TOP HAUSA NOVELS atOptions = { 'key' : '20e08520dad54dbf6d9e963271

Sanyi da zafi page 74

 EPISODE 74

Cikin hausansa da bata fita sosai yace "¡iee to!

Kanta ya bugu sosai, ta zubar da jini sosai dudda ina bata ruwan ganye dake kara jinin amman dudda haka bai ishetaba jinin sosai batada karfi zatana dinga yawan sumewa, buguwan da akama kanta yasa ta mance komi amman bazata dauki lokaci ne zata warke, komi zai dawo mata, ruwan data shiga ciki yasa sanyi ya taba abin cikinta amman tagama magungunan danake bata za'a dace, shima kan za'a dace da izinin Allah" kowa shiru yayi suna kallonta barin Riyad daya tsareta da idanu yana kallon yanda tadauki naman takai bakinta ta tsotsa tafito dashi kuma ta ijiye sai chan tasa hannu ta dauki wara tana kallo sai ta ijiye saita dangwalo nono takai bakinta tana tsotsan yatsanta, ahankali Riyad yafara tafiya kowa binshi yake da kallo har zuwa inda take gently ya tsugunna gaban tabarman yana wani irin kallonta, wasa take da abinci but jin mutum agabanta da kamshin turare mai dadi daya daki hancinta yasa tafara kallon tundaga kafanshi yana sanye da bakin crocs da dark brown yadi mai bala'in kyau sannan tadago kanta ta kalleshi hada ido sukayi ta tsareshi da idanu kaman yanda ya tsareta shima da idanu, wani irin lankwasa kai tayi tana kallon fuskanshi kaman taga abinda bata taba ganiba tanabin tundaga idanunshi har zuwa dogon hancinshi da kallo down to his lips, wani irin kyau yamata wanda ya banbanta da sauran mutanen yan garin har kayan jikinshi ma, saikuma tadauki kwaryan naman dasauri tasa hannu taciro nama daya ta mikamai, kallon naman yayi sai kawai hawaye ya cika idanunshi, ahankali yasa hannu ya amsa murmushi tamai daya bayyana duka hakoranta jin sahun tafiya yasa dasauri tajuyo takalli sauran mutanen dasuka taho, Muji ta hango yana kallonta shima rikeda soda a hannunshi na Gwaggo dawani irin sauri tashiga kokarin tashi tasa hannunta duka biyun tana kama kanta alamun yana mata zafi tana yatsine fuska dasauri Riyad yatashi wucewa tayi dasauri tana tafiya ahankali kowa na kallonta har gaban Muji hannunta tasa da sauri ta karbi soda a hannunshi tashiga kokarin budewa takasa saikuma tasake kallonshi tabashi, karba yayi ahankali muryanshi har rawa yake yace "nabude miki? Okay zan bude miki" dasauri yabude mata karba tayi takafa abakinta tass ta shanye tana lashe baki tasake saka empty bottle din abaki tana girgijewa saikuma ta kalli Muji dayakai bayan hannu yana goge idanunshi ahankali tace "bani" da sauri takai hannunta takama nashi tana budewa tana neman drink din ashagwabe tace "banimmili" wih duk yanda Muji yaso yadaure saiya kasa yafashe da kuka, he can't believe for the first time yau yanajin dumin hannun yarsa da tun tana ciki ya kada uwarta, ganin yana kuka yasa ta tsaya tai shiru tana kallonshi saikuma tafashe da kuka takai nata hannun tana gogemai hawayenshi Buba yataba bayanshi alamun yayi shiru, daurewa yayi yadena yace "nadena kuka to kinason soda?" Yanuna goran hannunta gyadamai kai tayi da sauri tana dakatar da kukan yace "to mukaje mota zan baki" ahankali tace "mota"? Gyadamata kai yayi yace "eh mota" juyawa tayi tana fadin mota mota mota mota mota tawuce wajen tabarman taxauna ahankali, tana kallon Riyad data sakemai murmushi tace "mota, mota, mota, mota" saikumai tamai murmushi again, kafin tazo dasauri takama hannunshi tarike tana kallon agogon dake writs dinshi saikuma takalli fuskanshi tace "mota?" Hannunshi Riyad yakai ahankali for the first time yadaura akan fuskanta dasauri takalleshi ta tsare idanunshi da kallo dataga suna tara hawaye, tace "sunana mota".




Post a Comment

0 Comments