata damar yin ishashshen bacci mai cike da ni'imar mafarkin Yusuf, d'inta a cikinsa.'

Washe garin ranar, ta zame mata mai sa,a, wato Basma, tazo sannan ga Hafsah, cikin zumud'i ta nufi Basma ta rungume ta. "Basma Yunus!!

Basma ta d'anyi murmushi H Hamid kin b'uya,"

Wallahi, bari naje wajen Aysha Taheer, na dawo.

"Ok, Basma ta fad'a tana bin bayanta da rakiyar wani kallo'..

*"Kuyi Hak'uri please wallahi bacci nke ji"*


*Hajeeyah Kareemerh*

[1/11, 12:09 AM] Hajeeyah Karimah (Writer): ♥♥♥♥

*ZAZZAFAN SO*

(Guba ne)

*A broken* 

*heart story*

  💔💔


Story and writing by:

*Karima Tijjani Mansur* 

*(Hajeeyah Kareemerh)*

*Dedicated to: Unique In Love Heart Members*





📄 *26*





*Tana* isa wajen Aysha suka tafa, taja hannun Aysha sukayi cikin class. Baifi mutum uku suka gani ciki ba, kasancewar, yawanci basu zo ba.

'Suka nemi wuri can baya suka zauna. 

Aysha ta na danna waya take cewa,

"H. Hamid, wallahi guy enki na sonki fa, ya damu yaji muryarki, you're lucky wallahi"

'Suka tafa.'

Ta mik'a wa Hafsah wayar, "yawwa ya d'aga"

'Hafsah ta mik'e ta koma wani desk en. 

'Hello'

"I miss you my baby!..

'Da kalmar daya tareta kennan.

Hafsah, taji ta cikin wata duniya mai cike da farinciki.

"Me too dear nah!"

"Baki nemana ai hafsah"

Taji dad'in kiran sunan nata da yayi har cikin zuciyarta.

Ta jingina jikin 'abin jingina' dake jikin desk d'in, babu abinda take sai murmushi.

"Am sorry dear, it's not my fault wallahi, Abbanmu ne ya hanani"..

"Hmm"

Tacigaba, 

Please ka daure ka zo wajen Abba, shine zai bamu damar kasancewa tare, please I beg you" 'Ta k'arashe maganar cikin murya mai rauni.'

"Hum" Yai ajiyar zuciya. "Okey" in sha Allah but ki bari kiyi candy koh, since 10days, remained.

"OK thank youu, dear'

"Hmm, dear friend enki asked me to attend her birthday nd graduation party,..and she asked me to come with you"..

"Hum, Hafsah tayi ajiyar zuciya.' Lokaci d'aya taji ba'kin ciki da kishi sun rufe ta, wai wanne irin rainin hankali basma ke mata ne"? "What did she mean?

"Baby, kinyi shiru"

"Hmm, dear please wai mene ya sa kamin haka? 

"What do I did?

"Hmm, me yasa kake yin waya da Basma, ban sani ba"?

'Ya kwantar da murya " Am sorry mai baby, I told you I just respect her.. Please zaki je party en koh"

"Noo bazani ba"

'Ta fad'a da fad'a.'

"Hmm, yai murmushi, yayi k'asa da murya "Am sorry, please kije zanzo muje dake, don Allah kinga basma is our friend"..

Ta maimaita cikin murya mai bayyana mamaki'

"Our friends,?' Hmm, let me tell you, basma is no longer my friend ehe"

"Hahh, your friend is my friend so, please calm down stop feeling jealousy, she's just a friend"

'Yayi maganar cikin dariyar da ta d'anso tafiya da ita, 'tana son dariyarshi.'

'Ta d'an share kawai ta binne kishin a k'asan zuciyarta, bata son ta b'arar musu d'an farincikin da suke ciki bayan sun dad'e cikin kewar juna'.

'Cikin shagwabar daya saba, yace, "Baby what about yours ina za,ayi namu party en"

Ta d'an hadi'ye takaicinta, da dane ai Abba abinda zai mata yana da yawa, amma yanzu bata tunanin za,ayi mata wani abu"..

"Kinyi shiru"

Yace da ita,

"Nothing, bana son party"

"Oh my baby, why?.. Mene yasa ke komai baki so?

"Hmm, babu komai, ka share kawai."

Yai ajiyar zuciya "Ok, but I will prepare something special for you"

Tayi saurin cewa thank you, but please ka barshi kawai"

"Baaby,?

"Uhum"

"Kina fushi da nine koh? 

"No, ni bana fushi da kai Allah" tayi saurin fad'ar hakan'

"So meyasa kike rejecting abinda nake so"..? "Babu komai wallahi dear", ni bana son party ne " 

"Ok, ya wuce'

"Yanzu yaushe zanzo ganinki?

'Tab'.. Ta fad'a a zuciyarta.

Shi ana ga-yak'i yana ga-k'ura'!!😅😅


"Hmm, sai bayan kazo kaga Abba." 

"Hm okey", yace mata kawai, don ta rufe mishi baki'

"I love you" ya fad'a mata babu tsammani, taji dad'i sosai, 

Me too dear"!

"Ok, sai anjima, koh, take care of yourself "

'Sai taji babu dad'i fiye da koyaushe idan suna waya yai mata sallama, da k'yar tace mishi,

"Bye bye,"

'Yai mata kiss, a wayar'

'Ta gaza cire wayar

daga kunnenta, har wata k'walla ce ta cika mata ido, sai yaushe abba zai yarda da Yusuf?

Tayi zumbur ta mik'e da ta tuna aika aikatar da Basma, tayi mata, ta mik'awa Aysha wayar, tare da cewa "Thank you sister," ta fita da sauri, tana huci, kishin Basma ya rufe ta...

'Tana zaune tana cin cake, Hafsah ta zauna gefenta tana d'an huci, 

"Am Basma ina son magana dake".

Basma na ganin yanayinta itama ta d'an daure fuska, "Uhum go ahead"

'Ta fad'a batare da ta bawa zancen Hafsan muhimmanci ba.

"Me yasa kike kiran yusuf a waya? Sannan mene zaki wani gayyaceshi partynki"

Basma ta d'an gyara zama, "Am H. Hamid dama shine kike wani huci?"

"So maida wuk'ar" ta fad'a tana kaucewa hafsan hanci. Hafsah ta m

do ke hannunta, 

"Kinga ki fad'a min dalili".

'Basma tayi dariya, "Nothing fa I just take him as my brother, so kuma nasan idan na gayyaceki partyn bazaki je ba, shine na fad'amishi, becouse partynma na dare ne"

"Hmm, waye ya ce miki bazani ba, kuma da kika fad'amishi shi zai sani naje,?..kinga please, kada ki k'ara kiranshi, kiyi ma delete contact enshi, Bana son irin haka ni"

Basma ta d'anji ta kaici, amma sai ta share, saboda har yanzu, ba,a zo inda take so azoba."

"Haha H. Hamid' kenan"

"Yanzu dai please kuzo partynnan ke da shi"

"Bazan zo ba" shi tunda kin gayyaceshi sai yazo ai"

"Hmm, H. Hamid, kenan, ai nasan yusuf zai zo"

"Mts, Hafsah taja tsaki sannan ta bar mata gurin.'

Basma tayi murmushi "Hmm yarinya ai dama baso nake ki zo ba yarinya"

'Yau Hafsah cikin nishad'i ta yini a gida, har da taya mama aiki. Mama taji, dad'in hakan har tana mata nasiha'..

"_Hafsah dama babu, wanda ya sauya miki a cikin gidannan amma duk kinbi kin damu kanki kin daina shiga cikin 'yan uwanki,.. ??_ _Mufa iyayenki ne, idan bamu miki fad'a ba wane zai miki, Don Allah ki gyara rayuwarki, ki daina abinda kike yi kinji"._


Ta gyad'a kai, "In sha Allah mama na daina".

"Yauwa, Allah yai miki albarka"

"Amin"

Abba ma yau yaga d'an chanji a tattare da ita, ('Yaga tana walwala'.) ya ji d'adin hakan, yau har hira sukayi da ita..

Dama ba a son ranshi yake d'aure mata fuska ba, kawai dai yana son 'horontata' ne.

'Yanzu har sun gama exam, kuma, ayau ne sukayi papper ta k'arshe yau kuwa yawanci duk sunzo da waya, bayan anfito daga exam akasha hotuna, da ('exchanging numbers,) ana farinciki ana kuma tunanin kewar juna.. _'Rayuwar makaranta kenan'_

'Gobe ne kuma za,ayi graduation party na makaranta, an gayyaci iyayen yara, sannan kuma kowanne dalibi an bashi damar gayyatar mutum uku banda iyayenshi.

Sai kid'e kid'e da raye-raye ake a ajujuwan, uniform yasha zane, da rubuce rubuce, musamman d'an k'aramin farin hijabinsu' ita dai Hafsah batayi ba'

Aysha ta tawo da gudu tana ihu 'Yeee H. Hamid you're lucky gaskiya'.. Ajin yayi shiru ana son jin me zatace,.. 'Aisha ta cigaba da magana'

"She's the first person that received 'A Congrats Text' from her hubby" class ya rud'e, "heyy.. Can wata ma ta d'aga "Am the second'!!!

Suka rud'e da ihu..

Basma tanajin, abinda akace kan Hafsah, ta cije lebenta, azuciyarta tace, "Hmm, yana son yarinyar anya kuwa.. Zanyi nasara?.. Wata zuciyar tace mata "You have everything he needs, and you can give him. So that _u are the winner"!!_

Tayi wani ihu da yasa kowa ya juyo da kallonshi zuwa gareta' 


"Heeyy,.. Celebration of new life"!! Ta buga hannunta akan desk wata ma ta d'ora nata, haka sukayi ta tawowa da gudu, suna d'orawa, sannan suka d'aga hannenyen suka watsar... Happy candyy!!

Azatonsu murnar candy Basma takeyi'

'Hafsah ta ja hannun Aysha suka bar cikin hayaniyar nan, suka zauna kan 'baranda'

'Kinga text en fa har uku Aysha ta fad'a tana mik'a mata wayar.

'Ta karb'a cikin zumud'i tafara karantawa'


_'Am very happy to witness this remarkable day, am wishing you happy graduation.._

_Wishing you best result, babynah.._


_"Hmm,.. My dear struggle has now ended,.._

_'Congratulations to myself bcoz, now, I know_ _I will get more Caring from you.. Happy_

_graduation baybee nah'_


'Hafsah tayi murmushi taji d'adin hakan sosai.. Sai ta hau 'typing' reply:

'Thank you my dear'

"You made me feel special.. Much of love to you."

Bata dad'e da turowa ba sai ga text na transfer 2000 credit, ya turo..

Can kuma text ya kuma shigowa, ('For aysha thank you')

Aysha har da tsalle, "Wow Hafsah kimin godiya naji dad'i wallahi..

Hafsah tayi murmushi kawai, tana son ta fad'awa yusuf taron da za,ayi gobe, tana kuma tsoron kada su had'u da Abba, don tasan Yusuf baizai tab'a yin yadda baza,a gane ba.

'Washe garin makaranta ta cik'a sosai, da mutane hall d'in taron yasha decoration, dalibai sunyi kyau cikin rigar graduation mai kalar dark blue da ratsin ja' suna kan kujerun da aka tanadar musu..

'Abba da Mama sun sami damar halarta.. Can idanun Hafsah suka hango mata wani kamar Yusuf, gabanta ya fad'i.. Tsoro da kishi suka had'ar mata. Kada Abba ya ganeshi ta shiga matsala, sai kuma kishin cewa basma ce ta gayyaceshi.. Haka dai tayi shiru cikin fargaba.

'Anyi jawabai masu muhimmanci da kuma nasiha ga d'alibai, daga k'arshe aka fara raba kyautuka, ga d'alibai masu hazak'a.

'Daga ajin maza aka fara, sannan bangaren mata, a B'angaren 'Art class' Hafsah ce ta farko a mata, wacce aka fara bawa kyautar d'aliba mafi hazak'a (Best student), sai monitor ta ajinsu, sai wata d'aliba sai Basma, d'alibai da yawa sun sami kyautukan.'

Ak'alla hafsah ta k'arbi kyautuka guda uku, sunyi hotuna da malamansu sannan aka nemi a fito waje domin iyaye su sami damar yin photona da 'ya'yansu.

' Hafsah tayi saurin zillewa, tayi bayan wasu ajujuwa, tace wa Aysha ta kira mata Yusuf don Allah, saboda ta nuna mata shi tun cikin 'Hall' don hafsah kusa da Aysha ta zauna.

Yana ta waige waige Aysha ta mishi magana "Am kaganta can". Ya biyota sukayi bayan class d'in.'

' Tun daga nesa yake mata murmushi, ita ma haka, yana k'arasowa tace your welcome dear"

Ya akayi kazo yayi murmushi, nasan za,ayi ne fa" 

"Thank you alot.. I hope ba basma ce ta gayyaceka ba"

Yai 'yar dariya, no ba ita bane" 

"Sure?

"Yes, I swear i just come for your sake.."

"No baby I trust you, basai ma ka rantse ba, thank you"

Ta mik'a mishi gift d'in ya karb'a yana cewa 

"Wow how lucky iam,? to have a Gifted and also the school over roller.. As my girlfriend"!..

Tayi 'yar dariya kana tsokanana ko? 

Sai ta lura ashe Aysha video take musu, ta nuna ta da yatsa kin ganki koh,"

"Perfect match" inji Aysha, "Yusuf yace thank you"

'Aysha ta musu, photona sosai kuma sunyi kyau, Hafsah, ta tuno ta baro su Abba, gabanta ya fad'i, ta kalleshi suka had'a ido, duk sai suka kasa d'auke idanuwasu kusan minti guda, Aysha kuwa na gefe tana faman musu video, sun burgeta sosai'

Atare suka saki murmushi,.. Ahankali tace baby na baro su Abba, so let me go to them, "

Yai mata murmushi "Okey' ahankali ya zaro wata leda ya mik'a mata.

"Ta girgiza kai" shima ya girgiza mata nashi kan'

Aysha ta mata alamar ta karb'a ta amsa ta mishi godiya'.

"Thank you dear".

"You deserve it"

Ta mik'awa aysha, ta rad'a mata

"Ki "ajyemin, ko yaushe ne zan karb'a. 

"Ok"

Suka taho taga alamun Yusuf ma biyo su zaiyi, ta juyo tace mishi, "Please dear, act like you were aysha's bros" 

"Okay"

'Ya fad'a yana murmushi.

'Hafsah ta d'aga mishi hannu, ta k'ara sauri ta wuce ta barshi shida Aysha'

Tana isa ta saki fara,a Mama wai Ashe chanjen gift aka min shine teacher d'inmu yace nazo achanja min"

'Ta k'arashe maganar tana mik'awa abba kyautar" ya karb'a yana murmushi Allah ya sanya albarka"

'Sunyi hotuna sosai, ita dasu Abba da bashir, da wasu k'awayen nata, Aysha ma wajen nata family ta tafi, akabar Yusuf gefe yana kallon su Hafsah yana murmushi, can ya hango basma ya tafi wajenta'

'Sunyi pictures shida ita, tacewa mamanta yayan k'awarta ne. 

Sai da aysha ta gama ta hango shi wajen basma aiko taje ta yafito hafsah, suka zo akayi pic en dasu, duk da Hafsah bata ji dad'in ganin shi, wajen basman ba, kuma dake basman 'yar duniya ce, sai ta dinga jan hafsan da hira, suna gamawa, suka wuce wajen su abba, aysha ta gaida mama da Abba, sannan yusuf ma ya gaidasu, gaban hafsah sai fad'uwa yake, mamakinta abba har hannu ya mik'a mishi, suka gaisa, Hafsah tace wa mama Mama wannan k'awata ce aysha" "Ok, Aysha angama school Koh "? Tace "Eh mama,"

"To Allah ya bada result mai kyau." "amin"

Aysha ta mik'awa Yusuf Wayarta, "Please yaya yi mana pics, 

Ya karb'a yana murmushi, yai musu ita da su mama, 

Sanan sukayi selfie a wayarshi shida Aysha da Hafsah"

'Shi dai Bashir baki ya saka don ya gane yusuf' lol

Abba yai wa Yusuf sallama to mu zamu wuce Allah ya sanya alkhairi.

"Amin dady"

Abba da Mama sun jera sunyi gaba yayin da ita da Aysha suna baya yusuf na tsakiyarsu ', cikin rad'a rad'a yake mata magana,

Please baby kizo partyn nan gobene"

No, bazan je ba?

"Why?

"Kawai.

"Ya Kalli Aysha "Please friend ki rok'e ta taje"

Aysha ta Kalli "Hafsah waike meye haka? 

"Hmm, Aysha baki ji, me basma tamin bane, nan ta d'an rad'a mata"

Aysha ta jinjina kai "Ok, kinsan basma, kiyi ahankali dai" "Ok" 

"Nima ta gayyaceni fa"

"Hafsah ta tab'e baki kawai"

Dai dai lokacin sunzo bakin gate, dake, a waje su Abba sukayi parking, har sun fita daga cikin makarantar su'

Yusuf ya d'aga mata hannu bye dear, naji dad'i yau sosai, kuma, zanzo gobe muje party"

"Please kada kazo dear kasan da akwai matsala... And please kada kaje party nan" 

Yai murmushi, 

"No baby dole ne wani yaje, because basma bazataji dad'i ba ke bakiyi attending ba nima haka"

"Hmm, ni dai bance kaje ba"

Sunzo daf da fita, saboda haka, ya d'aga mata hannu, 

Itama ta d'aga mishi "Bye bye dear "

Thank you aysha"..

Aysha ma ta mata bye bye"

'Ta tarar da su mama har sun shiga mota, itama ta shiga, tana fargarbar, 'Kada fa Yusuf yaje wannan partyn gashi babu, damar su tsaya suyi magana, sosai..'

Ta hango shi yana d'aga mata hannu, sanda motarsu ta hau kan kwalta'...














*HAJEEYAH KHAREEMERH*

 *CE*👌🏻

[1/11, 12:09 AM] Hajeeyah Karimah (Writer): ♥♥♥♥

*ZAZZAFAN SO*

(Guba ne)

*A broken*

*heart story* 

💔💔



Story and writing by:

*Karima Tijjani Mansur*

*(Hajeeyah Kareemerh)*

*Dedicated to:* *Unique In Love*

 *Heart Members*







📄 *27*




*Sun* isa gida cikin farin ciki, suna shigowa Mufida ta taso ta rungume Hafsah "Happy graduation yaya". 'Hafsah taji dad'i itama ta rungume ta "Thank you sisi na!"

'Mama ta shiga hidimar zuba musu abinci.. Yau girki na 'musamman' (special) akayi. 'Dama tayi shi tun kafin su tafi makarantar.'

'Bayan sun kammala ne, suka yi sallah, sannan kowa ya shiga yin tashi hidimar.

'Hafsah dai wanka ta shiga, bayan ta fito tayi kwalliya cikin sabuwar Atamfar 'Super Holland' tayi kyau sosai ko powder bata shafa ba.

Ta fito falo ta zauna shiru, shima d'in don kada Abba ya ganta babu walwala ne a cikin rana mai muhimmanci a wajenta irin wannan ya zargi wani abu.'

'Amma a b'adinin zuciyarta ('in side of her mind') abubuwane dank'are wad'anda suka sabbaba mata yin shiru.

'Na farko shine; Fargabar alak'ar dake tsakanin, basma da Yusuf, 'wacce irin mu,amalar girmama wa ce a tsakaninsu bayan, ta kasancewar basma k'awarta.. Da har zata sa Yusuf kasa k'in amsa gayyatar basma, bayan ita da take sanadin had'uwarsu tace bazata ba? 

'Na biyu shine kewar 'yan ajinsu da kuma bak'in cikin rashin samun hanyar yin waya da Yusuf. '

Sai na uku tunanin makomarta a wajen Abba.. 'Yanzu dai tayi candy, tana zuba idon ganin ''Shin zai bata 'yancin rik'e waya da kuma na tsayawa da saurayi''?

'Cikin wannan dogon tunanin ne taji kiran Abba d'aga d'akinshi.. Tayi saurin mik'ewa ta nufi d'akin.

'Da sallama ta shiga , yana zaune akan carpet ta tarar da shi, ta durk'usa sannan tace "Abba gani" ya sakar mata fuska, 'Fiye da koyaushe a kwanakinnan.' "Yauwa yaya, yanzu anyi candy koh? An zama yaya sosai" tayi murmushi ya mik'e ya nufi, k'ofar bed room d'in cikin d'akin, mintuna kad'an ya dawo da leda ahannu, ya zauna a wajen da ya tashi, sannan ya mik'a mata ledar yana fad'in, "To ga gift d'in Abba shima" ta mik'a hannu biyu ta karb'a tana godiya, Abba an gode Allah ya saka da alkhairi".. 

Ya amsa da "Amin yaya" sannan cikin nutsuwa yayi mata 'yar takaitacciyar nasiha.

("Hafsah yanzu kin girma fa, yanzu keya dace ki dinga tashin k'anne'nki su tafi makaranta ba ni ba ko mamanku." "Kuma kada ki ga kinyi candy ki sa wasa a ranki, yanzu lokacin da zaki fara karatu da kuma sanin rayuwa, saboda haka ki maida hankali don Allah, ki dinga addu,a kinji")

'Ta gyad'a kai "To Abba" 

"Yawwa Allah ya miki albarka ya bada result mekyau"

"Amin Abba" 

'Ya d'an nisa sannan yace,

"Ki bar batun party sai bayan exam ta fito za,a had'a miki babban party, kin ga sannan kin san matsayin jarrabawarki koh"?

'Ta gyad'a kai kawai'

Cikin nutsuwa ya sake ce mata,

"Yaya ayau naso in baki waya, amma na fasa, saboda dalilin da kema kin sanshi, amma zan duba na gani zuwa wani lokacin. 

Bataji dad'in hakan ba, amma yanzu, sai taji tabbas cewa laifinta ne'.

'Ta kasa koda gyad'a mishi kai ne'.

Ya kira sunanta "Hafsah!" 

Sai da ta amsa sannan yace yana nuna ta da yatsa'

"kada ki d'auka gama makarantar da kikayi ya baki damar yin magana da wani saurayi..ban baki wannan damar ba,.. Kada ki sake ki saurari wani, har sai kin turo shi ya ganni na mishi izini".. Kinji koh?

'Ta jinjina kai Eh" yauwa, to tashi kije'

'Sai taji duk jikinta ya d'anyi sanyi.

'Tana fita babban falo taji kiran mama,ta sameta a d'akinta, "Mama gani,"

Itama wani abu ta mik'a mata acikin wani d'an box akwati mai kyau, "Gashinan na happy graduation ne" taji dad'i sosai,

" Nagode mama" ta fad'a tana murmushi.

'Bed room d'in ta nufa, ta zauna kan gado, ta ajye kyaututan agefe, jinta take wata mai sa,ar iyaye, tabbas ta k'ara tabbatarwa kanta iyayenta na k'aunarta. Ta d'auki ledar Abba tana shirin bud'ewa, 'Mufida ta shigo da gudun, cikin wata 'Red gown' tayi kyau sosai, 

"Yaya ki fito falo,"

Hafsah ta zaro ido Menene? 

Tayi murmushi tana d'an rawa da k'afarta alamar a k'age take, ('She eager') 

"Surprise ne"

Hafsah ta mik'e.

Yaya ki chanja dressing, ta fad'a tana shigowa cikin d'akin sosai, ta bud'e drawer ta dakko wa Hafsah, wata T. Shirts purple sai wani wando light pink Hafsa tasa da sauri, tana son taje taga Menene'?

Tayi sauri tayi d'auri me kama da turban,  akanta da wani purple d'in d'ankwali, ta nufi wajen dressing mirror ta fesa turare, sannan suka fito.

Bashir, duk k'annenta ta gani, sai abokin bashir na'eem, sai wata k'awar Zainab dake a mak'otansu Nusaiba',

Tsaye suke sun kewaye table d'in dinning, sun d'ora cake akai.. Suna ganinta suka hau ihu happy graduation' suna tafi, ta shiga tsakiyarsu ta tsaya, suka yi photuna da wayar Mama, sannan aka fara irge "5..4..3..2..1.." Ita da Mufida suka rik'e wukar sannan suka yanka, sannan akashiga ci, ana b'ata fuska da cream, sai da suka gama sannan suka yi wasu photunan a wayar Abba, sai lokacin daf da magariba sannan suka gama, domin wak'a suka kunna a speaker na falo sukayi ta rawa isu-isu'

Hafsah yau farin cikinta babu misali, har ta manta da wani tunanin yusuf gaba-d'aya bayan sunyi sallah aka dora da kallo, ko bed room, d'inta bata shiga ba, sai wajen 11:00pm, kowa ya mik'e don yin bacci. 

Hafsah ta shiga toilet tayi wanka, ta saka rigar bacci sannan ta kwanta. A gajiye take sosai don haka ko takan gift en abba da Mama batabi,ba bare kuma wani tunanin Yusuf, bacci yai gaba da ita'.

Da safe ta tashi fresh babu wani tension sai bayan, sun karya ne, sannan ta dakko kyautukan nata.

'Na Abba ta fara bud'ewa, 'wani agogone mai kyau na mata, sai takalmi akwalinshi goalding color ya had'u, sai wani tsadadden turare.'

Taji d'adin kyautar sosai, tana murmushi ta bud'e box d'in Mama, wani zob'e ta gani mai kyau d'an k'arami. 

"Thank you my parents!!

Ta furta a fili.

'Da yamma tayi wanka cikin b'akar after dress da d'an mayafi, mama tace zata aikata wani gida cikin layinsu ta karb'o mata turaren wuta da Matar take siyarwa, ta fito ta nufi gate, aiko tana bud'ewa tayi gamo da Yusuf tsaye jikin motar shi, yayi kyau fiye da duk ranakun data tab'a ganinshi, ta dafe k'irjinta sanadiyyar bugawar da yake, shi kuma sai wani murmushi yake yi na farincikin ganinta cikin sauk'i. 

Cikin tsoro ta k'araso babu ko sallama bare sannu da zuwa ta fara mishi magana cikin tsoro, " Haba dear kafa san abba ya hana, yanzu ni aikena akayi".

Ta fara tafiya, gudun kada Tsautsayi yasa Abba ya gansu.

'Shima binta ya fara yi abaya, ta tsaya, sannan ta d'an juyo ta kalleshi, shi kuma ya hard'e hannayenshi a k'irji, 

"Please ka daina bina kaji, ka tafi"

"No, bazan tab'a tafi ba, zan raka ki ne"

Tayi shiru, sai kuma ta cigaba da tafiya, shi kuma ya cigaba da binta har zuwa gidan da zata.

Ta ca ke a k'ofar gidan, shima ya tsaya yana fuskartata, ahankali ta fara magana.

"Dear please Meyasa kazo?

"Hmm, baby ko welcoming nawa biki yi ba kin namin abu kamar baki son ganina koh"?

Tayi shiru, sai taga rashin kyautawarta'

Atak'aice tace "Am sorry you're welcome dear, please ka daina cewa bana farinciki da ganinka,.. Kawai ina tsoron Abba ne, yanzu ma Allah ne ya sa mama ta aikeni, da aikawa zakayi kirani koh? Ya jingina kanshi yana murmushi "Of course"

Ta sauke ajiyar zuciya, Ok"

Suka d'anyi shiru sannan yace am baby nazo ne muje party kinga nan da one hour ne za,a fara."

Ta d'ago ido ta kalleshi suka had'a ido ya kashe mata ido da'ya.

Ta girgiza kai baby nace maka bazan je ba fa".. Kuma nace kada kaje kaima please,"

"Hmm, Meyasa?

Kawai bana son kaje, ta fad'a tana d'an had'e rai"

Yai dariya, "Haha ke dai kada kije, amma, ni zanje"

Sai taji maganar ta b'ata mata rai'

Ta jinjina kai,

"Ok thank you"

Ta shige cikin gidan ta barshi tsaye'


_'Ni ko nace Hafsah dama Yusuf na yin laifi'_🤔😅



'Tayi sallama sanan ta shiga cikin falon gidan, bayan sun gaisa da matar, ta bata sak'on sannan ta fito.. Yana tsaye har lokacin, yana ganinta ya nufota "please baby, kizo muje." 

Ta yi mishi wani kallon tuhuma "No bazan je ba, ka wuce kawai"

Yai ajiyar zuciya "Hmm, ok,"

Ta fara tafiya, shikuma ya biyota don dakko motarshi dake k'ofar gidan su'

Ta juyo ta d'an tsaya ta kalleshi, sai b'acin ranta ya k'aru, taga ya mata kyau sosai, to meye na dole sai yaje wannan party?

Cikin b'acin rai tace mishi, tunda kace sai kaje, to kaje d'in, kuma kada ka min magana a hanya'.. Sannan na gode da abinda kayi min."

Ta na kaiwa nan tayi saurin wucewa ta barshi.

"Hafsah..baby.."!!

Yai ta kiranta amma taki koda juyowa, bashi da zab'i illa ya bita a baya.

'Tafiyar kurame sukayi har zuwa gidan su Hafsa. Ya tare mata hanyar shiga ita kuma ta tsaya cikin fushi da kuma tsoro tana kallonshi, cikin nutsuwa yace,

"Am sorry baby, kiyi ha'kuri don Allah".. Basma is important to us, ki bari naje please"

Takaici ya rufeta, ta d'aga mishi kai, kawai, wanne irin hali ne dashi, tana nuna mishi bata son abu amma shi kuma ya dage yana wani nuna mata important'

Ya d'an matsa mata ta rab'a cikin gate d'in, ya kirata a hankali "baby"

Ta kalleshi da ido kawai, ahankali yace "Bye Bye"

"I love you" sannan mata sassanyan murmushi wanda ya tsaya mata a rai har taji ya sakko mata da k'wallar kewa da kuma kishi'.

Ta d'aga mishi hannu kawai duk da tana jin zafin shi shima ya d'aga mata suka d'an b'ata lokacin kallon juna, sannan tunanin kada Abba ya zo ya ganta, ya fargar da ita ta wuce ciki babu shiri.

Shi kuma ya shige cikin motarshi cike da nishadi'..




*Hajeeyah Kareemerh ce*

👏🏼👏🏼👏🏼

[1/11, 12:09 AM] Hajeeyah Karimah (Writer): ♥♥♥♥

*ZAZZAFAN SO*

  (Guba ne)

*A broken*

*heart story*

  💔💔




Story and writing by:

*Karima Tijjani Mansur*

*(Hajeeyah Kareemerh)*

*Dedicated to: Unique In Love Heart Members*

*Much of love to you:*💘💘💘💘💘

*"My Namecy ina yinki irin sosai d'innan fa,(KARIMA TIJJANI ADAM")* *Kina k'aunar wannan novel.. Allah ya kawo mj na gari musha biki..* 💃🏼💃🏼💃🏼💃🏼








📄 *28*







*Ba* wajen partyn Ya nufa Kai tsaye ba. Don sai k'arfe 7:00pm za,a fara. 'Dama yazo ne da niyyar idan yazo su d'an fita shak'atawa daga nan sai su wuce wajen partyn.'

'Sai daya gama yawonshi, sannan ya nufi wajen partyn, gefe guda kuma da kewar Hafsah zuciyarshi. 'Yana jin dama da ita zasu je.'

'Hall (D'akin taro) ne mai d'an girma, wanda yasha decoration, an sanya kujeru da table aciki. Ya tsaru kuma yayi kyau sosai.

'Yawancin wad'anda suka halarci taron, matasa ne, maza da 'yan mata.. Anyi shigar peach colour da blue, sunyi kyau sosai.

'Anata surutu, ga kuma kid'a da yake tashi na slow music. 'Har zuwa lokacin da ita uwar gayyar ta iso, ita da wata k'awarta 'Jalilah'.. 

'Daf da zasu shigo cikin hall d'in ne, aka tsaya da kid'a, sannan 'MC' ya sanar da isowarta.

'she's coming, she's approaching, she's around the corner.. The big girl all over this hall.. 'Akayi tafi.. Sanan ya d'ora..

"I mean the one whose today is her day.. whose every one attended this party in honour of her... "Basma Yunus is coming...

'Akad'auki ihu da tafi.



'Ta had'u sosai doguwar wasu riga da (gown) wanda aka yi mata wata katuwar tsaga har zuwa guiwa, tayi kitson attach, tasha kwalliya sosai tasa dogon takalmi, suna rik'e da hannun juna ita da k'awartata da tasha wani makeken bak'in glass a fuskarta..

'Takowa suke cikin yauk'i da k'warewa, lokacin kuma, DJ ya saka musu Wak'ar 'Romantic' ta ('Korede Bello') har suka isa wurin da aka tanada domin zamansu..

'Daga nan ne kuma aka fara, gabatar da komai, ancashe sosai, inda Yusuf ma ba,abarshi a baya ba. Ansha rawa sosai.. Sannan aka nemi da ayanka cake, Mc ya fara sanarwa cewa, 'Hafsah itace zata taya Basma yanka cake'. Sunanta yasha kira a wajen, a matsayin best friend d'in Basma' (wannan tsarin Basma ne) 

Shiru babu Hafsah.'

'Mc ya bud'e murya yana cewa, 'muna bada hak'uri bisa ita wadda ake magana, bata k'araso ba..

'Yusuf ya mik'e cikin takunshi na kwarewa, ya nufi wajen Mc, ya mishi rad'a a kunne. Sannan Mc ya maida speaker abaki ya fara magana cikin k'arad'i.

"Am tabbas naji

dad'i kuma wannan shi ake kira da 'True Love'.. 'Don Allah atafa mishi, nan aka hau tafi akan abinda basu san ma me akayi ba.' ('Duk cikin turanci ake magana')

'Bayan tafin ya lafa ne, Mc ya fara yi wa yusuf tambaya, kamar haka' (ya kara mishi loud speaker')

'What's your name'?

My name is Yusuf 'Bashir Imam'.. 

You're...??

Hafsah's

Boy friend.. Yusuf d'in ya amsa,

Nan guri ya cakud'e da tafi.. Da ihu.. Mc ya cigaba, " you came to.. ??"Represent my girlfriend who's the Basma's best friend."

Yusuf ya kuma bada amsa, nan aka hau tafi.. 

'Mc yace ' wato dai uzuri ya tare wannan k'awa ta basma saboda haka ta turo jaruminta, domin ya wakilceta, "kaii don Allah atafa mata.. Aka d'auki tafi babu k'ak'kautawa, fiye da minti biyu sannan akayi tsit kuma. A lokacin aka kuma gayyato wasu k'awayen basma su biyu, d'aya gefen Yusuf d'aya kuma gefen da Basma take.. Basma ce ta rik'e wuk'ar sai tattausan hannun Yusuf akan nata wanda hakan ya k'ara mata jin nishad'in taron. Sai kuma hannayen sauran k'awayen nata..

'Aka fara k'irge 1,..2,..3,..4,..5, sanan aka yanka cake en🎂 wanda aka rubuta 'HAPPY BIRTHDAY BASMA'

'Suna gamawa aka kuma rud'ewa da ihu da tafi, inda DJ ya saki Wak'ar 'Happy birthday to you..' Yusuf ya yanki' wani madaidaicin cake ya saka mata abaki.. 'Aka hau yi musu tafi.. Daga nan nan aka cigaba da shagali, aka cashe sosai. Yayin da Yusuf ya fita domin d'akko gift d'in da zai bayar daga motar shi.

'Bayan an tsagaita da rawar, ne aka fara gabatar da gift ga Basma.

'Ta samu kyautaka da yawa tun daga kan greeting cards, zobuna, agogoba, da sauransu, bayan kowa ya gabatar da nashi ne, aka nemi Yusuf daya gabatar da nashi. Gurin yayi tsit ana zuba idon me zai bayar...

'Suna tsaye shida ita suna fuskantar juna, yayin da idanuwan kowa ke kansu sai mai camera dake aikin d'aukarsu, sai kuma wasu daga cikin mutane dake faman d'auka a wayoyin su.'

'Mc ya juya ga Yusuf ya kara mishi abin magana, sannan yace, "Your words to Basma".. 

'Cikin muryarshi mai d'adin sauraro da turancin shi, 'wanda ya kasance irin na 'yan asalin yaren, 'yace: 

"Happy birthday,.. Wish you long life and prosperity'.. Happy birthday once again our friend... 

'Taf Taf, aka d'auki tafi..'

'Sannan ya mik'a mata wani greeting cards da aka rubuta,


_'On your birthday I wish you much pleasure and joy;_

_I hope all of your wishes come true.._

_May each hour and minute be filled with delight,.._

_And your birthday be perfect for you'!_

_'Happy birthday to you'.._


'Basma ta sa hannu biyu ta amsa, tana murmushi, sannan..ya ciro wani akwatun zobe sai walk'iya yake, daga aljihunshi ya mik'a mata, shima ta amsa, akayi musu tafi, ahankali yace mata 'This is from Hafsa' .. Sai Basma taji wani abu ya tsarga mata a zuciyarta mai kama da kishi..

'Kafin k'wak'warta ta dawo dai dai, tafin daya karad'e cikin Hall d'in ya fargar da ita, ta mayar da hankalinta kan Yusuf dake, mik'o mata kwalin wayar 'iPhone' ta zaro ido sosai babu shiri ta amsa cike da tsakanin farinciki, wanda kafin Yusuf ya farga ta rungume shi cikin nuna jin dad'inta.. Nan kallo ya koma kansu, kowa a wajen da abinda ya ke sak'awa, wasu na ganin ta burgesu, inda wasu ke ganin abin 'ban-barakwai', 'tunda wai shi d'in ba sunan saurayin basman yake amsawa ba, (Saurayin k'awarta ne') tambayar anan shine wane irin k'awance suke??...

'Tunda jikin su ya had'u, kowannensu tunane tunane suka had'arwa zuciyarsa..

'Ita Basma jinta tayi cikin wata duniya, da har ta manta gaban jama,ah suke.. Sanan tanajin aranta ta kusa samun Yusuf koda kuwa ta wannan hanyar ce!

'Shiko Yusuf abinda zuciyarshi take karanta mishi shine, 'wannan abin ne kawai ya rasa a wajen Hafsah, amma gashi a karon banza wata dake amsa sunan k'awarta tayi mishi, wai kawai don nuna jin d'adin kyautar daya mata, kuma a gaban jama,ah babu tsoron komai..? Kawai sai zuciyarshi ta shiga kokonton anya ma kuwa Hafsah na sonshi'..

'Sai ya fara kushe tarban da ta mishi ranar 'Graduation' d'inta. Domin tun ranar ya zaci samun haka daga gareta, idan ya mata kyautar bajinta, wacce ke cikin ledar daya bata. 

'Niko nace, 'Yusuf ba sai idan hafsan, tama San meke ciki ba!'..🤔

'Tafin ya tsagaita yayin da Basma ta sakeshi a hankali, anan ne kuma aka saka musu Wak'ar da zasu cashe shi da ita, sunyi rawa sosai irin wadda ransu keso, kuma yanayin wayewarsu ta yarda da ita..

'Daga k'arshe dai, taro yayi wa kowa dad'i aka tashi ana nishadi kamar kada a tashi, wajen k'arfe tara na dare, sanan aka watse, sai 'yan tsirarun k'awayen Basma sai Yusuf da wad'anda baza,a rasa ba. An tattara komai na gift d'in driver daya kawo basma ya tafi dasu zuwa gida.. Yusuf ya d'an ya fitota suka d'an keb'e, ya fara bata hak'urin rashin halarta hafsah, har yana mata k'aryar cewa Mamanta ce babu lafiya. Basma ta d'an rage fara,arta da taji zancen Hafsah, abinda bai sani ba shine ita ai dama haka take so,' ta d'an daure tace mishi "Ok no problem'.. Ya d'aga mata kai sannan yace "shi zai tafi,"

ta kur'a mishi ido, 'Wanda shi kuma yayi mamakin kallon, har mamakin ya bayyana akan fuskanshi, sai ta kama kanta..

'Babu kunya tace mishi to su wuce mana, ya sauke su ita da k'awayenta tunda drivernta ya tafi yace mata..

"No problem"

'Suna tafiya cikin sassanyar motar tashi wanda sanyin AC ya sanyaya ga daddad'an k'amshi. Yanayin yana wa basma dad'i sosai, ji take bata tab'a yin irin wannan farin cikin ba tun da take a duniya.. Komai yanda ta so yakasance a birthday d'in haka ya kasance, 'dama cikas d'in shine zuwan Hafsah , kuma cikin sa,a bata zo ba.'

'Ita ce agaban motar sai kuma k'awayenta uku a baya, guda d'aya ce 'yar makarantar su wato 'Aysha daheer' wacce gulma ta sa ita ma ta tsaya har aka tashi, don so take ta kaiwa Hafsah cikakken bayani tun daga farko har k'arshe.. Shiyasa tana ganin su basma sun shiga motar Yusuf itama ta biyosu ta danna kai ciki, tace itama a sauke ta, tunda duka hanya ne'. Da yanayin Basma aysha, ta gane bataji dad'in hakan ba, amma ta share domin ganinta ba zai hana ta cika manufarta ba ayau.' Hakan basma ta sa aranta.

'Slow music ne ke tashi, sai hira jefi jefi da k'awayen basma na kusa da Aysha keyi wanda ko kallon juna basu yi ba, kasancewar babu sanayya a tsakaninsu sannan kuma kowa naji da kanta.. Aysha ta d'akko wayarta tana dannawa, amma ta kasa kunnenta sosai don jiyo abinda basma ke fad'a wa Yusuf.'

'Shi dai tuk'inshi kawai yake domin sauri ma yake ya je gida ya fara shirin zuwa club, domin zuwanshi gurin partyn nan da kuma abinda basman tai mishi ya saka mishi son halartar club d'in, ko ya samu wacce zasu jone, a daren.

'Cikin kashe murya Basma ta fara mishi magana, idonta na kan hannunshi dake tuk'i... Gaskiya na gode sosai fa' hankalinshi na kan titi ya bata amsa, "Kada ki damu aike, k'awan Hafsah ce"

Sai ta ji d`acin maganar aranta wato shi komai sai ya sako Hafsah aciki?.. Sai ta chanja hirar da cewa, "Gaskiya ka iya driving sosai. Yai murmushi sannan ya ce "Thank You"

Tayi wani fari wanda shi baima lura ba, sannan tace "Hmm, am yanzu ne kam dai dai time en da daddy na yace nima zan koyi driving" 

Yace "Is good" ba tare da koda ya kalleta ban, domin shi baya buk'atar surutu a lokacin.. Don idan yana tuk'i baya son a mishi magana.. 

Ita dai Aysha idonta na kansu, yadda zata fi fad'awa Hafsah komai dai dai..

'Tayi mamakinshi shi da basman. Hira basman ta dinga d'an janshi da ita wanda ya k'ara bayyana mishi tabbas ita ce tsarin rayuwarsu yazo d'aya, wato hirar club da sauransu.

A'haka aka iso inda Aysha zata sauka ta musu godiya ta wuce cike da mamakin abubuwan.



'Sai da suka sauke kowa sannan yusuf ya kai basman gidan mamanta, wai sai ta buk'aci ya shigo su gaisa, da yaki' ya nuna mata yana sauri ne, amma ko me ya tuna oho sai ya wuce suka shiga'

'Wata hamshakiyar mace ya gani taci ado sosai ta hakimce akan kujerar falon, suna shiga Basma ta fad'a jikin ta, "Mummy wallahi duk na gaji fa!"

'Matar tayi murmushi "oh sorry baby ai kece kun ja abin da yawa. Ta maido da kallonta kan yusuf dake zaune shima yana kallonsu yana murmushi, "mum good evening" how are you? "Am Fine, how's family" they're fine. Gud'

Ahaka sukayi gaisuwar tasu, sannan ya mik'e tare da cewa "Gud night" 

'Ta sakar mishi fuska sosai tana cewa "Ok bye bye ka gaida Mum"..

'Ita dai fa sun gaisa ne kawai, amma bata san alak'ar su da Basma ba, amma taji aranta yayi mata, kuma duk da bata barin 'yarta kula samari to tabbas zata iya barinta dashi domin daga ganinshi d'an manya ne'..

'Basma ta mik'e ta bishi sukayi sallama, wannan karon har da rik'e hannunshi su gaisa, ya tsaya shiru hannunshi cikin nata yana nazarinta sosai, tuni wani abu ya tsarga mishi cikin zuciya, ya zare hannunshi tare da yi mata murmushi, ya d'aga mata hannu alamar bye-bye ta tsaya har ya shiga mota tana kallonshi, ta saki ajiyar zuciya a hankali tana fatan Allah yasa sak'onnin data aika mishi ayau sun isa, kuma zasuyi tasiri yadda take so...

😇Muje zuwa dai..👍🏻👍🏻

*Hajeeyah Kareemerh*🍒

[1/11, 12:09 AM] Hajeeyah Karimah (Writer): ♥♥♥♥

*ZAZZAFAN SO*

  (Guba ne)

*A broken*

*heart story*

 💔💔




Story and writing by:

*Karima Tijjani Mansur*

*(Hajeeyah Kareemerh)*

*Dedicated to: Unique In Love Heart Members*







📄 *29*



*Lokacin* da Yusuf ya bar Hafsah kuwa tunda ta shiga gida jikin ta yayi sanyi, kawai sai taji tana buk'atar kad'aici.

'So take kawai ta keb'e tayi kuka, amma tana shiga gida bayan ta bawa mama sak'on ta juya da nufin wucewa d'aki, Maman ta kirawota, hakan yasa tayi saurin saita yanayinta ta dawo ta zauna, Maman ta kalleta cikin ido, sannan tace, "Ki je ki d'ora mana abinci kinji." Babu yadda ta iya haka ta mik'e ta nufi kitchen d'in, gabanta sai fad'uwa yake haka kawai takejin zafin Yusuf, saboda kafewa da yayi sai yaje Birthday d'in.. Sai wajen ana kiran magriba ta kammala, sannan tayi sallah, lokacin kuma Abba ya dawo, hakan ya tilasta mata fitowa falo ta zauna don ta lura baya son ganinta cikin d'aki idan ba lokacin bacci ba.'

'A dining sukayi dinner d'in, sannan 'Abba yace ayi musu tatsuniya, yana murmushi yace "Mama ce yau zata fara yi musu."

_('Abbansu Hafsah yana da wani ra,ayi: 'Wato ba koyaushe yake barin su kalli TV ba')_


Maman tayi dariya, sannan fara yi musu, ta tsuniyar "Na goma" duk sun nutsu suna sauraronta, har da Hafsan itama, sai da ta gama, Abba yace Hafsah tayi musu, tayi d'an murmushin kan leb'e, sannan tace, "Abba bashir yayi mana, ni sai na tuno wacce zanyi"

'Dukansu suka hau yi mata dariya, suna tsokanarta wai ta kasa.'

'Ita kuwa d'adi taji don sam batajin yin magana mai tsawo ko sauraron wani dogon zance a lokacin, sai da suka gama lokacin kuma baifi k'arfe takwas ba sannan Abba ya kunna musu 'Solar' kasancewar babu wuta, sannan suka saka wani tsohon film d'in ',(Home alone') suna kalla cikin nishad'i, hakan yasa hafsah taji d'adi sosai ta mik'e, 'Abba ya bita da kallo, sai ta kawo mishi uzurin cewa bacci take ji'

'Ya jinjina kai, sannan yace "Shikenan, kiyi addu,a," ya Kalli mama, ita ma ta kalleshi, itama ta karanta mishi nata mamakin', Na baccin da hafsah tace tanaji, a irin lokacin k'arfe takwas baifi da rabi ba'.. 'Abinda yaran sai k'arfe tara da rabi ko goma suke bacci, shima sai Abban ya kora su, saboda makaranta.'

'Hafsa ta kwanta shiru, ta takurawa zuciyarta kan dole sai ta gano, abin da ke tsakanin Yusuf da Basma.. Da har ya sashi kafewa kan zuwa birthday d'in don kada ran Basma ya b'aci.' Yadda zuciyarta ta karanta mata kenan..'

'Abubuwa da yawa zuciyarta tayi ta karanto mata wanda ita kuma gefe guda tayi ta k'okarin sai ta k'aryata hakan, don kada ta jawo wa kanta tarwatsewar farin ciki babu shiri'

'Da farko kawai ta sa wa ranta, Basma tace wa Yusuf 'Tana Sonshi ne..

'Sai kuma ta tuna a irin class na basma tana fad'ar cewa ita babu namijin daya isa tace tana sonshi'.. Sai ta sauya tunanin da cewa ' kodai kawai son kula maza ne da iyayi irin na basma yake jan hankalin Yusuf d'in zuwa ga kulata, ??

'Kishi ya baibayeta Wani b'angaren kuma na zuciyarta ya shiga rarrashinta, da nuna mata sam fa wannan tunanin ba haka bane, 'Idan ta lura da irin kallon da yusuf yayi wa basma ranar da suka fara had'uwa, sai kuma d'inbin soyyayyarta (ita Hafsan) da ke dank'are cikin zuciyarshi, wacce bata da kokontonta, idan ba lokacin da ta shiga rudu, irin wannan ba'..

'Da taga dai, ta rasa abin kamawa, sai kawai ta bari kalmomin Yusuf sukayi tasiri, itama zuciyar ta ta ta,allak'a abin da, 'Ganin kirkin basma da Yusuf d'in keyi, kamar yadda ya fad'a mata, wanda kuma hakan sanadinta ne ita Hafsan.'..

'Ta saki nannauyar ajiyar zuciya, sai lokacin taji dama-dama, sai kuma ta shiga nemawa zuciyarta hujjar da zata k'ara yarda da hakan.' sai tunaninta yakai kan ranar da yusuf d'in ya turowa Aysha katin 2000' wanda shima fa kawai albarkacinta taci don kawai, suna waya da wayarta.'

'Ahankali taji zuciyarta na hak'ura da lamarin har taji tausayin Yusuf d'in bisa mummunar fahimtar datayi mishi, take taji zuciyarta ta k'ara kamuwa da sonshi, taji kawai babu abinda take son ji sai muryarshi. Amma ina babu dama, hakan yasa ta tsunduma tunanin yadda suka rabu d'azu tana k'ara halarto irin kyan da ga yayi yau d'in... 

'Ahakan har tayi bacci'

'Washe garin ranar Yusuf na kwance a d'akinshi da daddare, yaji kira ciki wayarshi, ya duba yaga basma ce, ya d'aga kiran tare da kai wayar kunnanshi. "Hello"

Takai k'arshe wajen kashe muryarta wacce ta yi tasiri sosai a kunnuwanshi tace, "Hi, ya kake"? Am fine" "Ok gud, ya gajiyar birthday yai dariya, "Hah babu gajiya kuke cewa koh"?

'Itama tayi dariya "Oh Na manta fa you're Californian.!" suka k'ara yin dariya, sannan ta mayar da muryarta kalar ta tausayi, kamar mai yin kuka tace, "Yusuf,..

"Na,am." shima ya amsa cikin taushin murya' 

'Sai kawai ta saki kuka, hankalinshi ya tashi, ya rud'e ya hau rarrashinta, bai san ma me yake fad'a mata ba.'

"Am sorry baby, kiyi ha'kuri please calm down, ki fad'a 

min make faruwa waya tab'a ki ko Hafsah wani abu ya faru"?

Sai da tayi kukan sosai sannan ta saita muryarta cikin shashshek'a ta fara magana, wanda shi yanayin muryar ya d'auki hankalin shi'

"Am na rasa wa zan fad'a wa, damuwata sai kai,.. Cikin nutsuwa yace "Mata ina jinki" tayi ajiyar zuciya sanan ta cigaba," 

'Saurayina ne kawai don kazo birthday kuma yaga yadda kayi treating ena shine yace wai ya rabu dani!! Ta k'arashe maganar cikin kuka"..

Yusuf yayi shiru, yama rasa me zaice, tausayin basma ya rufe shi, cikin in, ina ya faro magana, " Um, d.. Do youu mean kun rabu kenan"??

"Of course".. Ta fad'a tare da k'ara rushewa da kuka..' "Oh my God"!

Yusuf ya fad'a, to Meyasa? A wanne dalilin, wato kishi yake da shi kenan,?? Yama rasa me zaice, sai kawai ya b'ige da rarrashinta "please kiyi ha'kuri, kada ki damu, I know it will hurt, but kiyi ha'kuri in sha Allah zaku sasanta kinji..'

'Zuciyarta ta dugun zuma, ita ba haka tasoji ba, amma sai ta kanne kawai, tace mishi, " I told you mun rabu kuma bana jin zamu k'ara yin wata soyayya ni da shi, so just pray for me 'Allah ya bani wanda ya fishi'

'Ya sauke ajiyar zuciya tare da cewa, "Amin."

Sai kuma ya shiga yi mata 'yar hira, yana kod'a kyan datayi a ranar birthday d'in 

Duk a k'okarinshi,

na ganin ya kwantar mata da hankali, domin ji yake, shine sanadin tarwatsewar farincikin ta, ita kuma abin nema ne yasamu, taji dad'in hakan sosai.'

'Da k'yar sukayi sallama.'

'Wai ko anya zancen Basma gaskiya t

ne??

'A gaskiyar zancen dai, shine, basma bata gayyaci manyan samarinta, wad'anda tasan zasu ji haushin ganinta da yusuf ba,..Amma da gaske ne tayi fad'a da wani saurayinta amma shima d'in kawai na rage zafi ne, baza,a kirashi da saurayinta na sosai ba, shine ta fa ke da hakan ta d'ora kukan makircinta akai, buk'atar ta kawai Yusuf ya tausaya mata, tana son tausayinshi yayi tasiri akanta, wanda shine zai zama mabud'in cimma dukkan manufarta, kuma gashi cikin sa,a ta sami hakan.'

'Domin ita tayarda da cewa, tausayi shike jawo soyayya..'!

'Basma ta kwanta har da burgima don murna, tabbas ta juyo k'amshin nasara.'

'Ana cikin haka kira ya shigo cikin wayarta tana dubawa tayi tsaki sanan ta d'aga.

"Hello basma iam Aysha d'aheer" 

"Ok, so ya kike"? 

"Lafiya lau"

'Suka d'anyi shiru sannan Aysha tace,

"Basma Yunus Manyan gari,"

"Hmm, basman tace cikin rashin kulawa, domin tun ranar birthday d'inta taji ta tsani Ayshan, saboda gani take kamar munafurci ne ya kawota.. Hafsah

ce ta turo ta donta kaimata munafurcin abinda ya faru kawai.'

'Amma dake ance bariki iyawa ne sai, ayshan ta chanja salonta, ta gyara muryarta tace,

'Gaskiya Basma, kin burgeni ranar nan fa, sai ranar na tabbatar H.Hamid jaka ce' 

Basma ta shek'e da dariya,

'Aysha ta cigaba, wato in banda hauka irin nata, ko yaushe zaki bari number Saurayinki a wayar k'awayenki?? 'Sannan kuma Kalli yadda don k'auyanci ta ki zuwa birthday d'in ta barshi shi kad'ai yazo, Basma tace "Hmm.'' So take ta gano inda Aysha ta nufa, Don tana tsoron kada dai bugar cikinta takeyi.'.. Amma hankalinta ya kwanta da taji Ayshan tace, "Ni wallahi ma sam gayen bai wani dace da ita ba, bafa type enshi bace."

'Sukayi dariya sosai ita da Basman, har Basman ta samu damar cewa, "Kema dai kya fad'a Aysha'.. "Hmm ai wallahi sam babu colour, yarinyar da babu inda take zuwa!!"

'Anan basma ta saki jiki sukayi hira, sosai da zata fad'awa Ayshan wayar da sukayi da Yusuf d'azu, amma sai ta fasa, suka kashe waya, Basma na farin ciki ta samu wata mai bata shawara akan al,amarin...


🤥 *Sabon salo*



.

*Khareemerh tijjani Mansur (Hajeeyah Kareemerh*

[1/11, 12:09 AM] Hajeeyah Karimah (Writer): ♥♥♥♥

*ZAZZAFAN SO*

  (Guba ne)

*A broken*

*heart story*

 💔💔


Story and writing by:

*Karima Tijjani Mansur* 

*(Hajeeyah Kareemerh)*

*Dedicated to: Unique In Love Heart Members*





📄 *30*







*Kimamin* sati d'aya kenan dayin birthday d'in, Basma, kullum Hafash zuba idon ganin Yusuf take yi, amma shiru.'

'Duk da tasan ita take hana shi zuwa, amma sai zuciyarta ta fara raya mata 'kodai ya manta da ita ne'? ('Zuciya kenan')

'Ita a yadda tayi kewarshi batak'i yazo d'in ba, idan yaso sai, tace wa Abba, 'Zuwa yayi ya amsa kiran da yayi mishi'...😅😅

'B'angaren su Basma kuwa, abu yayi nisa ita da Yusuf, kullum sai sunyi waya, kuma Basman ce ke kiranshi, shi kuma baya k'in d'aga wa

'Yau da sukayi waya ne, take tambayar shi, 'Wai shin yau zaije club ne? Yace mata bashi da niyya, amma idan zataje shima zaije, taji dad'in hakan da yace, 'wato idan hakane tana iya samun alfarma kenan a wajenshi?..

'To kwa tabbas zata gwada sa,arta.'

'Aranar da suka had'u a club d'in bayan sunsha rawa sosai, basma ta nemi dasu k'ebe tana so su tattauna, ya rik'o hannunta, ('Wanda zuwa lokacin k'aramin abune a wajen su su rik'e hannun juna') suka fito daga cikin hayaniyar zuwa harabar wajen inda aka ajye kujeru domin zama.'

'Kafin ta fara magana ya riga ta, don shima d'in yana da abin cewar da yake ganin bazai iya hak'uri har ta fad'i nata ba.' 

"Please basma help me" ta kalleshi da mamaki, "With what? 

'Ya marairaice please ki daure kije gidansu Hafsah, ki bata wayanki ina so muyi magana ne please"!

'Take yanayinta ya chanja wanda shima sai da yaga hakan, har ya karanta mata alamun tambaya a fuskarshi, sai tayi saurin wayancewa ta k'irkiro murmushin dole ta d'ora akan fuskarta.'

'Hmm, banyi maka promise ba, but zanje cikin satin nan. 'Yai ajiyar zuciya tare da ce mata "please basma help me, kinji,' na kuma bata waya ne, so i think Abbansu ya kuma k'wace wa.'" ta d'an cije lebe sannan ta daure tace mishi, "Ok don't worry"

Yai murmushi sannan yace, "Thank you"

'Ya kuma tattaro hankalinshi gurinta, sannan yace, "What about yours?

'Tayi wani murmushi sannan ta gyara zamanta tace cikin wata marainiyar murya,

"Nawa yana da wahala, bana jin zaka yarda."

'Ya girgiza mata kai had'i da cewa, "No, please tell me, zanyi miki kinji"

'Sai lokacin ta sami k'warin guiwar fad'amishi abinda ke ranta.'

"Um, tun lokacin da muka rabu da ex ena, yake min abubuwan da banjin d'ad'i, yana min maganganu a status, sannan yace wai ban isa na sami saurayi wanda ya kaishi ba, so ina son in nuna mishi k'arya yakeyi..' Tayi shiru data zo nan a zancen, yayin da shikuma ya bata duk hankalinshi, da yaji tayi shiru, yai mata alamar, 'Yana sauraronta ta, ta cigaba.'

"So please ina so ne ka dinga acting like you're my boyfriend.."

"What? Ya fad'a yana girgiza mata kai,

"No, I can't, am not like that, please am sorry to say 'bazan iya ba!"

'Basma ta d'ora mishi ido ta kasa d'aukewa, daman tasan hakan zai iya faruwa.'

'Sai ta shiga kawo mishi hujjoji marasa tushe, yadda zata gamsar dashi har ya yarda.'

"Am sorry if I hurt you, but ina cikin wani hali wallahi, nasan kuma Hafsah Kake tunani, to ka daina, I have an assurance that 'bazamu sami sab'ani da ita ba, ta fahimceni, kuma nima zanyi mata bayani, please help me"..

'Yai ajiyar zuciya, sannan ya fara magana cikin nutsuwa, "I can't gaskiya, kinga bani son in sami matsala ni da hafsah, 'sannan ex enki ina baki shawaran ki cancel duk wani abu da yake connecting enki dashi, kuma ki zuba shi a dustbin, ki daina damuwa da zancen shi, kawai, that's my advice"

'Tayi shiru, batason ta nuna nacinta a wajen shi, sai ta share kawai tace "Ok thank you, my friend" yai murmushi sannan ya maimaita

"Your friend"?

Ta d'aga mishi gira, "Yes, as your girlfriend's friend so we are friends" isn't it? 

Yai murmushi that's true"

'Sannan ya kuma mik'a mata rok'on shi, da ya tabbatar mata cewa ya damu sosai "So please yaushe zaki je gidan"?

ita ko lokacin haushin shi, takeji ma, amma sai ta kanne tace " zan tambayi mum enmu, kuma yanzu yawanci bata gida ita Hafsan, so banso inje bata nan"

"Please kiyi k'ok'ari kinji"

Ataik'aice tace "Ok"

Yai murmushi sosai "Thank you"

'To basma tana iya k'ok'arinta wajen yin, duk abinda tasan idan tayi zata ja ra,ayin Yusuf, misali 'Yanzu suna yawan had'uwa a gurare da yawa irin na shak'atawa, saboda haka duk inda ta sami dama tana k'okarin ta nuna mishi tabbas, ita ba irin hafsah bace, a fannin wayewa.'

'Takan mik'a mishi hannu su gaisa aduk sanda suka had'u, sannan idan hira ta had'asu tana k'ok'arin nuna mishi cewa ita fa tana cikin 'kewa'..

'Shi kuma har yanzu ya kasa fahimtar manufarta..

'Amma shima a nashi b'angaren akwai wani b'ahagon tunani a cikin zuciyarshi..

Amma da yake ance so sone, amma son Kai yafi, Yusuf, sai kawai ya yardarwa kanshi abinda zuciyarshi ta dad'e tana karanta mishi.'

A ganinshi sam baza,a kira hakan da yaudara ko cin amana ba.'

'Yanzu, 'kwance yake a d'akin shi, gaba d'aya yau babuy kowa acikin gidan nasu, shi kad'aine.'

'Ji yake komai yayi mishi zafi, har yake jin abin yau yafi na kullum.' ya tuno rabonshi da hakan tun yana makaranta, sai abinda ba,a rasa ba, kuma, ba wai rasa 'yan matan yayi ba, amma shi kawai yafi son 'yan matan can k'asar bawai na nan ba.'

'Hafsah ce kawai yaji yana so, kuma yaji zai ta dace da shi.' 'Shine ma dalilin da yasa, har ya d'auki wannan lokacin, wai yana jiran ta yarda dashi ne, to kuma yaga bata da niyyar hakan.. Gashi su 'yan matan nasa nacan, sunyi nisa dashi, sai dai a waya, kawai, shi kuma hakan sam baya wadatar dashi.'

'Yai shiru, yana tunanin abinyi, basma ce ta fad'o ranshi, yayi saurin d'aukar wayarshi ya danna kiranta, tana ganin shine ta share don zatonta zancen Hafsah zai mata, har ta tsinke, sai a kira na uku ne ta d'auka, yanayin da taji muryarshi, tasan akwai magana, a d'an sama-sama suka gaisa, tana shirin tambayar shi, make damunshi' ya riga ta, 

"Please basma kina gida ne?"

Tace mishi, 'Eh" 

"Please kizo gidanmu yanzu,"?.cikin mamaki tace gidanku, kuma"? 

"Yes, please ina son muyi magana ne"

Ta d'anyi shiru, sai kuma wani tunani yazo mata na 'gwara ta dinga mishi alfarma ko shima zai yarda da buk'atarta"

Tace "Ok" 

Yace "Zan turomiki address"

'Nan da nan tayi shiri, cikin wasu, da wando da suka matseta sosai, itama Maman tata bata nan, tana gama shiryawa text d'in ya shigo na address d'in, ta mik'e ta d'auki jakarta, tana fitowa harabar gidan ta gamu da Aysha tahir, taja tsaki a zuciyarta, wato zata b'ata mata shiri.' A d'an share suka gaisa, 

"A,a basma ina zuwa haka? 

"Hmm kinji ki da k'wak'wafi, to some where"

"Aysha ta kalleta sosai sannan tace "Oh lallai kin fa had'u sosai," Basma, tayi murmushi,

"Thank you"

"Muje tare mana, inji Aysha, wacce ta zuba wa basma ido, tana karantar yanayinta sosai,"

'Basma ta d'an had'e rai kad'an, "No, am sorry gaskiya, bazaki bini ba"

'Aysha ta rik'e baki, tana mamakin alamun tsoron data gani cikin idanun basma, da kuma sauyawar da tayi, 'sai ta jefa mata tambayar son gano, abinda take b'oye mata,

"Am lallai ma basma wa kika samu ne da har kike nuna min wariyar launin colour"

"Am um, kinga, am sorry ba haka bane, kawai dai, yau muka had'u dashi ne, so kinga ba zamu fara zuwa mu biyu ba."

'Aysha tayi wani murmushi, "Ok, hakane, kice kinyi babban kamu."

'Suka shek'e da dariya duka har da tafawa.'

'Anan Aisha taga asarar ta bar basma ta wuce ba tare da ta tabbatar da zarginta ba, don haka tace cikin siyasa.'

"Please basma kada kice na tsayar da ke wani application, nekeson zan tura, a wayarki, saboda shi nazo ma."

Basma tace,

"Oh, sauri nake amma ungo ki tura."

'Aysha na karbar wayar taga text, akai sai kawai ta shiga ta duba, Address ta gani, tayi saurin matse wayar zuwa silent, sannan tayi screenshots, ta shiga zendar ta tura, sannan ta zab'i application guda d'aya ta tura, ta goge history na photon 'screenshot' data tura, sannan ta dawo gallery ta goge shi, sanna ta duba logs taga wata number, wadda akayi kira baifi mintuna 25mins, ba da suka wuce, ta kalli number sosai sannan ta mik'awa Basma, wayarta, wacce ke ta faman gyara fuska da powder tun sanda ta bawa Aysha wayar.'

"Thank you"

'Inji Aysha basma ta karb'a suka jera suka fita, acikin layin basma ta sami 'Napep' ta hau tabar 'Aysha tsaye' tana d'aga mata hannu.'

'Aysha ce cikin daidaita' sahu' (Keke Napep) ta zaro wayarta ta kalli number da ta turo text a wayar basma, ta rik'e number, sannan ta saka a wayarta, number Yusuf, ce ta fito, wacce ita rabon daya kirata tun ranar da sukayi final papper, da tana tunanin, goge number d'in ma, 'sau uku tana saka wa, amma abinda ke fitowa a wayar kenan, mamaki ya cikata, da gida zata,' tace aranta 'Dole ne fa ta sanar da Hafsah, abinda ke faruwa, idan ba haka ba itama taci amanar Hafsan'

'Bata tab'a zuwa gidan su hafsar ba, amma, ta rik'e kwatancen da Hafsa ta tab'a yi mata.' 'Amma zata fara zuwa gida, ta d'akkowa Hafsa kyautar da yusuf d'in yai mata...

Ta isa gidan a gurguje ta ce wa Mamansu, zasu, je duba Hafsah ne ita da Basma, ta d'akko ledar sannan ta fito ta tarar mai adaidaitan yana jiranta, dama tsayar dashi tayi, ta fad'a mishi sunan unguwar da kuma, layin, ta shiga suka tafi, tana jinjina cin amana irin na Basma...






_Muje zuwa.._





*Hajeeyah Kareemerh ce* 👌🏼

[1/11, 12:11 AM] Hajeeyah Karimah (Writer): ♥♥♥♥

*ZAZZAFAN SO*

  (Guba ne)

*A broken*

*heart story*

 💔💔


Story and writing by:

*Karima Tijjani Mansur*

*(Hajeeyah Kareemerh)*

*Dedicated to: Unique In Your* 

*Love Heart Members*


*'Masoya na kune silar yin murmushi nah'*💃🏼💃🏼💃🏼😘😘😘😍😍😍 _Mom samhat, pretty, aysha Abdullahi (aysha sheka), Ayshaatou ('yan boarding book) ina yinku_ 💯 







📄 *31*





*A* k'ofar gidansu, aka ajye Basma, ta fito, ta tsaya gefen gidan, sannan ta d'akko wayarta, ta danna kiranshi, ringing d'aya ya d'auka. Yanzu, muryarshi ta fi d'azu yin sanyi.

"Hello,"

"Am gani a gate enku."

"Ok, ki shigo kinji"

'Ya kira mai gadi, a waya yace ya rakata har k'ofar sashinshi.'


Tana shigowa, mai gadin ya mik'e da saurinshi, "Barka da zuwa Hajiya" 

'Ta kalleshi kawai.' Ya shige gaba, tana binshi a baya, yana mamakin wacce irin bak'uwa ce wannan..??

'Asanin shi dai Yusuf, yana yawon daren shi, amma bai tab'a ganin ya kawo wata, cikin gidan su ba.'

'Azuciyarshi yace 'Allah ya shirya'

Ba wai don yana zargin, Yusuf d'in da wani abu bane, amma, bai ga dalilin da idan zaku tattauna wani abu da mace ba, har sai ka kirata gida kun keb'e..

'Suna isa dai dai bakin k'ofar wajen nashi, yai mata nuni da k'ofar, "Hajiya nan ne shashin oga Yusuf, d'in."

Ta yatsina fuska, sannan ta ce "Ok."

'Ta murd'a k'ofar a hankali, ta sanya k'afarta cikin wani madaidaicin, falo.

'A kwance ta hango shi, kan kujera 'Three seater', daga shi sai singlet da gajeren wando, ta d'an so razana, amma sai ta dake.'

'Ta k'arasa cike da yanga, ta nemi kujera mai kallon tashi ta zauna.'

'Shi kuma tunda ta bud'e k'ofar ya k'ura mata ido, har ta zauna, sannan ya mik'e zaune ya fuskanto ta sosai, ita kuma ta wani lumshe ido ta bud'e.'

'Ya saki murmushin daya nuna mata yaji dad'in ganinta sosai, sannan ya bud'e baki ya fara magana cikin k'asa da murya.'

"You're welcome"!

Tayi murmushi mai sauti, "Hmm, thank you."

'Ya karkatar da kai, "Zaki, iya..

zuwa.. dama"?

Tayi fari da idonta, "Hmm why not"?.

"Yai murmushi thanks alot"

Ahankali ya mik'e ya ya isa fridge ya d'akko lemo da ruwa da d'an plate da cup, duk a ciki, sannan ya tako har kujerar da take zaune, ahankali ta dinga jin fad'uwar gaba, amma sai tayi k'arfin hali ta dake, a zuciyar ta tana kishin ka da yaga hakan ya rainata, sai ma ta dinga k'ak'alo murmushin kan leb'e tana yi.


🤔 _k'arfin hali_😅

'Bayan ya ajye su akan d'an wani table, sannan ya zauna a wajen da yaji ya mishi, wato daf da ita sosai, sannan yayi gyaran murya, 

"Hmm Basma ma friends"

"Hmm, Yusuf, ya akayi ne"

'Cikin juyayyiyar hausarshi yace,

"Hmm mene ma ba,ayi bane, ke dai ki sha lemon nan kinji."

'Ya sunkuiya yana zuba mata a cup sannan ya mik'a mata, "Thank you."

'Tace dashi.'

Ta d'an sha yadda bazaice tayi k'auyancin kinsha ko kuma ta shanye ba."

'Ta dire kofin yayin da shi kuma ya ke kallonta cikin k'ura ido, tana k'ara k'awatuwa a idanunshi, wani b'angaren tana kore Hafsah, ta hanyar karanto mishi idan, itace bazata iya ba, saboda gidadancin ta, (ita Hafsan)

'Ita dai Basma jiran, cewar shi takeyi wato taji, ('Dalilin gayyato ta)

'Hum, yai wata gauruwar ajiyar zuciya sanan ya ce cikin muryar da take bayyana mata irin halin da ya ke ciki.'

"Am basma,.. Nasan kinyi mamakin inviting enki dana yi, koh,? '

'So kada ki damu, ni ina so ne mu k'ulla friendship ni da ke, yafi na da, and then ina so ki bani shawara da kuma k'arin bayani akan Hafsah."

'Ya k'arasa yana zuba mata idanunshi, ita kuma sai da ta d'anyi kokawa da tunaninta kafin ta k'arasa fahimtar inda dunkulellen zancen ya nufa.'

'Ta kuma jiyo muryarshi yana cewa, "kin dai son irin mu,amalan da Hafsah ke min, please kina ganin ya za,ayi na jure zama da ita haka,"

Basma tayi murmushi azuciyarta, amma sai ta gimtse da taji yace, "I don't mean zan rabu da ita ne, sai dai na fad'a mata zamanmu ba zai yiwu haka ba,.. saboda ita ne fa, for more than 1 year duba rabona da..".

'Sai ya katse zancen babu shiri, ita kuma ta hau ajiyar zuciya.'

"Dole ne kinga na samar wa kaina, solution koh"

'Ya fad'i hakan cikin k'aramin sauti.'..

'A gidan su Hafsa kuwa, tana kwance, a falo kan kujera, taji sallama, ta amsa tare da tashi zaune don tabbatar wa da wacce take tunani.'

"A Taheer!!

'Ta fad'a cikin k'araji suka rungume juna. 

'Aisha dai ahankali take sakin murmushi kawai.'

'Hafsah ta shiga hidima da ita, ta kawo mata lemo, ruwa da snacks har abinci ma da yaji nama acikin shi.'

'Aisha ta shiga tab'awa tana jimanta yadda zata ruguzawa Hafsah d'an farin cikin da ta ganta ciki yanzu, amma sai ta sami k'warin guiwa da ta tuna babu ishashshen lokacin b'atawa.




'Tayi goron numfashi cikin rashin sanin ta ina zata fara.'

"Oh dama zaki zo gidanmu Aysha."

"Hahh gani kuwa"

Kinyi k'okarin ganewa."

"Hmm Koh." 

"Sosai ma, don ma babu wuya gidan."

"Hakane kam."

"Ma manku bata nan ne"?

"Eh wllhi ba nisa tayi ba dai ta d'anje barka ne."

"Hmm, lallai kam shine ke kuma baki tafi islamiyya ba."

'Babu kowa ne a gidan, kuma kinsan munyi sauka mun ma juya bita ake tayi fa, ni hadda ma nake."

"Allah, izufin ki nawa?

"Ai na dad'e a ajin hadda tun kafin muyi sauka izufina 35"

"Kai Masha Allah, hafizai Allah ya bamu yaku."

Hafsah tayi dariya "Hmm Kinjiki."

'Sukayi shiru kad'an kowa na son jin ta bakin d'an uwanshi.'

Hafsah dai jikinta na bata akwai magana fa, da akwai abinda Aysha ke son fad'a a yadda taga yanayin ta.'

'Sai kuma, Ayshan ta daure tace "Hafsah ina Yusuf kuwa."?

'Dam' gaban Hafsah ya fad'i tare da jin wani shauk'i, tayi ajiyar zuciya sanan tace, "Aysha na rasa laifin da na mishi, ya daina nema na, ko zuwan nan na katsalandon da yake min, rabon da na ganshi yafi sati biyu tun fa ranar birthday d'in Basma.'

"Hmm, inji Aysha, lokacin da take ciro wayarta daga jaka, tayi saurin danna wajen videos ta kunna wa Hafsah ta mik'a mata. Cikin sha,awa da nishadi ta fara kallon, kafin daga bisani tayi nadamar d'ora idanunta kan wayar,

'Komai burgeta yake har zuwa lokacin da Yusuf ya bayyana cikin videon, sai kuma nishad'inta ya koma kishi, abin bai k'ara tsuma ta ba, sai da suka zo yanka cake, gashi ta kasa magana, har zuwa lokacin 'Gift, dake videon wani na k'arewa wani ke shigowa.' Aysha bata ankara ba sai k'arar Hafsah taji, tare da yin cilli da wayar gefe guda ta kifa sai wani sautin kuka mai tsuma zuciya.'

'Aysha ta san dole haka zai faru, amma yanayin sautin kukan ke tsoratata, kanaji kasan anayi ne cikin rashin sanin mafita kuma yana fitowa ne daga zuciyar data k'untata rauni ya baibaye ta matuk'a, kuma bata da mafitar hakan, kuka mai sa mai sauraro yaji kamar shima yayi kukan..

'Cikin rauni itama Ayshan, ta d'an daure ta fara magana.'

'Kiyi ha'kuri Hafsah yanzu ba lokacin kuka bane, ki k'arfafa zuciyarki don Allah, kiyi yak'i domin samarwa kanki 'yanci, in yaso daga baya kya koka, ni nasan anci amanarki, amma kiyi ha'kuri kuka mai zaiyi tasiri anan ba, don Allah ki tashi muje akwai sauran al,amarin da yafi wannan.'

Ta k'arashe maganar tana goge ragowar k'wallarta itama, sannan ta mik'a hannu tana tattaro wayarta data tarwatse, har 'Screen protector' d'inta ya fashe.'

'Hafsa tayi wata irin d'agowa cikin zafin nema, ta figo hijabinta daga kan gado batayi magana ba ta mik'e, ganin hakan yasa Aysha itama saurin mik'ewa, ta na duban fuskar Hafsah da tayi wani jajir ga kamanninta da suka d'an sauya saboda b'acin ran da take ciki. Aysha ta saka ledar kyautar Yusuf, cikin drawer Hafsah, sannan suka jera babu wanda ya kalli ma d'an uwanshi bare suyi wani zance.'

'Ita Aysha tsoron Hafsah ma, ta d'an fara ji a yadda ta ganta duk ta sauya lokaci d'aya.'

'Yayin da ita Hafsah, take jinjina irin wannan cin amana na babu zato da aka yi mata. 'Gefe guda kuma tana tunanin yanzu ina zasu je, don ita dai kawai taji tana son tabi Aysha ne zuwa ko ma ina ne.'

'Tafiya suke a hankali har suka isa get d'in gidan, hafsah tasa key ta kulle gidan, suka cigaba da tafiya, har yanzu zuciyarta na rad'adi, da tariyo mata lokacin da Basma ta rungume mata Yusuf d'inta, idanunta na zubar da zafafan, hawaye a hankali.'

Har suka tsare 'Napep' suka shiga ita dai tamkar kurma ko mutum- mutumi, zuciyarta ko fal k'una da zafi cikinta..'




*HAJEEYARKU CE DAI*👌🏼

[1/11, 1:38 PM] Hajeeyah Karimah (Writer): ♥♥♥♥

*ZAZZAFAN SO*

  (Guba ne)

*A Broken*

*Heart Story*

 💔💔



Story and writing by:

*Karima Tijjani Mansur*

*(Hajeeyah Kareemerh)*

*Dedicated to: Unique In Your Love Heart Members*





📄 *32*





*Kafin* su Hafsah, su isa gidan, yusuf da Basma, sun kai wani d'an mataki a shagala..'

( To dama abu ne da kowa ke buk'ata, sai kuma suka keb'e, sannan ga taimakon tattaunawar da sukayi ta tsawon wajen mintuna ashirin, wacce yawancinta Yusuf ne ya bayyana wa Basma cikinsa kaf, da duk wani sirri nashi, sanan ya b'ige da bata labarin rayuwarshi har da nuna mata photonan nan shi da yan matanshi na can wad'anda suka d'auka a yanayi daban daban.

Yusuf ya k'arasa hure mata kunnenta, sannan ya b'ige ga neman taimakonta bisa halin da yake ciki.')

Komai yayi tasiri a zuciyarta kuma sai yau ta k'ara yabawa dashi sosai, don haka, ta cire tsoron komai, bisa bin umarnin zuciyarta na ganin yanzu ne ya dace itama taji dad'in rayuwarta.'..

🤔

Suna dira daga 'Napep' yar tafiya kad'an sukayi sai ga gidan da Aysha ta tabbatar shine, ta kuma duba address d'in dake cikin wayarta.'

'Suka tura gate suka shiga, mai gadin wanda bazaifi shekara 37 ba, cikin shiga sosai kamar ba mai gadi ba, kana ganinshi kasan gidan 'yan boko yake aiki, yasa earpiece a kunne sai kad'a kai yake yi.'

Aysha ta mishi magana "Am kai yusuf na nan koh'?

Yace "Yes tare da kad'a kai.'

'Kaimu part enshi Kai tsaye tayi maganar'.

Dam gaban Hafsah yayi wata mummunar fad'uwar gaba banda wacce take ciki, tun d'azu.' ta ware idanunta ta kalli Aysha, kallon tuhuma dama gidan su Yusuf ta kawo ta.'??

Mai gadi, ya dakatar da tunaninta da cewa.' "Am sorry gaskiya oga baicemin zaku zo ba, so ku kirashi idan yace ku shiga sa..

Kai Malam bama son iskancin banza kasan matsayin mu kuwa..? 

Wuce muje ka nuna mana idan yaso ka tsaya kaga mu su waye a wajen 'Yusuf"??

'Aysha ta fad'a cikin fad'a-fad'a, cikin son yi mishi baraza.'

Baiyi magana ba ya wuce gaba suka bishi, yana tunanin wanne irin bak'in mata yau 'Oga Yusuf' yakeyi haka.'?

Har cikin part d'in ya kaisu sai da suka je dai dai k'ofar falonshi mai gadin ya tsaya, yana shirin yin 'Knocking' Aysha ta d'aga mishi hannu ta dakatar da shi.'

"No jeka thank you."

Batayi wani tunani ba ta tura k'ofar ta fad'a ciki Hafsah ma taga bata da zab'i illa ta bita, dukkansu wara idanu suke, kafin idanunsu su gama wayewa a cikin daki'n idon Hafsah ya hango mata su shi da wata da bata gama tantance wacece ba.'

'Zuciyarta ta buga da wani mugun k'arfi, ta yi saurin mutstsike idonta, ta k'ara dora shi kansu'

Nan ta hau waige waige kuma, idanunta yakai kan kofin Glass dake kan d'an table d'innan ta rarumo shi ta d'aga Kenan,..

Jikinsu ya basu akwai mai kallon su, babu shiri suka rabo, tare da juyowa sosai cikin muguwar fargaba.'

'Tsoro ne sosai ya shigi Yusuf yadda yaga Hafsa babu tsammani.'

'Ita kuma Basma ta hau soshe-soshen k'arya.'

'Zuciyar Hafsah ta tsaya cak cikin rashin sanin abin yi'

'Ko kwakwkwaran motsi ta kasa.'

Sai wani jiri jiri ma da taji yana kwasarta.'

'Me idonta ke nuna mata shigen al,mara,? Basma k'awarta? da Yusuf mijin da take fata.'

Ta d'an rufe idonta ta bud'e don tabbatarwa.'

'Aysha ce tayi k'arfin halin tafa hannayenta tare da cewa, dubunku ta cika munafukai, 'yan iska.. ' shed'anu.. Maciya amana, ta nuna Yusuf, lallai ka cika d'an iskan gaske..'

'Tana k'arasa fad'ar hakan Yusuf ya mik'e a zafafe ya wanke fuskar ta da mari.' tayi saurin rik'e kuncin, tana masa kallon k'askanci, shikuma sai huci yake yi.'

'Sai lokacin bakin Hafsa ya bud'e daga kullewar da yayi, ta mik'e cikin zafin nama tayi kan Yusuf.'

'Taci kwalar shi cikin rashin hayyaci, ta fara magana cikin kuka, da huci,

"k'arya kake Yusuf, yaushe ka zama munafikin mata..? Yaushe ka kware a yaudara..? Yaushe ka zama d'an iska??.. Yusuf ka cuceni.."

"Yanzu koh zaka aikata haka,.. karasa dawa zakuci amanata sai Basma..??

"Wayyo Allah, Yusuf ka cuceni wallahi, bazan yafe maka ba..'

'Tana k'arasa fad'in haka, ta sakeshi tare da hankad'ashi da duk k'arfinta.'

'Tun da tayi masa rik'on ya gaza aiwatar da komai banda kallonta da yake, sai tunani da dama cikin zuciyarshi.'

'Yasan dai bai kyauta mata ba, amma to ya zaiyi da rayuwarshi.'?

'Tana hankad'a shin yai saurin zama a kujera domin ya kusa fad'uwa, ya dafe kai cikin rashin sanin mafita.'

'Kamin yayi wani yunkuri yaji saukar wani bahagon mari a kuncinsa, asukwane ya d'ago don ganin wanne mai tsautsayin ne ya mare shi.'

'Aysha ya gani tsaye akansa tana huci, azuciye yakai hannu da nufin yi mata wani wawan duka, amma sai yaji an rik'e hannunshi, ya juyo rai a b'ace don ganin waye ya katse mishi hanzarin sa.'?

'Hafsah ya gani ta dakatar da shi cikin rawar murya mai rauni tace tana hawaye, "Yusuf dukanta zakayi, don ta rama abinda ka mata."

"Yusuf ka koya min darasi kuma na koya..' me nayi maka da ka saka min da wannan mummunar sakayyar.? Yusuf ka yiwa rayuwata illah, sai da na gama yarda da kai sannan kaci amanata..'

'Ta durkushe a gurin tana kuka mai tsuma rai.'

Shima a sanyaye ya durk'usa gabanta.'

"Hafsah believe me, banci amanarki ba, bakya tausayina koh, kiss and even hug baki rab'a yimin ba as my girlfriend, amma, Basma fa ita ta..''

"Ya isa! Ya isheka!! Ta fad'a cikin wani fad'a da wata murya mai k'ara gami da kuka, da haka basma ta fini a gurinka koh Yusuf, ta fad'a tana nuno, Basma data sab'a jakarta a kafad'a, tana gyara mayafi don shirin rantawa a na kare kafin hankalin Hafsa ya dawo ta juyo kanta.'

Nibance ta fiki wajena ba, idan ta bani abinda kika hanani kinga kowa matsayinshi daban',..

"Kai wanne iri ne Yusuf mai yasa baka ji ne, ehe, Meyasa ba zaka d'auka hakan laifi bane ko a addini.."

'Maganganun datake yi mishi kenan.'..

"Ta juya ga Basma, kin bani mamaki,kin ci amanata in sha Allah Allah sai saka min.."

'Ta finciko Aysha suka fita, inda Yusuf da Basma suka tsaya kallon kallo a junansu.'..

*Yours* 

*Khareemerh T Mansur*👌🏼

[1/12, 1:56 PM] Hajeeyah Karimah (Writer): ♥️♥️♥️♥️

*ZAZZAFAN SO*

(Guba ne)

*A broken heart story*

  💔💔



Story and writing by:

*Karima Tijjani Mansur*

*(Hajeeyah Kareemerh)*

*Dedicated to: Unique In Your Love Heart Members*

📄 *33-35*

*Basma* ta saki ajiyar zuciya tana wa yusuf kallon tuhuma, shikuma ya had'e hannayenshi biyu alamar Afwan sannan ya fice da hanzari, yafi su Hafsah.'

"Hafsah, hafsah baby.. Please ki tsaya mana".

'Kiranta yake amma Aysha sai faman janta take, tana d'aga mata kafada, alamar kada ta tsaya.'

'Abin mamaki sai ganin Hafsah, tayi ta fizge hannunta, ta d'an yi baya, ta tsaya cak.'

'Ya saki ajiyar zuciya, sannan ya k'araso cikin sassarfa.'

Am sorry Baby, wllhi banci amanarki ba, kuma, ki believing me, bazan tab'a rabuwa da ke ba, even if i got everything from Basma.."

"Ya isa,!! Ta fad'a cikin tsawa.'

Kana nufin hakan ba cin amana ne ba koh?"

'Ya dafa kai, ke kika janyo koma menene, i have tell you for multiple times, idan baki yarda dani ba, komai ya faru kada ki zargeni."

"And I swear to God, ko yanzu kika daina guduna, zan rabu da Basma."

"Ki yarda ban miki cin amanar rabuwa da ke ba'!

'Ji tayi hankalin ta na neman barin jikinta.

'Wanne irin soyayya kenan sukeyi, Zai rabu da basma idan ta aminta da buk'atar sa,.. Idan kuma ba haka ba zata zauna da kishiyarta kenan wato Basma??

"A hankalce ma abin babu tsari. 'Ta rasa wanne martani zata mayar mishi, iya bak'in ciki dai ta shak'a acikin kalamanshi, har wani abu ne ya tare, mata mak'oshi.'

'Ta girgiza kai cike da k'uncin rai tace cikin sanyin murya.'

'Yusuf na gode da sakayyar da kayi min.'

Kuma nagode, da matsayina da ka nuna min.' ta nuna kanta, "Yusuf wai ni kayi wa haka koh? "Na gode, wasu hawaye masu zafi, suka sakko zuwa, kan kuncinta.'

'Cikin gudu gudu, tayi saurin bar mishi wajen.'

'Kiranta yake amma ina tuni Aysha ta janye ta sukayi gaba.'

'Mai gadi ya yana musu a sauka lafiya,Hajiya.'

'Cikin sa,a suka sami Napep, cikin layin duk da GRA ne,

'Tunda suka shiga Hafsa keta faman aikin kuka, Aisha na faman rarrashinta, amma ina, abu yaci- tura, babu abinda take fad'a sai "Aysha yusuf yaci amanata, ya cuceni."

'Ita dai Aysha hak'uri kawai take bata.'

Sun kusa isa gidansu Hafsah, aka kira Aisha a waya, ta d'aga.'

"Hello mama,.. Ok, tom ina hanya yanxu zan dawo.'

'Ta Kalli Hafsah.' Kinga mama ce ke kirana, idan aka sauke ki sai ya wuce dani da nayi niyyar in raka ki gida.'

'Hafsah ta gyad'a kai kawai.'

"Amma don Allah Hafsah ki saita kanki kada mama ta gane, halin da ake ciki."

'Hafsah ta gyad'a mata kai.' ta d'akko 'Handkerchief' daga cikin Jakarta, ta mik'a mata.'

"Please ki goge hawayenki."

'Ta karb'a tana gogewa wani na k'ara fitowa.'

'Har k'ofar gida, aka kaisu.' Kuma, tun sanda suka shigo layin, ta cikin madubi, Hafsah ta lura da motar Abbansu dake bayansu.'

"Don Allah ki cire damuwa ki mai da komai kamar bai faru ba, please H. HAMID."

cewar Aysha kenan sanda akayi parking a k'ofar gidansu Hafsah.'

'Dak'yar Hafsah iya cewa, "Nagode, sosai Aysha ki gaida mamanku."

Tana fitowa daga cikin Napep, d'in motar Abba na sako kai, kuma ta tabbatar ya ganta.'

'Tayi saurin tura gate ta shige ciki tana k'ara goge fuskarta.'

'Tun daga yanayin data ga mama tasan da akwai matsala, gashi kuma maman ta k'ura mata ido tun amsa sallamar ta.'

'Tasha jinin jikinta sosai, sai lokacin ta tuna cewa 'rufe gidan tayi ta fita.'

'Tayi hanyar d'aki kenan mama tace, "Ke, zonan."

Cikin rawar jiki ta juyo ahankali take takawa takowa.'

"Daga ina kike"?

'Cikin tsawa maman ta tambayeta.'

'Nan ta hau kame- kame,..

"Um..wai ni..? in.. dama Aysha ce.."

'Mama ta daka mata tsawar data sata razana.'

"Zaki fad'amin min ko sai ranki ya b'aci."??

'Dai dai lokacin Abba ya shigo falon, jin mama na yin fad'a yasa yace, "Menene wai yake faruwa, lafiya."?

'Hmm inji mama, tare da yin kwafa 'k'

ta nuna Hafsah, da yatsa, gatanan sai ta fad'a maka tunda kazo kai.'

'Cikin rashin fahimta Abba yace,

"Me yake faruwa ne ki fad'a min me ta yi kuma."??

'Mama ta nuna ta, ka ganta, wai na fita na bar mata jiran gida, shine ta fice ta kulle gidan ta fice yawonta.."

'Abba yayi dogon numfashi, ya zauna kan kujerar bayanshi, ya kalli, hafsah data durk'usa a k'asa. cikin kaushin yace Ke, ina kika je. ehe"?

'Cikin rud'ewar murya tace "Abba dama Aysha ce tazo na rakata asibiti.."

"Shine kuma fuskar ki ta kumbura koh"?

'Ya katse hanzarin ta da tambayar.'

'Ta kai hannunta ta shafa fuskar, sai yanzu itama Mama ta lura da jan da idon Hafsah yayi.'

'Hafsah tayi kus, ta kasa bud'a baki tayi magana, sai hawaye ma da suka cika idanunta, na k'uncin da zuciyarta ke ciki.'

'Duka, da Abba da Maman ido suka zobo mata ta lura sosai da kallon tuhumar da dukkansu, suke mata.'

'Kwakwalwar ta chakud'e, gefe na k'okarin tariyo mata abinda ya faru da gidan su Yusuf, gefe na karanto mata tsoro da kuma neman abinda zata fad'awa Abba.'

'Ta d'an runtse idonta, kawai sai photon, abinda ta gani ya hasko cikin idonta, bata san lokacin da ta fashe da kuka ba, tama manta gabansu abba take.'

'Abba ya fusata, ya kawo mata duka, mama da zuciyarta ta shiga rud'u ta tare shi tana cewa, "Don Allah kada ka daketa ka kyaleta ta yi magana.'

Cikin fad'a Abba ya fara magana

"In kyaleta koh, kina sangarta ta koh? "Don iskanci daga tambayarta sai ta hau yiwa mutane kuka"?

"Yayi kyau, shikenan ki goyi bayan ta!"

'Ya Mike fuu yayi daki, yabar Hafsa durk'ushe a wajen, har ya dakko abinda ya zo nema ya dawo ya fice cikin sauri.'

'Mama da tun sanda ya shige tayi shiru ta rasa abin da zata cewa Hafsah ma.'

'Har wajen tsawon minti biyu, sannan maman ta k'irkiro abin cewa, cikin tsawa ta yi mata magana.'

'Zaki fad'i inda kika je ko sai nayi ball da ke anan wajen.'?

Hafsah ta d'ago a razane, har yanzu k'wallar bata daina d'iga ba.'

"Basma aka kwantar um.. a asibiti shine aysha,mukaje..Asibiti duba ta.."

'Tana dire zancen mama ta d'auka.

"Karya kikeyi"

"Wallahi Hafsah idan baki fad'amin gidan uban da kika je ba sai na k'arya ki anan."

"Wallahi, Mama can muka.."

Ta, doka mata tsawa.'

"Dubiya da tsakar ranar nan koh,?.. To uban meye ya kumbura miki ido, fuskarki tayi ja ehe."

"Um, wallahi tun jiya mama nake ciwon ido dama."

'Mama tayi shiru, ba, wai don ta yarda da shiryayyen zancen Hafsah ba, kawai dai ta shiga rud'ani ne.'

'Kuma akace,' 'Mace' tana da rauni.' To agurin mama, raunin shine yayi tasiri, sai tunanin ta ya chanja gabad'aya zuwa wani layi daban.' Bisa wani karatu da zuciyarta tayi mata.'

'Ta fara tuno abubuwan da suke faruwa tun had'uwar Hafsah da Yusuf.'

'Zuwan Hafsah gidan Hajiyah na k'arshe, sai babban tashin hankalinta 'ranar bikin uncle abdallah, fitar da hafsah tayi ita da wani.'.. To yau ma gashi ta fita ba,a sani ba, kuma yadda mama ta kiyasta tafi awa d'aya bata gidan.'

'Don ita kanta maman wajen awarta d'aya da dawowa. Mamaki da tsoro suka mamaye ta data ga gidan a k'ulle.'

'Duk da tana da 'Spare' na muk'ulli acikin jakarta, hankalinta bai kwanta ba sai da tayi ta zagayen mak'ota tana cikiyar ko Hafsah ta shigo.'

'A farko tunaninta ko ta gaji da zaman shiru ta shiga mak'otan, duk da tasan Hafsah bata da tsoron zama ita kad'ai cikin gida sannan kuma bata da shige shigen mak'ota.'.

'Ashe ita Hafsan ta tafi wani wuri can abinta.' To ina taje kenan,? Ita da wa,?

'Allah ya kiyaye kada dai Hafsah na k'okarin kama wani layi na daban ne.' idan ta duba zata ga gaba-d'aya Hafsah ta canja dabi,u.'

'Zaman shiru 

yawan tunani sai kuma b'oye b'oyen da ta tsiri yi mata yanzu, sai fita bada saninta ba.'

'Wanda ada ba haka bane.'

'To Meyake faruwa? ka da dai ace ansami wani ya gurb'atawa 'yarta tunani da kuma tarbiyyar da suka dad'e suna tattalinta.'

'Wannan tunanin na Mama, ya jawo abubuwa da dama..'

'Sallamar Hajiya ita ta farko da Mama daga dogon tunanin da ta tafi.'

'Ta amsa cikin sanyi, ta fara yiwa Hajiya sannu da zuwa.'

'Yawwa inji Hajiya, Hajiya ta zauna, sai lokacin ta lura da Hafsah, zatayi magana Mama ta hau gaisheta.'

"Sai da ta amsa, cikin sakin fuska, sannan ta juyo ga Hafsah,

"Ke kuma fa?

'Kinyi wani jugum dake ba kya gaida mutane"?

'Hafsah ta d'ago tare da dai dai ta fuskarta.'

'Hajiya sannu da zuwa, ina wuni.'

"Lpia lau"

'Hajiyan ta amsa, sannan ta dire tambayarta,

"Me akayi miki ne.'

'Kunya ta hana Hafsah amsawa, ita da tayi laifi kuma ake tambayarta me akayi mata'??

'Mama ta cafe zancen'

"Laifi tayi." 

'Hmm ko da naji, sai wani wuk'i wuk'i kike da ido kamar mara gaskiya."

"Ashe kuwa baki da gaskiyar."

'Mama taji gabanta ya fad'i rashin gaskiya kuma.'? To me Hajiya take nufi,?

'Kada dai ta gano wani abu, game da Hafsah, tun da dai ita Babba ce.'

'Nan lissafin Mama ya k'ara jagule wa.'

'Ta mik'e ta nufi kitchen don debowa Hajiyah abinci.'

'Lokacin kuma aka kira sallar la,asar, saboda haka Hajiya ta mik'e don yin alwala, ta kalli Hafsah, 

"Ja,ira sai ki tashi an kira sallah.."

"Naji yace kin k'are boko koh."?

"Ai, ashe bokon naku bana k'arau bane, kin gama secondira"

'Hafsa ta gyad'a kai.

"To Allah yasa albarka."

'Ta mik'e ta nufi d'akinta, tana godewa Allah, da Hajiya tazo da tuni har yanzu Mama na faman tuhumar ta.'

'Maimakon tayi alwala, sai alhinin abinda ya faru ya danne k'arfinta ta kwanta ta fashe da wani matsanancin kuka, tana jajanta wa kanta, wannan cin amana da aka dad'e anayi mata, da sai yau, Allah ya nufa ta sani.'

'Taci kuka ta goge Allah har ta tausaya wa kanta, babban abinda yafi tasar mata da hankali shine, 

'Yanzu a wanne matsayi take gun Yusuf.'?

'Ashe Yusuf duk soyayyar da yake karanta mata ta k'arya ce.'?

Ita data rik'i Basma aminiya, shine zata ci amanarta.'?

'Ashe da gaskene sauyin data dinga gani a wajen Basma.'.. Wayasan lokacin da suka d'auka suna aikata haka,? 

'Sun ninke ta abai-bai.. 'Ta k'ara rushewa da kuka, har da dukan 'pillow' saboda alhinin raina mata tunani da akayi.'

'Gaskiya sun raina tunaninta, takaicinta ajinta da aka zubar mata ranar birthday d'in Basma.'

'Ta tabbatar rabin 'yan class d'insu sun je, kuma an kira Yusuf da saurayinta, amma saboda su tabbatarwa da mutane sun rainata, kuma ita ba komai bace a wajen yusuf.'.

Yasa suka yi hakan.. '

'Tayi kuka har kanta ya fara ciwo, idanunta, sukayi jajir kamar an watsa mata barkono.'

'Har kiran sallar magariba bata fito ba, tana ta aikin kuka, amma babu shashsheka sai hawaye dake fitowa daga cikin idanunta, wand'a kana gani kasan tana cikin k'uncin zuciya, da taikaici.'

'Tana jiyo tafiyar hajiyah, amma ko lek'awa parlour bata yi ba.'

'Ta dai tashi tayi sallah sannan ta koma ta kwanta.'

'Mama kuma fushi take da ita, don haka ko lek'o ta batayi ba.

'Can kuma bangaren, mama tunani tayi kamar bata kyauta ba data hana abban hafsah dukan Hafsar, bai dace ta dinga katse mishi hanzarin ba, akan dukkan matakin daya ga ya dace ya d'auka akan Hafsar tun da ita ta gaza.'

'Ta saba tun da can bata dukan Hafsah, bare kuma yanzu da ta zama budurwa sosai.' 

'Ba kuma, don hafsan tafi k'arfinta bane, sai don shi dukan bashi da amfani.'.

'Amma to ya ta iya, wani lokacin dole sai an had'a da dukan, musammaman yanzu da Hafsah ke neman 'bujirewa, ta kama wani layi na daban.' A tunin maman, 'Wanda zancen Abba da mutane yayi tasiri akanta har ta ke zargin wani mummunan abu ayau ga Hafsan wato fad'ar da ake na,👉🏻 'BA,A SHEDAR YARAN YANZU'..

B'angaren zuciyar mama na wassafo mata wani abu, wani b'angaren na k'okarin korewa.'..

'Haka ta tilasta wa zuciyarta sai ta binciko gaskiyar zarginta. Hafsah ta gudu gidan Hajiyah tayi zance kuma ta tabbatar a d'akin uncle abdallah tayi zancen.' sanan ta fita da saurayi bada sanin kowa ba ranar biki, yau kuma ta fice yawonta (idan ma ita kad'ai d'in ta fita) batare da sanin kowa ba. 'Wanda dukka wad'annan halayen ba nata bane ada ba zata iya koda kwatanta yinsu ba, to Yanzu to 'Me TAKE SON ZAMA.'?

'Wai don ma mama bata ji halin da uncle abdallah ya gansu ba ranar.'

'Da akwai matsala inji Mama.'

'Iya k'arfin tunanin mama kenan..'😇👏🏼👌🏼#Hajeeyah Kareemerh.'

'Shiko Abba sai bayan anyi sallar magariba, sannan ya shigo gida.'

'D'akin shi ya wuce maman ta kai mishi abinci can, bai nuna mata komai ba ya saki jiki da ita har sukayi hira.'

'Bai sako mata zancen Hafsah ba sam, kuma tasan halinshi so yake ya barta tayi nata k'okarin, don haka tayi azamar chanja hirar tasu ta sako ta abinda yafi damunta ayanzu wato 'lamarin Hafsah.'

"Am Abban Hafsah baka tambayeni ya mukayi da Hafsah taka ba."?

'Cikin rashin bawa zancenta muhimmanci yayi d'an murmushi mai sauti.'

"Hmm to ai wannan ke da ita ne.

"Me yayi wa Abba zafi,? 'Bake tayiwa laifi ba, kin barta jiran gida ta fice nata sabgar,? to ni me ye nawa kuma ciki."??

'Nan da nan fuskar Mama ta sauya taji zafin kalamanshi fiye da tunani. 'Da bazata tanka ba sai kuma taga asarar hakan, don haka ta had'iye fushinta, tace,'

"Idan tamin laifi ai kaima ai tayi maka, kuma ko ba haka ba ma ai kafi kowa iko da ita."

"Hmm, ta yaya? Bayan gaki, kefa kika haifeta."

"Haba Abban Hafsah don Allah ka daina fad'ar haka."

"Hmm da Hakane Amina, ai da baki nuna min wai kada in tab'a miki 'ya ba koh'?

'Subhaanallah, wallahi ba haka bane, wallahi bada wani manufa bada manufa nayi hakan ba.'

"Hmm to ai shikenan nima bacewa nayi wani abu ba.

'Ki mata abinda ya dace kawai."

'Yana fad'a ya mik'e don fita masallaci sallar isha'i.'

'Hankalin mama ya tashi, tayi da na sanin hakan data mishi, data bari ya d'auki mataki akanta, ita gani tayi dukan bai da anfani, kuma ta tsorata da dukan da yayi wa Hafsan kwanaki.'

'Shi abinda kake tunanin zaiyi fushi akai to, ba,a kanshi yake fushin ba.'

'Yanzu ya zatayi idan ya zare hannun shi daga kan Hafsah'??😳

😀

'Mama kenan'!👍🏻

'To shima abba, a b'angaren shi, ba wai cire, hannun nashi zai yi ba.'

'To idan yayi haka mekenan yayi, ai kanshi yayiwa.' 

'Dole ne ya sa ido akanta ko dan hak'k'insu akanshi yake, bare kuma yafi sonta akan dukan 'ya'yanshi.'

'Kawai ya kyale mama ne, don kuma da gaske abinda ta mishi ya b'ata ranshi sosai.'

'Amma shima da akwai nashi tunanin akan matakin daya dace kan Hafsah.'

'Koda aka idar da sallah bai nemi hanyar gida ba, ya jima yana addu,a kan Allah ya taimake shi akan tarbiyyar Hafsah, 'Don yasan addu,ar ita ce komai bawai wani k'okarinshi ko fad'anshi ba..'

'Yasani tarbiyya da akwai wuya amma, kuma yasan yayi iya kokarinshi, sai kuma yanzu da wani keson wargaza mishi komai.'

'Shi dake tuninshi daban da na mama, yayi amanna tabbas 'Soyyaya' ce ke dawainiya da Hafsah har bata tsoron fushinsu yanzu, ya lura tanayin duk abinda zai zamar mata maslaha ne ga soyayyar ta ko menene kuwa zai biyo baya.'

'Shi abba ba takaicinsa bane soyayyar data fad'a, a,a abinda yake b'ata mishi rai shine kalar yaron data nacewa.'

'Ya tabbatar ba na nunawa bane in banda haka meyasa ya kirashi, yak'i zuwa.'?

'Amma yanzu ya zamar mishi wajibi ya nemi yaron koda a waya ne, don maslahar shi.'

'Saboda haka yasa a ranshi gobe zai kira shi..'

'Da wannan tunanin ya kamo hanyar gida.'

'A gidan kuma, yaran ne suka dami mama bayan ta fito daga d'akin Abba, 'Wai ina yaya.'?

'Nace muku tana d'aki meye zaku dameni.'?

"Mama bata da lafiya ne..?"

'Inji Mufida.

"Ban sani ba, kije ki duba mana." 'Cewar mama cikin fushi.'

'Mufida ta mik'e ta nufi d'akin Hafsar.'

'Tana kwance sai juyi take.' Bayan ciwon kan daya addabeta yanxu kuma ciwon mara take fama.'

'Ga kuma uwa uba ciwon da aka haddasa mata cikin zuciyarta.'

"Yaya, Yaya, wai baki da lafiya ne?

'Ta d'ago jajayen idanunta, ahankali ta bud'e baki murya a dashe saboda kuka tace, "Eh Mufida, bani da lafiya."

"Kaii, amma baki fad'awa mama ba.? 

Bari inje to in fad'a mata.

'Tana yunk'urin ce mata a,a, amma ina, ai tuni ta fice.'

'Daidai sanda ta dawo falo lokacin Abba ya shigo yaji tana cewa.'

"Mama Mama yaya bata da lafiya kuka take tayi ma."

'Mama ta d'an rud'e ta tabbatar kenan tun la,asar Hafsah keyin kukan nan, idan kuwa haka ne, to da akwai babbar matsala tabbas akwai abin da ya faru da Hafsan ayau d'innan kuma ta tabbatar mummunan abu ne, sai zarginta ya k'ara samun wuri.'

'Bata nuna damuwarta afili ba, ta dai mik'e ta nufi d'akin.'

'Abba ya jinjina kai sannan ya bita.'

'A kwance ta sameta sai juyi takeyi.'

'Maman tazauna, a gefen gado, ta tab'a k'afarta, abinda yasa Hafsah ta d'ago da idanunta, ahankali tace bani da lafiya.'

"To meya yake damunki"?

'Sai da tayi jinkiri, sannan tace, "Ciwon kai, kuma marata ciwo take."

'Mama tayi azamar k'ara yi mata tambaya, kana ji kasan a rud'e take matuk'a, kuma tana cikin tsoron faruwar wani abu.'

"Ke.. ke Haf..sah dazu ina kika je ehe.?

'Wani abu da Mama bata sani, ba shine da zarar tayi wa Hafsah tambayar 'inda taje, tana k'ara tuno mata da abinda ya faru ne.' sai taji bazata iya fad'a musu ba, kuma bazata iya rik'e kukanka ba.'

'Ta, rantse idonta don wani irin suka da taji zuciyarta nayi.'

'Wai shin Gaske ne yau taje gidan tayi Yusuf, har taga wannan mummunan al,amari.'?

'Tsawar mama ta firgitata da tace, bazaki fad'i gidan uban da kika je ba koh, cikin raunin murya tace, mama dubiya muka je.."

"K'arya kike.. Zaki fad'amin gurin wanda kika je idan na tattaka ki anan."

'Dam gaban Hafsah ya fad'i, har rawa jikinta ya fara yi, ka da dai mama tasan inda sukaje.'

'Muryar Abba taji da yake tsaye abakin k'ofa, yana cewa "Meye haka Amina, wacce magana kike yi ne ehe"?

"Yarinya bata da lafiya kina wani tuhumar ta da wani zancenki."?

'Ya juya kan Hafsah "Ke tashi maza, zaki iya tashi koh"?

"Ta gyad'a kai."

To tashi ki shiga toilet kiyi wanka, kisa ruwan 'Heater' dayawa kinji? Idan kin shirya kizo ki sameni.'

'Ahankali ta d'aga mishi kai.'

Gaskiya taji dad'in abinda Abba yayi yanzu.'

'Ahankali ta mik'e tana bin bango saboda dad'ewa da tayi a kwance har jiri takeji.'

'Mama ta daka mata tsawa, 

"Zakiyi tafiya daidai, ki daina bin bango ko sai na ci ubanki!"?

'Babu shiri ta dawo kan doka da oda, inda ita kuma mama ta k'ura mata ido.'😅😄😄

🤔 To wai me Maman ke nufi ne.'???😒

'Ruwa mai zafi ta had'a, tayi wanka dashi, tanayi tana hawaye, wanda sun ma k'afe sai rad'ad'i cikin zuciyarta.'

'Ga takaicin abinda mama take mata, sai taga wannan karon tafi Abba ma d'aukar zafi.'

'To meye dalili??

'Wata zuciyar tace,

"Hafsah kina jawo mata magana ne da yawa..!

'Da tayi wankan taji dad'in jikinta sosai, kuma taji, zuciyarta ta rage k'una, sai ajiyar zuciya da take ta faman yi.'

'Ta tarar da Abba a falonshi, yana zaune kan kujera. Zata zauna a k'asa yace ta tashi, ta zauna a kujera itama, sanan tace Abba gani.'

'Memakon ya amsa mata sai yace mata, "Kin ci abinci"?

"Ta girgiza kai."

Ya nuna mata tray da mama ta shiryo mishi abincin daya ci d'azu, gashi nan ki zuba kishi kinji.'

'Ta, gyad'a kai'

'Madaidaici ta zuba sannan, ta fara ci ahankali, abba na kallon 'television' jefi jefi yana kallonta.

"Kici fa abincin nan sosai."

"To"

'Ta fad'a.'

Taci fiye da rabin abinci ta sha ruwa, sai ya nuna mata apple da aka yanka akan wani k'aramin 'plate' ta, d'auki guda d'aya ta fara ci."

'Gaskiya taji dad'in jikinta, cikin abinda suka addabeta har da yunwa.'

"Kin fad'a wa maman naki inda kika je."?

Tambayar da Abba yai mata kenan babu wasa a fuskanshi.'

'Ta d'aga mishi kai, "Eh"

'To fad'amin'

"Dubiya muka je ni da k'awata"

"Ina kenan."

"A asibiti aka kwantar da ita."

"To ya sunan asibitin a ina yake"?

'Tayi d'if, to fa anzo wajen'

Sai da yace "Uhum"?

'Sannan ta samu tace, um bansan.. Au na manta sunan shi"

"Haha, 'Abba yayi 'yar dariya..' "Ya akayi kika manta"?

"Babu komai"

"Hmm, to meyasa ki ke ta kuka."?

'Tambayar ta razana ta.'

"Babu komai."

"Wani ya dakeki ne"?

'Ta girgiza kai.'

"Hmm tom yayi kyau "

'Ya tsare gida sosai ya kuma nuna ta da yatsa'

"Hafsah, Hafsah,!! Ki kiyayeni cikin sha,anin fita daga gidan nan batare da kin fad'a min ko kin fad'awa mamanki ba, haka kika ga bashir nayi? Ace k'aninki yafi ki hankali'? Wallahi kinji na rantse idan kika kuma fita ko nan da k'ofar gida ne bada sanina ba sai na yi mummunan sab'a miki.!!"

"Kin manta kwanaki koh? To zan hanaki fita gaba d'aya ma."

"Abba kayi hak'uri."

Kada in sake jin wata k'awa tazo kun fita ke da ita ko ina kuwa zakuje, kina jina"??

'Ta d'aga kanta.'

"Ki kiyaye kafin na sab'a miki fa"

"To Abba" 

"Ta shi ki fita saura inji labarin kink'i yin bacci."

'Ta wuce d'aki, ta kwanta' ko babu komai fad'an abba ya shige ta, da tana bin umarnin shi da bazata fita ba bare taga wannan abin bak'in cikin.'

'Ta d'akko Diary tana son ta rubuta wani abu a ciki, amma kuma ta kasa saboda cinkushewar zuciya.' Da ta d'ora biron akai sai taji hawaye ya cika idanunta."

'Ta cillar da Diary gefe guda, afili ta furta "Yusuf wai you choose to BROKE MY HEART??😭😭😭

'Ta kife kan pillow tana rizgar kuka har bacci ya d'auketa.'

'Washe garin ranar tatashi babu yabo babu fallasa, sannan kuma taji kwata kwata bata k'aunar fita ko da falo.'

'Ta daure tayi wanka ta koma gado ta k'ara kwantawa zuciyarta ce keson yi mata 'Karatun baya'

'Ta dinga tuno farkon had'uwar ta da Yusuf, halayenshi da ya dinga fito mata dasu, yadda Basma, ta fara chanja mata, da kuma zancen zuwanta birthday, sai kuma abinda ya faru ranar birthday d'in da kuma wanda idanunta suka gani jiya.'

'Ta rantse idonta, ta cije lebe, hadi da huro iska daga bakinta, ta dad'e tanajin ana cewa NZAFIN SO,' ko kuma 'SO GUBA NE.'

'Amma ita da yake tun farko rayuwarta bata ginu akan Soyyayya ba bata gane zancen sam.'

Tana jin haushin Jamila idan ta dameta da zancen 'Salim' ko ta zauna kod'a mata shi.."Ai Salim ya had'u, ina sonshi d'an beauty nah.."

'Wani lokacin har tsaki take yiwa Jamila, "Aikin banza shi mutum kamar kowa amma kita faman wani rawar kai kina kod'a shi kamar wata marok'iya sai kace da 'Gold' akayi shi.. Mtsw"😠

'Idan ta tuna jamila murmushi takeyi ta ce mata, "Hmm Hafsah bazaki gane ba ne."

'Akwai ranar da wata 'yar ajinsu a islamiyya tazo tana ta rizgar kuka, har da bubbuga benci, Hafsah har dariya taji ta bata. "Wai saurayinta ne ya zagaya yana son k'awarta.'

'Ko lokacin suna tare da Yusuf, amma hakan bai hana ta yin dariya ba, musammaman data ga bilhak'k'i kuka take yi."..

"Tana ambaton an cuceta."

'Ita dai dramar soyayya na burgeta.'


'Ashe marmari ce daga nesa.'😳

'To yau gashi abu ita ma ya sameta kuma ta rasa mafita.'.

"A tunaninta ko dai tayi wa Yusuf wani abu ne shiyasa ya rama.'?? 'Me yasa yanzu sai ka yarda da mutum, yake cin amanarka?..

W'ani Babban abin takaici shine gashi dai k'iri- k'iri tana jin zafin Yusuf, amma kuma gefe na zuciyarta na k'ara wassafo mata shi, da kuma karanta mata kada ta rabu dashi, tun da shima bai nuna mata ya rabu da ita ba.."

'Ita kanta tasan idan ta rabu da Yusuf, to tabbas tayi wa rayuwarta illa, tasan zuciyarta ma bata da jarumtar jure hakan.'.. Dole ne ta rungumi abinda yai mata, ta yi d'amarar kwato shi itama da k'arfinta, don idan ta barwa 'Basma' shi to tabbas ta tafka babbar asara, kuma Basma tayi nasara akanta kenan..'? Banda kuma dumb'in soyayyar shi dake dank'are cikin zuciyarshi, wacce bazata iya sadaukarwar da ita ba ga wata'..

'Ta sani aiki ne a gabanta ja, amma bata san ta ina zata fara shi ba.'

Dole ne dai tabi umarnin Abba idan tana son zaman lafiyarta, to idan kuma babu fita ta ina zata dinga had'uwa da Yusuf'?

'Tasha alwashin idan taga basma sai ta yi mata abinda bazata manta ba, sai ta d'and'ana mata b'akin ciki ita ma...'

Sallama ta jiyo a falo kamar ta Aysha, amma kuma kusan minti uku bata shigo d'akin ba kamar yadda ta saba.'

'Sai kuma taji an turo k'ofar. Mama ce tsaye kanta, "Sai ki fito ai." 'Abinda tace mata kenan, ta juya.'

'Ta mik'e ta fito, taga Aisha zaune, ta d'an saki fara,a, tazo kusa da ita ta zauna.'

'Ta lura da hararar da mama ke aika mata da ita.'

'Tayi yake sannan tace "Aysha Sannu da zuwa" 

"Yawwa" 

"Ya mamanku"?

"Lafiya lau wllhi."

'Duka sukayi shiru saboda ganin idon Mama.'

Ita Aysha nason tayiwa Hafsah zancen jiya kuma tana son kwantar mata da hankali, shi yasa tayo azamar tahowa lokacin baifi 11:00am, ba. Don tun jiya hankalinta ya kasa kwanta wa.'

'Hafsah ta lura da akwai magana don haka ta mik'e muje d'aki, "To" inji Aysha, taji kuma d'adin hakan.'

'Dama tunda tazo bayan sun gaisa da Maman, zata wuce d'akin Hafsan, mama tace ta dakata Hafsan, tafito.'

'Aysha na mik'ewa hankalin Mama ya yo kansu' fuskarta a d'aure ta kalli Hafsah, "Ina kuma zaku je"?

"Um bed room zamu shiga."

"Ba inda Zakuje, ku zauna anan."

'Har yanzu bata saki fuskarta ba.'

'Hafsa taji kunyar hakan, tare da jin takaicin Mama, "Meyasa take mata hakane yanzu."?

"Mama mai fara,a ga k'awayenta"?

'Amma yanzu duk ta sauya'?

'Dole ta dawo ta zauna ita da Aysha sukayi shiru.' sai can ne ma Ayshan k e sako mata hirar makaranta jefi jefi.'

'K'arar wayar Mama yasa ta shi da sauri ta nufi d'akinta, ta basu iska.'

'Tana zuwa tashi Aysha ta bud'e baki.'

"Don Allah Hafsah kada ki dinga saka damuwa don Allah wallahi bansan abinda zamu tarar ba da bazan kaiki ba, badai je gidansu Basma ne na tarar zata fita, kuma dana karb'i wayar ta sai naga yusuf ya mata text d'in address d'inshi.' ta dakko wayar ta tana nuna mata.'

'Ta cigaba da cewa, "Don Allah,ki cire Yusuf aranki don wallahi ba saurayin da za,a zauna da shi, bane."

'Hafsah ta zaro ido, zatayi magana kenan, Mama ta fito daga d'aki, tilas tayi shiru da bakinta.'

'Aysha bata jima ba ta mik'e, "To mama na tafi, hafsah sai anjima."

"Ki gaida gida."

'Mama tace mata.'

'Aysha ta mik'e don raka ta.'

"Mama ta murtike fuska, Saura ki fita daga cikin gidan nan."

'Suna fita daga falon Hafsah ta fara bawa Aysha ha'kuri.'

"Don Allah Aysha kiyi ha'kuri da abinda mama tayi miki, wallahi tun jiya bayan dawo take fushi."

'Aysha tayi murmushi,' 

"Babu komai wallahi."

'Amma don Allah ki rage damuwa wallahi har kin fad'a, daga jiya, ki daina saka abin aranki, kada mama tayi zargin wani abu."

"K'walla ta cika idanunta, Aysha dole na damu, Yusuf fa.." Kuka ya hanata magana.'

"Kiyi ha'kuri dai. 

"Ni dai shawarata ki cire shi daga ranki, don Allah, shine kawai maslaha."

"Hmm Aysha bazaki gane ba kawai."

"Allah ya kyauta, ki koma kada mama ta ga kin dad'e."

"To nagode Aysha ki gaida mamanku."

'Aysha ta d'aga mata hannu sannan ta fice daga gate d'in gidan.'

'Hafsah ta tsaya ta goge fuskarta sannan ta dawo cikin gida, ta tarar maman na zaune inda ta barta.'

'Zata wuce d'akinta kenan, Mama ta kirata.' 

"Ke zonan"

'Ta dawo ta zauna a kujera.'

"Mama gani"

"Wannan Yarinyar daga ina take"?

'Hafsah taji banbarakwai.'

"Um, k'awata ce ita fa mukayi photo ranar graduation."

"Bana son jaye jaye"

'Hafsah ta gyad'a kai kawai, tana Mamakin Mama.'

'Kuma, bana son zaman cikin bed room d'in nan da kike, ko uban wani ne yake korar ki daga falon'?

'Ta girgiza kai.'

"To kada in sake ganin kin kwanta."

'Dole ta nemi guri a falon ta kwanta, saboda idan tana, 'Menstruation' ciwon jiki take fama, ga kuma kasalar son kwanciya.'

'Mama da ta ga ta kwanta taji saurin cewa, "Tashi maza kije ki gyara daki'n abban ku, kuma, ki wanke toilet d'inshi."

'Badon ranta yaso ba haka ta mik'e ta nufi d'akin Abban, tana murje ido, to da wanne zataji da fushin mama ko kuma abinda ya dami zuciyarta.'

'To haka ne yake ta faruwa kullum har wajen sati d'aya, Hafsah da son yawan yin tunani, mama kuma da son matsa mata, ga kuma tambayoyi da take damunta dasu, "Kya ma fad'i inda kika je"

'Ita dai, Mama batun fitar nan, ya tsaya mata aranta.' 

'Hafsah ta kasa gano dalili.'

'Ko sanda ta fita ita da yusuf daga gun party, bata d'auki zafi haka ba.'

'Hafsah ji take ita kad'aice mai matsala a duniya.'

'Abinda Yusuf yayi mata ya ki barin zuciyarta ga uwa uba kuma kewarshi data dameta, tun ranar bai nemi inda take ba gashi bata da wata hanyar contacting d'in shi.'

'Tsoro ya cika zuciyarta.' shikenan basma ta k'wace mata yusuf d'inta da take so.'

'Matuk'ar zata tuno shi to tabbas sai 

tayi hawaye.'

'Ta yi rama, kallon daya zaka yi mata kasan tana cikin damuwa, duk maganar da mama ke mata kan zaman bed room taki ta daina.'

'Abin ya dami kowa cikin gidan, k'annenta sun lura ta rage walwala.' Bashir kullum sai ya tambayeta me yake damunta, amma amsar guda d'aya ce babu komai.'

'Abinda ya tashi, hankalinta shine, bashir yace mata, "Yaya Hafsah jiya antaso mu daga school naga wannan yusuf d'in shida k'awar nan taki a mota danja ya tsaida mu."

'Gabanta ya fad'i ta shiga damuwa sosai.'

'Kenan yusuf ya ajyeta.. Ya daina yayinta..? bazai rabu da basma ba,??.. 'Ta fita muhimmanci a wajanshi kenan...'??

'Ta kasa hak'uri har sai da ta zubar da hawayen tausayin kanta bayan fitar bashir. Ita dai son Yusuf ya zame mata 'GUBA'

'Abba, a dole ya kira Yusuf, a waya.'

"Hello." inji Yusuf.' 

"Assalamu alaykum."

'Inji Abba.'

"Wa alaykum salam"

"Ina magana da yusuf ne"?

"Eh nine."

"Yawwa, ka gane mai magana."

"A,a." ('Don Yusuf sam baiyi serving number ba')

"Okay Abban Hafsah ne.'

Yusuf yaji fad'uwar gaba, kada dai yarinyar ta fad'a wa ubanta abinda ke faruwa."

'Ya daure dai yace.'

"Daddy ina wuni"

"Lafiya lau. 

'Abba ya fad'a cikin fara,a.'

"Am dama so nake in tambayeka ka."

'Yusuf ya d'auke wuta saboda fargaba'

"Hafsah ta fad'a mak a ina son ganin ka"?

'Yusuf yai wata wawuyar ajiyar zuciya'

"Huuam, No, bata fad'a min ba daddy."

Abba yai murmushi lallai ma shida aka fad'a mishi a gabanshi.'?

'A lokacin ya gane inda yusuf ya dosa.'

"Abba yace ok shikenan.'

"Idan babu damuwa gobe ko jibi kazo, ina son ganinka."

'Ya yi shiru, sai da abba yace "Kaji"?

Sannan yace okay Daddy."

"Abba yace nagode sai anjima."

'Abba ya ajye wayar yayi shiru yana nazari, yasan da k'yar idan yaron zai zo.'

'Hakan ya tabbatar mishi irin yaran nan ne da ba aure suka shirya yi ba, sai dai su hure wa yarinya kunne.'

'Saboda haka ko yazo d'in ma zai san matakin da zai d'auka kawai.'

'Mama ma a neman tata maslahar, da suna waya da yayarta take ce mata, "Wallahi yaya da akwai matsala ne"

"Lafiya dai ko"?

"Hafsa ce dai."

Yayar tayi dariya, "Hmm amina kenan, kin iya dagula al,amra kila ma ba wani babban abu bane."

"Hmm, Yaya Yarinyar so take tafi k'arfina wallahi."

Ke amina wannan wacce shashashar magana ce, ki haifi 'yar ki dinga kiran tafi k'arfinki."??

"Ki dinga saita bakinki don Allah."

"Hmm yaya.."

'Kada ki fad'a min komai ki bari gobe zan shigo.'

"To shikenan, yaya na gode."

'Yayar ta kashe wayar tana dariya.'

'Washe garin wajen k'arfe goma sha biyu, Hafsa na zaune a falo, ta kasa samin nutuwar zuciyarta kiyasta wa take yau kome zai faru sai ta tura wa yusuf koda text ne.'

'Tana cikin tunanin ne 'Aunty Nafisa.' ('Maman ya Nazeer') Tayi sallama hafsah ta amsa mata kuma ta d'an saki fuskarta. 'Tayi mata Sannu da zuwa.'

"Mama na jiyo sallamar ta ta fito da sauri, Aunty sannu da zuwa." "Yawwa Ameena."

"Ina wuni" inji mama "Lafiya lau."

"Yasu Naseer da Fatima"?

"Duk lafiya lau suke, nazeer shirin Service ('NYSC') ma yake"

"Allah sarki Allah ya taimaka to."

"Amin, ya yaran gidan."

"Suna nan k'alau sun tafi makaranta ne."

"To ya Abban su Hafsah"?

"Lafiyar shi lau wallahi."

"To Masha Allah."

'Hafsah ma ta gaisheta'

"Bari in kawo miki lemo."

'Mama ta mik'e.'

"A,a ki zauna mana ga Hafsah."

"Ta Kalli Hafsah 'yan mata an yi candy koh."?

"Maza ki kawo min ruwa ne kinji, ki daina barin mama tana aiki ke kina zaune."

Hafsah tace, "To"

'Maman Naseer ta kalli Mama, "Muje ciki koh"?

'Suka mik'e duka suka yi daki'n mama.'

'Hafsah ta d'oro ruwa da lemo da cup a plate ta bisu da su.'

'Ta ajye sannan ta fito, ta dawo falo.'

"To Sannu kinji"?

'Inji maman ya Nazeer.'

.'Ta tsiyaya ruwa tasha, sannan ta kalli mama sosai cikin nutsuwa tace.'

"Me yake faruwa ne ke da 'yar taki."?

'Mama ta gyara zama cikin damuwa take karanto mata.'

"Kinga dai abinda tayi ranar bikin abdallah, to kafin nan sai da taje gidan Hajiya kakarsu... Nan ta zayya no mata duk irin abubuwan da Hafsa tayi har tazo kan fitar da tayi bata sani ba.'

"Ta, k'arashe zancen da cewa ni tsoro na ma, kada inje yaron ya lalata mata rayuwa..."

'Auntie tayi saurin d'ago mata hannu.'

"Haba amina, wannan wacce irin magana ce mara ma,ana kike yi.?? ina tunanin ki ya ke, da zaki yiwa 'yarki wannan mummunan zaton'?

"Allah dai yasa baki furta wa babanta wannan shirmen ba."

"Auntie kinga fa ranar data dawo har magariba tana aikin kuka, sannan kullum cikin tunani take, idan ba wani abu ba mezai kawo haka"?

"Hmm, kin bani da dariya amina, shiyasa kike kyararta kika zuba mata ido koh,? Gaskiya tunaninki yayi Kama da na yara."

'Kawai kuma don yarinya ta fita ta dawo bada saninki ba, sai ki hau zarginta koh."?

"To dai ki chanja tunani, don me bazaki jata ajiki ba kiji damuwarta, ai ko bata fad'a miki ba zaki fahimci me yake damunta koh."

'Ni kin b'ata min rai ma wallahi.' 

"Yanzu dai, koma menene zan tafi da ita tayi koda sati biyu a wajena.'

"Shikenan aunty, nagode."

'Ita kuwa Hafsah ganin babu kowa a falon kuma ga wayar mama data bari yasa tayi saurin d'aukar wayar tayi d'akinta tana godiya ga Allah.'

'Cikin azama ta hau rubuta text,

'Ban tab'a zaton zaka yi min haka ba, koda a mafarki,..idan nayi maka wani laifine, sai ka rasa ta hanyar da zaka hukunta ni, sai kaci amana ta,??.. Yusuf cutar da kayi min ba,a tab'a yi min irinta ba'..

'Nagode sosai, bisa sakayyar da kayi min.'.."

'Hafsah H. Hamid'

'Ai kuwa minti kad'an sai ga reply,

"Hmm Hafasah kenan, shine yasa kika sa Abbanku ya kira ni koh..'So ya kirani kuma yace min yana son ganina." Hm kin fad'a mishi ne koh.."?

"Tana cikin karantawa sai ga su Mama ad'akin, nan tayi tsuru-tsuru, mama ta rufeta da duka da hannu, tana fad'in kinganta koh.. Kinga dai abinda takeyi.'

'Maman ya Naseer, ta rik'e hannun Mama, tana fad'in haba ki bari mana Amina, don Allah kibi komai a sannu.'

'Suka zauna, sannan Auntie ta d'auki wayar, text d'in Yusuf, ta fara karantawa, ita ma kanta ya kulle gaskiya ne akwai abinda ke faruwa.'

'Sai kuma ta kuma duba na Hafsah, sannan hankalinta ya d'an kwanta.'

'Ta ajye wayar sannan ta kalli Hafsah.'

"Me yasa kika d'aukar mata waya"?

"Cikin kuka take cewa babu komai."

"To me kika yi da ita."?

"Ta, kuma, cewa babu komai."

"Hm, babu komai fa kika ce, amma kika d'auki wayar."?

'Cewar Auntie.' 

"Um, game nakeyi"

'Auntie tayi murmushi.'

To kada ki k'ara d'aukar mata waya.'

"To"

"Ta dafa kafad'arta.'

Tashi maza ki deb'o kayanki kinji, gida na zaki je, tun da yanzu bakya zuwa makaranta.'

'Hafsah bataji dad'in hakan ba, ta mik'e babu k'wari ta fara debo kayan daga cikin drawer.'

'Shaf ta manta da ledar nan ta Yusuf, aiko tana dakko wasu kaya, ledar ta fad'o.'

'Mama tayi saurin d'aukar ledar cikin rud'ewa ta ke cewa Auntie kin gani koh, ai mai hali baya fasa halinshi."

'Auntie ta karb'i ledar ta bud'e, sai taci karo da kwalin wayar mai tsadar gaske wato, 'IPhone' a ciki, sai wani tsadadden agogo, sai turare mai tsadar gaske, sai kuma, 'Greeting card'

'Auntie ta mayar da kulle ledar dama rubi biyu ce.'

'Hafsa ta gama shirya kayan sannan ta kulle akwatin, tasa hijabi, suka fito dukansu.'

'Auntie tace maza ki kai kayan cikin mota.'

'Ta ja akwatin tayi waje inda drivern auntie take.'

'Auntie ta kalli Mama bayan fitar Hafsah, "Ki bar komai a hannuna, ba wani abin tashin hankali bane ina zatan kyauta aka kuma bata, in sha Allah komai zai yi daidai.'

'Mama tace "Toh"

Ina wayarki kira Abbanta zanyi mishi bayani da kaina.'

'Mama ta danna kiran, bayan ya d'aga "Hello, barka da rana, ya aiki."

"Alhamdulillah, aiki yasani gaba."

"Allah sarki to "Sannu da k'okari."

"Yawwa."

"Dama, Auntie Nafisa ce tazo tana son kuyi magana ne."

"Okay to bata wayar."

"Sun gaisa sannan ta ce, nazo ne kuma sai Amina keyi min k'orafi akan Hafsa, to shine ina so abani ita don Allah in tafi da ita tayi koda sati ne a wajena."

'Abba bashi da matsala da ita, kuma yasan ta macece jajirtacciya,kuma

babba ce, don haka yace, "babu komai ai, yayi kyau wallahi, na gode sosai."

"Sai dai Don Allah kada a barta ta kula duk wanda yazo wajenta, kuma kada ta dinga yawo."

"To in sha Allah, na gane babu komai ai."

"Yawwa, wani yaro ne yake son wargaza mata lissafi."

"Auntie tace 

"Eh na fahimta, yaran yanzu ne babu abinda suka sani sai soyayya."

"Wallahi kuwa, Allah ya kyauta ya shige mana gaba."

"Ami'n inji Abba, to nagode fa, agaida alhajin."

"To zaiji in sha Allah."

'Ta, kashe wayar ta mik'awa mama.'

"Ki dinga yi mata addu,a, amma wannan ba wata matsala ba ce Babba, kinga shi baban nata ai ya fahimci komai."

"To auntie, nagode."

"To bari mu wuce."

'Auntie tace sanda Hafsah ta shigo.'

'Mama ta taka musu zuwa bakin gate.'

"Mama mun tafi."

'Inji hafsah.'

'Maman ta saki fuska sosai to hafsah in kuma auntie ta rik'e ki shikenan sai ki zama bak'uwa."

"Hafsah tayi murmushi, taji dad'in sakin fuskar da mama tayi."

'Suka shiga mota suna daga wa mama hannu. Driver yaja suka tafi.'

'Hafsah taji kamar tayi kuka, bata tab'a yin tafiyar data wuce kwana biyu, shima gidan Hajiyah take zuwa, amma taji auntie tace wai sati biyu zata yi..'

'Gaskiya zatayi kewar jama,ah da dama..

'Amma haka dai, zata hak'ura.'

'Sai kuma kalaman yusuf a text to kenan Abba ya kirashi,?? To me yake nufi da ita, da yake cewa wai tafad'awa abba koh..??

'Lallai ma Yusuf, 

Allah yaso ta sa number a blacklist, bayan shigowar text d'in saboda tsoron kada ya kira Mama.'

'Ta jingina jikin kujera, tana tunano ya zata kasance idan Yusuf ya guje ta...

Shikuma driver sai gudu yake kan titi har suka isa unguwar Kabuga, inada gidan Auntie yake..'👏🏼👏🏼👏🏼

*TO ALHAMDULILLAHI READERS, FANS, ANAN MUKA GAMA KASHI NA D'AYA NA WANNAN LITTAFI SAI KU JIRA KASHI NA BIYU, DOMIN JIN YA RAYUWAR HAFSAH DA YUSUF ZATA KASANCE.'??*

*A cikin..*👇🏼👇🏼👇🏼

♥♥♥♥

*ZAZZAFAN SO*

(Masoyin Kwarai)

💔💔

👏🏼👏🏼👏🏼👏🏼

*'Jikar waziri Ahmadu dai..!!*👌🏼

*(HAJEEYAH KAREEMER)*








♥♥♥♥

*ZAZZAFAN SO*

(Masoyin K'warai)

*Cigaban littafin Zazzafan so (Guba ne)*

💔💔



Story and writing by:

*Karima Tijjani Mansur*

*(Hajeeyah Kareemerh)*

*Dedicated to Unique in your love heart group members*





📄 *36*





*BAYAN SHEKARU SHIDDA.*



*Katafaren* d'akin, taron 'Meena event center,' ya k'awatu sosai, an cika ana jiran shigowar ango da amarya da ango.

'Tana zaune a nasu table d'in.. Ita da sauran k'awayenta.. Babu jima wa ango da amarya suka shigo tare da rakiyar k'awaye da abokai..'

'Alokacin ne kuma biki ya kankama, aka fara lik'i da rawa."

'Tunda tazo wajen bataci komai ba..

tayi kyau cikin ankon bikin na atamfa da peace d'in head.'

'A can b'angaren abokan ango kuma.. rawa suke casa, kasancewar Mc, ya basu fagen.'

'Kana ganinsu kaga wayayyu maza ajin farko, sam basu da hayaniya, rawar ma ba wani yinta suke bilhak'k'i, ba. Sai kudad'e 'yan dubu dubu, da suke ta yin ruwan su.'

'Ahankali angon ya jawo wani daga cikin su, ya dafa kafad'ar shi, yai mishi rad'a a kunne, 

"Mene haka ne please ka saki ranka don Allah kada wannan abin ya b'ata maka rai.'

'Ya lumshe idonshi a hankali ya bud'e.'

"Ok, but kasan dole ne fa abin ya dameni, matar nan fa taci mutunci na.'

"Na sani amma ka share please kada ka damu kaji? Kaje ka zauna ka sami nutsuwa."

"Ok.

"Baya ya wuce yana duba 'sit' d'in da babu mutane sosai, amma ko ina da jama,a, gashi tsarin duk na mata da maza aka cakud'a a kowanne table '

'Yaja siririn tsaki lokacin da ya isa daf da table d'in da Hafsa take, bai wani lura da su wanene akan table d'in ba, amma yasan dai matane su uku kawai.'

"Tunda ya zauna ya dafe kanshi da hannunshi.'

'Sauran 'yan matan ne su biyu suka mik'e, don jin cewa, an buk'aci k'awayen amarya na school da su fito suma.'

'Itama Hafsa mik'ewa tayi ta bisu tana cewa,

"Anisa, bari nima na biku, nayi lik'i.

'Sai da suka fara tafiya sannan ya d'ago kanshi.'

'Ya sauke ajiyar zuciya, yana kiran sunan Allah a zuciyarshi, a hankali ya fara jin nutsuwa na saukar mishi.'

'Sai lokacin ya tuna rabonshi da abinci tun safe, gashi yanzu har k'arfe shida saura kwata.'

'Hafsah tayi wa amarya lik'i tare da yi mata fatan alkhairi, sannan ta nemi da su Nabila su taho su koma wajen zamansu. 'Amma sukace mata ai su sai sun ca she.'

'Dama bikin wata 'yar ajinsu ne da suka yi degree tare da ita.'

"No nidai gaskiya i can't dance cikin wad'annan gayyar mazan kawai ni na tafi, ku sameni acan.'

"Alright"

'Inji Nabila tana tsokanarta ke kin fiya kunya wallahi.'

'Bata kula su ba ta wuce ta dawo wajen zamansu.'

'Tun da take takowa yake kallonta ita kuma sai taji kamar ta sauya waje saboda su kad'ai kenan zasu zauna a table d'in.'

'Zata wuce shi kenan taji yace a hankali,

"Nop, ki zo wajenki ki zauna babu matsala."

"A hankali batare da ta kalleshi ba ta zauna a kujera dama da shi amma tabar tazarar kujera d'aya a tsakaninsu.'

"I hope ban tsare miki guri ba."

'Ya fad'a cikin taushin muryar da taji sanyin ta har cikin ranta.'

"Ta girgiza mishi kai ahankali kawai."

'Su kayi shiru na d'an wani lokaci yayin da shi yake aikin kallonta.'

"Ita kuma duk bata jin d'adin zaman wajen so take kawai ta tashi."

'Gashi karo na wajen uku kenan tana jin ringing d'in wayar shi amma a yadda ta lura ko kalla bai yi ba bare ya d'aga.'

'Wasu maza ta gani wajen su biyar cikin abokan ango sun nufo su.'

'Suna k'arasowa da'ya ya zagaya bayanshi ya dafa shi, sannan ya fara yi mishi magana.'

"Please ukasha ka share abin nan don Allah, meye zaka sawa ranka damuwa.? Please feel free mana."

'Shiru shi dai baiyi magana ba.'

"Daya daga cikin su ne yace " ka bari a gama harkar bikin nan, zata gane kuranta, amma ya zaka zauna wata mace tasa ka maka damuwa.."

'D'ayan ne yai dariya har da tafa hannaye, "Ku kuna abinku, yayi muku banza ba kuga shi hankalinshi ba ya wajenku ba, no wonder ma haushinku yakeji, yana tad'in shi kunzo kun dame shi.'

"Ko ba haka ba ne UK"?

'Ya fad'a tare da dukar mishi baya.'

"Murmushi yayi shi dai kawai."

'Ita dai Hafsah Allah Allah take dukan su su tashi subar mata wajen saboda gaba d'ayan su sun dameta, gata ita kad'aice mace duk mazaa sun zo sun baibaye ta.'

'Wanda tun da suka zo baiyi magana ba, shine ya kalleta yace,

"Kinga please k'anwata ki dan miqo mishi wannan abincin ko zai ci."

'Tab, inji Hafsah acikin zuciyarta, a wanne dalilin zasu sata wani aiki kan wani mai ji da kanshi sai wani cika yake kamar ita ta mishi abinda akai mishi.'

'Ta kalli wanda yai mata maganar, sannan ta mik'e tare da cewa "Excuse me please"

'Ta rab'a ta gefensu ta, bar musu wajen.'

'Dukkansu suka bi bayanta da kallo har da shi d'in ma.'

"Wanda yai mata maganar shi ya fara yin magana.'

"Tab, lallai Yarinyar nan 'yar zafin kai ce, wato ba zatayi magana ba ma shine ta mik'e ta bar mana wajen kenan.?"

"Muna da aurenmu, bare taja mana aji wannan UK ta, yarfa ai."

'D'ayan yace Allah yaso bani ta yarfa ba.'

'Da bazan iya ha'kuri ba wallahi.'

'Sai yanzu wanda suka taru danshi d'in yai magana, bayan yayi ajiyar zuciya,

"To kada ka hak'ura d'in."

'Su rasa ma abinda za suyi mishi sukayi, sai kawai suka shek'e mishi da dariya.'

'Wanda ya mata magana, ya fara jawo hannunshi, "Wallahi sai ka taso kuwa mun tafi, duk hada hadar nan sai anyi dakai."

"Mubarak ka barshi yasha ko da ruwa ne mana."

'Take ya girgiza kai shima, "No bazan iya sha ba.'

'Ya mik'e ya bisu, a hankali take fad'o mishi a cikin ranshi, sai ya dinga jin damuwar shi gaba d'aya ta gushe, sai ma damuwar, tafiyar da tayi, ke damun ranshi.'

'Babu laifi ya saki ranshi aka sha hidima sosai da shi, sai dai kuma tun da Hafsah tabar wajensu, har aka tashi bai k'ara ganinta ba, lamarin daya d'an tashi hankalinshi kenan.'

'Misalin k'arfe takwas kenan na na dare aka tashi daga gurin bikin, kai tsaye shi gida ya nufa, bai tsaya wani hada hadar d'iban mutane ba saboda kiran da Baffa yai mishi tun yamma, yace ko k'arfe nawa ne idan ya gama yazo yana nemanshi.'

'D'aya daga cikin drivers (Direbobi) na gidan ya kira a waya, yace yazo ya kaishi gadon k'aya.'

'Yasan ba zai nutsu yayi tuk'i ba, saboda fargarbar abinda baffan zai fad'a mishi.'

'Driver yana fito wa ya nufi motar ya bud'e mishi ya fito, sannan ya gaishe shi..

'Ya koma gidan baya, yayin da drivern ya zauna a mazaunin driver ya bawa motar wuta.'

'Mintuna kad'an ya kaisu unguwar, inda sukayi parking a dai dai, k'ofar wani madaidaicin gida, driver ya fito ya bud'e mishi k'ofar sannan ya fito, ya fara takawa zuwa cikin gidan.'

'Kai tsaye sit room d'in gidan ya nufa don ya ganshi a bud'e.'

'Yai sallama aka amsa, sannan baffan yai mishi izini daya shigo.'

'Shida Hajiya ne a sit room d'in.'

'Cikin nutsuwa ya durk'usa ya gaida su, suka amsa tare da tambayar shi ya mutanen gidan.'

'Hajiyar ce ta mik'e ta nufi cikin gidan da dama ta sit room d'in zaka iya shigowa ko kuma ta k'ofar dake gefe.'

'Baffa ya kira sunanshi, "Ukashatu" 

Cikin ladabi ya amsa,

"Na,am baffa"?

Kasan dalilin kiran nan naka?

'Ya girgiza kai,

"A,a baffa."

'Yad'anyi murmushi sannan, yace, to zancen mu ne dai dai da aka saba shi."

'Ukasha ya gyara zama, har wani zufa yaji ya keto mishi, baya son ayi mishi zancen nan, bayan kuma gashi yau gaba d'aya ma ranshi a b'ace yake.'

'Cikin tunanin shi yaji yo, Baffan na mishi magana babu alamun wasa a tattare da shi.'

"Ya ake ciki to, kasan dai tun tini lokacin da muka baka ya cika koh"?

"Ya gyad'a kai, nasani baffa."

"To ya banji bayani ba har sai da na kirawo ka"?

'Ya muskuta, sannan ya fara magana

, "Ai baffa ba,a samu ba ne.'

.

"Nan take baffan ya rufe shi da fad'a,

"Wato ka maida mu abokan wasan ka koh?.. Ka d'auki zancen da wasa koh?? 

"Shikenan to yayi kyau abinda kayi, amma ka san bazamu zuba maka ido ba koh"?

'Tun da ya fara mishi fad'an ya sunkuyar da kanshi k'asa, sai da ya dire zancen shi sannan ya kwantar da murya yana bada hak'uri.'

'Ayi ha'kuri baffa, Allah ya huci zuciyarka, bani da burin in b'ata muku rai wallahi ayi hak'uri dai."

'Shima baffan sakkowa yayi, saboda wani tunani da yazo cikin zuciyarshi.'

"Wato ya dace su mishi uzuri, basu san dalilinshi nayin hakan ba, ga kuma larura irin ta jinnu da dai sauransu.'

'Don haka yace,

Ukashatu, ba muna matsa maka bane amma kasani aure shine cikar mutum, kuma, muna ganin ka kai munzalin da ya dace ace kaima kana da iyalinka, duba kaga shekarunka yanxu a k'alla sun kai talatin da shida, fa, to me kake jira, tunda kana da rufin asirinka, ka k'aninka ya gaji da jiranka har yana da 'yarshi?

Ya k'ara sassauta murya, sannan yace,

'Kodai baka da lafiya ne, baka fad'a mana ba"?

'Abinda ya ba ukasha dariya kenan har yayi dariya mai sauti, sannan yayi saurin toshe bakin shi, tuna wa da yayi baffan ba abokin wasan shi ba ne.'

'Baffan ma murmusawa yayi, sannan yace cikin sigar yi mishi, wayo ko dan idan yana da larurar ma ya sanar da shi.'

"Ka daina jin kunya, ko 'shi' yana nufin ('Abban ukashan') idan ka b'oye mishi ai ni bazaka b'oye min ba, kuma larura ai daga Allah take, wannan ba abu bane da zaka b'oyemana, sai ka fada mana koda a waya ne sai a nema maka magani koh"?

"Amma asani na, da yadda sa,anninka na nan gidan ma suke fad'a ba,a tab'a jin kayi lissafin aure cikin sha,anin ka ba sam."

'Ya d'an gyara murya sannan yace,

"Baffa in sha Allahu na kusa kawo muku ita, a dinga yi mana addu,a dai Allah ya taya mu zab'i na gari."

"Ami'n, ami'n, inji kawu daya saki murmushin jin dad'in furucin, sannan ya d'ora da cewa, 

"Kuma kaima ka dage da addu,a saboda da akwai shed'anun aljanu masu cutar da d'an adam."

"Hakane Baffa na gode sosai, Allah ya k'ara girma."

Ami'n, baffa ya fad'a yana mik'a mishi hannu alamar suyi 'musabaha' (Abisa al,adar kawun idan zasu yi bankwana da koda jinkansa ne.')

'Ukasha ya mik'a hannu sukayi musabiha, sannan ya mik'e.'

"To na barka lafiya baffa."

"Masha Allah, a gaida mutanen gidan, Allah yai muku albarka."

"Ami'n baffa ya fito yana, ajiyar zuciya, don yaga alamun sassauci a b'angaren K'anin mahaifin nasashi.'

'Ya nufi gate, ya tarar da driver ya d'an kwanta cikin motar yana jiran shi.'

'Yana ganinshi yayi saurin fitowa zai bud'e mishi gidan baya.'

Ya dakatar da shi, "A,a ka gaba zan zauna ina son zamuyi hira ne.'

'Driver yayi murmushin jin dad'in hakan, duk da suna gaisuwar mutunci amma yayi mamakin cewa hira da Ukasha yace zaiyi da shi, saboda yasan shi ba ma,abocin yawan magana ba ne da yawa, amma sam ba,za,a ce yana da wulak'anci ba saboda halin gidansu gaba d'aya na karamci ne, domin sun gaji girma da karamci.'

'Ya bud'e mishi gaban, sannan ya zagayo, shima ya zauna ya kunna motar sannan suka hau bisa titi.'

'Sai da suka fara tafiya sannan ya kalle driver yace,

"Malam najib, ina son tambayarka ne, amma don Allah ka Fad'amin gaskiya."

"To in sha Allahu, mai gida zan fad'a maka iya abinda na sani."

"Yawwa to, am nasan dai ak'alla zan baka shekaru kamar hud'u, amma ina son sanin wani abu ne tun da kai kana da aure, kuma, yanzu 'ya'yanka biyu kace koh."?

'Ya gyad'a kai, "Hakane mai gida, yanzu na uku ake shirin haifowa."

"Yai murmushi, Masha Allah."

'Sannan ya saita muryarshi, 

"Aganinka me yasa su baffa suka takura min da sai nayi aure."?

'Najib driver yayi dariya sannan yace,

Ai mai gida, bama sai an tambaya ba ka isa munzali tun yaushe, kuma, tunda ba wani abu ake jira na shiri ba (Kud'i) ai ya dace dai ace zuwa yanzu an mallaki iyali. Sannan hankalinsu zaifi kwanciya idan har kana da auren"

"Wane irin kwanciyar hankali kuma"?

"Najib yai 'yar dariya, sannan yace a zuciyarshi, "Bari na bi dashi ta yadda zai fi fahimta."

'Don ya fahimci, ba wai ukasha ya damu da auren bane, idan ya fahimta ma shi zancen ma baso yake ana yi mishi shi ba.'

'Sai ya kada baki yace, 

"Mai gida, sai kawai ayi hak'uri tun da manya sun nuna suna so sai a yi k'okari ko don biyayya.'

'Sannan shi aure yana sa a dinga ganin k'imar mutum ta musammaman.'

'Ya kalleshi, 

"To yanzu idan na fahimta wata tawaya ce kenan saboda bani da aure koh."?

"A,a mai gida, kawai shi aure yana cika darajar mutum ne."

"Yai murmushi, sannan ya gimtse, sannan yace,

"Bana son wulak'anci ne irin na mata."

"Alhaji ai ba kalar ku ake wukak'antawa ba gaskiya.'

"Hmm, haka kace, amma kada in maka shishshigi da sai ince, tsakaninka da Allah matar ka bata maka wulak'anci."?

"Kasan ni shine abinda na tsana a gurin mace."

'Ya fad'a yana yatsina fuska.'

"Eh to, wallahi mai gida batayi gata da sanin yakamata, ga tsafta, sai dai kawai kasan mata ba,a rabasu da jan aji wani lokacin."

"Yai murmushi sannan ya jingina jikin kujerar motar,

'Jin daga an tab'o matar shi ya fara zuba.'

"Ahankali yace Allah sarki, tunda haka ne, in sha Allah nima zanyi k'okari ko dan farin cikin su Abba.'

'Driver ya ce "Toh Allah ya zab'a ta gari, mai gida."

"Ami'n"

'Dai dai lokacin sunzo wajen wani store mai kyau, yayi mishi alamar da yayi parking a wajen.'

'Sai da suka tsaya, sannan ya kalle shi, 

"Muje kad'an sama mata kayan gayu, madam d'in taka tunda kace 'yar gayu ce, sai ka had'a harda na jaririn koh? "

'Driver ya hau fara,a "Godiya nake alhaji."

"Tare suka shiga, kantin.' 

'Kaya ake siyar wa na madaidaitan kud'i, amma sai kyau."

B'angaren atamfofi ya zab'ar mata uku masu kyau, amma ya mishi alamar daya k'ara, ya dad'a guda biyu saboda kada ya zak'e da yawa, babu abinda bai sashi ya d'aukar mata ba tun daga kan mayafai takalma, sark'oki da turare, da sauransu.'

'Sai kuma kayan Baby, sai takalman yara da yace ya d'aukarwa ya'yan nashi.'

'Shidai Najib har kasa godiya yayi, yasan kawai Allah ne yayi mishi katari, ayau d'in, don yana shirin fitowa ya nufi gida, Ukashan ya kirashi, kira yake kawai,

"Allah ya k'ara arziki, yasa a gama lafiya, Allah ya k'arawa alhaji nisan kwana."

"Ami'n yake cewa shi dai,

'Ya mik'a katinshi aka zara wajen dubu abba'in da wani abin.'

abinka da kud'in yanzu ba wuya kiji sun taru akan k'aramar siyayya bare kuma siyayya irin wannan.'

'Sai da suka fito yace mishi, to adinga taya mu da addu,a muma, Allah ya bamu nagari."

"Ami'n Ami'n, mai gida addu,a dama kullum muna saka ku a cikinta."

"Sun isa gida, ya sauke shi, sannan ya deb'e kayan shi ya nufi gida cike da jin dad'in yadda matarshi zatayi farin ciki da kayan, saboda yana yabonta sosai.'

"Ukasha kuwa, yana shiga cikin gidan yaji wata masifaffiyar yunwa, nan ya tuna rabonshi da abinci tun safe, lokaci guda kuma ya tuno da wannan Yarinyar ta d'azu a wajen biki, take yaji wata mummunar fad'uwar gaba, daya tuna bai ma san yaushe tabar wajen ba."

"A shagwaba irin tashi ne, ya nufi d'akin k'anwarshi yana buga mata k'ofa, saboda sanyi ne duk sunyi bacci, shiyasa ma bai nufi d'akin hajiyar tashi ba.

"Ita kam Fadwa, yasan ba bacci take ba, fadwa please ki fito mana.'

"Ta ajye wayar ta gefe, sannan ta mik'e ta zare key sanan ta fito,

"Kinyi bacci ne? 

"No, ta girgiza kai."

Ok plz ki had'amin abinda zan iya ci yanzu yunwa nakeji kinji."

"Ta gyad'a kai kawai, saboda tasan halin yayan nata da rigima bama tasan me zata dafa mishi ba, kuma may be idan ta tambayeshi yace ya fasa, ko ya zaci ya takura mata ne.'

"Ta nufi kitchen, ta duba taga da miya sai kawai ta, d'ora d'an ruwa ta dafa mishi taliya, sannan ta zuba ruwan tea madaidaici tasa mishi kayan k'amshi, ta juye a plask, amma saboda ta tsokane shi sai ta d'auki iya abincin kawai, ta nufi d'akin shi dashi.'

'Ta tarar ya idar da sallah, ta ajye mishi tana cewa bross, gashi toh."

'Ya d'aga mata hannu alamar godiya, sannan bayan ya shafa addu,ar ya kalleta,

"To ina coffee d'in kuma."?

"Tayi murmushi, kamar yace ta mishi da coffee, sai kawai tace, 

"Ai bakace min da coffee ba."

"Yazanyi in iya cin abinci babu coffee kin sani, amma shine zaki k'i had'a min"?

"To bari in samo maka."

"No ki barshi ai kinsan ina so, baki had'o min dashi ba, so kije ki huta kawai thank you, kinji."

'Tayi murmushi, wai shi dole sai ya nuna mata baiyi fushi ba kenan, bayan tasan wannan zai iya zama sanadin k'in cin abincin nashi ma gaba d'aya.'

'Zata yabeshi bashi da matsala a komai, amma a b'angaren nan, sai matarshi ta fahimce shi, idan ba haka ba zasu dinga samun matsala, saboda, shi mutum ne dayake son kawai ki fahimci abubuwan da yake so, da wanda baya so, idan ya nuna miki al,adar shice yin abu to ki rik'e ba sai kullum ya maimaita miki ba.' saboda bashi

da son yawan maimaita abu.'

'Shiyasa take mishi fatan ya samu mace, mai lura sosai, saboda banda wannan bashi da wata matsala shi dai.'

"Am yaya na fa had'a maka d'akko maka kawai zanyi.'

'Ya jawo hannunta sannan ya rankwasheta, 

"Kin maidani abokin wasanki koh,? saboda muna level da'ya ni da ke koh"?

yana nufin,👇🏼

(Duk basu da aure)

"Ougsh,! Yaya da zafi."

Ya sake ta, 

"Maza hurry up ki d'akko min yunwa nakeji"."

"Ok bros, tayi saurin kawo mishi had'e da cup da d'an plate ak'asan cup d'in.'

"Thank you, sai da safe, kuma, gobe ki fad'a ma su Maryam zaku je dinner d'in bikin nan, coz yana min k'orafin baku je yau yau ba.'

"Okey yaya saura kai, dama ku biyu kuka rage"

Ta fad'a tana Mik'ewa zata gudu.'

'Ya jefa mata key d'in shi, ta fita tana mishi dariya.'

'Ahankali yake dan shan tea d'in, sai yaji gaba d'aya ya manta da damuwarshi ta d'azu, sai kuma wata sabuwa tunanin yarinyar nan dake damun zuciyar shi, abin ya fara damunshi dak'yar ya iya cin abincin kad'an, duk kuma fargarbar yadda zasu k'ara had'uwa yake.'..

'Abin ya dinga bashi mamaki, sai yake tunanin kodai yarfa sun da tayi ne, yake jin haushin hakan"?

'To ai kuma shi baiji ko da d'igon haushin ta ba cikin ranshi, hasalima wani abu yake ji na mussamman game da ita, ji yake kamar ya mik'e ya tafi nemanta.'

'Ya dafe kanshi yana tunanin wannan wane sabon abu ne ke shirin samunshi..??

👏🏼👏🏼👏🏼👏🏼




*👍🏻Karima tijjani Mansur*

*Like me on facebook @ karima Tijjani novels*

*Luv u all*😘



♥️♥️♥️♥️

*ZAZZAFAN SO*

(Masoyin k'warai)

*Cigaban littafin Zazzafan so (Guba ne)*

💔💔

*By*

*Karima Tijjani Mansur*

*(Hajeeyah Khareemerh)*

*Dedicated to unique in your love heart*

📄 *37*

*Sai* bayan magriba HAFSAH ta koma gida.. Mama na kitchen ta wuce parlour inda ta tarar da abin murna.. 

Basheer neh qaninta ya zo gida hutun makaranta.

Yana ganinta ya taho da murnar shi

"Oyoyo aunty nah.!!"

Ta saki fara,a saukar yaushe Basheer.??

"Da yamman nan."

Ya fada tare da amsar jakar ta suka qarasa shiga cikin parlourn."

Kujera daya suka zauna ta riqe haba tana kallon Basheer.

"Oh ni Basheer sai wani girma kake haka.?

Yayi dariya Yana shafa dan gemun shi daya soma taruwa, Yasan shi ta gani shiyasa tace mishi haka.

"Mene ka wani tara gemu sai kace wani babba."?

Murmurshi yayi yana kallonta qasa- qasa yace "To ai shi dinne yaya."

"Hmm baka da kunya fah.!!

Mama ce ta shigo parlour, "To sarakan hira an hadu koh?? "Nace, an kira sallah"!!

Basheer ne ya fara miqewa "Aunty bari na dawo akwai hira fa."

"Okay Basheer itama ta miqe ta nufi hanyar dakin ta."

Yau wani irin farin ciki takeji, tana son ta ganta ita da Basheer suna hira shiyasa bataji dadin tafiyar shi karatu wani garin ba..

Duhu ya fara yi lokacin daya dawo suna zaune a parlour dukan su, Hafsah, Mufida, Amira, da Zainab mama tana toilet.

Hafsah kallon Basheer kawai take tana mamakin girman shi.

"Even She's just 25 knocking 26 shi kuma 24 yake."

'Ya miqe da wani irin tsaho irin na abban su sai farar fatar mamansu, cika da kyau sun bayyana agareshi ga wani dan gemu daya ajjye dayake qara mishi kyau.

Komai nashi cikin yanga yake dole ya burge yan mata.

"How time fly? ta fada a zuciyarta yaushe tayi candy ma? Lokacin da tayi candy shekarar ta 18 cif.

Ta sami tsaikon shekara daya bata shiga Jami,a ba (Tuna baya wato zamanta gidan Mama)

Yanzu haka ta kammala digirinta a fannin _International relationship_ sabanin burinta na son zama lawyer. tna wata na qarshe ashekarar service dinta wanda takeyi a wani gidan television.

Basheer ya nemi guri kusa da ita ya zauna.

"Aunty nidai hira nakeso muyi sosai."

Ya kalli su mufida.

"Amma Nidai bana son yaran nan suji mana hira."

Amira dake danna wayar ta ta dago ido ta kalleshi, sannan ta kalli mufida suka kwashe da dariya har da tafawa."

Ya miqe yana hararar su, yaja hannun Hafsah suka nufi dakin ta.

Yana matuqar ji da ita.

"Yaya ni nama rasa ta ina zan fara."?

Ya fada bayan sun zauna a dandaryar qasa, kan carpet din dakin.

"Meya faru ne Junior naga kamar a damuwa kake"?

Ya shafa gashin Kanshi daya taru yake ta faman kyalli.

"Hmm, babu komai boko ce kawai tamin yawa."

Suka kwashe da dariya dukan su.

Sannan ya dora cikin qasa da murya.

"Sai wata Christian girl data takura min."

Hafsah ta riqe hab'a. "Uhum? Tace dashi.

"Yes Aunty, yarinyar mayya ce wallah ta takuramin she can even comes to my room fah everytime."

"Even at n night"?

Hafsah ta tambaya tana zaro ido."

Ya jijina mata kai.

Yes sister, she's beyond your expectation fah ko tsakan dare ne zata iya zuwa min, rannan fa cemin tayi dole dakina zata kwana fah."

Hafsah ta riqe haba tace "Uhum??

"Ya kayi kuma.??

"Hum ya sauke ajiyar zuciya sai da na mata jan ido ta fita."

Ya jaro wayar shi ya nuna mata photon ta, "See her, wai blessing sunan ta.

Hafsah ta qare mata kallo sannan ta miqa mishi.

Class dinku daya"? Noo amma dai faculty dinmu daya civil engineering nake, ita kuma electric amma we're in the same level. 

Level 3 take nima haka."

"Hmm."

Inji Hafsah.

Yanzu ya zakayi da ita.

Mafita nake nema aunty nah. Ya fada da marainiyar murya, "Allah bazaki gane nacin yarinyar ba, ni da na zaci abin nata wasa ne, wai a haukar ta aure na zatayi."

"Hafsah ta toshe baki tana dariya."

Bashir ya danja siririn tsaki, ya ja kwafa yarinyar class less ce sam ba aji."

Hafsah ta kalleshi "Nidai suggestions dina shine..

Bashir ya bada gaba daya hankalin shi akan ta ya zaci wani abin arziki zata fada.

Fada min aunty mene ne, ya fada a zak'e (cikin zaquwa/ so eagerly)

Hmm Tana yar dariya da siririyar muryarta tace, zan fada a labaran mu, _A level 300 Muslim student proposed to a Christian his level mate)..._

Bai bari ta qarasa ba ya tareta cikin damuwa.

Haba aunty Don Allah ki maida abin serious, wallah am seriously worried, tana hanani karatu fa kuma bana son Abba fa ya sani."

"Hmm ga mafita ma, Kawai mu fada ma abban.. 

"Oh my God.!! Ya dafe kai.

"Plz Yaya ki bari mana."

Tayi 'yar dariya ta gimtse.

"Okay, me kake ganin zaa yi. Uhum?"

Yawwa ni cewa nayi Kodai na baki number nata ki kirata kici mata mutunci, as wacce aka zaba min agida za,a aura min."?

"Umm.. Bari muga lemme think deeply gaskiya zanyi tunanin wani mafitar. 

"Okey yaya ta thank you.

Tayi murmushi.

Hmm Basheer mai 'yan mata.

Shima dariyar yayi "Haha wallah Yaya na rasa what's wrong with 'Yan mata yanzu kowa tana son ka, banda ita akwai wasu fa.. Kawai su gwara Muslim ne kuma basa takuramin as she do."

"Um kace kana sonsu kawai."

"Noo Yaya kadan ne suke burge ni cikin su."

"Hmm kaji ba."

Ta fada, Sannan ta mayar da muryata serious tace, "And plz Basheer don Allah don't ruin any girls life, and not to broke her heart kaji, duk wacce baka so ka rabu da ita Kawai salin-alin bubu wulaqanci ko bata lokaci.

Ya kalle ta a sanyaye yana gyada mana kai, yasan abinda ta tuno, yasan dalilinta na fadar haka, yasan ta dan-dana."

"Kada ki damu Yayata ba haka nake ba."

"Thanks Yayana!!" ta fada tana murmushi.

Shima murmushin yayi jin tabashi girman, duk da yasan tasan yana da son girma.

Kallonta yayi shima, cikin wata nutsuwa, ya gyara zama sannan yace, "Yaya 

Kema akwai maganar da na keson muyi dake Don Allah."

Ta tattara dkukan nutsuwarta wajen shi, sannan tace cikin sanyi.

"Wacce magana ce haka Basheer."?

Ya danyi yar ajiyar zuciya, "Um ba wata magana bace fa mai tsaho, Kawai dai tambayar ki nake son inyi.

"Ina jinka toh."

"Don Allah yaushe zakiyi aure.!"?

Ta ke Yanayin ta ya chanja, "Basheer aure kake tambayata koh, ka gaji da gani na agidan koh, ko na tare maka damarmaki (dama) dayawa ne."?

"Calm down, my dear aunty, ya fada cikin qasa da murya. "Ba fa abin zafi bane, I just asked you ne saboda mu fara shirye shirye, ya qarasa fada yana dan murmushi.

A tayi ajiyar zuciya a hankali, "Ai na zaci ka gaji da ganina ne, fah."

"Rufamin asiri ya fada yana zare ido, ya nuna kanshi wane ni in gaji da yayata."

"Dariya yaga tayi ta jin dadi." Duk da hankalinta daya kwanta amma dole ne ya qarasa mata zancen, don yana son ta dauki zancen da muhimmanci, don haka yace.

"Aunty kinsan da na dawo me Abba yace.?

Ta girgiza kai.

"Ya ganni na girma, shine ya cewa Mama wai da mace ne ni tuni na isa aure har da yarana."

Nace, "Haba Abba a village dai, shine yamin dak'uwa, wai a gidan nan ma haka neh."

Aunty kinsan na tarar dashi kafin ki dawo ya fita.

Inaji yana qara wa mama bayani after nabar wajen, "Wai Kema yaga shuru bakya wani sauraron kowa bai san meke damunki ba, Gashi even mufida ita ma ta isa aure fah."

Ya sauke waccen maganar, har yanzu idonta na kashi ko motsa su batayi..ya dora.

"Plz Yaya I don't say that kin gunduri Abba ko mu, infact ma ba zamuji dadie ba ki tafi ki barmu, but ke macece, shiyasa kika ga hakan."

Ya daga hannun shi alamar roko. "Please before Daddy talk to you about it, please kiyi making wani decision akan abin kinji, Allah nasan baki rasa masu sonki bafa kawai baki bada fuska ne."

Kinji my beautiful aunty ki daure ki manta da komai, forget your fast, wani YUSUF and wata Basma, whatever ma yanzu you're beyond their classes, ki manta dasu plz."

Sai da ya ambaci YUSUF sannan yaga tayi murmushi.

"Hmm Basheer kenan, azaton shi YUSUF ne ya hanata kula wasu?? Ita ko wacce irin zuciya ce da ita da zata iya riqe abubuwan shekara wajen bakwai baya, _Broken heart Time_

Haka ta bawa lokacin suna.

Murmushi ta kuma yi sannan tace "Hmm Basheer kenan, naji toh naji don't mind zaka ganni da aure gobe goben nan."

Suka kwashe da dariya, ta fadi hakane don kada ya dauka zancen nashi ya sa mata damuwa wanda a badini ba damuwa kadai ba, har tunanin baya sai da ya dawo mata.

"Wato tunda Abba ya sake ya bayyana haka to Lallai abin yana ranshi."

"Aunty nah, amaryar gobe bari na barki toh.." 

Ya miqe yana cewa I think Abba ya dawo lemme go and tell him gobe yana da daurin aure."

Ta kaiwa bsyanshi duka ya fice yana cewa "Amarya- Amarya.

Bata da zabi illa ta bishi parlourn ita ma Don haka ta mike.

Ahankali take tafiya, tun daga nesa take qarewa mazauna palourn kallo, so take ta karanci, halin da suke ciki.'

Abbansu ne, wanda a kujerar farko wacce take facing TV, kana ganinshi shima girma yazo mishi a qallah zaiyi shekaru 55 zuwa 57, cikar kamalar shi na nan sai ma abinda ya qaru. Akwai cigaba sosai cikin al,amran gidan a yanzu fiye da shekarun baya, kama daga kan tsarin gidan daya samu gyara sosai, akwai qaruwar arziki duk da yana dab da retire baifi saura 'yan watanni ba, bayan haka ya shiga Fagen siyasa, kuma babu laifi ana damawa dasu, suna da kyakykyawan zato su sami nasara a zab'e mai zuwa, Wanda idan hakan ta faru, gwamna zai iya bashi matsayin kwamishina (commissioner) ko kuma wani mai bashi shawara wato (Adviser)

Mamansu ta qara, girma da gogewa ta zama wata babbar mace, akwai cigaba sosai akan fannin kasuwancin da take yi. 

Kana kallonta zaka gane babbar macece da take cikin kulawa, da kuma tsari mai kyau, kuma a tsaye take kyam kan al,amran Gidan ta.

"Zainab tana level 2 yanzu inda take karanta pharmacy, a qallah zatayi shekaru, 21. 

Sai Ameera, me jiran admission, sai mufeeda da take year din qarshe a secondary.

Dukkansu babu wacce baza,a kaita gidan miji taki zama ba, ko waccen su ta girma sosai akwai wayewa tattare dasu, ta fuskar komai, amma waye wa irin ta masu ilimin addini. Suna da class amma sam ba,a taba kwatanta su da masu wulaqanci ko wani girman kai..'

Hakan ya isa abin godiya ga Allah a wajen, iyayensu sun haifi 'ya'ya kusan dukka mata, kuma sun iya da tarbiyyar su, abin alfahrin daddy ne ace cikin yayanshi har da wacce ta hadda ce al,qur,ani (Zainab) yaso hakan ga Hafsah, amma komai nufin Allah ne, domin falalar sa ce, da yake bawa duk wanda yaso."

Itama tana da izufi talatin cif, akanta, wanda ba gazawa ce ko wani abin makamancin ta, ya hanata karasawa ba sai dai abin na Allah neh..'

Sauran suna iya kokarin su don suma suna karatun daidai gwargwado ciki harda Basheer.

Kullum fatan iyayensu shine Allah ya kawo musu miji na gari. Duk da ba su rasa masu sonsu ba sai dai abin komai lokaci ne.

"Yayah, ? Abba ya kirata kamar yadda ya saba karanta ko yaushe.

"Na,am Abba."

Yau Basheer yaxo koh, ana ta hira."

Tayi murmushi.

Kin gaji koh"?

Ta daga kai alamar "Eh"

"To aje aci abinci a kwanta koh tunda ya cika ki da hira ya fice koh."?

Dariya ta danyi, tabbas tana son ta kwanta ta huta.

Kitchen ta wuce, cike da farin ciki tana son wannan kulawar da take samu awajen abban ta, bata jin wani daga cikin su yana samun irinta, dole ta yi abinda zai dinga faranta mishi rai shima indai tana son ta dace da rahmar ubangiji.

Kad'an ta zuba abincin, ta fito ta sami guri akan center carpet kusa da, zainab da take fama da litattafai ta zauna. 

Mama ta kalli plate din, "Shikenan dan abincin da zakici Hafsah."?

"Banajin yunwa sosai mama."

Bama ta cinye abincin duka ba, ta tashi ta mayar kitchen, sannan ta musu sallama ta shige dakin ta, wanda mallakinta ne ita da mufeeda har yanzu.

Yayin da Ameera da Zainab suke da d`aki d`aya, sai dakin Basheer shi kad`ai.

Sallar isha ta fara yi sannan ta cire kayan jikinta ta mayar dana bacci.

A gajiye ta haye gadon ta kwanta da tunanin fal cikin zuciyar ta.

"Lallai maganar Basheer, abar dubawa ce, abin yana tsorata ta idan ta tuna wai ita ce me shekara 25, a duniya, lokaci yana matuqar gudu, bata tab'a zaton zata kawo irin wannan lokacin baa gidan mijinta ba, tasan haka ma burin Abbansu yake. 

Mates dinta da yawa anyi aurensu, ciki harda Aisha, wasu ma harda yara biyu harda masu uku, amma ba ta taba sawa ranta damuwar hakan ba, tunda tasani kowa da yadda Allah ya tsara mishi tashi rayuwar.'

Bazatace bata da masu sonta ba ko kuma wanda taji yayi mata, amma xata iya cewa zuciyar ta rabu da son wani D`an adam, kwatankwacin irin son da ta yiwa Yusuf, ko da rabin hakan ne.

Sai muka wani abu da ake cewa _"Ko wacce kwarya..._

Ita ba raina arziqi bace ko kuma buri da son abin duniya, amma ya zama wajibi ta duba wanda zasu samu daidaito, Domin shi zaman auren ba wai zamane na wata daya ko shekara ba, zama ne na din-din -din, ta yuwu tun kana iya jure tsanani da hakuri, har azo _level_ din da zakaji bazaka iya jurewa ba."

Saboda haka ita ba sauri take ba sam, abbansu ya hore ta da gudun gaggawa acikin al,amra.

Har tana tuna wata magana da take cewa, _''One day it will just happens, you will meet the one that will love you the way you deserved to be love, and you no longer have to fight for it.._

In ta tuna tana samun nutsuwar zuciya, da hakan, kuma tasan Tabbas wata rana zata iya samu, kasancewar tasha haduwa da wadanda kai tsayen zata iya cewa basu dace da ita d`in ba ta fuskar mu,amala, suna mata kamanceceniya da irin ta Yusuf, ko kuma ta fuskar dabi,u da Yanayin fahimtar rayuwa.

A haka har ta tattara su ta watsar ta mayar da hankalinta gabadaya kan karatun ta wanda dashi take fatan gina feature dinta.

To irin haka ce tayi ta gara rayuwarta da zamaninta, har kawo yanzu, da shekaru suka shud`a ba tare da ta ankare ba, amma yanzu bulaliyar da Basheer yayi mata ta farkar da ita, cewa Tabbas akwai buqatar ta matsa ta bawa 'yan baya waje, suma suci nasu zamanin. 

Don da tuni ma Ameerah tayi mata tsallake, sai aka samun akasin tafiya k`aro course da mijin da ta samu yayi wanda zai kai shekara d`aya, zuwa da rabi, da tuni ansa rana, kuma abinka da itama karatu take sai duk ba,a damu ba.

Da ire-iren qananun tunanin nan ta fada kogin tunanin tuno rayuwarta ta baya wato shekarun zaman ta gidan Mama, wanda ta kirasu da shekarun gwagwarmaya....







Muje zuwa.👍🏼



♥️♥️♥️♥️

*ZAZZAFAN SO*

(Masoyin k'warai)

*Cigaban littafin Zazzafan so (Guba ne)*

💔💔

*By*

*Karima Tijjani Mansur*

*(Hajeeyah Khareemerh)*

*Dedicated to unique in your love heart*

📄 *38*

*Zaman* ta gidan Maman Ya Nazeer, zama ne da zata iya fassara shi da "Zaman qaruwa da qarin ilimi tare da samun experience akan rayuwa.

Zama ne wanda bata samu takura ba sam a yayinsa, sai ma tattalinta da aka dinga yi sam baa son kukanta.

Idan Hafsah zatayi lissafin mutane muhimmai wad`anda suka taka rawa a rayuwarta to tabbas daga abbanta, sai mamanta sai kuma yayar mahaifiyarta wato maman Ya Nazeer, kamar yadda suke karanta..

Bawai don sun dauki tsahon lokaci tare ba, a,a sai dai taimakon da ta bata na tsahon wata uku kacal, amma shine zatace ya tallafi rayuwarta har kawo yanzu, wanda badon ita ba da tuni ta zama wata abu ta daban ba Hafsar da take ayanzu ba."

To dama hakane, wad`ansu mutanen suna da irin wannan baiwar, wad`anda zama kad`an zakayi amma ka qaru da abinda zai tallafe ka har qarshen rayuwa.

Maman ya Nazeer, ta jata a jiki, ta dawo da ita hayyacinta lokacin da ta fita daga cikin shi, ta nuna mata cewa tana da da ma lokacin da tayi losing duk wai hope nata, _she lost hope and she's completely broke._

Bata taba tunanin zata iya rayuwar da babu Yusuf cikinta ba, sai gashi maman ta nuna mata cewa zata iya kuma ta koyar da ita yadda zata iya d`in, kuma gashi ta iya d`in.

Dole ne ta gode mata bisa wannan d`au ki data kawo mata cikin rayuwa wanda bata da abinda zata saka mata dashi banda addu,a.

Shiyasa wani lokacin Hafsan, ke tuhumar kanta da laifin _butulci_ na bujerewa Soyayyar Gudan jinin matar da ta tallafi rayuwarta.

Amma takanji sassauci idan ta tuna cewar kai tsaye, Maman bata da masaniya bisa hakan sai dai hasashe, kuma baza,a iya cewa tak`i Nazeer kai tsaye bane, sai dai ace tak`i bada fuska gareshi yadda zai shigar da buk`atar sa, har ya gaji ya haqurar wa zuciyarshi.

Ahankali take tuno abinda ya faru.

#TUNANIN #BAYA

Wato bayan isar su gidan ita da Mama a wancan lokacin sun isa gidan babu kowa cikin sa, kasancewar yaran sun tafi makaranta.

Driver ne ya shigo mata da kayanta, inda Maman ta nuna mata wani dak`i mallakin yarta Fatima tace "Kai kayan naki wancan dakin."

Ta miqe a hankali, ta ja trolley din ta nufi d`akin.

Sun yini su biyu ita da maman cikin nishad`i har Maman ta sa ta tayi musu girki, sai wajen qarfe biyu da rabi sannan yaran gidan suka fara dawowa.

Da farko Nazeer ne ya shigo wanda shine babban d`a a gidan, sai fateema mai binshi, sai Al,ameen, sai Nour, sai Siddiqa.

Hafsah ce kadai a palourn ta qurawa TV ido, Ahankali yayi sallama, da takarda a hannunshi ta dago kai ta kalli mai shigowa, ta amsa sallamar, sannan ta kauda kan ta.

Murmushishi ya fad`ad`a, "Hafsy ce yau a gidan namu."?

Tayi murmushi, Nice "Ya Nazeer ina wuni."? Ta gaidashi tana mai dan duk`awa daga kujerar da take.

Ya sakar mata murmushi sosai, yarinyar akwai tarbiyya ga Ladabi, lpia lau, Hafsah, ya mama Ina su zainab"? 

"Suna lpia lau."

Ya qara kallon ta.

"Ina Mama nah"?

Ta kalleshi so take ya qara bayani ko zata fahimci zancen, wacce maman yake nufi.

Taji abinne banbarakwai babba dashi yana cewa Mamanshi.

"Ina Mamy nah nace."?

"Uhum. Maman ku."?

Yayi `yar dariya. 

"Yes, mamy nah, ai mamie tawa ce ni kad`ai k`wace min akayi aka min rubdugu."

Hafsah bata ankara ba sai jinta tayi tana k`yak`yata dariya, a zuciyarta tana cewa dama haka Ya Naseer din yake da hira.?

Ta sani dai yana zuwa gidansu, amma bai fiya jimawa haka ba, kuma ita bata cika zuwa gidansu ta kwana ba, idan ma tazo yawanci yana school.

Dariyar su Mama ta jiyo ta fito zuwa a palourn. "Oh dama nasani ai sai kai."

Ta fad`a tana kallon Nazeer d`in.

Yayi kanshi mazauni a kujera kafin yace a shagwab`e Mama wai Taraba suka tura ni."

"Taraba"? 

Mama ta maimaita, 

Kuma kana so."?

Ya girgiza kai, gaskiya A,a Mama nafison koda jigawa neh."

Okay zanyi yiwa sunusi magana, tana nufin qaninta wanda shi maman su Hafsah ke bi."

"Okay mamy na Nagode."

"Mamy yunwa nakeji." ya fada yana dan shafa ciki."

Sannan ya miqe ya nufi, Kofar fita daga palourn domin dakinshi yana daga waje ne.

Mama ta bishi da kallo, sannan ta kalli Hafsah.

"Ikon Allah kinga ya fice, tashi ki zuba mishi abincin kafin ya dawo kinji."?

Toh Mama ta miqe ta nufi kitchen din.

Plask ta samu guda biyu, ta zuba abinci a babban dayan kuma tasa miya, sannan ta shirya komai kan tray, lokacin data fito Maman bata palourn kawai sai ta ajye akan dinning, kusan minti uku bai dawo ba, sai ta jiyo muryar Mama nacewa, "Hafsah ki miqa mishi abincin kinji don da kyar idan zai dawo.

"To, kawai tace, ta kinkimi tray din tayi dakin shi.

Ad`an ka re taga k`ofar don haka tura wa kawai tayi ta shiga da sallama.

Daga cikin wani daki a dan palourn ta jiyo an amsa inda ya fito ya tarar da ita da kayan tray a hannu, aiko yace me zaiyi idan ba dariya ba.

Ya k`ame yana kallonta yana ta qyaqyata dariya yana nuna ta har Hafsah ta tsorata.

Sannan ya gimtse ya fara magana, cike da shaqiyanci,

"La-la-la-la, gaskiya kina so mama ta zane ni kenan.

ta kalleshi ad`an tsorace sannan ta qara kallon tray d`in.

Ya sa Hannu ya amshi tray d`in ya ajye sannan ya cigaba da magana k`asa-k`asa.

"Wa yace miki anan Mama ke zuba min abinci."?

"Ai Matsayina bai wuce wannan ba."

Ya d`auki plate daga kan tray d`in yana nuna mata.

"Anan ake zuba min abinci kin manta bani ne mai gidan ba." Ya Qarashe zancen yana zaro idanunshi.

D`an murmushi tayi a qagauce, saboda gaba d`aya ji take kamar akan qaya take.

"Bata saba ba sam, ace wai gata ga wani namiji, tsaye irin haka daga ita sai shi, idan aka cire Yusuf, da shi kuma ta bashi wani Matsayi na daban.

Bata da yayye maza, sannan ba wasu mazaa ke shigo musu gida ba har su sami damar hira dasu, idan ka d`auke auncle Abdullah, sai shi Nazeer d`in, sai wad`and`a ba,a rasa ba cikin `ya`yan `yan uwa suma kuma jefi-jefi ne. Su a familynsu ma mata sunfi yawa.

Sannan bata son maman ya Nazeer, taga ta dad`e, don haka ta motsa K`afarta da niyyar juyawa ta tafi amma sai ya katse mata hanzari da cewa.

"Ni al,majiri ne a gidan." Ya fad`a da marainiyar murya.

"Please zubamin, a plate sai ki tafi da sauran."

Ranta bai so hakan ba amma bata da zab`i tana bashi girma a matsayinshi na Yayansu.

Ta tsuguna, da sauri sauri, take zubawa, ta cika plate d`in.

"Kaii ai bazan cinye ba rage min."

Ta kwashe wajen kwatar (quarter) abincin.

"Yawwa ko kefa."

bata ce komi ba tasa mishi miya da nama tasa mishi salad.

Sannan ta d`auke ruwan da ke kan tray d`in ta ajye mishi sannan ta d`auki tray d`in.

Tana lura da kafe ta da Ido da yayi.

"Thank you Qanwaty!

Taji ya fad`a 

Bata ce komai ba ta juya tana sak`e sak`e a ranta.

_"Anya kuwa zata yarda, tayi koda  kwana uku ne agidan nan bare kuma sati, matuqar za,a dinga zata ayyukan hidima irin wad`annan."??_







📝 

*HAJEEYA KHAREEMERH*


♥️♥️♥️♥️

*ZAZZAFAN SO*

(Masoyin k'warai)

*Cigaban littafin Zazzafan so (Guba ne)*

💔💔

*By*

*Karima Tijjani Mansur*

*(Hajeeyah Khareemerh)*

*Dedicated to unique in your love heart*





📄 *39*





*Tana* komawa palour, fateema ta shigo ita ma da sallama, Hafsah ta amsa cike da farin cikin ganinta.

Itama da gudu ta qaraso ta rungume Hafsah tana murna da ganinta.

"Hafsy yau kece a Gidan namu."?

Hafsah tayi murmushi ita ma, Nice wallah auntie Fateema."

Fateema ta sake ta tana fad`in "Gaskiya naji dadie."

A palourn suka zauna suna hira, Fateema ta miqe taje ta zubo abinci ta dawo tana fad`in.

"Wata irin yunwa nakeji wallah."

"Sannunki.!!"

Hafsah ta fad`a tana qara kallonta.

"Level 3 kike koh auntie."?

( _Da ke ta girmi Hafsah da wajen shekaru uku._)

Eh, wata test mukayi mai zafi wallah."

Ta fad`a tana kai lomar abinci bakinta.

"Ke fa, kinyi candy kema koh."? 

"Eh result nake jira."

To Allah ya bada sa,a. 

"Amin."

Suna hirar, Ya nazeer ya qara shigowa, kamar tare suka shigo shida ragowar yaran gidan. Wad`anda murnar ganin Hafsah yasa suka cika gidan da hayaniya.

Ya Nazeer, shima da tashi hayaniyar ya fara musu magana, "Haba cai cai cai cai, kun dawo ai."

Mama ce ta fito itama, lokacin Fateema na tambayar Hafsah.

Amma dai kwana zakiyi koh."?

Mama ta cafe, "Ai Hafsah nan da sati biyu ma tana nan."

Wani murmushi Nazeer yayi, "Kice mun qaru a gidan."

Mama, tace sosai ma, ai kasan tayi candy fah."

Ya qara yin murmushi "Allah Mama."?

Sannan ya kalli Hafsah, sam bashi take kallo, ba. "Congratulations sister."

"Thank you."

Tace mishi nan aka barke da hira.

Mama ta kalle su, zan d`an fita.

"Fateema, Hafsah ku kula da gidan."

"To mama a dawo lpia."

"Tare Mama suka fice, ita da Nazeer don shi zai driving dinta.

Fateema taja Hafsah d`akin ta suka kule suna hirar Yaushe gamo."

Har dare mama bata dawo ba, sun gaji da hira sun dawo palour, suna kallo.

Sai can maman tayi sallama ita da Nazeer da kayi niqi niqi irin na amfanin gida.

Mama kenan _mace me kamar mazaa_, a kalla zatayi shekara Arba'in da biyar. 




Mijin ta Alhaji Dalhatu ya rasu shekaru uku kenan da suka wuce, ya barta da yara biyar, uku mata biyu mazaa.

To kasancewar a gajiye maman ta dawo bata samu zaman hira sosai da su Hafsah ba, taje ta kwanta babu jimawa bacci ya d`auke ta.





Da daren Hafsah suna kwance a d`akin Fateema, Hafsan tai jugum tana tunanin Basma da Yusuf. Su suna can suna jin dadin rayuwar su ita kuma sun barta nan cikin k`uncin zuciya.

"Aunty Fatee, Don Allah ara min wayarki."

Hafsah ta miqe kamar an tsikare ta tare da fad`in hakan.

"Okey ungo."

Fateema ta miqa mata wayar.

Hafsah ta zana number Yusuf a ciki sannan tayi saving. Kafin tace, "So nake kawai naga mai number d`innan a online."

"Hira zakuyi"?

Cewar Fateema.

Hafsah ta girgiza kai, "Aa dai kawai sa number zanyi, idan lokacin da za,ayi magana yayi zan miki magana.

"Tom."

Inji fateema.

Ai kuwa sai ga photon, shi a profile.

"Aa wannan ne me number."?

Fateema ta tambaya cikin zumud`i.

Hmm kawai Hafsah ta fad`a ta kafe photon da ido zuciyarta fal da bak`in ciki yaya ma za,ayi tayi sakacin da zata barwa Basma Yusuf, ai impossible.

"Gaskiya ya hadu fah."

Cewar Fateema, wacce fad`in hakan ya qara tun zira, Hafsah. Sai kawai ta miqa mata wayar ta kwanta cike da tashin hankali.

Dole ta nemi mafita, kuma ta tashi tsaye, tunda ana nema afi k`arfinta.

Wani abu ya maqale mata a mok`ogoro, zuciyarta ke wassafo mata basma, da irin rainin da tayi mata har yasa ta mata _Snatching_ mafi muni.

A kullum ta tuna bak`in ciki ne ke qara cika mata zuciya had`i da wata qiyayyar basma mara misaltuwa, bata taba jin ta tsani wani ba sai a kanta.

Nunkuwar tsanar kuma yana da alaqa da rashin samun damar daukar fansa _revenge_ ko yaya neh." Shiyasa abin ya tsaya mata arai, data tuna bata da wata dama fa. Kawai sai ta fashe da wani kuka me cin rai."

Fateema ma na cikin qarewa photon kallo kafin tabi Hafsah da kallo cikin mamaki, da damuwa, gaskiya akwai abinda ke damunta.

Cikin in,ina take fad`in "Ha.. Hafsah me menene."? Me akayi miki don Allah kiyi shuru.

Kukan take sosai ko zata sami relief. 

Fateema tayi cilli da wayar ta matso kusa da ita tana lallashinta.

"Kiyi hakuri don Allah, me aka miki ko nice."? 

Hafsah ta girgiza kai. 

Mama ce."?

Nan ma ta girgiza kai.

Ya Nazeer ne."? Shima ta girgiza kai.

Sai da ta tambayeta 

kowa na gidan amma tace babu kowa.

To wanene."?

Fateema an cuce ni, anzalince ni.!"

Ta kuma rushe wa da kuka.

Hakan ya qara rud`a 

Fateema.

To wanene Hafsah kodai in kira mama ne."? Ta fada tana qoqarin miqewa.

Hafsah ta ruqo ta.

Cikin kuka tace, kada ki fada mata don Allah ki kyaleni kawai nina san abinda aka min."

"To ki daina kuka, ki fad`amin menene, ko kuma in kirata."

Da kyar dai Fateema ta samu Hafsah tayi shuri amma fir tak`i fad`a mata komai sai ajiyar zuciya take. "Ki bari kawai, take iya ce mata.

A haka sukayi bacci, wanda ga Hafsah ba bacci ne kad`ai ba, bacci ne me cike da mafarkai, na Yusuf da Basma, marasa dad`i.




Da safe Fateema, tayi shirin makaranta, dukan su na palour banda Hafsah da take ta bacci.

Fateema taso fad`awa mama as abinda Hafsah tayi da dare amma tana sauri.

Sai da yamma bayan ta dawo suna zaune ana hira kawai mama, ta tashi ta shige d`aki, minti kad`an kuma sai ta k`wallowa Fateema kira.

Fateema ta miqe ta bita d`akin.

"Ina son dama inja miki kunne tun jiya sai kuma na manta."

Maganar da mama ta fara da ita kenan.

Bbu shiri Fateema ta tattara dukkanin nutsuwar ta ga Maman.

Mama ta d`ora, "Koda wasa kada ki sake ki ara wa Hafsah wayarki ta kira wani, saura kuma kiyi sakaci ta d`auka."

Dam! gaban Fateema ya fad`i jin wata doka mai tsauri irin ta mama.



Anya ta sanar da ita gaskiya kuwa, cewa Hafsah ta riga da ta ari waya."? 

Bare har ta fad`a mata zancen Kukan da Hafsan tasha jiya.

Idan hakane da akwai alamar tambaya kenan game da zuwan Hafsah gidansu, dama abin ya bata mamaki, don Hafsah bata wuce kwana d`aya a gidansu amma wannan zuwa na bazata, don mama sam bata musu zancen zuwan hafs

Idan haka ne Akwai abinda ya faru.

Don haka ta yanko tambaya tare da d`agowa don yiwa maman amma sai ta d`aga mata hannu.


   📝 

*HAJEEYAH KHAREEMERH*


♥️♥️♥️♥️

*ZAZZAFAN SO*

(Masoyin kwarai)

*Cigaban littafin Zazzafan so.*

*(Guba ne )*

  💔💔


*By:*

*Karima Tijjani Mansur* 

*(Hajeeyah khareemerh)*

*Dedicated to Unique in your love heart group members.*




📄 *40*





*Kada* ki tambayeni komai."

Kawai ki bi abinda nace.

"To mama."

Fateema ta amsa cikin ladabi.

Tashi kije ki turo min Hafsan.

To mama.

Ta miqe ta fita, ta sanar da Hafsah kiran mama.

Ta shigo cikin nutsuwa, doguwar riga ce a jikinta ta atampha.

Ta durk'usa a gaban maman.

Mama gani.

Hajiya Nafeesa ta fad`ad`a fara,arta sosai.

"Hafsa na. Ya naga duk kin fad`a"?

Bata jira amsarta ba tace, "Ki saki jikinki kinji kuma ki daina sa damuwa a ranki.

Sannan ta qara kallonta, "Ai babu wanda yake takura miki a gidan nan koh."? 

Hafsah ta girgiza kai da sauri. "Aa mama babu kowa."

Tayi murmushi, Yawwa idan ma akwai ki fada min duk wanda kika ga yana damunki ko da kuwa Nazeer ne."

Mama ta qarashe zancen tana dariya Hafsah ma dariya tayi.

So Maman take Hafsah ta saki jikinta da ita tana so ne ta saba hira da ita sosai a haka har ta saki jiki ta fada mata damuwar ta."

Tana son ta gano Menene matsalar ta ita da yaron.

"Ki bani labarin makarantar ku kinji Hafsah."?

Hafsah tayi d`an 

Murmushin jin kunya.

Ko bazaki bani ba"? "Ba mamanku tace ke kike daukar 1st position ba ko ba haka bane."?

_Duk cikin sigar wasa take mata tambayoyin._

Hafsah ta d`aga kai.

"Gud girl.!!.

baki tab`a zuwa ko ta biyu bane."?

Ta girgiza kai.

"Kin taba zuwa."?

um, sau nawa sau biyu."

Na uku fa."?

Aa. 

"To na hudu fah."?

Nan ma Hafsah ta girgiza kai.

Mama tana dariya tace "To sai na biyar."?

_Tana sane tayi mata tambayar don maman Hafsah ta fada mata komai._

Sai Hafsah taji kunya ta shiga boye fuskar ta cikin cinyoyi."

"Ahh, Hafsa kice kin taba zuwa ta biyar d`in."

"To garin yaya."?

Shuru babu amsa.

"Wasa kika tsaya."?

Nan ma shuru.

"Ki d`ago me yasa kike jin kunya."?

Hafsah ta dago tana noqe-noqe.

Kinaji nah."? 

Ta d`aga kai.

"Ki daina yin abinda zaki zo kiji kunya, ko kizo kiyi dana sani."

_"Kinga yanzu kin bata record d'inki."_

"Kin ga da tuni, idan kina bawa Yaranki ('ya'yanki) labari, _you claim and proud that_ baki tab'a tsallake na biyu ba koh."? Amma yanzu kin bata abin."

Mama ta fada da muryar nuna damuwa.

Ran Hafsah ya cika da kishin abin, _Tabbas ta tafka asara ba komai bane kuma sai don dalilin biye wa basma da son farin cikin ganin Yusuf._

A hankali idonta ya cika da kwalla ganin sam bata ribaci hakan ba illa bata record dinta da sukayi kamar yadda mama ta fad'a.

Mama ta lura da kwallar, duk da Hafsah taki barin ta ta zuba.

A hankali ta girgiza kai tace, "Me abbanku yace miki a time d`in daya ga result d`in.

A kunyace tace, "Yayi min fad'a yace kada na sake sakacin yin hakan."

"To Ke me yasa kikayi hakan Uhum."?

"Kina tunanin wani abu neh."?

Hafsah ta girgiza kai.

"To menene.. fad`amin me yasa kakai failing a lokacin."

Ta qara yin shuru.

"Wasa kuke koh.? Kin chanja qawaye koh, kuna zaman hira."



Gaban Hafsah ya fad'i, ya akayi Maman ya Nazeer take neman baro jirginta."??

"Kinyi shuru Ko ba haka bane."?

Bata da amsa, sai kawai maman ta bar zancen ta shiga wani.

Me yasa kike batawa mamanki rai."?

A hankali ta girgiza kai, "babu komai.

Babu komai amma kike yin abinda bata so."?

Idan mama ta lura fuskar Hafsah tayi rauni lokacin.

"Me yasa kike fita bada saninta ba."?

Duk Cikin qasa da murya maman take magana.

"To rannan ina kukaje ke da qawarki."? 

Gaban Hafsah ya fad'i, wannan fita ta zame mata jaraba. Sam ta tsani a tambaye ta ina taje."

Bayan inda taje d`in ba alkhairi ta ganowa kanta ba.

Ehe."? _Inji mama jin tayi shuru._

"Asibiti mukaje dubiya."

Wanne asibitin."?

Uhum.. A ina yake."?

_Hafsah bata iya qarya ba don haka ta kasa qirqiro amsa._

"Kin sami babu kyau sabawa iyayen koh."?

Tame daga kai.

To ki daina yin abinda zai b'atawa mama da Abba rai kinji.

"Tom."

_Ta fad'ad'a murmushi._

"Yawwa hafsy, gobe zaki raka ni wajen gyaran jiki na."

Ko Bakya son muje."?

Hafsah taji dad`in hakan sosai don haka cikin fara,a tace "Inaso mama."

"Yawwa jeki wajen su fateemah kuyi hira."

_Ta miqe ta fita mama ta bita da kallo._

Da daddare suna zaune suna kallo, Nazeer ya shigo ya zauna cikin su.

Abinda Mama ta lura dashi shine, kwana biyu Nazeer nason ya zauna cikin su ya dad'e musamman da daddare.

_Bata raya komai aranta ba._ 


A gurin Hafsah kuwa zaman nashi takura ce a wajenta. _Domin indai ya zauna sai ya tsokane ta, ko yayi ta janta da hira. Gashi tunda tazo gidan duk wata hidimar shi ita yake sakawa, Kama daga zuba mishi abincin, d`akkon kaza-da-kaza._


Amma banda haka tanajin dad`in zaman gidan sosai da sosai banda damuwar dake cikin ranta.

Yanzu ba yusuf ne kad'ai damuwarta ba, a,a harda damuwar Basma, so take ta d`auki fansar abinda tayi mata ko dan ta rage damuwar abin aranta.


_Da Wannan alwashin, ta kwana a ranta._


Gefe guda tana jin takaicin ledar kyautar ta da ke wajen maman Ya Nazeer, damuwar ta wayar dake ciki, da tana wajenta tabbas sai ta yi amfani da wayar ko mai zai faru kuwa, sai ta kira Basma ta huce fushinta akan ta. 

Ita da zata ganta ma babu abinda zai hana ta illatata.

Ta rasa me ya hanata d'aukar mataki a lokacin. Ko kuma lokacin bata da kwarin guiwar yin hakan. Saboda taga abinda zuciyar ta bata tab`a wassafo mata faruwar abu mai kama da hakan ba.



Tayi kwafa, yayin da Fateema dake karatu, ta bi inda take kwance da kallo, sam ta zaci Hafsah bacci take.




Washegari da safe tun wajen qarfe 11:00 na rana, Hafsah ta shirya ita da Mama suka fice zuwa wajen gyaran jikin Maman.




_Fateema`s touch_

Sunan wajen kenan, ya had`u sosai, ana gyaran jikin amare, gyaran gashi, wankin qafa da sauransu.

Lokacin da suka je, ana ta yiwa wata amarya gyaran jiki, suna kwa shigowa ma,aikatan wajen suka hau gaida Mama, wacce suke kira da Mommy. Cikin fara,a ta dinga amsawa sannan ta wuce ciki. 

Akwai wani d`an office madaidaici wanda yafi kama da palour, nan suka shiga maman ta zauna a kujera, Hafsah ma ta nemi waje ta zauna. K`amshi ne kawai ke tashi, gefe ga _show Glass_ turaruka ne aciki da humra duk na siyarwa.

"Baki tab'a zuwa wajen nan ba koh."?

Mama ta tambayi Hafsah dake faman kalle-kalle. Ita dai wajen ya burgeta sosai.

Tayi murmushi, "Mun taba zuwa da Mamanmu sau biyu, cikin nan ne dai ni ban tab`a shigowa ba."

Suna hirar aka k'wank'wasa kofa, mama, ta bada izini a shigo.

Lemo tazo ta ajye musu, sannan ta fita.

"Kisha lemon kinji Hafsah na ko kina son ki fita kiyi kallo."?

Ta d`aga kanta.

"To kisha sai ki je ki kalla.

"Tom."

Anyiwa mutane biyu gyaran k'afa dana gashi, wato _Saloon_ za,ayi wa ta ukun kenan mama ta sa aka kira mata Hafsah.

Ta miqe ta tafi kiran.

Tanajin dad`in zaman har suna ta hira da ma,aikatan wajen.

"Mama gani."

"Zauna kici abinci." Mama ta nuna mata abincin da ta musu order aka kawo.

Ta fara ci kenan, maman ta miqe ta fita, zagayawa don ganin meke gudana.'

Babu dad'ewa kuma maman ta dawo Hafsah nacin abincin tana janta da hira so take tayi mata wasu tambayoyi masu muhimmanci.

" `Yan mata kinga Yenda ake gyaran jiki koh."? 

Hafsah tayi murmushi, 

"Ko kina so ayi miki."?

Hafsah na murmushi ta d`aga kai alamar Eh."

"To anqi d`in sai dai anzo bikinki ayi miki yanzu sai dai ayi miki a fuska kawai." 

Cewar mama cike da zolaya.

Hafsah ta sinne kai alamun jin kunya.

"Ai kina da saurayi koh."?

Hafsah tayi murmushi jin kunya tana girgiza kai alamar a,a.

"Gidanku!! kina da dashi mana."

"Bani da shi.!!

"Au kikayi magana ko toh kina dashi."

"A,a mama" tayi maganar tana 'yar dariya.

"To wanda ya baki ledar nan fah."?

Ehe."? Inji Hafsah, ta ke yanayinta ya chanja, zuwa damuwa.

"Am um, ba saurayi na bane."

"Hmm, koh."?

Hafsah zaton ta mama ta yarda don haka qara d`aga kai alamar tabbatar wa.

Mamanki tasan da ledar."?

"Aa."

"To meyasa baki nuna mata ba..?

Bata da amsa don haka tayi shuru.

"Kiyi magana mana Hafsah."?

"Babu komai."

Kinga irin laifin da kike koh."?

"Daga yau kada in qaraji kin qara yin laifi me kama da wannan."

"Ta d`aga kai alamar, Toh."

Mama ta d`ora, "Kin ce ba saurayin ki bane, amma meya kaiki amsar kyautar shi, kuma meya sa kika karb`a."?

Hafsah tayi shuru tana tuno amsar da zata bayar.

"Um, am wallah.. hi, ba saurayi na bane."

To menene had`in ki dashi.

"Ni..ni bana kulashi yanzu." ta fad'a cikin in`inah..Fatanta kawai mama ta yarda da zancen ta."

_An kusa zuwa inda mama take son azo don haka tace:_ "To me yasa kika daina kulashi meya had'a ku."?

Ai k'iris ne hafsah bata sa kuka ba.

Take muryata tayi rauni, har rawa take yi.

"Babu abinda ya had`a mu."

"Hmm, kina wasa dani koh."?

"Aa Mama."

"To ki fada min gaskiya."

Shuru babu magana har wajen wucewar muntuna wajen biyu. Sai Hafsah dake faman kokawa da qwallar dake son zubo mata."

"Kawai na daina kula shi ne saboda mama bata so."

"Mama bata so, to meyasa."?

Mama ta tambayeta da sigar irin tayi mamakin maman ne."

Tasan ba zata sami amsa ba, don haka tayi amfani da damar wajen cewa, "Shine kuka fita dashi ranar bikin abdallah koh."?

Gaban Hafsah yayi wata mummunar fad`uwa, ta k'osa wannan lokacin ( _Moment_) d`in ya shud`e, ta gaji da tambayoyin, don ana neman qureta.

Mama bata jira amsarta ba ta d'ora.

"Kinga dalilin d`aya sa mamanki ba ta so koh.. Meyasa zaki bishi wani waje."? Ke aganinki ya dace kiyi haka."?

Cikin nadama Hafsah ta girgiza kai.

"Duk mutumin da bazai taya ki yiwa iyayenki biyayya ba, ki rabu da shi kinji." 

Hafsah ta d'aga kai alamar Toh."

Sai wajen la,asar suka tafi gida wanda a hanya tunanin Hafsah ya kasu kashi-kashi, wanda yafi tsaya mata a rai shine, nasihar mama, sai kuma jin asarar barin Basma, haka taci bulus. Dole ta bata mata rai ita ma kamar yadda tasa ranta dana iyayenta b'aci.

Sunje gida da daddare, mama ta kira fateema d'akinta, so take ta sa Fateeman wani aiki akan Hafsah.

"Fatee, kun tab'a wata hira ne da Hafsah, wacce tayi kama data samari."?

Fatima ta tsorata da tambayar don haka ta bud'e baki, gwara ta fad'awa Maman gaskiya kada taje tayi laifi don da alama akwai babban case wanda yake faruwa.

"A,a mama, saidai ta ari wayata tasa wata number, ta duba a Whatsapp amma bata kira ba kuma batayi magana ba."

"Me yasa baki fad`amin jiya ba."?

Mama ta tambaya da fad`a-fad`a.

"Kiyi hak`uri mama, bayan ta sa number sai ta tsaya kallon profile d`in kuma sai ta fashe da kuka."?

"Kuka kuma."

"Eh Mama."

"Amma duk kika k`i fad`amin koh."?

"Mama kiyi hak'uri."

Kada ki sake boye min abu makamancin wannan, tashi ki d`akko wayarki ki nuna min photon yaron..

Kafin na fad`a miki abinda zaki min..."

Nan Fateema ta miqe ta nufi d`akinsu don d`akko wayar.




Acan D`akin kuma, Hafsah ganin ita kad`ai ce a d'akin sai tayi alwashin kawai aiwatar da abinda zuciyarta ke raya mata, don ta sami dama, tana gudun kada ta wuce ta.



Cikin zafin nama ta d'akko wayar dake gefenta, ta danna wasu numbobi, ringin d`in har ya katse ba,a d`aga ba, ta qara dannawa karo na biyu. 

Wannan karon an d`aga.

"Hello."

Aka fad'a daga can b'angaren.

Cikin kaushin murya, Hafsah ta fara magana.


"Hi Master of snatching H. Habeeb Hamid ke magana.!!

"Hmm, I already know it's you _good for nothing.!!_

Kada ki d'auka abinda kika yi kinci bulus, karuwar gida kawai.".. Bata bari ta sami kalmar mayarwa ba ta d`ora.. _"Ashe ke b'arauniya ce ban sani ba, b`arauniya, mai sace samarin mutane, yar iska mara tarbiyya._

"Haha Haha, dariyar basma ta cika kunnen Hafsan, 

_"I already know zaki fadi irin haka tun ba yau ba loser.!!_

"Kiji kawai da rashin Yusuf da bazai kara dawo miki ba, idan kuma kina son ki tabbatar gobe k'arfe shida mu had'u _Garden_ idan kin isah.


"Qarya kike mayaudariya...


Iya zancen da kunnen Fateema yaji kenan anayi a wayar ta sanda ta shigo d'akin da azama ta warce wayar,

"Wacece..wacece mayaudariya.."??

Wa kika kira a wayata.. Me.. me yasa haka Hafsah."???

_Cikin in'ina fateema ke magana.._






  📝 

*HAJEEYA KHAREEMERH*

♥️♥️♥️♥️

*ZAZZAFAN SO* 

(masoyin k'warai )

*Cigaban littafin Zazzafan so*

*(Guba ne)*

💔💔

*By:*

*Karima Tijjani Mansur*

*(Hajeeyah khareemerh)*

*Dedicated to Unique in your love heart group members.*



I DEDICATED THIS PAGE TO YOU _(RUKKY NAILA GROUP 1)_ SURELY YOU ARE A TRUE FAN..  😊






📄 *41*





*Ki kyaleni..* Ni ki kyaleni.. Wallahi bazan rabu da ita ba, bazan bar mata shi ba.!"


Abinda Hafsah ke fad'a kenan cikin kuka, yayin da Fateema ta riqe ta a tsorace.

"Kiyi hak'uri Hafsah don Allah ki fad`amin me ya faru, wa kika kira.?


Cikin kuka tace "Nidai, kiyi hak'uri na daukar miki waya, amma ki kyale kawai.

Fateema taga bada da lokacin b'atawa don mama na jiranta don haka ta wuce zata fita. Ta kai bakin k`ofa kenan ta jiyo Hafsah na magana.

"Don Allah kada ki fad'awa mama, nayi kira a waya."

"To kawai fatima tace ta fita."

"Me Hafsan keyi."?

Mama ta tambayeta tana zama.

Cikin son rufawa Hafsah asiri fatima har zuwa sanda zataji aikin da maman xata sata don haka tace, "Babu komai tana kwance ne."

"Tom, muga yaron."?

Fateema ta budo profile d`in yusuf ta miqawa mama.

Muntuna uku tana qare wa Yusuf kallo, sannan ta miqo mata tare da jan siririn tsaki.

"Daga ganinshi bashi da cikakkiyar tarbiyya.!!"


Ita dai fateema kallo tabi mama dashi ta mayar da kai k'asa.

"Ki bani hakalinki nan.

Cewar mama, tana zubawa Fateema ido, yayin da ita kuma ta gyara zama ta bada hankalin nata ga Maman.

"Inaso ki dinga janta da hirar samari har ki gano min matsalar ta."

Fatima ta jinjina kai, mama ta d'ora.

"Akwai alamu yaron nan yana hure mata kunne, ada, don (Ameenah/maman su Hafsah) har qarar ta ta kawo min. Amma yanzu naga alamun tana da damuwa, kuma naga kamar yaron ya yaudare ta ne, shine nake son ki hilace ta da hira, ki gano min gaskiyar me ya faru."

"Kingane."?

Fateema ta jinjina kai "Eh, Mama." 

Yawwa, ku dinga hirar samari da ita, da kuma hirar makaranta.

"Toh mama."

"Yawwa nasan zaki iya koh."?

Fateema ta d'aga kai alamar Eh." Tana murmushi.

"Yawwa Allah ya taimaka yayi albarka."


Da Fateema taso ta fad'awa mama zancen wayar da ta tarar Hafsah nayi, sai kuma ta fasa, gwara ta kawo mata cikakken bayani gaba-d'aya."

"Ta miqe ta zata fita mama ta kirata."

Kada fa ki matsa mata da tambayoyi ki bari a hankali, zaki bi abin, ba sauri nake ba."

"Okay mama.!

"Yawwa."

Wajen Hafsah ta koma, ta tarar da ita tayi tagumi, ga gumi da ta had`a.

Fateema tazo kusa da ita ta dafa kafad`unta.

"Am sorry my sister, kin sani cikin duhu, kiyi hak'uri ki fad`amin me yake faruwa."?

"Ni yar uwarki ce ko ba komai, zan taya ki da shawara da addu,a."

Hawaye suka qara zubowa, Hafsah, "Kada ki damu, wannan abin ni ta shafa kawai."

"A,a wallahi nima ya shafe ni, don Allah ki fad'a min."

Shuru babu alamun, Hafsah zata ce komai, sai ajiyar zuciya da take tayi tana cije leb`e.


"Hafsy..Hafsy,!!

Nazeer ya kwalo-mata kira.

Har aranta bataji dad`in kiran ba, bata son abinda yake mata bare yanzu cikin yanayin da take, da ita kad'ai ce babu abinda zai hanata yin _burus_ dashi, amma kuma ga k'anwarshi gefenta dole ta amsa, ko dan gudun kada ta ji haushin hakan, tunda ance _d`an-uwa rabin-jiki."_

"Hafsah Ya Nazeer fa yana kiranki."

Fateema ta qara qarfafa mata guiwa da haka. Ala dole ta miqe, ta fita, bata da qarfin muryar da zata amsa.

Yana tsaye a parlour ta motsa baki, zatace _"Gani."_ ya tare ta.

"Haba Sisi na, kiran ma baza,a amsa min ba."?

"Banji ba ne." ta fad'a murya a dashe.

"Nidai ayi hakuri idan ni na b'ata miki rai, dama abinci za,a taimaka min dashi."

Ya fad'a yana qare mata kallo.

Abin ya bata kunya, taji kunyar kanta, ta dan saki rai sannan tace, "Ciwon kai nakeyi."

"Ayya sannu kinsha magani."? 

Ta girgiza kai.

'To kije kisha bari na zuba abincin da kaina."

Ta girgiza mishi kai, bata son ya dinga karantar k'osawar da tayi da shi don haka ta wuce kitchen.

Shi kuma ganin ya sami abinda yake so sai ya wuce d`akin shi.



Ranta ya qara b'aci bata son shiga d`akinshi sam, da yaran suna nan babu abinda zai hana ta basu su kai mishi. Amma babu yadda ta iya.

A bakin kofa ta tsaya. "Ga abincin."

Ta fad'a a qasan mak`oshi.

"Kiyi hakuri ki miqo min ciki."

"Shima yayo magana da ga cikin dakin.

Ta ajye abincin ko kallonshi bata yi ba, zata juya taji yace.

"Don Allah Hafsah, ki zo kiji."

Ta juyo ta tsaya tana kallon shi.

"Ki zauna mana please."

Ta dan d`osanu a Kujera.

Ya juyo gaba-d`aya Ya fuskanto ta.

Cikin marairaice murya ya fara magana.

"Jibi zamu shiga _camp_ Hafsah, gobe zan tafi in barku."

Shuru tayi tana, nazarin zancen, mene alfanun fad'ar kalmar nan."?

Tana tsakiya da mamaki taji yace.

"Zanyi kewar ku Hafsah.!!

Binshi da kallo tayi kawai.

"Baki da waya koh."?

Ta gaji da irin salon nashi me yake nufi, a irin wannan lokacin da take cikin halin k'ila wa k'ala, akan Yusuf, zai dinga zuwa mata da wani zance ?? don haka, ta had'e rai.

Ya lura da hakan, nan ya shiga tunani, 

_"Ya dace, ya bar yarinya da wannan batun don da alama hankalinta ba akanshi yake ba kuma, akwai sauran yarinta a tattare da ita."_

_Zai barta zuwa wasu lokuta yaga idan akwai rabon shi._

Ya saki ajiyar zuciya, "Okey thank you, kije ciki na gode."

Ta miqe kamar akan qaya take.

_Ya bi bayanta da kallo yana kissima abubuwa da dama, ko dai ya hakura ne kawai.?_

To, babu yadda Fateema bata yi ba, don "Hafsah ta fada mata dawa tayi waya amma fir taki fad'a.

Don haka ta rabu da ita, sai kawai tayi saving number, da Hafsan ta kira.

Daren Hafsah, cike da mafarke-mafarken Yusuf da Basma mara sa dad`in bada labari, haka ta wayi gari da alwashin sai taje inda Basma ta fad'a mata don a banbance tsaba da tsakuwa tsanin ita da ita.


Da sassafe, Nazeer ya gama shiri tsab, ya fito da jakarshi sab'e zai musu sallama, dakin Mamanshi ya fara shiga ta dad'e tana yi mishi addu,ar samun nasara da tsarin ubangiji..

"Amin mama Nagode." haka yake ta fad'a.

Suka fito shida mama zuwa palour, yaran duk suna nan dake Lahdi ce, mama ta qare musu kallo babu Hafsah aciki, "Fateema jeki kira Hafsah suyi sallama.

Yaji dad`in hakan sosai.

Tare suka dawo da Fateeman.

Ta saki fara,a kuma. "Har da cewa yaya tafiyar ce."?

Shiko abin nema ya samu, murmushi yayi mata. "Eh mun fito sai Allah ya dawo damu, kwana biyu kema ki huta da zubamini-zuba-mini."

Dariya, sukayi musu, mama nacewa, "Ah toh, ashe dai ka sani."

Har habar gidan aka fita raka shi, Hafsah taga bata da zab'i sai illa itama ta bisun. Don haka tabi bayansu.

Kallonta yake sosai, kallon da kowa yaso lura dashi. Kallon da Hafsah ta kasa fassara shi. Daga bi sa-ni ya d`auke idonshi yana da murmushi had`i da daga musu hannu bye-bye."

Yace musu. Driver yaja, suka dawo ciki anata hirar kewa.!

Kusan Yinin ranar Hafsah a d`aki tayi shi, tanata kissima abubuwa da dama a ranta.

_Tabbas sai taje ga Basma. Dole taje ta nuna mata, shuru shuru ba wasa bane, kuma dole ta nuna mata cewa tabbas tayi kafuwar da ita bazata tab'a yi ba har abada a zuciyar Yusuf._

Mama bata takura mata da tambayoyi ba yau, tun bayan da ta tambayi Fateema _"Ko akwai bayani.?_ fateema tace mata babu, amma kuma a bisa dole, ta labarta mata batun wayar da, Hafsah tayi a jiya.

"Ki dinga kaffa-kaffa da wayarki kema, sannan sai kin qara qaimi, kinsa dabara ko in koya miki dabarun."?

Fateema tayi dariya "Aa, ki bari mama, zan iya."

"Yawwa, ko kefa."?

Tun da rana mama ta zubawa duk wani motsin Hafsah ido, tana gani tayi wanka da la,asar ta shirya cikin kaya masu kyau, shirin dai yafi kama da na wanda zai fita.

Bata tanka, mata ba, amma a zuciyar ta ta kissima, _"Kada dai ace yarinyar nan wani ta jawo min gidan nan._

K'arfe 5:30pm, Hafsah nata kallon agogo, ji take kamar akan qaya take, gashi mama ta kasa ta tsare a parlour.

''Oh my God.!! Take ta fad'a a zuciyarta hira kawai ake, amma sam ba fahimta Hafsah take ba, hankalinta na can wani guri, zuciyar ta na raya mata abubuwa da dama bata so, Basma ta ce _tsoro taji_ shiyasa ta qi zuwa.

Ana hada wayar mama tayi qara, ta d'auka ta fara waya, sai kuma tayi d'akinta.

Damar da Hafsah ta samu kenan ta, wuce daki cikin hanzari Fateema na kwance ta ganta, da azama kafin tayi magana ta d`auki jakarta da mayafinta ta fice.

A parlour, sai su Al,ameen da Nour, ta kakkkalle su kawai ta fice.

Yaya Hafsah ina zaki."?

Inji Al,amin.

Abinda mama taji kamar kunnen ta ya jiyo mata take ta yanke wayar. Itako Hafsah, ai jin yaran sunyi magana tuni ta qara da gudu-gudu har ta isa gate ta bude kofa ta fice."

Fitowar mama kenan taci karo da Fateema ita ma.

Maman ta fara magana kenan tana tambayar yaran "Ku Hafsah ce ta...

Kafin ta Ida tambayar su taji fateema na cewa "Mama aiken Hafsah kikayi."?

Cikin rud'ewa mama, ta qarasa tambayar, "Nace muku Hafsah ce ta fita."?

"Har sun dan fara rud'ewa, suna in'ina, "A,eh" fita tayi, muma bamu san ina ta tafi ba."

Mama ta tafa hannaye tana salati, yarinya zata ja mata masifa, ubanta ya amince ya bata ita amma kuma tayi mata haka, du-du-du, ko sati bata cikasa a gidan ba.

Da azama mama ta figi mayafinta, fateema ta bita cike da rud'u.

Me yake faruwa da Hafsah ne, gaskiya bata san halin mamansu ba da bazata dinga, irin haka ba. Da ace ita ce, ai kashinta ya bushe..."

_Har rige-rigen fita suke ita da mama, kuma babu wanda yacewa wani uffan, to ina ma suka ga lokacin magana."??....._



  📝 

*HAJEEYAH KHAREEMERH*


♥️♥️♥️♥️

*ZAZZAFAN SO* 

(masoyin k'warai )

*Cigaban littafin Zazzafan so*

*(Guba ne)*

   💔💔


*By:*

*Karima Tijjani Mansur*

*(Hajeeyah khareemerh)*

*Dedicated to Unique in your love heart group member*





  📄 *42*



*Acan* wajen qarshen layinsu suka hango ta tana qoqarin tsare napep.

"Ki bita da sauri mana."

Mama ta fad'a da fad'a-fad'a.

"Gudu gudu, sauri sauri Fateema keyi tana, kwalawa Hafsah kira.

Ai kuwa ta jiyo kamar ana kiranta sai ta juyo.

"Innalillahi wa innaa ilaihi raji'un.

Shine abinda Hafsah ta shiga furtawa ganin mama na nufo ta, yau ta kad'e, ina zata kai kunyar mama."?

Allah yaso Nazeer baya nan da yaya zatayi, da kunyar shi."??

Bata bi takan me napep d`in ba ta juyo, suka had'u da Fateema, ta riqe hannun Hafsah jikinta duk yayi sanyi.

Ina zaki je Hafsah."?

Bata da bakin magana sai jikin ta dake yin rawa, tsabar tsoro m, lallai tayi ganganci da rashin tunani.

Suna qarasowa daf da Mama, takaici yaja maman ta daga hannu ta wanke ta da mari.

"Yau na tabbatar da cewa baki da mutunci yarinyar nan, shiyasa Amiina take cewa, kina neman fin qarfinta.!!"

Ta talle qeyar ta, ta tusa su gaba ita da fateema wuce muje gida ki fad'a min gidan uban wa zaki tafi."

Dukkansu sauri suke kamar zasu tashi sama, sai gasu cikin abinda baifi minti d'aya ba har sun iso gidan.

Kiii, mama taja Hafsah sai d'akinta.

"Nema kike ki wulaqanta ni koh, shiyasa zaki fita bada izini na ba koh."?

"Kuka kawai Hafsah keyi kukan nadama, da Kukan rashi.

Ki rufe min baki ko in tattaka ki anan, kuma idan baki fad`amin inda kikayi niyyar zuwa ba, sai naci mutuncinki a gidan nan.

"Idan kuma don in maida ki gida, kikai min haka ina mai tabbatar miki babu inda zaki, idan nace kin dawo nan babu wanda zan hana ni hakan..."

Takaici ya tuqe mama ta dafe kunci tayi shuru.

Tabbas yarinyar ta bata mamaki, ya akayi ta zama haka ne, yarinyar da aka santa da nutsuwa da ladabi da biyayya, amma gaba-d`aya ta chanja.

Kaii idan ka biyewa yaran yanzu sai ka b'ige da hakan jini ko ciwon zuciya.

Shirun Maman, ya tsorata Hafsah, tabbas an kai ta bango, shiyasa ta rasa abin cewa.

Tsanar Basma ta nunku a zuciyar Hafsah ninkin ba ninkin.

_Ba don ita ba babu abinda zai dinga kawo mata sabani da iyayenta haka._

Tayi mata Allah ya isa tafi dubu zuciyarta. Take hawaye suka fara zarya a kuncinta.

Mama ta riqe haba da takaici, kafin ta miqe zumbur, ta kaiwa Hafsah wani mugun bugu da takaici, Allah yaso ta kauce.

"Ni banyi kuka ba sai ke."? Saboda kin raina ni, zaki dinga kuka.? Me nayi miki.."? Tsabar sharri koh, dama haka kike ban sani ba, dama haka kike yiwa Aminan..?

Gaskiya kin cuci kanki kam, baki yiwa kanki adalci ba..

Cikin kuka ta fara bada hak'uri "Don Allah mama kiyi haquri, don Allah.."

Wallahi bazan qara fita ba, kiyi hakuri na daina don Allah kiyi hak'uri.

"Hum, Haquri ai ke ya kama 'yannan, wacce irin rayuwa kike son ki fara,? Duk qoqarin da ake yi akanki bakya gani koh."?

"Wallahi bazan qara ba don Allah Mama kiyi hak'uri."

Ta rage sautin muryar ta, "To ina kika fita zaki je."?

Cikin shashsheqar kuka tace, gidansu qawata."

"Gidan su kawar ki."? Mama ta maimaita da sigar tambaya.

"To me zaki je yi." 

Dif wuta ta d'aukewa Hafsah, sai jan majina da take yi.

"Ba tambayar ki nayi ba."

Shuru, ina ne gidan."?

"Gadon k'aya ne.!!

Hmm, ai kin koyi qarya kam, to ki sani ko zaki kwana kina rantsuwa na daina yadda da abinda zaki fad'a kuma dole ne ki fada min inda kika fita zaki je a yau d`innan, idan ba haka ba zan d`auki munanan matakai akanki, ciki harda sanarwa da Abbanki, abinda kikai."

Da sauri, Hafsah ta waro idanuwa, ita dai ta shiga uku, Yusuf da Basma na neman saka ta a bala'in da babu ranar fita daga cikin sa.

Cikin wasu zafafan hawaye ta durqusa bisa guiwowinta, abin gwanin tausayi, ta had'e hannayenta, tana rokon ta, "Don mama kiyi haquri kada ki fad'awa Abba, wallahi na rantse miki bazan sake ba, wallah bazan kuma yin irin haka ba."

Tausayi ta bawa Mama, don haka tace cikin had'e gira, idan haka ne toh ki fad`amin inda kika yi niyyar tafiya."

Wasu sabbin hawayen suka fara bin kuncinta banda nada, _"Indai zata labartawa mama inada tayi niyyar zuwa, yana nufin fa, sai ta fad'a mata tsakaninta da bamsa da yusuf, kuma dole hakan yakai ga sanin mama akan abinda idon Hafsan ya gane mata a gidan su Yusuf."_

Bazata iya ba.. Sam bazata iya fad'awa mama wannan zancen ba a matsayinta na yayar mahaifiyarta.

"Kinga koh.. Inba rashin gaskiya ba, me yake sakaki kuka idan aka kamaki da laifi irin wannan."

Maganar mama kenan wacce ta katsewa Hafsah tunani.

"Gi..gidan su qawata zanje wa walima."

"Walima kuma yaushe aka gayyace ki ban sani ba."?

Mama tayi mata zancen bawai don ta yarda da abinda ta fad'a d`in ba.

"Um.. tun ina gida ta kawo min katin.."

"Hmm.. Koh."? Inji mama tana tab'e baki.

Hafsah ta ja baki ta tsuke, tasan zancen bai karb'u ba sam.

"To ina ne wajen."?

"Gadon k'aya."

Hmm, saboda ban isa ba, ke kike iko da kanki shiyasa kika fice a sace koh."?

Bata da amsa illa shuru.


_"K`al!!_ mama tayi kwafa, ban yarda da wananna qaryar ba.

Ta nuna ta da yatsa, Tabbas sai kin fad`amin dalilin fitarki, kafin na d`auki mataki akanki. Sannan zaman gidan nan yanzu kika fara shi.

Maman ta dakata saboda kiran sallar magriba da aka fara yi, tana tuno yadda kusan kullum sai Amina (Maman Hafsah) ta kirata akan Hafsah, ta lura har yanzu hankalinta ya gaza kwanciya.

"Don Allah yaya ki taimaka ki saita yarinyar nan, wallah mahaifinta ma cikin damuwa yake, don ma kece shiyasa ya kwantar da hankali amma da babu yadda za,a ya barta taje wani waje a halin da ake ciki."

Ire-iren kalaman da take mata kenan kullum idan ta kirata.

"Kije kiyi sallah, sannan ki dawo nan bamu gama magana ba.

Ai kamar an sauke wa Hafsah wani abu mai nauyi daga kanta haka taji, ta gaji da wannan titsiyan na maman ya Nazeer, amma ko ma menene ita ta jawa kanta.

Tana shiga d'akin ta fad'a gado, minti kadan sai ga fateema daga toilet, tayo alwala. Ta d'an tsaya ta qareway Hafsah kallo kafin ta d`auki hijabi tasa ta tayar da sallah.

Hafsah kuwa kunyar Fateemah takeji, bata so tayiwa mahaifiyarta laifi irin wannan ba.

Sai da ta idar sannan ta hawo kan gadon, har lokacin Hafsah na kife, Akan cikin ta tayi rub-da-ciki, ta kwanta akan hannayenta ta rufe idanuwanta dasu, da alama kuka take.

Zama Fateema tayi sosai, akan gadon tana fuskantar Hafsah kafin ta fara magana, babu ruwanta da rashin d`agowar Hafsan don tana da yak'inin tana jinta.

"Hafsah, Allah ya gani badon wai cewa Mama mahaifiyata bace, kuma badon kinzo gidanmu bane zan fad'a miki haka, amma ke 'yar uwata ce, dole na fad'a miki gaskiya.. Tayi shuru, sannan ta cigaba.

_"Ban so kika yiwa Mama irin wannan laifin ba a yadda take daukar ki mai hankali.. Hafsah Ke ba yarinya bace, kuma ba ke kadai kike rayuwa ba, kina da 'yan uwa.. Meyasa idan kin shiga damuwa bazaki iya fad'a ba idan ba zaki iya fad'awa mama ba sai ki fad`amin in baki shawara, amma mene ne amfanin abinda kikayi."?

"Kin d'aukar min waya, kinyi kira, kuma kinki fad`amin wacce kika kira, sannan kina kuka na tambayeki dalili kinki fad`a, gashi yanzu kin yiwa mama laifi.. Ya kike so muyi miki.. Ko mune muke takura miki.."?

Fateema ta qarashe zancen da murya mai bayyana tsakanin damuwa.

Duk zancen da take, Hafsah bata d'ago ba, amma kuma tabbas zancen Fateema ya shige ta. Idan ba gaskiya zata k'i ba, to kuwa tabbas tasan gaskiyar kenan aka fad`ami mata.

Ta tsagaita da kukanta tana tuhumar kanta..

 _Tun farkon da aka fara abin nan babu shawarar wanda ta nema, babu wanda ta sanarwa idan ba aysha ba, itama ta bata shawarar da tayi watsi da Yusuf d`in da Basmar duka, amma tak`i jin zancen ta, sai ita da kanta take yanke wa kanta hukunci._


Jin tayi shuru, kuma babu alamun zatayi magana yasa Fateema, ta kuma cewa, _"Na fad'a miki ne a matsayinki na 'yar uwata amma idan kinga magana ta ta b'ata miki rai toh Allah ya baki hak'uri."_ Tana gama fad'ar ta miqe zata tashi tabar kan gadon, a nufinta ma ta bar dakin gaba-d`aya, amma sai taji Hafsah ta riqo ta gam.

Ta miqe ta zauna itama, fuskarta jajir, cikin dashewar murya ta fara magana.

"Nagode, Fateema, nagode, kiyi haquri, da abinda na yiwa mamanki, na sani nayi mata badaidai ba, don Allah ki bata hak'uri... Hawaye suka fara bin kuncinta. Ta cigaba da magana, Fateema, abinda akayi min ne bazai fad'u ba a baki, bazan iya sake labarta shi ba, don, idan zan fad'a ji nake kamar a yanzu abin yake faruwa... Fateema anci amanata, ancuce ni, an yaudare ni, an raina min hankali.. Na amince anci amana ta, anyi min snatchin mafi muni..!!.Kuka yaci K'arfinta ta kifa, kanta akan cinyar fateema, yayin da Fateema tayi shuru, itama zuciyarta tayi rauni, kome akaiwa Hafsah to tabbas bashi da dad`in ji, tun da tayi haka.

Dukan bayanta ta shiga yi tana bata hak'uri, tana rarrashinta akan ta fad'a mata abinda akayi mata, in sha Allah zata bata mafita.

Da kyar, ta samu ta shawo kan Hafsah, har ta fara magana kamar haka: _"Fateemah wacce kika ga na kira qawata ce, tun a makarantar boko, da ita nake shawara akan komai, ita take bani shawara akan saurayi na, na yarda da ita sosai......_


_Nan Hafsah ta bawa fateema labarin komai tun daga farkon had'uwar ta da Yusuf, da irin shawararin da Basma ta dinga bata, da yadda Basman ta fara shigewa yusuf har zuwa birthday d`in Basma, da abinda Aysha D'aheer ta nuna mata a waya, zuwansu gidan su, yusuf, abinda suka gani da idonsu, har zuwa jiya da Hafsah ta kira basma a waya, kawo fitarta ta yau.._

Rashin sanin, abin cewa, da d'aurewar kai, yasa, fateema zubar hawaye, gaskiya abin ya tab'a zuciyarta..

Bubuga bayan Hafsah kawai take yi alamun rarrashi...



Sai kawai, sukaji an turo kofar, mama ce ta shigo, babu mamaki idan aka ce taji duk abinda Hafsah ta fad'awa Fateema, don basu san dad'ewarta ba, ajikin k'ofar ta zo, ne da niyyar kiran Hafsah, don su d'ora daga inda suka tsaya, a tuhumar da maman ke yi mata, sai kuma taji Hafsah nayin magana, nan ta dakata taji komai, ita kanta abun ya shigeta, _Tabbas qawaye suna iya chanjawa 'yarka tarbiyya cikin kankanin lokaci._

Amma sai ta shigo kamar bataji komai ba, tayi wa Hafsah nuni data biyo ta, _Hafsah ta miqe ta fi maman suka wuce, d'akin ta, fatanta Allah yasa, maman bataji koda kalma d'aya cikin abinda ta labartawa Fateema ba..._

📝 




*HAJEEYAH*

*KHAREEMERH.*

♥️♥️♥️♥️

*ZAZZAFAN SO*

(Masoyin k'warai)

*Cigaban littafin Zazzafan so (Guba ne)*

💔💔

*By*

*Karima Tijjani Mansur*

*(Hajeeyah Khareemerh)*

*Dedicated to unique in your love heart*




📄 *43*





*"Kinyi sallar"?*

Kalmomin da mama ta fara da su kenan, daga isar su d'akinta.

Ahankali Hafsah ta girgiza kai..

"To me kika tsaya yi."?

"Babu komai."

Tayi mata nuni da toilet d'inta dake cikin d'akin, "shiga nan kiyi."

Ta wuce da sauri, babu b'ata lokaci tayo alwalar ta dawo ta tada sallah.

Bayan ta idar, har zuwa lokacin cin abinci, har zuwa lokacin bacci, mama bata k'ara yi mata tambaya mai kama da tuhuma, ko neman k'arin bayani akan fitar da tayi ba.

Ta tsammaci haka, a lokuta da dama, ko kwakwkwaran motsi maman tayi, sai Hafsah ta tsargu.

Amma maman sam ta share zancen. Hafsah kam ta zargi abubuwa da dama acikin zuciyarta, a hankali ta d'an saki jiki daga zaman d`ar-d`ar d`in da take da maman, ga kunyar marin da maman tayi mata ta lullub'eta. Ya akayi tayi kuskuren yi mata laifin da har ta iya kai hannu jikinta.? Tana matuqar nadamar yin laifin, da ta sani tayi mata koda k'aryar zuwa wani waje ce, duk da dai koma menene ya riga da ya faru, gashi tsoron had'a idonta da na maman take ko magana take mata kanta a k'asa, don wani kwarjini na musamman maman ta kara a idon hafsan, tun bayan ta tasha yatsunta biyar.

"Dakina zaki kwana Hafsah."

Maman ta fad'a lokacin da fateema ke shirin barin parlour don zuwa bacci, Hafsah ma ta mik`e da niyyar binta.

A sanyaye ta dawo da alama bataji dadin hakan ba.

"Ki je ki dakko duk wani abinda zaki buk'ata."

Mama ta sake kallonta ta fada mata haka.

Da sauri ta mik`e ta fice.

Tana isa dak'in ta tarar Fateema na kad'e zanin gado, ( _bed sheet_ ) taji shigowar mutum don haka ta ta waigo.

Ta saki murmushi, Aike Hafsah kin zama 'yar dakin mama.)

"Allah Fateema kunyar mama nakeji."

"Hmm, Hafsah kenan Allah baki da matsala fa, rashin sani ne ya sakaki yanke hukunci da kanki, amma mama sam bata da matsala, kinga ko ni da ni da nake matsayin 'yarta wallahi bana boye mata komai akan al,amran samari na."

Hafsah tayi ajiyar zuciya, "Ya zanyi in fara tunkarar mama da irin wannan zantukan shirmen.."? Ta girgiza kai, "Bazan iya ba.!!

"Hmm, shikenan." 

Cewar Fateema.

Hafsah ta chanja kayanta zuwa na bacci, sannan ta d`auki blanket, "Sai da safenki!!

Ta fad'awa Fateema, sannan ta fice. Fateema ta bita da kallo tana murmushi, tabbas tana da yak`inin cewa mama ba zata tab'a barin Hafsah ta shiga garari ba, don ta tabbatar maman taji hirar su kaf, daga ganin yanayinta.

"Ki kwanta a kan gado, ni ba kullum nake kwanan gado ba."

Maman tacewa Hafsah, bayan ta shigo, tana kan dardumarta tana jan carbi.

Ta d'ora, "Amma kiyo alwala tukuna, sannan kiyi addu,a."

Hafsah ta daga kai alamar "Toh."

Salin-alin Hafsah tayi baccinta, kuma taji dad`i da ba gefen mama ta kwanta ba, ji tayi ma kamar ba ayi mata chanjin wajen kwana ba.

Da asuba mama ta tashe ta, sannan ta fita tashin sauran yaran.

Bata barta ta koma bacci ba, _"Zauna yau kema kiyi lazimi."_ haka ta fada mata. Sai da rana ta b'ullo lokacin kuma maman ta gama shirinta na fita office, "Tunda ba zaki karya yanzu ba, sai ki kwanta, maybe karfe 2:00pm, ma ni na dawo, sannan asabe ( _tana nufin me aikinta_ ) zata zo, sai kuyi aikin tare kiyi mana abincin rana."

"To, mama me za,a dafa."? Inji Hafsah cikin ladabi.

Cikin murmushi tace, "Kin iya tuwo."?

Hafsa tayi murmushi itama tana d'aga kai.

"To kiyi mana shi, miyar agushi kuma saura naga bai tuk'u ba." Maman tayi maganar da sigar zolaya.

Sannan ta cigaba da cewa, "ki duba akwai komai cikin kitchen d'in, da kwai nama a fridge."

"To mama."

Suka fito palour tare.. Lokacin duk yaran sun Ida shiryawa har da Fateema. "Yawwa kuyi sauri tare duk zamu fita tun da kunga Nazeer baya nan bare ya kaiku." _Mama ta fada musu haka._

Kamar kuma tayi mantuwa sai, tayi sauri, ta koma d'akinta tare da kwalowa Hafsah kira.

Tana shigowa ta durqusa "mama gani, maman na tsaye bata zauna ba, tayi mata nuni, "Tashi tashi sauri nake."

Tana ida mik'ewa ta nuna ta da yatsa.

"Kada ki ga sai ke kad'ai a gida, kiyi tunanin, fita koda bakin gate ne, zan fad'awa mai gadi ma, kuma muddin kikayi attempting fita zaki gamu da fushi na.!!

Babu alamun wasa a fuskar maman tayi mata wannan maganar.

Daga kai kawai Hafsah, ke faman yi alamar, "Toh."

Azuciyarta, tana cewa, ( _"wane Tsautsayin ne zai qara fitar dani.!!_)

Sai na dawo, maman ta fad`a da murmushi kamar ba ita tayi wannan maganar yanzu ba.

"Adawo lafiya."

"Allah yasa, Maza ayi bacci, bye."

Ta fita tana daga mata hannu. Hafsah taji wata 'yar dariya tazo mata, ko ta mecece oho, ta fada kan gadon tayi shuru har bacci ya d`auke ta.

Sai wajen, sha d'aya, ta farka, ta nemi abu mai sauk'i tayi break dashi lokacin kuma, me aikin har, taci rabin wanke-wanke.

Hafsah tayi wanka sannan ta, fara shirin dora girkin, suna yi suna hira ita da me aikin, wacce bazata wuce shekaru 35 ba, tana da 'ya'ya uku da mijinta ya rasu ya bar mata. Duk a hirar su ne take fad'awa Hafsah.

Hafsah ta k'ara godewa Allah, a zuciyarta tana cewa, _"Gaskiya akwai masu buqatar taimako a duniyar nan!_

Sanda mama ta dawo, fara,arta ta zarce ta safiya, musamman da taga an gama komai gidan tsaf, kamar babu abinda ya faru, sai zolayar Hafsah ta take, "Toh zubo min Tuwon naki mana, nayi testing, ice ko babu hannun asabe a girkin."?

Suna dariya asabe tace, "Ita tayi abinta wallah, ai d'iyar taki ba daga nan ba, nima nace 'ko training d`in aure aka kawota ta d'auka.? Mama tayi murmushi kawai, Hafsah tabar gurin da sauri da alama taji kunya."!




Wasa wasa har kwana hud`u, da alama ma mama ta manta Hafsah tayi wani laifi.( _A ganin Hafsan don ganin yadda maman ke janta a jiki fiye da koyaushe_)

Tunda, Nazeer ya tafi taji gidan ya k'ara yi mata dad'i, jiya ne ma daya kira Fateema, suna waya yace ta bawa Hafsan, babu yadda zatayi haka ta karba suka gaisa.

Da yammacin ranar Juma,a tana taya mama gyaran drawer, sai ga ledar da Yusuf ya bata, dam, gabanta ya fadi tare dajin wani farin ciki ya mamaye zuciyarta, gaskiya tana cikin tsananin kewa, in ba don idon maman yakai kai ba, da babu abinda zai hanata da fe abarta ta b'oye.

Maman ta fi ta hanzari wajen sunkuyawa ta dakko ledar, ta lura sosai da yanayin Hafsan."

"In ba don Laifin da kikayi min ba ai da tuni na baki abubuwan ki ai." 

'Inji mama, tana so ne ta shigar da Hafsah hayyacin ta, ta dinga gane abubuwan da suke rufe mata ido suna kaita ne kawai suna baro ta babu wani riba.

_Don a kasan zuciyarta ko hafsah batayi mata wanna laifin ba, bata da niyyar bata wayar yanzu, don bata ga amfanin hakan ba._

Hafsah ta langab'ar da kai kawai, tana bawa kanta laifi.

Hakan ya bawa mama damar cigaba da magana, tabar wancen zancen ta kamo wani, don ta samu ta aika sak'oninta ga Hafsah.

"Hafsah.!!

Ta kira sunan Hafsah a hankali,

Cikin sanyi ta amsa itama.

Kuna zuwa islamiyya koh, Hafsah ta jinjina kai,

"Yawwa." inji mama.

Kinsan shikashikan musulinci koh"?

Hafsah ta k'ara jinjina kai, har yanzu da mamakin tambayoyin a fuskar ta.

"To fad'a min su."

Ta d`anyi shuru sai kuma ta tuna kada mama ta zaci ko bata sani bane, yasa ta shuru. Don Allah a hankali ta fara zayyyano su.

Tana gamawa mama tace _"To saura na imami."_

Hafsah ta fad'o su guda shiddan nan, tanayi tana kallon mama, so take taji dalilin tambayoyin.

Yawwa, 'ya ta."

Ashe dai baki manta karatun islamiyyar ba.

( _zuwa yanzu sun kammala gyaran, amma har yanzu ledar na hannun mama._ )

Mama ta zauna gefen gadon, Hafsah ta zauna kasa gefenta.

"To me ake nufi kaddarar da naji kin fad`a. aciki"? 

Hafsah ta kulle baki da alama bata san yadda zata faro bada amsar ba.

"Uhum."? Inji mama.

"Baki sani ba."

"Ta jinjina kai."

"Hmm.. To marin da na yi miki rannan shi ma ai kaddara sunan shi koh."

Kunya sosai ta lullub'e Hafsah ta sinne kai a cinyoyin ta tana dariya.

"Hmm, bada wasa nake miki ba Hafsah, tunda har an koya miki a makaranta, kuma kin iya kina fad'a to kuwa dole kiyi amfani dashi.

"Kinaji nah.."? Hafsah ta daga kai.

Cikin muryar nutsuwa mama ta fara mata jawabi.

_"Kin sani a makaranta, an koya muku, dole ne mutum ya nemi ilimi kuma dole yayi amfani da ilimin sa Koh?._

Hafsah ta daga kai.

Ta tausasa muryar ta. "Ki fada min gaskiya kinji kada ki boye min ni maman kice. " _Kina son Yusuf_ "? 

Hartar cikin Hafsah ta kad`a wani irin tsoro ya mamayeta. _Sunan Yusuf, kuma daga bakin mama."_?

_Kina son shi._"?

Mama ta k'ara maimaita mata tambayar. _"To ko kuma wannan wata dama ce ta samu, wajen dawo da yusuf bisa hanya, tunda har mama ta shigo cikin zancen."_ ?


Ganin maman bata buk'atar b'acin lokaci yasa Hafsah daga kai a hankali, sai kuma ga hawaye na d`iga. 

Mama ta tallafo ta da hannunta ta jigina ta da gefen k'afarta, "To menene na kuka kuma."?

Ba tambayar ki kawai nayi ba.?

Aka danyi shuru, kafin mama ta cigaba, "Idan nace ki daina kulashi zaki daina."?

Wannan tambayar daidai take da zubar garwashi a zuciyar Hafsah, don yanayin data shiga da jin maganar bazai misaltuwa ba, wannan karon kuka ta fara harda shashsheqa, _wanne irin zance ne wannan mara dad`in ji a kunnuwa."?_ Ita ta zauna ma ta kissima ('Imagine') rayuwar da babu Yusuf asara take gani saboda tasan, abu ne da bazai tab'a yuwuwa ba a wajenta.

Mama tasan za,ayi haka, don haka ba tare da nuna damuwa ba, akan Kukan da Hafsah keyi ta 

cigaba da, zubo maganganunta, wad`anda baza,ace basa shiga kunnen Hafsah ba, tanajine, amma tunanin ta na wata duniyar.

_"Hafsah ita rayuwar nan da kika gani, in bakayi-bani guri ake, nasan bazakiyi mamaki ba naji komai dake tsakanin ku da yaron nan, amma tambayar da zanyi miki shine, ya sunan matsayinki a wajenshi.?_ 

(zuciyar Hafsah ta raya mata _"wadda zai aura mana"_)

Itama k'awar taki mene nata matsayin."? (gaban Hafsah ya fad`i, _wannan tambayar kam babu amsa, don daidai take da k'ure._ )

"Bazan zarge ki ba don ina miki kyakykyawan zato, amma tsakanin ki da Allah kin tab'a jin labarin soyayya irin taku."?

Shin kin tabajin anyi haka..?

_Bari na fada miki gaskiya, _Duk ranar da kika sake kuka cigaba da alak'a ke da shi, to ki tabbatar kema ranar kin shirya zama irin Basma ne, ko kuma kin zama irin ta.!"_

Hafsah tayi saurin d`ago kanta kamar wacce aka tsikara _ita kuma..??_ Mama ce take mata wannan magana, bata fatan ta zama irin Basma, azuciyar ta ma tana cewa _"Inaa.. sai dai idan ranar ba ni Hafsan bace._

"Hmm, a yanzu dole kiyi mamaki har ki kalleni, amma zan gaya miki wani abu, _Ba,a zama inuwa d'aya idan hali bai zo d'aya ba.!!_

_"Saboda haka, kodai ki rabu da shi, ko kuma ki zama irinshi."_

Kuma kada ki d'auka wak'ar da yake miki na zai aure ki gaske yake.. Duk k'arya ne!!.

"Ni Hafsah banda ma rufewar idanu, ki duba kiga tun sanda kika fara kulashi wacce riba kika ci a rayuwar ki, banda koma baya da kakai ta samu."?

Iyayenki na d'aukar ki mai hankali, amma yanzu kin nuna musu ba haka bane.. Da an sanki da tsoro, da sanin yakamata amma yanzu komai randomly kikeyi, kawai gaban kanki kike, har kina iya fita bada sanin kowa ba.!! Sannan kin san a baki abu ki b'oye k'iki nunawa, idan da gaske sonki yake babu abinda zai hana abbanki ya kirashi yazo, ke inya yi niyya ma, abbanki zai bawa abinda zai baki yace a baki.."

"Da yana son cigaba da kulaki ku cigaba da mu,amala ai zai nemeki duk inda kike.. Amma duk baiyi haka ba, sai ke kike 

k'untatawa ziciyarki."?

_Ita dai Hafsah tayi shuru ma da Kukan tana sauraron gaskiyar dake yi mata d'aci, azuciyarta tana ta kokawar dole sai ta kare Yusuf daga abinda ake jingina masa."_

"Ke yanzu ba abin kunya bane, bayan sun kunyata ki agaban mutane an nuna baki da wani matsayi, sannan ki dawo kulashi."?

Wato kin nuna baki da class kenan, kuma babu wanda kike dashi sai shi koh."?

Abin da sukayi kin taba jin wani yaro mai tarbiyya yayi.."?

"Nidai bazan matsa miki ba, amma ina fad'a miki ki fitar da yaron nan daga zuciyar ki, ki d`auki kaddara, ayadda kika yi sati biyun nan ba tare daya nemeki ba, to ki saba a hakan ki cigaba da rayuwarki harki manta dashi. Zaki sami wanda ya fishi alkhairi in sha Allah."

Zuciyar Hafsah ta cika fal da kunci, so ya rufe mata ido, da da sa,arta take mata magana babu abinda zai hanata cewa, _"Ai Yusuf bani da wanda zaifi shi a wajena.!!_

Amma sai ta b'ige da cije leb'e kawai, mama fa tana fad'ar abinda bashi da ranar yuwuwa ne.

Ita ko Yusuf ya nemeta ko kada ya nemeta, ita zata nemoshi kuma tana da yak'inin bazai taba juya mata baya ba.!

Kamar mama ta karanta abinda ke cikin zuciyar Hafsah tace, "Nid'ai ina fad`a miki ne, duk da nasan maganata ba zata taba shiga kunnenki yanzun nan ba, amma kiyi tunani, sannan kuma daga nan zuwa duk ranar da kika sa aranki zaki rabu dashi, to kizo ni kuma zan fad`a miki hanyoyi da matakan da zaki bi in sha Allah, ko wanne irin so kike masa sai kin manta dashi."

Da a halin farin ciki, Hafsah take to da babu abinda zai hanata yin dariya, ji wasu kalmamomi wai _"wai na manta da Yusuf.!!_

Ashe kuwa ranar, zuciyata bata jiki nah.!! Abinda Hafsah ta sawa ranta kenan..

"Zaki iya tafiya, kuma daga yau zaki iya komawa dakin fateema da kwana har zuwa sanda kika ga ya dace ki tuntubeni idan zancen da na fad'a miki ya samu karb'uwa.

Da Wannan mama ta katse mata tunanin ta, wanda akwai hikima a cewar mama, _"Hafsah ta koma dakin fateema da kwana."_


Hikimar kuwa Itace, Hafsah da Fateema shekarunsu kusan d'aya ba kamar ita maman ba, sau dayawa yara sunfi yarda da shawarar sa,anninsu fiye da ta iyayensu ko kuma wanda ya girme su. Tasan Hafsah zata iya nemar shawarar Fateema akan zancenta.

"Nagode.!!

Haka Hafsah ta iya cewa kawai, shima don gudun kada aga rashin kunyarta ne, mama ta d'auka cewa zancenta bai sami shigaba."

Ki dinga addu,a, dai ki nemi zab'in Allah, shine kawai.



Sai yanzu taji sanyi, kuma taji mama ta fad'i maganar da inda addua ce zata iya cewa "amiin."

"Ki turo min fateema.!! 

Mama ta rufe da wannan kalmar.

Ita dai Hafsah gaba tayi kawai, don bakinta yayi mata nauyi, mamaki ma take mama da girmanta amma take son sanya kanta cikin al,amran soyayyar yanzu, Hafsah gani take ma anya mama tasan so kuwa da take ambata mata kalmar _rabuwa,_ _rabuwa._!!?

😅

Fateema na zuwa mama ta fara fad'ar sakonta babu b'ata lokaci, "Idan yarinya can ta nemi ki ara mata waya, ki bata, matuk'ar kin tabbatar yaron nan zata kira."

Fateema ta waro idanuwa da mamaki, ya mama da ake zaton zata gyara, kuma da b'atawa."?

"Eh..!! 'Inji mama ganin kallon da fateema ke zubo mata.

_"Ai ko ni bazan goyi bayan Hafsah ta cigaba da mu,amala da wannan mutumin ba.!!_

Fateema ta fada a zuciyarta.

Mama ta katse tunaninta.

"Tashi kije idan hakan ta faru, sai ki zo ki labarta min, dalili ne ma zaisa na hanata wayarta, da tatan zan bata."

Babu fuskar yin tambaya ko nuna rashin gamsuwa, don haka fateema tayi azamar mik'ewa tana fad`in, "To mama Shikenan.!!

Mama ta bi bayanta da kallo, hikimar ta shine "Don Hafsah ta sami damar yin shawara da Fateema, tunda Itace sa,arta zatafi yadda da zancenta fiye dana maman.

Gefe kuma, tana tunanin idan suka jone da yaron, menene mataki na 

gaba kuma..."?



Tabbas yarinyar na buk'atar addu,a, tuna cewa babu addu,ar da tafi ta uwa amsuwa yasa, taja waya don kiran Amina, cikin nutsuwa take kwantar mata da hankali, tana nuna mata komai ya kusa zuwa k'arshen addu,ar ta kawai ake da buk'ata."

_"Ki riqa yin addu,a nan da nan zaki ga komai yazo da sauk'i wannan ba wani babban abu bane can.._

Hakan maman ta fad'a mata...





📝 

*HAJEEYAH*

*KHAREEMERH*



♥️♥️♥️♥️

*ZAZZAFAN SO* 

(masoyin k'warai )

*Cigaban littafin Zazzafan so*

*(Guba ne)*

  💔💔



*By:*

*Karima Tijjani Mansur*

*(Hajeeyah khareemerh)*

*Dedicated to Unique in your love heart group members.*





📄 *44*





*Tun* bayan da Fateema ta koma d'akin babu wanda yace wa wani komai tsakanin ta da Hafsah, kowa na sak'awa yana kwancewa Hafsah zantukan mama da ta d`auke su marasa yuwuwa ke mata yawo, Fateema ma, su d'inne dai. _"Mene zai sa ace Hafsah ta cigaba da kulashi."?_

Shirun ya d`auke su lokaci mai tsaho, kafin Hafsah ta nemi guri ta kwanta don gani takeyi gwara ta k'irk'iro bacci, da zaman juya kalaman mama arai, masu tada hankali.

Da safe, ta tashi sakayau, babu wani _tension._ don ta sama wa kanta mafita, kawai gwara tayi watsi da abubuwan da mama ta fad'a mata ta manta kawai da ta fad'a mata su ta maida hankali akan dawo da Yusuf cikin rayuwarta, la-allah ko mama ta gane, abinda take fad'an zai faru ba faruwar zaiyi ba.

"Hafsah ta sawa ranta yiwa yusuf uzuri cikin abinda ya faru, da tasirin tuno maganganun shi.. _"Dama na fada miki duk abinda ya faru ke kika jawo.!!_

_Banyi miki cin amanar rabuwa da ke ba.!!_

To in dai kuwa hakane, ashe ita ce ta nisanta kanta dashi kenan,? Tana son dawo dashi cikin rayuwarta ba don ta biye mishi akan abinda yake so ba, sai dai da nufin, nusar dashi ya gane abinda yake nufin suyi, ba shine abinyi yanzu ba a wajenta. Abin mamaki kuma sai take yiwa kanta fatan samin nasara mai kama da yak'ini. Ta manta da cewa wanda yayi nisa baya jin kira, kuma mutum baya sauyawa lokacin d'aya, sannan Yusuf kallon da yake yiwa rayuwa da banbanci da irin nata kallon.

_Akwai aiki a gabana."_

Ta fada a zuciyarta tuno cewa bata san ma ta yaya zata fara jawo yusuf d'inba su dawo ma kamar da. Kafin azo ga batun chanja mishi ra,ayi.

Duk wata hanya an toshe, bata da damar kulashi, an hanata fita, gashi bata da waya, sannan tana kunyar ta k'ara aron wayar Fateema. Amma kuma gefen zuciyarta na bata kwarin gwiwa.

_"Hafsah kunyar Fateema ne zata sa kiyi sakacin da zaki rasa farin ciki."? Baki da isashshen lokaci fah"_

Ta ke taji cewa a zuciyarta, zata iya tambayar Fateema waya, tunda tana da yak'inin ba zata iya hanata ba, toh amma kuma idan ta sanarwa mama fah."?

_"Ki rok'eta akan ta rufa miki asiri.!_

wata zuciyar ta raya mata.

Wannan tunanin shine ya dinga yawo a zuciyarta har tsahon kwana biyu.

Abinda Hafsah bata sani ba shine, Basma har text messages, ta turo a layin Fateema, da taji shuru Hafsah bata zo inda tace su had'u ba. 

_"Hmm, dama nasan bazaki iya ba, hmm ke kin isa dama ki ja da Basma Yunus."?_

Sai da _text_ d`in yayi wajen kwana uku, sannan Fateema taga ya dace tayi mata _reply_ ba tare da ta sanarwa da Hafsa zancen _sms_ d`in ba don gani take yin hakan ma kamar iza wuta ne, amma kuma yarinyar bata chanchanci ayi mata shuru ba, don kada ta zaci ana tsoron ta ne.

Saboda haka da zuciya cike da kishi irin na 'yan uwantaka, Fateema ta rubuta _reply_ a zuwan Hafsah ce.

_"Ai idan kika ga mutum na tsintar abinda ke k`asa, to ya rasa mai zai ci ne, daga ke har shi kunyi min kad'an in zauna ina bibiyar k'azamar rayuwarku, ke dai da bakya ramin kanki sai kije kiji ta cusa kai da zubar da mutunci, ni nafi k'arfi d'aga murya akan abinda kika kula, don bansaki a layin mutane ba bare na zauna damuwa da abinda kika damu dashi, ai ke duk abinda zai burge ki to expired neh..masu hankali bazasu shinshina ba.. To kije ku qaraci k'azamar rayuwarku ni na wuce ajin kulaku dukanku._

Kalaman sunyi matuk'ar zafi a zuciyar Basma, ita da taso suyi ta jan zaren, tayi ta k'onawa Hafsah rai, amma ta sakar mata, anya kuwa ba karfin hali H. Hamid tayi ba.. Ya zaayi, ma tace Yusuf ya zama _useless_ a wajenta, bayan basma tafi kowa sanin irin son da Hafsah keyi wa yusuf d`in.

_"Kai k'arya kike kawai kinji ba zaki iya yakin bane saboda anfi karfinki. Dole ki rungumi sorry_

Abinda Basma ta aiko dashi kenan, zuciyar ta cike da zafin kalaman da aka aiko mata, _bansaki a layin mutane ba."_

Wato ana nufin ita dabba ce kenan.

" _Haha..ni fa na fad`amiki yusuf bola ce wacce nayar kika d`auka banda hakanw bazaki tab`a iya winning d`in heart dinshi ba yanzu ma da kike kurin, koda ace tabbas kwatuwa yayi daga wajena, ki tuna da yadda kika kwace shi mana, siya kikayi da mutuncin ki, kika maida kanki qaramar karuwa ko kin manta..."? Kuma n fad'a miki ki jira randa abinda kika tsinta zai tsere miki.!!_

Fateema ce tayi reply da haka. Kan Basma ya kulle, anya kuwa H. Hamid ce zata iya turo wad`annan kalaman, yarinyar da tasan ta da tsoro, wata zuciyar tace, zata iya fin haka ma, tunda kinfi kowa sanin me kikayi mata, kuma ai dama shiru-shuru ce, irinsu kuwa babu mai sanin zurfin cikinsu.

Kalmomin sun mata zafi ta rasa martanin mayarwa, sai kawai tahau turo da zage-zage Fateema ta ga asarar ta barta don haka ta tura mata reply d`in qarshe da nufin tayi block d`inta.

_Kanki ake ji..kuma nasan rashin abinyi ne yasa kike ta zagi haka, kedai kiji da asarar da kikayi, zagi kuma kanki kika zaga, kar ki k'ara turo min da text don bani da wata alaqa dake if not kuma...Hmm._

Tana kokarin yin block kira na shigowa ta katse kiran tare da yin block na number.

Fateema ta lura da yawan kallonta da Hafsah keyi da alama akwai magana a bakinta.

"Meya faru ne Hafsah." 

Tayi ajiyar zuciya sannan ta fara 'yan soshe-soshe.. "Um Fateema da.. dama don Allah waya zaki ara min in..kira."

Tayi ta rarraba zancen kamar me tsoron tambaya.

"Wa zaki kira."

Fateema ta tambayeta kai tsaye.

"Don Allah ki ara min so nake na tabbatar da wani abu."

Me zaki tabbatar."?

Nidai ki fad'amin wanda zaki kira."

Cikin matsuwa take, don haka ta muskuta.. "Don Allah kada ki fada wa mama na ari waya."

"A,a ni nace ki fadamin wanda zaki kira mana."?

"Nidai kiyi alk'awari bazaki fada mata ba.

"Hmm, to meye idan ta sani, nidai ki fada kawai." 

Hafsah ta k'ara cewa "Don Allah, kinji."

"To naji, ki fad`amin wanene."?

:Da gaske ba zaki fad'awa mama ba."

Hafsah ta tambaya tana murmushi so take ta k'ara tabbatar wa don gudun matsala.

"Kaii wai so kike na rantse neh, Allah bazan fada mata ba, Shikenan?."

Hafsah ta rungumeta "Thank you sister.!!

A kunyace tayi k'asa da murya tace, "Shi zan kira."

"Hmm", inji Fateema. 

Don ta yarda Hafsah ta shiga koro jawabin kariya.

"Kinga dai nice ban neme shi ba shiyasa, gashi bashi da hanyar nema na."

"Hmm, gaskiya.!!"

Cewar Fateema kuma da yake itama tana son a kira d`in don taga k'arshen _game_ d`in sai ta bada wayar.

"Ungo, amma with one condition."

Hafsah ta amsa cikin zumudi tana zaro ido. Mene."?

"Zaki sa wayar a hands-free naji."

Ita dai Hafsah _buk'atar maje hajji sallah_ don haka tayi saurin jinjina kai alamar yarda.


Take ta danna kiran waya, tayi ringim mai tsaho, aka d'aga. "Hello, akace daga can.

Taji muryar cikin ko ina na jikinta yaushe rabonta da jin muryar shi, har kwalla ta tarar mata a idonta, Basma tayi mata laifin da baya yafuwa.!

"Hello."

Itama tace da rawar murya.

"Wanene.""?

Aka tambaya, ita kuma ta rasa abin cewa sam, tayi d'if kwakwalwarta ta kunne, baya kawai take tunowa.

"Nace wanene."?

Aka k'ara tambaya daga can.

Cikin raunin murya tace, "Nice Hafsah ce fah."

"Hmm.." akace daga can, sannan ba,a b'ata lokaci ba aka katse kiran.

Mamaki da tsoro suka saka Hafsah daskarewa ta kasa motsi.

Yau..? Ita.."? Kuma yusuf..? Haka ta faru."?

Fatanta kawai komai ma ya juye ya zama mafarki.

Fateema taji tausayinta matuk'a kuma fuskar ta ta nuna hakan, musamman lokacin da Hafsah take mishi bayanin _"Nice fah Hafsah ce.!_

Akan idonta taga Hafsah ta k'ara danna kiran, amma ba,a d'aga ba.

Fateema tasan ko ta rarrashi Hafsah rarrashinta bazaiyi tasiri ba, zata b'ata bakinta ne kawai, kuma gwara ma ta kyaleta ta zubar da hawayen ko dan ta rage rad'adin zuciya.

Bata son sauraron kukan, don haka ta mik'e tabar d`akin sai kuma taga kawai gwara taje ta fad'awa maman.

Maman a parlour take zaune da wani littafi a hannunta, Fateema tayi sallama, ta d'an rakab'e a gefe, tana kallon maman. Mama ta dago ta kalleta don taga alamun bata zauna ba. "Menene kike rab'e -rab'e"? Tana Sosa kai tace, 

"Um, da dama Hafsah ce tayi kiran a waya.

"Matso nan ki fad`amin me ya faru."?

Ta ajye littafin a gefe ta bada dukkan hankalinta akan Fateema.

_"Kinga data kira, shine yace mata wa ye.. Tana cewa ita ce, yace hmm.. Sai ya kashe."_

Mama ta jinjina kai.. "Okay okay, shikenan, ba suyi wata magana ba"?

"Eh." inji Fateema.

"Ok jeki nagode."

Har ta dan fara tafiya sai kuma ta juyo cikin k'asa da murya tace, "Um mama don Allah kada kice na fad`amiki."

"Hmm." Mama taji d'an murmushi, tayi mata alama da hannu irin, _jeki kawai."_

Tun daga ranar damuwar Hafsah ta k'ara nunkunwa, har Fateema ta saba da ganinta tana kuka haka siddan. Abin ya fara damunta har take k'ara fad`awa Mama, "Mama Allah kusan kullum sai tayi kuka fa take bacci."

Jinjina kai kawai maman tayi tace mata, "Toh naji."

Aranar ne kuma mama tayi niyyar d'aukar wani mataki akai.

Da dare ta kira Hafsah d'akinta, "Baki yanke shawarar ba koh."? 

Hafsah taji jim, tana tunani, _wannan fa wata dama ce, gwara ta bawa mama dama ta fad'i abinda ke ranta ko zai zama mafitar ta, don ita kanta ta sani ta damu da yawa, kuma ta gaji da zama cikin k'uncin zuciya.

"Na takura miki koh.."? To tashi ki tafi."

Tayi daurin girgiza kai. A hankali tace, _"Aa wallahi mama, na kirashi ma bai yakashe."_

Sam Hafsah ta manta ma da mama take magana, abinda ke ranta kawai take son ta fitar.

"Hmm, kingani koh."? "Abinda nake fada miki kenan Hafsah kada ki damu kanki akan mutumin da bai damu dake ba, amma bakya ji."

Abinda mama ta hau fad`a kenan, wad`anda Hafsah taji mamakinsu, azaton ta fada mama zata rufeta dashi, akan kub'utar bakin da tayi.

Mama ta kamo ta, "Tashi ki dawo kusa dani kinji."?

Hafsah ta mik'e mama ta rik'e ta harda jingina ta da jikinta, cikin murya mai nuna alhini, take magana.


_"Hafsah ba laifi bane don kinso yaron nan, tunda so baya zama laifin mutum, abu ne da yake faruwa haka kawai. Sau dayawa mutane suna tsintar kansu akan soyayyar wanda bai dace su so ba, amma babu yadda zasuyi._

"Kinga abubuwan da na fad'a miki sun tabbata koh."? 

Hafsah ta jinjina kai. Don tabbas hakan ne.

"Zaki hakura dashi."?

Hafsah taji saurin d'aga kai, don ita kanta ta gaji, gwara maman ta fada mata ta gwada d`in idan zai curu.

Mama tayi murmushi, a zuciyarta tana hamdala.

_"Kiyi hak'uri Hafsah, ki d'auka hakan kaddara neh._

Kinji.

Ta d'aga kai kawai.

"Abubuwan da zaki guda biyu ne, na farko aiki ne da gangar jiki na biyun kuma aiki ne da zuciyarki. 




Nafarkon shine:

Addu,a.

_"Addu,a ita ce ta farko kuma ita ce maganin komai. Ki dinga tashi da dare kina fad'awa Allah damuwarki, ki rokeshi ya yaye miki dukkan damuwa._





_Sannan na biyu shine, ki ragewa zuciyar ki yawan tunani, kinajin tunanin shi yazo miki kiyi kokari ki kauda shi da wani abin."_




_"Sannan ki daina bari zuciyarki na k'awata miki shi, ki mishi kallo da idon da kowa yake kallonshi, kada ki sawa ranki yafi kowa, zaki ji kin rage wani kaso daga sonshi."_



_"Kada ki d'auka idan kin rabu dashi bazaki taba samun wanda ya fishi ba, ki tuna mutane, daban daban ne, kuma kowa nada tashi baiwar, zaki iya haduwa da wanda ba kiyi tsammani ba a lokacin kuma zaki gane, ashe wancan ba komai bane kawai son zuciyarki ke kawata miki shi."_



_"Kisa aranki zaki iya rabuwa dashi kuma, ba zaki iya sab'awa Allah saboda shi ba."_



_"Ki bawa, kanki da rayuwarki,  maimahimmanci fiye da shi, yadda zaki yardarwa kanki akwai masu buqatar ki aduniya banda shi, akwai masu son farin cikinki, ko shi baya so, akwai wad`anda suka damu dake kuma sun fishi yawa, saboda haka ba zaki wulak'anta rayuwarki akan mutum guda d'aya ba."_



_"Ki kalli alkhairan da ke tattare da sauran mutane, masu nuna suna sonki, kada Ki rufe ido akan mutum d'aya."_



_"Ki d'auka cewa, da zaki bawa wani dama, zai miki son da shi baya miki rabinsa, Hafsah meye amfanin damuwa da wanda ya nuna baya buk'atar ka."?_ 


_"Ki d'auki lokacinki da muhimmanci kada_

_ki k'arar dashi akan abinda bazai miki amfani ba, ko neman abinda bazai samu ba, kada Ki wayi gari lokacin kuruciyar ki ya shud'e amma baki amfani kanki, da sauran mutane da komai ba."_..



Mama tayi murmushi, _"Idan kika saka haka aranki, ina mai tabbatar miki, by time, zaki nemeshi a ziciyarki ki rasa, a hankali Soyayyar shi zata dusashe.!"_

Bance miki lokaci d'aya ba, don komai yana buk'atar lokaci, amma ki tsananta addu,a... Sannan kisa a ranki cewa zaki iya kinji.

Hafsah ta daga kai zantukan sun shige ta, sosai, indai har zasuyi mata amfani yadda mama ke nuna mata tabbas zata gwad'a.

A lokacin taji zuciyar ta ta cunkushe, da tunani daban-daban ta rasa na d'auka kawai sai ta mik'e a wajen ta kwanta sai kuma bacci.




Bayan ta farka ma hakane, taji zuciyarta tayi mata nauyi, maganganun mama sun tsaya mata a rai, a hankali ta fara hango gaskiya a cikin su.

Yusuf? Shine ya kashe mata waya.."? Jin cewa ita ta kira shi..? To wanne irin mantawa yayi da ita haka.. Lallai tabbas ya nuna mata baya buk'atar ta. Nan take kishin kai ya shiga zuciyar ta, taji aranta tabbas ita ma abu ce mai muhimmanci ba _Banza ba._ don haka ta sawa ranta cewa ba zata k'ara neman sa ba, matuk'ar bashi ne ya neme ta ba. Basma kuwa zata barta da Allah, don tasan komai lokacine, kuma alhakin ta bazai barta ba.

Kwanaki suka shud'e mama ta daina yi wa Hafsah magana mai kama data Yusuf ko makamancin haka. Gashi ita kuma Hafsah a kullum maganganun mama suna mata yawo a zuciyarta, ta rik'i wasu daga ciki, misali addu,a, da kuma daukar kai da muhimmanci, sai kuma muhimmanta lokaci, ahankali kuma da taimakon Allah, da amfani shawarwarin hazik'ar mace, wato _Haj. Nafeesah_ a hankali taji komai yana raguwa daga cikin zuciyar ta, har zuwa yau da zata iya claiming cewa babu d`igon son Yusuf ko ragowar damuwar shi aranta, ya zama tarihi, abin ya na bata dariya idan ta tuno lukutan, babu kamar ma irin musayar kalaman da Basma sukayi a text ita da Fateema a zuwan Hafsah ce, sai bayan ta fara dawowa hayyaci, Fateemah ke bata labari.

Zaman wata 3, tayi gidan mama wanda har Abba ya gaji dashi, tana zuwa gida, amma babu kwana, ita kanta tayi kewar komai, tana ganin tarairaya a wajen mamanta.

Sanda ta cika wata biyu, a iya cewa komai ya saitu, nutsuwar ta ta dawo, to lokacin kuma mama ta nemi da a barta tayi azumi anan, tunda yan kwanaki kawai suka rage.

Daga baya kuma, mama ta dawo da ita gida, godiya kuwa sara wacce, Alhaji Habib Hamid, zaiyi wa mama, yayi sai dai fatan alkhairi, don kud'i ko wani abin duniya, sunyi kad`an.

Duk wani labarin zaman gidan da Hafsah tayi da yar gwagwarmayarta mama ta bawa mamanta labari. Sannan ta mik'a ledar kyautar graduation d`in Hafsah wacce Yusuf ya bayar ga maman tare da cewa, "Ki bata sauran ta amfana kawai ita kuma wayar ki mikata ga Abbanta duk ranar da yayi niyya saiya bata a sanda yaga ya dace ta mallaki waya. _"Ikon Allah wai yaran yanzu sun fi bawa soyayya muhimmanci fiye da komai a rayuwa.!!_

Allah ya shirya mana su." Inji aunty Nafeesa, mama tace "Amin.

Ta karbi ledar duka, da niyyar bada kayan duka

abban da hannunsa ya bawa Hafsah, bayan sun gama hirar _yaushe gamo_ a d'akin sa, ya cire wayar, ya bata sauran. Bata ga amfanin su wajenta ba, tana baro d'akin ta bawa zainab agogon, ta bawa Ameera kuma turaren, tayi cilli da greeting card d`in mufida ta d`auke. Akan idon mama, tana murmushi zuciyarta tana godewa Allah.

Hafsah ita kanta tasan rayuwarta ta chanja, ta girma, kuma yanzu shine lokacin da ya dace ta maida hankali Don gina gabanta. ( _feature_) Tana gode wa mama, da ta tsamo ta daga garari acikin wad'annan shekarun nata, da lokacin ta kassara rayuwarta to da babu, wani zancen ta yanzu, don da bata tsinana komai ba a rayuwar, da tuni ta zama abar nunawa. Yanzu kuwa ita ce da digiri, guda aka, tana shirin karbar _certificate_ dinta na NYSC, kuma idan Allah ya taimake ta, zata fara aikinta.? Wai don ma ta bata shekara d'aya, wajen gyaran jarabawa, ( _da ke akwai Matsala a result d'inta na farko._) Lokacin Abba yayi amfani dashi wajen kaita makarantar koyon _computer,_ don rage zaman banza.

A irin haka ne wata ran a hanya takan hadu da Yusuf ko Basma ko kuma dukansu, sai dai a kalli juna kawai, Yusuf ne ma ke kokarin boye kanshi baya son su had'a ido, ita tausayi ma rayuwarsu take bata, daga baya kuma lokacin ta fara makaranta take jin labari yusuf d`in ma yabar k'asar ya tafi k'aro karatu.

Alhamdulillah Allah shine abin godiya. Haka Hafsah ke fad'a bayan ta dawo daga wannan doguwar tafiyar tunanin.

Zancen daya tsaya mata arai kuma shine zancen Bashir, Tabbas gaskiya ne, amma zata sanya tunani da hankali sannan da addu,a wajen samun abokin rayuwa na gari. Ta duba agogo k'arfe d'aya har da kwata, mamaki ya cikata, gashi idanunta sun yi nauyi, ta fara jin bacci sosai, amma tana son ta tashi ta roki Allah alkhairi a rayuwarta, don haka sai da tayi sallah raka,a biyu sannan ta kwanta.....


   📝 

*HAJEEYAH KHAREEMERH*


Not edited might you face typing error!!


♥️♥️♥️♥️

*ZAZZAFAN SO*

(Masoyin k'warai)

*Cigaban littafin Zazzafan so (Guba ne)*

💔💔


 *By*

*Karima Tijjani Mansur*

*(Hajeeyah Khareemerh)*

*Dedicated to unique in your love heart*


📄 *45*


*UKHASHA*

_______________

*UKHASHA* ABUBUBAKAR (KHADI) shine cikakken sunan shi, mahaifinshi kuma, ( _Khadi Abubakar_) Babban alk'ali mai rik'e da muk'amin _Grand Khadi_ a babbar kotun Shari,ar muslinci. Sannan kuma limamin masallacin Juma,a ne.


Abubakar Khady, d'a ne a wajen malam _Na,allah,_ shahararren malami, masanin addini, wanda ya rasu shekaru ashirin  da suka wuce. Ya bar mata hud'u da 'Ya'ya goma sha hud'u bakwai mata, bakwai Mazaa, mahaifiyar Khady Abubakar Itace uwar gida, kuma 'ya'yanta yawanci sune manya don babu wata tazarar shekaru tsanin aurenta dana abokiyar zamanta, saboda haka yaran nasu suke tashi kamar ( _sakwanni_) babu tazarar shekaru mai yawa tsakanin su. Sauran matan sun zo daga baya, wad`anda su kuma Allah bai basu rabo a cikin gidan ba, sai dai suma sunzo da nasu yaran daga wani wajen, duk sai aka zama d'aya babu banbanci, saboda had`in kai da yake zaunanne a gidan har kawo yau ana zumuncin, har takai acikin 'ya'yansu idan ba manyan ciki ba, basa sanin cewa  ba kakansu d'aya ba.


A D'akin su Khady Abubakar, malam _Ayyuba_ ne babba, kuma shine ya gado mahaifinsu sosai, ma,ana ya gado _malintar._ Sai kuma _Khady Abubakar_ shine na biyu, sai alhaji _Auwal,_ wanda suke kira da (Baffa)  Sauran duka mata ne, Haj. Zainab Haj,

Rukayya, Haj. Binta, sai Hajiya, Rabi, dukka suna da aure da albarkar 'ya'ya wasu suna zaune a garin nan, wasu kuma a wasu  garuruwan, kamar sokkoto, zamfara da sauran su.  'Ya'yan d'aya d'akin, su kuma mazan ne su biyar, mata kuma, su biyu,  acikin mazan biyu sun rasu a shekarun baya-bayan nan, sumbar iyalai da yawa.


Wani abu daya k'ara wa family d`in yawa shine duk cikin mazan babu mai mata d'aya banda _(Baffa_  na gadon k'aya,) kuma dukkansu daga matan har mazan, 'y

Ya'yansu zasu kai takwas zuwa goma sha, babu masu k'asa da haka. 

Akwai arzik'i da yalwa, a yawanci gidajen wanda sai dai na wani yafi na wani, _wannan kuma falalar Allah ce da yake bawa wanda yaso._ Akwai tarbiyya ga yaran nasu, suna da ilimi na addini da na boko. Anyiwa familyn kyakykyawar sheda kuma an sansu sosai. wato _malam Na-Allah family._ 


*GIDANSU UKHASHA* 

____________

Gida ne daya kunshi mata biyu, da yara goma sha d'aya. Hajiya Hafsah, wacce suke kira da _Haj._ Itace Babba, ta fito ne, daga tsatson sarauta, gaba da baya, kuma ita  k'anwa ce ga sarki mai mulki a yanzu. Sannan tana aiki a wata makarantar 'yan mata a Matsayin _principal._ Amma baifi 'yan watanni sukayi saura tayi _retire_ ba. 


Sai kuma Haj.Kubra suna kiranta da _Mama._ Itace ta biyu, tana aiki a wani asibiti a matsayin _Nurse_


  A 'ya'yan Haj. Hafsah, Ukhasha shine na uku, Babbar 'ya a duka gidan mace ce,  tana aiki da _Ministry of Women affairs, sunanta _Hajiya Na'ima_, a Abuja take da zama ita da yaranta da mijinta. Sai kuma _Dr. Sunusi_, Babban likita a asibitin Malam Aminu kano, yana da aure da yara uku, sai _Ukhashatu,_ kwararen engineer, wanda ya kware a harkar 'Civil engineering' Sai _Nura_ k'aninshi, shi kuma bangaren shari,a ya karanta, shine yayi aure, shekara d'aya data wuce, sai kuma _Fadwa,_ Itace autarsu,  tana shekara ta uku a Jami,a. 


D'akin mama kuma, _Nasir_ shine babba, wanda shine sa,an _Nura_, ( _wato sa,an mai bin ukhasha a d'akinsu_) sai _Maryam_, zata bawa Fadwa kusan shekara d'aya, sai _Zainab_, _Abdullahi,_ _Najeeb,_ sai autarsu ( _Mahseen_) Itace auta, duka gidan, shekarunta bazasu wuce goma sha biyu ba. 


Idan har ba zaman gidan kayi na wani lokaci ba, ko kuma dama ka sansu, toh babu yadda za,ayi ka iya banbance 'yan wannan d'akin da 'yan wancan. Rayuwa ake ta had'in kai babu banbanci.


~_Connect with page 36_ (Inda ukhasha ya dawo gida daga party)~


*UKHASHA*

_____________

Yana ta son ya kauda tunanin ta, amma ya kasa, Yarinyar ta tsaya mishi arai, duk wani motsi nashi sai ya tuno ta. Matsalar d'aya ce, bai san a ina zai k'ara ganinta ba, bai san ita dawa suka zo bikin ba, bai san a wanne dangin take ba, na amarya ko na ango. _"Ya ilaahiy"_ Ya fad'a a hankali fargaba kawai yake, yana fatan kada Allah ya d'ora mishi son abinda bazai samu ba.


Wayarshi ke ta k'ara amma ko kalla baiyi ba, bare yayi tunanin d'agawa, don ya tabbatar idan ya d'aga komai zai iya faruwa, zai iya fada mata maganar da sai tayi da na sanin kiranshi.


K'arar shigowar text yaji, kamar zai share sai kuma yaga gwara ya duba.


_Allah ya huci zuciyarka, don Allah kayi hak'uri in sha Allah this wouldn't be happened again, na ajye wayar ne shine maman ta d'auka ta kiraka.. Plz am sorry, u know bazan iya jure abinda kake min ba plzx._


Ya sa, hak'oran sama ya cije leb'en shi na k'asa, daya tuno irin bak'ak'en zantukan daya sha a waya..


_"Mara mutunci,_

 _mugu azzalumi wallahi ka sakar min kur,war 'ya in ba haka ba zaka ga abinda zai biyo baya.._ _Don tsabar mugunta ka asirce min yarinya!! Wa yasan abinda kake mata kana son ka lalata min yarinya!!_

~_To ba alk'ali ba koma waye mahaifin naka bazai hana nayi shari,a da ku ba.!!_~


Babban abinda yafi b'ata mishi rai shine, mahaifinshi da aka ambata. Meye dalili..? Shi baice yarinyar dameshi ba da irin bak'in nacinta sai shi wai za,a ce ya asirce ta.? Allah ya sawwak'e, ai ko  asiri yake bazai yiwa wannan 'yar ta ta ba, yarinyar da bai tab'a ji kalarta ko wani abu ya nata ya burge shi ba sam. 

_Wai lalata.!_ shi ake cewa zaiyi lalata da wata yarinya..? Akan me zata yi masa wannan sharrin.. Ta taba ganinshi k'ofar gidanta."? Kawai tsabar sharri irin na mata, don 'yarta ta nace mishi tana son  ta rabata dashi sai ta fake dayi masa sharri, ai kuwa idan haka ne dole ya d`auki mataki akai, duk nacin yarinyar sai ta daina kulashi ko bata so, sai dai in ta mutu, tun da abin ya na neman yazo da sharri..


Gyangyad'i yake tayi saboda gajiya, sai ya mik'e kawai ya kwanta, bai bi takan wayar ba ma, ranshi a b'ace, _amma yarinyar akwai k'arfin hali da naci.._ 

Shi banda bazai iya ba, ai shine yake da abin cewa, badon ba halin shi bane cin fuska, da babu abinda zai hana shi mayar mata da munanan kalamanta kan 'yarta.

_"Ai yarta ce mayya, ita ce ke bibiyarshi, ga mugun naci sam bata da zuciya._

 Amma da ke bazai iya ba wayar kawai ya katse ya kyaleta.


Har ya fara bacci ya tuna gwara ya kashe wayar, idan ba haka ba, zata iya cigaba da damunshi da kira don zata aikata. Gefe kad'an na zuciyashi, yana tausaya mata, bai tab'a ganin inda ake irin abinda yarinyar ke mishi ba, wani _"Makahon so"_  take mishi. Yayi imanin idan yace ta kyale mahaifiyarta tsaf zata barta!!

 Ya nemi tsarin Allah daga fad'awa irin wannan son.


Yadda ya d'auka  shine, su mutanen yanzu, ka so su tsa ka-tsaki shine maslaha, don yana da tarihi na soyayya kala-kala  musamman a cikin abokansa, wad`anda suka _ZAFAFA_, k'arshe suka k'are a asibiti.


Yana mamakin kansa, bai tab'a jin ya kwana da wata arai ya tashi da ita, ya ku ma kwana ba, sai dai wani lokacin ya kan b'ata lokaci akan tunanin _Bahijja_ shima ba wai begenta ba, a,a kullum cikin tunanin yadda za,ayi su rabu salin alin yake, ba tare da ta zargeshi da b'ata mata lokaci ko kuma k'inta ba. Amma duk wasu hanyoyi ya gwada  basuyi amfani ba, ya sha fad'a mata, tayi hakuri tayi aure, shi a gida za,a bashi mata amma tak'i sai dai ta ji shi kawai, har fada' mishi take, _"Taji, ta amince ya auri uku ya cikashe ta hud'u da ita wallahi zata yarda.!!_


*HAFSAH*

______________

Misalin k'arfe sha d'aya da rabi na, safe, sun gama karyawa, dake kuma _weekend_ ne babu makaranta, kowa ya kama abinda zai fishshe shi. Gidan tsaf yake an share babu datti, sai k'amshi kawai ke tashi.


A parlour Hafsah ce zaune bisa kujera three seater,  ta dora _Laptop computer_ akan hannun kujerar. Sanye take da riga da skirt na atampha, wanda suka d'an  kamata, babu d'an kwali akanta. Gashinta wanda dama can bai cika ci ka ba, sai dai tsaho ta tufke shi da ribbon, farar fatar ta sai shek'i take, babu alamun kwalliya a fuskar ta, idan ka kalleta zaka ga babu abinda ya sauya daga ita idan har ka santa ashekarun baya, komai cikin nutsuwa take yi kuma a hankali babu gaggawa.  Kana kallonta zaga ga alamun hutu da wayewa atattare da ita, ba mamaki kuma ka k'i yarda cewa Bashir k'aninta ne, saboda yanayin jikinta bata da girma sam, sai dai matsakaicin tsaho.


Da Sallama Abba ya shigo palourn daga d'akin mam. Hafsah ta amsa tare da rankwafawa tana gaida shi, _Abba Barka da safiya."_

 Ya kalleta sosai, "Sannu Yaya, bakya son saka d'an kwali koh..?"

Ta danyi murmushi tana shafa gashinta da ke ta shek'i, ta kalli gefe da gefe kamar zata ga  dankwalin a wajen.


Har yanzu yana kallonta. "Baki bi su zainab d`in kitson ba ke."?


Cikin nutsuwa tace, "Eh abba ba ba sai nayi kitson ba, ai nayi _saloon."_

(Duk shirye shiryen bikin Fateema suke k'anwar Ya Nazeer  )

Yayi kyau, "Ki saka d'an kwali toh."

Ta mik'e zata wuce d'akin.

 "Nima zan fita wani meeting ne."

"To Abba a dawo lafiya."

"Allah yasa Yaya."


Zai fita kenan Bashir ya shigo, ya zube har k'asa "Barka da asuba."

Abba yayi dariya "Asuba ko rana."?

"Ko dan ku baku son tashi da wuri koh."? 


Ya fara tafiya Bashir na binshi a baya.

"Ya kuke fama da baccin nan a makarantar kuwa."?

Basheer ya sosa kai, "Ai Abba hakura ake." 

"To da kyau ai."

Cikin ladabi yace "Abba fita zaa yi ne."?

"Eh zanje wani meeting ne, kasan an kusa yin _primary election_.

"To bari na raka ka Abba."

Abba yayi murmushin jin dad'i "Yawwa, _amma dai ka sa hula koh."?_


Ya kalli jikinshi riga ce _long sleeves_ da dogon wandon _Jeans._


Yayi murmushi, sannan da sauri ya wuce cikin gida, duk da d'akinshi kafin a shiga ciki ne, yana shigowa palourn, Hafsah na fitowa daga d'akinta, tana d`aura d'ankwali.

"Gud morning sister of mine.!

"Morning _Junior_ "

( _Haka ta dawo kiranshi._)

 Tana tahowa shi kuma ya tsaya, bata gama k'arasowa ba yace, "Anjima da yamma zamuje park idan na dawo, yanzu zamu fita da Abbah ne."

"Okey tace mishi."

"Ina mama, kice mata mun fita da Abba."

Ya fad'a cikin sauri, sannan ya juya. D'akinshi ya bud'e ya d'akko hular ya kifa akanshi, yana murmushi, yasan da Hafsah zata gani babu abinda zai hana tayi ta mishi dariya.

Murmushinshi ya k'ara fad'ad'a yana son yayarshi yana son farin-cikinta.


"Haha, kufa yaran yanzu kwalliyar ku da ban ce!"

Cewar Abba sanda Bashir ya k'araso inda yake.

Ya bud'ewa Abba d'aya gefen, sannan shima ya shiga mazaunin _driver._

Don ance ka sako hula, sai ka sako ita kad'ai..? "Ai ana nufin ka sako kayan da ake sawa hula."

Ya k'arashe maganar yana dariya.

Bashir ya sosa, k'eya, "Ai kada na bata lokaci ne shiyasa."

"Hakan ma yayi, ai naga haka kuke yi yanzu, _asa kayan bature, a d'ora hular bahaushe!!."_

"Kuna kwaikwayon rappers kuke ce musu ne ko hip -pop" 

"Bashir yayi dariya, kawai."

"To yayi, _bridged_ muka nufa, nan za,ayi taron.

Abba ya fad'a sanda Bashir ya tada mota.

Mai gad'i ya bude musu gate, suka fita, suna tafiya suna hira irin ta d'a da mahaifi.


__________________


Shiri suke, sosai duk sun baza kayan kwalliya a d'akin, mai yi musu kwalliyar fuskarta ko powder babu, Fadwa kenan, take wa  su Maryam da Zainab kwalliya, kasancewar ta iya kwalliyar zamani. ( _makeup artist ce ita_)

Shirin zuwa partyn Abokin Yayansu Ukhasha suke wato Jabeer (JB). Shima Ukhasha  yana d'akinshi yana shiryawa. 

Zainab ce da ake shafawa powder tace, "Yaya Fadwa muyi sauri fa kinga,  kada Yaya yayi ta jiranmu..Kinsan halinshi zai iya tafiya ya barmu."

Bata tsaya da abinda take yi ba tace, "Kedai ki tsaya kiyi kyau kawai, yanzu k'arfe nawa ne ma kwata-kwata"?


Sai da ta gama mata tsaf tayi mata d'auri, dama ta gamawa maryam. Ta d`auki mudubi kenan zata fara da fuskar ta, wayarta tayi k'ara, maryam tayi saurin kai hannu ta d'auka, Fadwa ta miko hannu, maryam tayi gefe da wayar tana cewa, "Don Allah kiyi sauri Yaya ne fa bari na d'aga."

Hello..

"Ina ta jiranku fah."

"Mun kusa gamawa Yaya."

"Hmm, kada ku batan lokaci don Allah, me ita Dadwan keyi sarkin k'ak'ale-k'ak'ale."

"Yaya ta gama, d'aura dan kwali take." 

"Please Kice tayi sauri kunga sai kirana suke."

"Tom."

Ya katse wayar don jin kira ya shigo a zaton shi ango ne.


Sai kuma yaga Bahijja, kamar bazai d'aga ba sai kuma ya tuna wani abu.

Bai bata damar magana ba yace, "Kinga zan fita ne,  idan na dawo zamuyi magana."

Ya katse kiran, sannan ya k'arasa d'aura takalmin shi, ya mik'e ya nufi mudubi dake manne jikin bango, k'asan shi anyi wata 'yar kanta mai kyau, kayan shafe shafe ne na maza, da sauransu akai. Babu wasu tarkace dama a d'akin, drawer ce me biyu wacce ta cika da kaya, sai akwatuna, suma kayan ne dai aciki, sai abin d'ora takalma, sai madaidaicin gadonshi, gefe da gefen shi da _bed side drawer_ ya dora mata littafai aciki da wajenta.


Ya kalli kanshi sosai a madubin, sannan yasa hannu ya gyara zaman hularshi yayi kyau matuk'a cikin _Brown shadda_ da sukayi ankonta, bai da kiba sam, sannan ba dogo ne irin sosai ba, yana layin tsakiya dai, fatar shi ba fara bace tas, amma tana da haske sosai, yana da saje a fuskar shi, haka dukkan jikinshi akwai gashi, amma basu cika cika ko tsayi sosai ba. 

Akwai shi da kwarjini idan ka kalleshi, bashi da yawan magana barkatai musamman inda bai da sanayya ko sabo da mutanen gurin, amma yana 

da hira harda zolaya indai ka mishi farin sani. Bai bata lokaci sosai wajen tsayawa kallon kanshi ba, ya fesa turaruka masu sanyin k'amshi, sannan ya fito, daga d'akin kawai.


Lokacin suma k'annen nashi sun gama shiryawa, sunyi kyau sosai, cikin shigar _blue black lace_, mayafansu mayalwata, baza,a ce sun fito da tsaraici ba. Sai kuma suka b'ige da zaman d'aukar photo. 


_Wani abu game da Khady Abubakar shine, baya hana 'ya'yanshi mata zuwa biki, ko wani taro, indai har  ya yarda da tsaftar mutanen, sai dai dole zasuyi shiga ta mutunci, wacce dama kullum cikinta suke, sannan ba,za,a barsu su tafi su kad'ai ba, sai dole ke da 'yar uwarki ko yayanki ko k'aninki. Sannan basa sakewa su haura k'arfe takwas na dare.


_Aganishi ka hana yarinya mace zuwa taron biki, kamar shiga hak'k'i ne da kuma bada k'ofar shigowar b'araka, don a yadda yaran yanzu suke muhimmanta biki, to idan ka hanasu dole su nemi hanya ko da bada saninka ba, har gwara ma a fita da saninka, kuma matuk'ar ka tarbiyyantar dasu yadda ya dace, babu abinda zasu yi  na zubar da mutunci ko makamancin haka._


Yanzu haka ma sai da ukhasha ya nemi izini a wajenshi, sannan da k'yar ya yarda.


"Ku idan zakuyi biki kuyi iya ku mazaa, mana, amma kun hada har da mata."?


Ya sosa k'eya, "Akaramakallahu, ai na matan ne, gayytar mu sukayi.


"Ku bar angon ya je shi d'aya mana, tunda abin na mata ne."

Bashi da bakin magana sai yayi jim, kafin ya tuno abin fad'a, don baya son yawan tsawaita magana irin haka da Abban nasu, don ba,a nasara akanshi, sai dai idan yayi niyyar abu kawai zaiyi.


"Shiyasa zan kaisu tunda an gayyace su."

" Zaka kai ku dai, ai har da kai kaima zaka ce zaka kaisu, kawai kun bata abu ne yanzu, mata na biki kuce sai kunje.. Shi ango ai da walima aka sanshi ita  yake had'awa shi."

"Tuba muke, ranka ya dad'e."

"Yaushe ne kace."?

"Yaune da yamma.

 "To Allah ya kaimu amma ba,za,a kai dare ba koh."? 

"In sha Allah."

Ukhasha ya fad'a. Don yasan ba tambaya bace a wajen abba umarni ne kawai, yana nufin kada akai dare, don yasan partyn da aka fita, dayin magriba ai dole akai dare.

  Cewar shi ta 👇 

( _amma ba za,a kai dare ba koh."?_ ) Girma ne da kuma iya magana yasa yake umarni da sigar tambaya, Don babu mamaki idan sunyi daren kaji yana tuhumar su,   ~_"Bance kada akai dare ba."_?~


K'ofar d'akin da suke ya nufa. Ya tsaya a bakin k'ofa "Kuyi sauri fah, ni na fito."  Da sauri suka fito, suna zolayar shi, "Yaya anyi kyau fah.!!


_______________

Suna zaune a kan kujeru, a wani wajen shak'atawa, Bashir Hafsah Zainab Ameera da Mufida.


Idon Hafsah ne ya hango mata wata kamar idon sani a wajenta, ita da wani suke tahowa, cikin takun k'asaita, kayan jikinta kamar sa b'arke saboda kama tan da sukayi, babu ko mayafi a jikinta. Suna k'ara nufo su tana k'ara wayewa da wacece, nan ta hau tab'a Basheer tana nuna masa ita da yatsa, "Basheer, ka ga wata, wallahi Jamila ce, ba bari dama na dad'e ina nementa."


Tayi zumbur zata mik'e Bashir ya rik'ota, "Haba sister ki bari mana, ki daina nuna su, me zaki mata idan kinje."?

"Ka barni Bashir, baka san na dad`e ban ganta ba, nayi shekara biyu rabon da na ganta." 

Zata kuma mik'ewa  ya kara rik'eta 

"Plz ki bari yanzu ba fa kamar da bane, ki kyaleta kawai, babu lallai ma ta kulaki."

Nan ta hau mishi magana fad'a-fad'a kamar zatayi kuka, "Don't you know for how long nake nemanta amma kuma zaka hanani, kasan me nake ji araina.. I hate Wannan rayuwar da Jamila take, bazan iya dinga zuba ido ina gani ba..


Yasan halinta da saurin kuka, don haka, ya shiga rarrashinta, "I'm sorry aunty ba hanaki zuwa zanyi ba, amma ki jira ita tazo kinga da alama ma ta ganki, kuma tunanin da kike akanta yana da wuyar yuwuwa yanzu fa, ba,a iya chanja mutum lokaci d'aya. Bata ce mishi komai ba ta mik'e ~_"Ai idan da alkawari ba zata ga Jamila ta share ba, ko a wanne hali take ciki kuwa._~

 Shima dole ya tashi, yawa sauran k'annen nashi alamar su biyo su kawai, ya musu nuni da su dakkowa Hafsah jakarta.


Jamila na hango, Hafsah, ta rabu da wanda take tare dashi tazo da gudu ta rungume ta, sun nuna jin dad`in ganin juna kafin, Jamila tace, Ai ina ganinki sometimes street haka ko wani waje, akwai distance tsakanin mu that's why bana miki magana.


Hafsah dai bata iya cewa komai ba, sai murmushi, kallon Jamila kawai, take, gaba-d`aya ta chanja, idan baka mata kyakykyawan sani ba ba zaka gane ta ba.


Jamila ta miko mata waya, lokacin su Ameera sun k'araso inda suke, ta daga musu hannu, ga mamakinsu duk sai da ta ambaci sunan su, "Ameera Zainab, Mufida, sannunku."


Ta kalli Bashir daya tsaya can gefe, bata mishi magana ba, shima kallon nata kawai yayi, ta mik'awa Hafsah wayarta samin phone dinki anan, munyi magana naga kina sauri nima ina sauri.

Hafsah tasa mata, ai kafin tau

 k'ara kalma d'aya Jamila tabar wajen tana d'aga mata hannu.


Hafsah tayi ajiyar zuciya, zainab tace, "Yaya is she your friend Jamila."

Hafsah ta jinjina kai, ba zata iya magana ba.

"Chab." Ameera tace.


Mota suka shiga Basheer, yaja bai yiwa Hafsah maganar Jamila ba sam, Hafsah kam gaba d'aya yanayinta ya sauya ya koma damuwa, tsoron Allah ya k'ara shigarta, wai Jamila ce haka, babu ko mayafi, wacce a da bata iya yawo Inba da hijabi ba."? Kishin hakan ya cika zuciyarta, bai dace ta zuba ido tabar Jamila haka ba, ko ba komai ada ta amsa sunan k'awarta, ita gashi ta zama wani abu, amma Jamila fa, sam abinda take babu mai alfahri da ita.

Take ta sawa ranta zata yi iya kokarin ta wajen dawo da Jamila kan hanya, ita kanta tasan abin yana da matuk'ar wuya aiki ne ja, amma kamar jahadi ne, to kuma babban k'alubalen shine rashin sanin ta ina zata fara."?


Su Bashir nata hira ita kuwa tsit kake jinta, yana kallonta ta madubi, sai yaji ta bata mishi rai ma. _Duk wannan sauyawar da damuwar akan mutum d'aya, da babu alak'ar kusa ko ta nesa yanzu Tsakaninsu, matar da take yin abu bisa saninta, kuma da hankalin ta da ilimin ta."? Mene zaisa ta damu kanta, tunda ita maiyi d`in tana ganin daidai ne._


_________________

UKhasha tuk'i yake sosai, yayi watsi da tsokanar da su fadwa ke mishi, shakiyan ci ne kala kala, _Wai gaskiya yaya tunda Yaya Jabeer yayi aure kaima ya dace, kayi tunda dama ku biyu kuka rage._ Yayi burus dasu baice musu komai ba. Yanaji fadwa na bawa maryam labarin, _Bahijja_ da ke sune a baya. Sukayi shewa harda tafawa,  ya juyo rai a had'e.

"Bana son shashanci, Allah zaku fita daga motar nan kuna min ihu a mota."


Haha.. Dariya suka mishi, ya juya kawai ya cigaba da tuk'inshi.. 


Wani Uturn suka zo  daidai, lokacin Basheer shima ya taho dake mik'ewa zasuyi street su, shi kuma ya riga ya taho, Allah, ya kiyaye aka d'an bigi bayan motar tasu kawai. Dukkansu parking sukayi, kafin Bashir ya k'araso shi har yazo inda suke, _"Yi hakuri mai gida._  Abinda Basheer ya fara fad'a masa kenan, ya daga mishi hannu, _"Bakomai bakomai, muyi hakuri duka._  motar taku batayi komai ba."?


"Eh.. Inji Basheer "Hope kuma haka." "Babu koma, ka dinga kula kawai k'anina"!!


Karaf idanunsu suka had'u dana Hafsah. Yaji wani shock, Tabbas Itace.

Itama fad'uwar gaba taji, _kamar ta sanshi fa._


Bashir na shirin juyawa zai koma mota, _Dan Allah k'anina kaji mana._


Basheer ya dawo da mamaki. 

"Me kace."?

"Um.. K'annen nan naka ka taimaka min da d'aya."

Bashir ya kalleshi da mamaki.

Me yake nufi kenan.?

Yayi k'asa da murya don yasan tambaya yake shirin yi mishi.

Kaga bamu da lokaci kana sauri ina sauri, taimaka min da number.


Bashir yayi jim, kafin yace okay.

Ya sa mishi number, yayi saving.

Ya mik'a wa Bashir hannu sukayi musabiha, "Nagode sosai abokina."

Bashir ya shiga mota, shi kuma ya k'arasa inda yayi parking, ya buda motar, gaba-d'aya yanayinshi ya sauya zuwa sanyi, akan idonshi suka wuce, da alama su ba wajen bikin zasu ba.


Yayi amanna Allah ne, ya dube shi ya k'ara had'a su. Su Fadwa sunyi mamakin sauyawar shi lokaci d'aya. 


Basheer kuwa ya tafi yana mamaki, mutumin nada kyan mu,amala, shifa aka bugawa amma shine ya fito...


Mufeeda ta ji bazata iya shuru ba tace, Yaya naga kamar kunyi exchange numbers da wancan."

"Eh.."

Kawai yace mata, don bai son fad'ar dalili don baisan wa ya gani cikinsu ba, aranshi yaji yana fatan _Allah yasa Hafsah ce._


Da suka zo wucewa ma sai da ya d'aga wa Basheer hannu, sannan yaja tashi motar...


_Addu,a Kawai yake axuciyarshi Allah ya taimake shi akanta ta yarda dashi..._


     📝 

*HAJEEYA KHAREEMERH*


♥️♥️♥️♥️

*ZAZZAFAN SO* 

(masoyin k'warai )

*Cigaban littafin Zazzafan so*

*(Guba ne)*

💔💔

*By:*

*Karima Tijjani Mansur*

*(Hajeeyah khareemerh)*

*Dedicated to Unique in your love heart group members.*




📄 *46*




*Allah-Allah* yake ya dawo gida, ya kira number da ya karb'a, number da ko sunan mai ita bai tambaya ba.

Biki yayi dad'i sosai. Ango da amarya kowa na cikin farin ciki, anci an sha, sannan an sha rawa, gobe shine kai amarya.

Ko a wajen bikin ma kiran bahijja wajen uku, amma bai ji bama saboda k'arar kida bare ya d'aga.

Sanda suka dawo gida kuma, wajeny misalin tara na dare, shi kanshi shakkar shiga gidan yake saboda Abba bare kuma k'annen nashi. Babu yadda ya iya biki ne na aminin shi, ya kamashi ne sosai abin, banda haka shima ba son hayaniyar biki yake ba, kuma muddin baiga k'annen shi gurin bikin ba bazaiji dad'i ba, shiyasa yaje da su na yau.

Yana parking suka fito, shima ya fito, bai wuce ko ina ba sai d'akin abban dake gefe.

Da sallama ya shiga, amma ba,a amsa ba, sai akayi gyaran murya alamar ya shigo.

Ya sami guri ya zauna, yana jiran abban ya gama jan charbin da yake. Carbin k'ato ne irin mai dubun nan, Allah ya so ya kusa gamawa, yana kammalawa ya kalleshi.

Ai kafin Abban yayi magana Ukhasha yayi. "Afwan akaramakallah, bamu dawo da wuri ba, abinne ba,a fara da wuri ba.."

Ya d'aga mishi hannu kawai.

"Mun gode, Allah ya k'ara girma." Zai mik`e Abban ya dakatar dashi da hannu. Ya dawo ya zauna.

Yayi gyaran murya kafin yace, "Kaje kiran da Baffan yayi maka koh."?

"Wata fad'uwar gaba ta ziyarce shi, _Abba yasan da maganar kenan, indai haka ne toh dole ya k'ara k'aimi don idan har Abba ya fara sa baki a maganar abin bazai mishi kyau ba._

"Eh naje Abba."

"To madallah, sai ayi k'ok'ari tunda ansan aje na wasu.

Ukhasha ya sunkuyar da kanshi kawai, a zuciyarshi yana cewa, _Ai ni na riga na samu.!!_

"Za,a iya tafiya, Allah ya bamu alkhairi."

"Amin, Abba sai da safe."

Ya fita, shima kanshi sauri yake yaje ya gwada number nan.

Yana ta k'okarin kira amma kiran Bahijja dake ta shigowa ya hana sau biyu yana _rejecting_ ya gaji ya d'aga rai a b'ace yace, "Wai ke meye hakane, ki kyale ni da-Allah, haba.!!

Ya katse kiran, sannan ya hau kiran number, _is switched off ake ta ce mishi_ amma ya k'i yarda sai kira yake yana kumawa,

har ya gaji ya daina, gaba-d`aya yaji ranshi babu dad'i to ko dai alhakin yarinyar can ne da yayi wa tsawa, tunda yasan irin son da take mishi bai dace ya mata haka ba. Nan take ya yanke shawarar ya kirata ya bata hak'uri ko shima Allah zai taimake shi, don ya tabbatar indai bai samu number ba ayau to tabbas ba zai iya barci ba, yarinyar ta rikita shi lokaci d'aya, musamman yau daya k'ara ganinta, ai ji yayi jininshi na tafasa, gaskiya ba k'aramin al amari ne ya same shi ba.


Ya lalubi, number Bahijja, ya kira, ringin kad'an tayi ta d'aga tare da sakin ajiyar zuciya. Shuru yayi itama tayi shuru, shi har ga Allah tausayinta ke tsarga mishi a zuciya. "Me yasa bakiyi bacci ba.?

Kawai ya fara da haka. Cikin shashshek'ar kuka ta fara magana, ba kaine kace kada na k'ara kiraka ba."?

"Ya isa toh, kiyi hak'uri kece kika batamin rai, ina gaban abbana kina ta kira.

Murna ta cika zuciyarta, yau ita ce, ukhasha ke bata hak'uri."? Wacce irin rana ce yau data zo mata da sa,a haka."?

Yana ji a kunnenshi tana sauke ajiyar zuciya, ta ma rasa me zata ce.. "I'm sorry.." Yaji tace, kana jin muryarta kasan tana cikin farin-ciki, shi kuma zuwa yanzu ya k'agu ya kashe wayar.

"Ok, kiyi bacci kinji." 

Yace mata haka, amma ita sam bata son su katse wayar, yadda take jin farinciki yau, sai ta b'ige da mishi shagwab'a. _Um..um._

"Kinga koh, meyasa haka toh ina miki magana sai ki k'iji, ni inason nayi bacci ne toh."

Sai kuma ta shiga hankalinta. OKey Dear ka hak'ura da abinda mamana ta maka."?

Cikin k'osawa yace mata yes."

"Thank you."

"Okay gud night."

Yace mata, tare da kashe wayar.

Ita kuwa farincikin daya sa mata Allah ne kad'ai yasan yawanshi. Tayi wani juyi akan gado cike da murna. Sai murmushi take, _Yau Itace ya nuna damuwa da ita haka.. Duk da ba yau kad'ai yake cewa ta daina kiranshi ba, amma tasan duk ranar da yayi mata irin haka, baya k'ara saurarar ta. amma yau shine har da biyo kiranta..? Gaskiya taji dad`i da alamun nasara sosai a tattare da ita.



Mamanta ce ta shigo, ta tsaya akanta, bayan ta k'are mata kallo, ta lura da wayar dake hannun ta tace, waya kike da wannan mara mutuncin yaron koh."?

Ta ke ta had'e rai, "mama please ki bari, stop abusing him, ni banga me ya miki ba fah!!

Uwar Tayi kwafa, "Hmm, idan an zage shi sai me, banzar yarinya kawai, idan bakiyi wasa ba, sai na k'wace wayar taki ma.

Yar ta juya mata baya tana k'un-k'u ni.

_Bahijja, yarinya ce wacce bazata wuce shekaru 19, ba, asalin yaren mahaifiyar ta Ibra ce, mahaifinta kuma, bahaushe ne, mahaifiyar ta basa tare da mahaifinta, sun rabu tun tana yarinya, kuma ta hana shi ita. yarinyar na da kirki sab'anin mahaifiyarta, bata dad'e da kammala karatun ta na secondary ba.


A tsarin Ukhasha da ra,ayinshi, sam babu irin yarinyar a rayuwarshi, yanayinta, shekarunta, yanayin tarbiyyar gidansu duk baimishi ba sam, abinda yasa ma mu,amular su tayi tsaho haka, saboda yana tausayin yarinyar, gashi shekarunta sunyi k'ank'anta ace tana fuskantar abu irin haka, ban da wannan da tuni ya yanke mu,amalarsu ko ta Yaya ne..

Kawai shi ya yarda kaddara ce ta had'a su.


_Wato wata rana ne, garin anyi ruwa irin na asubahin_ _nan, shi kanshi badon dole ba, da bazai fito ba a lokacin, amma haka ya fito aiki. Kuma ranar sai ya chanja hanya akan hanyar da yake bi, saboda yayi sauri yaje inda zashi don ya so ya makara. Akan hanyar ne ya gamu da yarinyar cikin uniform, tana tsaye bakin titi, ta rasa mota. Da kanta ta tsaida shi, ganinta da uniform yasa ya tsaya._

_Sai da ta shiga, sannan tayi mishi magana "Ina kwana.."? Don Allah can gaba zaka ajye ni, na rasa mota ne."_

"Okay, yace, mata bayan ya amsa gaisuwarta.

Hankalinshi nakan tuk'i, ya manta wayar shi akan kujerar da zata zauna ya bari, sai dai ya lura kamar ta d`auke wani abu sanda zata zauna.

Lokacin da aka k'araso makarantar su, tace masa ya tsaya anan zata sauka.

Ta mik'a mishi wayar, kawai yasa hannu ya karb'a.


 Tana ta godiya. 

Shine ma ya tambayeta sunanta,

"Babu komai, ya sunanki ne, tace _Bahijja_ "kaifa.? Yace "Ukhashatu."

Tayi murmushi ta juya tafi.




To tun a washegarin ranar, shi dai bai san ya akayi ba, kira yake ta shigowa wayar shi, da wata number, tun bai d'agawa har ya d'aga take ce mishi, Bahijja ce."

Tambayar farko daya mata shine, "Ina kika samu number ta."?

Tayi dariya kawai, tak`i bashi amsa, sai cewa tayi, "Godiya na kira nayi maka."

"Kada ki damu." 

Yace mata.

"Zamu iya dinga gaisawa a waya."?

Shi kuma ganin ta yarinya, kawai sai yace, "Eh k'anwata amma sai kin fad'amin inda kika samo number.

A wayarka na gani.

"Hmm.."ki daina d'aukar wa mutum waya."

Tace "Toh. 

"Kayi saving number."

Zanyi, sa anjimanki."

Tun daga ranar take kiranshi, watarana ya d'aga watarana ya share, shi bai kawo komai a ranshi ba, ganinshi yarinta ce , kawai. Bai ankara ba har sun shafe wata uku.

Lokacin tace mishi ta gama makaranta.

Yayi mata murna. Sannan tace, "Ko zai zo partynta."?

"Bana zuwa party.!!

Yace mata.

Tayi shuru bata yi magana ba. Sai bayan da ya manta, kawai sai gata a gidansu, abinda ya tada mishi hankali kenan, ya akayi tasan gidansu. Ta kirashi a waya, ka ganni k'ofar gidanku za,a barni na shigo."?

Yayi dariya sannan ya gimtse, "Idan kika ce wajena kika zo za,a barki mana.

Shi duk cikin wasa yake maganar.

Minti kad'an ya jiyo ta window d`in d'akinshi suna magana da Fadwa a harabar gidan. 

Tambayar ta take, "Don Allah ina zata ga ukhasha."

Ita kuwa Fadwa cikin mamaki take ta jero mata tambayoyi, wanne ukhasha."? Anan gidan, ke wacece, bama gurin Zainab kika zo ba."? Dake taga ba zata wuce sa,ar zainab d`in ba.

Babu shiri yana jin muryarta yayi sauri ya fito, lallai yarinyar bata da hankali da gaske take kenan.

Ya rasa da fuskar da zai tare ta, sai kawai ya had'e rai, "Ke dama da gaske kike."? Ita kuwa murmushi take na jindad'in ganinshi.

_"Eh, ai nasan gidan ku dama."_

Bashi da lokacin b'atawa wajen tambayarta ~_"Tayaya.?_~


Kawai sai yayiwa Fadwa nuni alamar _taje inda zata._

yana gani tana kunshe baki alamar dariya take mishi.

Yayi kwafa azuci, 

"To kije gida, kada mamanki ta nemi ki, kuma ki daina fitowa irin haka, mata basa zuwa wajen maza."

Ya fad'a yana kakkauda kai.

_"To gashi_ ta mik'a mishi, ledar hannunta. Bai karb'a ba ya tsaya yana mata kallon mamaki.

"Kayan party d'inne."

Nagode yace mata, rai a had'e zai juya ya barta gun, yaji tace, "Don Allah ka karb'a.

Baya son su tsawaita, Allah ne ma ya rufa mishi asiri abba baya nan.

"Ya mik'a mata hannu, ya amsa.

Cikin k'osawa ya mata alama, _kije gida, kije gida._ yace da ita.

Yana k'ara kallon shigarta, riga da skirt na atamfa matsatstsu, sai siririn mayafi.

Tayi Jim tana kallon shi. Shima wani tunani yayi.

_Za,a iya zargin shi fa, musamman ma,aikatan gidan._

Allah yaso a iya nan suka tsaya.

Wuce muje yace mata, don yaga kallon da take mishi yayi yawa.

Don gwara agansu tare d'in.

Sai da suka zo bakin gate d`in fita, yace mata, _"Maza kije gida na gode ki gaida mama kinji."_

Tana murmushi ta d'aga mishi hannu. Ya juya ya koma ciki da ledar a hannu.

Yana shiga yayi wurgi da kayan, a k'asa, suka zubo daga cikin ledar, memo ne, me photonta ajiki, sai tarkacen su snacks.

Lallai dole yasan abinyi, tun kafin abubuwa suyi nisa , ai baisan yarinyar haka take ba.

Sai daya kintaci taje gida ya kirata.

"Ke ya akayi kika san gidanmu."

"Um da dama na sani fah."

"To ke a ina kike."

"Can gaba da layin ku."

"Kada ki k'ara min haka, kada ki sake zuwa gidan mu."

Ya fad'a cikin kaushin murya.

Sai ta fara kuka, tana fadar wasu maganganu da bai bi takansu ba, wai ita sonshi take, ta gaji kwana biyu bata ganinshi, kuma don tazo gidan su shine yake mata fada haka."?


Shidai ya katse wayar yana, takaici. Ya zama wajibi ya yanke alak'arsu dama ya gaji.


Tun lokcin duk wani block yayi amma, chanja layi take, kamar me aiki a companin _SIM card_ da yayi block zata chanja number ta kirashi, har ya gaji ya daina, idan ta kira ya share, amma haka zatayi ta kira kamar bata da aikin yi sai kiranshi, ala dole yake d`agawa ko dan ta barshi yayi aikinshi sosai. Ya gaji da abubuwan, shine ya d`auki matakin tunda yarinya ce, bara ya bita ta yadda kwakwalwarta zata iya d'auka. "Ya kirata da kanshi wata rana yace, za,a bashi mata a gidansu.

Amma ga mamakinshi bata nuna alamun damuwa ba tace, "Ta ji yayi ta biyu da ita zata jira shi.!!

Gaba-d`aya lamuran yarinyar sun dame shi, shi ba abin ya sauya number shi ba, yana da abubuwan da suke da matuk'ar muhimmanci akan number, Misali account d'inshi na banki, da sauransu.




Wasa-wasa watansu shidda shida ita, ana fama, Allah yaso babu wanda yasan da ita idan ba Fadwa ba, itama saboda ta ganta rannan ne.!


_Sometimes yarinyar na bashi tausayi, wani lokacin ta bashi haushi, yau dai tausayinta ne yafi yawa saboda shima ya fara bin layin da take bi yaji ya akeji.._ 😂



____________

Abisa dole ya hak'ura da kiran number Basheer don tak`i shiga sam, haka ya kwanta jiki a sanyaye babu k'wari, fargabarshi shine _"Kada dai ace wrong number ya bashi.!!_





_________________

Bayan su Hafsah sun koma, gida, d'aki tayi shigewar ta, tana ta tunani, so take ta samo hanyar da zata fara kudurinta akan Jamila. _Ki jawota ajiki._ wata zuciyar tace mata haka.

Kuma tabbas taga hakan don idan basu shak'u ba ko babu alak'a mai k'arfi a tsakaninsu irin ta da, babu yadda za,ayi ta iya aiwatar ta abinda ke ranta.

_Ya ilaahiy ka taimake ni._ Addu,ar da take tayi aranta kenan. Zuciyarta na k'ara hasko mata hoton Jamila a da da kuma yadda take a yanzu data ganta a yau.

_Dama can ana fad'a mata Jamila na zuwa unguwar, har gidansu tana zuwa, kawai dai wajenta ne bata zuwa._

Ta d`auki wayarta kamar zata yi wani abu da ita sai ta tuna cewa, ba ita ta amshi number Jamila ba, Jamilar ce kawai ta karb'i 

tata Number.




Tana kwance, zainab ta shigo d'akin, da waya a hannunta, cikin k'asa da murya tace "Yaya ga Na'eem zaku gaisa a waya yace na baki."

Hafsah ta girgiza kai, alamar ba zata karb'a ba. Zainab tayi saurin katse wayar don kada a bata mishi lokaci ko Hafsah ta fad'i wata magana mara dad'i, ya jiyo.

Suka fuskanci juna Hafsah ta fara magana. 

"Bana ce ki daina kula yaron nan ba."

Zainab tayi shuru ta sunkuyar da kai, haka kawai Hafsah bata son Na'eem ita kuma bata ga aibunshi ba.

"To zan fad'awa abbah tunda haka ne." Hafsah ta k'arasa fad'a.

"Haba Yaya wai me Na'eem din yayi ne.."?

Zainab ta fad'a cikin shagwaba.

"Ban sani ba, nidai nace ki rabu dashi."

Zainab ta turo baki sannan ta tashi ta fita.

_Duk da Hafsah bata fiya takura ba, amma bata barin k'annenta su fad'a halin da zasu cutu, haka kawai taji Na'eem bai mata ba, kuma don taga alama ba aure ne gabanshi ba kawai yana son ya b'ataw K'awarta lokaci ne._

_Shi kuma daya fuskanci cewa Hafsah bata yinshi, shine yake zuwa da siyasa, ko yaushe idan ya kira a waya sai yace a bawa Yaya su gaisa._

_Hafsah bata son hakan tana ganin ba zata zuba ido, k'annenta su fada irin halin da ta tab'a shiga ba shiyasa take tsaye kam akansu, duk wani motsinsu akan samari ta sani._





BASHEER

________________ B'acin ran Hafsah bai barshi ya zauna a gida ba. bayan sun dawo gida, yayi alwala ya fice, don ya tabbatar idan ya sake suka zauna zaman hira da ita, hirar Jamila zatayi ta masa, shikuma ba zai zauna sauraro ba, don haka daga masallacin, ya nufi wajen wata _snooker_ can bayan layinsu. Bisa Tsautsayi kuma, sai wasu suka fara cha-char baki har takai sun fara kokawa, akan musun _snooker._ Basheer ya shiga tsakiya, har da shi a masu rabon fad'an gashi wajen an cika. Lokacin kuma wayarshi na aljihun wandon shi ba baya, sai da komai yayi _settled_ sannan ya nemi hanyar dawowa gida, lokacin an kiran sallar isha'i.

Sai da ya shigo, gida, yayi alwala, zai fita ya laluba aljihunshi don yasa wayar a chaji, yaji babu komai.

Gun Hafsah ya nufa, tana palour tana cin abinci, _"Sister an sacen wayata fah._

"Ta zaro ido, a ina yaushe kuma."?

Gashi ban ganta ba, "Ina tunanin wajen snooker da naje ne." 

Bata ce komai ba, tahau kiran wayar amma _is switched off_ ake ce mata itama.

_Basheer ya fice, kawai ya nufi masallaci ya barsu suna, jajantawa.._




📝 

*HAJEEYAH KHAREEMERH*

♥️♥️♥️♥️

*ZAZZAFAN SO*

(masoyin k'warai)

*Cigaban littafin Zazzafan so*

*(Guba ne)*

💔💔

*By:*

*Karima Tijjani Mansur*

*(Hajeeyah khareemerh )*

*Dedicated to Unique in your love heart group members.*




📄 *47*






*Da* safe Ukhasha, da kiran number Basheer ya karya, amma _still is switched off._

Wata irin zufa ce ta hau tsatstsafo mishi, _ya Ilaahi_ anya kuwa number daidai ce, kada fa ace _yaga samu yaga rashi._

Ya tuna cewa yana da d'aurin auren _JB_ dole ya tashi ya hau shiri. Yana toilet wayarshi nata ringing.

Har ya fito, kira na k'ara shigowa, ya duba, sunan _JB_ ne ya fito wato angon.

_UK me kuke nufi ne, ya zaku barni ni kadai gashi har na shirya banga ko dayan ku ba."_

"Kai Dallah can wanka nake, kaga sarkin zumudi dududu, k'arfe tara da rabi fa yanzu, zaka dami mutane." 

_"Iyehh, Lallai ma UK wato kaima kabi layin su Mubarak kenan koh, kada ka manta ni yayanka ne yanzu."_

Ya shek'e da wata dariya, "Haha, gaskiya ne, dan rainin wayo."

_Please UK don Allah ka taho."_

_

"Okey ganinan Allah, k'arasa shiri zanyi kawai.

"Yawwa aboki, abokin gwauran taka."

"Hmm, Allah sai kasa na fasa, zuwa yanzu."

Ahh yi hak'uri, rufamin asiri.!!

Ukhasha yace, 

"Kai da bikin naka ma, damuwa ya gadar min."?

_"Ahaba UK kada dai wannan matar, ta k'ara kiranka neh."?_

"No no no, ba ita ba, wata yarinya ce fah ranar yinin nan."

"Oh wai wacce akace ta yarfa ku koh."?

Suka shek'e da dariya duka.

Hmm, au kace har kaji labari, gaskiya su _NZee_ (_Nazeef _)munafukai ne.!!

"Ka bari kaidai ku nutsu don sai kun nemo min ita kaida amaryarka.."

_"Haha, UK ashe gaske ne, kenan ka zurma".._

Yai ajiyar zuciya. "Ya na iya.? Suka had'a baki _JB na cewa "Allah ne ya kamaka"_ 

Shima na cewa "Allah ne ya kamani ni."

Haha, kaima ka fad'a ko da kanka, amma babu komai aboki Allah ya sanya alkhairi.

To ya zakayi da 'yar kwailar can. 

"Kai chab zaka b'atan rai wallah, kusan yadda zakuyi da ita dai."

_"Hmm, Allah ya kiyaye ka Aboki, amma akwai dan barwa.!_

Amin ango, bari na shirya kada mu b'ata lokaci.

An kammala komai anyi d'aurin aure, su Ukhasha ansha zirga zirga har zuwa lokacin kai amarya. Hidimar da suka shiga ne, yasa ya d'an manta da damuwar shi, don bai ma samu ya zauna ba. Allah-Allah yake washegari tayi, ya bujurowa da ango abinda yafi damunshi, wato inda zai sami 

Hafsah..





___________________

Ta tsammaci kiran Jamila amma shuru, sai yau da daddare, sai ga kira, da wata number.

"Hello, 

Hafsah ma tace Hello,

"Kina magana da Jamila ne."

Murna ta cika Hafsah, "Oh ya kike.?

"Lafiya lau, wannan ne number sai kiyi save."

Okey Hafsah ta fad'a.

"Bye bye."

Jamila tace, tare da katse wayar.

Hafsah bataji dad'in takaitacciyar wayar da sukayi ba, taso suyi 'yar hira, don ta gano wane mataki Jamilan ke kai."?

Amma kuma taji dad`in samun number, tayi saving d'inta da nufin gaba ita zata kira..

Ukhasha, yayi juriya, har ya bari akayi Kwanaki uku, da bikin Jabeer ( _kafin ya fara mishi zancen Hafsah_ ) 

Duk kwatancen da yayi mishi kuma, sam Jabeer ya kasa gano wacece.. 

Kuma yaga alamun Ukhasha d`in ya damu sosai.

"Wai Aboki na baka san sunanta ba neh."?

Um kai dai bari JB wallah, na fada maka har ganinsu na karayi ranar dinner d'inka, ( _Ya bashi labarin yadda abin ya faru._) ka ga amma kullum sai nayi trying number amma har yau _is switched off._

Kasan taimakon da zanyi maka."

JB ya fad'a.

"A,a"

Kaga nan da k'arshen sati zamu, d'aga (_zasu bar k'asar_) so kazo gobe kawai akwai photos da video na biki ko za,a dace.!!

Murna ta cika ukhasha, kuma fa JB ya kawo shawara.

"Wow thank you angon Aisha, gobe da asuba zaku ganni.

"Hah, kazo d`in kaga mana." 

"Nagode kai dai."

"Okay UK ana tare fah."

Sukayi sallama, suka katse wayar.

Ya tashi ya nufi d'akin hajiyarshi.

Suna zaune ita da su maryam da Fadwa suna kallo.

Ya nemi guri a k'asa ya zauna, Hajiya ta kalleshi a zubo maka abinci."?

Ya daga kai alamar "eh.

Maryam jeki zubo mishi abinci.

"To Hajiya." 

Sannan ta mik'e ta mik'e, ta fita.

Sai lokacin kuma ya kalli Tv, d`in, wani shiri ake gabatarwa, dama an hasko wata mata ne tana ta jawabi, sai yanzu aka hasko mai gabatar da shirin.


Gabanshi, ya fad'i, saboda bayyanar fuskar da yake ta bulahin nema.

Ya ware ido, yana kallonta, yanayinta, kamannin ta, Itace dai daya gani a zahiri.

Zata fara magana, kenan d'if TV ta d`auke da alama NEPA ne suka d`auke wuta.

Ranshi yayi bak'i ya mik`e zai fice, shi ko jira ma a kunna solar ko yaje ya kunna ma baiyi ba.

Hajiya ta kalleshi. Ina kuma zakaje."?

Ina zuwa Hajiya.

Ya fice ya nufi d'akinshi.

Number JB ya kira.

_"Ya akayi kuma."?_

"Kaii yarinyar nan zata zautani fah."

_Meya faru."?_

Wallahi a TV na ganta yanzunnan tana gabatar da program.

"Hmm, kaii UK kodai zaucewar ce ta sa take maka gizo."?

"Ka manta, ai ban zama _majnoon_ d`in ba tukuna.

Jabeer yayi dariya, "ah to naga abin naka yayi over ne, ni ka dameni ma fah.

Hmm, to ya zakayi dani, ni nace ku gayyatota bikin ku."?

"Hmm, haka kace koh."?

"Aa sorry Yayana tuba nake."

Abin ya bawa JB dariya, _"Lallai, su Mubarak su zo akwai labari._

A,a JB kada kamin haka plz ka san halinsu bazan iya dasu ba.

Shikenan toh, amma ko ban fad'a ba zasuji labari kaidai sai kazo.




Washe-gari daya je, Gidan JB, bai bata lokaci ba ya k'ara mishi jawabi, amarya na zaune na jinsu, sai da angon yayi tambayeta sannan ta magantu, _"Aysha kin gane ta._?

"Ina tunanin ko H Hamid, ko kuma Ummi nuhu, sune suke service a gidan tv."

Please ki taimaka bari naga photos d`in.



Photo album, na bikin suka miko mishi, sai da yaje kusan tsakiya kowanne photo kallon k'urilla yake mishi, ango nata zolayar shi shida amarya. Sannan da kyar yaga wani photo, ta gefe, fuskarta bata fito sosai ba, anyi, musu tana lik'i.

"Wannan ce.!!

Ya fad'a da sauri kuma da k'arfi.

ango ya karb'a ya mik'awa amaryar.

"Eh Itace.

Tare suka hada baki shida JB wajen cewa, "wacce daga ciki."?

"Hafsah H. Hamid ce."

Azuciyar shi ya maimaita sunan _Hafsah_ sunan hajiyarshi kenan fah.!!

"Duba don Allah ki taimaka min da number ta." 

"Ai kasan chanjin layin nan da nayi Allah yasa akwai contact d`in."

Ta fada tana duba cikin wayar, kaf babu number aciki.


Ta dube shi itama ya dan bata tausayi wallah kaga babu.

_Innalillahi."!!_

JB ya dafa shi, kada ka damu, ai bazamu bar k'asar nan ba, sai an samar maka solution, don bazan zuba ido a zautar min da UK ba.!!

Ukhasha, yaso ya tambayi amaryar _"ko tasan gidansu ta kwatanta mishi.?_ Amma sai ya fasa, yaji nauyin hakan, kada suga kamar ya takura musu.

Abisa tilas ya hak'ura, ya dawo gida a sanyaye, don kafin ya taho ma, sai da aysha ta gwada number wata k'awarsu, don ta turo musu number amma wayar tak'i shiga..

_Sun rabu akan, ana samu JB zai turo mishi. Yayi musu godiya sosai, sannan yabar gidan.._

A takaice dai sai ranar alhamis da dare, sannan number tazo, wajen ukhasha, shima da daddare wajen k'arfe shad'aya, duk zumud'inshi, dole ya hak'ura zuwa da safe. Yayi godiya ga Allah ba adadi.




Washegari sakayau yake jin shi, cikin nishad`i da karsashi yayi shirin fita office.

Ya nufi d'akin hajiyarshi ya mata sallama, sannan ya fito. Har ya isa bakin motar shi zai sa mata _Key_ yaji an kwalo mishi kira. _Yaya Ukhasha!!_ 

Mahseem ce autarsu cikin uniform.

Ta Kara'so da gudu ta d'ane shi.

"Muhaseem zaki karya ni fah.

Tayi dariya. Sannan ta sake shi.

"Yaya don Allah na bika ka sauke ni a school."?

"Eh muje." Ya zagaya ya bud'e mata k'ofar ta shiga. Sannan shima ya dawo ya shiga ya zauna. Ya tada motar aka bude musu gate, suka fita.

Suna tafiya tana damunshi da hira, "Yaya, wai yau Friday koh."?

Eh, ya akayi."?

"Zaka je dani Masjid d`in abba."?

"Waya ce miki mata na zuwa masjid."?

"Our islamiyya teacher, kuma su yaya Maryam suna zuwa wataran, amma sunki suje dani."

"To zanje dake, amma ni ba masallacin Abba nayi niyyar zanje ba, amma tunda kinaso to zamuje sai ki shirya da wuri, nima zan dawo da wuri."

"Thank you, Yaya."

Tayi shuru, sannan ta kuma samun abun cewa, "Yaya wai aunty Fadwa tace wai an kusa bikinka."?

Yayi murmushi me sauti, _"Kai fadwa ta raina shi, wato abin ma har ya kai a gaban Mahseem suna gulmar shi._?

Ta katse mishi tunani "Eh Yaya."? 

Ya d'aga mata kai, alamar Eh."

"To ya sunanta."?

Ahankali yace mata, "Sunan Hajiya ne da ita."

"Yehhh, yaya mu dinga ce mata hajiya itama."

"To, kiyi mana addu,a idan mukaje masallaci."

"Yaya me zance toh."

_Kice Ya Allah ka taimaki Yaya ukhasha!!._

"To yaya zanyi, dama "Abba kullum sai yace mu dinga yin addu,a."

"Yawwa, 'yar autar mama, nagode.

Yayi parking, sannan ta fito, don anzo k'ofar makarantar su.

"Yaya adawo lafiya, zan shirya da wuri. 

Ya daga mata hannu. Yana gani ta hango wasu k'awayenta ta tafi da gudu wajensu, sai ta bashi dariya ma.




Sanda ya dawo har Mahseem ta gama shiryawa, lokacin, shikuma, yana d'akinshi ya gama shafa mai, tazo bakin k'ofa ta tsaya.

Yana jiyo, hayaniyar su Zainab daga cikin gida, suna tsokanarta, _"Inyeh yau za,a masallacin Abbah!!_

"Salamu alaikum. Tayi sallama daga waje, yayo mata magana daga ciki, don bazai bata izinin shigowa ba, "Mahseem ki jirani kinji, kije d'akin Hajiya."

Ta koma ciki shi kuma, ya cigaba da shi shirin shi, cikin nutsuwa, gefen zuciyarshi da tunanin Hafsah, so yake sai ya dawo daga masallacin sannan ya gwada kira. Yana so ne sai yayi addu,a sosai ya nemi d'aukin Allah da alkhairansa cikin abin.

Yayi kyau cikin farar shaddar shi, da bak'ar hula, bakin takalmi, da kuma agogo.

Ya nufi d'akin hajiyar, shi kanshi daya ga Mahseem sai da dariya tazo mishi, taci hijabi har k'asa, ga tasbaha a hanunta.

hajiyar bata nan ma. Tana ganinshi ta taso da gudu ta rik'e hannunshi.

Shima ya kama nata, idon Fadwa akansu, zatayi magana irin ta zolayar data saba ya kafe ta da ido. "

Zoki mana photo, sai kiji dad`in kallon mu sosai."

"Kai Yaya ni baku nake kallo ba.!

Ta matso ta amshi wayar, tayi musu, sannan ta mik'a mishi kayarshi.

_Ya karb'a sannan yaja hannun Mahseem, suka fita, tana mishi hira.._




📝 

*HAJEEYAH KHAREEMERH*



♥️♥️♥️♥️

*ZAZZAFAN SO*

(masoyin k'warai)

*Cigaban littafin Zazzafan so*

*(Guba ne)*

💔💔

*By:*

*Karima Tijjani Mansur*

*(Hajeeyah khareemerh )*

*Dedicated to Unique in your love heart group members.*

📄 *48- 49*

*Yaune,* suke yinin, Fateemah, sun kacame, a wajen biki, ana ta rawa... 

Bikin na matuk'ar dad'i a gurinsu, sun had'u duka 'yan matan, har da matar Nazeer ma, anata rawa, da yake, yinin iya mata ne babu mazaa, ko ango bai halarci wajen ba.

Adaidai wannan lokacin kuma Ukhasha nata kiran number Hafsah tana ringing amma ba,a d'aga ba. Da ya kira karo na uku, sai ya hak'ura kawai.

Yayi shuru ya zuba wa _number_ ido, tunani yake kodai, ya hak'ura ne."? Sai kuma yayi wani tunani. _"A yadda take, kuma tana irin wannan aiki a media, dole baza,a rasa, masu damunta da kiraye-kiraye haka ba. Saboda haka zai jinkirta zuwa wani lokaci kawai._

Zai cigaba da addu,a idan da alkhairi akan abin, Allah ya sauk'ak'a mishi samunta. Wani tunani mara dad'i ya d'arsu aranshi. _Yanzu idan an riga an bada ita fah?_

_"a,uzubillah_ 

Ya fada a fili, bai ma san ya zai kwatanta halin damuwar da zai shiga ba idan haka ta faru..

Da Wannan tunanin kuma ya shiga wani tunani, na daban, wata zuciyar ta karanta mishi.

_To ita yarinyar mutane da kabar ta da damuwa akanka, ya zakayi da ita.. Ko kana ganin zaka samu yadda kake so, alhanin kana da alhakin wata akanka."?_

A hankali ya furta, _"Allah ya gani bana sonta, bazan iya zama da ita ba._

_To ka sama mata mafita, tunda kana kokarin kulla taka soyayyar a wani waje._

Wata zuciyar ta fad'a mishi haka.

To wacce irin mafita, menene mafitar."?

Ya tambayi kanshi.

Kamar an tsikare shi ya jawo wayarshi, ya danna kiranta.

Cike da farin ciki ta d'auka.

Tayi mishi sallama, ya amsa cikin sakin fuska. Tana mamakin sauyawar shi, cikin kwanakin nan.

"Bahijja!!

Ya kira sunanta.

Na,am.

Ta amsa ad`an sanyaye don tana tsoron abinda zai fito daga bakin shi.

_Sau dayawa indai zaiyi mata magana mara dad'i yafi bata hankalin shi, da kuma jawo hankalinta._

Yaushene ma kika ce min zaki cika _twenty years.?_ 

Farin-ciki ya mamaye ta. _Kodai party zai had'a mata ne."? Sai kuma ta tuna irin gidansu, sannan ta tuna data gayyace shi partyn graduation, yace mata baya zuwa party._

Tana son jin abinda zai fad'a mata don haka tace, "Nan da _three months._

"Okey.." yace mata kawai.

Tayi shuru tana son taji k'arin bayani.

_Wato ma ko 20yrs yarinyar bata cika ba. Ya fada a zuciyarshi. Baya son ta shiga damuwa a k'ananun shekarunta. Tabbas ma yaga tsaurin ido da k'ok'arin yarinyar, da har ta iya furta mishi tana sonshi, ashekarun haihuwa fa zai iya bata goma sha uku fa. Sai kuma ya tuna _shekaru ba sune abun dubawa ba indai da so._

"Meya faru neh Dear."? 

Tambayeshi, jin yayi shuru babu k'arin bayani. 

Babu komai, kawai na tambayeki ne.

Ta danyi jim, kafin tace, _"Okey"_

"Yaushe zaku fara lecture, a makaranta."?

Ya tambayeta.

Nan da _2weeks_ fah. Tana jin dad`i a ranta, yana janta da hira.

"Ina mamanki."?

"Tana nata room."

Ta fada da mamakin tambayar kodai wani abu ya k'ara faruwa neh. Kafin ta samu damar magana, 

ya saita muryar shi, cikin nutsuwa ya fara magana yace. 

"In tambayeki Bahijja ."?

Ta danyi shuru kafin tace, "Um."

"Please ki fahimci tambayata kada ki _getting dina wrong."_

Cikin sanyin jiki tace, "Toh inaji."

Kasan zuciyarta na tsoron abinda zai fito daga bakinshi.

Meyasa, da maman ki ta nuna bata son mu,amularki dani baki d`auki mataki ba.??

Tayi d'if don bata da amsa.

"Uhum."? Ya sake ce da ita.

"Me ta k'ara yi maka ne,?_was something wrong happened again.?_

Ta tambayeshi da damuwa.

"No, no no, kawai naga ta damu akan abin ne, kuma nima nayi tunani to this time ya dace ace muyi mata biyayya, mamanki ce tana da hak'k'i akanki, kuma zata fiki sanin what's right for you."

Ya fad'o maganar kai tsaye.

Ai kawai sai ya fara jiyo shashshek'ar kukanta. "Why all this dear, kawai kace abinda mama ta maka ne, ba zaka iya d'auka ba, but since when muke tare da kai and you knew that mama bata so kuma bakayimin wannan tuhumar ba sai yanzu."

Ahankali yace, _"Calm down plz, ki daina kuka mana._

Sukayi shuru kafin yace, _ Bahijja Kinsan girman iyaye kuwa.."?_ _Kinsan girman da Allah ya basu.? Mamanki nada hak'k'i akanki, duk abinda bata sa mishi albarka ba cikin rayuwarki bazai yi miki amfani ba yadda kike so. Ina son muyi magana da ke, amma ki cire aranki don cewa abinda tayi min ne yake damuna, wallah is not, kawai naga time yayi da za,ace kin mata biyayya, ke ba yarinya bace, please mu hak'ura da wannan alak'ar, mu chanja mata suna, ki dawo k'anwata zaifi mana dad'i kuma mamanki zata fi amsar hakan pleasse!!_

Kamar ya bata sakon mutuwa, haka kalaman nashi suka shige ta fiye da koyaushe da yake fad'a mata irinsu, a muryarshi ta fahimci da gaske yake ya gama shirin tsinke zaren alak'arsu. Sai ta fashe mishi da kuka mai tsuma rai, shi kanshi sai da ya cire wayar daga kunnenshi sannan ya mayar.

Zuciyar shi ce ta karanta mishi, _"Ukhashatu idan fa tausayinta zaka tsaya, sam ba zaku je inda kake son aje ba._

_Cikin dakewa yace, "Ki daina kuka, ke banda abinki mene abin kuka cikin wannan maganar, ni da ke fa bamu muke da ikon kanmu ba, kiyi tunani, akan abinda nake hango mana, alak'ar yaya da k'anwa ita tafi dacewa damu fiye da wacce muke yanzu."_

Ta saki ajiyar zuciya, "Me nayi maka laifin me nayi maka."?

"Ya salam, Bahijja, me kwa kika min, me zaki yi min, me yasa kike tunanin kinyi min wani abu."?

Cikin bacin rai ta tace,

" Eh mana, saboda naga gaba-d`aya ka nuna ka gaji dani, baka son cigaba da kulani koh, wai baka ganin irin son.."

Sai ta k'ara saka kuka, tana tausayin kanta, _wai mene haka ne, wane irin soyayya aka jarabce ta dashi."?_

Kiyi hak'uri kinji, ina sama mana maslaha ne ni da ke, bama son gaba ki zargeni."

A fusace ta cafe zancen, _Idan kayi aure ba."? Saboda ni baka buk'atata cikin rayuwarka, baka sona._

Yayi shuru, yana juya zancen, kuma fa, hakane, zancenta baya son ta zarge shi, ranar da zata wayi gari an d'aura mishi aure. Amma yanayin maganar ta bashi mamaki, hakika bata cikin hayyaci da har ta iya fada' mishi magana da irin wannan sigar, da babu _respect._

"Bansan me zance miki ba Bahijja, amma kin san halin da ake ciki, ina fad'a miki ba ba tun yau ba, Abba na yayi min zab'i!!

Babu shiri ta dawo da kukanta. _Kenan zancenta na kan hanya aure zaiyi._

Don girman Allah, kiyi hak'uri kiyi addu,a, Allah ya had'aki da mafi alkhairin zab'i cikin rayuwarki, ki daina kukan nan, ni ba ce miki nayi mu rabu ba fa, na sama mana mafita ne, kuma na miki alk'awari zan zame miki Yayan da xakiyi alfahri da shi kiyi hak'uri kinji.!!

Abinda ya shiga fada mata kenan, don ya rasa, abin cewar komai daya tanada don ya furta mata ya fad'eshi, yasani rabuwarsu ba zata zo da sauki yadda yake so ba.

"Nagode, Nagode, abinda tace mishi kenan. Ta katse waya.

Yayi jim yana tunani, gwara taje tayi tunani, don bashi da wani abin k'ara mata akai, ya tabbatar idan ta nutsu zata sakko kuma yayi kudirin bazai k'ara nemanta ba, gwara ta fara koyar rayuwar da babu shi. Amma bari ya k'ara da tura mata sakon waya yana so ne ta yarda da abinda yake zuwa mata dashi ta laluma, kafin ya janye jiki, ta k'arfi idan yaga abin ya faskara.

_Wallahi ban tab'a sawa raina zan wulak'anta mai so na ba.. Bahijja ban san ya zanyi ki fahimce ni ba, amma ki d'auka wannan shine maslaha agaremu, kiyi hakuri kiyi tunani akan maganata._

Iya abinda ya iya rubuta mata kenan.

Ta duba sakon, tayi shuru tana tunanin abubuwan daya ce, da kuma abinda zaifi zamar mata mafita..

_______________

Tazarar kwanaki biyu ya bawa Hafsah, bai k'ara kiran number d`in ba sai ranar litinin.

Haka ma, Bahijja tun ranar bata k'ara kiran shi ba, hakan ya masa dad'i, _gwara ta saba,_ amma a k'asan zuciyarshi akwai tausayinta fal.

*HAFSAH*

_______________

Tana kwance, tana hutawa, ta gajiyar bikin da suka sha, a yammacin ranar litinin. Danna wayarta take, tana k'ara kallon photonan da sukayi.

Kira ya shigo cikin wayar da wata number, ta d'aga ta kara a kunnenta.

*UKHASHA*

______________

Ba k'aramin farinciki yaji ba, ganin an d'aga kiran nashi, ga seconds har sun fara tafiya.

"Assalamu alaykum."

Ya fad'a cikin nutsuwar murya.

Muryar ta shiga cikin jikinta sosai.

"Wa alykm salam."

Ta amsa da k'aramin sauti.

"Barkanki da yamma, ina fata kin yini lafiya."

Damuwarta shine taji da wa take magana, amma babu yadda zatayi dole ta amsa gaisuwar shi.

"Lafiya lau Alhamdulillah."

Tayi saurin tambaya. "Am sorry ban gane me magana ba."

"Okey hakane." kai tsaye yace. "Sunana _Ukhashatu Abubakar_

Tayi shuru tana son ta tuno ko tasan me irin sunan.

Bai barta da wannan ba sai ya k'ara mata da, "Ina magana da Hafsah ne koh."? 

Ahankali tace "Eh itace. Sai dai banajin ni Hafsan kake nema."

Muryarta tayi mishi dad'i don haka ya kashingid'a, sannan yayi murmushi me sauti. 

"Me yasa kika ce haka."?

Mamakon ta amsa, sai tace cikin k'osawa. 

"Kafad'a min wanene kai yadda zan gane inaga zaifi koh"?

"Ayi hak'uri toh, amma na fad'a miki sunana.

"Bansanka ba ai."

Ta fad'a kai tsaye.

Ya k'ara tattara nutsuwar shi.

"Naga kin gaji dani bari na miki bayani."

"Hmm.." tace mishi, kuma kamar yasan hakan ne.

(Muryarshi tafi komai jan hankalin ta.)

"Sunana Ukhashatu, kiyi hak'uri na kiraki bada izininki ba."

Yad'an dakata, yayin da ita kuma ta bada dukkan nutsuwar ta gareshi.

Bazan boye miki ba, samun number ki ba abu ne mai sauki ba, _i witnessed that._

"Kiyi hak'uri naga babu hanyar da zan iya miki magana ne idan ba ta wayarki ba."

Tayi shuru don babu abin cewa.

"Na rok'i abani number ki ne sai kuma nayi dace aka bani.

Waye ya baka."?

kiyi hak'uri zanyi miki bayani gaba.

"To ina ka sanni ni.?

Hmm, na ganki a wurare da dama."

ka fad`amin, kawai."

Na ganki a television ne kina _program_ d'inki."

Bata san sanda tayi murmushi ba tare da cewa sai kuma ina."?

Shima murmushin yayi, zan fad'a miki sauran amma ba yanzu ba.

"Hmm, ka fad`amin wanda ya baka number ta.

"Allah ne ya bani."

Ya fad'a da zolaya.

Hmm, _I knew that._

Tace mishi.

Ya k'ara yin murmushi, "Yawwa don shi na rok'a kuma ya bani."

Bata k'ara cewa komai ba.

Suka danyi shuru.

Sannan tace, "Okay toh sai anjima."

"Kiyi hak'uri by time zaki gane wane ni, sannan ki min alfarma guda d'aya."

"Tame fah."?

"Kiyi saving d`in nombar nan don Allah.

"Banyi alkawari ba.!"

"Girmanki ne ai, nagode, ki huta lafiya.

Ya katse wayar lokaci d'aya.

Ya barta da tunani.

Wanene wannan, me nutsuwa, dad`i da kuma sanyin murya."? Me yasa ya kirata ya mata haka."? Babu alamun k'uruciya a Yanayin muryarshi da zantukan shi, bare tayi tunanin rainin hankali ne irin na samari.

Yace, _by time zata gane wanene shi._

To Yaushe yake nufi kenan."?

Yace _Allah ne ya bashi number ta._

Yana nufin ba zai fad'a mata inda ya samu ba kenan.?

Kai akwai alamar tambaya.!! 

Ita ko irin mutanen da ke kiranta ne, ba haka ta saba amsa gaisuwar su ba, yawanci ma anfi kulata a chat ko ta email. Idan kuwa aka kirata kai tsaye za,ace _muna jin dadin shirinki, kina burgeni wallahi, abubuwa makamantan haka dai._

_Amma shi fa?_

Sam ba da haka yazo mata ba, sai ma afuwa da yake ta nema akan ya kirata, bada izini ba. Kuma yace a TV ya ganta, ta kasa yarda da hakan.

Duk yanda akayi yayi mata kyakykyawan sani, data gaji da b'ata lokaci wajen tunane tunane sai kawai ta share abin, amma fa takan tuno muryarshi lokaci zuwa lokaci.

Bangaren shi, farin cikin daya shiga bazai misaltu, bisa jin muryar ta da yayi ayau d'innan.

"Alhamdulillah Alhamdulillah yake ta maimaitawa. Azuciyar shi, yana addu,ar Allah ya mallaka mishi ita.

Kowa na gidan ya gane yana cikin farin ciki yau, haka kawai ya fita yayiwa driver ( _wanda ya kaishi gidan baffa_) kyauta, bisa tuno kalaman shi masu hikima.

_Ranka ya dad'e ai aure yana cika darajar mutum ne.. Tunda manya sun nuna suna so sai ayi musu kodan biyayya._

To shi ba auren yayi ba ma, amma farin cikin da 

yake ciki Allah ne kad'ai yasan adadinshi.

Bai k'ara kiran ta ba, har washegari, gwara ya barta ta huta, tunda babu sanayya a tsakaninsu, bata sanshi ba sam. Kada ta gaji da shi.

Sai da daddare ya kirata bayan kwana biyu, batayi saving number d`in ba, amma muryarshi ce tasa ta gane shine.

"Assalamu alaykum.

Ta amsa mishi itama.

"I hope ba kiyi bacci ba na tashe ki." Ya fara da haka.

"No." Tafad'a.

"Kingane mai magana."? 

Azahiri amsar ita ce "Eh, amma saboda ta ja _class_ sai tace, "Aa."

Yayi murmushi, 

_"To Ukhasha d'innan ne dai mai nacin nan."_

Ya bata dariya babu shiri. _"Hmm_ tace mishi kawai.

Yayi k'asa da murya, yana rok'o.

"Please ki taimaka kiyi saving number nan mana."?

"No banyi alkawari ba." 

"Meyasa."

"Saboda bansan ka ba."

Cikin marairaice murya, irin ta wanda ake tuhuma yace, 

"Wallahi sunana ukhasha, ba karya na miki ba.!!"

Ya bata dariya sosai, wannan wanne irin mutum ne, mai barkwanci haka Allah ya had'ata dashi..?

Gashi sai yayi magana kamar bashi yayi ba, da nutsuwa a muryarshi sosai haka daga jin shi babba ne da saita ce, _irin rainin hankalin samari ne._

"Hmm, inda ka sami number ta shi nakeson in sani."

Ta fad'a bayan ta gimtse dariyarta.

"Oh tun a duniya ne fah na samu.!!

Sai da tayi da gaske sannan ta tsayar da dariyarta wannan karon.

"Hmm, Bazaka fad'amin ba koh."?





Post a Comment

0 Comments