TOP HAUSA NOVELS atOptions = { 'key' : '20e08520dad54dbf6d9e963271

GWAMNATIN JIHAR KANO TA TURA MATASA KASASHE DABAB DABAN DAN YIN KARATU

 Gwamnan jihar Kano
Abba Kabir Yusuf ya tura Ya'yan Talakawan jihar Kano 1001 zuwa kasar India
Domin karo ilimi mai zurfi yaran da aka zabo bisa kokari da cancantan su

SHIRIN INGANTA ILMI A KANO: Yadda Gwamnatin Abba Gida-gida ta bi gida-gida ta kwashi ɗalibai 1001 zuwa karatu ƙasashen waje
Gwamnatin Jihar Kano ta zaɓi ɗalibai 1001 da ta fara ɗaukar nauyin karatun na digiri na biyu a ƙasashen waje.

Yayin da wasu za su yi na su karatun a Indiya, wasu kuma a Uganda za su yi na su kwasa-kwasan daban-daban.

Gwamna Abba Kabir Yusuf ya ƙaddamar da Shirin Bada Tallafin Karatu Ƙasashen Waje, wanda aka fara ranar Alhamis da jigilar ɗalibai 550 daga Kano.

Gwamna Kabir ya ce ya ɗora wannan gagarimin aikin alheri ne daga inda tsohon Gwamnan Kano, kuma madugun Kwankwasiyya, Rabi’u Kwankwaso ya tsaya, a lokacin mulkin sa.

Ya ce ayyukan alherin da gwamnatin Kwankwaso ta yi wa al’ummar Kano a baya, su na da muhimmancin da ba za a iya daina ci gaba da su ba.

Kabir ya ce ga shi nan ƙarara ana ta cin moriya da amfanar waɗanda suka je waje karatu a ƙarƙashin gwamnatin Kwankwaso, inda wasu na riƙe da muƙamai sosai a gwamnati da sauran fannonin ayyukan yau da kullum.

Ya lissafa wasu da suka haɗa da Kwamishinan Ilmi Mai Zurfi, Dakta Yusuf Ibrahim, Shugaban Sashen Ƙididdigar Alƙaluma na Jihar Kano, Farfesa Aliyu Isa Aliyu da Mashawarci na Musamman a Fannin Ƙirƙire-ƙirƙire, Dakta Bashir Muzakkir da sauran su.

Gwamnan ya ce, “Bari na bayyana cewa shi wannan shirin tallafin gurbin karatu waje, madugun mu Sanata Rabi’u Kwankwaso ne ya ƙirƙiro shi.”

Ya ce Kwankwaso sai da ya ɗauki nauyin rukuni-rukunin ɗalibai har rukuni uku zuwa ƙasashe 16 daban-daban.

“Wannan ƙoƙari ya sa an samu nasarar samar da daktoci, masu digiri na biyu da dubban ƙwararrun likitoci, injiniyoyi, matuƙa jirgin sama da gwanayen ayyukan harkokin jiragen ruwa da sauran su.

A jawabin sa tun da farko, Kwankwaso ya gode wa wannan gwamnati ta Abba Kabir, ganin yadda ta ci gaba da ayyukan alherin da ta fara a lokacin ya na Gwamnan Kano.

Ya ja kunnen ɗaliban su kasance masu ɗa’a kuma jakadun Kano da Najeriya nagari a duk inda suka samu kan su.

Ɗaliban da dama sun gode wa Gwamnatin Kano, Gwamna Abba da kuma Kwankwaso.

Kafin tashin su sai da Gwamna Abba Kabir ya damƙa wa kowa kuɗaɗen alawus ɗin sa na daloli a hannu, aka kira su taron dina a Gidan Gwamnati, sannan kuma Gwamna da Kwankwaso suka raka su har cikin jirgi.

Abba da Kwankwaso ba su bar filin jirgin Malam Aminu Kano ba, sai da suka ga tashin jirgin da ya ɗauki ɗaliban.

Ko kunji Dadi wannan abu da Gwamnan yayi?



Post a Comment

0 Comments