TOP HAUSA NOVELS atOptions = { 'key' : '20e08520dad54dbf6d9e963271

Liverpool da Chelsea za su yi takarar ɗaukar Victor Osimhen daga Napoli

 

Victor Osimhen

ASALIN HOTON,GETTY IMAGES

Liverpool da Chelsea za su yi takara da juna wajen neman ɗaukar ɗan wasan Najeriya, ictor Osimhen, idan tattaunawar tsawaita kwangilar ɗan wasan da Napoli ba ta cimma nasara ba.(Mirror)

Akwai yiyuwar ɗan wasan gaban Roma, Tammy Abraham, mai shekara 26, zai koma taka leda a gasar Premier idan kociyansa, Jose Mourinho ya bar ƙungiyar ta ƙasar Italia. Tuni dai Chelsea da Aston Villa da kuma Brentford suka fara bibiyar ɗan wasan Ingilan. (Teamtalk)

Chelsea da Brentford na bibiyar ɗan wasan gaban Charlton da Ingila, Miles Leaburn, ɗan shekara 19, wanda ya ci kwallo shida cikin wasa 10 da ya buga wa ƙungiyar sa.(Daily Mail)

West Ham ta shirya biyan Euro miliyan 40 don ɗaukar ɗan wasan Juventus da da kuma Italia, Manuel Locatelli, mai shekara 25. (Tutto Juve)

Feyenoord za ta sanya farashin Euro miliyan 100 kan ɗan wasan gaban Mexico mai shekara 22, Santiago Gimenez, wanda ake alaƙantawa da ƙungiyoyi irin su Real Madrid da Tottenham da Arsenal da kuma Chelsea. (90min)

Brentford na duba yiyuwar ɗaukar ɗan wasan Ingila da Celtics , Matt O'Riley a cikin watan Janairu. (Teamtalk)

Post a Comment

0 Comments