TOP HAUSA NOVELS atOptions = { 'key' : '20e08520dad54dbf6d9e963271

WAYASAN GOBE 1-4

 Wa yasan gobe?

▶1⃣ safiya Abdullahi musa huguma 🌺🌺🌺🌺🌺🌺  Zaune take dirshan bisa carfet din dake mamaye da qaton dakin nata,ta tanqwashe qafafunta yayin data tallafe kumatunta da dukka tafin hannunta,lokaciguda kuma ta zubawa food flask din abincin dake gabanta ido,a zahiri idan ka dubeta zakayi tsammanin flask din take kallo sai dai sam ba haka bane zuciyarta da ruhinta sun lula wata duniya ne ta daban,da yunwa ta shigo gidan saidai sam ta kasa sa koda loma guda ta abincin a bakinta,cikin kwanakin tana cikin wani yanayi wanda ta kirashi da jarraba ko musifa dake tunkaro rayuwarta
Wannan ne karo na hudu a rayuwarta da idaniyarta tayi tozali dashi saidai ya zame mata masifa,tun daga ranar da ta dora idonta akansa wani baqon lamari ya ziyarci zuciyarta da gangar jikinta,zata iya kiran lamarin da zazzafan so wanda ya zamto mata tamkar harara a duhu,dalikinta na fadar haka kuwa shine wanda zuciyarta ke budurin a kansa baisan Allah yayi ruwan halittarta ba a doron duniyar subhana,tayi kukan tayi takaicin yadda zuciyarta tayi mata rashin adalci ta hanyar kamuwa da soyayyar wanda batasan koshi waye ba?,meye sunansa?,a ina yake?,taja doguwar ajiyar zuciya sannan ta jawo flask din ta bude da niyyar taba wanu abu a ciki kota tsira daga fadan umminta,ilai kuwa tana loma ta biyu taji sallamar ummin tana daga tsaye ta dubeta tace"yanzu fadila tun shigowarki kika damemu da zancan jin yinwu amma kusan aqalla awa guda banga wani abun kirki da kika ci ba?,tadan yamutsa fuska tace wlh ummi da yunwar na shigo amma kinga na kasa ci"ummi tace ,haka dai kika iya kullum kamar wata qanqanuwar yarinya sai anyi fama dake akan cin abinci ko?,yayi miki kyau ai kinsan ulcer dai ba gidanku daya ba bare kice idan ta kamaki zata miki sassauci,tayi dan murmushi tace kiyi haquri ummi insha Allahu yanzu zan kawo miki flask din empty,ummin tadan harareta tace ai jikina kunne ne,fadila tadan qumshe dariyar da keson subuce mata,har takai bakin qofa ta juyo tace"af na manta ki shirya yanzun zaki kaini gidan alh salim kwana biyu su shiru muma shiru"tadan sosa kanta dake a tsefe saidai ta tufke shi da band tace anya ummi zan gane ma gidan?,ungo wannan ja'ira cewar ummi da ta watsa mata daquwa yace"nima in banda abbanku yace in tafi dake zaki maku siyayyar kayan make up da da driver zanyi tafiyata"tayi ko saurin miqewa tace yauwa ummi dama jiya nayi masa zancen kayan,tace ato minti goma ki sameni ina falo ina jiranki,ta amsa tana qoqarin shiga toilet dinta dake manne da bedroom din ⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜
Tsaf ta shirya cikin abaya baqa mai sulbi saqar qasar dubai wadda aka mata ado da jajayen dutsina masu sheqi,ta nannade tulin gashinta tayi a cuci dashi sannan tayi rolling da wani dan kyakkyawan jan mayafi,simple make up tayi amma kasancewarta tana da wani sassanyan kyau sai ta fito gwanin sha'awa,ta daura agogo na fata ja sai plate shoe da tasanyawa qafarta mai ja ne mai baqaqen igiyoyi,wayar hannunta kawai ta dauka hade da key din motarta ta sake kallon kanta a madubi,cikin zuciyarta ta qaryata masu cewa abu mai duhu baya giwa baqi kyau,duk da cewa ita din ba baqa bace irin matan nan ne masu launin fata(chaculet colour)wasu kuma suce black beauty,fatarta batayi haske can ba kuma kai tsaye ba zaka kirata baqa ba tamkar irin black american haka yanayinta yake,fadila nada wani irin kyau mai sanyi wanda tashin farko bazaka gama tantance kyawunta sai kuna tare wato qananun kyau ne da ita,ba abu mafi daukan hankali a tare da ita irin qirar jikinta cocacola shape,idanunta manya masu dauke da gazar gazar din gashi wanda hakan ke taka muhimmiyar rawa gun tafiya da zuciya gami da ruhin mazaje da dama,goshinta kam irin qananun Gashinnan ne kwance luf wanda ko tayi dauri basu boyuwa,muryarta a sanyaye take cike da wani sirri wanda idan tayi magana take janye hankalin jama'a da dama,fadila tako ina Allah ya bata zubi da tsari wanda yasanya take burge mutane ba maza kawai ba hatta ga yan uwanta mata ma,sai dai gwanar miskilanci ce,sam magana bata dameta ba,tafi ganewa tayi karance karance maimakon zaman tadi,fadila yanzu haka daliba ce a jami'a bayero kano tana karantar mass com,duk da cewa abbanta yayi mata sha'awar karantar medicine ganin cewa mass com bana mutum ne mara son magana ba amma data nuna masa tafi sha'awar mass com din sai ya barta da zabinta kasancewarsa mutum ne mai sauqin kai,sai ya maida zabin nasa kan 'yar uwarta farida,alh abbas ahmad shine mahaifin fadila dan kasuwane mai rufin asiri,domin Allah ya bashi wadata irin wanda ko wane dan adam ke fatan samu ba abunda aka nema a gidansa a ka rasa,asalinsa bafulatanin bauchi ne,yana sana'ar sai da shaddodi da yadiddika cikin kasuwar kwari,yakan tura babban dansa wasu lokutan china ko india domin shigo da kayan su kuma zuzzuba a shagunansu dake cikin kasuwar,ya auri mahaifiyarsu haj amina a maiduguri cikakkiyar shuwa ce wadda Allah ya qaddari aurensu tun bayan da yayiwa manemanta dintinkau a zuciyarta,anan garin kano suka ci gaba da zama tunda anan kasuwancin nasa yake,haihuwar farko suka sami da namiji inda yaci sunan ahmad,baiyi wani tsawon rai ba Allah ya karbi abinsa,shekara daya tsakani suka sake samun wani yaron aka mayar masa da sunan ahmad din,daganan haihuwar tayi musu dif tamkar aun daina,wanda a tsakanin har amina ta soma fuskantar qananun maganganu irin na dangin miji duk da cewar ba a kusa suke ba,sai bayan shekaru goma Allah ya sake qaddara musu samun wata haihuwar,ta haifi 'yar kyakkyawar budurwa taci sunan fadila,shekara biyu tsakani Allah ya sake kawo wani rabon nan ma mace ta haifa aka sa mata farida,kasancewar fadila mara saurin girma sai suka taso kai daya da farida idan ka gansu zakayi tsammanin twince ne don kamarsu daya saidai farida tafi fadila garin jiki da kuma farar fata,tasowarsu tare yasanya komai daya ake musu hatta makaranta tare aka sanya su,sai da suka shiga jami'a ban bancin course ya raba su,shekara shidda da haihuwarsu umminsu ta sake haihuwar da namiji inda aka sa masa muhammad tun daga lokacin kuma haihuwar ta musu bankwana Babban wansu ya ahmad yayi aure tuni da matarsa anty hafiza harsun samu albarkar twince duka mata ,rayuwar gidan rayuwa ce mai ban sha'awa cike take da son junansu suka taso girmama juna da qaunar juna,sai dai tsakanin fadila da farida akwai tsokana fada da wasa na tsakanin sakuwa da sakuwa sai dai duk da haka farida na respecting din fadila 🌺🌺🌺🌺🌺🌺 S.A huguma [10/16, 12:18 PM] 💍🍬🛍Salma🛍🍬💍: 🌺🌺🌺🌺🌺🌺 Wa yasan gobe?  Safiya Abdullahi musa huguma  🌺🌺🌺🌺🌺🌺 ▶2⃣  Sun fito kenan daga gidan farida ta shigo da motarta layin (da yake ya ahmad yayi qoqari bayan kammala secondry sanda suka samu admission a jami'a ya sai masu yan qananan motoci rio,yace tunda fadila baqace ta dauki fara farida kuma ta dauki marun)farida ce ta soma jan burki ta tsaya don tasan halin mutuniyar zata iya shigewarta tace"ummi ina zaku je?" "Gidan alh salim kwana biyu haduwa tayi wuya shine zanje dubasu"cikin tsokana ta kalli fadila tace "wlh ummi gwara da kika banbaro kifin rijiyar nan kika fito da ita inaga tafi shekara dubu bata je gidan uncle abba ba"fadila ta watsa mata harara tace"ni sa'arki ce"ta qyal qyale da dariya tace sorry yaya fadila"fadila tayi saurin yiwa motar key suka wuce,suna tafiya a hanya suna hira jefi jefi da ummi abinsu gwanin sha'awa har suka isa gidan,gidan na jerin gidajen kundila housing estate dake maiduguri road,gidane irin na masu naira da suka ci suka tada kai,mai kula da qofa ya dage masu wakeken get din gidan cikin fara'a suka shige kasancewar akwai sanayya mai yawa tsakaninsa da ummin Ummi ce a gaba fadila na binta a baya har suka isa tafkeken falon gidan ,haj maimuna na zaune bisa luntsuma luntsuman kujerun dake kewaye da falon kallo suke ita da yaranta sumayy da rabi'ah,sallamar su ita ta dauki hankalin su suka juyo hade da amsa musu,haj maimuna ta miqe cikin girmamawa tana cewa lale marhabin haj kune tafe da yammarnan ,ummi tayi murmushi tace ai kuwa dai kam"ta sake fadada fara'arta tace sannunku da zuwa ai......,maganar haj ta katse ta kama baki tace"a'ah yarannan yau yaushene?,ta fadi tana kallon fadila,dukkansu sun fahimci me take nufi suka qyal qyale da dariya suka ce momi yau laraba,ta gyada kai tana cewa lallai ba shakka ta bawa ranar samu,wlh haj bazan iya lissafa yaushe rabon fadila da gidannan ba,"ummi tace"hmmmm to wlh yauma da qyar na banbarota don taji zamu biya store ne zata kwaso kayan make up shine ma qarfin biyonin"momi ta sake gyada kai cike da mamaki tace lallai yau mun tashi da bismillah haj ku zauna mun tsaya zance na barku a tsaye,dukkansu suka zauna sannan suka fara gaisawa fadila ta gaida momi a kunyace ,ta amsa mata tana cewa"kyaji kunya mana mara zumunci ,sam farida ta fiki zumunci "sumayya dake kusan sa'a ga farida tace"wlh anty fadila faridammu ta fiki zumunci"fadila ta dan harareta da taga idonsu ummi baya kansu tace"ta dai fini qafar yawo yaufa sai da zamu fita ta dawo tun azahar wai ta tafi gidan qawarta "sumayya tace "to ai zumunci taje"fadila ta dan tabe baki tace"ke ni qyaleni yawon farida yafi qarfin qafata ko ina a kano kika kwatanta mata ta sani "sumayya da rabi'ah sukai dariya suka ce "kai anty don dai ke bakison fitarne shi yasa kikace sister ta fiya yawo" Hira suke suka tsinci qanqanuwar muryar
yarinyar na sallama ,ta saki hannun wanda ya riqota da gudu ta fado falon,momi ta cewa wanda ya kawota din sannu isah,yace yawwa haj ya juya ya fice,rabi'ah tace oyoyo ifti na,muga kitson,da gudu ta fada cinyarta ta janye hular da ka rufe mata kanta da ita tana nuna mata,kalbace mai kyau twisting wadda aka lafe jelar ta da beads masu kyau,kasancewar yarinyar nada tsawon gashi sai ta kwanta lub tayi kyau har dokin wuyanta,tace anty sumy tayi kyau"sumayya tace gsky qawata ba magana "ta bata hannu suka tafa,ta miqe tayi gun momi ganin ummi yasata duqawa ta gaidata,ummi ta amsa fuskarta dauke da fara'a momi tace"har yanzu fushi ake kenan da ni shi yasa ni baza'a nuna min kitson ba"cikin magana irin tq shagwababbun yara tace "ba cewa kikayi ayimin mai zafi ba"sai kuma ta juya ta koma gunsu sumayya tana bata lbr,ummi ta kalli momy tace"wai iftihal din Aliyu ce wannan?"momi dake tsiyayawa ummi lemo a cup tace"itace mana kinga yadda ta girma ko?"ummi ta jinjina kai tace"ba shakka gata nan kuwa masha Allah,ina zaton ai ba zata wuce shekara bakwai ba ko?"momi tace "idan watan nan ya mutu sabon wata ya kama yakai ashirin zata cika shida",sai bayan sunyi magariba suka fito,tuni iftihal ta maqale wa fadila domin cikin qanqanin lokaci suka saba,don fadila ba daga baya ba gun son yara,bare iftihal yarinya ce kyakkyawa ga wayon tsiya,har bakin mota suka rakosu sumayya na yaba kyawun motocin nasu,fadila tace idan kina so ki amsa mana,sumayya ta kama baki tace rufamin asiri kada kisa yaya aliyu ya babbalani kina ganin abba zai sai mana ma ya hana wai har yanzu bamu da hankali sai randa muka qara nutsuwa?fadila tayi dariya tace "sai kace yau aka haifeku""kema dai kya fada sister cewar rabi'ah,dai dai nan ummi da momi suka qaraso momi ta miqawa fadila baqar leda tace"to ga kayan kwalliyarnan aje ayi tayi ana samo mana sueukai"a kunyace ta amsa tana mata Godiya,momin tace to sai wata shekarar kenan,fadila ta sadda kai qasa tace"a'ah momi insha Allahu zaku dinga ganina"Allah yasa inji momi,ummi tace"wai ni kuwa ina Aliyu ne,na kwana biyu rabon da na ganshi fa"fuskar momi ta canza zuwa yanayin damuwa tace"hmmmm,mtsw,ke dai bari kawai haj kwanan nan zaki jiyomu da shi,Aliyyu fir ya guji aure yaqi fidda mace yayi aure,yafi ganewa kasuwancinsa kawai nayi har na gaji hakanan abbansa kullum zancen kenan amma yaron nan sam yaqi mai dakansa"ummi tace"addu'a kawai zaku ci gaba da yi masa Allah ya kawo ta gari kada a kuma komawa 'yar gidan jiya a bata goma daya bata gyaru ba"momi ta gyada kai tace hakane,Allah ya zaba mana abinda yafi alkhairi"tace amin Daqyar iftihal ta rabu da fadila harsai da ta laluba cikin motarta ta samo mata chaculet sannan ta yarda ta barsu suka tafi,basu tsaya ako ina ba sai a shop rite dake ado bayero mall,ta nufi parking space ta gyara tsayuwar motarta sannan ta kashe,ummi ta zaro kudi cikin jakarta ta miqa mata,tace maza kiyi da jiki ki fito"tasa hannu biyu ta amshi kudin tana qoqarin maida murdin motar ta rufe ne ummi tace"saura ki kwaso kayan zaqi da sanyi ki koma gida ki guji maqiyin naki abinci"tayi murmushi kawai tace baza'a siyo ba ummi ta rufe motar ta shige,cikin nutsuwa take daukar musu abinda tasan suna da buqatarsa ita da farida har ta kammala,har zata nufi kanta ta tuna bata dauki turarenta ba blue lady,cikin sauri ta koma,hankalinta yatafi ga turarurrukan tamkar ance ta kalli gefanta,tsaye yake shima yana zaban nasa kalan,yana sanye cikin shadda dinkin tazarce blue Black ce ta haska farar fatarsa matuqa,ta gefan tana iya hango qaya taccen sajensa dake kwance luf bisa tsararriyar fuskarsa,ga tsinin hancinsa nan yayi das qasan farin qal din glass dake bisa fuskarsa,kyakkyawan idonsa wanda gashin idon suka yiwa rumfa suna juyawa cikin farin glass din nasa yan karanta rubutun dake jikin kwalin turaren,kansa ba hula sai sumarsa dake kwance an dan saisayeta,ya zari turaren kwali uku cikin sassarfa ya juya yabar gun,samun kanta tayi da bin bayansa zuwa inda zai biya kudinsa ,kusan tare suka biya sai dai sam shi bai lura da ita ba ya juya ya fita ta sake bin bayansa,tafiyansa ma abar kallo ce tamkar wani saraki haka yake takawa,daga nesa tadan tsaya a harabar adana motocin don batason ya ganta,cikin aljihunsa yasa hannu ya zaro key ya bude wata baqa sidiq din mota qirar range rover ya shiga yayi mata key ya jata da gudu ya bar gun,jan ajiyar zuciya tayi gamida lumshe idonta hadi da dafe goshinta da tafin hannunta"inna lillahi wa inna ilaihir raji'un allahumma ajirni fi musi bati wa akhlifni khairan minha"abunda take ta nanatawa kenan,wannan wace iriyar musibace zuciyarta ke son jefata ba gaira ba dalili?,ta bude idonta ahankali jikinta ba laka ta soma lalubar inda tayi parking Cikin motar tayi dif zugi da radadi take ji,ba abunda zuciyarta keyi sai zillo cike da dimbin qaunarsa,shi wa?,ita kanta bata sanshi ba,ummi nata mata hira tana cijewa tana amsa mata har suka isa gida,farida na falo ta baje kolin takardu da alama assignment takeyi,batason ta dameta da hira don haka tadan daure fuska,itama faridan data fuskanci hakan bata ce mata komai ba illa sannu da zuwa ya kuka barosu?,ta amsa mata ta haura sama inda dakinsu ita da farida yake,ta watsa siyayyar tasu kan gado zuciyarta cunkushe ta cire kayan jikinta ta fada toilet da niyyar sakarwa kanta ruwa ko zataji sanyin zuciyarta  Muje zuwa S.A.M huguma✍🏻 [10/16, 12:19 PM] 💍🍬🛍Salma🛍🍬💍:  🌺🌺🌺🌺🌺🌺 WA YASAN GOBE?  ▶3  SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA 
🌺🌺🌺🌺🌺🌺 Lotion kawai ta shafa bayan ta fito ta feshe jikinta da body spray ta lalubi rigar bacci doguwa har qaurinta ta zura don bacci take da muradin yi, ta daura zani a sama ta sanya hijabin sallarta ta gabatar da sallar isha'i, ta dora da shafa'i da wutiri, bayan ta shafa addu'o'inta tabi lafiyar gado, a maimakon bacci yazo mata sai tunani ya mamaye gurbinsa, ba zato ta tsinci kanta da zubarwa kanta da kanta hawaye na tsananin tausayin kanta, a cikin jikinta da zuciyarta take jin ta shiga halin tsaka mai wuya, zuciyarta na bulayi da lalube cikin duhun son wanda bai ma san tana yi ba, farida ta shigo dakin hade da sallama hakan ya sanyata saka hannu tana goge hawayen cikin dabara don bata son faridan ta gani, faridan tadan kalleta jikinta yaso ya bata tamkar yar uwarta na cikin damuwa, don haka jikinta sai ya danyi sanyi ta shigo ne da niyyar tsokana don flask guda ummi ta ciko da abinci tace kada ta sauko da shi sai ta cinye Farida ta ajjiye flask din a gefan gadon ta janyo dressing chair ta zauna tana fuskantar fadilan tace"sister lafiya naga kamar fuskarki ta nuna kamar kina cikin damuwa? ,ta qaqalo murmushi sannan tace"ba abunda ke damuna just na gajine fitar nan da nayi"farida ta girgiza kai ba don ta yarda ba tace"ok,to ga abincin ki nan ,ummi tace " kada ki sauko mata da shi sai kin cinye tana daga kwancen ta zubawa flask din ido tace"har gabana ya fadi wlh, ina zan kai wannan abincin? ,farida ta qyalqyale da dariya tace"ni dai yar aikece kuma na isar da saqo,qafafunta tayi saman tiles din daya mamaye da qaton dakin nata Ta daura zani a sama ta sanya hijabin sallarta ta zari flask din, farida ta kalleta tace " a'ah ina zuwa? "Ba tare data kalleta ba ta juya tana shirin fita sannan tace"jirani ina zuwa"farida ta bita da kallo tana dariya ciki ciki ,ta qofar baya fadila ta fita ta bulla bakin get din gidan,kai tsaye ta nufi gun idi mai gadinsu, mutuminta ne dama da hangota kuwa ya miqe yana cewa " uwar dakina"miqa masa flask din tayi tace"yi sauri ka juye idi"cikin qanqanin lokaci kuwa ya juye abincin ya bata flask din yana zuba godiya Ta tarar da fadila na waya da alama da saurayinta take, ta koma gefan gadon ta zauna tana kallon faridan har ta kammala tsaki fadilan tayi, farida tayi murmushi tana kallon flask din da fadila ta dawo dashi don tasan kwanan zancan, bata son idan zatayi waya tayi mata a dakinta,fadila ta harareta tace"bana gaya miki ki daina shigomin daki idan zaki shirmen wayarki ba? ,tace tana gyara kwanciyarta akan sofa qwaya daya dake dakin " sorry anty na"tana dan murmushi tace kiyi haquri ⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜ Tun bakwai na safe take a kitchen dama haka al'adarta take, idan bata da lecture to Itace mai shirya musu breakfast haka da rana ko da daddare,girki yana daya daga cikin hobby dinta hakan ya sanya ta zama gwana ta fannin abubuwan ci da na sha, Awa daya da rabi ta kammala komai ta koma dakinta tayi wanka ta shirya kasancewar tara da rabi tana da lacture,dakin ummi ta shiga bata nan sai muhammad ta tarar yana kan gadonta yana bacci,dala masa duka tayi tace"tashi malalacin banza eight thirty amma kana bacci ina school din?"cikin magagin bacci yake murza ido yace"wlh nayi wanka bacci ne ya daukeni"tace"oya tashi ka shirya idan zan wuce na sauke ka na baka eight minute"da sauri kuwa ya duro daga kan gadon ya shige toilet Bangaren abbansu ta wuce tare da diba masa breakfast dinsa ta tafi masa da shi,yana zaune kan kafet din falon hannunsa dauke da jaridar daily trust,haka yake a al'adarsa bayan ya dawo a masallaci yakan yi azkar da tilawar qur'ani idan gari ya dan sha kuma sai ya karanta jarida kafin ya fita aiki,fadila ta shigo da sallama, ya masa yana dubanta fuskarsa dauke da murmushi,ta dire kayan abincin ta rusuna tana gaidashi ya amsa yana fadada fara'ar shi yace"sannu fadila da qoqari hala yauma anada da lacture din safen"kanta a sunkuye tana qoqarin hada masa kunun shinkafa da yasha madara tace"eh Abba",ummi ce ta fito daga bedroom din Abban hannunta dauke da doster da alama goge goge ta gama,fadila ta gaidata tana qoqarin tashi tace"abba zan tafi"ya dubeta sannan yace"ai banga kin ci komai ba haka zaki tafi?""abba zan karya a capteria idan na.......... Ummi tayi saurin katse ta da cewa"yi mana shiru wlh abbansu idan taje ma bacin take ba farida ai ta gaya min wai ba zata iya cin abinci a waje ba,wannan yarinya na rasa meke damunki anya lafiyarki qalau kuwa?",abban yayi murmushi yana dakatar da ita"dakata umminsu,fadila lafiyar ta qalau,kin manta yawon asibitin da muka dinga yi da ita tun tana qarama?,haka dai halittarta take"ya juya ga fadila yana tura mata cup din da ta hada masa kunun yace"maza zauna kici wani abu kada ki qara bata ran umminki kinji ko?"tamkar zata sa kuka😟 ta zauna tana cewa"to abba"yaci gaba da cewa"gashinan fadila tafiki abin arziqi shi yasa ta rainaki tana ganin kanku daya,ummin tace sai rawar kai da gwanintar yin girkin amma saidai wasu su ci mata,abban yayi murmushi yana kallon yadda take tura abincin kamar magani😣 Kafin ta kammala muhammad ya shigo don haka abban ya sallamesu suka fita tare,suna mota muhammad ya dameta da surutu,ta daga masa hannu ✋🏻hadi da cewa kaga malam bafa aku na dauko ba🐔idan kuma kai aku ne ka gayan"ya qyalqyale da dariya😂 yace"anty ke dai ba dama mutum yayi hira dake sai kice ya dameki shi yasa yaya farida ke burgeni ke halin ya ahmad kikayo kun fiya kwafsawa wlh,ta harareshi sannan tace"ai da itan da kai duk zamuce ta tadda mujemu idan mutum baiyi surutu ba baya burgeku,kada Allah yasa mu burgekun muyita kwafsawar,idan ka qara magana kuma sai na saukeka anan" take ya rufawa kansa asiri yayi shiru🤐 Taso makara saboda ajiye muhammad da tayi don ita ta saba da wuri take zuwa don ta samu sit din gaba,bata da wata qawa bare ta tarar mata hakan ya jawo batayi parking din motar ta daidai ba ta nufi ajin cikin sauri Lacture din ta daukesu awa uku har da mintina,kanta ya dauki chargy sosai,don haka da fitowarta ta samu wani guri dake nesa kadan da ajinsu bashi da yalwar jama'a sosai yafi kusa da inda suke ajjiye motocinsu idan sunzo,gurine mai wadatar shuke shuke ita kuwa ma'abociyar son tsirrai ce [8/8, 3:24 PM] LOADING......  gun na burgeta saboda son tsirran da take dashi,tamkar a cikin iska ta ke jiyo qamshinsa,gabanta ya tsananta faduwa,ta gefan ta ya wuce saidai bayansa kawai take iya gani,ahigar suit ne a jikinsa masu dan karen kyau da sheqi,kayan baqaqene sai tsintsiyar hannunsa da ta gani wadda yake daure da agogon fata baqi,gefansa wani ne ke biye da shi riqe da takardu da brief case,sam sai ta kasa dauke idanunta daga kanshi👀,hakanan gabanta yaci gaba da faduwa cikin zuciyarta take fadin inna lillahi wa inna ilaihir raji'un"har ya danyi nesa da ita sai taga ya waiwayo,cikin wani irin sauri ta dauke kanta tayi wani sashen da shi zuciyarta kamar ta tsinke ta fado,ganin yayi gaba tayi hamdala da Allah yasa bai lura da ita ba,tana tsammanin jikinsa ne ya bashi ana kallonsa👀,a sace taci gaba da kallonsa har ya bacewa ganinta,taja ajiyar zuciya sannan ta dauke idonta daga kallon hanyar ta jawo jakarta ta zuge ta fiddo da wayarta tana danne danne,ta doshi kusan minti aahirin a gunbtana hutawa sai sannan ta tuna zata fa gidan ya ahmad,da sauri ta miqe tana gyara yafen gyalenta,atamfa ce ajikinta dinkin riga da skirt ne,atamfar England ce dark green mai ratsin yellow,sai mayafinta da takalminta agogo da jakar hannu duk yellow,fadila ba qarya ta iya daukan wanka don duk munin atamfa takai aka mata dinki ya saka komai kushe da hassadarka baka isa kace batayi kyauba haka Allah ya bata wannan baiwar,tana tattare komatsanta tana sanyawa a jaka taji ana kwada mata kira,a nutse ta dago tana neman daga ina wannan kiran mafarautan ke fitowa?,wata class mate dinta ce binta auwal fadila taci gaba da binta da kallo har ta qaraso,"fadila abbas yaufa kinyi tabargaza"abinda ta soma cewa kenan,fadila tace"kamar ya fa?"tana dubanta tace kinyi wrong parking kin toshewa A.s mai tama hanya"ta sake dubanta cikin rashin fahimta tace"waye haka kika bi kika rude?'binta ta zaro ido😳 tace"kar dai kice min baki san a.s mai tama ba,hadadden guy din da duk nigeria bama kano ba ansan da zamansa"fadila ta dakatar da ita ta hanyar cewa"na gode"taci gaba da mayar da kayanta jaka Iya dube dubenta ba wanda ta gani sai mutum daya👀,a tsammaninta idanunta ke mata gizo,sai dai har ta qaraso gun shi din dai ta gani,yana tsaye hannayensa harde a qirjinsa fuskarnan a murtuke,ta qaraso ne da niyyar bashi haquri sai dai lura da irin kallon qasqancin da yake mata mata yasa tayi banza da shi kai tsaye ta nufi motarta ta bude,ta zauna a seat din tana qoqarin jan murfin ta rufe taji an dafe murfin motar,ta dago ta dubeshi,yana tsaye yana mata irin kallon dazun,cikin qasaita taji yace"baki da ladabin bada haquri ga wanda kika aikatawa laifi?"duk da yadda zuciyarta ke sake ninqaya a zuciyarta,muryarsa mai sanyi ta kwanta a zuciyarta,amma ta dake gami da cewa cikin zuciyarta"duk da dumbin qaunar da nakeji taka a zuciyata hakan bazai sa na bada girma da jan aji irin na 'ya'ya mata,ta dauke kanta sannan tace"ai shi wanda akawa laifin baisan darajar bil'adama ba"ya saki murfin motar hadi da watsa hannayensa yace"ok,ba laifi"ya saki murfin motar,cikin wata iriyar gaggawa taga ya amshi key din tasa motar daga hannun wanda suke tare ya bude motar sa ya shiga cikin gwaninta ya take motar ya kurda ya matse motar fadilan ta yadda itama bata isa ta fita ba harsai da ya gogeta,ya kashe motar ya zare maqullin ya rufe motar ya fito yana cilla maqullan yana cafe wa ya danyi tsalle ya haye bayan motar ya zauna,da hannu ya kirashi yadan yi masa rada ya amshi tak ardun hannayensa shi kuma ya juya da sauri ya bar gun
Sarai fadila ta fahimci abunda yake nufi saboda haka ta zaro wayarta ta nemi number farida ta kirata"hello farida kin shigo school?"tace"eh ya akayi?""kizo ina parking space ki daukeni mu wuce"farida tace"me ya sami motar ki?""kinga idan zaki zo kawai kizo malama""ok sister gani nan" Cikin 'yan mintina sai ga farida horn tayi mata ta miqe ta fito ta kulle motar ta gabansa ta shige ta nufi farida,dai dai lokacin ta jiyo saukowarsa daga bayan motar,wata yar qaramar mota ce tayi parking a gabansa kusan tare suka shige motocin,ta madubin motar farida suka hada ido ta sakar masa tsaki hadi da murguda baki,cikin zafin nama ya balle murfin motar ya fito da sauri tacewa farida"yi sauri ki bar gurinnan,tamkar kuwa tasan meke faruwa ta figi motar ta bar gun  Muje zuwa [10/16, 12:21 PM] 💍🍬🛍Salma🛍🍬💍: 🌺🌺🌺🌺🌺🌺  Wa yasan gobe?  Safiya Abdullahi musa huguma  🌺🌺🌺🌺🌺🌺  ▶4⃣  Sai da motar ta saitu akan titi sannan tace mata"gidan ya ahmad fa zamu"ok" inji farida,"sister wai me ya faru naga kamar wadda aka biyo a guje?"taja tsaki tace"wani dan rainin hankali ne yaso wulaqantani bai san bana daukan wulaqanci ba"ta bata lbr yadda sukayi da shi akan toshe ma juna hanya da sukayi,me farida kuwa zatayi idan ba dariya ba,"kefa 'yar wulaqanci ce shi yasa ban fiya saki cikin lamarina ba,a yar madaidaiciyar harabar gidan sukayi parking,kai tsaye suka nufi falon gidan,ba kowa cikin falon da alama matar gidan na ciki don haka suka dinga kwada sallama,daga kitchen matar gidan ta fito anty hafiza kenan kyakkyawar bafullatana,tana ganinsu ta saki fara'a😊 cikin barkwanci tace"lallai yau baquntar tamu ce"suka saki dariya😀dukkaninsu suka gaidata cikin girmamawa ta amsa musu cikin kulawa tana tana tambayarsu ummi,suka ce tana lpy tana gaidata,fadila ta zaro packet na chaculet tace gashi injita a baiwa twince,wai ni ina suke nema anty?""tace yau ai ranar school ne suna can amma suna hanya don bala ya tafi dauko su,""na manta wlh"ta fada tana qoqarin kwanciya bisa doguwar kujera"anty hafiza tace"ah ya haka ina murna kuku tazo kuma naga tana neman bin lafiyar kujer?"fadila ta dan murmusa 😊tace " anty yau saidai amin afuwa yau kasala nake ji""na miki"inji anty hafiza,farida dake canza tasha a t.v tace"qyaleta anty muje na canjeta yau tsokano fada tayi sauran kadan taci na jaki badan Allah ya kawoni na ceceta ba""tab wucenan wlh wa ya isa yayi gangancin taba mana ita?😳""fada mata dai anty😏"cewar fadila,suka shige kitchen nan suka barta a falon Gyara kwanciyarta tayi don taji dadin yin tunaninsa,shi wa?,idan bata manta ba A.S mai tama binta tace da ita,A.S mai tama ta shiga maimaita sunan ita da zuciyarta,"to me A.S mai tama take nufi?"A dai duk inda aka zaga farkon sunansa ne,to ahmad ne ko ko abubakar ko abdul?,oho itama bata sani ba,wani murmushi ne ya subuce mata😊 sai tunaninta ya dawo kan abinda ya faru tsakaninta dashi dazun,sassanyan muryarsa ta dinga yi mata amsa kuwwa a kunnenta,kyawawan idanunsa yanayin zubinsa da tsarinsa,sai ta tuna sanda ya fito a fusace lokacin data murguda masa baki ta harareshi,nan ma dariya ce ta subuce mata,"lafiya kuwa?"ta tsinci muryar farida na tambayarta,ta hade rai tace"lpy lau me kika gani?"farida ta dan tabe baki tace"hmmm tun dazunfa kike murmushi har da dariya ke kadai kamar wadda ta fara soyayya"da sauri fadila ta kalleta tace"lallai yarinyar ni kikewa wannan titsiyen?to gyada na zama na soye qarewar soyayya"anty hafiza dake zaune saman kujera bata sa baki ba sai yanzu tace"um um yaya fadila wannan fa sign ne na falling in love😜"fadila ta miqe daga kwanciyar tana cewa"kai anty,please kada ki biyewa shirmen farida,ita 'yar sa ido ce komai ta gani idonta na kai,kuma sai ta sanya ma question mark😏",ta gyada kai sannan tace " alright idan tayi wari maji,Allah yasa alkhairi ne""amin amma ba abinda zaiyi wari ma anty",nan gidan suka wuni har 'yan biyu suka dawo suka yini tare da su,suna son yaran sosai ko dan su kadaine jikokin gidan nasu,sai bayan magariba sukayi sallah sukaci abinci har yaya ahmad ya dawo ya tarar da su,bayan sunyi shirin tafiya ne ya ahmad ya baiwa ko wacce 4000 anty hafiza kuma ta basu turarurruka. to daren ranar sam fadila bata samu bacci ba,kusan kwana tayi tunanin A.S maitama,duk da ta danji dadi don aqalla tasan yanzun yasan da fuskarta a duniya,koda bazai iya shaidata ba bare tana tunanin mawuyacine ace yayi saurin manta ta ko dan irin karon da suka yi,har washegari da taje school bai janye motar tasa ba,sun dauki aqalla sati guda a haka sannan taje ta tarar ya cire,a gida tace ne kawai tana tana garage ana duba mata ita ⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜ Cikin wannan yanayin suka soma attachment,ranar laraba aka turasu domin tattaunawa da wani fitaccen dan kasuwa,ita da abokiyar karatunta ne hafsat sai wani ma'aikacin gidan radion khalid da zasu tafi tare qarfe hudu na ranar larabar. cikin yellow din atamfa ta shirya mai zanan blue din qananun taurari,skert ne rafa da riganshi wanda dinkin yayi mata cif a jikinta kamar don ita aka qera atamfar,ta maqala qananun fashion na dutse masu kalan blue,ta daura dan siririn agogo na fata ,qafanta blue din hill shoes ne mai madauri sai mayafi data yafashi a kafada bayan ta soka daurinta wanda ya fito da dogon gashinta ta qasan daurin,jakarta ta dauka 'yar madaidaiciya wadda ake maqaleta a gwiwar hannu ta feshe jikinta da turaren shamsul imarat,shigar ta haska fatarta sosai ta fito dagwas da ita,farida dake nade a tsakiyar gadon fadilan tana charting ta dago ta dubeta"gsky yaya fadila kinyi masifar kyau,tsiyar abun daya da baki kula kowa,sai ance anasonnki kuma ki kama mita bayan laifinki ne saiki yi shiga ta janye hankali kuma kice ba wanda ya isa ya kalaki"banza tayi mata ta dauki wayarta dake kan dressing mirror ta fice,farida ta dan daga murya yadda zata jiyota tace"a dawo lpy antyna Allah ya hadaki da mannau ya biyoki har gida😜"bata dai ce mata ci kanki ba ta wuce dakin ummi don tasan a wannan lkc tana daki tana azkar,daga bakin qofa ta tsaya don ta kusa makara tace"ummi zan tafi""to Allah ya tsare hanya ki kula sosai kuma kuna kammala abinda kukaje yi ki taho gida kada ki yadda kiyi dare a waje"tace insha Allah ummi",acan gidan radion suka hadu,bata shiga ba ta yiwa su Hafsa waya su fito su wuce don a motarta suka tsara za suyi tafiyar,Hafsa na zaune a baya yayin da khalil ya shige gaba,tsaf fadila ta gama karantar manufarsa saidai tayi banza da shi tamkar bata fuskance shi ba,tun zuwanta gidan yake rawar qafa a kanta saidai ya kasa furta mata kamar sauran maza da yawa,tana da wani irin kwarjini ne a idanunsu ita sam baya burgeta,ya fiya surutu shi yasa sam bata son ko aiki ne a hada ta da shi,kamar yanzun ya takura mata sai zuba yake shi ala dole sai ya burgeta,Hafsa na baya tana ta tuntsira dariya 😂don tasan halin kayarta sarai,daqa qarshe c.d plate ta dauka tasa sannan yayi shiru A hankali suke binkwatancen har suka gano gurin,qaton get din gun aka bude musu gu ne a tsare ahankali aka dinga nuna mata inda zata bi har taje inda aka tana da don ajiyar motoci tayi parking suka fito,ta jingina jikin motar tata tana qarewa gun kallo,tamkar ma'aikata gun yake saidai ya tsaru sosai komai neat,khalil ya qarso gunsu bayan yaje yayi tambaya yace muje can sunce mu jirashi yana fitowa,wani dan gune da ka qawatashi da flastic din kujeru da teburinsu kowanne yaja kujera guda ya zauna sun dan dauki mintina har fadila ta soma qosawa da zaman jiran Tun daga nesa da ta hangoshi qirjinta ya hau luguden bugawa,ji tayi tamkar ta tashi ta bar gurinsai kuma taga idan tayi hakan ta bada kanta,don haka sai ta basar ta zarme da bude jakarta ta soma fiddo da kayan aikin da zasu buqata,qashin mayen tutarensa da taji ya mamaye gurin shi ya tabbatar mata da qarasowarsa,sallamarsa ta same tabbayr mata da hakan dukkansu suka amsa saidai ita ta kasa dago ido ta dubeshi ta fake da laluben jaka,ya .iqawa khalil hannu sukayi musabaha hafsat ta gaidashi,sai a sannan ta dago kanta caraf suka hada ido👀 saidai ga mamakinta dauke kansa yayi tamkar bai taba ganinta ba,a hankali ta radawa hafsa"da wa za muyi hirar ne?""gashinan a gabanki a.s maitama "inji hafsat"take taji ta dan rude amma cikin dabara ta gayyato dakiya da nutsuwa ta yafawa kanta,kasancewar Ita ce mai tambayoyin jfsat da khalil na tayata da rubutu dolenta ta jawo kujerarta ta sake matsowa daura da shi ta sanya 'yar qaramar recorder dinta a tsakiyarsu suka sake zama verry close aunyi face to face sosai,wani yanayi ya dinga shiga zuciyarta da gangar jikinta wanda hakan ya haifar mata da kasala,tanason tayi.masa tambaya ta farko saidai ta kasa,har sai da hafsat ta dan dungure sanna tayi ta maza ta dago ta fuskanceshi👀,saidai ga mamakinta hannauensa na harfe ne bisa qirjinsa yana mata wannan salon jallon rainin nasa😏,da fari munason muji ainihin cikaken sunanka,ta fada yayin da ta mayar da dubanta kan radio dinta taga tana nadar sautin yadda ya kamata,shiru taji har yayi yawa ta dago ta sake dubansa a karo na biyu,saia taga ya saki hannunsa ya dauke idonsa daga kanta ya kalli khalil yace"ko zakuyi musayar aiki ita ta ta karbi rubutun kamar ba zata iya aikin ba"khalil ya dan rusuna yave ranka ya dade zata iya haka tsarin aikin yazo"ya kalleta cikin gatsali yace"zaki iya?"batayi qasaaqwiwa ba tave aisai an gwada aknsan na qwarai"ta mayat masa da irin yanayim yadda ya yi mata tambayar,cikin ransa yake jinjina rashin kunyarta tare da fafin nasan maganinki" a zuciyar sa ya fadi hakan  Ku biyoni muje...... 


Post a Comment

0 Comments