TOP HAUSA NOVELS atOptions = { 'key' : '20e08520dad54dbf6d9e963271

LABARI DAGA KADUNA

 Gwamnatin Kaduna ta rufe wata makaranta a Zariya bisa zargin kashe ɗalibi



Gwamnatin jihar Kaduna da ke arewacin Najeriya ta rufe makarantar 'Al-Azhar Academy Zaria' kan zargin mutuwar wani ɗalibi mai suna Marwan Nuhu Sambo, bayan yi masa hukunci sakamakon fashin zuwa makaranta da ya yi.


Cikin wata sanarwa da shugaban sashen lura da makarantu na jihar Dakta Usman Abubakar Zaria, ya fitar, a madadin kwamishinan ilimi na jihar, ya ce an ɗauki matakin ne har zuwa lokacin da za a kammala binciken ainihin abin da ya faru.


Sanarwar ta ce ma'aikatar ilimin jihar a madadin gwamnatin jihar Kaduna ta kafa wani kwamiti na musamman da zai bi diddigi domin gano haƙiƙanin abin da ya faru.


Tuni dai kwamitin ya ziyarci makarantar, da kuma gidan mahaifin ɗalibin domin yi danginsa ta'aziyya tare da ziyartar gidajen wasu abokan ɗalibin, kamar yadda sanarwar ta bayyana.


Haka kuma tawagar ta ziyarci asibitin da ya tabbatar da mutuwar ɗalibin a hukumance, da ofishin 'yan sandan Zariya, inda ake tsare da shugaban makarantar da mataimakinsa, da kuma maƙabartar da aka binne shi.


Sanarwar ta kuma yi kira ga al'umma da su kwantar da hankulansu, tare da bin doka da oda, yayin da ta ce ma'aikatar ilimin jihar na ci gaba da gudanar da bincike kan lamarin, domin tabbatar da gask iya da adalci.

Post a Comment

0 Comments