TOP HAUSA NOVELS atOptions = { 'key' : '20e08520dad54dbf6d9e963271

Babu so page 63

       *_❤‍🔥BABU SO....!!❤‍🔥_*

                 _(Miya kawo kishi?)_




              *_Bilyn Abdull ce🤙🏻_*


*_BABU SO👉🏻AREWABOOKS_*


*_63_*



.........Tsaf ya shanye jambakin, zaune takai tana sauke numfashi, shima barin wajen yay da ɗan hanzari, tanaji ya buɗe toilet amma bata iya ta ɗago ba. Babu jimawa ya fito da alama wata sabuwar alwalar ya sakeyi. Ƙofa ya nufa batare daya yarda ya sake kallonta ba yana faɗin, “Ki tashi kiyi salla”.

       Iska ta furzar mai ƙarfi da dagowa tana kallon kanta ta cikin mirror, sai kawai ta samu kanta da kai hannu ta shafi lips ɗin nata da sakin murmushi. “Fitinanne”. Ta faɗa a hankali tana mikewa. Itama alwalar ta ɗauro, bayan ta gabatar da salla samun kanta tai da komawa gaban mirror ta sake gyara fuskarta da ƙyau cikin simple kwalliya. Kwalli, lipstick ɗin daya saka mata ta ɗan gyara girarta siririya da ƙara powder. Ita a karan kanta sai da ta tsaya kallon kan nata dan wani ƙyau taga ta kara, tai guntun murmushi da ɗaukar turare ta ƙarama jikinta..


          Ana idar da salla ya dawo gidan, saboda makara salla daya nema yi bai shiga sashen Fadwa ba ya wuce, yanzu kam daya dawo sai ya fara nufar can, wannan ƙa'idarsace, akowace salla in har yana gida sai ya tabbatar da mace tayi hankalinsa ke kwanciya, ko yana office yakan ƙokarta ya kira domin tambayar kinyi salla, hakan ya ƙara ƙarfafa Fadwa domin waya takan ɗauki hankalinta ta kasa tashi yin salla akan lokaci kafin zuwanta gidansa matsayin mata. A bedroom ya sameta ta idar da salla fuskarta duk babu walwala. Ya ɗan tsura mata ido na wasu sakanni kafin ya ƙaraso ciki sosai. Sau ɗaya ta kallesa ta janye idonsa da masa sannu ciki-ciki.

     “Wani abu ya faru ne?”.

Ya tambaya a maimakon amsa mata sannun da tai masa. Batai magana ba, sai dai ta sake ɗan tsuke fuska. 

   “Nasan kin jini fa”.

Kamar bazatai magana ba sai kuma ta ɗago idanunta dake tara ƙwalla tana kallonsa, “Soulmate karka juyamin baya dan kayi aure, maƙiya zasu iya yimin dariya”.

     Mamaki shinfiɗe akan fuskarsa yake kallonta. “Juya baya kamar ya? Anyi wani abu ne?”.

      “In ma ba'aiba ga hanyar yi nan an ɗakko ai. Tunfa da matarka ta dawo gidan nan yau baka sake leƙoni ba, kana ganin hakan adalci ne? Yaufa ko zuwa kacemin na tashi nai salla bakayi ba, kuma tun ɗazun kana'a sashenta ita dan daga can ka wuce massallaci, gaka nan harda canja kaya alamar yin wanka”.

   “Dama kin saka a ringa miki gadina ne? Ko kuma shiga sashen nata ma akwai wata ƙa'ida ta mintunan da zanyi na fito? Ni da matata kuma kina tuhumata dayin wanka kamar wanda ya ajiye wata karuwa”.

       “Niba haka nake nufi ba, amma dai koyaya ai sai kana adalci. Jiya yini guda kuna tare a asibiti, hakama yau tun fitar safe da kai kuka dawo tare kana a sashenta”.

  Sosai ɓacin rai ya bayyana akan fuskarsa, idanunsa daya tsareta da su har suna canja launi. “Okay ke da sokike na watsar da ita kenan a asibitin nazo na tare a wajenki bayan nine sanadin zuwanta can. Ko kuma dan kar ranki ya ɓaci bazanyi wanka a sashenta ba?. Look Fadwa idan kikace zaki ɗaukemu zuwa wannan layin bazaki taɓa shan lalai a wajena ba. Idan kin manta bara na tuna miki, Juwairiyya matata ce, idan yanzu na shiga inda take ta rayamin kasancewa da ita zan samar da wannan farin cikin nai wanka na fito koda anjima hakan zai ƙara bijiromin idan ma wannan kikema zagaye-zagaye zargin nayi. K da ita duk abu ɗaya kuke a wajena, ina fatan kuma tsaida adalci akan kowaccenku. Duk wacce take da wani tuggu nason rinjayata gareta ita kaɗai na cutar da ƴar uwarta ALLAH ya hanata wannan damar ko wacece a cikinku. Abu na ƙarshe dazan gaya miki shine daga yau ki sani *_Ina son Juwairiyya!_* bawai cushenta akai minba kamar yanda na fahimci ke tunaninki ke kaiki. Yanda na aureki domin so bisa jagorancin iyaye haka itama na aureta, kuma koda ace iyayenmu basu ɗaura mana aure ba ni da kaina *_Zan nema aurenta_*, dan hakan burina ne, hatta wannan gidan da sunanta aka ginashi itama, kema shaidace tunda sashe biyu kika tarar. Kinga sai ki sakama zuciyarki salama, ki nisanta kanki da zama mai fuska biyu a gareni, dan bazan daina kasancewa da ita ba domin farin cikin. Sannan ita bata taɓa nuna damuwa da kasancewata a wajenki ba abinda ke gabanta takeyi, mtsoww stupid har kina faɗamin wai na dinga adalci”. Ya juya ya fice a fusace.

      Da gaske Fadwa tayi mutuwar zaune tun fara maida mata raddi da yayi, ga wata irin zufa dake jiƙa duk sassan jikinta sharkaf. Buga ƙofar da yay da ƙarfi ya sata zabura ta dawo hayyacinta, rawa lips ɗinta suka fara alamar magana take sonyi amma taƙi fita, sai kuma ta mike zumbur tana rarumar wayarta ta kunna fitila duk da kuwa ɗakin akwai hasken wutar nefa. Tabbas maganin data zuba ɗin gashi nan, sannan ya taka kuma ai kamar yanda Aunty Safarah da Mama suka tabbatar mata idan ya taka babu wani magana da zatai ya musa mata. Hakama zoben da suka bata na mallaka har biyu gashi a hanunta, sun kuma tabbatar mata mata da yawa suna rububin saya kuma yana aiki akan mazajensu. Mi (hakan ke nufi?) ta tambayi zuciyarta ƙirjinta na bugawa da sauri-sauri idonta ƙyam akan zoben mallakar dake a yatsanta tana murzashi da tunanin ko batayi dai-dai bane ɗazun daya sshigo. 

       *_(Mata ku daina ruɗar da kanku da wannan zoben da kuke saya, wai miyasa munada ilimi amma basirarmu ke toshewa akan kayan matane?. Kwanaki nai wata baƙuwa, kamar wasa muna hira sai aka kai har kan illar shaye-shayen maganin mata da wasu mata suka maida tamkar ibada a rayuwarsu har ana ribatarsu da su ana basu kayan tsubbu a zuwan maganin mata kamar dai fadwa. Sai kawai take bani labarin ai wani zobe ma ya shigo wai na mallaka. Ana saidawa dubu uku har sama da haka. Ban ɗauka abin serious ba sai a wajen wani taron suna. Hhh abin dariya, mu anan yankin ma tsabar dukan hancin da akema mata zoben ana saida musu ne a 5k 6k 7k har 10k idan aka tabbatar ke hamshaƙiya ce, kunsan kuma su wannan manyan matan sunfi son ace abu nada kuɗi mai yawa sunfi bashi daraja. Humm abin mamaki wai sai ga mata na mugun rububin zobe kamar ƙiftawar ido ya ƙare, har wasu na shiga damuwa basu samu ba. 🤦🏻haba mata mi muke son mu zama ne wai dan ALLAH? Shin wai mallakar nan mizata amfana miki? Nasan kowace mace tana so mijinta ya sota ya kuma ƙaunaceta, amma sai nakega akwai hanyoyi masu ƙyau da zakibi shi namiji ya soki domin ALLAH. Sannan ku fahimta da ƙyau wlhy namijin bahaushe komin son da yake miki da wahala ya lalace a jikinki koda yaushe kamar wasu a cikin ƙabilun nan. Ɗabi'ar da suke nuna mana kuma ba itace rashin so ba, dan kinga mace na nanaye a media da miji bashike nufin ita ƴar gata bace, dan kinji mijin novel ya lalace jikin mace karki ɗauka dole naki mijin sai ya kasance a haka ki yarda yana sonki. Wani abun ana sakashine kawai dan nishaɗi. Mu kiyayi zantuka ko labarai ga ƙawayenmu su gidajensu kaza kaza ta yanda hankalinki zai tashi kiga gazawar mijinki, wlhy koyaya mijinki yake sunansa jan gwarzo, idan kika nutsu yanada tasa baiwa da kalar soyayya da farin cikin da yake baki kema ba sai lallai irin wancan da kike hange ba. Idan kina cikin wani ƙunci a gidan aurenki ki ɗauka harabawace ke kuma bautar ALLAH kikeyi sakamakonki nagaresa, idan kikai haƙuri sai ya sakaki a aljanna. Amma mu kiyayi zurmawa akan shaye-shayen magungunan matan nan da bamusan kansu ba suzo suna mana illa a banza a wofi, su kansu wasu a cikin masu saidawar basu da ilimi a kansu bamu kawai sukeyi. Ki samu mai inganci wanda kika yarda da hadinsa da mai saidashi ki saya kisha gwargwado bata yanda zaki saka kanki a dana saniba kizo kina jama kanki illa da kwasar imfection a banza a wofi. Kuyi hakuri masu magani nasan akwai nagari acikinku dan kowane sana'a akwai na kwarai akwai na banza. Masu na banzar suke bata na kwarai da disashesu akasa ganinsu a idanun al'umma. amma dan ALLAH mata a kiyaye, zoben nan da sayensa gara ki samu kazarki kici tai miki amfani babu abinda ke tattare da son zuciya dake zama ɗorarre).


       Sashensa ya nufa rai ɓace, ya zube a falo yana cigaba da jan tsaki, shi ya rasa mike damun waɗannan yaran, musamman ma Fadwa, dan Anaam ita kai tsaye take abunta bata iya ɓoye-ɓoye ba. Kuma tunda ya santa haka take, tunda ko'a shigowarta gidan nan ya hukuntata sau da yawa akan yima Fadwa abu amma hakan bai hana ta ƙara gobe a zahiri babu wani ƙumshe-ƙumshe. Itako Fadwa yau ta nuna ita mai kirki ce, musamman idan da Anaam a waje, anjima ya sameta tana baƙin rai da ƙananun magana akan Anaam kaza-kaza. Ya rasa mike damun tunaninta, shi kuma ya tsani wannan banzan halin dan yana kamanceceniya dana munafukai. Ƙwafa yay mai ƙarfi, a ransa yana ayyana zaima tufƙar hanci....


       ★★★


  “Blood zan baki wata shawar dan ALLAH ki fahimceni”. Aysha ta faɗa tana direma Anaam plate na abinci data dafa musu a gabanta. 

     Wayar da take latsawa ta ajiye, da maida hankali ga Ayshan. “Tofa shawarar mi kuma blood?”.

  “Ta zamanki a wannan gidan. Na fahimci gaba ɗaya a haguggunce kike, sai dai na miki uziri domin rayuwace da baki saba da ita ba kuma baki santa ba. Kin tashi a rayuwar da kowa yana komai akaran kansa kuma kai tsaye batare da wani munafunci ba ko boye-boye, dolene a wannan gaɓar kisha wahala sai dai nai alƙawarin bazan bari hakan ta faru ba. Blood daga yanzu dan ALLAH komi Fadwa zatai miki ki daina nuna ƙinsa a gaban Yaya koda ace bai miki ɗin ba, domin na fahimci da wannan makamin take amfani wajen kai miki duka a tsakaninki da Yaya. Ki duba ranar yanda ya nuna jin haushinsa akan abinda kikayi, wlhy ina ganinta sanda take murmushi, hakama yau da muka dawo, dan munafunci hardafa rakomu nan”

    Murmushi tayi da ɗaukar spoon ta fara cin abincinta dan tafi son cinta da zafi. “Amma blood ban katseki ba, miye amfanin kwaikwayon halin wani bayan hanyace mara ƙyau, ɓoye ƙinta kamar yanda take ƙina bashine zaisa na birgeta ba ko shi na birgesa. Tsakanina da ALLAH idan nace zan zauna shanye haukar wannan matar zan kamu da ciwon hawan jini, nafi yarda da kamun na maka a wuce wajen dan nasan itama munafunci kesata yimin wani abun”.

      Sallamarsa ta tilasta Aysha haɗiye abinda tai yunƙurin faɗa, dole ta juya tana amsa masa. Anaam kam kallo ɗaya tai masa ta ɗauke. Shiko kasa ɗauke nasa idon yay a kanta, ko sannun da Aysha tai masa hannu kawai ya iya ɗaga mata. Kujerar dake facing Anaam ya zauna. Hakan yasa Aysha miƙewa a ɗan ɗarare tace, “Yaya a kawo maka abincin?”.

      Abincin ya kalla na wasu sakanni, sai kuma ya miƙe daga inda yake ya koma kujerar da Anaam ke zaune kasancewar 2sitter ce. “Bara naci kaɗan anan kawai”.

    Cikin jin daɗi Aysha tai murmushi, Anaam kuwa ɗagowa tai idanu a ware tana kallonsa, ya ɗaga mata gira da kashe mata ido ɗaya yanda Aysha bazata lura ba, da sauri ta kalli sashen da Ayshar take, sai dai ita hankalinta ma ba kansu yake ba. 

         Spoon ɗin hanunta ya zare da sakin guntun murmushi, yana motsa lips ɗinsa a hankali alamar akwai abinda ya faɗa. Batai tunanin da gaske yake ba, sai ganin ya ɗiba yakai bakinsa tayi. 

    “Wai da gaske kakeyi?”.

Ta faɗa cikin magana ƙasa-ƙasa dan kar Aysha taji tana waro masa idanu da ƙyau.

          Shima ƙasa yay da muryar tasa cikin kwaikwayonta da kashe mata ido yace, “Bayan wannan zahirin kina buƙatar ganin wani ne?”.

    Idanun ta ƙara warowa sosai “Are you ok?”.

  “I'm not...”.

Ya bata amsa a taƙaice yana danne dariyarsa dan da gaske tayi bala'in diriricewa. Tsabar son ƙureta abincin ya ɗibo yakai bakinta. Da sauri takai hannu zata kare. “Idan kikaƙi amsa ALLAH cak zan maidoki jikina sannan na baki wanda na tauna a bakina kuma a gabanta harda tsotse lipstick ɗina”.

        Yanda ta saki baki da hanci tana kallonsa ya sashi dungure mata kai yana murmushi, tana buɗe baki da nufin yin magana ya juye mata shi. Dole tai saurin rufe lips ɗinta dakai hannu ta kare bakinta. Dai-dai nan Aysha da ta wuce kitchen batare da sun sani ba ta dire babban tray data shirya abinci kamar yanda akema kowanne magidanci a saman centre table ɗin gabansu. Lokaci guda suka sauke ajiyar zuciya, Anaam ta kalleta shiko ya fiske fuskarsa na komawa normal kamar ba shine ke murmushin ba.

       Aysha na ƙoƙarin barin falon Anaam tai saurin faɗin, “Blood ina kuma zaki? Kizo muci abincin mu”. Da sauri Aysha ta shige bedroom ɗin baƙi kamar ma bata jita ba. 

   “Yaya ka gani fa ka koreta?”.

“So take ki samu ladan da mata ke samu kema, tunda garden ɗina kin haɗa baki da doctor ɗin can kar naje barruwa.”

    Maganarsa ta farko kawai ta fahimta. Dan haka cike da basarwa ta bashi amsa. “Matarka ai tana dafa maka ta samu ladan, kaga ya wadatar da kai ai”.

        Shima fahimtar hakan ya sashi juya harshe zuwa yaren Maley.

  “Ke minene naki sunan?”.

     “Kanwarka kaima da kowa an sani”.

       “Really?”.

   “Yap!”.

“Idan suka ganki da tsarabar furen garden sai su cireni a jerin Yayun naki ai ok”.

      “Kai ka san wani garden Yaya”.

“Kema kin sanshi sai dai ƙari. Ni fa janbakin nan ya tsolemun ido a bani na shanye kayana k......”

    Abincin data ɗebo ta juye masa a baki kamar yanda yay mata shima ɗazun, dole ya haɗiye sauran magan

ar itako ta shiga ƙyalƙyala dariya dan lauma babba ne........✍




Post a Comment

0 Comments