TOP HAUSA NOVELS atOptions = { 'key' : '20e08520dad54dbf6d9e963271

Cikekken Bayani Kan Kisan Kae Da Akayi a Misau


 Garin Misau...


Kisan wannan yaro babbar barazana ne a cikin garin misau. Babu shakka abinda makashin yaron ke fada a gaban jami'ai ƙaryane tuƙuru. Wannan ya ƙara bayyana wa jama'a cewa tabbas akwai dalilin da yasa wannan makashin ya aikata wannan mumunan kisa. Sannan bisa ga alamu tuhumar da ake yi wannan makashi akwai sassauci marar ma'ana a ciki, wanda ya kai ace masu faɗa a ji sunyi gaggawar jan hankalin jami'an akan wannan babban al'amari.


Amma Har a yanzu bamuji wani mutum mai faɗa a ji da ya tsaya a kan wannan al'amari dan a tsayar da adalci akan wannan al'amari ba, duba da yanda binciken ke tafiya, akwai alamun an shirya masa zantuttuka da zai bayyana a jama'a sai dai kuma yanzu ba jahilai ne ke cikin garin misau ba. 


A garin misau akwai mutane, ƙungiyoyi da malamai da in sun yi magana koda a hikimance ne zai yi tasiri, duk da cewa a wannan gaɓa babu zancen boye ra'ayi, amma har a yanzu shiru kake ji. In kaji wani yayi magana to irin mu ne wanda Maganar mu ko ƙofar gari bata zuwa. 


Amma ku sani muddin akai sakaci da wannan al'amari to an daure wa ta'addanci gindi kuma kada wani shege ko wata shegiyar ƙungiya ta sake ce mana wai tana aiki don kishin garin misau. 


Daga ƙarshe kuma kowa ya sani wallahi hakki sai ya bi duk wanda yake da daman da zai aiwatar da Alkhairi koda da baki ne kuma yayi shiru. Game da yaro kuma Allah zaiyi hukunci a kai komin daɗewa. Allah ya gafarta mana ameen.

Post a Comment

0 Comments