TOP HAUSA NOVELS atOptions = { 'key' : '20e08520dad54dbf6d9e963271

Yan Sanda Da Sojoji Sun Ceto Mutane Hudu Da Aka Yi Garkuwa Da Su A Katsina

 






Rundunar ‘yan sandan jihar Katsina ta bayyana cewa an ceto mutane hudu da aka yi garkuwa da su a karamar hukumar Dandume tare da hadin gwiwar sojoji a ranar Asabar.

Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar, ASP Abubakar Sadiq-Aliyu, wanda ya bayyana haka ga manema labarai, ya ce an samu nasarar ceto mutanen ne a lokacin da suke sintiri na yau da kullum a kewayen kauyen Dankolo.

Ya ce, “A kokarin tabbatar da tsaron rayuka da dukiyoyi, ‘yan sanda tare da hadin gwiwar sojoji sun ceto wasu mutane hudu da aka yi garkuwa da su a wurare daban-daban a jihar.

Kakakin Yansandan ya kara da cewa, an yi wa wadanda lamarin ya rutsa da su gwajin lafiya domin tabbatar da lafiyarsu, kuma an miƙa su ga iyalansu

Post a Comment

0 Comments