TOP HAUSA NOVELS atOptions = { 'key' : '20e08520dad54dbf6d9e963271

KUYANGA NOVELS


 KUYANGA...* 📿

*_🌈KAINUWA WRITERS ASSOCIATION_*

```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```

https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

*Nabilancy Luv* 💘

(Auntyn S&S)

          1-5

Sarki Abdallah Adalin Sarki ne mutum me kamala da Son talakawansa Wanda yake da mata Uku sai yara biyu matarsa ta farko uwar gidan itace Hauwa,u Anace mata *UMMAH*

Mebi mata itace Saratu *MAMAH* sai ta Uku amaryar sarki itace Fatima Amma *FATU* akece mata

UMMAH macece me tsananin kishin gaske Tanada gadara da iko ita din yar gidan Sarautace tana buga ikonta agidan sarki domin sarki Abdallah yanaji da ita don haka take buga sha,aninta ackn gidan kowa shakkarta yakeyi tundaga fadawa,Bayi maxa da Kuyangin gidan da duk wanda ke cin gidan har kishiyoyinta D'anta Daya jal Yarima Anwar Wanda aka shagwaba shi da Gata Awaje yayi karatunsa Tundaga Sakandare har tagaba da Sakandaren wanda ba karamar tabarbarewar tarbiyya zamansa acan yaja masa ba don tun daya gama karatunsa yaki dawowa Yasamu guri xan babu kwaba babu harara

Har saida labarin abinda yakeyi yadawo kunnan me martaba yai masa aike takakkiya aka taho dashi

Yayi masa fada sosai har kurari yaimasa yace inhar baidaina ba zai yi masa Aure ackn dangi zai laluba yadaura masa Aure da koma wacece

Aikin Anwar acan neman matan banza turawan nan sun sassanshi haka abokan banza yake mu,amula dasu basu da aikin komai saibin club club ana lolewa da mata anashan Giya ana raye raye

Amma yafi Ronce da wata baturiya data nace masa mesuna RIHANNA wacce duk wulakancinsa takan shanye Abu daya yasa yake d'anshan mintinta tasan takan iya kulawa da d'a namiji duk luggar yaudara da iya Romance ta kware

Inda tayi musu zarra kenan gata da kishin tsiya tasha zane mata masu kawo masa hari Amma ahakan yake yakiceta yaje yashana da wacce yakeso danma tana shakkarsa da bazata bari yasakeba

Anwar yanada isa da jinkai jinsa yake tamkar sarkin wani zubin to kullum azuciyarsa yana jin kome zaiyi babu wanda ya isa yakawo masa cikas tunda shi din dan sarkine me jiran gado

Mahaifiyarsa ke kara sakawa yaji izxa aransa akullum takan nusarsa cewar shine sarkin gobe duk da shi bawani son yazama sarki yakeyiba tunda yasan inya zama sarki dole yazauna guri guda kuma yabar duk abinda yakeyi knn.

Sarki Abdallah akullum cikin bakin cikin Abinda dansa Anwar yakeyi yakeji aransa wanda yarasa yadda zaiyi dashi don yakintsu tunda shine babban dansa wanda wataran dole shine sarki agarin

Yasan da cewar Mahaifiyarsa ke xugashi tunda yahaneshi da zaman turai tace abarshi yahuta acan kafin wani lokaci bata son abinda zai bata masa rai

Sauran matan Sarki su idone nasu domin ta tsakiya MAMAH bata taba haihuwa ba itako Amaryar sarki FATU ta haifi Danta namiji tsiransu shekara biyar da Anwar yaron sunansa LAMIDO

Ummah bata kaunar FATU da D'anta sbd Fatun bata dade da zuwa gidanba ta samu ciki

Ko MAMAH data rigata xuwa bata qullaci fatun ba domin MAMAH macece me tawakkali duniya bata dametaba

Kowane d'a daga cikinsu tadaukeshi tamkar ita ta haifeshi

Amma tun tasowarsu da suka girma sai tafi kaunar Lamido domin shi yarone me hankali magana ma bata dameshiba a Nigeria yayi karatunsa

Lokacin daya isa shiga jami,a alokacin Sarki yaso turashi Turai shima Amma sai FATU taki amincewa sbd a ganinnta xaman turai ga yaro ba uwa ba uba na bata yaro da canza masa halinsa mekyau zuwa mara kyau tunda shima Anwar dayaje ba haka yakeba ada daga baya yakoyo wasu dabi'un

Sarki bai bata rai akn hknba domin takawo masa kwararan hujjojinta akan rashin son zuwan nata Turai yakuma gamsu

MAMAH ma bataga laifin taba domin tasan komai kuma kansu ahade yake su biyun

Sautari UMMAH takance wai sun hade mata kai

Sukuwa shakkarta da sukeyine yasa basa shiga Sabgarta

******

Tun Dawowar da Anwar yayi Nigeria kusan wata biyar yaji yagaji da zaman atakure yake baya futa club balle korawa da neman mata sbd babu dama duk inda yayi ido akansa suke inma yayi awajen gari Sarki zai iyaji azo ace yabatawa gidan suna shiyasa yafison yafita away

Rihanna tayi ta damunsa akan inhar bai dawo Turai ba zata hado kayanta ta biyoshi ta nemi inda yake

Hankalinsa yadaga dan yasan zata iya shiko yasan inhar tazo kashinsa yagama bushewa ackn gidan

Ba shiri yahau hada kayan dazai tafi dasu domin yai mata Alqawarin zaitaho cikin Satin domin ma kwana biyu yabata zaitafin

Da tunanin yanda zaishawo kan Sarki yabarshi yatafin yashiga cikin gidan Bangaren Mahaifiyarsa domin yafara kai mata zancen su samo mafita tukun

Yana tafe afarfajiyar gidan yana tafiyar Jinkai da wani shankamshi da Rangaji ackn Shigar Alfarma ta sarauta

Bayi maza Da kuyangu mata nata aiyuka suna wuceshi tareda durkusawa suna kai gaisuwarsu ga Yarima sarkin gobe

Wata *KUYANGA* Yakurawa idanu dayaga tanata sharar gurin ajiye dawakai kanta ba dankwali dan gyalen data yane kanta ya xame bata saniba

Farace shar gata da hips ga nashanu suncika mata kirji

Ta dago zata bar gurin yakwalla mata kira

Aguje takaraso gareshi da biyayya ta durkusa tana gaidashi

Yakara kallonta na sakanni kana yace ckn shanqamshi "me kikeyi acan?

Da rawar murya tace "ina..,ina yin..,Shara nakeyi...

Yace "Dama Sharar gurin Dawakai nakune mata kona Bayi Maza?

Tayi kasa da kai tace ckn rage murya "Allah yataimaki Yarima tuba nakeyi ba aikina bane MAHBUB nake tayawa yatafi wani uzurin.

Yace "MAHBUB!wanene kuma *MAHBUB?*

Tahau kame kame tazaci ko laifi tayi

Tace "Abokin shawaratane tamu tazo daya.shima yana tayani Aiki shiyasa nake tayashi

Ayanda take maganar yabashi Sha,awa bakinta me kama da anzana heart yatsurawa idanu yaga tana motsashi ahankali

Koda tayi shiru shima shirun yayi yana kallonta kawai

Wani abu yaringa ayyanawa aransa

Dataji shi shiru saita dago kanta dasauri tayi tsammanin yatafine saitaga ashe yana gun


Post a Comment

0 Comments