TOP HAUSA NOVELS atOptions = { 'key' : '20e08520dad54dbf6d9e963271

KOTUN KOLI DAKE ABUJA TA GANO AKWAI RUDANI A TAKARDUN DA SHUGABA AHMAD TINUBU YA GABATAR WA KOTUN

 Kotun koli ta saurari ƙarar da Atiku Abubakar ya shigar, dangane da sahihancin takardar shaidar Bola Tinubu da ya samu daga jami’ar jihar Chicago. 



Atiku na jam'iyyar PDP na zargin cewa shugaban ƙasar ya gabatar da takardun jabu na jami'ar jihar Chicago Da yake magana kan ƙarar a ranar Litinin, mai shari’a Okoro ya koka kan wasiƙun da CSU ta bayar kan takardar shaidar Tinubu

 kotun-koli-ta-hango-kuskure-a-wasikun-jamiar-csu-kan-takardun-tinubu

FCT, Abuja - Kotun ƙoli a ranar Litinin, 23 ga watan Oktoba, ta bayyana cewa akwai wasiƙu masu karo da juna daga jami'ar jihar Chicago (CSU) kan takardar shaidar karatun Shugaba Bola Ahmed Tinubu. 



Mai shari’a John Okoro, jagoran kotun mai alƙalai mutum bakwai da ke sauraron buƙatar da Atiku Abubakar, ɗan takarar jam'iyyar PDP, ya shigar kan nasarar da Tinubu ya samu, shi ne ya bayyana hakan a ranar Litinin, 23 ga watan oktoba. 

Post a Comment

0 Comments