TOP HAUSA NOVELS atOptions = { 'key' : '20e08520dad54dbf6d9e963271

Magana ta qarshe da yaron da aka dabawa wuqa yayi Akan kin jinin musulunci

 "Umma, lafiyata ƙalau", su ne kalmomin ƙarshe na yaro Musulmi ɗan shekara shida da aka caccaka wa wuƙa, har sai da ya riga mu gidan gaskiya, a wani laifin da ake zargin na ƙin jinin Musulunci ne a ƙarshen mako.

Kawun yaron ne ya bayyana haka, lokacin da ɗaruruwan mutane suka taru a wurin jana'izarsa.

Ranar Litinin ne masallacin da ke ake kira Mosque Foundation a Bridgeview na wajen birnin Chicago ya tumbatsa da mutane, inda har ma wasu suka gudanar da sallah a wajen haraba.

'Yan sanda sun ce an far wa Wadea al-Fayoume ne saboda shi Musulmi ne.

An gudanar da jana'izarsa, yayin da mai gidan da suke zaman haya ya bayyana a gaban quliya inda aka tuhume shi da aikata kisan kai ga ƙaramin yaro. Mutumin da ake zargi ɗan shekara 72, an yi za


rgin cewa ya fusata ne saboda yaƙin Israel da Hamas.

Masu makoki sun fito daga sassa da dama a faɗin yankin, wasu ma daga can nesa, don bayyana alhini da takaicinsu a kan wannan kisa.

Mahaifiyar Wadea, Hanaan Shahin, mai shekara 32 ta yi matuƙar jin raunuka a harin, kuma ba ta samu halartar jana'izar ɗanta ba, daidai lokacin da take ci gaba da samun sauƙi a asibiti. Na kaɗu sosai, amma ban yi mamaki ba," cewar Sadia Nawab, wata mahaifiyar 'ya'ya uku da ke zaune a kusa da masallacin.

"Muna cike da fargaba game da 'ya'yanmu, da kuma ƙarin damuwa a kan yaran da ba su da wani ƙarfi daga ko'ina suke cikin faɗin duniya, amma a yanzu suke Falasɗinu, da kuma Gaza."

Post a Comment

0 Comments