TOP HAUSA NOVELS atOptions = { 'key' : '20e08520dad54dbf6d9e963271

Sanyi da zafi page 76

 EPISODE 76

Anatse take bude idanunta tayi shiru tana kallon sama dudda AC dake aiki adakin but zufa goshinta yake, tundaga ranan da aka saceta har zuwa abinda yafaru jiya akan carpet adakin nan suke dawo mata wani irin kunya taji yakamata tana kara tuna mahaifinta da yanda yayi kuka da borin datama Ammi da muryan su Mom da Haleema da wasu dataji gently ta taso tazauna takai hannunta tana taba kanta tayi shiru sai kawai takai bayan hannunta ta göge fuskanta kallon dakin tashigayi hango hijabinta akan kujera yasa ta tashi takai hannu ta dauka ta saka tabude kofa, Ahankali tana addu'a Allah yasa bayanan don batason abinda zaisa su hadu ganin baby kowa yasa tafito tana kallon ko'ina dakin yahadu na bala'i saukowa tashigayi harta karasa saukowa falon saikuma ta kalli kitchen da kofan yake abude dasauri ta dauke kanta tunawa da abinda tayi, bude kofa tayi tafito tana kallon hadaden compound din tayi hanyar kofan datagani tana budewa taga fadawa yanda suka zube suna gaidata saida ta firgita da sauri tawuce su tafice tana kalle kalle ko za'a kasheta batasan wani hanya zatabi taje side din Ammi ba amman haka tacigaba da tafiya ahankali babu wani abu fake mata ciwo kawai bakinta ba dadi ne kadai hango wani flat datay exactly irin na Ammi yasa tai wajen tabude kofa ta shiga komi iri daya da side na Ammi bude kofan flat din tayi tana budewa tayi ido biyu da Muji daya watsa magani abaki yahadiya da sauri ya kalleta saikuma yataso yazo wajen dagudu juyawa

tayi dasauri karaf taji yakama hannunta cikeda so yace "Rashida"

Chak ta tsaya taki juyowa jikinta kawai yayi sanyi tadawo daidai ahankali yace "Ya jikin?" Kin magana tayi, ahankali yace "dan Allah ki shigo nayi magana dake, dan Allah dan girman Allah nace kinji Rashida" kasa motsi tayi dan janta yayi hakan yasa tabishi Suka shiga cikin falon still taki kallonshi to her biggest suprise saitaga ya sauke guiwowinshi kasa dasauri ta koma baya tana kallonshi yanda Babba dashi yayi kneeling tanajin wani iri hade hannayenshi yayi yana kallonta yace "Rashida | take full responsibility for my actions, nasan kin tsaneni kin tsaneni Rashida dan girman Allah ki gafarceni find a place kiyafeni ko zan sami kwanciyan hankali I'm sorry y'ata, Rashida dan darajan Allah kiyafemin kinji" yayi maganan hawaye na gangarowa daga idanunshi dasauri tadauke kanta idanunta na taruwa da hawaye she don't know but something is her ya chanza she remembers maganganun Haleema and she wanna be a better person mahaifinta yayi kuskure but harda influence na wasu mugaye she knows she's pregnant cus ta tuna maganganun Dr a asibitin da aka kaita, batason tayi feeding baby nata this hatred datake dauke dashi azuciyanta cus Ammi did not feed her hatred dudda an cuceta but ta taso da ita tana gwada mata kyawawan halayyan mahaifinta ne, she wants to change for good forgive and forget taso mijinta and just live happy ta cikama Mama burinta, saukan hawayenshi taji akan kafarta hakan yasa ta kalleshi kuka yake yabata tausayi ahankali tace "Abee" dawani irin sauri Muji yakalleta wasu sababbin hawaye na zubomai daga idanu ya kalleta ahankali ta zauna agabanshi tace

"kasan l've always wanted to call mahaifina da Abee kanason sunan"? Fashewa da kuka sosai Muji yayi saikawai ya rubgumeta tsam tsan ajikinshi tai lamo tai shiru tana tuna Mama she knows how much Mama loves mahaifinta dudda yamata laifi but Mama bata tsaneshiba ahankali Rashida ta dagoshi takai hannunta tana sharemai fuska tace "maganin me kakesha?" Yana kallonta kaman zai hadiyeta yace "na B.P ne" gyadamai kai tayi tace "meke maka ciwo?" Dasauri yace "babu komi wih yanzu

I'm the most happiest father aduniya" dan murmushi tamai sai kawai ya manna ma forehead nata kiss ahankali tace "inaso naje wajen Ammi Abee nayi wanka yunwa nakeji sosai" da sauri yatashi yana dagata yace "muje muje kici" har side na Ammi sukaje nan nan yake da ita Ammi na zaune suka shigo a kunyace Rashida ta rufe fuskanta da hijabi Ammi ta kalli Muji ganin yanda yake murmushi yasa Ammi tace "Baffan su kaine" tahowa ajen Ammi Rashida tayi har lokacin fuskanta a boye sai kawai ta rungume Ammi tace "Ammi sorry na miki kiriniya" Dasauri Ammi ta kalleta saikuma ta kalli Muji dake murmushi sosai Ammi tace "Alhamdulillah Alhamdulilah Allah mun gode maka, My Baby" kankameta Rashida tayi taki nuna fuskanta dasauri Muji yayi dinning yace "taho kici abinci" dasauri Ammi tace "maza tashi kije kici kidena zama da yunwa tunda bake kadai bane" batai musu ba ta tashi tawuce Babanta ke serving nata Ammi sai kallonsu take tanajin dadi sosai taci pepper soup aduka wanda ke kullan kasan tarage sannan ta tashi tawuce sama shikuma Muji yadawo falon yanaba Ammi labari cikeda farinciki.

Bayi tafada saida tafarayin brush sannan tai wanka kawai she's happy hakanan she's feeling very happy, agaban madubi ta tsaya ta cire bandage na kanta taduba bayin taga sunada first aid box tayi dressing kan nata da ya warke sosai sannan ta tattare kan tayi parking tafara wanka tana tuna yanda Ammi ta mammata wanka da ruwan zafi sosai tayi wankan sannan tadauro alwala taja towel tazo bude kofan tayi ta hada ido da Riyad dake gaban kofan yayi folding hannu yana jiran fitowanta dawani irin sauri tajuya zata koma yakama hannunta kulle fuskanta tayi yana jawota zuwa jikinshi tace

"wat are you doing in my room?" Ahankali yana sata ajikinshi batare daya damu da ruwan dake jikinta ba yace "I come to talk to my small baby not you" yakai hannunshi yadaura akan cikinta, kabar da hannunshi tayi a kunyace zata fita daga jikinshi da sauri yace "mehaka? Kunya kikeji small girl like you tasan namiji har yamata ciki" dukawa tayi ta manna kanta akan guiwanta tace "nika fita kona kira Ammi da Abee wih kaga salloli zan rama" dukawa yayi yana lekata yace "okay kiyi ki gama we are leaving this place gidanmu zamu yau" makemai kafada tayi kawo kanshi yayi ya manna mata kiss a cheek ahankali yace "I'm glad you're okay Wife welcome back" yana maganan yatashi yayi kofa dasauri tadago kanta tabishi da kallo wani irin sonshi takeji aranta bana wasaba.

Saukowa kasa yayi yadan kalli Ammi yace "Ammi uhmmm zamuje gidanmu anjima" wani mugun kallo Ammi tamai tace "to baka isaba sai anyi bikinku" Dasauri Riyad ya kalli Baffan shi kaman zaiyi kuka hakan yasa Muji yace "haba amai afuwa abasa matara duk randa sukaga dama sai ayi bikin, kai jeka zakuje gida abinku" Wajen Muji Riyad yaje yabashi high five sukai dariya Ammi ta kadakai yayi wajen kofa wayanshi yahau ringing tsayawa yayi yaciro wayan ganin Papa yasa yayi shiru saikuma kaman zai maida wayan aljihu sai kawai ya dauka yakai kunne yayi shiru kusan 5min har Ammi tadaga kai tana kallonshi kafin ahankali yazare wayan daga kunnenshi saikuma yadawo falon Ammi dake kallonshi tace "ya akayi?" Anatse yace "Ammi it's Mom Dad, yakira wai dan Allah dukanmu muzo Grace hospital dan girman Allah he wants to see all of us including my wife I don't know why" Shiru dukansu sukayi Muji yace "muje Ammin su?" Dan ijiyan zuciya ta sauke tacd "okay anjima kafin kuje gida saimu biya"

Gyadamusu kai yayi yafice Ammi da Muji kuma sukahau hira gwanin ban sha'awa they don't use to be close before but yara sun maidsu so close.

Wuraren 8:20 Ammi tashigo dakin ta kalli Rashida data shirya fikin wata atampa tace "muje" gyadama Ammi kai tayi ta tashi ta taho Ammi sai kallonta take cus tayi kyau fitowa sukayi tundaga saman

Riyad ke kallonta yanda ta yafa Babban gyale tai kyau sai wani glowing take kin kallon Riyad tayi Munir yace "cousin dinmu" murgudamai baki tayi dasauri yace "Ammi kin ganta ko ba mun shirya ba"

Dariya Ammi tayi tace "kacire ni daga fadan nan naku Munir kutashi muje" tashi sukayi taki kallon Riyad Munir sai hira yake mata tabiyemai sukai gaba Muji na kallonsu tareda Ammi da shi kansa Riyad din mota biyu sukayi da gangan ta shiga motan Babanta da Ammi ke ciki shi da Munir suka shiga daya sai kumbure kumbure suke har zuwa hospital din data rasa mesukazo yi dan tasan ba shine na kanta ba.

Suna shiga sukaga Papa tsaye sai zagaye yake yana ganin su yataho wajensu da sauri saikuma duk tsaya suna kallonshi, ahankali yace "thank you for coming, dan Allah come with me" yayi gaba suka bishi abaya har zuwa gaban dakin da Mom keciki dasuke Jin ihunta from there gently yabude kofan yace "ku shigo" Riyad na sako kanshi yajuyo da bala'in sauri tsigan jikinshi na tashi itama Ammi dasauri tajuyo hakama Muji itakuma Rashida tsaf ta shige ciki duk suka bita da kallo ta taka har zuwa inda Mom take tana kallonta tana ihu da muryanta <

dasauri tajuyo hakama Muji itakuma Rashida tsaf ta shige ciki duk suka bita da kallo ta taka har zuwa inda Mom take tana kallonta tana ihu da muryanta daya dishashe tana kokarin fixge hannunta tayi susa tace "wayyoo Allah na kuyafemini dama akwai azaba haka aduniya? Dama akwai cuta mai bakin azaba haka aduniya? Rashida kayakuri kiyafemin nasa an sama mahaifiyarki Hiv naso kasheki kema Allah baiyiba Rashida dan darajan Allah kiyafemin ko susan nan ne nasamu Allah ya dauke mini" kujera Rashida taja tazauna tana kallon Mom in agony da tsantsan ciwo da kawai ganinta ahaka saitaji satisfaction da bata tabaji ba, murmushi tayi Allah ya sakama Mama, murmushi take sosai feeling so happy and satisfy.




Post a Comment

0 Comments