TOP HAUSA NOVELS atOptions = { 'key' : '20e08520dad54dbf6d9e963271

MATSIN RAYUWA DA AKE CIKI NA WUCIN GADINE CEWAR SHUGABAN NIGERIA TINIBU

Najeriya, Bola Ahmed Tinubu ya ce gwmnatinsa na gudanar da tsare-tsare da manufofi da nufin samar wa 'yan ƙasar ci gaba mai ɗorewa Tinubu na wannan jawabi ne a lokacin da wakilan ƙungiyar Musulmi ta kudu maso yammacin ƙasar suka kai masa ziyara ranar Juma'a a fadarsa da ke Villa, kamar yadda Jaridar Daily Trust ta ruwaito. Shugaban ƙasar ya ce ƙasar na buƙatar sadaukarwa domin samun ci gaba. “Abu ne da ya shafi makomarmu. dole ne mu samar wa kanmu makoma mai kyau. Allah ba zai ɗora mana abin da ba za mu iya ba. Allah na da dalilinsa na kawo mu wannna matsayi, Abubuwa na ƙara tsananta, amma da yardarsa (Allah), za su yi sauƙi"". Tinubu ya kuma kare matakinsa na cire tallafin man fetur da cewa ya yi hakan ne domin tseratar da ƙasar daga durƙushewa. "Mun kwashe kimanin shekara 40 muna ta ƙoƙarin kauce wa matakin (cire tallafin mai). Za mu sha wahalar matakin a yanzu, to amma domin tseratar da ƙasarmu daga durƙushewa, ya zama wajibi mu cire tallafin mai". “A tarihin ƙasashen da suka ci gaba, babban abin da ya kawo musu ci gaban, shi ne ɗaukar matakai masu tsanani da shugabanninsu suka yi a lokacin da ya dace kan dalilan da suka dace''. Shugaban ƙasar ya ce matsalolin da ƙasar ke fuskanta a yanzu na wucin-gadi ne, inda ya tabbatar wa 'yan ƙasar cewa daɗi na zuwa a gaba. “Za mu yi bakin ƙoƙarinmu, kuma tattalin arzikinmu zai bunƙasa domin ci gaban 'yan ƙasarmu, ina da tabbaci kan haka, za mu yi aiki don tabbatar da haka", in Tinubu.

Post a Comment

0 Comments