TOP HAUSA NOVELS atOptions = { 'key' : '20e08520dad54dbf6d9e963271

Kotu Ta Sanya Ranar Yanke Hukunci Kan Zaben Gwamnan Jihar Adamawa

   Kotun sauraron kararrakin zaben gwamnan jihar Adamawa ta sanya ranar yanke hukunci kan nasarar gwamna Ahmadu Umaru Fintiri,  'Yar takarar gwamna a inuwar APC, Aishatu Binani, ce ta shigar da ƙarar tana ƙalubalantar sakamakon da INEC ta bayyana. 

 Idan baku manta ba zaben gwamnan Adamawa ya ja hankali sosai bayan REC ya bai wa Sanata Aisha nasara. 


Kotun ta ce a ranar 28 ga watan Oktoba, zata yanke hukunci kan ƙarar da Sanata Aishatu Binani, ta kalubalanci nasarar gwamna Ahmadu Fintiri a zaben da ya gabata.

Sanata Binani, ƴar takarar gwamna ƙarƙashin inuwar jam'iyyar APC ta shigar da ƙara, inda ta nuna ba ta gamsu da nasarar Gwamna Fintiri na jam'iyyar PDP ba.

Post a Comment

0 Comments